You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min tea, ""Zahrah kin gudu a hannun gayen nan ko?"""

"""Eh zuzu!"" Na fadi haka, ina kiranta da Zuzu saboda jin dadin sunan, Zulaihah ta girme ni, don kusan sa'ar Munaisah ce, a ™alla zasu kai shekaru ashirin a duniya."

"""Zahra'u! Ina kara baki shawara kada ki zama bolar da kowa zai zuba shararshi akai."" Na gode na sha tea din kaWan,"

"sannan ta shirya ya kwashi kayan mu kala uku nata uku nawa uku. Muka fito tana rike da hannuna. Sai lokacin na ga jini yana zuba. ""Zuzu mutuwa zan yi?"" Na tambayeta, Addah ta fito ta sha kwalliya kamar wata yar tsanar roba, domin bakin nan har da jan baki,ta kalle ni ""za a koma asibitin ne?"" Gyada kai nayi, murmushi tayi sannan ta ce mana.""tow ita Zulaihah da zata bi ki can, ta manta tana da kwastamomi ne?"""

"""Zan tura miki dubu talatin ta account Winki!"" Kallonmu tayi kafin ta ce mana, ""Anya Yaran nan baku cin junanku? Wannan shakuwar tayi yawa ku gaya min gaskiya me yasa kuke zartas da hukuncin junanku. Idan kuna cin juna ne na sani domin a bani kasona domin banga amfanin tara munafukai irinku, kuna cutata ba. """

"""Yanzu addah don Allah wani yace miki, muna soyayyar jinsi ba zaki ji wani iri b?""wani tsalle tayi ta koma gefe can,""Kambu wallahi bani jin kome,kawai kudin daki zaki kara min na saka a muku shamaki da gulmar su Munaisah an kashe boss."""

"""Allah ya shirya ki Adda"" inji Zulaihah muka fita, har waje ta biyo mu, muka tari taxi muka gaya mishi inda zai kai"

"mu,kamar ba zai amince ba, sai kuma ya ce muje. Haka muka tafi har zuwa asibitin,kamar zan yi hauka domin kuwa ciwon ya taso ni a gaba. Haka muka isa har asibitin aka karbi katin, muka shiga."

Dr Umaima.

"Tun dawowarsu bata wuce gida ba, domin yadda Zahrah ta arta aguje tasan sai an dawo da ita dole, don haka bata da wani aiki amma ta kasa tafiya, tana ji kamar akwai abinda take son ta sani dangane da yarinyar, tana asibitin har awa biyu. Aranta tana jin kamar ta tafi, amma ˜wa™walwarta na gaya mata zata zo, haka ta cigaba da tsayuwa har minti ashirin ya wuce idanunta yana kan wayar,minti takwas yazo zai wuce shima daidai babban hannu ya daura kan minti na tara, siririn hannu ya wuce kan taran kenan,taji dirin motarsu, ajiyar zuciya ta sauke tana tsaye idanunta na kan kofar."

"....... Dakyar nake jan numfashi, domin zuwa yanzu na fahimci akwai dalilin da yasa jinin yake zuba, muna isa har"

"bakin kofar Emergency,ya tsaya Zuzu ta fito da ni. Muka shiga cikin asibitin."

"""Kun dawo?"" Ta tambaye mu! ""Eh Aunty, gashi jini yana ta zuba."""

"""Gudun da ta arta lokacin da muka isa ya haifar mata da zubda jinin"" ta fada tana rike ni na kwanta, Zuzu ta fita tare da biyan mai motar kuWinshi, ta dawo anan aka wuce wani daki dani, Zuzu tana zaune cikin tararradin mai zai faru."

***

"Addah tana fita bata tsaya ko ina ba, sai gidan Malam Sammani wani dan arewa ne,da yake harkan malunta irin masu duban nan, kallonta yayi yana shafa gemunshi. ""Zahra'u!"" Ya kara zana sunanta a kasa, ya saki ™asaitacciyar murmushi.""yarinyar nan yar baiwa ce kamar yadda Yarki ta ce, tauraronta karfin tsiya ne da shi, domin ta gaji haka daga Uwarta,da kin barta da dan uwanki da ba karamin arziki zai yi ba, sai dai ™addarar da kika kirkira da hannunki ya shiga tsakaninku da arziki, sai dai kici a jikin yarsu. Wato yarinyar nan jiya tauraronta ya hadu da wani raunannen tauraro, kuma Qaddarar da ba a san me zata haifar ba gobe ta shata tsakaninsu. Ban san me zai faru gobe ba, amma tafiyar ™addara tana nan da riskanku baki Waya. Idan kina son zaman lafiya ki bi yarinyar nan zaki huta kowa zai huta, bayan ita babu wacce zata iya mallakar arziki domin duk inda ta shiga sai ta had'a arziki."""

"""Allah gafarta Malam, ina da mafarki akan Zulaihah ita fa?"""

"Share ™asar yayi sannan ya rubuta sunan Zulaihah. Dariya yayi sannan ya ce mata. ""kamar yadda baiwa take a gaban Uwar gijiyarta haka Yarki take a gabanta"""

"""Don Allah Malam duba min na sauran. "" Murmushi yayi ya ce mata. ""Sunansu;"""

"""Munaisah!"" Rubuta sunanta yayi yasannan ya kalli Addah. ""Lallai kin hada masifar da ba zaki iya kashe ta ba, sai Allah babu kome a tare da ita sai bautar da zaku mata, amma.kuma zaki dan huta a jikinta kamar yadda kike hutawa a yanzu."""

"""Ummi fa?"""

"Rubuta itama sunanta yayi, sannan ya ce mata. ""Ita wannan igiyar ruwa ce, duk inda ruwa ya jata bi zata yi. "" ""Malam kace Zahrah zata. "" Rubuta sunan Zahrah yayi ya cika tiren, yana murmushi ya ce mata. ""Har ki mutu ba"

"zaki daina cin arzikin ta ba"""

"""Malam kana nufin babu wanda zai."""

"Hannunshi ya kai kirjinshi, ""na gama aikina indai ba so kike nai miki karya ba,kuma duk inda zaki je babu wanda zai gaya miki wani abun da ya wuce haka, idan aka gaya miki akasin haka karya aka miki wallahi."""

"Kudi ta ajiye mishi, ya girgiza kai ya ce mata.""Ni yau bani bukatar kudi, can kasa nake son na rage gajiyata."" Wani irin malolon bakinciki ne ya cika Addah, ta ce mishi ""tow Malam"" haka ta cire kayanta, suka kwanta a dan farin buzun malam na aiki, bayan ya rufe kofar, ai kuwa yazo bai wani mata wasa ko wani abu ba,. malam kamar jaki haka ya zo mata, yana sama da kasa akanta, surfeta yake yana zuba mata rashin mutunci, ta hanyar saduwa da ita kamar wata bebin roba, Addah ta ci azaba a hannun malam kamar ba gobe."

***

Operation Anaconda plan.

"Suna isa bakin ruwa suka shiga cikin jirgin, kowa ya ajiye kayanshi ban da Captain da ya nufi inda matukar jirgin suke, ya fito da Map na inda zasu ya shimfida akan wani table."

"""Likitan soja, Captain akan ruwa."""

"Murmushi yayi ya cigaba da warware taswirar, sannan ya fito ya sarawa Commodore Magaji Abba Chindo ya ce mishi. ""Ko zaka zo ka duba taswirar!"". Kafin ya rufe baki Magaji Abba Chindo ya kai mishi naushi, da sauri ya rike hannunshi."

"""Please Sir kazo ka duba abinda na ce maka."" ""Idan naki fa """

"""Shi kenan!"" Ya fada yana wucewa, ""Guys idan Captain ya dake ni zan bishi sau da kafa, idan kuma na dake shi,kada na kuma ganinshi ya hauro kan ruwa sannan zai zama driver na."""

"""Commodore!!!!"" Wasu daga cikin sojojin suka fara kiran sunayensu, wasu na cewa. ""Captain!!!"" ""Look ni bana son faWa!"""

"""Sai kayi sai kayi!!!"""

"Dama a cikin sojojin akwai waWanda suke bayan Commodore, wasu kuma suna bayan Captain, na farko yana da matu™ar kamun kai,.yana da nutsuwa da sanin ya kamata, sannan duk inda suka shiga lokacin sallah yana yi zai gabatar da sallah."

"Babu ruwanshi da hassada ko kyashi,gashi mutum ne mai yawan alkhairi da kyauta, bai da girman kai baki"

"Waya, haka Allah yayi shi, abu daya mutane suka sani shi ne, akwai kauna da amana a tsakaninshi da duhu."

"""Indai kai ba shege bane, ka zo ka gwada mana mazantakarka, matukar ba cin kanka kake a cikin duhun nan ba, ka"

"zo nan, ka gaya mana shin hannunka domin aiki da sarrafa bindiga take zaune, idan kuma domin mulmula doguwar tsokar da take tsakanin cinyoyinka.."""

"Dariya aka kwashe ban da sauran sojojin da suke tare da Captain, suna masifar jin haushin Commodore,amma babu yadda suka iya, sai dai a wannan karon alamar dai maganar tayi tasiri....."

#thedambuje

"[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*ZINARIYAR MACE *

"*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*"

Na gyaran nono. Na sanyi.

Dilka tare da hadin sabulu.

Duk Wani nau'in maganin mata.

"Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani."

*08089965176*

*07084653262*

*004*

*Captain*

"Juyawa yayi ya kalli Magaji Abba Chindo da yake mishi dariya, idan ya sake suka yi faWa. Tow yau ba zai iya samun"

"nutsuwa ba, don haka ya saki dan ™aramin murmushi ya ce mishi. ""Sai a ka yi rashin dace, ni mata-maza, bana haWa jikina da yan maza, musamman waWanda basu dauki aikata sabo illa ba."" Daga haka ya juya abinshi, shiru wurin ya Wauka, abin ya bawa Magaji Abba Chindo dariya, amma da ya nutsu sai ya fahimci da gaske Captain magana ya gaya mishi. Mikewa yayi zuwa ciki jirgin don da suna daga waje ne."

"""Kai magana ka gaya min?"""

Murmushi Captain ya yi sannan ya ce mishi.

"""Kaga ni bana son tashin hankali, kayi hakuri ba magana na gaya maka ba."" Kurawa juna ido suka yi, sannan ya fauce Map din hannun Captain ya yaga gida biyu."

"""Naga yadda...!"" Kafin ya rufe baki Captain ya zabga mishi marin da sai da ya daina gani. D'ago shi yayi ya ce mishi. ""Kada ka sake wani yaji wannan labarin domin zai maka dariya, kada ka kuma aikata abin da kayi. Ni idan kaci zarafina zan yafe maka. Amma idan ka taba aikina zan baka sakamakon da yafi haka. "" Wato marin nan, ya shiga Magaji domin kuwa hakorin shi na wannan bangaren har yana girgiza."

"Sauran matuka jirgin duk hankalinsu na kan aikinsu, babu ruwan su kuma haka da Captain yayi shi ne zaman lafiya, don haka, A hankali ya juya tare da fita daga dakin, Captain ya gyara takardan, bayan Mr Oke ya mika mishi salatep, ya gyara suna hira sama sama."

"Lokacin sallah yana yi suka fita baki Waya, musamman Domin a yi sallah wanda Captain ne ya jasu, sannan aka"

"Wauko abinci da wasu daga cikin sojojin suka dafa, mika mishi aka yi ya kalli agogon ya ce musu. "" Na koshi!"" Haka suka kyale shi, ya tashi tare da Waukar abin hango wasu abubuwan, yana me duba gabansu."

"Komawa ciki yayi ya dauki wata waya,ya shiga duba sakon."

"_Sir mutanen nan basa gudanar da kome sai dare yayi,hankalin kowa ya koma tsoron dare. Kada ku shigo da rana domin zasu gudu_ mai da wayar yayi ya ajiye, taya zai yi facing Commodore? Haka ya daure ya fita ya zauna a gabanshi."

"""Yallabai!"" Cikin wani irin yanayi Commodore yake kallon Captain kamar ya shake dan banza amma yanzu ya fahimci gayen ya wuce tunaninshi. Mari daya yayi mishi, hakorinshi yake girgiza ina kuma da sun daku, tow kuwa kareraya shi zai yi ya tara dan iska a gefe kenan? ""Meye?"" ""Inda zamu shiga basa kome da rana, sai dare."""

"""Tow me kake so nayi?"" Ya faWa yana nad'e hannunshi a kirji. ""Ina ga a tsaya nan, sai mu duba nisan kafar ruwan, idan nisan ba yawa sai muyi musu shigar dare."""

"""A matsayinka na wa?"" A hankali yayi kasa da kanshi kafin ya ce. ""A matsayina na soja, kuma shugaban rukunin sojojin da suke aikin sirri, mataimakin ka. Na bada shawara kuma na fita."" Ya faWa yana me mikewa daga gaban Magaji ya nufi dakin iko. Jikin Magaji ne yayi sanyi, kudirinshi shine a kashe Captain a wannan lokacin, kuma ba zai fasa ba."

"Don haka ya mike tare da fito da sabon tsarin da ya sauya, a ka'idar zuwansu nan. Shi ne shi zai jagoranci wasu daga cikin Yaranshi su isa har inda ake zaton abin, amma son zuciya irin nashi, sai ya kalli Captain ya ce mishi. ""Kai da team dinka zaku tafi inda ake badakalar, ni da team dina zamu zauna a nan. Domin ba za a rasa wanda zai iya kawo farmaki ba, idan kuma ba a samu ba kunyi nasara, ga fireworks sai ku sanar da mu."""

"""Amma Sir wannan abin babu tsari, taya kana shugaban sojojin kuma kace Captain zai jagoranci wasu daga cikin mu, kuma mutumin da bai tab'a rike bindiga ba, aikinshi kawai sanin meke faruwa."""

"""Shi namiji ne, idan har ya cika namiji ya jagorancin tafiyar."""

"""Na amince "" ya faWa tare da ware wasu daga team Winshi. ""Zamu tafi in sha Allah hakkina ne, na bawa rayuwarku kariya,ku yarda da ni in sha Allah zan mai daku cikin iyalanku lafiya."""

"""Mun amince "" suka fada, sannan ya shiga musu bayani tare da tara su a cikin wurin tukin jirgin, yana nuna musu yadda tafiyar zata kasance."

*** Addah

"Kallon Addah mutumin yayi ya ce mata. ""Ki kula da zuciyarki kada ki aikata abin da zai dame ki, ita yarinyar babu"

"ruwanta."" Kasa magana tayi can ta daure ta ce mishi."

"""Yanzu haka 'yata zata kasance? Babu wani cigaban rayuwa sai ta karuwanci? Karshenta."""

"""Ba farinciki da nutsuwa ake nima ba?"" Ya tambayeta yana gyara zaman wandonshi, domin yana matukar jin dadi Adda tana cikin mata na musamman da yake mu'amala da su. Murmushi yayi yana faWin, "" A gaskiya bakya tsufa "" dauke kai tayi ta gyara jikinta, sannan ta dauki jakarta ta bar dakin, tana fita waje ta sauke ajiyar zuciya, tana jin wata iriyar tsanar Zahra. Duk inda zata aiki akan zahrah sai ta bada kanta bata san me yasa haka ba, yarinyar ta shiga ruyuwarta ita da take tutiyar ta samu hannun jari, ashe bala'i ta daukowa kanta."

"Hadiye bakinciki tayi ta shiga kasuwa tayi sayayya. Sannan ta dawo gida ta mikawa Ummi wata leda, ta ce"

"mata. ""Ki girka mata wake da hantar mu kai mata asibiti!"" ""Tow ai basu bamu kati ba"" ""eh idan kuka isa ku kira Zulaihah."""

"""Hmmm!"" Inji Munaisah, ta cigaba da gyaran farcenta, domin tana son zuwa saloon a mata fixing farce. ""ina son zuwa saloon dai, domin farce na da kaina yayi datti."" Da Ace Munaisah ta san halin da Adda take ciki ba zata fara fadar ita zata saloon ba, dauke idanun tai kanta ta wuce Wakinta. Sai da tayi wanka ta cire roban condom din mata ta wurga cikin masai din, sannan ta wanke gabanta tass. Sannan ta gyara ta fito, Adda ta san darajar gyaran jiki, shi yasa take gyara jikinta. Duk da abin da take yi be dace ba, amma kuma ita ta dauki haka a matsayin wata hanya ta samun kudi cikin sauki,"

"Aiki take amma a zahirin gaskiya gangan jikinta ke jagorantar aikin, amma zuciyarta da kwakwalwarta basa bata"

"haWin kai, baki daya ta kashe rayuwarta domin yau ta samu riba, tana son ace yau ta zama wata hamshakiya, amma wani ikon Allah rayuwarta da na Yarta ne a lalace, wanda take ganin ta maida ita baya an gaya mata ba zata iya kome da ™addarar ta ba, ""hmmm!"" Ta fada tana kallon tilin kayan da ta sauke daga wardrobe Winta, tana mamakin me yasa"

meta da wannan aikin? Lallai ya kamata ta mike wannan lamarin sai kace an saka mata hannu. Jin muryar yan matan

da suke mata aikin abinci suka shigo gidan yasakata mikewa

"""Ina Zahrah take?"" Jin murya Shamsiyah yasata fitowa daga cikin Wakinta tana kallonsu. ""Tana asibiti ba lafiya."" Daga"

"haka ta nuna musu kome da kome da ta sayo, sannan ta wuce Wakinta ta kwashe kayan. Wurin karfe daya na rana Zulaihah ta kirata. ""Wai Addah ba za a kawo mana abinci ba ne?"" Runtse idanuwan ta tayi kafin ta lailayo wata uwar ashar ta maka mata, ""babban ,,, ubannki! Ba za a kawo ba kina da abinda zaki fada ne? Shegiya mara mutunci."""

"""Addah dubu dari aka ba™i, idan ba zaki d'aga kafa ba, ki dawo min da kudin mu maza, dawo da saba'in xan baki talatin din."""

"Kamar ta fasa ihu tayi shiru, kafin ta ce mata. ""Bana son iskanci, nace ba za a kawo muku ba ne? An jima za a kawo muku."" Ta fada a fusace, ""Adda ihu kike mana fa?"" Inji Zulaihah. ""Yanzu don Allah na ce muku ba zan kawo ba ne, ku yi hakuri me da me kuke bukata?"""

"""Yawwa a hada mana da kofi biyu, kayan tea flask da kuma special abinci dare da rana. A kula da mu kamar baki Hajiya Addah."""

"""Shi kenan za a kawo muku."" Wannan shine asalin dole kanwar naki. Haka suka kashe wayar, kowa najin babu dad'i ita Addah tana ganin kamar Zulaihah bata kyauta mata, ita kuma Zulaihah tana haka ne domin huce takaicin Mahaifiyarta."

***

*Zahrah*

"Ruwa aka sanya min, bayan an kara duba min ciwon, shi ne aka fito dani, yanzu dai sun saka min ruwa da wasu allurai. Ina jin wayar Zulaihah da Addah, a hankali barci yayi gaba da ni. Ban farka ba, sai wurin karfe uku, na samu Munaisah da Ummi suna hira sama-sama. Zulaihah bata dakin, kallonsu nayi kafin na ce musu. ""Kunzo ne?"" Domin ban kawo a raina zasu zo ba. Kallona suka yi kafin suka ce min. ""Eh amma ke taya aka yi ana yin abun arziki ta kasa ke taya kika kare da gefen cikinki?"" Shiru nayi ban ce musu kome ba, shigowar Zulaihah da Dr Umaima yasa ni kallonsu ina kakaro murmushi. Ganin su Ummi da Munaisah sai Dr ta kara yarda wani lokaci halittar kyau da hasken fata bala'i ne, domin kuwa Munaisah hancinta da huji, kunnenta kuwa har saman kunnen a makale suke da barima har da na gwal."

"Sannan ta kara kallonsu ganin yadda suke wani, iyayi yasa ta sha jinin jikinta waWannan yan matan sun fini wayewa da gogewa a bariki, ni din kamar sabuwar yankar rake ce, shi yasa har nake gadon asibiti tow ko da ta koma gida ta ji kaninta yana bata labarin ai gida gida, Magaji Abba Chindo ya sa aka yi ta niman wata yarinya da ya dauko daga cikin gari. Kallona tayi tana mamakin anya ba ni ba ce? Duba min ciwon tayi tana faWin. ""Kin yi sallah kuwa?"" Girgiza kai nayi. ""me yasa kike wasa da sallah."". Kura mata idanu nayi kafin na bude baki ta daura da cewa. ""Sallah tana kare mutum daga aikata alfasha, idan har kika kiyayye sallah, a duniyar nan babu wanda ya isa ya cutar da ke, sai dai abin da Allah ya rubuta xai same ki."""

"""Na gode zan kula, bana wasa da sallah amma daga faruwar wannan al'amarin nayi wasa da sallah har subhi da zuhur sun wuce ni"""

"Murmushi tayi sannan ta juya tana kallon Zulaihah. ""Idan kika hada mata tea, tayi sallah ko a zaune ne sai ta sha rabin kofi."""

"""Abinci fa, domin gashi an kawo."" ""Sai jibi saboda tumbin ta ya tabu, tasha tea din idan babu abinda ya faru, zata iya cin abincin."""

"""Shi kenan"" ta faWa tana hada tea din, sannan ta fita daga cikin Wakin, haka Zulaihah ta rike ni har ban daki ta taimaka min nayi alola, sannan na dawo dakin na gabatar da subhi da zuhur, ina idarwa na amshi tea na sha, ciwon ciki ne ya sako ni gaba, kamar zan mutu kiranta Zuzu tayi suka shigo dakin. Wuce dani wurin scanning aka yi, aka min anan suka ga Winkin cikin bai yi da kyau ba, akwai bu™atar a sake min wani aikin yau. Alluran rage zafi tayi min, sannan suka wuce aka fara shirin, a lokacin Adda ta kira su Ummi tana faWa akan me basu dawo ba, suka gaya mata ai aikin aka kuma shiga dani, babu shiri Addah ta nufo asibitin, domin abin ya bata tsoro kada garin niman duniyarta, na rasa rayuwata. Bata san amsar da zata bawa Shad'ari ba."

"Haka kuwa ta iso a gigice, tana tsaye har aka fito dani. A galabaice jikinta yayi matukar sanyi, ita tsoro take ji"

"kada na mutu, haka suka bi ni har dakina, ""Likita ya aikin?"" ""In sha Allah an dace, dama na farko munyi shi tare da bin raunin ne, amma na yanzu mun yi shi ne da bin duk inda yake ciwon."""

"""Hmm! Kuma nawa ake bukata? Domin akwai kudi a hannunsu."" Kura mata idanu Umaima tayi kafin ta ce mata. ""Allah sarki, ai Captain ya biya kome babu abinda ake bukata duk kudin da za a cire a insurance Winshi za a cira."""

"""Kai madalla."""

"Murmushi Addah ta sake tana faWin. ""Don Allah ko zaki taya ni amsar kudin hannunsu, ki ce musu akwai wani abu da"

"za a saya."" ""Hajiya anya kece kika haifi yaran nan?"" ""Kai haba daya Kyakyawar me dogon hanci da dogon gashi, ita ce na haifa. Ita kuma mara lafiyar da wancan me doguwar riga ruwan toka ubansu daya kanina ya haife su, ita kuma daya fara tas din can itama yar Kani nace, Zahrah ce ta dauki duhun fatar Uwarta ai kin gansu nan."" Gaba Doctor Umaima tayi ta barta a nan tana surutu, haka kawai take jin Addah bata mata ba, Indai zaka kawo Yara ka daura su kan wani yanayi mara daWi, meye ribarta? Itama Adda dakin da aka kwantar dani ta shigo, tana tsaye sai yamutsa fuska take tana faWin. ""Ita dai wannan shegiyar ta san hanyar b'adda kudi loko-loko, ban da iskanci da wulakancin taya zaki kare a gadon asibiti akan ciwon da bai taka kara ya karya ba, mtsew."" Ta ja tsaki tana isa bakin gadon yarinyar nan yar bala'i, a ranta domin kuwa ta ga yadda ran kowa yake a b'ace idan ta cika mita kan yanayin da ake ciki."

"""Tow ai ku muje ko, tunda an yi aikin a sa'a"" ta fada tana barin dakin, haka suka bi bayanta ban da Zulaihah"

"da take zaune, ta saka ni a gaba tana kuka. ""Ya Allah kai ka jarabce mu Ubangiji ka tashi kafadar Zahrah."" Ta cigaba da kukanta, har aka yi sallar la'asar tayi sannan ta koma ta zauna. Shigowa Dr Umaima tayi tana faWin. ""Kuka ya isa haka, ki ci abinci."""

"""Ba zan iya ci ba, bayan Zahrah tana kwance."""

"Shiru suka yi, sannan Dr ta ce mata. ""Matar nan Mamarki ce?"" Rintse idanunta tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi a jikinta, don dai Allah ya ™addara zata zo a tsagin addah ne amma da ba zata tab'a yarda a ce Addah mahaifiyarta ce ba."

"""Eh Mamata ce."""

"""Allah sarki naga kuna kama sosai."""

"""Eh haka mutane ke faWa muna kama da Adda, shi yasa duk lokacin da wani ya ganni sai ya tambayeta ko ya tambaye ni."""

"Daga haka tayi shiru itama Dr Umaima bata zake sai ta san kome akanta ba,

Please Login or Register in order to submit comment