You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

NUMBER 08130269641*

Laces ATAMFOFI SHADODDI

Materials Kayan yara Veils Huluna. etc

"[3/7, 10:49 AM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*031*

"""Ni a sanina ban ki shi ba, tunda nice na kawo shi nace ina son shi, ashe don haka ya faru uziri ya dace ayi min ba fushi da b'acin rai ba."" Ta fada tana kuka sannan ta cigaba da cewa. ""Na amshi kuskure na."" Juyawa Zaytoonah tayi ta koma gareta, ta zauna tana me dora mata Baby Zahra a saman cinyarta.""Ammy ki daina kuka, don Allah."" Ta fada tana jan hancinta. ""Dole nayi kuka, yar uwarki ta rasu baku gana ba, mahaifinku ma haka duk laifina ne."""

"""Bana jin Didi ta rasu, baffanmu kan jikina ya bani baya raye, amma Didi fa ina jinta a raina sosai da"

"sosai."""

"take."""

"Rungume su tayi tana faWin, ""duk inda take, tana cikin kariyar Ubangiji, Allah zai shiga lamarinta a ko ina"

"Wato idan har aka samu irin ahalin Sheikh Aliyu Wodabbe, zai yi wahala wata fitina ta sauko ba tare da an"

"samu warakar shi ba, tun da suka ji labarin mutuwar Baban Zaytoonah, hankalin kowa ya tashi haka yasa"

"Zaytoonah rikice musu, tare da nisanta kanta da Mahaifinta, duk da kowa yaso mata bayani amma taki fahimta. Haka yasa taje har gaban Sheikh Aliyu Wodabbe, ta ce ita ya mata lamuni zata bar gidan ta tafi neman danginta da suka rage a duniya. Shine ya kira Aminatu da Yafendo da Sumeye, Zaytoonah tana zaune a wurin."

"""Na kira ku ne, domin Zaytoon tana son ta tafi neman ahalinta."""

"Da sauri Ammynta ta d'ago kai tana kallonta cikin wani irin rawan jiki tace mata. ""Ba dai tafiya zaki yi ki bar ni ba?"" Girgiza kai tayi tana kara faWin. ""Kiyi hakuri nayi laifi wallahi nayi laifi, nasan nayi laifi tunda kike shirin gudu na, don Allah kiyi hakuri. Amma kada ki tafi kiyi hakuri na had'aki da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama."""

"Kwalla ne masu zafi suka shiga zubo mata, tana kallon yadda mahaifiyarta take kuka da dukkanin zuciyarta, mikewa tayi ta bar wurin, haka yasa Yafendo bin ta dakin. Kuka ta saka tana kara jin zafin Ammyn har Hamma tasa ya roke ta, duk shirin da suke da Hamma sai da ta mishi rashin mutunci, amma yanzu ta zauna tana mata wani kuka mara hujja. ""Idan kin shirya ki gaya min, akwai kanwata da muke Yayan mata a Yola, tana aure a can idan kika tafi zasu tayaki niman sauran danginki. Amma kafin nan bari na gaya miki wani abu. Da ace Allah bai nufa an ga Aminatu da wuri ba, ta wuce wani wurin da lalurar gushewar hankali ga kuma cikinki, tow kuwa ba makawa bamu san abinda zai faru ba, imma da tun lokacin kin mutu ke da ita, ki godewa Allah tunda har kika taso an tab'a miki gorin yar mahaukaciya? Tow hauka tuburan Aminatu tayi, da ta warke kuwa ko da wasa bata kaunar ka tambaye ta, bayanta ki godewa Allah da mari kika sha a duk lokacin da kika tambayi bayanta. Saka ran mahaifinki zai biyo sawunta yasa Malam dakatar da ita har na tsawon shekaru Domin tsakaninki da yar Uwarki, tazarar me yawa ce. Ba zance kiyi hakuri ba domin an zalunce ki, amma a matsayina na mahaifiyar Aminatu dole na kare mutuncinta da rayuwarta, tana kuka ne don ta rasa abubuwa masu muhimmanci a rayuwarta, sannan tana shirin rasa ki a karo na uku. Ke baki jin tsoron kukan da take yi wata rana yarki ta saka ki?"""

"Da sauri ta d'ago kai tana kallon yafendo bakinta yana rawa ta ce. ""Yafendo!"" ""Mahaifiya ce ita, bai dace a saka ta kuka har haka ba, hakan zai tab'a rayuwarta da lafiyarta."""

"Daga haka ta bar dakin, har ta kai bakin kofar ta ce. ""Ba fata nayi miki ba, kina da damar yin fushi da kuka da fada, da ihu amma ki sani itama an mata uzuri domin ba laifinta ba ne, haka Allah ya shirya lamarinshi da ace mutum yasan abinda goben shi zata bayar da zai gyara wanda yake ganin ya dace da shi, ki yi hakuri na baki hakuri ne a matsayina na mahaifiyar Aminatu. Ba a matsayin kakarki ba ki dauka a wani wurin aka miki kuskure to ina mai kara baki hakuri."" Daga haka ta bar dakin, tabbas Yafendo ta tsayawa yarta at least ta nunawa Jikarta itama tana son Yarta, ba zata sake damuwa ya cutar mata da Aminatu ba, kamar yadda tana ji tana gani aka hanata akan Yar uwar Aminatu."

"Wannan abubuwan yasa Zaytoonah, hakuri da mata uzuri, amma bakiWaya bata jin dadin rayuwarta. ""Ammyn ina son tafiya Nijar na cigaba da karatu a can!"" Ta fada tana kallon Ammynta. ""Indai haka zai saka ki farinciki na amince, zan kira Dadah na gaya mata, sai ki tafi can Allah yasa haka shine mafi alkhairi."""

"""Amin Ammyna, in sha Allah zan binciko mana inda Didi take."" Inji Zaytoonah. ""A'a kada ki wahalar da kanki, in sha Allah zata zo gare mu."" Cikin shashekar kuka ta ce mata. ""Muma dole mu neme ta, ba zamu jira sai tazo ba."" ""Hmmm kin dai ce tana raye ne, amma yadda nasan rigimar su da mutanen garin nan zai yi wahala idan bata mutu ba."""

"""Wallahi tana raye tana raye na rantse da Allah."" Haka suka yi ta kuka a tsakaninsu. Har bayan an sha ruwa Malam ya kirasu ya musu nasiha da addu'ar idan Zahra tana raye Allah ya bayyanata, idan ta mutu Allah ya mata rahama."""

"Haka suka yi ta addu'a, sannan suka tashi. Duk da dai zuciyoyinsu babu dad'i amma kuma haka bai"

"hana su sakin ransu ba, domin kuwa kowa yana jin ciwon abin da ya faru. Musamman Ammyn gani take kamar da wata a kasa, haka kawai ba zata samu lalurar gushewar hankali ba, sannan daga baya, taji kamar zata mutu idan aka tambaye ta, me ya faru ko ina mijinta yake."

"Wannan abin ya sakata cikin damuwa, bayan sunyi sahur, Ta kira Yayarta ta gaya mata, cikin farinciki da murna ta ce tazo tana bukatar abokiyar hira. Sannan ta gaya mata dalilin zuwan Zaytoonah karatu zata yi, Itama ta karfafa mata gwiwar haka, dake Allah ya taimaka dukkansu suna da abun yi domin itama Aminatu koyarwa take a nan Jami'ar Cameroon."

"- South Africa. Sai da aka kai ruwa rana, kafin suka bashi hutu tun zuwan shi bai matsa ko nan da can ba, yana makale da aikinsa, sannan da ya nemi hutu kin bashi suka yi, sai da ya koma ya rubuta musu ajiye aiki. Da shugabansu ya gani a fusace ya yaga takardar. ""kana da hankali kuwa? Kasan yadda muke alfahari da kai da zaka so ajiye aikinka?"" Kusan soja da bala'i da masifa da ihu, shi dai bai ce kome ba yayi shiru yana sauraren Commander Winsu. Har ya gama sannan ya dauko wata takarda, ya rubuta mishi an bashi hutun sati biyu. ""Sir mahaifiyata ba zata fahimce ni ba, sannan ina son a bani koda wata daya ne, nasan is too hard na samu wannan kwanakin. Amma idan na ajiye aikin zata fahimci ita din abar girmamawa ce."" Dake Commander din Muslimi ne kuma dan arewancin Nijeriya, murmushi yayi ya ce mishi. ""Abdul Majid Mamman Ba'are, nasan waye kai Chairman guda da yake gudun matsayinsa. Sai dai an haife ka ne domin ka zama soja, ba wai kayi aiki da sojoji ba, zan baka wata gudan amma ka sani can kujerar da kake gudu, zata bibiye ka a duk inda kake matukar kana raye. Kasa yayi da kanshi yana kallon takalminshi da bai daura igiyar ba, ""mahaifiyarka tana son ka rike matsayinka ne, domin hankalinta zai fi kwanciya. Sai dai ba abu me sauki bane a wurinka. Kayi imani da hawa saman teku domin aikinka, ka dauki kamfanin a matsayin teku ne, ta gaya min kome akanka da kuma kamfanoninku."""

"Bai ce mishi uffan ba, yasan halin shi sarai ko abokan aikinshi ba karamin mita suke akan wannan halin nashi na rashin magana ba, har kawo ™ararshi suke amma babu abinda ya sauya, wani irin murdadden hali ne dashi, yaki sabo da kowa aikin shi kawai yake baya kula kowa baya harka da kowa baya shiga harkar kowa, ina ka fito aiki ina zaka aiki. Haka yasa ko irin yan matan nan babu me shiga sabgar shi, domin sun tabbatar da cewa shi din ba daidai ba ne, kuma bai da lokacin mace."

"""Shi kenan Allah ya tsare, ka dawo lafiya."""

"Salute yayi sannan ya dauki takardar, ya nufi hanyar waje, yana kallon agogon hannunshi. Sam bai dauki rayuwarshi da zafi ko fadi ba, asalima ya ajiye kanshi inda yake ganin nan Allah ya ajiye shi, bai tab'a nuna fad'in rai ko kuma nuna cewa shi din wani ba ne, yasan yana da dukiya me yawan gaske, amma haka bai tab'a damunshi ba, asalima shi yafi saka kanshi a matsayin kananan mutanen da suka taso cikin talauci da wahalar rayuwa."

"Wannan yasa baya jin girman kai ko wani abu, meye a rayuwar da wata rana mutuwa zaka yi, sannan magana ce babu wanda ya isa saka.shi, shi bai saka kowa lallai dole a kula shi ba, kuma baya jin lallai dole sai yayi magana duk wanda yaji haushi to ya daukarwa kanshi dala ba gammo ne."

"Daga headquarter Winsu, airport ya wuce dama da shirinsa ya fito, ba zai sake a kai azumi na biyar bai sha ruwa a gaban Hajiya ba, domin yana tsoron Allah yana tsoron fushin Hajiya, don haka yana zuwa bai samu jirgin nijar ba, sai"

"na Algers ya samu, bai wani b'ata lokaci ba ya biya yana jin yana isa nan da awa biyu, zai samu na nijar tunda yasan basu rabuwa da masu shiga da fita a kasar, haka yasa shi bawa zuciyarshi hakan."

"Bayan wani lokaci jirginsu ya tashi, bayan awa biyu suka sauka a Algers, yana zaune a inda zasu jira jirgin nijar. Wata Kyakyawar budurwa, tazo ta zauna a wurin murya kasa-kasa take faWin. ""Ni zanzo ne kawai amma ba wai don ina da ra'ayin haka ba, don bana kaunar abinda ya haWa ni da BA'ARE family."" Da wutsiyar idanu ya kalleta. Tab'e baki yayi tare da kauda kanshi, ashe akwai masu tsanar BA'ARE family ba shi daya ba ne. Kiran fasinjoji nijar yasa suka mike baki daya, wani abin mamaki shine sit dinsu kusan wuri guda, zama tayi tana faWin. ""Mame sai nazo, ni dai bana son zuwa kika kira ni, Allah ya gani ba zan sauka ba, meye a cikin wannan gidn ban da masifa da hakkin Hajiyarsu Aryan kada ki biyewa Appa domin zai kai ki ya baro ki ne, nafiki sanin waye shi. """

"Ta kashe wayar tana jan tsaki, kauda kai yayi tare da saka facemask Winshi, baya jin zai iya hayaniyar yarinyar nan, ban da yasayi kujerar da ya koma VIP. Wuraren biyar da rabi suka isa nijar, bayan sun isa ne suka yi ta fitowa. Aryan da yazo daukar Majid din ya hangota. ""Maisarah!"" Tawowa wurinshi tayi, tana murmushi. ""Ya Aryan kazo dauka ta ne?"" Watsa mata harara yayi yana faWin. ""Hammayo dai!"" Ya nuna mata shi, da yake bayanta. A hankali ta juya tana kallonshi baki sake. ""Dama tare muka zauna shine bai nuna min ya sanni ba?"""

"Murmushi Aryan yayi yana amsar jakar Majid. ""Barka da hanya, muje na ajiye ku baki daya."" Haka ta fito tana jan jakarta, shi sikagon ana jan nashi, yana isa wurin motar ya bude baya ya shiga, tsayawa tayi tana kallonshi. ""Shiga gaba!"" Haka ta shiga tana mamakin duk gaishe shi da Aryan yayi bai amsa ba, sai dai buga bayan shi da yayi, wannan"

"irin lifestyle din yana matukar burgeta, ta madubin gefenta take kallonshi, ya wani zauna like king yayi crossing leg,"

"hannunshi dukkan biyu ya baza su kamar wani wanda yake kan karagar mulki. He look like king . ""Ya Aryan!"" Ta kira sunanshi a hankali, ""hmm!"" Ya ce mata. ""Amma Hammayo yana da nasaba da sarauta ko?"" Gyara zaman madubin gaban yayi yana kallon Majid din da yayi wanann zaman, murmushi yayi yana faWin. ""Me kika gani Maisah?"""

"""Hmm! Zamanshi da halinshi."""

"""Masarautar Agadaz, itace babban tushen nasabarsa "" duk abinda suke fada yana jin su, kawai amsawa ce bai da niyya kuma ba zai amsar ba koda yana da niyya. Shi yarinyar ta cika rawan kai, shi yasa ba zai magana ba."

"Haka sukayi ta hirarsu tana kara kallonshi a madubin gefenta, tana jin wani abu yana cika mata kai da ruhinta, a karon farko da ta haWu da irin namijin da take fata, ita kan zuwa nijar ya mata rana.. har suka isa Aryan ya sauketa a gidansu, sannan ya wuce da Majid. ""Hammayo kayi kasuwa wallahi, kaga har yanzu bata shiga gida ba, gaskiya wannan karon zamu sha biki bayan sallah."""

"Bai ce mishi uffan ba, suka shiga cikin gidan su, ajiyar zuciya ya sauke tare da kai hannu ya bude kofar, ya saka kafarshi ya fito a hankali, yana jin kamar bashi ba. Haka ya nufi cikin gidan bayan ya cire facemask, ana gaishe shi. Amsawa yake da kai kawai. Har ya isa falon Hajiya tana zaune Amaan yana kwance a saman Kujeran, dama ga azumi ga rashin lafiya da yake boye musu. Cikin kulawa da wani irin idanu Majid ya zuba mishi ido yana karantar shi, tabbas Amaan bai da lafiya domin har fatarshi tayi duhu, amma sanin ba wani shiri suke ba, yasa shi yin fuskar shanu ya wuce gaban hajiya yana faWin. ""Gani nan nazo Hajiya."""

"""Kaje ka sauke ibadar da yake kanka."" Mikewa yayi ya wuce dakinshi, bai fito ba sai da aka fara kiran sallah ya sauko a hankali, ya samu duk sun hadu a falon ana addu'a, zama yayi aka yi da shi sannan ya dauki dabino da ruwan dumi ya sha, sannan ya koma gefe yana sha yana kallon Amaan da yake rike cikinshi. Suna gamawa suka wuce masallaci, Hajiya tayi nata sallah a gida, bayan sun fito suka dawo aka cigaba da buda baki. ""Amaan baka da lafiya ne?"" Da sauri ya kalli Majid. ""Eh amma da sauki domin anyi min aikin basir ne."""

"""Allah ya baka lafiya."""

"""Amin ai da sauki yanzu."" Inji Hajiya, ""fatarshi tayi duhu kai ma ka gani ko Hamma?"" Hadiye yawu Majid yayi yana diban farfesu. ""Duhu sosai."" Ya fada yana cigaba da cin abincinsa. ""Ba fa kome lafiya ta lau, bana jin kome wallahi."".""Eh ku ci abinci kawai."" Haka suka cigaba da cin abincin, har suka gama sannan Amaan ya wuce dakinshi da yake falon Hajiya. Da idanu Majid ya bishi. ""Ai kusan wata biyu kenan da samun matsala da Matarshi, ta kwashe Yaranta."""

"""Allah ya kyauta."" Iya abin da ya iya faWa kenan domin ba zai iya magana ba, sai da yaci abinci ya koshi, suka tafi sallah Isha da taraweeh, sannan suka dawo aka zauna ana hira. Ya lura da Amaan din da yake yan zabure zabure, yana kallon wayarshi. A hankali ya dauke kai. Kamar bai ganshi ba."

"Shima latsa wayarshi yake. ""Assalamu alaikum!"" ""Wa'alaikimun Salam, Maisah kece a gari?"" Murmushi tayi tana faWin. ""Hjiya tare da Hamma muka zo ai!"" Juyawa tayi tana kallonsu. ""Kin ga basu gaya min ba."" Shigowa tayi ta gaishe su sannan ta zubawa Majid idanu da yake ta latse-latse waya kamar baya wurin. ""Hajiya kin sha ruwa lafiya?"" ""Lafiya lau, da fatan kin iso lafiya."""

"""Alhamdulillahi,"" a hankali ta Ciro wata yar ™aramar camera recorder. Hajiya tuntuni ina tason na baki wannan abin amma Allah bai nufa ba, don Allah ki ajiye a wurinki. Wata rana zai miki amfani, amma yanzu ba zai miki amfani ba, ki dai ajiye kawai."""

"""Tow maisah."" Sai lokacin ya d'ago kai yana kallonta. ""Kun leka Nana kuwa?"" Mikewa yayi ya nufi hanyar sama, Aryan ma ya nufi hanyar waje. ""Allah ya shirye ku?"" ""Amin Ya Allah!"" Inji Maisarah. ""Ke zomu je na kai ki gida."""

"""Tow!"" Har zata mike ta rike hannun Hajiya. ""Koda kin ji labarin wani abu ya biyo baya, tow ki sani saboda wannan Camerar ce, don Allah ki adana shi da kyau."""

"Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tana faWin. ""In sha Allah babu abinda zai faru."""

"Haka ta mata sallama ta bar falon, ita kuma Hajiya ta bi Majid dakinshi, ta kai mishi, tare da cewa. ""Yarinyar ba yau take nuna min da wani abu ba, rayuwarta na cikin hatsari a yau ba gobe ba, nake son ka amince ka aureta. A daren nan ba sai gobe ba........."

#Mai_Dambu

"[3/9, 6:39 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*032*

Sakin baki yayi yana kallonta kafin ya tattaro nutsuwarshi da abin da zai gaya mata Hajiya ta bar dakin

"bakiWaya yanzu shi me zai cewa Hajiya? fisabilillahi Hajiya bata mishi gentle ba, shi fa auren familyn Ba'are gani yake kamar shiga lahira ne babu guziri, yo da guzirin ma ya aka kare balle ka shiga babu abin da zaka kare kanka. Yasan wani tarko ne ba wani abu ba ne,uban waye zai kashe ta a wannan lokacin da kowa yake ibada. Gyara kwanciyarshi yayi kamar ba zai tashi ba, can kuma ya mike tare da sauka ya saka takalman ya nufi hanyar waje. A falo ya samu Hajiya tana waya. Fita yayi yana kallon yadda garin yake, hannunshi sakale a cikin aljuhun wandonshi. A hanyar shi ta shiga gidan ya had'u da Aryan da yake dawowa daga rakiyarta. ""Ina zaka Hammayo?"" Sosa wuyar shi yayi yana kallon Aryan Win. ""A irin wannan yanayin me yasa baka wuce gidanka ba?"""

"""Na raka maisarah gida ne, domin wurin ya cika duhu kuma mace ce ta dauki kasadar fita a wannan lokacin. Tana bukatar wanda zai rakata gida."" ""Hmm!"" Ya faWa suka wuce zuwa gida, zama suka yi a harabar gidan. ""Hamma kamar akwai abinda yake damunka?"" Girgiza kai yayi, yana kallon sama. ""Ban san me yasa hajiya take jan wasu abubuwan ba? Nafi Hajiya son nayi aure, amma kuma a haka na lura kamar bata yarda bani da lafiya ba ne, idan na auri Maisarah me zan mata? Sannan abin da nake boyewa zata iya cutuwa idan tasan halin da nake ciki."" Ya fadi haka a hankali, shi kanshi Aryan sai yake ganin kamar sa'a yayi da Hamman shi yake gaya mishi irin wannan al'amarin, wanda kowa yasan halinshi da boye abinda yake ranshi."

"""Wayyo Allah taimako!"" Suka ji Ihun Maman Maisarah, kallon juna suka yi, kafin su shiga Mamarta suka samu tana ihu. Shiga cikin gidan suka yi har da ita, dakin yarinyar ta nuna musu. Kur suka mata, aka rasa me bakin magana. ""Don Allah ku taimaka min, kada ta mutu."" Da sauri Aryan ya wuce kitchen dinsu, ya dauko wuka ya yanke igiyar da ta daure wuyarta da shi. Fita da ita aka yi, a lokacin su Nana sun iso. ""Lafiya?"" Yanzu Aryan ya rakota muka gaisa, da yake taje gaida Hajiya Sa'adatu, shine bayan tafiyarshi, naga an kirata a wayarta, ta dauka ban san me aka gaya mata ba, amma naga ta fita zuwa tsakar gida, daga nan ban bi ta kanta ba, ashe igiyar shanya ta dauko ta rataye kanta."""

"""Kun yi ja'ira yar banza, waye ya gaya mata mutuwa shine mafita, me ma aka mata da zata kashe kanta, bayan ni ban mutu ba, ku kaita asibiti."" Kallon Aryan Majid yayi, cikin wani irin yanayi da baya son ya zarge shi. Amma sai ya dauke kai kamar bai damu ba, haka suka tafi asibiti suna zuwa aka karbesu kusan kwana suka yi akanta, kafin wurin karfe biyar na Asuba likitocin suka fito daga cikin dakin da take. ""Ya take ciki?"" ""Alhamdulillahi zamu ce, sai dai bakiWaya ko zata rayu bai zama dole ta mori kanta ba."""

"""Akan me?"""

"""Saboda kashin da yake haWe da bayanta, da spinal code dinta ya karye."" ""Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, me yasa na kiraki? Kin rayu cikin firgici da tsoron kada a kashe ki, yau gashi ke baki mutu ba. Ke baki rayu ba."" Mamanta ta faWa cikin kuka da danasanin abinda ya faru, domin da tasan haka zai faru ba zata so Maisarah tazo ba, haka yasa ta cigaba da kukanta har gari ya waye, wannan faruwar lamarin ya kara saka tashin hankali a zuciyar mutane, musamman yan cikin gidan. Abin da yafi hurting ran mutane, shi ne a daren Aryan ne ya kaita gida, haka yasa baki daya ya shiga yanayin zargi da tuhuma. Karfin imani da tawali'u yasa Aryan bai haukace ba, amma sai da ta kai ya zauna yana kuka kamar karamin yaro a gaban Hajiya. Shi kanshi Majid tausayin Aryan din ya™e ji amma baya son maganar gaskiya shi daya ne abin zargi a cikin gidan. Domin shine ya ganta na karshe kafin faruwar lamarin. Amma kuma maganar gaskiya bazasu ce shi ya aikata ba, sannan ba zasu ce bashi ba ne. Dole bincike ne zai tabbatar da haka."

"Ba karamar girgiza Alhaji Kamilu yayi ba, domin bai tab'a kawowa hakan zai faru ba. Sai dai da Hajiya"

"tayi mishi maganar binciken abin da ya faru. ""Wani bincike kuma? Babu wani binciken da za'a yi, domin nasan"

"™arshe a cikin gidan nan aka samu wanda yayi wannan aika-aikan."""

"""Ai gara a bincikan hakan zai saka mu daina zargin Aryan domin kowa yaji ta hadu da Aryan abin da yake ayyanawa a ranshi akwai wani kudiri ko wani abu na daban."""

"""Na sani, sai dai hakan ba zai haifar mana da d'a mai ido ba, Allah ya bata lafiya kawai."" Ya fada yana kara jin wani irin d'aci a ranshi domin Allah ya gani yaji zafin al'amarin, sannan duk wanda yayi wannan aika-aikan yasan abinda yake yi, shi yasa yayi amfani da rakota da Aryan yayi da zuwanta gidan Hajiya."

"Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke, sannan ta ce mishi. ""Shi kenan, tunda baka son binciken Allah ya bata lafiya. "" Ta"

"fada tana mikewa, tare da leka dakin Maisarah da take cikin Unconscious. *Idan wani abu ya fito bayan kawo miki wannan Cameran tow tabbas abin da yake ciki babban al'amari.*"

"Wani irin zufa ne yake zubowa Hajiya, duk abinda yarinyar nan ta gani ba karamin al'amari ba ne, haka yasa ta nufi gida zuciyarta na wani irin zillo."

***

Zahra

"A matukar gajiye na dawo, dake Allah ya taimake ni Amirah sugrah tana wurinsu, ina shigowa aka kawo ta, yarinyar nan taki zama, ""kuje da ita kawai, na gaji gajiya zata kara min."" ""Tow Tante!"" Suka fita da ita, ina kwance a wurin har wurin biyar, tashi nayi na nufi kitchen. Dama tun safe na surfa wake tare da dafa kwai, wanke-wanke na shiga yi, ina gamawa na zuba mishi kayan miya. Na zauna na markad'a shi. Ina tsaye har yayi laushi na juye ina nazarin nayi ta manja ko mangyad'a. Karshe haka nayi ta mangyad'a, na zuba kwai da kifi. Sannan na duba geron da na bawa Barakatu

Please Login or Register in order to submit comment