You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba mata allura a ciki. Yana kallon yadda take kallonshi kamar irin ta farka daga cutar makanta, ya sani tana mamakin yadda aka yi babu abin da ya same shi. Sai da ya gama sannan ya dawo gabanta ya riko hannunta, ya saka a fuskarshi.""Hajiyana nine Majid Mamman Ba'are gani nan lafiyana lau, ki kwantar da hankalinki."" Murmushi me had'e da hawaye ta sake tana kallonshi har barci yayi nasarar gaba da ita. ""Nana muje na kai ki gida kinji."" Kallonshi tayi a kaikaice irin zata kafta mishi rashin mutunci. Yadda ya saka fuskar sojojin tuni hankalinta ya dawo jikinta, ""hmmm muje!"" Ta ce tana shirin mita. ""Nisah kema idan ba da motarki kika zo ba, zo muje na ajiye ki kada na kuma ganinki tunda kuka zaki na mana asibitin. """

"""Don Allah kayi hakuri ba zan kuma, na daina kukan."" Ta fada tana k'amk'ame jikinta alamar ba zata fito ba, ""ok muje ki ga jikin Aryan da Amaan."" Mikewa tayi suka fita, har dakin a lokacin Aryan yana Sallah, yana idar da sallah. ""Hamma Aryan?"" Ajiyar zuciya ya sauke. ""Ya jikinka?"" Ta fada tana kuka, ""Ya isa Auta, ba gashi naji sauki ba. Bar kuka ina fatan babu abinda ya same miki ko?"" Girgixa mishi kai tayi tana share hawayen da yake zuba mata. ""Bari na kai matar nan gida "" ""kaga matar nan a kofar dakinka, ni ba matar nan ba ce."" Ta fada tana wani dauke kai, ita fa gara mata ma Majid da wannan me kalar zabiyar haushi ya™e bata, balla mishi harara tayi. ""Don kana gadara da Alhaji yana tsaye sai ka kashe min jikoki, dan banza me kama da mutanen boye."" ""Muje!"" Majid ya faWa mata, domin ya lura jaraba take nima. ""Aikin banza kishiya da shashasha, da ka kafe ni da idanun kamar na mayu kurwana kur, idan ma ka kirkiro hatsarin ne don su mutu kaci kasonsu kayi karya, ina sane daku munafunkin banza munafikin wofi."" Maganar Nana tayiwa Aryan tsauri amma kuma sai yayi murmushi ya ce mata. ""Ai ke zan fara turawa lahira, domin na gaji wannan gwal din wuyarki."" Wani dafe kirji tayi, tana nuna shi tare da kallon Majid. ""Kaji ba, yana shirye shiryen turani lahira bayan ban ga matarka ba, dan bakin ciki wannan sarkan na matar Alhaji ne ko mutuwa nayi bata cikin gadona."""

"""Ai kuwa ki saka idanu sai kin garzaya barzahu bari a sallame ni, domin zan fara aikatar da aikina ne akanki."" ""Wallahi baka isa ba, sai kotu da yan sanda sun shiga tsakaninmu, na rantse da Allah ba zan yarda ba, ko tuntube nayi Alhaji kai zaka nimo min lauya domin Ariyan ya shirya kisan kai, ya ga baya tow na rantse da Allah sai nayi fatalwa ko na mutu na kwaci hakkina."""

"""La fatalwa ma zaki zama?"" ""Kwarai don ba barin hakkin jinina zan yi ba."" Ta fada tana hura hanci kamar ta doka mishi sandan hannunta. ""Tsuhuwa lokacinki yayi, sai a fara shiri kafin na zo."" ""Alhaji kana jin shi ko."" ""Muje ki daina biye mishi, cinnaka Aryan ba zai kashe ba, balle dan mutum nayi mishi wannan shaidar tun daga duniya har lahira ba zai kashe wani ba."""

"""Au hatsarin da ya ja musu fa?"""

"""Muje a hankali zaki fahimci abin da yake faruwa."" Haka ya fita da ita, "" Nabeeha wai zan iya kashe ..."" Hannu ta saka mishi a baki, ""Tsakanin harshe da hakori ana samun sab'ani, haka tsakanin mutum da mutum ana samu, Aryan ban kowa a duniyarka ba, sai adalcinka har abada ba zaka b'ata hannunka da jinin kowa ba in sha Allah."""

"Ta fada tana kuka, tana son Mijinta kuma bata ji a ranta zata zarge shi ba. ""Idan Hamma!"" ""Hamma Aryan, itama Nana gurbata mata tunani ake da zancen banza, muji da halin da Amaan da Jamilah suke ciki."""

"Shiru dakin ya dauka, babu wanda ya kuma magana, sannan Mijin Jamilah da dangin shi suna asibitin, hatsarinsu yasa videon Amaan ya mutu, sai aka koma labarin hatsarin domin abin ya faru ne da safen jiya, kuma kowa ya ga yadda abubuwan suka faru, sai aka shiga yayyata videon hatsarin da yadda abin ya faru, sama da labarin Hajiya da Amaan. Wannan al'amarin ya faru cikin kwana Waya, sai ya zama kome ya tafi kamar bai faru ba, don haka"

Majid shima yayi amfani da nashi kwarewar yasa aka binciko mishi wanda ya sake videon Amaan. Ai kuwa gayen yaci

uban dokar sojoji.

"* Tunda Majid ya bar Tani a Wakinta har gari ya waye bata fito ba, koda Hajiya Fauziya tazo gidan a daki ta same ta,"

"don ta kawo mata tsegumi ganin halin da take ciki yasa, bata iya bata labarin ba. Domin ta same ta ta birkita dakin tana niman abu."

"""Tani lafiya?"""

"""Lafiyan kenan wayata nake nima."" Kallonta Hajiya Fauziya tayi baki sake ta ce mata. ""Ban gane wyaarki ba, wanene a gefen gadonki?"" Juyawa tayi ta ganshi ta ce mata. ""Ikon Allah, ban san yana wurin ba."" Ta dauka da sauri har yana kokarin faWuwa a hannunta, ta shiga kiran Sajjid.."

"""Dauka mana."""

"Katse kiran aka yi ta kuma kiranshi, sai da tayi bugu uku sannan aka Wauka a make ya ce mata. ""Dalla me zan miki?"""

"""Idan kana cikin Niamey tow ka gaggauta barin garin nan, Majid na gaya maka Majid. Wallahi kafin wayewar gari nayi kashi ya kai sau goma maza ka bar garin nan ka kashe wayarka kada ka kunna sai nan da wata uku na gaya maka kada ka dawo Nijar """

"""Babu inda zanje, ina garin nan wallahi."""

"""Na gaya maka kamar kare zai kashe ka, domin ko ya kashe ka babu abinda zai faru, ya fika gata ya fika kome ka kyale kome ka bar garin nan daga baya zamu yi magana don Allah."" Ta fada a raunane, ""Ni dai ban ji dadi ba, kawai zan tafi ne ba don ina da ra'ayi ba."""

"""Jeka don Allah da kuma ni."" Kit ya kashe wayar yana mita. Itama zama tayi dabas da malmalan duwawunta tayi da kasa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya me nauyi domin sai yanzu taji abu ya wuce mata, d'ago kai tayi a matu™ar gajiye ta kalli Hajiya Fauziya."

"""Uwar me kika zo yi?"""

"""Hmmm! Hmm dama na gaya miki Aryan ya farfaWo sannan an kama kama mutanen da suka yi ta."""

"""Je ki don Allah domin kin zama tauraruwa mai wutsiya, ganinki babu alkhairi domin nasan sharri ke tafe dake, don haka tafi wanda nake ciki ma ya ishe ni wallahi."""

"""Hmmm daga abin arziki, amma tunda bakya son na gaya miki shi kenan."" Ta juya tana jin haushi kamar zata rufe Hajiya Tani da duka, don tazo da mugun labarin cewa an kama yaron da suka saka aiki. Don ba iya Sajjid yake mocking Amaan da yan uwanshi ba, har da taimakonsu *Kuyi hakuri babu yawa*"

*¦ 300* 08130269641

#Mai_Dambu ce....

"[4/17, 8:10 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

036

"Tuntube Nana ta yi zata fad'i, Majid ya tare ta . ""Innalillahi kaga ni ba? Ka ga ni ba tun ban bar asibitin ba ya fara ™o™arin ganin bayana."" Shi dai bai ce mata uffan ba, har suka isa wurin Motarshi. Bude mata yayi ta shiga. Don jaraba glass Winta ma sai da ya kusa faWuwa ta riko ta saka a juye, da wutsiyar idanu Majid ya kalle ta. Yana tab'e baki har suka bar Asibitin. ""Hajiya!"" Ya kira sunanta, bayan ya zare glass Winta ya saka mata shi. ""Na'am Alhajin Allah."" Murmushi yayi cike da takaici, domin tun fil azal ya dace su samu wannan soyayyar amma basu samu ba, sai rana tsaka. ""Ka kira sunana kuma kayi shiru, ni bana son haka idan ka san ba magana zaka yi ba ka daina min haka, sai a kira mutum ya dauka wani abin arziki zai samu amma ayi shiru, ai wannan wulakanci ne."" Bai ce mata cikanki ba har suka iso gida, zata fita taji kofar motar a rufe. Fito da yar karamar bindiga yayi ya ajiye, zare idanu tayi waje. ""Hmm Alhaji me zaka yi da bindigarka haka?"" Gyara zama yayi yana faWin. ""Duk wanda ya gaya miki labarin abin da ya faru, tow ki kirani ki tambaye ni kinji ko? Kada na kuma jin kina zargin wani kina jina?"""

"""Alhajin Allah, da akan wannan zaka min kashedi ai ba sai ka rike bindigarka ba, kawai ce min Nana kada na kuma jin kin zargi kowa, zan ce maka Allah ya huci zuciyarka bawan Allah ba zan kuma ba."""

"A ranshi yana jin dadin yadda take saurin razana, da hawa hanya. Idan da wata ne hayaniya zata mishi. ""Kin ga dai ni ban ce kome ba, kawai abin da nake so zan saka miki lambata kawai ki gaya min kome ya faru"

"zan baki amsa."" Ya dauko wayarshi ya kunna mata videon abinda yake faruwa na hatsarin, taga dai ba Aryan din"

bane ma yake tukin Jamilah take tukin.

"""Hmmm! Amma fauziya tsinanniya ce, ita ta kawo min labarin Aryan ya tafi ya watsa min jikoki a titi mota tabi ta kansu."""

"Lumshe idanun yayi ya ce mata. ""Je ki kinji Matar ™arfen daga ke ba ™ari."" ""Alhajin Allah ka maida bindigar nan."""

"""Tow matar ™arfe."" Ya ajiye shi a asusun motarshi. ""Hmmmm. Alhajin Allah yaushe zaka saya min nama."" ""Jeki za a kawo miki."" ""Alhajin Allah baka saka min wayarka a wayata ba."" Ya karbi wayarta da yake makale a wuyarta har da igiya domin cire mishi tayi, yayi abinda zai yi ya mika mata. Layin sai tarin bashi."

"""Taya kika ci bashi haka?"""

"""Ina zan sani tunda Yar gidan Hafiza Waukar wayar take, ba dare ba rana matukar na ajiye zata Wauka."" Hafiza stepsister Winshi ce, yarta tazo hutu. Ciro kuWi yayi ya mika mata, ""Ga Barka da sallah Winki."" ""Allah ya kara bud'i, na gode sosai."" Ya bude mata motar ta fita, ya juya ya bar gidan bata shiga gida ba, sai da ta daina hango Motarshi ta shiga gida."

"""Nana Oyoyo ya masu jikin?"" Kuru tayiwa Hajiya Fauziya, kafin ta ce mata. ""Ke dai Allah ya tsine gulma da munafurci da yake kokon ranki, munafuka Annamimiya. Kika saka ni zargin dan marayan Allah da yake kwance cikin jinya, kai fauziya ke tsinanniya ce wutar munafukai ya tabbata akanki. Munafuka makira. Allah ya isa min shi yasa Rabi take burge ni bata shiga harkar kowa amma ke kullum munafurci yana cin gindinki."""

"Tass ta wanke Hajiya Fauziya da kanta a kasa, ai Nana ta iya tozarci idan ka sake ka takaleta a gaban uban Kowa zata wanke ka kai din banza ina ruwanta tunda kai ka tab'ata."

"Asibiti kuwa sai yamma can Amaan ya farka, Jamilah ce dai sai du'a'i domin hankalin kowa ya tashi ya dace ace ta farka amma al'amarin ya ci tura. Haka yasa likitoci suke kanta ba dare ba rana."

"Hajiya ta farka itama, sai dai babu wanda ya bata labarin halin da Jamilah take ciki, ko lokacin da Amaan ya shigo"

"dakin dakatar da Majid tayi ta hanyar juya musu baya. ""Ya tafi bana son ganinshi."" Alama Majid yayi mishi da hannu suka fita. ˜o™arin danne hawayen da suke son zubo mata tayi domin bata son tayi mishi kuka, idan tayi mishi kuka, bata san wacce irin rayuwa kuma zai yi ba, sai tayi ™o™arin danne abin a ranta, ""Kiyi kukanki amma ba da nufinmu ba, kiyi jininki zai sauka sosai. Kiyi kuka ba ragwanta bane jarumta ce, rago shi yake ihun, jarumi hawaye yake zubarwa domin ya samu sauki a zuciyarshi. Hajiya bature ya ce ""courage doesn't mean you don't get afraid, courage means that you don't let fear stop you,"" kiyi kukanki Ummina, kiyi kuka idan baki ba zai dame ki har karshen mu, ba iya shi ba hatta mu rashin kukan zai haifar da abubuwa dayawa."" Zama yayi a gabanta yana murmusa mata ya ce. ""Kina nufin Allah ba zai jarabce mu bane? Idan bai jarabce ki ba, Ummina ki binciki girman alakarki da Allah, domin shi baya jarabtar kowa sai wanda yake da kusanci da shi. Hajiya Ummina, Allah baya duban marasa nima a wurinshi sai masu nima, kada ki ce Allah bai amshi addu'arki ba ne, a'a ya amsa yana son ya ga girman hakurinki ne, Ummina Allah baya waiwayar waWanda suka manta da shi, yana waiwayar masu ambaton shi ne. Ya amshi addu'arki na neman shiriya akan Yaranki, ya tab'aki ne don yaga hakurinki idan kika yi hakuri ya kara miki alkhairi akan haka. Hajiya Ummina kiyi hakuri domin rabonmu yake wahalar dake, Allah ya nufa ta hanyar mu zaki ta haduwa da kalubalen rayuwa. A madadin Yan uwana bakiWaya muke nimawa Amaan Mamman Ba'are, yafiyarki da albarkanki."" A hankali ta saki kuka me sauti, yau Majid ya tunatar da ita Allah, a wannan halin da take ciki. ""Ki godewa Allah da aka farga da lalurar shi idan kuma da gawarsa aka samu da wannan labarin fa? Hajiya akwai abinda kai a wurinka babban al'amari ne, amma a wurin Allah karamin al'amari ne."""

"Dafe kirjinta tayi, tana kuka har da shasheka.""Kiyi kukan ki samu sauki Hajiyata, domin da haka ne ba zan tab'a yarda hawan jini ya sake tab'a min ke ba, amma idan kika yi shiru zuciyarki zata yi sauki tunanin da zaki ta ajiyewa domin ganin ya zaki yi, zasu tafi shaidan da miyagun mutane ba zasu same ki ba, domin kin rigada kin cire."""

"""Ba zan iya cire abin da na gani akan Amaan ba, ji nake kamar ba zan yafewa kaina ba."" Ta fada tana kuka, ""Zaki iya fa, amfanin kukan kenan ya sauke min kaso me yawa na damuwarki, kuma ba gazawa ba ce, amma tabbas zaki manta idan kika tuna inda Amaan yake raye, Hajiyata har da laifinki wurin barin Amaan ya faWa wannan halin."" D'ago kai tayi tana kallonshi. ""Wallahi da gaske nake gaya miki, domin amman yana bijire miki ba shi yake nufin ki kyale shi yayi yadda yakeso ba, na sani dukkanmu kece kika haife mu, amma samuwar Wayanmu yana iya shafe halin kowannen mu da yake ciki, Hajiya tun ranar ™ari kika bar tubani, domin da kin tsaya akan Amaan da haka bai faru ba, bakiWaya kina tunanin idan kika takura mishi zai kauce ta wata hanyar bayan kyale shi, shi ne fadawar shi halaka, Hajiya wani hanzari ba gudu ba, ni kina son nayi aure. Amma baki san me yake damuna ba, Hajiya idan xan yi auren na su macen da nake so, karshe xan iya zama me karkon kifi daga ruwa zuwa wuta. Hajiya idan har da gaske ke Uwa ce, yanzu ya dace ki tsaya akan Amaan ba kyale shi ya rayu babu wani a kusa da shi ba."""

"""Duk ™o™arina akanku dama na gaza ne?"" Murmushin karfin hali yayi mata, ya ce mata. ""Har kwanan gobe ba zan"

"kiraki raguwar Uwa ba, domin duk inda ake bukatar uwa jaruma kin kai wurin, sai yan kura-kurai da ba za a rasa ba, amma ai kin yi ™o™ari domin zaki iya lashe kambun uwa ta musamman a duniya."""

"Majid yayi maganar da yasa jikinta yayi sanyi, don bata taSa kawowa gazawarta akan Amaan shi ya"

"haifar mishi da lalacewar shi ba, yasa tayi shiru sanin ya kara mata aiki yasa shi fita ya sayo mata magani har da me saka barci, ya b'alla mata ta sha. ""Tabbas nice na taimaka mishi wurin lalacewa, domin a lokacin gani nake idan ban barshi yayi yadda yake so ba, zai iya lalacewa."""

"""Yanzu ai mun rufe wannan chapter Win ko Hajiyata."" Ya zauna yana kallonta, Waukar wayarshi yayi yana danne- danne. Shiru yayi domin yana son tayi shiru ta kwanta. Kuma hakan ce ta faru, da ta gama yan nazarinta, kafin ta kwanta barci yayi gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke ya kara karfin ac din dakin sannan ya nufi jikin windown dakin ya tsaya yana kallon waje. Dole ne a gare shi ya fuskanci kowacce matsala."

"Wayarshi ce tayi kara ya dauka, ""Majid Mamman Ba'are, na ga sakonka. Allah yasa haka shine mafi alkhairi, kuma ka dauki matakin da ya dace. Kasa da duniya ba zasu manta da alkhairinka ba."""

"""Na gode Sir"" ya faWa, haka suka yi sallama, yana jin wani sabon nutsuwa yana saukar mishi ya ajiye aikin soja ya huta. Yanzu dama biyu gare shi ya tsaya asibiti ko ya karbi kamfaninsu."

"Sai dai wani abu da yake ganin zai fi mishi, zaman asibiti domin akwai abinda yake tuna mishi military section."

Murmushi yayi yana jin wannan shine mafarin farincikin shi.

"Sai da aka sallami Hajiya da Aryan, amma Amaan yana cigaba da jinya. Domin har zuwa lokacin ana kan zancen mishi tiyata ne, don duburarshi dole aiki za ayi mishi."

"Manyan likitocin da suka kware akan tiyata, har da shi Majid a ciki suka jagoranci tiyatar farko, domin zama yana shirin gagararshi. Koda akayi aikin farko za a iya cewa an samu nasara, tunda har an samu yana iya zama tare da yin bayan gari da kanshi."

"Jamilah ce dai da alamu sai yadda Ubangiji yayi da ita, a wannan yanayin Zaytoonah da Mamarta suka zo, har da Yafendo."

"

Camp.

"Wato al'amarin Addah sai a hankali, domin kuwa idonta ya lalace. Duk yadda aka so a gyara amma abin ya ci tura, a duk lokacin da Addah ta kalli idanunta, ta kuma tuna cewa saboda Zahra idanunta ya lalace, tana kara jin matukar tana raye Zahrah tana raye sai ta rusota daga sama, sai tayi kaca-kaca da duk wata daukakar Zahra."

"Jin za a shigo dakin tayi maza ta boye madubinta, bayan Ummi ta rigada ta gani. ""Kina kallon idanunki ne?"" Ummi ta tambayeta babu wani abu a ranta, amma dake tana kallon kamar izgilanci Ummi zata mata, ita kuma zuciyarta daya tayi maganar. ""Kina min dariya ne don na rasa idanuna Waya? Ai ba ayiwa ™addarar wani dariya yau gare ni gobe ga wani."""

"""Ke dai kika sani, abin da yake zuciyarki kike faWa, amma ya daga tambayarki kawai zaki hau surutu kamar wacce aka zaga."""

"""Shegiya munafika, algunguma."""

"""Eh na yarda amma ban kai ki ba, makashiya me sayar da Yarta domin duniya da abin cikinta"" ""Ni kika zaga karuwa kawai, wacce ta zubda cikin shege."""

"""Kanku ake ji, farka da makaho."" ""Lalatacciya mazinaciya."""

"""Duk abinda muka aikata ai laifinki ne, domin kece kika aika mu, bari ki ji ko jahannama zan shiga ina fatan Ubangiji yasa tare dake ne, gani ga ke. Ina kallonki kina kallona."""

"""Tsinanniya muguwa, in sha Allah ba zan shiga cikin jahannama ba."" Addah ta faWa tana mikewa, Ummi ta ce mata. "" Kika sake hannunki ya tab'a ni sai na miki shegen duka, idan kina ganin wasa ne Bismillah."" Ta fada tana mikewa a fusace tana watsawa Addah harara."

"""Ni nace zan dake ki ne? Kawai don kin ga na tashi sai ki fusata."" Lokaci guda tayi sanyi, domin tasan Ummi bugun kato zata mata."

"

"Wata biyu da sallah, karatu yayi zafi domin kuwa, gashi bani da lokacin kaina sai na karatu zuwa yanzu babu wani"

"da yake tare da ni sai su Maman Barakatu, a wurinsu Amira take zaune, idan na dawo haka zan huta na shiga cikin gidansu. Dake motar da ake kai ni makaranta sun bar min ita, ni kuma kunya nake ji na ja motar."

"Ina kwance kamar ruwa ya cinye ni, nifa sai yanzu na gano raguwa ce ta gaske. Domin kuwa idan na dawo"

"nayi sallah na kwashi abinci, to nan nake bajewa, habawa bana iya tabuka kome kai Allah na gode talaka bai iya samun wuri ba, sai na baje nayi ta nishi dai-dai kamar wata tsohuwar akuya."

"" Duk yadda Hajiya taso danne abin, kasa rike zuciyarta tayi. Domin ganin har Yafendo a Nijar yasa zuciyarta laushi ta shiga fesar da abinda yake ranta, tana faWa tana kuka. ""Wannan sirrin Yaranki ne, ko kin gaya mana sai dai mu baki hakuri kamar yadda Abdul Majid ya gaya miki, kin bar Amaan don yana nunama Majid kiyayya kike gudun kada wani ya sani ya yi amfani da hakan ba? Tow ga shi nan yadda aka wayi gari, Wa garin ya waya? Addah na sha gaya miki duk abinda ya faru dake ba laifin kowa ba ne, laifinki ne akan Yaranki ya dace ki tsaya. Don Allah kada ki kara barin haka ya faru."""

"Cikin shashekar kuka ta ce mata. ""Har yau baki ji labarin batula ba ko?"" Murmushin karfin hali tayi tana faWin. ""Ta rasu fa, ni kan.har nayi mata addu'a Allah ya mata rahama."""

"Amma!""Ni kuma ina ji a jikina Batula tana raye, kamar tana kusa damu."""

"""Kawai kina jin haka ne don kin saka hakan a ran ki ne amma ni nasan bata raye."" ""Ammi don Allah rike min, Mimi."" Ta mika mata Yarta zata fita, ""ina zaki?"""

"""Zan tafi wurin Hamma Abdul a can asibiti."""

"""Hmm! Ki dauki yarinyarki me shegen kukan tsiya."" Inji Mamanta, ""barta ba zata yi kuka ba."" Da sauri ta fita bata ma tsaya ba. ""Zaytoonah tana son Majid sosai."""

"""Bana jin akwai bukatar ayi wannan zancen, domin kowannensu ™addarar shi daban."" Inji Yafendo tana shigowa. ""Yafendo ko don zumuncinmu!"" Inji Hajiya."

"""Malam ya gaya min cewa duk yadda muke son, su had'a kansu haka ba zai yiwu ba. Domin kuwa kowa da ™addarar shi da rabonshi"""

"""Kuma ai babu adalci ace Majid ya auri bazawara da Yarinyarta a duba dai."" Inji Maman Zaytoonah, ""kada na kuma jin irin wannan zancen."" Inji Hajiya."

Dariya Yafendo tayi domin tana jin dadin yadda suke tsayawa junansu.

"A can asibitin kuwa, dama da gayya Majid yaki komawa gida, don idan ya koma suka yi idanu biyu da Zaytoon ba barin shi zata yi ya huta ba, shi yasa shima ya hana kanshi komawa gidan....."

300¦

0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400

#Mai_Dambu ce.

"[4/19, 4:22 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*037*

*Aunty Nuratu Salihu Abbai gaisuwarki ta musamman ce. Tare da Team Hajiya Tani ikon God *

"A harabar gidan suka hadu da Nana, kallon uku saura kwata Nana tayi mata, kafin ta dauke kai kamar ba zata amsa"

"gaisuwar da take mata ba, kafin ta amsa ta ce mata. ""Ina zaki haka?"" Tana hura hanci. Zuciyar Zaytoonah daya ta ce mata. ""Wurin Hammayo zan je a asibiti."" Ta mikawa Driven food flask, wani haWe fuska. ""Ce miki yayi yana jin yunwa?"" Ta fada tana wani haWe rai, ""A'a kawai nayi mishi irin abincin da yake so ne."" ""Au ya gaya miki ba'a bashi abincin da yake so ne?"" Gajiya da Jarabar Nana Zaytoonah tayi ta wuce zata shiga mota, Nana tayi bake-bake. ""Wallahi bakya shiga ki je wurin shi."" Fitowar Aryan tare da Nabeeha suka samu ana rigima, ita kan Zaytoonah zuba mata idanu take, sai masifa Nana take. ""Kai Ariyan wannan yarinyar me kama da muciya da zanin me take nufi da Alhajin Allah?"""

"Juyawa yayi ya gama duba ko ina bai ga me kama da abinda ta siffanta ba ya ce mata. ""Wa kenan?""

Please Login or Register in order to submit comment