You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tabbatar musu tana lafiya, sai gashi sun kawo mata kayan aurenta da duk abinda ake na al'adar kasar nijar. Shima ganin ya auri yar babban gida, basu bar kasar ba, sai da ya ajiye musu kayan auren da ake a cikin kayan har da zinari babba tukwaicin budurcinta....."

#past #entangled #revals #lovers #Dambuje

"[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

"_ Wai page biyu kuke so, Yasin kuyi maneji mana masoyan Addaririya_"

"Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai"

albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.

Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.

MARKADADDIYAR GYAD'A

HADADDEN KAYAN SHAYI

GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA. GARIN TUWO

GARIN KUNU YAR ASALI CURRY ME DADI

SPICES TYME

YAJIN DADDAWA ME KYAU GARIN DAN WAKE

JAN YAJI MAI DAD'I...

BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.

"ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA. WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU."

ZAKU IYA TUNTU�ARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590. MUNA DAKON SAYAN DAI-

DAI KO SARI.....

*015*

"A bangaren Nana ta dai sassauta kiyayyar ta ne don, iyayen Sa'adatu babu wanda ya isa ya kawo musu raini sannan daga mazan dangin har matan kana ganinsu kaga wadanda suka san ciwon kansu, ga wanka da matan suka yi na arziki zaka fahimci sun tashi cikin arziki da wadata domin gwala-gwalan da sukayi kwalliya da su, bayan tafiyarsu ne ya fara ginin part din Sa'adatu ya zuba mata kome nata, da zai tafi wurinta ya dauko mata yan kunnenta babban set da karami ya kai mata,"

"A lokacin da laulayi nata yayi sauki kenan, haka ta rike shi da daraja, bai gayawa kowa Sa'adatu tana da ciki ba, amma yadda yake lissafin zata haihu bayan sun gama jarabawa zai kaita wurin danginta ta zauna sai tayi"

"arba'in ya dawo da ita. Haka kuwa aka yi domin suna gama jarabawa, ya zo ya zauna ko zata haihu amma ina shiru"

haka.yasa shi daukarta suka tafi kasar Iyayenta. Lokacin da ta ganta a cikin danginta. Ranar kwana tayi tana kuka tana jin wani irin son danginta..ga iyayenta ga Abbati sai shiga da fita yake yana kawo mata abinci da ta ce tana so.

"Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are sai da yaji wani iri domin kuwa yarinyar ba tsarar shi ba ce, don Abbati ya"

"nuna mishi wanda aka so ta aura, yaro ne Matashi amma haka ™addara da rabo ya shiga tsakani. Ranar da suka isa a daren ranar ta haifi d'anta namiji, babu wanda yasan tana nakuda, tsabar kunya da wauta."

"Yafendo mahaifiyarta tana dakin Mallam mahaifinsu, suna sallar nafilla da mallam wanda suke kiran shi Babaji, taji kukan jariri, bata yarda kunnenta ya jiyo mata ba, sai can ta kara jin kukan. Ai sallama tayi ta nufi dakin ta, anan ta samu Sa'adatu da Kanwarta Kabo, an rasa wanda zai yi wani abu, sun saka Baby a gaba. Dariya abin ya bata ta ce. ""Danejo jaririn kuka kasa a gaba. Keda kabo shine baku fita kun kira Sumai ba?"" Tana jingine da gadon, tana sauke ajiyar zuciya. Bata ce kome ba, itama Yafendo fita tayi ta kira Sumai, Uwargidanta kenan, ita tazo ta gyara Babyn tsaf, ta wanke Sa'adatu a lokacin, sannan suka saka turaren wuta, domin ita Sumai fulanin chad ce, tana harkar turaren wuta. Kafin wani lokaci gidan ya cika da kamshi, Sa'adatu ana kiranta danejo, Babaji yana kiranta da Hajiya. Kasancewar sunan Mahaifiyarshi ce kuma Hajiyar ce da gasken gaske."

"Da asuba aka gayawa Alhaji Mamman Ba'are, Hajiya ta haihu.don da fari bai fahimci wacece Hajiya ba, sai da Alhaji"

"Nasiru Wodabbe ya zauna ya mishi bayani, sai ya gane ya kuma ce musu. ""In sha Allah Hajiyarta za a kirata."". Haka ya fita Masallaci, ya shiga gidan don ance mishi ta haihu amma basu gaya mishi me ta haifa ba, sai da ya shiga Sumai take murmushin farinciki ta ce mishi. ""An samu da namiji, ango ba cefane."" Zubewa yayi a kasa ya zuba sujudul shukur, kafin ya fashe da kuka, aka mika mishi Yaron, jikinshi yana rawa ya fito da yaron har gaban Babaji, ya ce mishi.""ka saka mishi sunanka."" Murmushi Babaji yayi ya amshi yaron ya mishi huWuba, a madadin yasaka mishi Aliyu, sai ya saka mishi Abdul Majid. Ya mika mishi. ""Gashi nan Abdul Majid, kukan ya isa haka. In sha Allah zai zame maka fitila a duk wani Mabudin alkhairinka."" ""Mallam baka saka sunanka ba?"" Ya faWa hawaye na zuba mishi. ""Suna na ba shine mai muhimmanci ba, sunan da zai zame mishi alkhairi ake bukata."""

"Malam yaji dadin wannan kara da Alhaji Mamman Ba'are ya mishi, shi kan kuka yake tayi, don gani yake kamar ba dan shi bane, har asibiti aka kai Yaron aka duba lafiyarshi. Sannan suka dawo kwanan shi biyar ya dawo Nijar ya gayawa Nana ai Sa'adatu ta haihu, bata wani damu can ba, sai da ya ce mata namiji ta haifa shine bayan suna suka je ita da Hadiza da Harirah. Ba karamar hidima aka musu ba, duk iskancin Nana da wulakanci sai da ta rena kanta, domin tazo inda ake magana ta arziki wato kudi kumbar susa. Domin su suka je Barka, sai gashi sun dawo da kayan arziki niki-niki. Madadin haka ya janyowa Sa'adatu farinjini sai tsanarta ya kara cika zuciyar Hadiza da Nana, ita kan Harirah tun farkon ganin Sa'adatu da hakorin hajji jikinta ya bata daga babban gida ta fito, shi yasa bata wani takurawa kanta wurin kishi me zafi ba."

"Watansu guda suka dawo kano da kaya niki -niki, suka cigaba da zuwa makaranta. Da dattijuwar da tazo da ita"

"daga garinsu me suna Inno, ita tayi ta renon Abdul Majid har suka yi arba'in da wasu satika sannan Inno ta koma ita kuma ta cigaba da karatunta, sai da suka yi wata hudu sannan suka tafi marad'i, kwanansu uku suka wuce Niamey. Wayyo rawar kai a gurin Alhaji Mamman Ba'are ba acewa kome, haka tayi musu sati Uku. Don zasu koma makaranta kuma har cikin azumi suna karatu. Haka da zata dawo Alhaji Mamman Ba'are yayi ta mata hidima."

"Har suka dawo, kaunar da yake nuna musu ya janyo mata bakin jini, haka suka yi ta jigilar karatu ga danginta daga garinsu ana yawan mata aike, lokacin da Abdul Majid ya cika shekaru biyu, suka tafi Umara da shi, Abbati ya biya mata da Abdul Majid. Lokacin sun samu hutu koda suka dawo, Nijar suka sauka a can ta huta domin lokacin zata shiga aji hudu ne, ga zata tafi IT, wannan zuwan ta fahimci kamar bayan son ganinta har ta gama hutun zata koma, ya zo domin sau biyu suka hadu, da zata koma ya mata kome, ya ce kada ta kuma zuwa Nijar."

"Tunda ta dawo bai kuma waiwayonta ba, Allah ya so Abbati baya wasa da zuwa ganinta duk bayan wata uku, bata taSa gaya mishi tana cikin matsi ba, ba kayan abinci shima Abbati idan yace zai zo Mahaifinta zai cika mota da kayan abinci akawo mata . Sannan Yafendo tana turo mata da kayan sayarwa turaren wuta da wasu abubuwan da babu anan, haka yasa ta samu damar tsayawa da kafarta."

"A can Nijar kuwa, Alhaji Mamman ne ya hadu da wata mata sun haWu tun a lokacin zuwan shi Mali, sun dan tab'a soyayya sai gashi ta kuma dawowa rayuwarshi,. Bayan da ta fahimci ta kare mata, tun da suka hadu ta kara jan ra'ayinshi suka fara soyayyar bariki, kuma dama can yar barikin ce shima ba zai ce ba yar barikin bace domin bai san.yadda aka yi ya fada tarkonta ba."

"Tunda ta dawo rayuwarsa tayi bincike a cikin matansa wacece yafi so, a binciken ta gano Sa'adatu da"

"danta. Anan ta fara shige da fice, sai da ta cire mishi su a ranshi, sannan ta aza mishi kiyayyar Abdul Majid, idan ya ga yaron kamar zai kashe shi. Don haka yace kada ta kuma zuwa gare shi, don yaron."

"----- Bayan ta gama IT, ta koma makaranta Allah ya taimaka akwai kudi a hannunta dasu ta biya kudin makaranta, ta cigaba da karatu, suna cikin karshen zangon da zasu gama makaranta, yazo a lokacin Abdul Majid bai wuce shakara biyu da rabi ba. Da murnar yaron ya tawo gare shi, Alhaji Mamman yasa kafa yayi kwallo da Yaron, tana wanka ta ji ihun Abdul Majid, da sauri ta fito daga ban daki, ganin Alhaji Mamman Ba'are ya rufe yaron da duka, yasa ta isa wurin ta dauke shi, tana faWin. ""Yaron da babu ruwanshi me yayi da zafi?"" Kame gashin kanta yayi ya rufeta da duka, har da kwallo da ita, wulakancin da yayi mata Allah kaWai ya sani, ya kuma jan ta har cikin Wakin, haka Abdul Majid ya tafi bakin kofar yana buga kofar yana kiran sunanta ""Hajiya!"" Yana buga kofar, Alhaji Mamman Ba'are kuwa, ya kwana biyu bai tab'ata ba, haka yayi ta sukuwa akanta kamar ya samu jaka. Yana gamawa ya tashi yayi wanka ya gyara jikinshi, ya saka aka sauke musu abincin yayi tafiyarshi,"

"Bai kara waiwayarta ba, sai bayan sun gama exam ana batun zuwa bautar ™asa, ya samu tana fama da laulayi,"

"lissafi yayi kafin ya sakata gaba suka je asibiti aka duba lafiyarta, sannan suka dawo ya kuma rufe Majid da duka, ya kara saka mata doka. Tana gama bautar ™asa Masters zata wuce. Haka yasa suka zama kamar bayi, a wannan zuwan da yayi har da Hajiya Tani da ya mai da ita yar gida. Amma idanuna Harirah yana kanta, domin bata yarda da ita ba, koda tayi magana akan hakan sai da suka kwashi yan kallo. Tana ji tana gani Tani ta samu damar k'amk'ame kome a cikin gidan."

"Wato tani wata irin Shaidaniyar mace ce, da ta gallabi kanta da duk wanda yake kusa da ita. Musamman ta"

"kananaye kowa har da kannenshi da Nana, babu wanda ya isa ya d'aga mata murya. Domin idan kayi magana Alhaji Mamman Ba'are zai ce ka fita ka bar mishi gida, haka yasa kowa ya sha jinin jikinshi. Kowa ya rufawa kansa asiri, kuma ai wargi wuri yake samu. Akwai wani lokaci da Hajiya Rabi ta rufe ta da duka, ai kuwa Alhaji Mamman Ba'are yana shigowa ya samu Tani a inda Hajiya Rabi ta dake ta, babu bin ba'asi ya rufe Hajiya Rabi da duka, sannan ya kwaso mata kaya ya watsa a waje, da guzirin sakinta."

"Wannan abin ya tashi hankalin mutanen gidan, domin saura igiya daya a tsakaninsu, haka sai da aka yi da gaske"

"ya dawo da ita, ya kuma kafa mata doka, tun daga ranar Tani take zuba mulki kuma babu wanda ya isa magana, sannan itama Tani tasan cewa yana biye mata amma mafi yawan hirarsu zai sako sunan Sa'adatu. Hankalinta a tashe ta nufi wurin Malaminta ya rufe mishi baki da zuciyarshi."

***

"A Kano tayi bautar ™asa, kasancewar Abbati yazo, tana gamawa ta wuce kasarsu a can ta haifi Amaan aka turawa Alhaji Mamman Ba'are sakon haihuwarta, dake a can kamfanin labarin ya same shi, Kuma dayake aikin bai shafi jaririn ba cikin farinciki ya tsayar da dan aiken ya bashi sako ya kai musu, amma shi dai bai taka har can ba, har tayi arba'in ta koma Kano. Dan abin da taxo da shi suka cigaba da rayuwa, bai kuma zuwa ba sai da Amaan ya cika wata takwas, ya turo Alhaji Abubakar Abzin, ya kara biya mata masters ta cigaba da karatu, haka tayi ta fama da Yara biyu ga karatu, koda Alhaji Abubakar Abzin bai zo ba, akwai mutumin da yake kawo mata sako."

"Lokacin Abdul Majid yana da shekara uku da rabi, Amaan yana da shekara daya da rabi, domin har ta yaye shi. Sai"

"ga Alhaji Mamman Ba'are da Tani dauke da d'anta karami da ta haifa bata jima ba, kuma abin mamaki shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are ya kasa cewa kome akan dan na farko shi bai ce dansa ba ne, sannan kuma bai ki yaron ba, a wannan zuwa da yayi, rayuwar Abdul ta fara fuskantar matsala, abin da ya kawo haka, shine tunda suka zo gidan suka saka shi a gaba da duka, na safe daban na rana daban, idan suka mishi wannan dukar, zasu saka shi a daki a rufe shi, a manta da shi ita kanta Sa'adatu bata da ikon ciro shi, idan ta ciro shi kuwa Tani ta sakata a gaba da masifa sai kace ita ta haife ta, idan Alhaji Mamman Ba'are ya dawo kuma ta gaya mishi ya rufe ta da duka, ita uwar a wahale yaron a wahale."

A hankali Abdul Majid ya zama kamar dolo matukar Alhaji da Tani suna gidan zai na wani irin sizing kamar

"zai suma. Tsoro da firgici na Uban ya kara cika zuciyar Yaron, satin su hudu suka bar gidan, shine ya dawo daidai amma kuma sai ya xama ko sauti yaji mai karfi, zai zabura yana niman inda zai boye kanshi. Gashi zama da mutane bai saka ta saki jiki da kowa ba, haka yasa bata mu'amala da kowa."

"Wani zuwan Mahaifinta taron Malamai na Afirka, yazo ya ganshi bai tsaya ba, ya dauke shi zuwa gidan"

"Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ajiye mishi Yaron yana faWin. "" Malam Muhammad ka kalli yaron nan kamar akwai sihiri ko?"" ""Ikon Allah yanzu dan wannan yaron aka yiwa asiri haka?"" Murmushi Sheik Aliyu Wodabbe yayi ya dauki Yaron. ""Idan anyi ne don a ga bayan shi, in sha Allah ba zasu ga bayan shi ba. Sai ya zame musu gaggarabadau.."" ya dauke yaron yana murmushi, ""Alaraini kayi hakuri kada ka mai da musu sharrinsu."""

"""Ni ban musu ba, kuma ba zasu min na kyale ba. Kasan waye ni kuma kasan daga ™abilar fulanin da na fito, wallahi ba zan bari ba."" ""Don darajar Ubangiji kayi hakuri amma shi ka tsare shi."" Huci yake kafin ya sab'a yaron zai fita Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ce mishi. ""Kawo shi!"" Mikamai yaron yayi, sannan ya tafi ya koma wurin Sa'adatu. Ya tambaye ta meke faruwa da Yaron, amma bata ce kome ba sai kuka. Haka yasa shi fahimtar tana da damuwa amma ba zata fada ba, sati biyu ya yi a garin tare da tsayawa akan Yaron."

"Wannan zuwan ya zame musu alkhairi, domin kuwa har makaranta aka saka yaron, bayan tafiyarshi Alhaji"

"Mamman yazo da Tani. Hmmm ganin yaron yana makaranta da nutsuwa. Hankalinta ya tashi a wannan lokacin da ta saka mishi kahon zuka, domin kuwa duka take mishi wani lokaci idan zai tafi makarantar domin har gida ake zuwa daukar shi, amma zata hana a kai shi, duk da Sa'adatu tana son mata magana tsoron abinda zai je ya dawo yasa take rintsa idanunta."

"Bata taSa hanawa ba, sai sau daya tana laulayin cikin Aryan da aka zo za a dauke shi, Tani ta hana. Kasa hakuri tayi ta ce mata. ""Gaskiya ba zai yiwu ba, ya tafi makaranta domin ba zai zama ya rasa nutsuwa ba, a gida bai huta ba sannan a can inda zai huta kice ba zashi ba, wannan ba yi bane ."" Ta kamo danta ta fi da shi. Tana komawa cikin gidan Tani ta saka sakatar gidan zata rufeta da duka, ita dai bata san me ya faru ba, sai dai kawai an balle kofar gidan ne aka d'aga daga kan Tani da ta suma."

"Koda Alhaji Mamman Ba'are ya zo don yaji labarin abinda ya faru, shima tsorata yayi da Yanayin Sa'ade,"

"don haka ya tattara kayan Tani da d'anta. Bai kuma takowa gidan ba, har ta haifi Aryan ita da kanta tayi mishi huWuba. Haka tayi ta rayuwa can wurin danginta kamar sun manta da ita, haka shima bangaren mijinta ya manta da ita, sai da ta kai dole ta cire Abdul Majid a makaranta. Dake makarantar Sheikh Muhammad Taj Kalarawi ne,. Ya daina ganin yaron domin Allah ya daura mishi son Abdul din, wani ikon Allah sai kamar an dakatar da shi da zuwa duba su. Haka ya watsar da tunaninsu.. yara uku babu abin da zasu ci, don haka kawai ta fita ta fara aikatau, tana wanke-wanke da abinci, a bakin titi, karshe ma karatun da take ne ya tsaya, akwai wani karamci da kanawa suke dashi, kasancewarta bakuwa kuma daliba, ganin bata zuwa aka tashi wasu daga cikin dalibai suka nimo labarinta, haka yasa makarantar B.U.K suka dauki nauyin sauran lokacin da ya rage mata, wannan karamcin da suka. Mata yasa bata iya mantawa da su ba, sannan daliban tsangayar suka hada mata kudi ta kama sana'a a cikin gidan, ba sai ta fita ba."

A bangaren yaranta ta saka su a wata makarantar gwamnati. Haka suka ta rayuwa da dadi ba dad'i. Har suka gama ta

"cigaba da xama a Kano, a hankali ta rungume Yaranta, ta cigaba da sana'a idan suka cinye jarin, sai ta nemi aikatau a gidan mutane."

"Abdul Majid tun yana primary yake da kokari, sai dai daga lokacin da aka mishi tsawa, zai birkice ya koma kamar dolo, haka yasa wani lokaci yake hakura da makarantar ya zauna a gida."

"Akwai gidan da take aiki, Yaron gidan ya nimeta da lalata, ita kanta bata sani ba. Sai da ta ganta a Office din yan"

"sanda, an rufeta, tayi tayi ta musu bayani amma ina sharri aka mata, haka ta bar Yaranta a gida ,babu kowa sai Allah, tayi kuka tayi bakinciki har cewa take ita da ganin wannan rayuwar da mutuwa tayi ya fi mata, akan wannan rayuwar domin tana cikin tasku. Tun safe da Yaran suka karya har rana bata dawo ba, har dare babu labarinta, haka Abdul Majid yake goyan Aryan idan ya gaji ya sauke shi. Kwana suka yi babu kowa a gidan sunyi kuka har sun yi shiru. Washi gari da safe suka tashi babu Mamansu. Har rana bata dawo ba, dalilin da yasa Abdul Majid ya fita bakin shagon unguwar kenan ya sato bread,. Babu wanda ya lura da halin da suke ciki."

"Haka aka rufe shi da duka yana rungume da bread din, yaki sakewa sai dukan shi ake yi, makocin sune ya ga"

"ana ta dukar shi, shine ya karbe shi. An farfasa mishi jiki. Mutumin da yake lura da shige da ficen su, yaga yau bai ga Mamansu ba. ""Abdul Ina Mamanku?"" Yana sheshekar kuka ya ce bata dawo ba, har lokacin yana rungume da bread din,. ""Me yasa ka daukar musu bread."" ""Aryan da Amaan yunwa suke ji Hajiya bata dawo ba."" Jikin mutanen da suka dake shi ne yayi sanyi. ""Nawa ne kudin bread din?"""

"""Dari ce!"" Biyan kudin yayi ya saka yaron a gaba har gida, ""ina mamarku take aiki?"""

"""Ta can ne?"""

"""Tow ka jira ni ina zuwa."" ""Tow!"" Gidan shi ya koma ya amso musu kunu da dumammen tuwo, ya kawo musu Aryan da Amaan suka ci sai da suka kusan cinyewa sannan suka koshi, Aryan ya koma ya kwanta sannan Abdul Majid yaci kadan ya bar musu, yadda Mamansu take yi ta ci kadan ta bar musu sauran...."

~~~~~~~~~~~~~~

"```Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136```"

#Mai_Dambuje.

"[2/17, 5:06 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*016*

"Mutumin nan bai yi kasa a gwiwa wurin neman Mutanen unguwar tare da mai unguwa, ya zauna a tsakiyarsu ya ce musu. ""Akwai matar nan yar kasar Nijar, tow gaskiya a da ina ganin mijinta yana zuwa, amma a yanzu an dauki shekara biyu ban ga mijin yazo ba, sanan ita kuma tana yawan fita aikatau domin ina yawan ganinta ta fita da sassafe ta dawo da la'asar lis, tow kada na kaiku da nisa Matar nan dai jiya bata kwana a gida ba, sannan ku yi nazarin idan mune ya zamu ji? Sannan yarinya ce domin bata kai talatin ba, don Allah ku duba lamarin."""

"""Hmmm! Waye ya sani ko yawon bin maza ta tafi."" Inji wani mutum a wurin, tsawa limamin unguwar yayi mishi. ""Mene ne hujjarka?"" Sunkuyar da kai yayi, kafin liman ya ce. ""A yanzu muje gidan, ko akwai yaron da zai fada mana inda take zuwa aiki."" Haka suka mike bakiWayansu, suka tafi har gidan, sun samu Aryan yayi kashi ya b'ata jikinshi. Haka Mutumin farko ya kira Matarshi ta wanke su, sannan ta dauko musu kayan Yaranta, suka kasa sannan ta riko hannun Abdul Majid suka fito. ""Abdul Majid!"" ""Hmmm!"" Ya fada yana komawa gefe, domin har yau yana fama da rashin sakewa. ""Kasan gidan da Mamanku take zuwa aiki?"" Gyada kai yayi. ""Ok Maman Luba tafi da sauran, bari ya kai mu inda take zuwa aiki."""

"Haka suka saka Abdul Majid a gaba, har gidan dake tana zuwa da shi yana taimaka mata da Aryan yana wasa da shi, koda suka zo gidan babu wanda ya yarda yayi musu maganar Sa'adatu, sannan babu wanda ya kula su, sai da yan unguwar suke gayawa musu ai tun jiya da hantsi yan sanda suka tafi da ita office dinsu."

"Ba karamin kaduwa suka yi ba, domin kuwa har an rasa me magana, haka suka mai da Abdul gida, sannan wasu"

"suka wuce kasuwa, wasu kuma suka hakura da kasuwa suka nufi Office din yan sanda nimanta. Musamman Baban Luba mutumin

Please Login or Register in order to submit comment