You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wakinsa, An bankaWo wani babban al'amari game da shi, in da lamarin mutuwar matarsa ya sha ban-ban da abun da aka sanar game da rasuwar ta ta, ashe ´an bindiga ne suka yi garkuwa da mai Wakinsa, har ta haihu a hannunsu, daga ™arshe ta rasa ranta."

"A wata majiyar kuma, aka ce da sanya hannunsa a yin garkuwa da matar ta sa in da ya kasheta yayi tsafi da gangar jikinta, kwatsam wata yarinya ta zo da jariri a zuwan Wan matarsa ne, duk dan a Satar da hankalin mutane, da tunaninsu daga kan zargin shi wannan za™a™urin bawa da yake jin cewa ya fi kowa gaskiya da adalci, masu bibiyarmu ko menene ra'ayinku game da wannan labari?!"

"Hannun adam har rawa yake yi a lokacin da ya kammala karanta labarin, wani irin wahalallen gumi ya din ga"

"tsatstsafo masa, ya aka yi maganar nan ta fita? Waye ya yi masa wannan yankan bayan?."

"Jiki na rawa ya ajiye wayar, ya mi™e tsaye, jin kansa ya fara sarawa, yana neman rasa nustuwarsa, bashir ya tashi zai yi masa magana, amma tuni adam ya sulale ya bar wurin."

"Kafin ya cimmasa, ya hau motarsa yayu mata key, ya fice daga restaurant Win da gudu."

08081012143

"*Paid book ne ¦ 500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*"

"Gudu yake sosai a kan titi, Bashir ya hau motarsa ya bi bayansa, amma ya kasa cimmasa."

"Ko da Adam ya ™arasa gida, wani irin horn ya din ga yi kamar tashin hankali. A gigice masu tsaron ™ofar suka buWe masa gate ya shiga da motar, ko da ya fito ko rufeta bai yi ba ya wuce sashin Ammi."

"A can cikin gidan kuwa, bayan sallar isha'i, wata hadima ta shiga ta sanar da ammi cewar mummy na son ganinta."

"Mamaki ne ya cika ammi, meya kawo mummy a wannan lokacin? Ba tare da wani Sata lokaci ba, ta tashi ta fita falonta, ta tarar da mummyn tare da autarta ru™ayya."

"Ta kalli ammi ta yi murmushi ta ce ""Barka da warhaka giwar mata""."

"""Barkanki dai, kuna lafiya?"""

"""Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?"""

"Ammi ta amsa da ""Alhamdilillah"""

"""To Allah ya ji™anta da rahama"""

"""Amin ya rabb"""

"Mummy ta gyara zamanta ta ce ""To, ni dai giwa idan wani abun na yi miki dan Allah ki yafe mini, ban san me na yi"

"miki haka ba, ai ko ban samu shigowa ba, ya kyautu a ce kin aika mini jaririn na gani, nima jiakana ne, amma har su Fauziyya suka zo aka hanasu jaririn, yaran nan ko muna so ko ba ma so tsatsonsu Waya fa, wannan abun babu in da zai kaimu, ni dai ki yafe mini, amma a bani yaron na ganshi"""

"Ammi ta Wan dubi mummy, kamar ba a wurin zaman makoki suka din ga yi da ita a gabanta suna yasar mata da"

"maganganu ba, ta basar ta ce ""Bari a kawo shi ki ganshi"" tayi maganar ba tare da ta tanka wancan maganganun da ta yi da fari ba."

"Iman ce ta Wauko sabir, ta kawo wa mummy shi, ta sanya hannu ta karSe shi, tana wani irin murmushi ta ce"

"""Tubarkallah masha Allah, wannan yayi wayo sosai, sai dai ni kasa gane ma da wa yake kama a tsakanin aishar da takawa"""

Ammi kawai ta kalleta ba ta ce komai ba.

"""To wane sunan aka saka masa?"""

"""Mahmud, ana kiransa sabir""."

"Da sauri Mummy ta kalli Ammi ta ce ""Mahmud kuma? Sunan Mahmud ya ci kenan?"""

"Ammi ta ce ""Eh, sunansa ya mayar masa"""

"Mummy za ta yi magana, Adam ya faWo Wakin kamar wanda ya ™wato a hannun miyagu."

"Tun a falon ya fara Salle rigarsa, saboda wani irin gumi da yake yi, ™afafuwansa kamar ba zasu iya Waukarsa ba."

"A gigice ammi ta tashi ta bi shi tana kiran sunansa, sai dai bai iya tsayawa ba, Mummy ma tashin ta yi ta bi bayansu,"

tana tambayar ko lafiya.

"Kan gadon ammi ya haye, jikinsa ya fara wannan mazarin, kamar wanda ake bugawa gangi."

"A gigice ammi ta ce ""Iman, Wauko maganinsa maza"""

"Da hanzari iman ta fita ta bar Wakin, ammi Cikin damuwa ta ce ""Takawa meyafaru ne? Meyake damunka?"" Bai amsa"

"mata ba, sai runtse idanuwansa da ya yi."

"Iman ta dawo da jarkar maganin da ake shafa masa, ta buWe ta tsiyayo, ta fara ™o™arin shafa masa, amma ya juya"

"kansa ya ce ""Kar ki shafa mini, a hayyacina nake, jikina zai daina rawar ne, ku lulluSeni"" duk yadda ammi ta so shafa masa ™in yarda ya yi, sai lulluSe shi da aka yi."

"Bin maganin da kallo Mummy ta din ga yi, sannan ta ce ""Wai giwa harzuwa wani lokacin zaki bar yaron nan ya cigaba"

"da rayuwa da wannan larurar ba tare da kin nema masa magani ba?"""

"""Ina iya ™o™arina, Allah ne bai kawo ™arshen abun ba"""

"""To kina zaune Allah za kawo ™arshen lamarin, shi meye wannan Win da ake shafa masa?"" Ganin ammi ba ta bata amsa ba ya sanya iman cewa ""Magani ne"""

"""Mi™o mini na gani"" ta yi maganar tana tsare iman da ido, iman ta Wauka ta mi™a mata, ta karSi jarkar ta din ga"

"jujjuyata, tana nazartar meye a ciki, amma ta kasa ganewa, ta ajiye robar ta ce ""Shikenan, ga wannan yaron, amma akwai bu™atar ki mi™e tsaye fiye da da, ko kuma ya dauwwama cikin nakasa"" kamar dai Wazu, a yanzun ma ba ta samu amsa daga ammin ba."

"Bashir kuwa tun da ya ga Adam ya Sace masa, ya ha™ura ya koma, dan bashi da tabbacin in da zai nufa ya bi adam"

"Win, kuma ya kira shi bai Waga wayarsa ba."

***

"Rumaisa kuwa zazzage kayanta ta yi da aka bata, na wurin Ammi da na turaki. Turmi biyar ammi ta bata na atamfar tare da turare mai ™amshin gaske."

"Turaki kuma ya sanya an cika mata ledoji da kayan dubulan, da uban kilishi fal da soyayyen naman kaza, sai kuma turaruka, ga kuma nono mai kyau kusan galan guda da man shanu. Ruma ta din ga yashe baki tana murna."

"Mama ta ce ""Eh dole ki yi murna mana, a dalilinsa kin samu iyayensa sun yi miki sha tara ta arziki ke kuma kina yi wa"

"Wan su rashin mutunci"""

"Ruma a ranta ta ce ""Hmm mama ba zaki gane bane ba, baki san girman laifin da mutumin nan yayi mini ba, sai na"

"tabattar masa da abun da na gaya masa ai"" mama ta yi ta mita, amma ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai ma tunanin gobe in Allah ya kaimu za ta koma makaranta abun da ba ta so."

"Sai da ta zo kwanciya barcci, sannan wata irin kewar sabir ta sake kamata, ta rungume fulonta, ta rintse idonta, ta"

din ga hango fuskarsa yana kallonta yana lumshe idonsa.

"Kamar an kunnawa zuciyarta wuta, haka ta din ga jin wata irin ™ishirwar son sake ganin sabir, tamkar ta yi tsuntsuwa ta tashi. Ta sake rintse idonta, tana sake tuna yadda take kwana gata sabir a asibiti, ganinsa da ta yi yau ta sake jin du rintsi duk wuya sai an bata Wan ta."

"Haka kurum ta hau kuka, tana sake jin tsana da haushin adam a zuciyarta, a ganinta duk shi ya ™ulla a ™wace sabir a hanata shi."

"Cikin ikon Allah, takawa ya farfaWo gaba Waya, ammi ta saka shi a gaba ta din ga tambayarsa a kan meyafaru har ya shiga wannan yanayin."

"Ya Soye ya™i gayawa ammi dalili, ya ce mata bakomai, kamar kullum ta din ga yi masa nasiha tare da fatan Allah ya"

bashi lafiya da mafita a kan lamuransa.

"Washegari da safe rumaisa kamar ta saka kuka, mai sunan baba ya kafa ya tsare, ya sanya rumaisa a gaba ta shirya"

"cikin uniform Win ta da suka sha guga, kamar ta fashe saboda takaici, ba ta son makarantar nan, ya sakata a gaba ya tafi kaita makaranta."

"A ofishin shugaban makarantar ma, sake jajantawa rumaisa abun da ya sameta malamai suka yi, suka yi mata barka"

da dawowa tare da fatan Allah ya sanya ta nutsu zamanta a hannun ´an bindiga ya zame mata darasi.

"Gaba daya hankalinta ba ya kansu, tunaninnta kawai yadda za ta ga sabir, mai sunan baba ya gama clearing Win abun da yakamata, aka ce ta tafi aji, amma ajin baya zata koma saboda an riga an yi mata nisa a karatu."

"""Kaii repeating aka yi mini, kenan ba zan yi candy da wuri ba, taS wallahi ba..."" Gum ta rufe bakinta ba ta ™arasa maganar ba, saboda kallon da mai sunan baba yayi mata, tana ji tana gani aka mayar da ita ajin baya."

"A ranta ta ce 'Wallahi ba zan zauna a ajin baya ba, sai a zata ma da™i™anci ne ya saka aka yi mata repeating"""

"Da aka fita break, ´an ajinsu da suka yi gaba, suka din ga tsalle suna murna, rumaisa ta dawo."

"Sam ta ™i shiga sabgar kowa, ta Wau littafinta ta din ga zana hoton sabir a bayan litattafan ta. Har aka tashi ba ta san me aka yi ba."

"Da ta koma gida mama tana ta murna, tana tambayarta ya aka yi a makarantar?"

"Rai a Sace ruma ta ce ""saboda tsabar tsanar da mai sunan baba yayi mini, ya sa aka yi mini repeating, wallahi ba zan"

"zauna a ajin nan ba, ni ajin yan candy ma zan koma"" ganin rumaisa za ta Sata rai, ya sanya ta shareta."

"Can rumaisa ta kuma cewa ""Mama dan Allah in anjima, ki ce yasir ya rakani gidan su hauwwaliya na duba ™afarta"""

"Mama ta ce ""Kuma kin yi tunani mai kyau, kya je ki gaishe su, su ga kin warware sosai, amma sai gobe in Allah ya"

"kaimu"""

"""Dan Allah mama in je yau"""

"""Goben in Allah ya kaimu ma sai na ce ba zaki je ba"""

"""To ki yi ha™uri, Allah ya kaimu goben""."

"Adam kuwa gaba Waya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar sa™on ko jabir ya zo, a bashi"

ha™uri ba zai iya ganin kowa ba.

"Ya kulle kansa a Waki, ya kunna wayarsa ya hau social media, ya ga yadda labari ya baza ko in, ga tarin kiran waya da sa™onni daga ´an jarida, mutane sai comments suke kala-kala."

"Ganin wayar na neman caza masa kai, ya sanya yayi jifa da wayar, gaba Waya ya ji ya rasa ™warin gwiwar da zai sake fuskantar duniya, da ™udurinsa na son kawo ™arshen yi wa ™asa da harkar tsaro Sarna. Ya ji ya rasa ™warin gwiwar bincikar waWanda suka yi garkuwa da matarsa."

"Sai da Ammi ta yi da gaske, sannan ya buWe Wakinsa, har ya samu ya ci abinci, amma bai gaya mata abun da yake"

"faruwa ba, saboda kar ya sake Waga mata hankali."

"Rumaisa yau ji take yi kamar salla, saboda yau zata kuma zuwa ta gano Sabir, dan a yanzu babu abun da yake faranta"

mata rai sama da haka.

"Yau da rumaisa ta je makaranta, ™in zama ta yi a ajin da aka kaita, ta tafi ajinsu ta yi zamant, ta ce ba ta ga wanda ya isa yayi mata repeating ba, sai dai a gaji a koreta daga makaranta gaba Waya, wanda da za ayi mata haka da shi ta fi so, dan ita ba ™aunar makarantar take yi ba."

"Mai martaba a yau da kansa ya dira a gidan su takawa, wanda hakan ya sa gidan ya cika ma™il da hadimai, da"

"jami'an tsaro, masu kaiwa suna komowa, tun daga farkon titin har cikin gidan. Bai sauka a ko ina ba, sai a sashen Ammi."

"Mummy na jin labarin zuwan mai marataba, ta tarkato yaranta ta bazamo sashin ammi, da sunan zuwa kwasar gaisuwa a wurin mai martaba sarki."

"˜afa da ™afa ya zo ya yi wa Adam ta'aziyyar mutuwar aisha, sakamakon baya gari lokacin da abun ya faru."

"Mai martaba ya numfasa ya ce ""Turaki yayi mana bayanin komai yadda al'amarin ya faru, sai dai bai kamata a"

"Soyewa duniya gaskiyar abun da ya faru ba, ma™iya za su iya amfani da wannan damar, wurin cutar da kai, kamar yadda zancen ya fasu har wata gidan jarida suka wallafa, kuma ba zai wuce saboda ™o™arin da ake yi wa ™asa ba, ya sanya miyagu ke ta ™o™arin bayyana laifinka, amma ayi ha™uri a daure, a cigaba da abun da ake yi kar a fasa Allah zai shiga lamarin"""

"Adam ya risuna ya ce ""In sha Allah, muna fatan mai martaba ya cigaba da sanya mu a addu'a""."

"""Addu'a kullum cikin yi muku ake, kuma ko dan albarkacin mu babu wani abu da wani zai iya yi ya cutar da ku a kan"

"gaskiya a ™asar nan, a cigaba da ™o™ari. Ita kuma 'yar mu Allah ya ji™anta ya raya mini wannan kyakykyawan jikan nawa"" yayi maganar yana shafa kan Sabir da yake hannunsa."

"Mummy ta risuna tana ""Allah ya taimaki mai martaba, mun gode da wannan karamci, Ubangiji Allah ya ™ara girma da Waukaka ya ™ara maka lafiya da nisan kwana"""

"""An gaisheki amaryar Galadima, , ´ar malam kin ™i halin malam, mai martaba ya amsa kuma yana godiya"" wani irin"

"takaici ne ya kama mummy, jin yadda hadimin mai martaba ya amsa mata."

"Aka karSi jaririn aka mi™awa ammi, shamaki ya dubi ammi ya ce ""Mai martaba ya bawa jariri gidaje guda biyu, ya"

"bashi dawakai guda uku, sannan mai martaba ya yi umarnin a gina masallaci sadaka ga mahaifiyarsa. Sannan idan ya shekara uku a duniya mai martaba ya ce a kai shi umara"""

"Nan dogarai suka Wauka da ""Godiya yake mai martaba, godiya yake Allah ya baka yawan nasara. Mai bayarwa da"

"dama hagu ba ta sani ba"""

"Takawa ma risinawa yayi, suna yi wa mai martaba godiya."

"Dogaransa suka kare shi ya tashi tsaye, har zai fita ya hangi iman a gefe a zaune."

"Ya ce ""Ahhh giwa, wannan buzuwar ´ar ta ki tana nan dama, ko da yake an ce mini bafullatana ce? ta daina zuwar"

"mana, Allah ya ji™an mai babban Waki, lokacin da muka kai mata ziyara a Saudiyya kan ta rasu, take tambayar ina wannan buzuwar ´ar ta giwar Galadima, a lokacin bamu sani ba ko kuna tare ko kin mayar da ita, mai babban Waki tana sonta"""

"Ammi ta yi murmushi ta ce ""A'a muna tare mai martaba, ai tun da kuka saka baki a kan maganar nan, muke tare da"

"ita"""

"""Allah sarki, baki fuskanci wani abu ba binta, wata™ila albarkacin yarinyar nan ne Allah ya kawo muku yaron nan"

"cikin aminci, Ubangiji Allah ya yi jagora, Allah ya raya mana su baki Waya"""

Ammi ta amsa da amin mai martaba.

"Ba ™aramin ™ulewa Mummy ta yi ba, yadda mai martaba ya mayar da hankali a kan yaran ammi, har da agola, amma"

ita ko kanta bai bi ba.

"Mai martaba na tafiya, mummy ta fice fuuuuu ta bar sashin ita da su Fauziyya."

"Bayan fitar su Ammi ta ce ""Iman, mun yi laifi fa daina zuwa gidan mai martaba da ki ka yi, balle ki je gaishe shi, kin"

"ga har ya magantu, Allah sarki mai babban Waki, lokacin kina ™arama rigingimun da aka yi ta yi a kan ki, cewa ta yi sai na bata ke, na din ga kuka, ita tsaya mini a kan ri™onki""."

"Iman ta ce ""Ammi tsoron zuwa gidan nake, fulanin yola ta hana ni zuwa, saboda yarima Hashim, kin san ai abun da"

"aka yi mini su da Mummy"""

"Ammi ta ce ""Na ji, kar ki yi kuka, jikina na bani mijinki mutum ne na gani na faWa, karki damu autata"""

"Kunya ce ta kama Iman, Nusaiba ta ce ""To ni fa, ko ita kaWai ake yi wa Addu'a"""

"""Ke dai nusaiba baki da girma sai na jikinki, kishi ki ke iman Win?"""

"""To shikenan ma, ni na yi zuciya"" Nusaiba ta tashi za ta fita, iman ta tashi ta bita da gudu tana yi mata dariya."

"Ammi ta mayar da hankali a kan adam, da fuskarsa sam babu walwala, ta dube shi a tsanake ta ce ""Mai martaba"

"yake magana a kai ne, na ji yana cewa an yi amfani da gaskiyar abun da ya faru ana sukarka, meyafaru?"""

"Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Wata gidan jarida ne suka yi posting a social media, cewar aisha ta mutu a hannun 'yan"

"bindiga, ko kuma ni na kasheta na yi tsafi da gangar jikinta tun da ba aga gawarta ba ma"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, adam waye ya aikata wannan abun? Waye ya fitar da wannan zancen har da sharri"

"haka?"""

"""Nima ban sani ba, Wazu na Wauko wayata a mota, kira daban-daban da sa™onni daga ´an jaridu, suna bu™atar wai"

"na ce wani abu a kan lamarin na kashe wayar ma gaba Waya""."

"Ammi ta dafe kai, ta rasa me ma za ta ce ko ta yi? Abubuwa kullum sake rikicewa suke yi."

"Da la'asar yasir ba dan yana so ba, ya saka rumaisa a gaba zai kaita cikin gari, suna tafe yana mita, sai da suka je titi,"

"sannan rumaisa ta ce ""Dan Allah Yasir taimakona zaka yi"""

"""Taimakon me?"""

"""Dan Allah gidan su sabir zaka rakani na je na ganshi"" wani mugun kallo ya yi mata ya ce ""Ba zani ba, yaushe ki ka je"

"ki ka ganshi? Ba zani ba ba nan muka yi da mama ba""."

"Ri™e hannunsa ruma ta yi ta fara kuka ""Dan Allah yasir, wallahi na kasa bacci jiya, ba zamu daWe ba dan girman"

"Allah"" ganin tana kuka ya sanya jikinsa yin sanyi."

"""Kin yarda zaki wanke mini uniform, ki Waukar mini jakata zuwa islamiyyar"""

"Da sauri ta ce ""Eh wallahi na yarda"""

"""Shikenan mu je, saura idan bu™atar ki ta biya, ki yi mini rashin kunya""."

"""Ai ba ma zan yi ba"""

"Ya tarar musu abun hawa, suka hau suka tafi."

"Suna tafe yasir yana danna waya, can ya ce ""Kaii"""

"Ruma ta ce ""Menene?"""

"""Wani labari na gani, ke dama baban sabir Win nan shi ne Adam Sharif Galadima?"""

"""Wai wannan mai tona asirin mutanen, ba wani nan ba shi ne ba"""

"""Dan ubanki ™arya zan yi miki?"""

"Rumaisa ta ce ""TaS, ba shi bane ba, shi wannan yana abun arziki ne?"""

"Yasir ya ce ""Ke ba wannan ba, wani labari aka wallafa wai, ya sayar da matarsa yayi tsafi da gangar jikinta, kuma"

"jaririn da aka ce nasa ne, ™arya ne rainawa mutane hankali ake"""

"Wani takaici ne ya turnu™e rumaisa ta ce ""In ji uban wa?"""

"'oho, wani gidan jarida ne suka wallafa"""

"Rumaisa ta ce ""To rubuta musu ka ce ™arya suke yi, wannan yaron nice nan na zo da shi"""

"Yasir ya ajiye wayar ya ce ""A'a ba ruwana"""

"Rumaisa ta ce ""Zan yi waya katsina a kawo mini wayata ni na rubuta, wannan ai sharri ne"""

"""Ke dalla rufewa mutane baki, zaki saka na ™i rakakin wallahi"""

"Ta ri™e bakinta ta ce ""Na daina in sha Allah"""

"Da haka suka ™arasa gidan su Adam, rumaisa har da Wan tsalle za su je ta ga Sabir."

"Sai dai rumaisa ta yi ta mamakin ganin layin duk kashin dawakai, duk da abun mamaki bane, amma yanayin wurin ya"

nuna an yi wani sha'ani a wurin.

"Yanzu babu wanda yake yi wa rumaisa shamaki da shiga sashen ammi, sai dai ta jira ta ce wurin ammi suka zo, ak"

shiga da su sashen Ammi.

"Ko da ammi ta ga rumaisa sai da mamaki ya kama ta, shekaranjiya rumaisan ta zo, yau ma kuma gata."

"Ammi ta Soye mamakinta, ta yi musu maraba, a nutse Yasir yake gaida Ammi, rumaisa kuwa ko gaisawar ba ayi ba, ta koma kusa da ammi ta Wau Sabir."

"Shi kansa takawa kallon rumaisan take, wannan nacin na ta ya fara yawa."

"""Rumaisa ya mamanki"""

"""Tana lafiya ™alau"" ta ™arasa maganar tana jujjuya sabir da yake bacci, wai sai ya tashi ya ganta."

"Hakan kuwa aka yi sai da sabir ya buWe ido yana mi™a, wasa rumaisa ta yi masa, ya geSare baki ya fara murmushi."

"""Laaa kun ga, yayi mini dariya, Yasir kalli yana yi mini dariya, ya gane ni, sabir ummanka ce rumaisa ka gane ni ko?"""

"Ammi ta ce ""Ikon Allah, ko bacci bai fiye dariya ba, lallai ya ganeki, ke ya fara yi wa dariya""."

"""Kaii dama kewarsa ce ke damuna, na yi ta mafarkinsa, na cewa mama a rakani mandawari na duba ´ar uwarmu Hauwwaliya, na cewa yasir dan Allah ya rakoni na ga sabir Wina"""

"Ammi kallonta take tana murmushi, tana jin daWin yadda sabir ke yi wa rumaisa murmushi."

"""Rumaisa baku gaisa da baban sabir ba"" ruma ta Wago ta kalleshi ta ce ""Ni ma bai kulani ba, yauwwa ammi wai da"

"gaske shi yake shayar da shi?"""

"""Shi wa?"""

"Rumaisa ta nuna Adam ta ce ""Haka ya ce mini, wai idan aka bani sabir bani da abun da zan shayar da shi, na ce masa ana bashi madara, wai ba a bashi madara shine yake bashi abun da ake bawa jarirai wai ni idan an bani sabir me zan bashi?"""

"Paid book ne ¦ 500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*"

"Dariya ce ta kuwa kufcewa ammi, ta ce ""A'a rumaisa wannan maganar dai taku ce ba tawa ba"""

"Takawa dai ko kallonta bai yi ba, dan ya fuskanci yarinyar ba ta da kunya sam."

"""Amma dai ammi ai ni ban taSa ganin maza suna shayarwa ba, shi kuma ya ce mini haka, kuma dai na ga shima"

"™irjinsa babu komai"""

"Ammi rasa amsar da za ta bawa rumaisa ta yi, can sai hankalin rumaisa ya Wauke daga kan maganar."

"""Ammi"" ta faWa a hankali."

"""Na'am umman sabir"""

"Rumaisa ta washe baki ta ce ""Wayyo daWi, ammi na ji daWi, Allah ya amsa dukkanin bu™atinki, na fili da na Soye ya biya miki bu™atunki na alkhairi, na ji daWi da ki ka kirani umman sabir"""

"""Amin rumaisa, in dai kin ji daWi, ina son ki din ga saka baban sabir a addu'a, Allah ya biya masa bu™atunsa""."

"""To ammi, ai saboda ke zan yi masa addu'a ba dan halinsa ba"""

"""Subhanallah, meye da halin nasa?"""

"""Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne"""

"Wani ™arfin hali sai rumaisa, mace da Wan ta, amma tana faWin ba ta san halinsa ba ne."

"Ammi ta ce ""Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da"

"shiga sabgar mutane""."

"""To ni dai saboda ke zan yi masa addu'a kawai"""

"""Yauwwa rumaisa, ma™iya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir"

"ba Wan sa bane ba"""

"Ruma ta waro ido ta ce ""Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala'i, to"

"shi kuma yayi shiru"" ta yi maganar tana ™are masa kallo."

"Sai kuma ta sake cewa ""To shine yayi kuka da aka faWi haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?""."

"""A'a ba kuka ya yi ba, addu'a dai zaki din ga yi masa"""

"Ruma ta ce ""TaS, ammi kin san wani abu?""."

"Ammi ta ce ""A'a""."

"""Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a"

"unguwarmu ce mini ake ™anwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da ´an unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faWa. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko....."

"Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa ""Bari mu tashi mu tafi""."

"Ammi ta girgiza masa kai, ta ce ""Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir"""

"Ta sake gyara zama ta ce ""Tun da na fuskanci ´an unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi"

"mini ba zance na yi ba. Allah kaWai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa

Please Login or Register in order to submit comment