You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wanda"

"suka rasu, babu wadda nake jin daWinta nake zartar da hukunci komai Wacinsa ta karSa sai Aisha. Na tafka babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba, Allahn da ya bani ya fi ni son ta, ban so ta mutu a wula™ance haka ba, sai dai ba zan zargi sirikina ba, Wana ne shima, kuma ba zai cutara da aisha ba"""

"Rumaisa da hawaye ya fara zubo mata ta ce ""Tabbas anty aisha tana da kirki, kowa cewa yake yi bana jin magana,"

"amma ita ta fara cewa rashin ji na yana burgeta. A makaranta bana gan karatu, amma ta ce mini mai kaifin basira ce ni, ta yi ta kula da ni a hannun 'yan bindiga kan ta rasu, amma mijinta ne ba shi da kirki ko kaWan, shiyasa na™i magana a gabansa""."

"Turaki ya yi murmushi ya ce ""Tabbas takawa yana da zafin rai, amma mutumin kirki ne sosai""."

"""Na san a ™ule yake da ni, yanzu ba dan kai ba tsaf sai ya zaneni a wurin nan, ita rayuwa idan mutum yana son ya ci"

"ribar abu ba ha™uri ake a bishi a sannu ba? Idan haka zai din ga yi komai ya tunkara sai ya faWi. Kuma dai naga Wan sanda ne shi, mai ya hana ya kai mana agaji lokacin muna hannun 'yan bindigar, da bakinsu fa suka ce jami'an tsaro ne suke basu gudunmawa, to yanzu kuma dan Allah me zai yi bayan mai faruwa ta faru""."

"Zuba mata ido kawai turaki yayi, yadda take zaro magana, tana arranging Win ta, tamakar tana karantowa, kuma ba"

zaka taSa cewa yarinya ce mai kamar shekarunta take faWa ba.

"Ya gyara zamansa ya ce ""Haka ne, kema kin yi magana mai kyau, amma yanzu dai ina jin ki""."

"""Baba"""

"Ya ce ""Na'am yarinyar kirki"""

"""Amanatun amana, zan gaya maka komai, gani ake ni Yarinya ce amma ina da wayona, ta ™arfin tsiya fa ya ™wace"

"mini Wa, ko tausayina ba ya ji alhalin anty aisha ta ce ta bar mini shi halak malak. Zan gaya maka komai, amma shi ba zan gaya masa ba, kuma wallahi na san abubuwan da shi bai sani ba""."

"Duk girman turaki, ruma ta iya kallonsa ta ce masa amanatun amana, tare da yi masa kashedin, kar ya gaya wa kowa"

abun da za ta gaya masa.

"˜warin gwiwar ta, da rashin tsoronta a ™ananun shekarunta ne ya fi bashi mamaki, kuma tsara zancenta da kaifin basirarta ya burge shi."

"Ya ce ""Kar ki damu, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai ke sai Allah""."

"Nan rumaisa ta gyara zama ta fara yi masa bayanin abubuwan da suka faru, duk a hirarta ta ya fuskanci ba komai ta"

"gaya masa ba, amma a hakan ta yi ™o™arin yi masa duk wasu bayanai da yakamata ya sani, sai dai kan ta kammala, hawaye ya wanke mata fuska, sai gogewa take da hijjabinta."

"Shi kansa turaki kasa jurewa yayi, cikin dabara ya goge hawayen da yake shirin zubo masa, yana jin labarin wai-wai a kafafen watsa labarai, bai taSa zaton masifa da tashin hankalin ya kai haka ba, kuma ta bakin rumaisa ne idan aka fara haWawa da 'ya'yan masu faWa a ji ana sacewa wata™ila a mayar da hankali a kan maganin abun, kuma abun kunya ne ga jami'an tsaro, ace an sace matar jami'in tsaro kuma an kasa ceto ta har ta rasa ranta."

"Uwa uba azabar da rumaisa ta sha kan ta fito da jaririn, shi kansa ya isa abun tausayi duba da ™ananan shekarunta, gashi sai nanatawa take ita fa aisha ta bar mata Wa, amma adam ya ™wace mata."

"Ya duba gefen sa, ya Wauko wani handkerchief mai matu™ar kyau da taushi, sai ™amshi yake yi, ya mi™awa rumaisa"

"ya ce ""karSi nan ki goge hawayenki, kukan ya isa haka""."

"KarSa ta yi, amma ta kasa gogewar, saboda kukan da ya ci ™arfinta."

"Usman kuwa ba ™aramar mita yayi ba, a kan abun da rumaisa ta yi, tun da suka fito yake mita."

"""Ban taSa ganin yarinya mai azababben taurin kai, na tashin hankali kamar rumaisa ba, gaba Waya yarinya kamar wata majanuniya, ita duk wata hanya ta masalaha ba ta santa ba, idan ta akasin masalahar ma aka biyo mata ta fi misbehaving, ba a gane gabanta da bayanta kamar Wan wake""."

"Adam kam azabar takaici, bai bari ya iya tankawa ba, gani yake gaba Waya yarinyar ta gama raina masa hankali."

"A nutse turaki ya din ga rarrashin rumaisa, yana yi mata nasiha, har sai da ya sanya ta Wan yi murmushi ta ce ""Baba"

"ka iya magana a nutse wallahi, ni yadda kake magana ma daWi yake yi mini"""

"Abun da ta faWa Win sai da shi ma ya sanya shi murmushi, ta kai handkerchief Win da ya bata fuskarta,"

"Ta lumshe idonta ta ce ""Wayyo ™amshi, baba ban taSa jin turare mai daWin wannan ba, kamar na suma dan daWi""."

"Jan rawaninsa yayi ya rufe fuskarsa, dan dariya rumaisa take neman ta saka shi."

"Hadimai ne suka yi sallama, suka shigo masa da kwanukan abinci a kuloli da kuma akushi, aka zo aka jere su a"

gabansa.

Rumaisa ta dinga kallon fulasai na alfarma.

"Turaki ya ce ""Ga abinci nan, buWe a ciki ki zaSi wanda ki ke so ki ci""."

"""A'a na ™oshi, mama ta hanani cin abinci a waje""."

"""To ai nan gidanku ne, ki ci duk abun da ki ke so""."

"Ta nuna masa akushi ta ce ""Wannan menene?""."

"Ya Wauko akushin ya ajiye a gabanta ya ce ""Sunansa akushi""."

"""Akushi da rufi, sai sarki, kenan kai ma sarki ne?"""

"Ya girgiza mata kai ya ce ""A'a, ni ba sarki bane ba""."

"""To dama ba duk masu rawani ba sunansu sarki ba"""

"Turaki ya murmusa ya ce ""A'a ba kowane mai rawani ne sarki ba, kowa akwai sunan mu™aminsa"""

"Ruma ta din ga kallon akushin nan, ta saka hannu ta buWe, ta ga dubulan fal a ciki"" tayi iya ™o™arinta wurin tuna sunan sa amma ta kasa ta ce ""Mmm ya ma, abun da ake kaiwa idan an yi aure mai sugan nan sunan shi kenan""."

"Ya kuma mi™o mata wani akushin, ya ce ""Gashi nan, duk duba ki ci wanda ki ke so""."

"Ta bubbuWe kulolin nan, wata irin miya ta alfarma, ta sha naman kaza yanka manya manya. Ta ce ""Mama ta yi mini"

"kashedi a kan banda rashin ji, kuma idan na yi wani rashin ji, yaya usman ya gaya mata zaneni za su yi""."

"Turaki da bai ji ya gaji da surutun rumaisa ba, kuma bai jin zai gajin ya ce ""Ki ci ba zan gaya masa ba, ba zata sani ba""."

"""Hmm ba ka san halin mama ba, yaya usman sai ya gane, amma dai bari na ci wannan""."

"Ta saka hannu ta Wau dubulan, ta fara ci, dama rumaisa gata mayyar suga, tana ci tana lashe baki."

"Kallon rumaisa kawai yake yana murmushi, yarinya ce ™arama, ita a yanzu babu abun da yake damunta, sai dai ta yi"

"ciye-ciyenta ta faWi abun da take ji a ™wa™walwarta shi ne dai-dai, sai dai yanayin yarinyar ya nuna ba za ta yi ™arya ko ha'inci ba, kuma tana da Wan karen wayo."

"Hajiya Sauda ce ta shigo, sai dai ta yi turus, ganin yarinya zaune a gaban turaki tana cin abinci a kwanonsa, duk da ta"

"bawa ™ofa baya, ba ta iya sanin kowacece ba."

"""Mai girma turaki wannan kuma wacece? Meyasa take cin abinci a kwaonka, kwanon da ko 'ya'yan cikinka ba su da"

"wannan damar""."

"Šan turus rumaisa ta yi, amma ba ta waiwayo ba, ta kuma mi™a hannu, ta Wauko alkaki, tana taunawa tana jin za™in"

sugan har cikin kunnuwanta.

"Turaki ya Waga kai ya kalli mama ya ce ""Ba™uwata ce?""."

"""Ba™uwarka kuma kamar yaya kenan?"""

"Ya kalli rumaisa ya ce ""Yarinyar kirki, je ki ki kirawo mini takawa"""

"Rumaisa ta mi™e ta ce ""To baba""."

Sai a lokacin ta juyo suka yi ido huWu da mama.

"Rumaisa ta wani lumshe ido, ta ce ""Ina wuni"". Kallon banza ta yi wa rumaisa, ta ji gaba Waya yarinyar ba ta yi mata ba, idonta kawai zaka kalla ka gane tattacciyar mara kunya ce."

Rashin amsawar ta ta bai WaWa ruma da ™asa ba ta fita falon.

"Usman na ganinta ya harareta, sai dai bai tsinke da lamarin rumaisa ba sai da ya ga tana lashe hannu tare da"

gutsurar wani abu a hannunta.

"""Kar dai yarinyar nan ciye-ciye ta je ta zauna ta na yi? Ya tambayi kansa."

"""Wai ka zo in ji baba mai rawani"" ta yi maganar tana kallon adam ba tare da ta kama sunansa ba."

"Bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da danna wayarsa."

"""Magana nake maka, ana kiranka"""

Still bai amsa mata.

"""Takalmawa ake ce maka ko me?, sunanka dai Adamu ba wani Adam ba to ka zo in ji baba mai farin rawani"""

"Wata irin tsawa aka bugawa rumaisa, wadda sai da ta tsorata, ta kusa faWuwa!"

AYSHERCOOL

"paid book ne, ¦ 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu™atar vip ko"

"special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*"

"A razane ta waiwaya tana kallon in da aka yi mata tsawar, wasu dogarai ne su biyu suka shigo suna baza riga,"

shigowar ta su yayi dai-dai da lokacin da rumaisa ke gatsali da sunan takawa.

"""Hattara dai yarinya, hattara 'yar talakawa, ba a furta wannan sunan hakan babu girmamawa"""

Šayan ya juya ya kalli Adam ya ce

"""gaba salamun baya salamun, takawarka lafiya magajin saraki, basarake Wan basarake jikan basarake, mai babban suna, takawa magajin takawa, motsawarka lafiya Wan gidan giwar galadima jikar fulanin gombe, ayi mana izinin bata horon yadda ake girmama wannan suna""."

"Adam ya girgiza kai, tare da Waga musu hannu, Wan risuna masa suka yi, sannan suka nufi sashin turaki, dan neman iznin shiga wurinsa."

"Rumaisa ta ce ""Yau na ga masifa, to naga annabawa ma ana faWar sunansu, sai sunan wani mutum gama gari ace ba za'a faWa ba, taS kun haWu da wahala, wai wani ´ar talakawa sai ka ce su masu kuWi ne""."

"Usman ya ce ""Dan Allah maiyasa ba ka saka sun Wagata sun zaneta da bulala ba? Wata™ila a samu hankali ya"

"shigeta""."

"""Yaya usy ai ni yanzu na wuce duka yasin, sai dukan ruwa bari na je na gaya wa baba mai rawani ka ce ba zaka zo ba"""

ta wuce ta koma wurin turakar turaki.

"Dogaran nan ta tarar a tsaye, suna jiran iso, amma ta zo ta saka kai zata shige."

"""Ke! Ke hattara dai, tsaya a nan ina zaki ba ayi miki iso ba?"" Ai ba ta ko tsaya ba, ta daka tsalle ta shige da gudu, ta"

tsaya tana jiran ko zasu biyota.

"""Wallahi tura ta kai bango, abubuwan da ka ke aikatawa sun isa haka, kai ko kunya ma ba ka ji? Ka mayar da"

"'ya'yanka ba komai ba, sai guda Waya shiyasa Allah ya kasheta a wula™ance, saboda zaluntar 'ya'yanka da kake yi, kuma idan ba ka yi wasa ba, kuma ba ka nemi afuwar yaranka ba, kaima a yadda ta mutu haka za ka mutu."

"Ka binne wa mutane gaskiya, kun haWa kai da giwa da Wanta sai rainawa mutane hankali ku ke yi, tayaya za ace wannan yar yarinyar ce ta dawo da jariri, ta yaya aka tabattar Wan aisha ne, wata™ila ma wani abun suka ™ulla, ya haihu da wata aka kashe aisha aka kawo yaron a matsayin nata, ba abun da ba zai iya faruwa ba, tun da dai 'yar ka ce ba tawa ba, matsalar ku ce"""

"Turus rumaisa ta yi tana bin Hajiya saudat da ido, ta gama zubarta, ta nufo hanyar fita, cikin tsawa ta cewa rumaisa"

"""Ke kuma ban hanya ko na yi gaba da ke"" maimakon rumaisa ta matsa, sai ta tsaya tana ™arewa ™wayar idon mama kallo, ba tare da tsoro ko shakka ba."

"Babu tsammani, rumaisa ta ji an ja ta gefe, an bar hanyar da mama zata wuce."

"Hajiya sauda ta yi wa adam wani mugun kallo, ta fice. Rumaisa ta ™wace hannunta, ta ™arasa gaban turaki ta ce ""Baba, mai ya sa ka tsaya matar nan take maka masifa, kai ba sarki bane ba? Ai ba a Wagawa sarki murya in ji mama, haka ta ce mini kan mu zo nan"""

"Turaki ya ce ""Yarinyar kirki, sarki a waje yake sarki, amma wani sarkin a gida bawa ya fishi power, kar ki damu zaki"

"gane me nake nufi "" ya kalli Adam ya ce ""Takawa, Biliyaminu nan sun kawo sa™on 'ya ta, ba sai sun ganni ba, na ta ne a kai mini ita har gida, Allah ya yi miki albarka""."

"Rumaisa ta ce ""To baba dan Allah ka saka baki ya bani Wana sabir, kaga na gaya maka anty aisha ta bar mini shi"

"wallahi, amma ya ™wace mini shi, kar na kai shi kotu ne a ga kamar ban kyauta ba, kuma ina ganin girmanku kai da mamansa, amma da wallahi nima kotu zan kai shi wurin al™ali, wata a unguwarmu ta taSa bawa mama labari wai a kotu an ™wato mata Wan ta daga wurin mijinta an bata"""

"Turaki ya girgiza kai tare da murmushi ya ce ""Subhanallah, ba za ayi haka ba, ai mu yanzu mun zama 'yan uwa, za a"

"duba lamarin in sha Allah, sa™onki yana mota Allah ya tsare""."

"Rumaisa ta mi™e tsaye ta ce ""To na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya maka bu™atunka na alkhairi Allah ya sa ka zama sarki, ka zama shugaban ™asa baba"""

"Sunkuyar da kai turaki yayi, yana rife fuskarsa da rawani, dan sha'anin na rumaisa ba ya ™arewa."

"""Wuce mu tafi ina da wurin zuwa"" Adam yayi maganar a kausashe."

"""Ai ko ba ka ce ba zan tafi, ba sai ka kaWani kamar wata akuya ba"" ta yi maganar tana ficewa waje."

"Tun da ta fito usman ke cigaba da aika mata harara ko ta ina, amma ta yi kamar ba ta gani ba, haka suka fita suka"

hau motar takawa.

"Suna tafe a hanya, babu wanda ya kula rumaisa a cikinsu, usman ya ce wa Adam ""Ina ga idan muka ™arasa titi ka ajiyemu, sai mu samu abun hawa mu ™arasa gida""."

"Adam ya girgiza kai ya ce ""A'a zan kai ku gida, akwai kaya ma, ba zai yiwu in ajiyeku a hanya ba"" daga haka suka Wan"

shiga taSa hira suka cigaba da tafiya.

"Tafiyar su takawa babu daWewa, Samha ta dawo, har ta shiga Wakinta ta canza kaya ta fito, ba ta ga gilmawar mama"

"ba, dan haka ta bita Waki."

"Ta iske mama na ta ™ananun maganu, da mita."

"""Mama, wai baki san na dawo ba? Ke da waye ki ke ta mita haka ne?""."

"""Ba dole na yi mita ba, ubanku na nema ta ™arfin tuwo ya mayar da ni mahaukaciya""."

"""Ohh mama, kullum cikin case da Alhaji, yakamata ku daina zuwa yanzu""."

"""Ke dalla rufe mini baki, mai za a fasa? Ai yanzu aka fara ma ba ayi komai ba, na rasa abun da yake shiryawa da shi"

"da adam, sai Soye-Soye suke yi, da rainin hankali wata shu'umar 'ya ya kawo masa, wai ita ta dawo Wan wurin aisha daga hannun 'yan bindiga"""

"Cikin rashin fahimta samha ta ce ""Yan bindiga kuma, wasu 'yan bindigar kenan kuma? Ba a can in da take karatun aka ce ta haihu ba? To meya kawo ´an bindiga ban gane ba""."

"Hajiya Sauda ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Ke, adam wani abun yake shiryawa, aisha ba wani a ™asar da taje karatu da ta"

"mutu, a hannun'yan bindiga, da suka yi garkuwa da ita, ta haihu ta mutu a wula™ance ko gawarta ba wanda ya gani, waya sani ko shi ya cinyeta ko ya kashe ta yayi tsafi da gangar jikinta""."

"Cikin rashin fahimta samha ta ce ""Mama kin yi wa kwanyata dabaibayi da zantukkanki, na gaza fuskantar ko da guda"

"daga ciki, ki yi mini bayani gwari-gwari. ³an bindiga ne suka bi ta can suka sace ko kuwa?""."

"Nam mama ta fayyacewa samha komai, duk da gargaWin da turaki yayi mata a kan hakan."

"Salati samha ta yi, tare da tafa hannuwa cike da tsananin mamakin sar™a™iya da ruWanin lamarin, a fili ta ce ""Oho"

"musu, ko ma dai yaya ne, a wannan karon nasan babu abun da zai hanani mallakar takawa""."

"She™e™e mama ta kalleta ta ce ""Wai ke samha wace irin mara zuciya ce ne?, Au ke yanzu duk abun da ya faru da ke a"

"baya, da irin cin kashin da yayi miki baki ha™ura da batunsa ba?"""

"""Dan Allah mama karki ce komai, wallahi ina son sa haryanzu kuma abun da ya faru, ya riga ya wuce, dan Allah kiyi"

"ha™uri ki bani goyon baya a wannan karon na auri adam dan Allah"""

"""Kin ga tashi ki je, ina da abun yi yanzu""."

"Samha ta haWa hannayenta biyu cikin magiya ta ce ""Please mama""."

"""Na ji, amma jeki yanzu, ki bari na yi tunanina"" Samha ta tashi ta bar Wakin mama, tana ta nazari da zancen zuci a"

kan abun da maman ta gaya mata.

"Nusaiba ce ke ta bawa iman labarin rumaisa, da abun da ya faru Wazu da suka zo, zasu je gidan turaki. Iman ta ce ""Allah sarki, na ji ina son ta tun ban ganta ba, ai mu duk mai son waninmu muna son shi""."

"Nusaiba ta ce ""Ke kin ganta, wallahi yarinya ce sosai, dan ba ta kaimu ba ma ko kaWan, na yi mamakin yadda ta iya"

"tsira da sabir""."

"Iman ta ce ""Ai babu mamaki a cikin lamarin Ubangiji, babu abun da bau iya ba""."

"""Gaskiya ne, amma wai ya maganar uncle J ne, kun kuma magana da shi?"""

"Haushi ne ya kama iman ta ce ""Dan Allah ki rabu da ni da wani uncle J"""

"""Dole na yi miki maganarsa, ke ma kin san rasuwar nan ce ta hanashi cigaba da bibiyarki, ina son nema miki mafita"

"ne, idan ya je ya biyo ta saman fa kamar yadda ya gaya miki?"""

"Iman ta Wan yi jimmm sannan ta ce ""Bakomai, Allah ya fishi, mu bar maganar nan sai wani lokacin*."

"Lura da yanayin yadda iman ba ta son zancen, ya sanya Nusaiba jan bakin ta ta tsuke."

"Rumaisa kuwa bayan kayan takaicin da ta turawa su usman, suna tafe a mota tana yi musu wa™e-wa™e, tayi wannan"

"wa™ar ta saki ta kama wata, gashi galibin wa™o™in na indiya take yi, sam ba ta san ma me suke faWa ba, kawai dai tana yi ne, kuma cikin ikon Allah daga usman har takawa ba wanda ya tanka mata har suka ™arasa gidan rumaisa."

"Usman ya kalli Adam ya ce ""Mun gode ™warai da gaske Allah ya saka da alkhairi""."

"Adam ya ce ""Bakomai, ni ne da godiya ai""."

"""Hmm ai Yakamata in ™ara ma da baka ha™uri, a kan abun da rumaisa ta yi, ka yi ha™uri dan Allah"" Adam yayi"

"Murmushin gefen baki ya ce ""Kar ka damu, akwai sa™onta a mota amma, bari na buWe booth Win"""

"Ruma buWe motar tayi, ta ruga da gudu cikin gida tana kwaWa sallama."

"Kaya ne fal a booth Win Adam, da wanda ammi ta bawa rumaisa da wanda turaki ya bayar a bata."

Usman ya Wauka ya yi wa Adam godiya suka yi sallama ya ce a gaida mama.

"Ko da ya shiga gidan, rumaisan ya tarar har ta tuSe kayanta tayi Wai-Wai wai ta gaji."

"""Dan ubanki ni bawanki ne? Da zaki bar ni da kwaso miki kaya dan baki da kunya?"" Shiru ta yi ba ta ce komai ba,"

ganin irin kallon da yake yi wa rumaisa ya sanya sanin cewa akwai abun da rumaisa ta yi.

"""Usman, ya aka yi ne? Kun je Win?"""

"""Eh mun je, amma ba ta sauya zani ba, ta yi iya shegen na ta da ta saba"""

"Mama ta kalli rumaisa ta sake kallon usman ta ce ""me ta yi?"""

"Nan ya gaya mata iskancin da ta din ga yi, mama ta girgiza kai ta ce ""Wai rumaisa me bawan Allah nan yayi miki da ki"

"ke yi masa wannan rashin mutuncin? Duk jan kunnen da na yi miki ba ki ji ba kenan?"""

"""Mama na faWa komai fa"""

"Usman ya ce ""To amma meye na cewa sai mun fita, a matsayin sa na mijinta yafi kowa bu™atar sanin meyafaru da"

"ita""."

"Mama ta ce ""Meyasa baka kama mini ita ka zaneta ba""."

"Ya Wan Wage kafaWa ya ce ""Ai kin san wasu lokutan sa'a ce da ita, daga zuwanmu ta dinga zuba tana yi wa dattijon"

"shishshigi tana ce masa baba, aikuwa ya dinga biye mata, saboda sakarci har da ci masa abinci a gabansa"""

"Huzaifa da yake banWaki yana jin hirarsu, yana fitowa ya ce ""Sai ka ce mayya daga zuwa ba™unta ki hau cin abinci"""

"Aikuwa ta ce ""To zigazigi wutar ma™era, mai zuwa lahira da ™o™on dambu waya kasa da kai gwanin na iya""."

"""Kin rufe mini baki ko sai na taushe shegen bakin naki"""

"""Wallahi mama ni ban ci abinci ba, wannan abun na kayan gara mai kamar kashin nan da suga shi kawai na ci""."

"A fusace mama ta ce ""Ni rufe mini baki, bera kawai"" haka ta koma ta tura baki tare da jin haushin yadda kowa yake"

caccakarta.

"Adam sai da ya fara biyawa yayi sallar la'asar, yana komawa mota ya tarar da missed calls Win Bashir."

"Bin kiran yayi, bayan bashir ya Waga sun gaisa ya ce masa akwai issue, su haWu a wani wurin cin abinci bayan sallar"

isha'i.

"Adam ya amsa masa, ya yanke shawarar fara zuwa gida, kan lokacin sallar isha'i sai su haWu da Bashir."

"Ko da ya je gida, Ammi ta din ga tambayarsa yaya suka yi, da fari basarwa yayi, da ammi ta matsa ya gaya mata"

cewar rumaisa ba ta yi magana a gabansa ba sai da ya fita.

"Ammi ta yi shiru ta ce ""Wai ni anya Adam babu wani abu a tsakaninka sa yarinyar nan ´ar tsamar da ku ke ta yi"

"yawa, ta rainaka da yawa""."

"Ya girgiza kai ya ce ""Ni ban santa ba sai a dalilin abun nan da ya faru, dan haka ni babu komai a tsakanina da ita"""

"""To, amma ina kyautata zaton akwai wani abu mai muhimmanci a bakinta, tun da ta™i faWa a gabanka""."

"""Haka nake tunani nima, amma zan koma wurin turaki, sai mu yi magana""."

"""To shikenan, Allah ya yi jagora"""

Ya amsa da amin.

"Kamar yadda suka shirya, suka haWu da Bashir a wurin cin abinci, ya tambayi adam mai za a kawo masa ya ce ba ya jin yunwa."

"Bashir ya ce ""A'a ba zai yiwu ba, sai ka ci abinci ko na koma da labarin da na zo da shi""."

"Da ™yar adam ya yarda a kawo masa chips, bashir ya din ga yi masa hira, tare da gaya masa ya kusa komawa abuja wurin aiki."

"Adam dai bai iya tankawa ba, jira yake kawai ya ji me Bashir zai ce masa."

"""Wai ni kuwa ya ake ciki da maganar binciken da ka ke yi ne, na mutanen nan mutane hukuma fa suke jira, su ji"

"sakamakon binciken ku, gashi wa'adin da kwamitin da gwamnati ta kafa ya cika ya wuce, amma ba su ce komai ba, kaima kuma kun yi shiru."

"Adam yayi ajiyar zuciya ya ce ""Bashir, sawun giwa ya take na ra™umi ai, ™asar da ba ta damu da halin da al'ummarta"

"suke ciki ba, tayaya zan cigaba da wahalar da kaina, a hukumar tamu ma kana gani sun rabu biyu, wasu suna goyan bayanmu wasu ba sa yi, a ™asa kuwa talakawa ne kawai suke supporting Winmu. Ni yanzu hankalina yafi karkata ga binciko wanda suke da hannu wurin sace matata, dan a jikina nake jin na jikina ne""."

"""Kenan kana nufin zaka fito ka cewa duniya sace matarka aka yi, bayan an gama jita-jitar a ™asar waje ta zo haihuwa"

"ta mutu?"""

"""Bashir dole hakan zan yi mana, ba zan bar mutuwar aisha ta tafi a banza ba, ko da haka yana nufin zubewar kimata"

"ne a idon duniya""."

"Bashir ya jinjina kai, ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ya Wan daddana sannan ya mi™awa adam."

"Adam ya karSa ya fara dubawa, shafin wata jarida mai suna ciki da gaskiya ya buWe masa."

"Yana shiga ya ci karo da hotonsa, tittle Win labarin aka rubuta dara ta ci gida."

"Shahararren jami'in tsaron nan na farin kaya, mai jagorantar wata tawaga da ta zama babbar barazana ga manya"

"Sarayin ™asarmu, ko kuma dai ace, shugabannin da yake yi wa sharrin sata, wato Adam Sharif Galadima. Kwanaki kaWan bayan kamala zaman makokin mutuwar mai

Please Login or Register in order to submit comment