You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

roba, ya fito ya bawa rumaisa, ta karSa ta ta™ar™are ta shanye shi a ma™warwa uku tayi jifa da jarkar."

"Ya kalli rumaisa a tsanake ya ce ""Na ji kin ambaci dawanau, ke 'yar kano ce?"""

"""Eh, dawanau asibitin mahaukata ne, dan Allah idan ka san kano ka kaini, kar jaririna ya mutu, bashi da lafiya"" tayi"

maganar cikin magiya.

"Ya ce ""Ok babu damuwa, amma Meyasa na ganki a haka? Ina hijjabinki kalleki futu-futu fa, ga raunuka a jikinki, kalli"

"kanki yana zubar da jini, jikinki babu hijjabi, ™afarki babu takalmi, dole ayi zaton ko baki da hankali""."

"""Kwana kusan sittin fa a dajin nan, saceni aka yi, dan Allah ka tashi ka mayar da ni gida"" salallami mutanen wurin"

suka Wauka.

"A take ya ciro id card Win sa, ya nunawa mutanen, shi jami'in tsaro ne, dan haka ya ce zai tafi da rumaisa babban asibiti na cikin garin katsina."

"Rumaisa ta ce ita fa ba ta so a kaita ko ina sai gida, ya fuskanci yarinyar kafaffiya ce, dan haka ya ™yaleta ya ce ta taso"

"sai ya Wauki wakilcin mutum Waya su tafi, su tsaya su yi reporting wa police, su wuce da ita asibiti."

"Sai dai duk yadda rumaisa ta so ta tashi ta kasa, saboda ji ta yi ™affuwanta kamar ba nata ba, ™arshe sai Waukarta aka"

yi aka saka a motar suka tafi.

"Sai dai fa fafur ta hana kowa jaririn nan, yana ™an™ame a jikinta, jin abubuwan take kamar a mafarki, Allah ya"

"kuSutar da su, ta din ga jera hamdala ga Ubangiji."

"Sai dai rumaisa na sanya ran an kama hanyar kano ne, ta gansu a asibiti, aka zo da wheel chair, aka Worata a kai,"

nurses zasu karSi jariri ta ce ba ta san zance ba.

"Emergency aka shiga da su, aka yi ta lallaSa rumaisa ta bayar da jariri ta ™i, ta ce idan aka matsa mata, ko da rarrafe sai ta gudu daga asibitin."

"Kasancewar mutumin da ya tsinceta shi ma ba Wan gari bane ba, idanya barta babu wanda zai kula da ita, ya sanya a"

"ka bawa rumaisa Wan taimakon gaggawa, ya Wau rumaisa tare da rakitar 'yan sanda biyu, suka taho kano."

"Suna tafe a hanya rumaisa tana ta surutai, masu kama da na fita a hayyaci, ta ce wanna ta ce wancan, ita dai gata nan kamar mai barci kuma kamar zautacciya."

"Ba su suka iso kano ba sai bayan tara na dare, suka biya suka kuma report ga police na kano, aka yi rubuce-rubuce,"

sannan suka wuce da rumaisa asibiti.

"Suna zuwa aka karSi su rumaisa, da tuni hankalinta baya jikinta, tun a hanya aka sai abin ci aka bata, amma ta™i ci, ba ta ma da nutsuwar da zata ci Abincin."

"Aka zare jaririn hannunta, da a yanzu numfashi ma yake neman ya gagare shi, da yawa sai da wasu suka yi hawaye,"

"ganin halin da jaririn Wanyen haihuwa yake ciki, cibiyarsa ta ya™une tayi ba™i, jikinsa duk ™azanta, aka samo kaya aka saka masa aka wice da shi nursery domin bashi taimakon gaggawa."

"Ita kanta rumaisan sai ka kai zuciyarka nesa zaka iya taSata, saboda yanayin da take ciki na ™azanta da dauWa, ba yadda ba su yi ba su kwance Wan kwalin ™ugunta, amma aka kasa, ™arshe suka ™yaleta suka fara kokawar ceto"

"rayuwarta, ita kanta sai da aka saka mata oxygen, saboda sama-sama take numfashi, aka Webi jininta aka tafi yi mata gwaje-gwaje."

***

"Kusan mintuna uku tana zaune a dining tana ta juya cokali a cikin kofin shayin, amma ta kasa Wagawa ta sha ko da sau Waya, sai zancen zuci take. Jin an dafa ta ne ya sanya ta Wago a hankali ta kalli ammi, a take ta fara ™a™aro murmushin da bai wuce iya leSenta ba."

"Ammi ta ja kujerar kusa da ta iman, ta zauna ta ce ""Autana, ko ban tambayeki ba na san abun da ki ke ji, kuma na san ke mai juriya ce, dan haka kar ki saka maganganun da wambai yayi a ranki, ki manta da komai, ki mayar da hankali a kan karatunki, da kin kamma sakandare, zan turaki Mexico wurin laila, ki nutsu ki yi karatunki a wurinta, kuma in sha Allah zan sama miki miji na gari, mai tsoron Allah wanda zai ri™e mini ke tsakani da Allah"""

"Iman ta rungume Ammi ta ce ""Ni dai a'a ammi, zan zauna a tare da ke, bana son mu rabu, zan cigaba jure komai in"

"rayu a kusa da ke""."

"Ammi ta yi murmushi ta ce ""Duk abun mutum dai dole sai aure ya rabamu, watarana sai mutum ya tafi gidan miji"""

"Iman ta ce ""Sai mu tafi tare, duk wanda zai aureni, sai ya yi wa ammina nata Wakin""."

"Yana sanye da farar jallabiya, ya Wora rigar sa™i ta sarauta, da farar hula, yana tsaye yana kallonsu, ya Wan yi gyaran"

"murya, hakan ya sa suka Wago suna kallonsa."

"Ammi ta ce ""Ina zuwa haka?"""

"Ya gyara agogon hannunsa ya ce ""Zan je gidan turaki ne in gaishe shi""."

"""Amma ina fatan ba wani abun zaka je ka gaya masa ba, ka tayar masa da hankali?"""

"Takawa ya girgiza kai alamar a'a, iman ta ce ""Yaya a dawo lafiya""."

"""Allah ya sa, ki kula ki sha magungunan ki a kan lokaci""."

"Ta jinjina kai ta ce ""In sha Allah"" daga haka ya fice daga falon."

"""Ammina, bari na je na sha magani na Wan kwanta""."

"Ammi ta ce ""To babu laifi, amma dan Allah kar a je a zauna ana tunani, idan na gani ba zan ji daWi ba""."

"Iman ta yi murmushi ta ce ""Ba zan yi ba in sha Allah, in dai kina nan Ammi wane tunani zan yi?"" Tayi maganar tana"

mi™ewa tsaye tana yi wa Ammi murmushi.

"Ko da ta je Wakinta, ta tarar da baba uwani tana ta yi mata bincike bincike."

"""Baba uwani"" ta kira sunanta a razane ta waiwayo ta kalli iman ta ce ""A'a uwar Wakina kin shigo?"""

"Iman ta ce ""Eh, amma me ki ke nema ne?""."

"""A'a babu abun da nake nema, baki gani ba, gyara Wakin nake yi, ke da ba lafiya ba, kaye-kaye nake yi miki ai""."

"""Amma baba uwani na sha gaya miki, gyaran Waki ba aikinki bane ba, ya zaki din ga wahalar da kanki da yawa haka,"

"kiyi wancan aiki kuma ki zo ki yi wannan""."

"""To imanuwa idan ban yi miki ba wa zan yi wa, kuma gashi ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba, na san sai ki ce zaki yi da"

"kanki ma""."

"Iman ta girgiza kai ta ce ""Kar ki damu baba uwani, ki yi tafiyarki kawai, za a gyara Wakin ma ai babu datti, ina son in"

"Wan kwanta ne""."

"""To Shikenan babu laifi, ki huta lafiya"""

"Iman ta bi bayanta da kallo, daga bisani kuma ta je ta nemi wuri ta kwanta."

***

"Cikin ™osawa take wayar, cikin yanayi mai kama da faWa-faWa ""gaskiya Khalifa na gaji da gafara sa ban ga ™aho ba, ai yakamata ace zuwa yanzu result ya fito""."

"""Ke duk result Win da ki ka gani bai yi miki ba, wanne ki ke jira? Meyasa kin fiye wutar ciki ne?"""

"Samha ta ce ""Au haka ma zaka ce, ni na kasa gane wannan yawon da hankali, ni fa na fara jin tsoro""."

"Dariya Khalifa ya yi ya ce ""Haba jaruma, wane irin tsoro kuma? Ai mun yi kaso mafi yawa na aikin, sauran ke zaki yi"

"wa kanki fighting, ki bi komai a hankali, idan ki ka yi gaggawa aiki zai iya kwaSe miki, dan ni babu ruwana. Nan ba da daWewa ba, zaki ji labari mai Wan karen daWi""."

"Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Shikenan, Allah ya sa"". Ta ajiye wayar ta yi shiru tana tunanin maganganunsa."

"""Anty Samha, Anty Samha!"""

"Waiwayowa Samha ta yi ta kalli yarinyar a Wan hasale ta ce ""Lafiya ki ke yi mini wannan kiran haka?"""

"""Anty Samha kin gan mu, zuwa muka yi baki yi murna ba?""."

"""Na ji, jeki wasanki, idan na fito ma gaisa"""

"Yarinyar ta Wan Sata fuska ta ce ""Shikenan, naga uncle takawa ya zo, bari na je na gishe shi""."

"Da sauri Samha ta ce ""Jannah, bana son shirme da gaske ki ke yi ko kuwa?""."

"""Wallahi da gaske, ga motarsa can da hadimansa, yana wurin Baba suna gaisawa"""

"""Shikenan, na ji jeki maza"" janna na fita samha ta tashi ta canza kaya, ta hau feshe-feshen turare."

"Takawa yana jin daWin mu'amala da turaki, dattijon akwai nutsuwa da kuma dattaku, ba shi da hayaniya sam balle"

faWa.

"Sun daWe suna hira, sai da takawa ya fara shirin tafiya sannan turaki ya ce ""Amm..wato akwai maganganu da muka ji suna ta yawo a kanka, a cikin masarautar nan, sai dai bamu yanke maka hukunci ba. Maganganu ne marasa daWi da maimaita su ma bashi da wata fa'ida, amma duk da haka zamu jadadda, a din ga kula a ™ara kiyaye martabar addini da kuma al'ada, ba zamu so zancen nan ya je kunnen mai martaba ba, mussaman yadda ake ji da kai, yake sonka, muna ta ™o™arin da™ile jita-jitar, mun sani shaye-shaye ba halinka bane ba, dan da kana yi, zamu gane, amma a cigaba da kiyayewa tare da ri™e addu'a""."

"Adam yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya Wan risuna ya ce ""Za'a kiyaye in Allah ya yarda, Allah ya ™ara maka"

"lafiya, zamu wuce""."

"""To madalla, Allah ya tsare ka isar da gaisuwata ga mahaifiyarka, ka ce kwana biyu bamu ga aiken mutan daji ba"

"ma'abota nagge"" yayi maganar a nutse cikin sigar barkwanci."

"Takawa ya Wan murmusa, tare da du™awa daga nan ya tashi ya fita."

"A falo ya tarar ana ta shirya abinci, Janna ta ™araso gabansa ta risuna ta ce ""Barka da wannan lokaci uncle""."

"""Barkanki dai janna, kwana biyu bana ganinki, ya makaranta?"""

"""Lafiya ™alau"""

"Ya ce ""Masha Allah"". Yana Waga kai ya yi tozali da matar da ya tsana a duniya, mahaifiyar su Jamil, wato mama, bai"

"san ya aka yi suka san ya zo ba, dan ta ™ofar baya ya shiga sashen turaki, ya nemi ayi masa iso."

"Ta washe baki ta ce ""Takawarka lafiya toron giwa, gaba salamun baya salamun, galadima magajin galadima, da haka"

"za a wuce ban san an zo ba? Ai yakamata mu gaisa ko""."

"""Ai ban zaci idonki biyu ba, barka da wannan lokaci"" yayi maganar yana Wan risunar da kansa ™asa."

"Kan ta amsa samha ta fito tana murmushi ""Takawa, yau kai ne a gidan namu? Zaka tafi babu ko sallama da mun yi"

"faWa da kai kuwa"" wasu irin matsatsun kaya ne a jikinta riga da skirt, ilahirin surar jikinta ko ina a matse."

"""Ku yi mini afuwa, dama ina da niyyar shigowa""."

"Mama ta ce 'Amma na ga kamar kana shirin tafiya, da ka yi Wan waken zagayen, ga abinci nan na saka a kawo maka"

"ai""."

"""Ayi mini afuwa sauri nake ne, ana jirana, zan sake yin zuwa na musamman na barku lafiya"" bai ma tsaya ba balle ya"

ji mai za su sake cewa ba ya fice.

***

"Šan ™ura mata ido yayi, bacci take kamar babu rai a jikinta, yanzu babban fatansa ya san daga in da take a nemo 'yan uwanta, su zo su san abun yi a wanke mata wannan dattin na jikinta, ko ita ma ta samu ta ji daWin jikin nata."

"A hankali ta buWe idonta, ta Wan motsa jikinta da yake ta yi mata azabar ciwo."

"Ya ce ""Alhamdilillah, kin farka?"""

Ta yi masa ™uri da ido tana kallonsa.

"Ya dur™usa a gaban gadon ya ce ""Ki bani lambar wayar wani a gidanku, a sanar musu kin dawo""."

"A hankali ta buWe baki ta ce ""Haka muka yi da kai?"""

"Ya ce ""Me fa?""."

"""Ina Wana?"" Ta tambaye shi."

"""Yana sashin jarirai ana kulawa da shi, kin san ya galabaita""."

"Rumaisa ta ce ""Lallai baka sanni ba, ni fa a kan yaron nan, sai na tayarwa da kowa hankali, a bani Wana"""

"Zai yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ciro wayar daga aljihunsa, ya kalli screen Win wayar ya ce ""Jarababbe, na san na shiga uku da masifarka yau""."

"Ya Waga wayar ya saka a kunnensa ya ce ""Ya?""."

"""Abun da ya kamata ka ce mini kenan?""."

"Bashir ya ™ara nutsuwa ya ce ""Sorry man, na san na yi maka laifi, am sorry for that, wani emmrgency case ne ya"

"faru, na bayar da taimakon da zan iya, yanzu haka ina Asibiti wata yarinya na tsinto a katsina ta kuSuta daga hannun 'yan bindiga""."

"""Ina ruwana, ta ina hakan ya shafe ni? Ni abun da ka yi mini ka kyauta kenan? Na rantse da Allah muka haWu sai ka"

"gane baka da wayo""."

"Ruma ta yi ™uri da ido tana sauraren muryar da ko daga maye ta farfaWo, ba ta manta mai ita ba."

Ayshercool

08081012143

"*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*"

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*

"*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ˜URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE˜I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*"

"*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*"

"*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai"

"da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*"

*Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

"*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*"

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

"*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*"

"*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*"

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

"*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*"

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*

*14. Supplement na whitening/glowing skin*

"*15. Supplement for Acne, dark spots remover*"

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da

"kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*"

"*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai"

"ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*"

"Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba"

"a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*"

"Bashir ya san iya tijara zai sha ta a wurin takawa, dan haka ya shiryawa karSar da duk wani hukunci da zai yi masa, ya"

"kwantar da murya ya ce ""Tuba nake, ka bari zan zo in sameka, na gaya maka ina Asibiti ne""."

"""Kar ka sake ka zo in da nake, idan ka zo haWuwarmu ba zata yi maka daWi ba"""

"'shi wannan kowa ma yi wa masifa yake yi?' ta tambayi kanta, can kuma ta ce '˜ila ma ba gaske bane mafarkin da na saba nake yi'."

"Maganar Bashir ce ta dawo da ita hayyacinta ""Haryanzu ba ki gaya mini ko sunanki ba, mun kawo ki unconscious, ki"

"gaya mini sunanki, ki bani lambar wayar wani a gidanku, na kirasu ga abinci nan na kawo miki, yan sanda suna jirana na je na kai report""."

"""Ina jaririna?"" Shine abun da ya fito daga bakin rumaisa."

"""Na gaya miki yana nursery, an saka mishi oxygen ana ™o™arin ceto ransa""."

"""Idan wani abu ya same shi ba zan yafe maka ba, kuma wallahi sai na saka yayyena maza sun zane ka"" ta yi maganar"

tana hawaye.

"Bashir ya sake nutsuwa, yayi murmushi ya ce ""ba zata kai mu ga haka ba, babu abun da zai same shi sai abun da"

"Allah ya ™addara masa, trust me, yanzu bani lambar wayar""."

"Ta Wan rausayar da kai ta ce ""Allah ya sa ba mafarki nake yi ba, ni na manta lambar kowa, bari na baka ta Yasir,"

yayana ne ta sa na tuna.

"Ya ce ""Ok, gaya mini"" yayi maganar yana ri™e wayarsa."

"Ta gaya masa lambar cif, yayi saving ya ce ""Tashi ki ci abinci, yayata zata zo ta zauna da ke, kan 'yan gidanku su zo""."

"Ta girgiza masa kai ta ce ""Ni ba zan ci komai ba, sai na ga mama""."

"Bashir ya ce ""No, ba za ayi haka ba, ki daure ko kaWan ne"""

"""Ni dai ka tashi ka kirawo mini ita kan na farka daga baccin da nake yi"" tayi maganar tana kuka har da sheshshe™a."

"Ya ce ""To shikenan, bari na je, yayar tawa zata zo, sunanta Asiya, za ta zauna da ke"""

Ba ta ce masa komai ba ta cigaba da share hawayenta.

"Mintuna talatin da fitarsa, sai ga yayarsa Asiya ta iso, ta tarar da rumaisa tana barcci, dan haka ta nemi wuri ta zauna"

"tana jin tausayin yarinyar, mussaman yanayin da ta ganta a ciki."

***

"Kasancewar yasir ya iya gyaran kayan Electronics sosai, ya sanya ya buWe Wan case da yake gyare-gyaren sa, ko yanzu da yake ta aiki yana yi ne ba dan yana jin daWin aikin ba, sai don rage kewa da kuma damuwa."

"Wayarsa ce ta fara vibrating, yana ji yayi banza sia da ta kusa katsewa, sannan ya Waga ya yi sallama."

"""Wa'alaikum salam warahmatullah, ina magana da Yasir ne?"""

"Yasir ya ce ""Eh ni ne""."

"""Yauwwa, sunana Bashir kibiya, ni jami'in tsaro ne dan Allah idan ba zaka damu ba, ina son haWuwa da kai a babbar"

"headquarter 'yan sanda ta bampai"""

"Waro ido Yasir yayi ya ce ""YallaSai me na yi? Wallahi ni ban yi wani laifi ba"""

"""Na sani malam Yasir, ni yakamata na zo da kaina ma, amma wani abu ne ya ri™eni ka zo da gaggawa ka sameni"""

"Jiki a sanyaye Yasir ya kashe wayar,ya kwashe kayansa, yana tunanin wa zai jewa da wannan maganar, babu yadda za"

ayi a gayyaci mutum bamfai ace lafiya lau.

"Ya tsaya a ™ofar gida ya kasa shiga gida, sai rarraba ido yake yi."

"Abdallah ne ya fito daga cikin gidan, Yasir ya ce ""Alhamdilillah, zo ka ji wani abu""."

"Abdallah ya ce ""Ya aka yi?"""

"Kamar Yasir zai fashe da kuka ya ce ""Wani ne ya kirani, wai na je bamfai yana jirana kuma ni wallahi tsoro nake ji"""

"Abdallah ya ™are masa kallo sannan ya ce ""Kai, ka gaya mini idan wani abun ka aikata, Kodayake da ruma tana nan"

"sai in ce ko ita ake nema, amma kuma ks tabattar ba 'yan iskan gari bane ba, ko a cikin abokanka wani ke son raina maka hankali ba?"""

"Yasir ya ce ""Bana tunanin hakan, mutumin muryarsa ba ta yi kama da haka ba""."

"Abdallah ya ce ""Bani lambar"" Yasir ya bashi lambar ya saka a wayarss ya kira, yana kira Bashir ya Waga, suka gaisa"

"Bashir ya ce ""Bawan Allah, yayan yasir ne ni, ina son jin dalilin da ya sanya ake nemansa a bamfai?"""

"Bashir ya ce ""Eh, abu ne mai muhimmanci, da laifi yayi gida zamu zo mu kama shi ai, ku hanzarta dan Allah"""

"Abdallah ya ce ""To shikenan babu damuwa ""."

"Ya katse wayar ya kalli Yasir ya ce ""Zancenka gaskiya ne, ka san wani abu? Kar mu gaya kowa, zo mu je mu ji koma"

"menene, sa ji daga baya"" Abdallah ya ™wararawa Yasir gwiwa, suka kama hanya suka tafi."

***

"Ammi ta fito babban falo, ta dubi Waya daga cikin barorinta ta ce ""Maza je ki korawo mini iman"" ta amsa mata cikin girmamawa, ta tafi."

"Bai fi mintuna bakwai ba, sai ga Iman ""Ammi gani, Allah ya sa ba laifi na yi ba?""."

"""Ai laifin ki ka yi, na gaji da zaman Wakin nan da ki ke yi, jikinki ai da sau™i yanzu, ki shirya zamu je gidan Jamil, an ce"

"matarsa tayi Sari"" Wan Sata fuska iman tayi kamar zata yi kuka."

"""Menene ko ba zaki ba?"" Ammi tayi maganar tana tsare iman da ido."

"""A'a zan je, bana son na je na tarar da Anty samha ne"" tayi maganar kamar ta rushe da ihu."

"Ammi ta kalleta a tsanake ta ce ""Meye tsakaninki da Samhan da ba kya son haWuwa da ita?"" Sai kuma ta sha jinin jikinta jin abun da ammin ta ce."

"""Bakomai Ammi, bana son fita ne"""

"""Aikuwa sai kin fita, maza muje in shiryaki, kar ma ki Sata mini lokaci"" Nusaiba kuwa sai dariya take yi, ganin ammi"

"ta saka iman a gaba wai ita zata shiryata. Hakan kuwa aka yi, Ammi na tsaye iman ta shirya cikin ba™ar abaya, da ta karSi kyakywar farar fatarta, sai Waukar ido take yi, ta Wora mayafin a kan ta, sai dai kwantaccen gashinta sai da ya bayyana."

"Tare suka fito da Ammi, tana janyo hannunta, ita kuma kamar ta fashe da kuka, sai tura baki take yi. Haka suka jera da Nusaiba da iman da ammi."

"Nusaiba ta ce ""Allah ammi kin shagwaSa yarinyar nan da yawa, ji wata taSara da take yi""."

"Ammi ta ce ""Bar ni da ita, sai na zaneta tukuna"" haka suka fito harabar gidan a tare."

"Tun daga nesa yake kallonsu, ya tattara nutsuwartsa a kan Iman, tamkar ba bugun Nigeria ba haka take."

"""Ruky wannan ma 'yar gidanku ce?"""

"Ru™ayya ta waiwaya ta hango su Ammi, a fusace ta dube shi ta ce ""To ba 'yar gidan nan ba ce, tsintota aka yi aka"

"ri™eta a gidan nan, babu wanda ya san danginta ma, wata™ila ma ba ta da uba"""

"Maimakon ya fusata sai ya ce ""Wow, amma dai a ™asashen Larabawa kuka tsinto ta ko? Ko irin Afrika ta gabas Win nan""."

"""A'a africa ta sama, aka tsinto ta aikin banza "" ta tashi fuu ta shiga ciki."

"Tashi yayi yana kiran sunanta, amma bata ko sake waiwayo wa ba ta tafi."

"""Wallahi na gaji, ni da gidan ubana saboda bala'i ban fiye zama ba, ko na kawo ba™ina ba, da gayya idan bar zan yi"

"ba™o mu zauna a harabar gidan nan, sai wannan banzar yarinyar ta fito, ita kuma ammi ta wani sako su a gaba riii kamar shanu, duk yadda na ™allafa rai a kan gayen nan, yana ganinta ya hau wani surutu, ji nake kamar na zuba mata wuta a fuska uban kowa ya huta""."

"Mummy da take jin ta tayi shiru ba ta yi mata magana ba, ta ™araci bala'inta ta gama, amma Mummy ta fara hasala,"

"duk yadda suka kai ga Sata iman, ba ya wani tasiri sam. Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce ""daga yau idan kin yi ba™i, ku din ga shigowa falon waje, kuna zama, ku bsrni da ita,

Please Login or Register in order to submit comment