You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin ofar."

"Ruma ce a tsaye, ta gama fitsarin ta mie tsaye tana kallon yadda fitsarin na ta ya gauraya da jini, duk da ba wani"

mai yawa bane ba.

"""Meye haka?"""

"Cikin rawar jiki ta nuna masa ta ce ""Mai sunan baba ka ga, fitsarin jini nake, mutuwa zan yi"" tayi maganar idonta na"

cika da hawaye.

"""Yaushe ki ka fara irin wannan fitsarin?"""

"""Yanzu kawai na gani"" tayi maganar tana dafa bango, saboda jirin da take ji."

"Ya waiwayo ya kalli Yasir ya ce ""auko mata zanin mama"" Yasir shima jiki na rawa ya tafi Wakin mama, dan hankalinsa ya tashi sosai."

"Ya sake duban Usman ya ce ""an Wora mata ruwa ya yi zafi, ta yi wanka"" cikin damuwa Usman ya ce ""To meya"

"sameta?"""

"Ya Wan Wage kafaWa ya ce ""May be is her fisrt period"""

"A razane Aliyu ya ce ""What! Rumaisan? How old is she? Yarinya ce fa sosai"""

"Usman ya ce ""Ikon Allah"""

"Mai sunan Baba ya mia mata zani ya ce ta Waura ta fito. Ta Waura ta fito ya bata kujera ta zauna, Usman ya zuba"

ruwa ya wanke banWakin. Ruma kuwa jikinta sai rawa yake yi tana tunanin arshenta ne ya zo.

"Usman ne ya fita sayo pad, sai dai babu wanda ya san ya ake amfani da ita."

"Gaba Wayansu suka diririce, musamman ganin yadda ruma ke kuka, Huzaifa kamar ya tayata kukan, ita sam ba ta san"

"menene ya sameta ba, mai sunan Baba ne kawai yake ta wani basarwa."

"Aka kai mata ruwa tayi wanka, usman ya tattare kayan da ta cire, ya zuba a bokiti ya zuba musu ruwa."

"Gaba Waya mai sunan Baba ya rasa ta ina ma zai fara, gaba Waya baya manta lokacin da aka haifi ruma, kamar jiya aka haifeta haka yake gani, wai ita ce yau period ya zo, yarinyar da ko ciwon kanta ba ta sani ba, ban da tarin rashin"

"hankali da rashin kunya ba abin da ta sani, duk wani abu da ya shafi rayuwa ba saninsa ta yi ba."

"Sai da yayi browsing, sannan ya ga yadda ake amfani da pad, ya nuna mata, har zuwa yadda ake discarding Win ta, ta"

"karSa ta saka, sannan ta saka kaya."

"Ya kalli su Usman ya ce ""Su basu wuri, za su yi magana"" ba musu duk suka fita."

"Ya kalli ruma ya ce ""Kalleni nan"" ta Waga kai ta kalleshi."

"""Ko akwai wani abu da ya haWaki da wani?"""

"Ta ce ""Eh"" gabansa yayi wata irin mummunar faWuwa ya ce ""Menene?kuma waye shi?"""

"""Wani mutumi ne, ruwan kwata ya watsa mini da motarsa jiya da safe""."

"""Ba wannan nake nufi ba, ko akwai wani wanda yayi miki abin da bai dace ba, ko wasan banza ko ya kai hannunsa"

"jikinki?"""

"Tunowa ta yi da takawa, yadda ya cakumota, amma tayaya za ta fara yi wa mai sunan Baba wannan bayanin, ai kan a"

"kai ga takawa, ita zai fara tattakawa, a karon farko da ta yi masa arya ta ce ""Babu kowa"""

"""To idan ma akwai ki ka i faWa, idan na gano sai na yankaki na zuba a rijiya, kuma wannan yanayi da ki ka shiga, duk"

"wanda ki ka bari ya taSaki ko yayi miki wasan banza, ciki zaki yi kuma mutuwa zaki yi"" gaban ruma ne yayi mummunan faWuwa, meye makomar taSata da takawa yayi? Ta yi ciki kenan?."

"Haka suka shimfiWa tabarma a tsakar gida, suka kewaye ruma, yau har masu zuwa ball ba wanda ya fita, suna ta jera"

"mata sannu, ban da masu fifita da masu ba ta abinci."

"A haka mama ta dawo ta tarar da su, cikin mamaki ta dube su ta ce ""Wai har yanzu jikin ne?"""

"Usman ya ce ""Tun da ki ka fita a haka take"""

"Mama ta ce ""To Allah ya ara afuwa, wallahi ina can muna fama, da yar aka samu aka Wora yarinyar nan, tana jin"

"jiki, sannu 'yar auta"" ruma dai ba ta amsawa mama ba, ta sake lafewa a cinyar Aliyu."

"Mai sunan Baba kuma yana gefe kamar mai gadi, yana kallonsu."

"Mama ta kalli kayan ruma da suke shanye, gidan ko ina tsaf, amma ko girkin dare ba su Wora ba."

"Mama ta ce ""Yasir, tashi ka Wora mana ko taliya ce a ci da daddare"" gaba Waya basu da walwala kamar wadda aka ce"

musu ruman mutuwa ta yi.

"Cikin damuwa mama ta ce ""Wai me yake faruwa ne duk na ga kun yi jugum-jugum? Duk dan ba ta da lafiya ne ku ka"

"zo ku ka tare a wuri Waya haka, ba an sayo mata magunguna ba?"""

"Duk shiru suka yi, suna sunkuyar da kai aka rasa mai iya yi wa mama bayani."

"""Mama fitsarin jini fa nake yi "" Ruma ta yi maganar daga kwance."

"""Wane irin fitsarin jini kuma? A garin yaya?"" Mama ta yi maganar a tsorace."

"Usman ya Wan yi gyaran murya ya ce ""Wato ainihin, muna tunanin, wato ko.. abin nan na mata da suke duk wata, wato haila shi ta fara"" waro ido waje mama ta yi ta ce ""Ban gane ba"""

Mai sunan Baba ne ya karSa yayi wa mama cikakken bayanin abin da yake faruwa.

"Mama ta yi salati tare da tafa hannu ta ce ""Ruma haila, iko sai Allah girma ya riga hankali zuwa, a yanayin jikinta ban"

"taSa kawo zuwan wannan abun yanzun ba, ikon Allah"""

"""Mama wai menene ya sameni?"""

"""Girma ki ka yi"" mama ta bata amsa."

"Mama ta sake kallon igiya da kayanta a kan igiya, ta jinjina kai ta ce ""Lallai anwar maza, yanzu har Wan kamfan ma"

"ku kuka wanke mata? Iko sai Allah to Allah ya shiga lamarin, amma akwai badaala""."

"""Mama wai mutuwa zan yi?"""

"""Ba mutuwa zaki yi ba, abin da yake hana 'yan makarantar ku salla shi ne ya zo kanki"". A gaban su Yasir mama ta"

"zauna tana yi mata bayanin komai, sai a yanzu ta gane wasu daga cikin karatun da aka yi musu a Islamiyya in da suka dosa."

"Gaba Waya jikin ruma yayi sanyi, babu babban abin da ya tsorata ruma, sai cewa da mama ta yi ita ma yanzu za a din ga rubuta mata zunubi idan ta yi saSo."

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku, dan Allah kar a rubuta mini zunubi""."

"Aliyu da ta kwanta a kan cinyarsa ya ce ""Wallahi sai an rubuta miki, gara tun wuri ki nutsu ki shiga hankalinki"""

"""Astagfirullah, dan Allah mama kar a rubuta mini zunubi, ba na jin magana, dan Allah mama kar a din ga rubuta mini"

"zunubi bana son na mutu yanzu. Wayyo Allahna"""

"Mama ta ce ""Iko sai Allah, na ga yadda za ayi wannan lamari da wannan yarinyar mara kan gado""."

"Har zuwa washegari aka samu zazzaSi ya sauka, amma jikinta babu wari, mama da kanta ta kaita banWaki za ta yi"

"mata wanka, sai dai pad Win jikinta ba ta Saci ba, mama tana yi mata wanka ruma tana Soye irjinta. Mama kawai ta yi dariya ta cigaba da silleta."

"Da ta fito da ita kuwa, tuni sun haWa mata tea, Yasir ya Wauko mata kayan sawa, har da pad Win da zata saka."

"Mama kawai girgiza kai ta yi, gaba Waya sun wani nutsu sun damu, duk saboda anwarsu."

"Ruma ta yamutsa fuska ta ce ""Ni ba zan saka wannan abar ba, damuna take yi?"""

"Mama ta ce ""A haka zaki zauna?"""

Ruma ta Waga kai alamar eh.

"""Aikuwa kya Sata jikinki, a haka jininki ya are, ni babu ruwana"" mama kan ta mazewa take yi, amma lamarin ya zo mata a bazata, ba ta taSa kawo wannan abu nan kusa a kan ruma ba."

"Da yar ruma ta yadda ta saka pad Win nan, duk nasihar da mama tayi mata, tare da bayani, lokacin salla na yi ta Wau"

buta ta ce ita alwala za ta yi.

"""Wai ke wace irin yarinya ce ne haka? Ba na yi miki bayanin babu salla, babu azumi, ga duk wadda take haila ba""."

"""To ni mama da wanne zan ji, kin ce mini za a din ga rubuta mini zunubi,. Yanzu kuma kin ce ba zan salla ba, in shiga"

"wuta kenan?"""

"""Wai ke Meyasa duk bayanin da za ayi miki, ba zaki tsaya ki fuskanta ba sai dai ki yi ta wauta, Allah ne ya Wauke miki,"

"sai kin yi tsarki zaki yi salla"" Aliyu yayi Maganar a fusace dan ya fara gajiya da halin ruman, ana mata bayani tana bauWewa."

"Tun ranar da ya Wan zubo Win nan, bai sake zubowa ba, ruma ko wawwaran motsi ba ta yi, ga pad ta isheta gaba"

Waya abin duniya ya isheta.

"Tun daga kwana Wayan nan ya Wauke, mama da kanta ta kaita banWaki ta koya mata yadda ake wanka, babu babban"

"abin da yake cigaba da Wagawa ruma hankali, cewa da mama ta yi, ita ma za a fara rubuta mata zunubi."

"Ta tattara laifin kacokan ta Wora shi a kan takawa, wanda a dalilinsa duk haka ta sameta, dan daga watsa mata taSo ya sa ta fara rashin lafiya, wannan abun ya zo mata."

"Mama ta ce a bar tafiyar su katsina, sai bayan ruma ta gama warwarewa zuwa wani satin."

***

"Takawa kuwa har zuwa yanzu, bai daina jin muryar ruma ta na zuwar masa ba, abin har mamaki yake bashi. Wasu lokutan a zahiri yake jin muryar tana yi masa gizo, gashi tun daga ranar yau kwanaki huWu kenan, bai sake arba da wani abu da ya shafe ta ba."

"Haryanzu zuciyarsa ta kasa nutsuwa da cewar ruma mutum ce, duk da sidi ya tabbatar masa da binciken da ya yi a kan ta da makarantar da take zuwa, wanda makarantar yayi niyyar zuwa, amma suka haWu a hanya."

"Tunawar da ya yi cewa yana da tafiya Abuja jibi zai je wata ganawa ta musamman da wasu lawyoyi, tuna hakan ya sanya shi dawowa nutuswarsa, ya bar tunanin ruma ya tashi ya fice."

"Gidansu ya tafi, ya je ya samu Ammi dan sanar mata da batun tafiyar sa. Cikin damuwa Ammi ta ce ""Ina fatan ba a"

"kan mutanen ne zaka yi tafiyar ba, ka je ka cigaba da bin diddiginsu su illataka ba?"""

"Takawa ya ce ""A'a Ammi, tattaunawa ce da wasu lauyoyi, kwanaki uku kawai zan yi na dawo"""

"""To Allah ya kaimu, ka kula sosai takawa, ka rie azkar sannan ka sanya Allah a ranka, kar saboda kana da matsala da"

"wani ka sako shi a gaba da niyyar fansa, ka saka Allah a cikin lamuranka"""

"""In sha Allah ammi"""

"""Allah Ubangiji ya tsare, zaka ci Abincin dare a nan ne, ko kuma gida zaka tafi?"""

"""Ina da ayyuka a gida Ammi, ku ci abincinku kawai""."

"""To Shikenan, Allah ya tsare"""

"Ya amsa da Amin, ya tashi ya fita."

"Yana daf da kaiwa in da motarsa take, motar Mummy ta yi parking. Ta buWe ofar motar ta fito ta nufi Adam tana"

wani irin murmushi.

"""Manya gatan wasa, a gidan ka wuni ashe, kwana biyu ba ka shigowa mu gaisa"""

"""Na yi busy ne"" ya bata amsa a taaice."

"""Ashe Abuja za ka tafi, to Allah ya tsare"""

"an turus ya yi yana tunani, ya aka yi ta sani? Amma kasancewar ba ya son yin doguwar magana, mussaman da ita,"

"ya sanya bai tsaya bin diddiginta ba, ya buWe motarsa ya shiga."

***

"Sarai ruma ta warke, mama ta sake haWa mata kayanta, sai dai dare ya raba, ruma ta na cikin net Win ta tana ta bacci,"

"mama kuma ta zubawa jakar da ta haWawa ruma kayanta, haka nan ta ji ba ta son tafiyar da ruma za ta yi, kuma ba ta ji za ta iya hana tafiyar ba, ba ta taSa rabuwa da ruma na lokaci mai tsawo ba sai wannan karon, gaba Waya jikin mama a sanyaye yake, ba ta da wani kuzari, zuciyarta na raya mata ko ta hana tafiyar da ruma, amma daga asan zuciyarta ba ta ji ta yarda da wannan shawarar ba."

"Tun asuba ruma ta fesa wanka, sai murna take ba ta taSa tafiya mai nisa da wayonta ba, mussaman barin Kano,"

"mama dai jiki a sanyaye take taya ruma shiryawa, tana yi tana mata nasiha, a kan ta nutsu har su je su dawo, ban da gantali da neman magana."

"arfe goma na safe, suka kammala shiryawa, Aliyu ya Wau jakar kayan, suka tafi, ruma sai Wagawa mama hannu take"

"tana murmushi, yayin da mama ko murmushin ta kasa, ruma ta Wauko wayarta ta wurin Yasir, ta saka a jakarta."

"Gaba Waya su kansu sauran yayyen na ta, jikinsu a sanyaye yake, kamar su ce a fasa tafiyar da ita, daga arshe da ta gallabe su, suka ce Allah ya raka taki gona."

"angaren takawa ma, yau ta kasance ranar da zai tafi Abuja, ya biya gida ya yi wa Ammi sallama, sannan ya Wauki"

"mai kaishi airport, ya dawo da motar. Sai dai tun a daren jiya yake jin ba ya son tafiyar, duk da ba yau ya fara tafiye- tafiye ba, amma yana jin sa wani iri, kamar akwai wani abu mai muhimmanci da zai yi nesa da shi, yana tsaye yana gyara agogon hannunsa, Ammi sai kallonsa take yi."

"Ya kalleta ya ce ""Ammi, ya dai na ga kina ta kallona?"""

"""Haka kawai bana son ka tafi ne, ji na yi kamar na ce ka fasa""."

"Murmushi ya yi ya ce ""Ammi kenan, sai ka ce zan bar gari, saudiyya fa sai da ns kwana ashirin da takwas, kwanaki"

"uku fa zan yi kacal na dawo, ki yi mini addu'a, idan su Nusaiba sun dawo daga makaranta, ace musu na tafi"" Ammi ta jinjina kai ta ce ""Allah ya tsare"" ya Wau jakarsa ya fice."

"Huzaifa da Yasir, sai da suka raka su Aliyu tasha, suka hau mota, Ruma sai Waga musu hannu take, ta na yi musu"

"gwalo, wai ba za a tafi da su ba."

"Tun da suka baro tashar suka nufo gida, jikin Yasir yake a sanyaye, Huzaifa na ta magana, amma ya kasa amsa masa."

"""Wai lafiya na ji ka yi shiru?"""

"""Huzaifa, ji na yi ban yarda da motar nan da su ruma suka hau ba"""

"Ya kalli Yasir cikin mamaki ya ce ""Saboda me?"""

"""Mutanen da suke cikin motar ne ba su yi mini ba sam, ni duk wani iri nake ji a jikina!!!"

Ayshercool

08081012143

"*Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haWa mini document Win littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da"

"abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haWa mini document Win littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*"

"*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*"

"Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Aliyu ya ce ""Magana ake miki, ihun me ki ke yi wa mutane?"""

"Ta Wan Wago ta kalleshi, idanunta sun yi ja saboda gajiyar tafiya ga bacci da bai isheta ba ga kuma razana da ta yi."

"""Mafarki na yi na tsorata"""

"""Kuma shine ba zaki yi addu'a ba,waye ma ya ce ki kwanta ki yi bacci da la'asar Win nan?"""

"Gwaggo ta ce ""Daina yi mata faWa, wannan ba laifin kowa bane laifin babarku ne, bana tunanin ta na nemawa"

"yarinyar nan maganin tsari, wataila aljanu ne ko kuma mayu suka tsorata ta, bana raba Waya biyu suke bibiyarta"""

"Ruma ta waro ido ta ce ""Mayu kuma, ni fa wani mutum nake gani, ki daina tsorata ni"""

"""Ahaf sai kuma ki yi, ko dai maye ne, ko kuma aljani shi ya sa ki ke ganinsa, kurwarki ya ke son lashews"" shiru ruma"

ta yi tana tunani a kan mafarkin da ta yi.

"""Aikuwa sai dai ya ci kansa, ba dai ni ba"""

"""Tashi kiyi sallar magariba, a samo mini gaushi, na turara miki tsakin kuka da tazargade haWi da turaren mayu, koma"

"menene zai barki, ai kaf zuriyarmu kurwarmu tafi arfin maye, aljan kuwa sai dai yayi ya barmu"""

"Aliyu ya girgiza kai mutanen karkara sun yarda da camfi, kuma ba ka isa ka sauya musu ra'ayinsu ba."

"Takawa kuwa a hankali ya gama watstsakewa a kan gadon ba tare da ya motsa ba, a hankali ya furta ""Wai me na yi"

"miki ne haka ki ka sakani a gaba, wace irin jaraba ce wannan duk in da na motsa yarinya Waya nake gani, wannan idan har ba aljana ba wataila tana da wani mugun nufi a kaina, Allah ya shiga tsakanina da ke""."

"Rurin da wayarsa ke yi ne, ya sanya ya mia hannu a hankali ya janyo wayarsa ya duba, magariba ta riga ta yi, ya tarar da missed call rututu, wanda na Ammi duk ya fi yawa sai na Jabir."

"Ammi ya fara kira, bugu Waya ta Waga cikin damuwa ta ce ""Ina ka shiga ka ajiye wayarka nake ta nemanka ba ka"

"Wagawa?"""

"Ya Wan gyara muryarsa ya ce ""Ammi na ajiye duka wayoyin ne na fita, shi ya sa""."

"""Amma bai kamata ka ajiye wayoyi ka fita ba, ka saka hankalina ya Waga sosai, amma ya na ji muryarka a haka, ba ka da lafiya ne?"""

"Yayi Murmushin arfin hali ya ce ""Haba Ammi, lafiyata alau mura ce ta kamani, da na motsa sai ki ce bani da lafiya?"""

"""To ai dole sai ina yi ina bin diddigi, tun da ba cikakkiyar lafiya gareka ba, Ubangiji Allah ya tsare"""

"""Amin Ammi, na gode"" ya katse wayarz ya tashi a hankali, ya ji jikin da saui yanzu ba kamar Wazu ba, ya lallaSa ya"

"shiga banWaki yayi alwala, ya dawo ya yi salla."

***

"Har zuwa dare, ruma ta i sakin jikinta, kamar ba ita ce mai shegen surutun nan ba ta bi ta takure a wuri Waya kamar mara kuzari, gaba Waya ji take jikinta babu wari. Yaya Aliyu ne suke ta hira da Gwaggo, da wasu daga cikin samarin gidan da suka shigo, duk yadda suka so su yi wa ruma wasa ta kulasu tai, ta koma gefe ta takure ta sha kunu."

"Cikin damuwa Gwaggo ta ce ""Rumaisatuna, wai menene gaba Waya kin i sakin jikinki sai ka ce wata bauwa, me yake faruwa ne?"""

Sheshshea ruma ta fara sheshshear kuka.

Gaba Waya hankalinsu ya dawo kanta.

"""Menene, me ki ke so?"" Ta yi shiru ba ta ce komai ba."

"Aliyu ya ce ""Ba magana ake miki ba?"""

"""Gida"" ta faWa tana rushewa da kuka."

"""To dan ubanki nan a titi kike ba a gida ba?"" Aliyu yayi Maganar a hasale dan daga tahowarsu zuwa yanzu, ruma ta"

kai shi bango.

"""Ni mama nake son gani, ka kira mini ita a waya"". Gwaggo ta ce ""To shikenan, yi shiru a kira miki ita. Ka ga illolin"

"rashin zumunci ko? Yanzu da ana zuwa da ita, yaushe zata yi kuka dan tana cikinmu, ai duk abu Waya ne, amma kalli yanzu kallon bai take yi mana, yi maza ka kira mata ita ko ta daina kukan""."

"Takaici ya rufe Aliyu, kamar ya tashi ya naWawa ruma duka, sai iskanci take kamar wadda aka kawo yaye, ya kira"

"mama a wayarsa, ya jefawa ruma jikinta."

"Mama na Waga wayar ruma ta saka kuka, cikin kiWima mama ta ce ""Lafiya kuwa ruma, menene?"""

"""Mama gida, ni ba zan iya bacci ba"""

"Mama ta ce ""Haba ruma, ai sai ki Waga mini hankali, ba kun sauka lafiya ba ko wani abun aka yi miki?"""

"""Ba ayi mini komai ba, ni kawai gida a kusa da ke zan kwana, kuma ina son in ga su Yasir da Abdallah da yaya usy""."

"""Ke dai ki na da shirme, to da aure aka yi miki fa, dangin mahaifinku ne fa nan ma gida ne ruma, duk abin da ki ke so"

"za su yi miki, dan Allah ki daina Waga musu hankali"""

"""To ni gaskiya ki ce a dawo da ni gida gobe, ni so nake na ganki dan Allah""."

"Mama ta ce ""Ke ki mayar da hankalin ki, bana son sakarci fa, meye haka ne ruma, kawai daga zuwa baunta ki tayar"

"musu da hankali, ko sai na haWaki da babana?"""

"Da sauri ruma ta ce ""A'a""."

"""To ki nutsu ki daina yi musu kuka"""

"Ruma tana share hawaye, wasu na gangarowa ta ce ""To, na daina""."

"""Yauwwa, sannan ki yi fitsari kan ki kwanta, kar ki yi musu fitsarin kwance kin san dai kashedin da na yi miki ko?"""

"""Eh"""

"""To ki nutsu, sai da safe ki gaida gwaggon"""

"Usman ya karSi wayar a hannun mama ya ce ""Ke ruma, maman nono za ta baki da zaki din ga kuka ke mama, to idan"

"ma shayar da ke take yau an yayeki"""

"Cikin shagwaSa ta ce ""Yaya ussy""."

"Ya amsa da""Na'am anwar maza""."

"""Yaya usy ina son in ganka""."

"""To idan kin gannin lada za a baki? Zan gayawa Ali, idan kin samu miji a nan mun bar musu ke, su aurar da ke""."

"Aliyu ya fizge wayarsa ya ce ""Ba katin banza ne da ni ba, kar Allah ya sa ki daina kukan, dama akwai karnuka da suke"

"yawo a garin da daddare, idan baki nutsu ba, a ofar gida zaki kwana""."

"Gwaggo ce kawai ta din ga rarrashin ruma, ta gyara mata kan gadonta na arfe ta kwanta."

"Tsananin gajiyar mota, da baunta ya sanya bacci kwashe ruma."

"angaren mama ma, hakan take, kewar ruma take sosai, tun yamma su Huzaifa suka fuskanci hakan suke tsokanar"

"mama suna mata dariya, wai yau an Wauke mama 'yar gudaliyar ifrituwarta, duk ta damu."

"Mama ta din ga basarwa, irin ko a jikinta Win nan, amma tun da ta ji kukan ruma hankalinta ya ara tashi, cikin dare"

"kuwa kasa bacci tayi, sai kallon wurin shimfiWar ruma take yi. Sai yanzu take jin ina ma ba ta bayar da ruma an tafi da ita ba, dan gaba Waya hankalinta ya i kwanciya."

***

"Samha ce zaune a wani katafaren office, tare da Khalifa wakili, sai juyi yake a kan kujera yana kallonta yana mata murmushi, ita kuwa ta yi tsuru-tsuru kamar Sera ya kwan a gadon kyanwa."

"""Ki kwantar da hankalinki mana, babu wani abun damuwa a ciki fa"""

"""Khalifa, dan Allah kamar yadda muka yi yarjejeniya, tare da yin alawari a fari, dan Allah kar ka cutar da Adam, ni yanzu haka ma fa a tsorace nake"""

"Yayi wata makirar dariya ya ce ""Lallai kin damu da shi da yawa, kar ki ji komai fa, kin fara naki Sangaren, saura Waya Sangaren suma za su yi nasu role Win """

"""Amma haryanzu ba ka gaya mini su waye Waya Sangaren ba, kuma aikin me zasu yi ba su, bayan da fari ce mini kai"

"deal Win ni da kaine kawai""."

"""Saken da ki ka yi na rashin ba da amsa da wuri ya sanya third party joining deal Win, kuma na ga za su taimaka sosai,"

"shi ya sa na haWaku ku duka a tafiyar, amma ki kwantar da hankalinki ba wata matsala"" Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Shikenan, ni zan wuce sai ka ji ni""."

"Ya ce ""To a sauka lafiya, zamu yi magana"" bayan fitar Samha Khalifa yayi wata uwar dariya ya ce ""Yaro man kaza, zaki"

"gane baki da wayo"""

"angaren samha ma bayan fitarta jinjina kai ta yi ta ce ""Yaro bai san wuta ba sai ya taka, da na yi achieving abin da"

"nake so, zan nuna maka wacece mace, zaka gane ba ka da wayo, kuma zan gano wanda ka sako a cikin sabgar nan bayan ni, zan baka mamaki""."

****

"Ko da garin Allah ya waye ma, aka yi alwala aka yi salla, ruma ta gaida wanda ta ga zata iya gaisarwa, ta koma ta yi shiru abun ta."

"Lawisa ta dubi ruma ta ce ""Sannu, kina buatar wani abun ne?"""

"Ruma a ranta ta ce ""Wannan yarinyar kin isheni wlh"" a zahiri kuwa ruma ta shareta, dan ita ji take kamar a kan wuta"

"take, ba ta son zaman gidan nan."

"Aka yi abin karin kumallo, kunun tsamiya da wainar gero, ga kunun na daka ne, sai amshi yake, sai dai tun da Aliyu"

"ya ga an kawo kunu, kuma kunun babu suga yake kallon ruma ya ga, wani action za ta yi, za ta sha ne ta yi kara ko halin za ta nuna."

"Ta kalli kofin kunun, ta kalli Aliyu, amma ya kawar da kansa, ya na shan nasa."

"Lawalli da yake yayan lawisa ya ce ""Rumaisa ki sha kunun mana"""

"""Bana shan kunu"" ta faWa a raunace."

"Ya ce ""Au mutan birni ba cimarku ba ce ba, Gwaggo dafa mata shayi, bari na sayo madara a shago, a sayo miki"

"burodi"""

"Dariya ruma ta yi ta ce ""Meye kuma burodi, buredi ake cewa ai"" karo na farko da tun da ta zo ta yi dariya, gaba Waya hausar ta su wani iri take jin ta."

"Shima ya yi dariyar ya ce ""To shikenan buredi bakanuwa""."

"Ta ce ""Banda buredi, shayin kawai zan ci wainar geron"""

"Aliyu ya galla mata

Please Login or Register in order to submit comment