You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake tsuke fuska ya Wam risuna ya ce ""Barka da zuwa"""

"Wambai ya ™i kulashi, shi kuma Adam bai tashi ba."

"""Wato wuyanka har yayi kaurin da zan aika maka ka zo, ka yi burus da kirana ko?"""

"Yayi shiru bai ko motsa ba, sai ma alamun Sacin rai da suka baiyyana a fuskar shi."

"Da sauri Ammi ta ce ""Allah ya taimake ka tuba yake yi, ayyuka ne suka sha masa kai, ga rashin lafiya da....."

"""Ya isa binta, dama ke ki ke goya masa baya yake abun da ya ga dama, bai san darajar mutane ba sai zuciya ta banza"

"da ta wofi, tabbas na fara gazgata jita-jitar da ake yi a kansa, na cewar yana shaye-shaye, duba da yanayin abubuwan da yake aikatawa, kalli yadda yake muzurai kamar zai kai mini duka, kalli yadda yake yawo a gari, kamar ba jinin sarauta ba, kalli ™ananan kayan da ke jikinsa, duk wani abu da ya shafi al'adar gidan nan nema yake ya watsr da ita, saboda kawai ya raina mutane."

"Cikin dakiya Ammi ta sake cewa ""Tuba yake, ayi masa afuwa""."

"Adam a zuciyarsa kuwa ji yake yi tamkar ya tashi yayi tafiyarsa, don cigaba da sauraren wambai, na iya sanya wa ya"

"WuWWura masa ashar ya huta, saboda takaici."

"Wambai ya mayar da idonsa kan Ammi ya ce 'Na san kina sane da maganar da take yawo a cikin masarautar nan, na"

"yayi shaye-shaye yayi yim™urin yi wa waccan yarinya fyaWe, yayin da daga wata majiyar muka samu labarin ba fyaWe bane ba, wani abu ne a tsakaninsu daban, to dukkaninku ku sani, ko da Wan uwana baya raye, ba zan lamuncin mutunci da martabar gidan nan ta lalace ba, a hakan ka ke saka ran sarauta ta shiga hannunka, kana shaye-shaye ga kuma wannan mummunar maganar, ba zan lamunta ba, tun kan maganar nan ta je wurin mai martaba, zan yi wa tufkar hanci, ni na san abun yi. Ke binta ina mai baki umarni a kan lallai wannan yarinya 'yar tsintuwa, ko dai ki nemi ahalinta ki mayar musu da ita, ko kuma ki nema mata miji ta tattara ta bar cikin gidan nan, na baki nan da abun da bai wuce watanni biyu ba, ta daina amfani da kyawunta tana barazana ga mutuncin gidan nan ba. Labarai suna zuwar mana, yadda ake ta samun akasin auren 'ya'yan jamila saboda ita, to ki san abun yi tun kan ku kai ni bango "". Iman ta yi shiru ta sunkuyar da kai, ta ri™e yatsun Ammi tana wasa da su, tana Wan murzawa da ™arfi, saboda azabar Sacin rai da damuwa."

"Haka wambai ya ™arewa Ammi cin mutunci ita da yaranta, a gaban Mummy, daga bisani ya sallame su."

"Tun kan su gama watsewa daga falon, iman ta fashe da kuka, mussaman da ake ce wai ita ce ke barazana ga"

"mutuncin gidan. Adam rasa abin da zai ce ya yi, bayan fitar wambai Mummy ta ce ""Sai ha™uri fa binta, yaran yau me ka haifesu ba ka haifi halinsu, a zage a bawa yara tarbiyya, kan a samar mana da abun kunyar da zamu gagara kallon duniya, ko mu rasa sarautarmu gaba Waya"". Babu wanda ya tanka mata a cikin su, har Adam da yake zaune yana jin ta."

"Bayan fitar Mummy Adam ya ce ""Ammi, Allah fa bai ce in bi wan ubana ba, ke da marigayi kune yake wajibina na"

"biku, dan haka babu ni babu wannan tsohon da zuriyarsa har gaban abada, ba zan ™ara zuwan kiran da zai yi mini ba, kuma ba zan sake zama a gabansa na yi masa kallon uba ba, ita kuma Mummy haryanzu kin hanani dama a kanta, shikenan idan har zamu cigaba da zuba mata ido, to fa zata cigaba da ™o™arin ganinmu a rana ne. Ni ban damu ba dama can ni Wan iska ne mara mutunci a cikin masarautar nan, amma ba zan cigaba da lamuntar wula™anta iman ba, ko dan saboda ita yakamata ko sau Waya ki kareta"" ya ™arasa maganar a matu™ar zafafe, ya tashi ya bar falon."

"Daga Nusaiba har iman saka Ammi suka yi a gaba suna yi mata kuka, ta rasa abun da zata yi, ta rungumesu duka a"

jikinta tana ajiyar zuciya.

"Tabbas takawa yayi gaskiya, ha™uri da kawaicin da take nunawa a kan abubuwan da ake yi wa iman da ma iya kanta da yaranta, yayi yawa, sai dai ba tana yin hakan da wula™anta iman ko 'ya'yanta ba, sai dan gudun kar ayi ™o™arin"

rabata da ita.

***

"Ko arzikin ganin tafin hannunta rumaisa ba ta iya yi, saboda duhun da ya mamaye ilahirin dajin, sai kukan abubuwa daban daban da take ji, lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma ta ji shiru kamar babu wata halitta da ta wanzu a cikin dajin."

"Sai yanzu ta gane a wurin 'yan ta'addam nan a rahama take, ko ba komai tana jin motsin mutane, idan ta gaji kuma tana yi musu kuka ko da zasu hantareta, wani irin sauro da kuma wasu irin ™wari ne suke gasa mata cizo ko ta ko ina."

"Ta yi iya ™o™arin ta ta nannaWe jaririn, dan kar ™wari su cije shi, sai numfashi yake sama-sama, jikinsa ya Wau zafi, ita"

"kanta rumaisan zazzaSi ne a jikinta, ga wata irin azababbiyar ™ishirwa da kuma yunwa da take ji. A haka ta jingina a jikin bishiya tana addu'a tana kuka ™asa-™asa, ba dan tana tausayin jaririn nan ba, da kuma tsoron wanda ya kashe kansa makomarsa wuta ba, to da babu abun da zai hanata ta kashe kanta."

"A hankali take sauke numfashi tana soshe-soshe, babu alamar tana jin bacci a idonta."

"Kamar wadda aka tsikara, ta tashi tana laluba hanya, tana tafiya a hankali, hannunta Wauke da jariri. Hayaniya ta fara"

jiyowa sama-sama ana maganganu.

"Dan haka ta din ga nufar in da sautin yake fitowa, tana nufar sautin tana hango hasken wuta yana ci, da alama dai mutane ne a wajen. A haka har ta cin musu, ta laSe tana le™awa, kusan zata iya cewa wata ™aramar masan'anta ce ta sarrafa makamai iri iri, manya da ™anana dan wasu ma ba ta san su ba, wasu suna shaye-shaye wasu suna ta shirya makamai, yayin da wasu ke ™idaya kuWi."

"""Kai har labari ya cika gari artabun da aka yi a dajin nan, mutuwar su sha tara duk ta cika jaridu, kuma haryanzu"

"babu wata ™ungiya da ta Wau alhakin kai wa su sha tara hari"" cewar wani da yake ta murza sigari."

"""Kuma ba jami'an tsaro bane ba, a cikin mu ne dai, kuma an kwashe mutanen suka yi garkuwa da su ba"" wani ya"

bashi amsa.

"""Haka na ji, daga sama an bada umarnin abi sahunsu, akwai wani jariri da wata mata ta haifa, ana son a tabattar da"

"baya raye, gobe akwai operation, dole a gano suwaye suka kai harin""."

"""Haka ne, amma yanzu a gama ware kayan nan, su je su rarraba, da safe a bar gari da su, kai yellow, ku zo ku Winke kuWin nan a cikin buhunhuna a kai su a daren nan, mutanen cikin bukkar nan kuwa duk wanda ba a kawo kuWin"

"fansar sa ba, ku ™addamar masa kawai""."

"Hawaye ne suka ziraro a fuskar rumaisa, wato nan ma wata tawagar ce ta daban, atishawa jaririn hannunta yayi,"

hakan ya janyo hankalinsu in da take.

"""Kai anya ba wani naman jejin ne a wurin ba, ku duba mana""."

"Rumaisa kuwa tuni ta bar wurin, tana addu'a, amma yadda suka dalle wurin da fitila a ya tsorata ta, dan tuni ta saka"

"ran an gansu, sai dai ta samu cikin ganyayyaki ta zauna tana mayar da numfashi."

"""Ni yanzu ya zan yi, ya Allah ko ban kuSuta ba ka kuSutar mini da jairirin nan na karSi amanar sa, Allah kar ka sa"

"rayuwarsa ta salwanta"" ta yi addu'ar a hankali."

"Da ta Wan ji dama-dama sai ta tashi ta cigaba da tafiya a hankali, tana shashafawa tana duba hanya, saboda babu haske kuma tana haWawa da addu'a."

"Jin gajiya tayi mata yawa, ga zazzaSi ya kamata sosai da sosai, ya sanya ta nemi wuri ta zauna, ta ha™ura da cigaba da"

"tafiyar, ta tattaSa ™irjin yaron zuwa hancinsa, ta ji yana numfashi, amma a galabaice, ga jikinsa zafi sosai."

"A haka ta takure da shi a jikinta. Ba ta sake sanin meyafaru ba, sai farkawa ta yi ta ga rana ta Waga sosai a kanta, ta duba jikinta duk fatarta tayi wani irin ba™i da kore-kore, ga ™afarta tayi tsami, saboda ciwukan da ta ji, da hanzari take sake lalube jaririn nan, amma babu abun da ya same shi, sai galabaita. Ta sake kwantar da shi a gefenta, ta lulluSe shi, tayi taimama ta yi sallar asuba da ta tsere mata."

"Har ta nemi wuri ta zauna, saboda gajiya da rashin ™warin jiki, amma zuciyarta ta tunatar da ita idan ta cigaba da"

"zama, yaron nan yana iya rasa ransa, dan haka ta tashi da ™yar, tana tattara yawun bakinta ta haWiye, saboda azabar"

"™ishirwa amma bakin nata a bushe yake, ta cigaba da bin hanya tare da fatan Allah ya fitar da su."

***

"Tun da garin Allah ya waye mama a rikice take, kaiwa kawai take tana komowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa abun da yake yi mata daWi."

"""Mama, dan Allah ki nutsu ki kwantar da hankalinki, kin san fa jininki ya hau""."

"Ta girgiza kai ta ce ""˜yaleni Abdallah, zuciyata ce take ta bugawa, ko dai an kashe rumaisa, ko kuma tana cikin"

"mawuyacin hali, na kasa samun nutsuwar zuciya""."

"""A'a mama, kar ki yi wannan fatan, ko sakawa kanki wannan tunanin, sharrin zuciya me kawai, amma in sha Allah"

"tana nan a cikin ™oshin lafiya"" Huzaifa ya yi maganar cikin damuwa."

"""Ba zaku gane me nake ji ba, ku ™yaleni kawai""."

"Aliyu kuwa tafe yake a hanya, ya je shago ya sayo abu, sama-sama ya ji ana kiransa, sai ya ji kamar muryar rumaisa,"

"nan da nan ya tsaya, ya waiwaya sai ya ga Habiba ce, tafe da kayan miya a hannunta, kan ta cim masa ta faWi saboda sauri, ya ™araso wurinta da sauri yana ""FaWin sannu, kk bi a hankali kar ki ji ciwo"" ba ta damu ba ta mi™e tsaye ta ce ""Yaya Aliyu gidanku dama zan je, mafarki na yi rumaisa ta dawo, shi ne na ce Allah ya sa gaske ne, na taho in ganta""."

"Shiru Aliyu yayi yana kallonta, yama rasa mai ze ce mata, a ransa ya ce 'Haka mama ta yi irin wannan mafarkin, Allah"

ya sanya ya zama gaskiya'

"A zahiri kuwa ya ce ""Ki na ji na ko Habiba?"""

"Idonta ne ya tara hawaye ta ce ""Dan Allah kar ka ce mini ba ta dawo ba""."

"""Ki yi ha™uri kin ji, amma rumaisa ba ta dawo ba, muna ta addu'a dai""."

"Kawai ta dur™usa a wurin, ta haWa kai da gwiwa ta saka kuka."

"A Wan rikice ya ce ""Tashi kar mutane su ce wani abun na yi miki""."

"Ya ri™e hannunta ya Wagata, sai kuka take yi."

"Sai yanzu ya ™ara tabattar da soyayya da sha™uwa da ke tsakanin rumaisa da Habiba, bayan duk saSanin da suka din ga samu, amma ta™i nutsuwa saboda rashin rumaisa."

"Ya kai mintuna ashirin yana rarrashinta, ba tare da ya ™osa ba, saboda ™aunar da ta nunawa rumaisa, ya sa yake jin kamar rumaisan ce take kuka."

***

"Takawa kuwa ya shirya cikin wani farin yadi, yana ™o™arin saka hula, message ya shiga wayarsa."

"*Adam ka Wan yi mini uzuri, abu ya kamani zan je katsina, sai in Allah ya kaimu gobe zan shigo kano*"

"Wani takaici ne ya kama takawa, a ganinsa bashir ya gama raina masa hankali, cikin hasala ya kira wayar Bashir"

"amma ya ji ta a kashe, ko uwar me zai je yi a Katsina oho."

"Wata irin ™wafa yayi, ya kwashi mukullin motarsa da wayoyinsa ya fita, yana jin zafin abun da Bashir yayi masa."

***

"Rumaisa kuwa ita kanta ta san ta galabaita, dan ta fara fidda rai da rayuwa. Tsakankanin wasu ciyayi ta kutsa, kawai ta ganta a wani fili, ta tsaya cak tana kallon wurin, idonta ya sauka a kan wani mutum a tsaye ya gama fitsari gefe ga bindigarsa."

"Yana waiwayowa suka yi ido huWu da rumaisa ""Ke wacece, me ki ke yi a nan?"" Ja da baya ta fara yi, ya Wauki bindigarsa ya nufeta. Ai ba ta san lokacin da wani kuzari ya zo mata ba, ta juya da gudu ta bar wurin, aikuwa ya bita, Wan uwansa da yake cikin ciyayi, shi ma ya fito ya rufa musu baya."

"Sosai take gudu tsakanin rayuwa da mutuwa, ta yi wa jariririn nan kyakykyawan ri™o, tana jin yadda numfashinta ke"

"barazanar rabuwa da huhunta, ™arfinta ya fara ™arewa, amma Wan ragowar hope Win da take da shi na samun damar yin rayuwa ko jaririn nan ya rayu, ya sanya ta cigaba da bawa kanta ™warin gwiwa, ba ta iya gane meye a gabanta, saboda azabar wahala dishi-dishi take gani, babu zato babu tsammani ta yi karo da wani nannauyan abu, mai ™arfin gaske, ™atuwar bishiyar kuka ce, da rumaisa ba ta ankara da ita ba, suka yi karo, a take ta silale ™asa ™eyarta ta bugu, jini ya fara zuba, jaririn ya faWi a gefe Waya."

Ayshercool

08081012143

"*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*"

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*

"*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ˜URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE˜I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*"

"*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*"

"*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai"

"da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*"

*Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

"*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*"

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

"*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*"

"*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*"

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

"*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*"

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*

*14. Supplement na whitening/glowing skin*

"*15. Supplement for Acne, dark spots remover*"

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da

"kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*"

"*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai"

"ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*"

"Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba"

"a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*"

"A harabar gida takawa yana shirin fita, suka kiciSis da Jabir, jabir ya dube shi ya ce ""Ina zaka ne haka? Na ga yau"

"Saturday babu aiki?""."

"Adam yayi ajiyar zuciya ya ce ""Bashir ne yake yi mini yawo da hankali, sonake mu haWu ayi wadda za ayi, amma sai raina mini hankali yake, na ce zan bishi Abuja ya ce na jira yazo kan da kansa, kawai sai kuma ganin message Win sa"

"na gani, wai za shi katsina, uban me zai je yi a katsina?"""

"""To amma yanzu ina zaka je?""."

"""Zan je na yi aikina da kaina ne"" ya bashi amsa yana kallon agogon hannunsa."

"Jabir ya gyara tsayuwarsa ya ce ""Kayi aikinka ko ka Satawa kan ka lokaci, wata ™ila akwai dalilin da ya sanya yake yi"

"maka yawo da hankali, ka yi ha™uri ka bi komai a hankali, ka bashi yau zuwa gobe in Allah ya kaimu mana""."

"Adam ya girgiza masa kai ya ce ""No, ba zan iya ba"" ya juya zai nufi mota. Jabir ya ri™o shi ya dube shi ya ce ""Bashir amintaccen ka ne, bana tunanin zai yi wani abu da zai yi maka yawo da hankali, ko ya cutar da kai, Please ka bashi ko"

"zuwa gobe in Allah ya kaimu ne"" da ™yar jabir ya lallaSa takawa dan ba laifi Adam akwai ba™in taurin kai""."

***

"A hankali take motsawa, ta fara ™o™arin juyawa, dan gaba Waya a tunaninta bacci take yi, sai dai ta ji wani irin azabar raWaWi a ™eyarta, zuwa kanta da wuyanta, a hankali ta tashi zaune tana waige-waige."

"Jaririn yana nan in da ya faWi, yana ta motsawa a hankali yana zura hannunsa a bakinsa, yana ta numfashi sama-"

"sama. Rumaisa ta zuba masa ido hawaye na zuba daga idonta, haryanzu jikinsa da ™azantar haihuwa, duk ya fita a hayyacinsa. Wani irin jiri take ji, ta kalli in da ta faWi ta ga jini, na in da ta fasa ™eya ta faWi."

"Ta kalli ™ugunta haryanzu tana Waure da Wankwalin Anty Aisha da ta bata, ta ja jikinta zuwa kusa da jaririn, ta ri™e hannunsa tana kuka ""Ka yi ha™uri yarona, na kasa baka kulawar da yakamata, kaga nima yarinya ce ban san me kake bu™ata a matsayin ka na jariri na, na rasa yadda zan yi mu bar wurin nan, dan Allah kar ka mutu kamar yadda mamanka ta tafi ta barni"" tayi maganar kamar tana yi da sa'anta."

"A haka cike da tsananin muradin cigaba da rayuwa, ta sake Waukarsa ta mi™e cikin ™arfin hali, ta cigaba da tafiya, sai"

"dai ba ta je ko ina ba ta kasa, ta silale ta zauna a jikin wani dutse ta zubawa sarautar Allah ido."

"Kamar a mafarki rumaisa ta ga wasu irin dandazon shanu sun cika wurin, ita dai ba ta san ta in da suka Sullo ba, ta"

"hangi mai kiwonsu, yana ta ratsawa ta cikinsu. A gefenta ta din ga ganin wata inuwa, ta Waga kai sai ta ga wata bafulatana, doguwa do jerin ™orrai a kanta, ta kalli rumaisa ta ce ""'yar nan dan Allah taimaka mini na sauke ™orran nan""."

"Ruma ta harari matar ta kawar da kai, kamar ba ta ga a halin da take ciki ba, take cewa ta sauke mata wannan uban"

"™waryoyin, can matar ta kuma cewa ""Rumaisa da ke fa nake"" ruma ta kalli matar cikin mamaki za ta yi magana ta fasa, ta kwantar da yaron, ta mi™e ta kamawa matar suka sauke ™orran."

"Ta koma ta zauna ta na cigaba da kallon jaririnta, matar ta din ga auna nono, ba tare da kuma tankawa rumaisa ba, can rumaisa ta ce ""Dan Allah baiwar Allah ki taimaka mini da ruwa da nono na bawa yaron nan, ni ko ba zaki bani ba, shi ki bashi dan Allah""."

"Matar ta yi murmushi ta ce ""Ai na zata ba zaki kulani ba, na tashi na yi tafiyata""."

"Ta mi™awa rumaisa battar ruwa, ta karSa ta Wago jaririn za ta bashi, matar ta karSe shi ta bashi ruwan, sannan ta"

"buWe wata ™warya ta tsiyayo madara fresh ba a daWe da tasota ba, ta fara bashi, aikuwa duk da bashi da lafiya, haka ya din ga karSa yana sha, kamar zai cinye da mazubin."

"Rumaisa sai murmushi take, ganin ya samu ruwa da abun da zai ci."

"Matar ta kalli ruma ta ce ""Ba dan halinki ba bari na san miki ruwa ki sha, ruma manyan gari, ruma kaya da yani,"

"gwagwarmaya na gaba ba ta zo ba kuma ba ta wuce ba""."

"""Wai ke a ina ki sanni?"" Ruma ta tambayi matar."

"Matar ta yi murmushi ta ce ""Ke waye bai sanki ba, karSi ruwan ki sha, kar kuma ki manta ki kula da amanar da aka"

"baki, Allah ya taimake ki baki mini rashin kunya ba, Kodayake jikin ta ™aura yayi la'asar, wallahi da a dajin nan zan barki, amma ki ka taimaka mini, sha ruwan na rage miki hanya "" rumaisa ba ta gama gane me matar ke cewa ba, ta karSi abun ruwa ta kafa kai, sai dai ma™warwa biyu ruwan ya ™are ba ta ™oshi ba."

"Lumshe ido rumaisa ta fara yi, tana jin yadda kanta yake ™ara nauyi, ta karSi yaronta daga hannun matar ta rungume, sai sunkuyar da kai take, kamar ta yi shaye-shaye saboda ji take kamar zata fita daga hayyacinta."

"""Ke!ke! Baiwar Allah me ki ke yi a gefen titi haka?"" Rumaisa ji ta yi kamar ta farka daga bacci, ta buWe idonta sosai,"

"irin zaman da tayi ta rungume yaron a haka take, sai dai a wani wurin ta ganta daban, jeji ne wurin sai dai tana zaune a gefen titi, kwalta WoWar."

"""Me ki ke yi a nan, ina zaki je?"""

Ta Waga kai ta kalleshi amma ta ba ta kula shi ba.

"""Ko dai mahaukaciya ce ne? Wannan yaron na waye, ni da na zaci tsohuwa ce ashe yarinya ce, daga ina ki ke Wan"

"waye a hannunki?"""

"""Šana ne"" ta bashi amsa."

"Mutumin ya ce ""A'a ba dai Wanki ba, ina hijjabinki, ina ne gidanku?""."

"""Kai dan Allah ka ™yaleni haba"" tayi maganar tana neman wurin kwanciya."

"""Karki kwanta da jaririn nan a wurin nan, ki gaya mini in da zaki in kai ki""."

"Ta kalleshi ta ce ""Ka san Worayi?""."

"""A'a wanne gari ne?"""

"""Tun da baka sani ba Shikenan, na gode sosai"" gani yayi kamar maganar da rumaisa take yi, haukacewa ta yi ba a"

"hayyacinta take ba. Wata dan™areriyar mota ce ta yi parking a wurin da mutumin yake tsaye a kan rumaisa, da tuni mutane suka fara taruwa a wurin."

"""Bawan Allah lafiya, meyake faruwa ne?""."

"Ya kalli na cikin motar ya ce ""Wallahi kaga yanzu nake dawowa, na biyo hanya ns ga wannan yarinyar da jariri, ta ma"

"dai ™i bari na ga yaron, amma kamar dai mahaukaciya ce""."

"""A'a dawanau ce ni ba mahaukaciya ba, kai haka ake tainako ™ishirwa nake ji, amma ko ruwa bai bani ba yake ce"

"mini mahaukaciya""."

"Na cikin motar ya Wauko ruwan

Please Login or Register in order to submit comment