You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

balle ace a taka mace da tsohon ciki, abun da ban tausayi."

"Daga mama har ammi kowa sai goge hawaye take yi, sabir ne ya motsa ya fara kuka, mai sunan baba ya sanya hannu"

ya Wauke shi ya fita da shi waje.

"Ya ™urawa yaron ido, sunan mahaifinsu rumaisa ta saka masa, ya tuna irin faWi tashi da sadaukarwa da mama take yi a kansu, tun suna yara har zuwa yanzu da suka zama mutane ba ta daina ba, amma shi wannan Wan bai san wannan ba, hasali ma tasa uwar tana kawo shi duniya ta mutu ta bar shi a dokar daji a hannun yarinyar da ita kanta ba ta san ciwon kanta ba, ta yi kwanaki tana gararanba da shi a daji babu ko wando a jikinsa ga ™azantar haihuwa."

"Wani irin tausayin yaron ya kama shi, ya rungume shi a ™irjinsa yana shafa bayansa, wata irin ™wallar tausayin yaron"

ta cika masa ido.

"Abubakar kuwa tamkar wani daga cikin 'yan uwansa ne suka suma aka kwantar da su, sai kai wa yake yi yana"

"komowa, sai da ya ga lokaci na neman ™ure masa sannan ya Wau jakarsa ya tafi."

"Ko da su Usman suka zo mamaki ne ya kama su, ganin halin da su mama suke ciki, fuskokinsu Wauke da damuwa,"

"idon mama yayi ja saboda kuka, ammi kuwa har a lokacin kuka take yi. Aliyu ne ya fara maganatuwa ya ce ""Mama lafiya kuwa? Meyafaru ne?"""

"Mama ta girgiza masa kai ta ce ""Lafiya ™alau, ya kuka baro gidan an gama komai?""."

"Usman ya ce ""Mama, ya zamu ga kuna kuka kuma ku ce lafiya ™alau, meyafaru?"""

"""Baban yaron nan ne babu lafiya, ashe mahaifiyar sabir da ake ta fama da rumaisa a kan ta yi bayani ta™i, ashe"

"rasuwa ta yi, a hannun'yan bindigar ta rasu""."

"Dafe ™irji Aliyu ya yi yana Innalillahi wa Innalillahi raji'un, usman kuwa sak yayi duk da bai san matar ba, amma"

tausayinta ya kama shi.

"""Mama rumaisa kuwa na da hankali, kuma shine ake ta fama da ita ta yi mursisi ta™i faWa, saboda tsabar rashin kan gado"""

"""To ka san halinta da ba™in taurin kai, yanzun ma babana ne ya sakaya a gaba ya zare mata ido, amma yan sandan"

"da suka zo suma ™in kula su ta yi""."

"Cikin damuwa usman ya kalli Ammi ya ce ""Dan Allah ku yi ha™uri, wallahi yarinyar nan haka take sai a hankali wasu"

"lokutan, bai kamata ta Soye abu mai girma irin wannan ba, ku yi ha™uri Allah ya ji™anta da rahama ya sanya ta huta""."

"Ammi ta ce ""Amin, ku daina ganin laifinta a kan gaskiyarta take, yanzu ihu ake bayan hari, kamata yayi a kai musu"

"Wauki tun suna hannun 'yan bindigar. Ba ta yi mini komai ba, babu abun da zan ce wa rumaisa sai fatan Allah ya rayata, ya shiryata ya tsareta na gode sosai da sosai"". Ta kai maganar tana kuka."

"Usman cikin damuwa yake duban Ammi ya ce ""Ki yi ha™uri, sai a gode Allah da ya kuSutar da Wan ta, ko ba komai za"

"a kalla ace ga Wan Aisha, kuSutar yaron nan kawai ya ishi a godewa Allah, duk da ya karSi uwarsa, komai yayi daidai ne, ki yi ha™uri, ki yi ha™uri Allah ya yafe mata, ya kula mana da jaririnta, ku yi ha™uri dan Allah kuka ba mafita bane, duk da dole ne jin zafi a duk lokacin da muka rasa makusanta mu da muke so, amma ayi ha™uri, duk jarrabawar da Allah ya yi wa bawa dai-dai ce""."

"Duk da ba wasu shekaru ne da usaman ba, amma ammi har cikin zuciyarta ta ji daWin yadda suka nuna damuwa a"

"kan ta. Ta ce ""Na gode Allah ya yi albarka"""

"˜asan zuciyar ammi kuwa, tashin hankali ne mai yawan gaske, dan al'umar sun yi dagulewar da ba ta san ta ina zata"

kamo bakin zaren ba.

"Sai wajen azahar rumaisa ta farka, ji take kamar ba a gaske ta faWa musu mutuwar Aisha ba, mai sunan baba ta gani zaune a gefen gadonta, yana juya Sabir yana murmushi gefen baki, mai sunan baba da kan ka ga dariyar sa aiki ne ja,"

"ruma za ta iya cewa tun da ta buWi ido a duniya ba ta taSa ganin mai sunan baba ya Wauki Wan wani ba, wani irin daWi ta ji da ta gan shi Wauke da Sabir."

"Ya dubi ruma ya ce ""Sannu kin tashi?"" Ta jinjina masa kai alamar eh."

"""Babu wata matsala dai ko?"""

"""Eh babu, baban mama kana son mai sunan babanmu ko?"" Ya jinjina mata kai, a lokacin da yake gyarawa sabir"

"kwanciyar sa a hannunsa, duk da ba wani ™warewa yayi a iya Waukar yara ba."

"""Mai sunan baba dan Allah kar ku bari a rabani da shi, wallahi mamansa ta ce ta bar mini shi, da gaske nake ba wasa"

"ba"" kallonta kawai ya yi bai ce mata komai ba."

"Ammi kuma na kan dadduma tana jin su, amma ba ta tanka ba."

"Su Iman sun kira wayar ammi har sun gaji, dan ™arshe ma kashe wayarta ta yi ma gaba Waya, dan ba ta san me za ta ce musu ba."

"Adam kuwa ya shafe awanni a emergency ana fama, domin a ceto ransa, sam zuciyarsa ta ™i bugawa yadda yakamata, bpn sa ma an kasa picking Win sa, ga numfashin sa ma yayi ™asa fiye da yadda ake so, su kansu likitocin sun fara fidda rai, da ™yar da taimakon Allah ya farfaWo ya samu bacci, sai da ya yi baccin ne sannan aka fito da shi a ka bashi Waki."

"Wunin ranar da su Aliyu aka yi ta sintiri a kan Adam, in an jima usman ya zauna ya yi ta yi wa ammi nasiha yana ba"

"ta ha™uri. Sai da aka fito da shi, sannan aka ce ammi ta je ta ganshi."

"Aka yi mata jagora har Wakin da yake, dan har ta fara fitar da rai a kan sa, jin shiru-shiru ba a fito da shi ba, ta zaci ko"

shi ma ya rasun ne.

"Ta tsaya tana ™are masa kallo, ga robar ruwa nan a sa™ale, shi kuma idonsa a rufe yana bacci."

"Ta kama hannunsa a cikin nata, ta saka hannunta Waya tana shafa kansa ta ce ""Na sani akwai wahala, amma ka ™ara jurewa, tun da na haifeka a kullum akwai fejin ™addara da kake buWewa babi babi, da an wuce wannan sai wannan,"

"na sani da wahala amma ka ™ara jurewa addu'a ta tana tare da kai yarona. Allah ya shiga lamarinka Adam, Allah ya cigaba da dafa maka ya baka ikon cin jarrabawa"" tayi maganar tana rushewa da kuka."

"Bashir ya ce ""Ammi, addu'a nan dai, ita zaki cigaba, kar jininki ya hau fa, kuma yanzu mun gano bakin zaren, tun da"

"ta tabatta ta rasu, sai mu san abun yi na gaba, Allah ya yi mata rahama""."

"Aka din ga rarrashin ammi ana bata baki, daga bisani Bashir ya sallami direbanta, bayan magariba bashir ya ce zai"

"mayar da ita gida, ya dawo ya zauna da Adam."

"Mama ta ce ""A'a, ita zata kwana a wurinsa"""

"Aliyu ya ce ""Haba dai, saboda rashin kara ka wuni kana kaiwa da komowa, ita ma ta wuni a nan kuma ace ku kwana,"

"ai ba wani abu, ko ni sai na zauna na kwana da shi""."

"Ammi ta ce ""Kar a Wora muku Wawainiya"""

"""Wallahi ba wata Wawainiya, Allah ya bashi lafiya kawai""."

"Daga gida har wurin adam kowanne tana son ta zauna, amma ya zama dole ta zaSi tafiya gida, domin kuwa ba ta son"

"kowa ya farga da abun da ya faru kan su sanar da kansu, ta san rashin zamanta a gidan, kan iya jefa zargi a wurin masu son ganin bayanta, dan haka a dole ta yarda Bashir ya Wauketa ya mayar da ita gida."

Aikuwa a falo ta tarar da su Nusaiba a zazzaune fuskokinsu duk babu daWi.

"Nusai ce ta fara cewa ""Ammi akwai matsala ne, tun safe mun kira wayarki ba kya Wagawa hankalinmu duk ya tashi,"

"yanzu uncle Jamil ya bar gidan nan yana nema ya Waga mana hankali wai ina takawa yake?"""

"Gaban Ammi ne ya faWi, kar dai ya san wani abun ne, ta buWe baki da ™yar ta ce ""Ya ce muku wani abun ne?"""

"""A'a kawai dai yana tambayar mu wai ina yake, baya samunsa a waya, ya je gidansa ma baya nan"""

"""Babu wani abu, ban zaci zan kai haka ba nima, amma ai gani na dawo"""

"Buutt baba uwani ta fito cikin girmamawa ta ce ""Allah ya ja zamaninki, ha™i™a yau mun wuni cikin zulumi da tashin hankali, mussaman da baki wuni a gida ba na tambayi su auta, sun ce ba su san in da ki ka tafi ba, ga wayarki ba ta"

"shiga duk sun shiga damuwa kamar marayu""."

"Ammi ta ce ""Gani na dawo, uzuri ne ya ri™e ni, zan shiga in huta, kar wanda ya shigo mini""."

"Iman ta ce ""Ammina abinci fa?""."

"""Na ci"" ta faWa a ta™aice ta wuce sashinta."

"Nusaiba ta ja hannun iman, ta yi ™asa da muryarta ta ce ""Anya kuwa babu matsala?""."

"Jiki a sanyaye Iman ta ce ""Nima haka nake tunani, amma ta ce kar wanda ya je in da take balle mu ji""."

"Nusaiba ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Bari mu jira zuwa Allah ya kaimu da safe mu gani"""

"Iman ta amsa da ""Allah ya kaimu ya sa lafiya"""

"Tafiyar Ammi babu daWewa Adam ya farka, Aliyu ya yi masa sannu, ya Wan jinjina masa kai."

"Ya yin™ura zai tashi, Aliyu ya taimaka masa ya tashi zaune, ya bashi ruwa ya sha."

"Aliyu ya ce ""Zaka ci wani abun ne?"" Adam ya girgiza kai ya ce ""Salla zan yi""."

"Aliyu ya taimaka masa ya kai shi banWaki yayi alwala, ya dawo da shi ya shimfiWa masa abun salla, ya jero sallolin da"

"suke kansa, sai dai bai tambayi Aliyu komai ba, can kamar an mintsine shi ya ce ""Da gaske ™anwarka take matata ta mutu ko?"""

"Jiki a sanyaye Aliyu ya ce ""Haka ne, amma dan Allah ka karSi ™addara ka yi ha™uri, ka ga da ™yar likitoci suka ceto"

"ranka, mahaifiyarka na cikin damuwa, kar ka sake sawa hankalinta ya tashi""."

"Hawaye ne ya taru a idon Adam, ya haWiye wani abu mai Waci, da sai da adams apple na ma™ogwaronsa ya motsa sosai, cikin rawar murya ya ce ""Jikina ya daWe yana bani ta rasu, amma zuciyata ta ™i aminta da hakan, ina jin zan"

"sake ganinta, zan sake kallon fuskarta, ashe bankwana na yi da ita, na san ko gawarta bani da ikon gani, balle in binneta da hannuna ina yi mata addu'a da tuna biyayyarta da soyayarta, wayasani ma ko yar da gawarta suka yi ta lalace a haka, sun tozarta ni, sun tozarta iyalina. Amma ni musulmi ne, muslmi ne ni tabbas, dole na yi imani da ™addara. Ku rarrashi ™anwarku, amma a gobe in Allah ya kaimu zan karSi Wana, zan je gaban sirikina, kuma uba a wurina, in sanar masa komai, ya Wauki duk matakin da yake ganin ya dace da ni""."

AYSHERCOOL.

08081012143

"*paid book ne, ¦ 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*"

"Wani irin tausayinsa ne ya kama Aliyu, duk yadda adam ya so Soye hawayensa kasawa yayi, ya barsu suka din ga"

zuba son ransu.

"Da ™yar Aliyu ya Wan yi gyaran murya ya ce ""Kamar yadda ka ce kai musulmi ne ka yarda da ™addara, to Yakamata a"

"ga hakan a aikace, ka yi ha™uri in sha Allah sirikinka zai fuskance ka, Allah ya yi mata rahama""."

"Mama ce ta yi sallama a Wakin tana faWin ""Aliyu ya tashi kuwa?""."

"Ta tarar da su a zaune, mama ta ce ""Alhamdilillah ala kulli halin, Allah mun gode maka, sannu ka ji?"" Ya jinjina wa"

mama kai yana share hawaye.

"""Ayi ha™uri, a fawallawa Allah, yaronka mahaifiyarka da sauran makusantanka suna bu™atar ka, ita tata ta ™are ta yi"

"shahada sai fatan Allah ya karSi shahadarta, ayi ha™uri, Aliyu je ka Waki ka kawo ruwan shayi da abinci ya samu ya saka wani abu a cikin sa""."

"Aliyu ya tashi ya fita, yana fita lokitan dare ya shigo, ya dudduba Adam aka bashi maganinsa na dare, likita ya jaddada masa ya kula da magani da dokokin da aka saka masa."

"Sam Adam ba ya fahimtar abun da likitan yake faWa, mama ta mi™a masa kofin shayi cikin kulawa ta ce ""Daure ka sha, ka ga an baka magani, dole sai ka ci abinci"" kallon mama kawai yake yi, wato duk in da uwa take uwa ce, yadda ta ke ta nuna kulawa a kansa sai ya ji daWi, duk da tarin damuwar da yake ciki."

"Duk da ba zai iya tantance manufar kulawar da mama take bashi ba, amma tun da ya taso kulawa Waya ce yake gani ta zahiri, wato kulawar ammi ban da haka galibi masu yi masa murmushi suna yin sa ne da biyu."

"Da ™yar ya karSi kofin shayin, ya Wan sha kaWan ya ajiye, mama ta yi ta masa nasiha, da rarrashi cikin siga ta dattaku"

da manyance.

"Ya Wan murza zoben hannunsa ya ce ""Da ke da iyalinki, babu abun da zan iya ce muku sai godiya, a rayuwata na daWe ban ga mutane masu karamcinku ba. Amma dan Allah ku yi ha™uri da abun da zan faWa, ina son zan karSi yarona, dan Allah a rarrashi mamansa, na san zata tsaneni fiye da da, amma ni ba zan iya da rigimarta ba, a bata ha™uri zan Wau yaron nan zan tafi da shi wurin kakansa, sai hukuncin da ya yanke a kanmu""."

"A take mama ta ji babu daWi, domin ita kanta ta sha™u da jaririn ba kaWan ba, ya shiga ranta."

"A zahiri ta ce ""Babu laifi, Ubangiji Allah ya raya shi bisa tafarkin addinin musulunci, ya ji™an mahaifiyarsa. Amma ina"

"fatan ba zaka rabamu da shi gaba Waya ba, dan a halin rumaisa bana jin za ta iya ha™ura""."

"Yayi murmushi ga hawaye na zuba daga idonsa ya ce ""Za ta saba in sha Allah, ba zata damu sosai ba amma yarona"

"yana bu™atar kariya ta musamman, ba zan manta soyayyar da ta nunawa gudan jinina ba"""

"Jiki a sanyaye mama ta ce ""Babu laifi, Allah ya ji™an mahaifiyarsa, kai kuma ya baka lafiya"" da haka mama ta yi musu"

"sallama ta koma Wakin da rumaisa take. Ta kwanta tana facing Win Sabir, tana ta baccinta, ta saka hannu ta ri™e masa nasa hannun suna bacci."

"Tausayinsu ne ya kama mama, amma babu yadda ta iya, haka ta shiga harhaWa wa sabir kayansa, a daren ta haWa komai cif a wuri Waya."

"Suma ta haWa musu nasu kayan, dan ta ji likitan yana cewa washegari zai sallami rumaisa, tun da ita ma ta warware sai abun da ba a rasa ba."

"Sai da ta kammala, sannan ta yi alwala ta tayar da salla."

"Da asubar fari, sabir ya tashi yana 'yan koke-koke, mama ta Wauke shi ta yi masa wanka, ta bashi madararsa, ita"

"kanta mama tana matu™ar ™aunar yaron da tausayinsa, ta Wauke shi ta goya shi a bayanta, ta yi sallar asuba, ta tashi ruma ta yi salla sannan ta fita daga Wakin."

"Harabar asibitin ta koma ta kira mai sunan baba, tana shiga ya Waga, ya gaida mama, ta amsa masa sannan ta ce ""Babana, dan Allah da gari yayi haske ka taho asibitin nan, yau za a sallami rumaisa, kuma yau za su karSi Wan su, ka san halinta sarai, jiya da daddare babansa da ya farfaWo ya ce zai karSi Wan sa ya tafi da shi ya gabatar da shi a danginsa, sannan ya sanar da rasuwar uwar Wan""."

"Mai sunan baba ya Wan yi shiru sannan ya ce b""Babu laifi, zan shigo in sha Allah, amma a bita a hankali dan Allah, ko"

"a bari na zo tukuna"""

"Mama ta ce ""ai shi ya sa na ce sai ka zo Win"""

"Bayan sallar asuba, Adam ya karSi wayarsa a hannun Aliyu, ya kira ammi, suka yi magana, ta ji daWi sosai da jin muryarsa, tayi masa addu'a da fatan alkhairi."

"Ya kira Bashir ma suka gaisa, tare da sanar da shi, ya je ya taho da Ammi."

"Kiran jabir ne yake ta shigowa tun bayan da ya kunna wayar, kamar ya share sai kuma ya Waga."

"""Wai ina ka shiga haka baka Waga wayata? Ya ake ciki ne akwai wani labari ne? Ko ka koma wurin yarinyar?"""

"""A'a ban koma ba, zan koma bacci yanzu zan zo gida in sameka anjima"" bai ko tsaya saurarar mai jabir zai ce ba, ya"

"kashe wayar ya ajiye, haryanzu ya kasa gazgata maganganun rumaisa, wai Aisha ta mutu, ganin abun yake kamar almara, sai yanzu ya gane ka rasa mutum ka ga gawarsa wata ni'ima ce, ba irin tunanin da bai zo masa a kan gawar Aisha ba."

"Abun mamaki yau ruma ta™i komawa bacci, mama har tambayar ta ta yi ba zata koma bacci ba, ta ce ba ta ji."

"Ta dubi in da mama ta haWa kayansu ta ce ""Mama wai tafiya zamu yi ne an sallame ni?""."

"""Eh, in anjima za a sallame mu"""

"""Yeeee dama na gaji da zaman asibitin nan wallahi, yau sai gida, ga kayana ga na babyna nima na samu mai sunan"

"babana, sai dai Allah ya sa kar yayi halin mai sunan kakanmu"" tayi maganar da sigar tsokanar mama, amma mama ba ta tanka mata ba."

"Har gari ya waye ruma idonta biyu, ta damu mama a kan ta bata sabir, amma mama ta hanata."

"Wajen ™arfe tara, Usman da mai sunan baba suka zo, ruma tana ta murna zata tafi gida, dan zumuWi ta ce abincin"

ma sai ta je gida zata ci.

"Usman ya din ga kwasar kayansu yana fitarwa, sai murna take yi yau ba kwanan asibiti, dan takardar sallama kawai"

suke jira daga likita.

"Bashir ne ya shigo Wakin rumaisa, ya kalleta yayi murmushi ya ce ""Yau sai gida uwar rikici"""

"Ta yi murmushi ta ce ""Šan uwanmu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, jin godiyar nake ma ta yi kaWan a baki, amma zan din ga yi maka Addu'a idan na yi salla"".."

"Yayi murmushi ya ce ""Kai masha Allah, amma na gode ™warai da gaske, sister na asiya ma tana gaishe ki, ita ma ba ta"

"da lafiya ne. Amma kin je kin duba baban sabir kuwa?"""

"Ta Wan yi turus tana kallon mama, mama ta ce 'Yanzu zan sakata a gaba mu je ta duba shi, sai mu tafi""."

"Bashir ya ce ""Yauwwa mama, dama ga ammi can ma ta zo sai ku yi sallama, ai bai kamata ku tafi babu sallama ba""."

"""To ai yaya Aliyu ya ce bai mutu ba, har ya tashi"""

"""Haba rumaisa, idan da kara yakamata ki je ki duba shi, ko dan albarkacin sabir Winki""."

"Usman ya ce ""Sai ka lallaSata ma, wuce mu je, kuma saura mu je ki yi rashin kan gadon naki, ya saka dogarai su saita"

"miki zama""."

"Suka Wunguma zuwa Wakin da takawa yake, suka tarar ammi na zaune a kusa da shi, ta ri™e hannunsa, tana share"

masa hawaye.

"Ammi na ganinsu tayi murmushi ta ce ""Kun fito? Yau ban ™araso mun gaisa ba rumaisa, hankalina ne a tashe"""

"Ruma ta dur™usa ta gaisheta, ta amsa mata cikin girmamawa."

"Usman ya ce ""Ki yi masa sannu mana""ta dubi Adam za ta yi masa magana, amma gabanta ya faWi, ganin gaba Waya"

"idonsa ya koma ba™i, yana fitar da haya™i."

"Mannewa ta yi bayan usman, tana le™o shi, taga ita yake kallo, amma idonsa yana ta haya™i, kallonsu take yi, tana"

"jiran ta ji wani yayi magana a kan idon takawa, amma ta ji babu wanda yayi magana da alama su ba sa gani."

"""Ba zaki yi masa sannun ba?"""

"Ta sunkuyar da kanta ™asa ta Wan zuro kai ta ce ""Sannu, Allah ya bada lada"" tayi maganar a rikice dan a razane take, bata taSa ganin idon mutum a haka ba."

"Bashir ya ce ""Ladan me kuma rumaisa, shi da ba shi da lafiya?""."

"""Au ba lada ba, Allah ya warkar da shi"""

"Usman ya ce ""Yau kuma meke damunki ne?"""

"Mama ce ta kwance Sabir daga bayanta, mai sunan baba ya karSe shi, ya ™arasa gaban gadon Adam ya ce ""Allah ya"

"™ara lafiya, ya ji™an mamansa, kamar yadda ka bu™ata ga yaronka, Allah ya raya shi, Allah ya biyaka Wawainiyar da ka yi da ™anwarmu"". Adam ya karSi Sabir, yana ™o™arin mayar da hawayen idonsa."

"A rikice ruma ta ce ""Ban gane ga Wan sa nan ba, da shi zan tafi ai, ni anty aisha ta bar wa shi"" tayi maganar tana"

"nufar Adam, amma mai sunan baba ya tare ta ya ce ""Juya mu tafi"" karo na farko da ta tsaya ta saka idonta a nasa ta ce ""To ka karSo mini Wana""."

"""Ni nake magana ki ke mayar mini?""."

"""Haba mai sunan baba, ya za ayi a ™wace mini yarona, dama abun da aka shirya kenan? Mama ki saka baki"" ta dubi Ammi ta ce ""Dan Allah ku bani yarona, na sha wahala kan mu tsira tare, idan aka ™wace mini shi, mutuwa zan yi,"

"wallahi ina son sa sosai, Wan uwanmu yaya bashir, dan Allah ka karSo mini Wana"""

"Gaba Waya sai tausayin rumaisa ya kama su. Ammi ta ce ""Kina ji ruma, ki kwantar da hankalinki, babu mai rabaki da yaronki, zamu je a kai shi cikin dangi ne, kuma in sha Allah za a din ga kawo miki shi ki ganshi""."

"Rumaisa ta fashe da kuka ta ce ""Da na san haka ne, gara na zauna mu mutu a dajin, da da wannan mutumin ya ce in"

"tafi ba zan tafi ba, gara a harbeni, kwanana biyu ba ma bacci ni da sabir, saboda sanyi yana kuka, kwanana uku ina bulayin hanyar da zamu dawo, kuma a ™wace mini shi bayan mun sha da ™yar, ba anty aisha ba sabir Wina. Dan an ga ni yarinya ce za a ™wace mini Wa"" Mai saunan baba ya dan™i hannunta zai yi waje da ita, tana kuka tana mi™a hannu tana ""Dan Allah ku bani sabir Wina"" tun da ruma ta fara kukan nan tana zuba, ko Waga kai Adam bai yi ba ya sunkuyar da kansa ™asa."

"Kuka sosai rumaisa take yi, tamkar an ce mata mama ta mutu, bashir ya rakosu yana ™o™arin rarrashinta, amma mai"

"sunan baba ya ce ya rabu da ita, ya buWe mota ya sakata, amma sai mi™a hannu take taka kuka."

"""Ki rufewa mutane baki, idan an baki Wan ya zaki yi da shi, ke wace irin yarinya ce da ba a isa a gaya miki, ko ki rufe"

"mini baki, ko na casaki a wurin nan"" mai sunan baba yayi mata wata irin tsawa mai razanarwa."

"A gigice ta ™an™ame mama tana ™o™arin haWiye kukanta, amma ta kusa ™warewa saboda kuka, ga hawaye ga majina"

"har da yawu, saboda kuka."

"Ammi na tsaye tana hango rumaisa yadda ake fama da ita, wani irin tausayinta ya kamata. Allah kenan ya karSi uwar"

"yaron, kuma ya sanya soyayyarsa mai tsanani a wata zuciyar."

"A hankali ta juya ta koma Wakin da adam yake, yana rungume da jaririnsa."

"Ammi ya dube shi ta ce ""To me ka yanke? A ganina mu bari nan da ko kwanaki biyu ne ka gama warwarewa""."

"Adam ya girgiza kai ya ce ""Ammi, ba zan taSa warkewa ba, barin lamarin ina sake jinkirta loka8, abubuwa caSewa za"

"su cigaba da yi, daga nan gidan turaki zan wuce, zan je na sanar masa da laifina gaba Waya duk hukuncin da ya yanke a kaina shikenan""."

"Cikin damuwa Ammi ta ce ""Kana ganin hakan shine mafita?""."

"""Ammi dole ita kaWai ce mafita, na yi zaton aisha tana raye ne dama, shi ya sanya nake ta jinkirtawa, amma na yadda ta rasu yanzu, yanzu zan fara fuskantar mai girma turaki, daga baya kuma sai na fuskance ™alubale na gaba""."

"Ammi ta Wan yi shiru yana kallon ™asa, daga bisani ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Shin, Ubangiji Allah ya yi mana jagora"

"baki Waya """

Ya amsa da amin.

"Bashir suka shigo tare da likita, likitan ya dubi adam da yake rungume da jariri ya ce ""Allah sarki rumaisa, gaskiya ta sha™u da yaron nan, ba ka kyauya ba da ka ™wace mata Wa"" Adam ya sunkuyar da kai ba tare da ya iya yin magana ba."

"""To Yanzu me yake damunka, zan rubuta maka teses na yi reviewing file Win ka, na ga vitals Win ka duk normal""."

"""Sallama nake so"" ya faWa a ta™aice."

"""Meyasa zamu sallameka? Dole mu ri™e ka zuwa gobe in Allah ya kaimu mu ga

Please Login or Register in order to submit comment