You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng NI DA YAYA SADEEQ


Love story 2021 typing free book



Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya (Sbeauty)

EWF📚💪


TSOKACI

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, ban ƙirƙiri littafin NI DA YAYA SADEEQ
saboda wani ko wata ba, nayi ne saboda nishadantar da Al'umma gami da faɗakar da
su, kuma wannan shine littafina na farko fatan zakuyi hakuri da kura kuran da zaku
ci karo da su.

SADAUKARWA

Wannan littafin sukutum ɗin sa, sadaukarwa ne ga mahaifiya ta. Hajiya Rukayya
Muhammad (kamfani)


_________________________________

Shafi na farko

‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

_______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda, isaka na kaɗa bishiyar mangwaron
da ke tsakiyar gidan mu, ganyen ta na faɗowa ƙasa gunin burgewa, dambu ne a gabana
cikin wata y'ar samira inaci ina suɗe yatsun hannu na, saboda dambun yayi min daɗi
kamar kar ya ƙare.

Ƙawata Ladiyo ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da
jini, koda na ɗaga kaina na kalle ta bance mata uffan ba, illah maida kaina ƙasa da
nai na cigaba da cin dambu na, sai da na cinye dambun tas sannan na kora da ruwa,
kana na buɗe baki na iya ƙarfi na nayi wata ƙatuwar gyatsa, wacce da gani kasan
tarashin mutunci ce, irin wacce idan yaya Sadeeƙ yana guri nayi yake buge min baki.

Kallan Ladiyo nayi na taɓe baki na ce "Ladiyo wai lafiya kika zo ki ka tsaya min a
kai? Ko aiko akayi?".

Ladiyo da dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana
iya faɗa min na gwasale ta, tana kuka take faɗan abinda ya faru cewa "ina yaron da
jiya muka barar mai da markaɗe?".

"Eh na tuna shi me yafaru?".

"Yanzu haka daga aken da Ummata tai min gidan su Zulai anso mata kuɗin zubin a
dashi nike, bayan na anso kuɗin, kan hanya ta ta dawowa na haɗu da yaron, wai ashe
nan ne layin su, shine yai tamin ruwan duwatsu tako ina, har wasu abokan sa da suka
gani suka taya sa, Allah ya taimake ni baban
Ramma yazo wucewa, shine da yaga abinda ke faruwa, ya tsawatar musu, shine suka
ƙyale ni, amma wallahi inaga da sai dai a ɗauko gawa ta saboda jifan da suka min
bana wasa bane, ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani saƙo gunki cewa, idon ki
idon shi sai ya fasa miki goshi".

"Kan uban nan, yanzu dama acikin ƙauyen nan a kwai wanda zaija dani, har ma yace
zai fasa min goshi, to ƙaryarsa taci ƙarya, wallahi kaf ƙauyen Dande banga mai tara
ta gaba da gaba ba, kin san dai ko ta baya sai an shirya, to amma tunda yace haka
muzuba ni dashi, shege ka fasa, ɗan halak sai yanka, kafin ya fasa min ni zan fara
zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji daɗin fasa min nawa da hujja".

Inna da fitowar ta daga ban ɗaki kenan da buta a hannun ta, bayan ta aje butar ta
ce "wai ke da wa siddeeƙah? Kike mulmulo irin wannan ashar ɗin, kamar bakya zuwa
islamiya"? .

Cikin sakalci na ce "yo Inna bakiga Ladiyo bane?".

Sai alokacin Inna ta lura da Ladiyo da ke a tsaye gindin rijiya hannun ta ɗore bisa
goshin ta.

"Na ganta sai akai yaya"?.

Cikin ƙosawa da tambayar da take min na ce "yo wai ke Inna bakiga goshin ta bane a
fashe jini yana zuba?".

"Na gani man, ai tunda taƙi rabuwa dake, tana tare da wahala, gashi ta zama lusara
bata iya taɓuka komai, amma tsokana fal cikin ta, tsokana kuwa tamai ƙarfi ce".

Na ce "yo Inna wanda yafasa mata goshin ne nima yace ace min ido na idon shi sai ya
fasa min, shine abin yabani dariya da takaici har kika ji nayi wannan ashar ɗin,
kuma wallahi idan duka ƙauyen nan gatan shi ne wallahi sai naci ubansa, duk abinda
zai faru ya daɗe bai faru ba, be san wace ce Siddeeƙar Inna bane shiyasa, amma ko
yaran goye aka amaba ta masa suna na, nan take jikin sa yake fara rawa saboda karo
dani babu daɗi".

Banyi aune ba naji anbige min baki, a masifance na ɗago da kaina dan naga wani mai
tsaurin idon ne, da har ina magana zai bigen baki.

Diriricewa nai, ganin shi a gaba na nasan ko ba a faɗa ba shine ya bigen baki,
ɗan ƙaramin baki na na zumɓuro. Yayin da muka haɗa ido ya wani kashe min idon sa
ɗaya. Yana cewa "shegiya mai zubin aljanu, bari na fara cin naki uban, kamin shi
yaci nasa, shashasha kawai, naga ƙafar ki a waje kiga yadda zanyi da ke, sakarya
daƙiƙiya kawai, ba arabi ba boko, sai yawan gaɗa a dandali, ke fa ko a cikin matan
ƙauyen kin fita zakka, saboda kinfi su wauta da tumasanci, saboda kin ga Inna na
ɗaure miki gindi kina yin abinda kika ga dama, kina ganin kamar gata take miki, to
ki sani Inna ta riga da ta gama cin kasuwar ta, ke kuma yanzu kike fara tasowa.
Saboda baki san komai game da rayuwa ba, kwata-kwata ma nawa kike? ko 14 years old
baki kaiba amma kin addabi mutanan gari, kullum ana cikin kawo ƙarar ki muna bada
haƙuri".

Ladiyo dake tsaye har yanzu kamar wacce aka dasa ya kalla, irin kallon nan na
gargaɗi kana ya ce "ke yama kike da suna?".

Ladiyo dake a tsaye hannun ta akan goshinta, cikin rawar baki da rikicewa ta ce
"Ladiyo".

"Oho koma dai maye sunan naki maza ki bi nan". yai mata nuni da hanyar fita gidan."

Ya kuma cewa "ko a ƙofar gidan nan idan kika bari na kuma ganin ki, to ko na lahira
sai yafiki jin daɗi, bare kuma in ga wa'innan y'an ƙafafuwan naki a cikin gidan
nan, Allah sai na ɓaɓɓallaki".
A kausashe ya ce "Ina fatan kinji abinda nace miki? idan kunne yaji gangar jiki ta
tsira. "Oya maza ɓace min da gani, kamin nayi ball da ke".

Ladiyo jiki na 'bari ta bar gidan mu, a ɗari da hamsin.

Kallo na yayi muka haɗa ido ya wurgo min harara, ramawa nima nayi, gami da haɗawa
da ƙunƙuni ciki-ciki na ce "nima fa idon nan ba fina akai ba, da har ake wani min
barazana da su, kuma mu zuba ni da kai, zaka san ka bige min baki".

"ke! Me kike cewa?".

Sai alokacin Inna tai magana, saboda tasan ɗazun ko tayi ba mai sauraron ta, ta ce
"haba Garba,
waini me yarinyar nan taimaka ne daka tsaneta? ba nason haka fa, tun ba yau ba
nasha faɗa maka, amma dake ka rainani bakajin magana ta, ko kaɗan saboda kaga ni
kaka ce, to alhaji ƙaramin zai zo ai, tunda watan ya kusan ƙarewa, idan kai ban isa
da kai ba shi na isa dashi. Kuma shine mahaifin ka, idan yafaɗa maka wataƙil kaji
nasa tunda ni kaƙi jin nawa".

Ya san halin Inna sarai da mita, dan haka sai ya kawo wasa a maganar ya ce "haba
hajjaju makkatun mu karrama, ranki shidaɗe, ki daɗe kiyi ƙarko, kiyi shekarun
bishiyar dabino, wane ni ai ban isa in raina ki ba, duk da cewa nike aurenki amma
ke ke bada umarnin, Kuma yadda Kiki ce hakan ake yi, ina mai tabbatar miki bani
kuma shiga shirgin ta daga yau".

washe baki Inna tai, cikin jin daɗin furucin shi ta ce " ko kaifa Garba shikenan ya
wuce amma da kasa ka y'ar mutane gaba sai ramewa take, shiga ciki yanxu zansa ta
kawo maka abincin naka.

💋💋💋💋💋💋
_Kar ku manta kuyi_

Comment
Shear
Vote

_I love you all_

💋💋💋💋💋💋

*S BEAUTY CE ✍️*

NI DA YAYA SADEEQ


Love story

Na

Siddiqatulkhaireey Yahya
(S beauty ✍️)


*EWF*✍️
_________________________________

Page 02

‫بسم الله الرحمن الرحيم‬
_________Inna tace, "daure ki tashi ki kaiwa yayan ki abincin sa, kinga daga aiki
ya dawo ya gaji ga yunwa".

Ɗaure fuska ta nayi ina turo baki nace, "ni dai Inna bazan kai mishi ba, duka na
zaiyi, baki ga yadda yake bina da kallo kamar wani tsohon maye ba, kwana biyu bai
samu ya dakeni ba, kinsan halin muguntar sa ba sai nayi masa laifi ba, yana iya ina
shiga ya rufo ƙofa, ya jibge ni, kin san
shi kullum cikin jin haushi na yake".

"A haba, yau dai Garba ko kunnan ƙashi ne dashi bazai dake ki ba, kina kallon yadda
na tsawatar mishi a gaban ki, idan ko har ya kuskura ya taɓa ki saina haɗashi da
Alhaji Ƙarami, tashi maza kije ki kai mai yar albarka".

"Yo ina abincin nasa yake?".

"Yana kitchen mana, inda kika ɗauko naki".

koda na ɗauko abincin a saman kaina na ɗorashi ina ɗigir-gire.

"A a fa kada tsautsayi yasa ki zubar mai, kinga yana cikin fushi, babu abinda
bazai iya miki ba". A cewar Inna

"Haba Inna bazai zube ba sai dai idan kece kike so ki zubar dashi, amma ai ba yau
nikeyi ba, kuma bai taɓa zubewa ba".

"To Allah ya bada sa'a" ta faɗa tana mai shigewa ɗaki abinta.

Ni ko na cafke da "Amin hajiya Inna".

Ina tafe ina 'yan waƙe na, ina tafa hannu, hanyar ɗakin yaya Sadeeq na nufa saboda
yana daga hanyar waje ne. Koda nazo bakin ɗakin ban tsaya yin sallama ba, kuma ban
buga kofar ba, duk da yasha yimin gargaɗi a kan indaina shiga masa ɗaki, ba tare
da nayi sallama ya bani izinin shiga ba, ko kuma na buga masa kofar. Amma tsabar
taurin kai irin nawa sai naki yin ko ɗaya acikin umarnin shi, kawai bankaɗa ƙofar
nai, Ina tura ƙofar na bankaɗa labule nakutsa kaina ciki. Yanayin da naga yaya
Sadeeƙ ne yasa nasaki wata uwar ƙara, har saida kular abincin kaina ya faɗi,
murfin kular ya buɗe dambun ciki ya watse.

A fusace yah Sadeeƙ ya nufo ni, kamar mayunwacin zaki, kamin in ankara ya wanka min
kyawawan maruka, haske nagani wal-wal a idanu na, har saida ji na ya d'auke na
wasu 'yan daƙiku, ba wani abu ne ya firgita ni ba, illah ganin sa da nai babu riga,
kirjin sa ɗauke da yalwataccen gashi baki siɗik dashi, kwance luf-luf bantaɓa ganin
ɗa namiji haka ba tunda nike a rayuwa ta, ja da baya na fara yi, ina rawar baki,
yayin da shi kuma yake nufo ni, haƙiƙa na furgita dashi matuƙa. Saboda haka na fara
ihu iya ƙarfina, yadda Inna zata iya jiyo ni, tazo ta cece ni.

Takaici na ne ya kuma kama shi, cikin zafin nama ya cafko ni, belt ɗin jikin
wandan sa ya zaro, sai alokacin nai yunƙurin guduwa daga ɗakin. Amma ina aikin gama
ya riga ya gama, saboda riƙe yake gam da hannu na, maida ƙofar yai ya rufe harda
samata kye da sakata, kana ya soma duka na, kamar Allah ya aiko shi, kota ina zabga
min belt ɗin yake yi. Ihu nikeyi da duka murya ta, saboda naga so yake ya kashe ni,
tun kamin lokaci na yayi.

Inna dake cikin ɗaki tajiyo ihuna da gudu ta fito tazo bakin ƙofar ɗakin sa, buga
ƙofar tafara, tana kiran suna na da ƙarfin ta, ganin ba kiran sunan nawa ne mafita
ba yasa tafara kiran sunan yah Sadeeƙ, Garba Garba kada ka kashe 'yar mutane na
shiga uku, dan Allah ka yaƙuri ka ƙyaleta haka nan, komai tai maka ai tadaku,
bazata ƙara ba daga yau insha Allah".

Tun ina iya jiyo muryar Inna tana magiya har nadena jiyo ta, nasan tagaji ne saboda
bata jure yawan magana yanzu sai hawan jinin ta ya tashi.

Sadeeq kuwa kunnen uwar shegu yayi kamar bashi Inna kema magiya ba, tuni Inna
hawaye sun fara zarya a kan kuncin ta, saboda tasan yah sadeeƙ, ba ƙaramin aiki ya
ɓallo ba.

Ni kuwa har muryata ta dashe ko sautin ihun nawa ya daina fita, hawaye ne kawai
suke zubar min, kuma har yanzu bai dena duka na ba, saida yaiwa jikina ruɗu-ruɗu,
ya tabbatar da ya min lis, sannan ya tsaya yana haki, kamar wanda yai dambe da
ƙartai, "shiiiiiiii" ya faɗa yana wani irin huci.

Gefe ya koma gami da harɗe hannayen shi guri ɗaya, kana ya saki murmushin muguntar
daya saba.

Ni kuwa duk da dakuwar da nai, baki ba bai mutu ba, saboda cikin raina cewa nike,
"mugu, baƙin azzulumi, burin ka yacika kaci zalina, kuma Allah sai yasaka min" .

Wata doguwar ajiyar zuciya naja kamin na fara sauke numfashi da sauri da sauri".
Cikin isa da taƙama ya ce "idan naƙara jin kinja ajiyar zuciyar nan wallahi saina
sako farkon dukan nan, koma nayi miki mafiyin wanda nai yanzu".

Ya cigaba da cewa "so nake kiyi shiru kamar bakya gurin nan, ke ko numfashin ki kar
naji saukar shi, hakan ne kawai idan kikayi zaki temaki kan ki, ki fita da ƙafun
ki, batare da anzo an ɗauke ki ba".

Nasan halin yah sadeeq sarai, ba ƙaramin mugu bane, saboda haka nayi Kamar yadda
yace kan kace me? numfashina ya fara neman ɗauke wa, ina ta ƙoƙarin dawo dashi ba
tare da yah Sadee'k ya gane ba. ji nike kamar ana so a zare min raina saboda
azabar dukan dana sha, gaba ɗaya jikina raɗaɗi yake, ga kaina da nike jinsa kamar
zai bar gangar jikina ya faɗi kasa.

Lura da yanayin yadda nike ciki ne yasa yaya Sadeeƙ cewa " kaɗan ma nai miki
wallahi, saboda batun yauba nasha faɗa miki ki dena shigo min ɗaki kamar ɗakin
arna, ke bama ɗakina kawai ba, duk inda zaki shiga ki shiga da sallama a matsayin
ki na musulma, Amma dayike kunnen ki na ƙashi ne, ina gama faɗa kike watsar da
maganar anan, to wannan shine na ƙarshe wallahi idan aka ƙara ai koki baki sallama
ba kika shigo zakiga abinda zan miki".

"Shashasha, Tashi kiban guri, na gaji da ganin wannan mummunar fuskar taki, gashi
kin tsura min ido kamar sa'anki ne yake magana".

Tashi tsaye nayi Ina layi ina bin bango har na iso bakin ƙofar na buɗe. Ina fitowa
naci karo da inna dake faman sintiri. Kamar wacce tayi ƙarya. Cikin sauri Inna
takomo ni. zubewa nai a jikin ta babu numfashi, ihu inna tafara tana kiran ya
Sadeeƙ da karfin ta, Garba inalillahi wa'innah ilaihi rajiun, shikenan ka kashe ta.
Garba ka kashe 'yar mutane, ba zaka fito mukaita asibiti ba, ina magana kayi shuru,
yah sadeeƙ yana jin Inna, amma yai banza da ita, kasancewar yasan halin inna da
zuzuta abu, shiyasa ya'ki fitowa.

Can dayaji ihun nata yaƙi karewa sai ya sanya jallabiya me ruwan madara Yafito. A
zaune yaga inna dirshan, ni kuma ina kwance a jikin ta kamar matacciya, yayin da
Inna keta faman jijjiga ni tana sumbatu kamar wacce tafara taɓuwa.

Ko ƙala bai ce mata ba ya wuce mu, cikin gida yashiga ya buɗe fridge yaɗibo ruwa me
sanyi acikin kofi, koda Inna tagan shi da kofi batasan meye aciki ba, ta buɗe baki
zatai mai magana kenan, ya antaya min ruwan duka ajikina cike da mugunta, wata
doguwar ajiyar zuciya na sauke ina ƙan-ƙame jikina ina ƙara shigewa jikin Inna,
kallon sa kawai tayi saboda takaicin sa ba zai bari tayi magana ba.

Amma ganin ina motsi yasa taɗanji sanyi aranta, ta ce "Siddeeƙa sannu". haka dai
taita kiran suna na tana min sannu, amma sai dai na kalle ta da ido kawai, saboda
bazan iya magana ba.

daƙyar na iya ɗaga hannu na, na miƙa mata, saboda banji daɗin kwanciyar da nai ba,
so nike in tashi, Inna ta fahimci nufi na saboda haka ta kama hannun nawa. Tana
fadin "sannu Siddiƙa sannu kinji, Allah zesaka miki".

Sai a lokacin na iya magana cikin wahalal-liyar murya nace "Inna zan mutu inaji
ajiki na karshena yazo".
Nafaɗa ina rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Itama kukan ta saka, tana faɗin "bazaki mutu ba 'yar Inna sai dai shi ya mutu, zaki
tashi Insha Allah".

Hannun Inna na kama na d'ora a 'kirjina na ce "Inna nan ɗi na kusa da zuciya ta
zafi yake min".

"ciwo yake miki?"

"eh Inna, Ji nake yi kamar ba ajiki na yake ba".

yah sadeeq da yake a tsaye tun sanda ya kwara min ruwa na far faɗo yake jin diramar
da muke yi, bakaramar dariya muka bashi ba, amma yasan babu halin yin dariya
yanzu, sai abin yayiwa Inna yawa.

Dabara ce ta faɗo masa, Saboda haka yaje ɗaki ya ɗauko wayar sa yazo yake mana
video,

Acewar sa idan ya shiga ɗaki ya kalla abinsa yayi dariyar sa san ran shi".

Cikin muryan kuka Inna tace, "Garba ashe rashin imanin ka ya kai haka, kayi mata
dukan mutuwa bai isheka ba kazo kana ɗaukar ta hoto. Bakomai kana lokacin ka". Ta
kuma fa shewa da kuka ta ce, "yanzu Garba ba zaka zo kafaɗa min yadda zanyi da ita
ba ko? tunda ka illata ta shike nan burin ka ya cika, to kiramin ubanka awaya
nasan duk inda yake yaji ina neman sa zai zo yanzu da gau-gawa, idan kuma baya
garin zai turomin Wanda zai share min hawaye".

Ɗan ta'be baki yai, Sannan ya matso inda nike, ya tsugunna hannun sa ya ɗora a kan
wuya na, yaji da zafi sosai

Ya cewa Inna "ki ɗauko mata hijabi in kaita asibiti naji jikin da ɗan zafi".

"Au ɗan zafi ne ko? Garba Allah zai saka mata mugu, kaje ɗakin ta ka ɗauko mata
kowani iri ne".

Ya ce "Inna bafa dake zani asbitin ba a gida zan barki".

Inna na salati tana tafa hannayen ta ta ce, "Garba me kace? Kana nufin na ɗauki yar
mutane na baka katafi da ita kai kaɗai kaje kai mata wani abun, nasan saboda tsabar
baƙin halin ka ko gawar ta ma ba zamu gani ba, to ban yarda ka tafi da ga kai sai
ita ba, kafata kafar ka maza shiga ciki ka taho min nima da mayafi na".

Kallon mamaki sadeeq yabi Inna dashi sannan ya taɓe baki ya ce, "bari na fara
fidda motar waje sai nazo na ɗauko muku". Inna ta ce "da dai yafi maka, saboda
bazan bari kaje ka kuma cin zalin ta ba, Nima se Allah ya tambayeni".
Fita daga gidan yaya sadeeq yayi.

Ina kuka nace, "inna wallahi bana son zuwa asbitin nan".

Ta ce "ya zakiyi Siddiƙa, daurewa zakiyi dama ba a zuwa asbiti sai idan ba ada
lafiya, duk ni naja miki da daki ka ce ba zaki ba na rabu dake ai da haka bata faru
ba".

Yah sadeeq ne ya dawo yatarar da Inna tana shere ƙwalla, bai ce mana komai ba ya
wuce cikin gida sai gashi ya dawo da hajabi na, da maya fin Inna.

Yana zuwa ya miƙowa Inna yace "dan Allah ni kuna ɓata min lokaci ina da abin yi
kisa ka"

Amsa Inna tai bata kula shiba saboda ya gama kaita bango, sai da tayafa mayafin ta
sannan tafara ƙoƙarin ɗagani amma ta kasa, saboda shekaru sunja kuma tun ina
jaririya a cikin tsumma na take ɗawainiya dani, saboda haka tace ma yaya sadeeƙ,
Taimaka ka ɗaga min ita nasa mata hijabin.

Yi yai kamar bai ji abinda ta faɗa ba. Komai ya tuna oho. Sai gashi yazo ya ɗaga
ni, kana ta saka min hajabin.

yasan Inna baza ta iya ɗauka ta ba, saboda haka ya fara jan hannu na, yana cewa
mu je ko, saurin daka mai tsawa tai ta ce "wai Garba lafiyan ƙalau kuwa?"

Bai ce mata komi ba yasaɓa ni a kan kafaɗar sa, saboda yayi min mugun ta yazuro
kaina ƙasa sosai, jini na sai dawo min kai yake yi, a haka muka isa bakin motar, a
gidan baya ya aje ni, sannan ya shiga gurin zaman direba. Inna ma baya tashigo
tana mita. domin Allah ya mata mita, koda yiki yawancin tsofaffi sunada wannan
mitar, kai na nadora kan cinyarta ina matso kwalla bawani babban asbiti ya kaini ba
illah asbitin dake cikin ƙauyen mu asbitin shi kaɗai ne asbiti, kuma babu wasu
kwararrun ma aikata acikin sa.



Comment
Shear
Vote

Sbeauty ce✍️
NI DA YAYA SADEEQ


Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya (S beauty ✍️)

EWF✍️
__________________________________

*Page 03*

‫بسم الله الرحمن الرحيم‬


Asbitin gabaɗayan sa a lalace yake, saboda ginin jar ƙasa ne, wani ɓangaren ma duk
ya rushe, ɗakunan da ake kwantar da marasa lafiya guda 4 ne kawai, Sai office 1 da
ma'aikatan asbitin suke zama a ciki, gabaki ɗaya asbitin gado biyu ne.

A bakin asbitin yayi faking, Asbitin bashida kofar shiga ko ta ina shiga a ke
saboda ba a kewaye yake ba, ya ɗauki kusan seconds goma a cikin motar, kamin ya
kashe ya fito,
sai da ya fara buɗewa Inna ta fito, kana ya buɗe bangaren da nike yaɗan zuro jikin
sa ciki ya miƙo hannu ya janyo ni, Inna faɗi take "kabita a hankali ba cikakkiyar
lafiya gare ta ba".
Ɗauka ta yayi irin ɗaukar da a kewa jarirai, kana ya nufi asbitin,
Inna biye da mu a baya.

Da yike yah sadeeq sananne ne a gari bama iyaka kauyen mu kaɗai ba harda birni,
saboda babban ɗan sanda ne.

Wata nurse ce ta hangomu da sauri ta ƙaraso inda muke, cikin rawar jiki tace
"yallaɓai cikin wancen ɗakin zaka kaita zatafi hutawa, babu mutane da yawa a cikin
sa". Tafaɗa haka tana nuna mai ɗakin da yatsan ta manuniya, "alright" shine abin da
kawai ya faɗa.

Ɗakin da a kace ya kai ni shine ɗakin da ake ji dashi a cikin asbitin, saboda a
kwai siminti da gado guda ɗaya tak, mun tarar da mara lafiya a kan gadon kwance,
saboda ya ɗora ni aka sauke mara lafiyar gunin ban tausayi, gashi masu jinyar ta
basa kusa.

"yallaɓai ɗora ta a kai". A cewar nurse ɗin data sa aka sauke mara lafiyar.

Be yi mamaki ba, saboda ya saba kawo ni asbitin, kuma irin haka ne take faruwa.

Ɗora ni yayi akan godon, kana ya fice abin sa.

Da sauri Nurse ɗin tabi bayan shi tare da wa'inda suka cicciɓi marar lafiyar da aka
sauke a kan gado.

Bai jima ba saiga shi ya dawo tare da wata nurse, hannun ta rike da wani ɗan
karamin farantin silba, sai kyalli yake, kan wani teburi na katako ta ijiye, sannan
ta matso kusa dani, ta ɗora hannun ta a kan wuya na, "a kwai zafi a jikin ta
yallaɓai, zazzaɓi ne ya kamata". Nurse tafaɗa tana duban shi, kin tanka mata yai,
dan kuwa kunnan uwar shegu yai mata.

"Meke damun ki?". Nurse ta tambaye ni,

"Duka jiki na ciwo yake min, amma kirji na yafimin ciwo".

Fuska ta ta kalla da kyau sai taga shatun hannu tace "kamar dukan ki akayi ko,
domin shaidar hannu ya bayyana a kan kuncin ki raɗa-raɗa".

Na buɗe baki zanyi magana kenan yah sadeeq ya wurga min harara.

Kallon nurse ɗin yai ya ce "ke maye aikin ki?".

"Duba mara lafiya". Ta faɗa bakin ta na rawa.

saida ya ɗaure fuskar sa babu alamun wasa a tat-tare da shi yace "to kiyi aikin ki,
dan wannan bai shafeki ba, kiyi abinda ya dace".

Cikin in-ina ta ce "to ranka shidaɗe na tambaya ne saboda nasan irin maganin daya
dace na bata, amma kaya ƙuri naga kamar ranka ya ɓaci".
Be kuma bi ta kanta ba yafi ce daka ɗakin, tasha fama dani sosai kamin na bari
tasoka min allurar da za ai ƙarin ruwa, shima saboda naga yah sadeeq ya dawo ɗakin
ne.

Banfi minti 25 da samin ruwan ba, baccin wahala ya ɗauke ni, koda na farka bayan
wasu awanni da bazu wuce 2 ba, sai naga momy zaune a kan wata farar kujera, irin
tarobar nan, da alama daka gida aka zo da kujerar ma, mamakin ganin ta ne ya
kamani, miƙewa nai zaune na jingina filo a baya na, kallon ta nikeyi ina muts-
tsuka idanu, ban gama mamaki ba saida naga Khadija, tashigo ɗakin hannun ta ɗauke
da kular abinci, da kwano, Umar, na biye da ita a baya.

tashi Momi tayi tamatso da kujerar ta kusa da gado na ta zauna, tana kama hannu na
"sannu kinji Allah zai saka miki ya jikin naki?". Momy ta tambayeni muryan ta ɗauke
da damuwa.

Madadin na bata amsa sai na jefa mata tambaya "wai momy yaushe kuka zo? kuma waya
faɗa muku bani da lafiya? Inna dai bata da waya yah sadeeq kuwa nasan ko mutuwa
nayi bazai kira ku ya faɗa ba".

Ta ce "Babu wanda ya faɗa mana, daka kaduna muke hutun makarantar su Khadija ne ya
ƙare, shine zamu koma Abuja, nace mu biyo tanan, can gida muka fara zuwa bamu sami
kowa a ciki ba, kun bar ko ina abuɗe, hakan ne yasa naji a jiki na ba lafiya ba,
shine nakira yayan ku awaya.
Shine ya shaidamin bakida lafiya ne ya kawo ki asibiti. To a take na tambayi sunan
asbitin, nan fa ya ce "asbitin Dande".

daga haka muka yi sallama na kashe wayar.

Sanda mukazo hajiya Inna ke bani labarin

Please Login or Register in order to submit comment