You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kashe.

Sadeeq ya ci gaba da cewa "ai ni yanzu na shiga uku, Daddy ya gama jamin abun kunya
a gari, ni ba mai laifi ba da sai na ringa yawo da abun fuskar da zan sauya kama".

Farooq dariya harda riƙe ciki yace "wallahi aiki ya ganka yanzu za ka fara nidai
ɗan kallo ne, saboda ko na baka shawara ba lallai ne kayi amfani da ita ba amma
bari na gwada baka".

Sadeeq yace "wallahi Farooq na tsani yarinyar ne ji nike da ma na mutu na huta da
dai nayi rayuwa da ita amatsayin mata ta".

"Kana ruwa aboki na, to kai wai me yarinyar nan tayi maka ne haka da ka tsane ta".

"haba Farooq wai har kana buƙatar ƙarin bayani, bayan komai a bayyane yake, kasan
nafi san na auri wayay-yiyar mace, mai aji da yanga wacce ta gama digiri dinta, in
so samu ne ma ace ta fara aiki, koda kuwa wani iri ne sannan kuma kada shekarun ta
suyi 'kasa da 25 to ko bata da masifar kyau in dai tana da wa'innan abu buwan da na
lissafa maka zan aure ta".

Zai ci gaba da magana Farooq ya dakatar dashi ta hanyar faɗin dakata malam "ai na
ɗauka kabar wannan banzan tunanin da kasa a ranka zaka ro'ki Allah ne yayi maka
za'bi mafi alkairi, ashe ba haka bane, to ina so kasan har yanzu Siddi'ka yarinya
ce ba a haka zata ci gaba da rayuwa ba, ko kana da yaƙinin cewa baza ta canza ba?
Ya faɗa yana kallan Sadeeq d'in".

"Eh Farooq". Sadeeq yace yana ɗaga murya "bazata canza ba a haka zata gama rayuwar
ta🤔 saboda irin zuciyar uban ta gare ta, kuma bugu da ƙari rashin jin maganar ta
yayi yawa, kaf ƙauyen Dande babu wan da bai san ta ba, ko ina idan na wuce ana
nunani, saboda an san ni yayan ta ne, nasan ma dan suna jin tsoro na ne da tare ni
zasu dunga yi, nafisan yarinya natsats-tsiya mai kunya, kaga ita kuma duk bata da
su".

"Hhhmmmm Sadeeq nidai shawara ta anan ita ce kabi komai a hankali kada kayi gag-
gawa, amma ni banga laifin Siddy ba rashin jin magana da kace yarinta ce take damun
ta, wataran idan akace tayi zata ce ba tayi ba, sharri ake mata".
"Sa'ar Jiddah ce fa mai yisa Jiddah bata yin duk wa'innan abu bu wan da Siddi'ka
keyi?".

"To ai Sadeeq kasan yara kowa da kalan ƙuruciyar sa, idan ka bibiya a kwai abinda
ita Jiddahn ta keyi Siddi'ka kuma koda kuɗi akace tayi ba zata yi ba, kuma idan ka
lura Siddi'ka goyan kaka ce duk abinda tayi sai ace daidai tayi ba a nuna mata tayi
kuskure, amma da ina tabbatar maka da sai tafi Jiddah hankali".

Taɓe baki sadeeq yayi yace "wallahi ina raga mata ne saboda gwaggo Amina, amma
yanzu tunda ta shigo gona ta zan koya mata darasi😢 zan nuna mata tayi babban
kuskure, da Daddy yace zai aura mata ni, da tace mai A a bata so na ".

Kafaɗar sa Farooq ya daka sannan yace "Allah ya bama mai rabo sa'a". Ya fice a
ɗakin

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

*GARIN ABUJA*

Koda na buɗe ɗakin na same shi atsaftace, kamar yadda nayi zato saboda duk zuwa
haka nike samun shi.

Da sallama ɗauke abaki na, na shiga sannan na maida ƙofa ta na rufe, kan gyararran
gadon na faɗa ina maida numfashi, wash nagaji matuƙa, daga haka baccin gajiya yai
gaba da ni ba tare da nayi sallar la'asar ba, daman sai da muka yi azahar agida
muka taho.

A cikin baccin ne nayi wani mummunan mafarki wanda ban taba yin irin sa ba tun da
nike arayuwa ta, ban fahimci me mafarkin ya ƙunsa ba tsabar ruɗanin dake cikin sa,
A firgice na farka amma nakasa yin salati saboda ban saba ba, ina ta zaro ido na
alamar tsoro nakasa firta koda kalma ɗaya ina son in tuno abinda nagani acikin
mafarkin, amma na kasa, sai wani masifaffan ciwon kai daya saukar min a lokaci
daya, sosai tsoro ya shigar min har banason nayi motsi saboda sai naga kamar za a
kama ni, bugun zuciya ta ya tsananta, yana bugawa da sauri da sauri sakamakon buga
ƙofa ta da naji anayi.

Kara duƙun-ƙune kaina nayi a cikin bargo, daka waje naji ana fadin "Ummi ce ki
buɗe".

Jin muryan Ummi da nayi yasa nayi han zarin saukowa daka kan gadon, jiki na ɓari
na buɗe ƙofar ta shigo, rungume ni tayi tana ihu Bata lura da yanayin da nike ciki
ba, turanci ta fara su burbuɗa min bayan tasan bawani ji nike ba, amma tsabar
iyayin Ummi takeyim shi, Jin ban rungume ta ba kamar yadda muka saba yasa tasake
ni, tana kallo na.

tace "sisi kamar bakya hayyacin ki, meke damun ki".

"Bacci na tashi". Haka na tsinci baki na da furtawa, bansan meyisa na ɓoye ainihin
abinda yasa yanayi na ya sauya ba.

"Haba koda naji". ta faɗa tana kama hannu na, muka fito daga ɗakin, ɗakin ta muka
shiga wanda ya kasan ce a tsaki yar nawa da na Khadija.

"Amma yakamata kiyi wanka sisi kicanza kayan jikin ki, kin ma yi kokari da kika yi
bacci dasu a jikin ki ni yaushe zan iya".

"Ai ke ki ka ce Ummi, ni kin san na saba ko a ƙauye kayan da nasa dasu nike yin
bacci, duk sabun tar su bana sauyawa izuwa na bacci, duk da ina dasu".
Wata uwar ƙara ta saki a razane na kalle ta "lafiyan ki ƙalau kuwa Ummi?".

"lafiya ta lau sis naji kin anbaci kauye ne kinsan ni da 'kauye amana, don Allah yi
ki fito wanka kizo ki bani labarin Dande".

Ban kuma cewa da ita komai ba, na nufi bayin wankan ta masha Allah shine abinda na
faɗa bayan na buɗe bayin naga ko mai na cikin bayin fari ne ƙal kamar a zuba abinci
a kasan a lashe, saboda yadda kasan tayil din ke sheƙi ga wani sihirtaccen ƙam shi
da yake tashi.

A hankali na ɗaga ƙafata na shiga bayin duk da banyi addu'a ba amma na shiga da
ƙafar hagu, cikin kwamin wankan na shiga na kunna famfon ruwan zafi da na sanyi na
daɗe a cikin ruwan ɗumin sannan na fara wanka ina gamawa na ɗaura tawul, kana nai
alwala na fito.

Ina fitowa ana kiran sallar magriba.

A gefen gado nasamu Ummi zaune tana buga game a laptop.

Saida ta dube ni tace "gaskiya sis kin daɗe sai kace kina canza fata gashi kuma
kina nan yadda kike".

Ban kula ta ba na nufi durowar kayan ta saboda suna yimin dai dai, bayan na buɗe na
ga wata doguwar rigar yadi mai laushi me run madara fitet ce ba tada wani kwalliya
amma duk da haka ɗin tana da kyau,
ban wani damu da saka bra ba nafi sa haf bes, sif ɗin haf bes na buɗe na ciro,
sannan na bude na fant na ɗauko sabo, wanda na gansa da 'yar takar darnan a jiki
alamun ba a sa ba, da yake duk nasan inda suke harda na siket din ciki haka na
fiddo duk abinda nikeda buƙata.

Sannan na nufi gaban madubi na zauna kan kujerar dressing mirror, na fara shafa mai
ina gamawa na ɗauki turarukan ta masu ƙamshi da tsada na fesa a jiki da kaya na,
duk kuwa da wasu ba akaya ake fesawa ba amma saboda ni ban sani ba haka nai ta
fesawa, saboda a lokacin Ummi ta shiga bayi, doguwar rigar na saka na dakko dadduma
don rama sallahr da ake bina sannan inyi wacce muke cikin lokacin ta

Ina cikin yin sallar Ummi ta fito daman dad dumar na kar kata ta yadda mutane biyu
zasu iyayin salla akai

Ko da na idar ban wani tsaya yin addu a ba na cire hijabin.

ƙasa na sauko, anan na tarar da duka 'yan gidan, kowa yana nan harda Aunty Bilkisu
da yaranta guda biyu Samahir da da Maheer, Khadija da Umar ga Momy sai Jiddah da ke
ta faman danna waya ko me take danna wa? oho, ahankali na ƙarasa saukowa daka kan
benan, gurin Momy naje na rungume ta nace "Momy ya gajiyar hanya". Ina mai hawa kan
cinyar ta na zauna.

Tace "Siddi'ka rigima ni ban san yaushe zaki girma ba, saboda wani abun idan kika
yi ko Umar auta ba zaiyi ba".

Momy nidai naji saboda bazan taɓa girma da hawa cinya ba".

"Sarkin san jiki" Aunty Bilkisu ce tafadi hakan

"La Aunty Balki bari inzo mu gaisa".

"Wai bana hana ki cemin Balki ba? Ni suna na bil'kees". Ta faɗa tana gyara sunan,
mu kwa muka kwashe mata da dariya.
Dai dai nan Ummi ta sauko muka dasa firan da ita Samaheer ce kan cinya ta ina yi
mata wasa tana ƙyal-ƙyala daria

Suwaiba mai aikin gidan ce ta shigo tace "Hajiya na kammala yana kan dinning".

"To" Momy tace sannan ta kallo mu.

"Oya kutashi muje muci abinci dan nasan kowa anan yana jin yunwa".

Kamar jira muke duk muka miƙe, muka nufi dinning kowa ya zauna muna ci muna ɗan
taɓa fira, taliya ce sai faten dankin turawa da yaji hanta sai farfesun naman kaza
mai yaji, babu laifi Suwaiba ta iya girki dan idan Daddy baya nan ita take yin duk
wani abu da za aci ko a sha, saɓanin idan yana gida Momy ke girkawa tace su khadija
su

bayan mun gama cin abinci muka dawo falo muka 'kara dasa sabuwar fira har aka kira
sallar isha'i duk da Jiddih tunda na sauko magana bai had'ani da ita ba saboda ita
ta nada jin kai ga san nuna ita wata ce ni kuwa ba zan d'auki iskanci ba dama ba
shiri nike da ita ba saboda abu kad'an ke had'a mu mu fara dambe kowa bai san raini


NI DA YAYA SADEEQ


‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Page 11

Bayan mun idar da Sallar isha'i wata firar muka cigaba da yi, idan Khadija tayi
nata nima sai nayi nawa hakama Umar, yayin da Jiddah ke faman cika tana batsewa
tana jan dogon tsaki, ko ita da wa oho.

yanzu haka Umar ne ke bamu labarin wani Almajiri daya shiga bara gidan wata amarya,
sai mijin yace "almajiri kawo kwanon ka". Sai amarya ta leko ta amsa, ta zuba masa
abincin, Koda ta miko mai kwano sai ya amsa yatafi zauran gidan yana kuka, sai
mijin amaryar yabiyo almajirin, ya tambayesa meye dalilin kukan nasa "ko abincin ne
ba zai isheshi ba?". Sai almajiri ya girgiza kai, sai mijin amaryar yace "to meye
kake ma kuka?". Budar bakin Almajiri sai cewa yayi "shi ba komai ya sashi wannan
kukan ba illah yana tsoran agama aure kyawawan mata kafin lokacin su yai.

" Idan ke/kaine ya zaki/ka yi", haka ya jefe musu tambaya aikuwa nan sukaita tafka
muhawara suna shirme

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Sadeeq kwance a kan gado, wayar shi a hannu yana cikin Instagram, sai kallon hotuna
yake, kwatsam idanuwan sa suka sauka akan hotan wata yar budurwa, acikin zuciyar sa
yace "daga ganin ta tanada aji kuma ba zaka ce mata 'karamar yarinya ba domin zata
iya kaiwa 25 years old da haihuwa". Kara shiga account dinta yayi nan take hotunan
ta da take dorawa suka bayyana sosoi Sadeeq ke kallon hotunan, sunan account din ta
ya kalla yaga anyi rubuta kamar haka *Zuby officially*

"Wow" ya fada afili Suna mai dadi *Zuby* haka yaita maimaitawa bata da wani kyau a
fuska, kuma ba wani haske gareta ba, amma dagani ta 'kara da na kanti, 'kirjin ta
cike yake da dukiyar Fulani tana da dirin jiki.

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

*ABUJA*
Ba muyi wata dinner ba, kasancewar bamu dade da cin abincin ba, shayi Momy tasa
Suwaiba ta hado mana yaji ni'inal da kayan kamshi, mukai ta kurba kamar wasu
larabaw😂
Bayan mun gama kowa ya watse, amma nikam sarkin tsoro d'akin Ummi nayi tana
'ko'karin rufe kofar nai saurin turawa
Da mamaki tace min "sisi yadai". "Anan zan kwana" na fad'a yayin da nike shigowa
ciki, ta maida kofar ta rufe

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Ahaka rayuwa ta cigaba a gidan Momy, tsakanina kuwa da Jiddah babu jituwa, zan iya
cewa tun nazo gidan magana bai shiga tsakanin mu ba, kuma babu Wanda ya lura a
gidan saboda tun asali kowa yasan bama wani shiri, yau kimanin kwana bakwai kenan
da aurena da Sadeeq amma har yau ban sashi a cikin ido naba gashi su Khadija har
sun koma makaranta.

Muna falo ni da Momy a zaune, sai Suwaiba dake faman zirga zirga ta kai ta komo
tana kokarin hada abincin rana, kafin su Khadija su dawo, "dauko min waya ta a
bedroom dina" cikin sauri na mike domin Momy batasan simi simi, bayan na dawo nace
"Momy gashi nasamu wayan ma tana ringing". "Kawo mugani waye ya kira" ta amsa tana
shafa screen d'in wayar sannan ta kara a kunne
"Wa'alaikumussalam". shi ne abinda naji Momy tace kafin tace "lafiya lau". Ta kara
da cewa "wallahi Sadeeq zan cimaka mutunci fiye da yadda kake zato, kasan dai yanzu
ba kamar da bane kana da nauyi a kanka, amma kayi burus da mu dama gwada ka nayi
naga hankalin ka, to maza maza kazo gobe inason magana da kai na fada maka idan
kuwa ba haka ba zanyi mummunan saba maka".

Cikin fushi Momy tace "bazan saurare ka ba Sadeeq, baka da abinda zaka fada min na
yarda, kaima kasani domin bakada wani uzuri kayi abinda nace maka kawai".

Tana gama fadar haka ta kashe wayar.

Jim kad'an saiga wani kiran ya sake shigowa daga yadda naga Momy ta daga wayar na
gane yaya Mubarak ne, d'an yayan ta, na sanshi sosai ya nada mutunci da yana nan ne
da zama, amma yanzu yatafi India saboda ya karasa karatun sa a can, kallo na tayi
kana tace
"bani ruwa mara sanyi nasha". "To" nace na mike cikin natsuwa koda na dawo har ta
kammala wayan.

𝐘𝐚𝐮 𝐬𝐡𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐢𝐲𝐢 𝐭𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐛𝐚 𝐤𝐮𝐲𝐢 𝐡𝐚𝐤𝐮𝐫𝐢 𝐝𝐚𝐬𝐡𝐢 𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐡𝐚𝐫 𝐧𝐚𝐠𝐚 𝐫𝐮𝐰𝐚𝐧
𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧 𝐳𝐚𝐧 𝐲𝐢 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐚𝐧𝐣𝐢𝐦𝐚 𝐢𝐧𝐬𝐡𝐚 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡

Love you 💖💋💖💋💖


NI DA YAYA SADEEQ


‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Page 12

Washe gari da misalin 'karfe 11am na rana, a lokacin Su Khadija suna makaranta,
Momy ma ta fita ma'kota gidan wata 'kawarta Hajiya Nafisa, amma tace ba dadewa
zatai ba, zaune nike ni kad'ai a falo kan kujera ina kallon TV, bakin sa d'auke da
sallama ya shigo, koda yaga ni ce zaune a falon sai ya gimtse bai 'karasa sallamar
ba, gami dap d'aure fuska kamar bai ta'ba dariya ba, ni ma nayi kamar ban ganshi
ba, tsawa ya daka min "dan ubanki baki iya gaisuwa bane ko nan d'in gidan uban ki
ne? Ko da yike shima ubanki' tarbiyar bata ishe sa ba bare kuma kema ya baki".
Inajin zafin gorin da Sadeeq yake mini har cikin raina a lokuta da dama

ya cigaba da cewa "idan ba mummunar 'kaddara ba mai zanyi dake kucaka ki kalle ki,
ki kalle ni, kin tafka babban kuskure da kika yarda Daddy ya hada auren nan, zan
shayar dake madarar azaba, gida na zai zame miki tamkar kabari, ke koda sunana ki
kaji an ambata sai gaban ki yayi mummunan fad'uwa ,saboda bakin rijiya ba gurin
wasan makaho bane, ki fara tunanin yadda zaki rubuta littafi mai suna *NIDA YAYA
SADEEQ* saboda irin zaman da zakiyi a cikin gida na ya ciki ki rubuta".

Duka wannan maganar da Sadeeq yayi kaina a 'katsa wasu hawaye masu zafi suna
gangaro mini, narasa mai nayiwa Sadeeq da har ya tsane ni haka? Ban ta'ba tunanin
tsanar da ya kecewa yayi mini ta kai har haka ba, ban tanka masa ba illa mi'kewa da
nayi na nufi hanyar sama na fara taka steps kenan ya da katar dani ta hanyar fadin
"na tsane ki Siddi'ka na tsane ki, kuma bazan taba sonki ba a duk sanda ki kaji
nace ina sonki to kada ki ta'ba yadda dani saboda yaudarar ki zanyi ba gaskiya
bane". 😭

Hawaye masu 'kuna suka cigaba da gangaro min a haka na 'karasa haura steps din,
Suwaiba da ke faman dafa abinci a kitchen taji duk abinda ya faru tsakani na da
Sadeeq

'Dakina na shiga na fad'a kan gado, hawaye mai zafi yana zuba daga ido na, ni da
kaina ina jin tausayin kaina saboda a sani na da yaya Sadeeq bai ta'ba cewa zaiyi
baiyi ba duk abinda yace zaiyi to sai ya aikata sa

A cikin kukan na d'aga hannaye na sama na ce "ya Allah ka bayyana mahaifiya ta a
duk inda take, a fadin duniyar nan, ya Allah kasa tana a raye saboda inason rayuwa
tare da ita, ya Allah kada kabama wani bawan ka sa'ar cutar da ita".
Mama. Na fad'a haka yayin da na d'aga kaina sama ina kalla, "bansan maye dalilin ki
na cewa ko bayan babu ranki a daura wa 'yarki aure da Sadeeq ba, nayi alkawarin ni
Siddi'ka zan zauna da Sadeeq koda kuwa hakan na nufin zai zama ajali na, ha'k'kin
ki ne nayi miki biyayya a sanda kike a raye da kuma abinda kika bani umarnin sa
koda bayan ranki, Mama ta ina sonki". Na 'kare maganar da wani irin kuka mai tsuma
zuciya.

Allah sarki Siddi'ka ni kaina ta bani tausayi ban san sanda na saki waya ta tafad'i
a kasa ba saboda ido na ya cika da hawayen 😭 tausayin halin da take ciki da 'kyar
na samu na daidai ta kaina na d'auki waya ta na fita daga d'akin naja kofar na rufe

Momy ce zaune ita da Sadeeq a falon 'kasa, sai zazzaga masifa takeyi "Sadeeq kabi
duniya a hankali ko ta d'aga ka zata aje ka, Wallahi Sadeeq ina guje maka ranar da
zakayi ladama amma kuma ladamar zata kasan ce da ita gwamma babu saboda ka makaro,
ka kasa d'aukar kaddarar ka a yadda tazo maka".

Shi dai Sadeeq jin Momy kawai ya keyi amma baiga wata ranar ladamar da zata zo mai
ba, kuma ma ladamar ba akan kowa ba sai akan Siddi'ka, yaji takaicin kalaman Momy,
saboda har cikin ransa ya ke jin kiyayyar Siddi'ka.

tace "dama akan maganar makarantar Siddi'ka ne yasa nace kazo, tunda kai ba kayi
hankalin haka ba, kasan dai an koma hutu, so nike ka kaita makarantar su Khadija
saboda akwai koyarwa sosai kuma kaga tana da saurin d'aukar abu bazata sha wuya
ba".

Yana sosa 'keyarsa yace "Momy gaskiya ni boarding school zan kaita acan katsina
nama gama komai yanzu haka ranar lahadi zan kaita".

Momy bataji dad'in abinda Sadeeq ya aikata ba tare da ya nemi shawar ta kona Daddy
ba, saboda haka tayi mai fad'a sosai kuma tace "bata yadda ya kai Siddi'ka boarding
ba".

da yake Sadeeq ya iya dad'in baki kamar d'an siyasa yasan kalaman da zai fad'a ayi
saurin yadda dashi, nan take ya siye Momy da da'd'ad'an kalamai har ta amince masa.

A zahiri Sadeeq 'karya ya keyi, ba wata register da yai mata, yana dai da burin yin
hakan, saboda bai son ya kaita jeka kadawo, yasan su Momy zasu takura masa ne, amma
boarding sai idan anyi hutu tazo, ko babu komai zai samu sau'kin abun,
Bugu da kari yana san ya shigo da batun auren sa da Zuby nan bada jimawa ba, saboda
a halin yanzu soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin su sun aminta da junan su har
sunyi alkawarin aure duk da basu taba ganin juba ba, yau Sadeeq zaije ganin ta
saboda itama anan garin Abujan take, kusan karfin zuwan nasa ita ce, domin yana
matukar 'kaunar Zuby kuma yana da muradin ganin ta.

Momy ce ta katse shurun da cewa "kuma aji nawa za a sata?".
"Momy ya danganta da yadda suka gwada ta kinsan yarinyar kwata kwata ba tada
'kwa'kwalwa, yanda kika san dusa haka kanta yake, Allah dai yasa ko JS1 ne su
d'auke ta".

"Js1 fa kace Sadeeq! Ina laifin 2 idan 3 bai samu ba, to ban lamun ce ba ban yarda
ba kayi duk yadda za kayi,ta gama primary School fa, kai kan ka shaida ne akan
makaranta da ta gama, kuma kada na 'kara jin kace bata da 'kwa'kwalwa zan sa'ba
maka".

"Uhm" dai Sadeeq yace

Daga haka ya mi'ke "Momy ni zan fita a kwai wani aiki da zanyi zuwa anjima zan dawo
zan kwana biyu anan kafin na koma ".

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾


𝑫𝒂 𝒃𝒂𝒛𝒂𝒓 𝒌𝒖 𝒏𝒊𝒌𝒆 𝒓𝒂𝒘𝒂 𝒎𝒐𝒔𝒐𝒚𝒂 𝒏𝒂 𝒊 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒚𝒐𝒖 𝒂𝒍𝒍
💋💋💋💋💋💋💋

💋💋💋💋💋💋💋


NI DA YAYA SADEEQ

Page 13


˙·٠•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬٠·˙

Ya Allah ina rokonka da dukkan kyawawan sunayen ka ka kiyaye duk wani musulmi daka
shiga mawuyacin hali kabamu lfy me amfani kasanya mana haquri da juria ya Allah ka
kwantar mana da hankulanmu ya Allah kada kabamu ikon butulcemaka koda ka
jarabcemu 🙏

Page b13

A gaggauce yayi faking motar sa ya fito, ya shiga cikin gidan yayi sa'a babu kowa a
falon sai TV da aka bar sa a kunne yana 'kira'ar alQur'ani mai girma, darect sama
ya haura bai zarce ko ina ba sai d'akin sa, yana shiga ya aje wayoyinsa ya cire a
gogan hannun sa, sannan ya fad'a bayi bai wani d'auki lakaci ba ya fito d'aure da
towel a 'kugun sa da wani a hannun sa yana tsane ruwan kansa sa, gaban madubi ya
zauna mayuka ne kala kala da turaruka masu 'kamshi da tsada ya shafa wannan ya
mutstsuka wancen, saida yabi yagama shafa ko wanne, sannan ya fesa body spray mai
sanyin 'kamshi. wata dakakkiyar shadda fara ya d'auko wanda aka 'kawata ta da ado
da dinkin zamani, hular zanna bukar ya ciro ya a je a gefe, sannan ya d'auko agogon
hannu da safa da ba'kin takalmi mai sheki, a tsanake ya shirya abin sa tsaf sannan
ya d'auki wayo yin shi ya fito. Da sauri sauri yake sauka akan step d'in tun kan ya
'karasa saukar yake jin hayaniyar su Momy bai so haka ba, saboda yanzu saita tsare
shi da tambayar ina zashi "Momy". Sadeeq ya fad'a alokacin da ya 'kara so cikin
falon, gabad'aya yaran jinin jikin su suka sha, saboda basu san ya zo ba Siddi'ka
kuwa batayi mamakin ganin sa ba, bakin ko waccen su na rawa suka fara gaidasa ya
amsa fuska ba yabo ba fallasa "yau she kadawo gidan sadeeq? Kuma ina zaka haka kaci
wannan kwalliyar sai kace sabon ango". Yana sosa 'keya yace "wallahi Momy ban jima
da shigowa ba bikin wani aboki na zani anyi daurin auren jiya yau ake dinner shine
nike ta sauri kada nayi latti".
"A dawo lafiya".

Tun a hanyar sa ya kira gimbiyar, ya shaida mata yana hanya, 'kara kwatanta mishi
unguwar tayi, da misalin 'karfe 8:17 ya isa cikin unguwar, daganin ta ma'aika ne a
cikin ta saboda gidajen kusan duk iri d'aya ne kamar quarters haka unguwar take

Bayan yayi faking a gefen wani gida, ya d'auko wayar sa da ke ajiye a gefen sa
yad'an shafa screen d'in sai ga number tafito da suna Baby a jiki call ya danna sai
da ta fara ringing sannan ya kara a kunne

Ringing biyu ta d'auka ajiyar zuciya ya sauke yace "Baby na" daga can 'bangaren
cikin shagwaba tace "my kazo ne?".

Cewa yayi "akasi aka samu Baby, bayan na gama waya dake sai ga kira da ga office
din mu wai ana son gani na, to babu yadda na iya kin san aikin gwaumnati, shine na
juya a kalar tafiyar hanzu haka ina hanya ban isa ba ha'kuri na kira na baki".

Zuby da ta gama shiryawa zuwan, Sadeeq d'in kawai take jira, batasan sanda kwalla
ta fara zubo mata ba, cikin shagwa'ba take fad'in "amma my kasan dai bazan ji dad'i
ba wallahi har Abbah na sanar masa kuma yana gida inason ka gaisa da shi ga Momy da
tun sanda ka shaida min zaka zo na fad'a mata tasa aka shirya maka abin ci yanzu
mai kake so na ce musu?". ta kara sa maganar tana fashe wa da kukun shagwa'ba

Tun Sadeeq yana dariya ciki ciki har saida ta fito fili saboda yadda Zuby ke
shagwaba gunin ban dariya ga kuma kasala da yarasa ta maye ta saukar masa duk a
lokaci daya

"Haba my wai dariya naba ka?". Niyar fashewa da wani kukan take yi, yayi saurin
cewa "gani a 'kofar gidan ku kisa mai gadi ya bud'emin get ko ba shine mai ba'kin
get ba?".
Shuru tayi saboda bata yadda da abinda yace ba
Jin shurun yayi yawa Sadeeq yace "ko in koma ne?".
"Wai da gaske My kana 'kofar gidan mu?".
"Na ta'ba yi miki 'karya ne?".

"A a". Ta bashi amsa

"to kisa abud'e min get".

Ihu ta saka 'kamar 'karamar yarinya ta cilla wayar kan gado

SADEEQ da kallo yabi screen din wayar yana mamakin Zuby d'in wani lokaci idan tayi
abu saita koma kamar Baby amma duk da haka tana matu'kar burge sa saboda son ta a
kullum 'kara dad'uwa yake yi acikin zuciyar sa, a yanzu haka yanajin idan ba ita
bazai iya rayuwa da wata 'ya mace a matsayin matar sa ba.

Mai gadi ne ya wangale get d'in Sadeeq ya sulala da motar sa ciki, kana ya nemi
guri yayi faking
Bai fito daka cikin motar ba wayar sa ta hau 'kara a kasalance ya d'auka ya kara a
kunne, daga d'ayan 'bangaren tace "My ga Rahmatu nan yar aki zata kaika falon
baki".

"Banga kowa ba ni".

"to baby ka fito daga cikin motar mana zaka ganta".
Ta fad'a tana 'kara gyara tsayiwar ta a jikin balakona, saboda tun sanda ya shigo
take le'ken sa, har kawo yanzu da take waya da shi tsaye take ko motsin kirki bata
yi sai Murmushi da take yi zuwa zuwa mai wuyan fassaruwa.

Da ya bud'e murfin motar saida ya d'auki 10 seconds sannan ya fito da 'kafar sa,
guda bayan wasu seconds din ya fito da d'ayar, Zuby dake la'be a balakona mamaki
jan ajin irin ma Sadeeq take yi, saboda

Please Login or Register in order to submit comment