You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka dai na baro sa yana ta
zab ga godiya kamar wanda akace an gafar ta masa gabadaya zuniban sa.

A inda na bar sa anan na same sa tsaye da waya annu yana dannawa nace "baka tafi ba
yah Farooq?".

"ina zani fa ni da nike jiran mu shiga tare".

Nace "to shikenan tunda ka nace halan akwai abunda kake son yi muje".

Ina gaba yana baya har muka karasa cikin katafaron falon gidan in da naci karo da
Sadeeq har saida ya turo ni saboda shi zai fita ni kuma na kutsa kai abinka da mara
nutsuwa, shi kuma yayi ya dunfaro kofar ne cikin zafin nama, ihu na fara ina kiran
sunan Daddy saboda kaina ya dan bugu da bango, shi kuwa yaya Sadeeq yayi tsaki sun
fi biyar yana kara jin tsana ta a zuciyar sa yarinya sai tsinannan sharri to shi
yanzu mai ya mata da take so ta tara mai jama'a?".

Daga kan da zaiyi sai yaga Farooq a tsaye jingine da jikin ban go ya harde yannayen
sa a kirji sai Murmushin mugunta yake wa Sadeeq

A hasale Sadeeq yace" malam maye?".

"Nishadi mana ko kar nayi?". Farooq ya fad'a still kuma yana dariyar sa

"kallon kan ka ka rainawa hankali Sadeeq ya bi Farooq da shi kana yace bani wuri ni
na wuce kana bata min lokaci".

A dai dai lokacin Momy ta fito tana fadin "yaya lafiya ke dawa".

Sam bata lura da Farooq ba sadeeq ta hanga a gurin aikuwa ta fara yi masa fada da
tana cewa "a haf ai nasan sai kai sarkin cin zali in dai kaji kukan yarinyar nan a
gidan nan to ba kowa bane face kai".

Kallo na tayi tace ke tashi rabu dashi kiyi masa Allah ya isa tunda bazai daina ba
Allah zai saka miki ".

Ina gunjin kuka na mike ina fiki fiki da idanu na ina kara matso kwalla a haka na
haura sama na wuce daki na na kwanta a kan gado ina kallon sama ina jin zuciya ta
babu dadi.

Farooq na shaafa keya yace" Momy ina kwana?".

Sai a lokacin Momy ta waigo inda yake fuskar ta a sake
Tace" lafiya lau Farooq yaushe kazo ne?".

Yace" shigowa ta kenan "

Tace" madallah ya Hajiyar taku?".

" Suna lafiya suna gaida ku".

"Masha Allah muna amsawa, kar dai tafiya da gimbiyar kazoyi ?". Ta tambaye sa

Yace "eh Momy".

Tace "bai fada maka ta fasa zuwa ba?".

"Eh bai fada min ba amma yanzu dana shigo kan na kara so cikin gidan na hadu da ita
abakin get shine take sanar min cewa ta fasa zuwa".

Tace "yauwa sai kusan yadda za'ai dan Daddyn ku ya kusan gama shirya wa kuma yana
so yaji matsaya ne kan ya tafi". Tana gama fadar haka ta bar falon.

A hankali Farooq ya kara so inda Sadeeq yake ya dafa kafadar sa yace "aboki na
akwai matsala fa amma kana nuna kamar abin bai dame ka ba bayan kai ne mutum na
farko daza ka fi kowa shiga damuwa idan har yarinyar nan tace baza ta ba, ni
wallahi mamaki kake bani yar wannan yarinyar ta gagare ka sarrafawa sai kace ba
namijin duniya ba ko girman kan ne zai hana ka shaho kan ta? To idan shine zai fi
kyau ka aje sa a gefe saboda.... ".

"dallah malam dakata ya kake magana kamar kana bani umarni nifa kaga wannan karatun
da za tai kanta za tai mawa ba ni ba saboda haka idan ma karatun ne tace baza tai
ba kwata kwata ni ba damuwa ta bane bayan ita zan iya auran gudu uku wa'inda suka
fita komai, so kada ka tsaya bata yawun bakin ka ".

Farooq yace" nifa ba nufi na ka bata hakuri ba, ba kace yarinya ce bata da wayau ba
kuma bata san komai ba, to ai shaho kanta ba zaiyi wahala ba shine nike so kayi
mata yan dabaru
ko ka fasa kara auren ne?". Ya fada da alamar tambaya

Yace" ban fasa ba amma kada ta gano ni fa kasan bana son raini".

"haba babu abinda zata gano kawai shiga ciki zan turo maka ita".

Yace "to shikenan kai anan zaka zauna?".

"eh".

Farooq ya fad'a yana mai samun kan kujera ya zauna yace "kasa a kawo min ruwa da
dan abin tabawa".

"To" yace ya haura sama.

Khadija ce ta sauko bayan sun gaisa ta nufi kitchen ta hada masa kayan ciye ciye
da ruwa kana ta dora akan katon tirai tazo ta aje masa akan tebur zata tashi yace
"ina zuwa ki zauna muyi fira bana son zama shiru ni".
Komawa tai ta zauna ai kuwa nan Khadija tai ta basa labari yana kwasar dariya

* * * * * * *

Nan Abba ya bar Mama da Zuby cikin jimamin magan ganun sa, tabe baki Mama tayi ta
kamo hannun Zuby suka zauna akan kujera tace" wai meke faruwa ne dan ni wallahi ban
fahimci inda kalaman Abban ki ya dosa ba".

Sai da Zuby ta sauke gwauran numfashi kana tace "kina nufin Abba bai fada miki suna
son su hada aure na da Maheer ba?". Tai maganar ne cikin sigar tambaya

Mama tace "bai fada min ba amma in dan wannan ne ki kwantar da hankalin ki ban ga
aibun Maheer ba ni".

"Haba Mama ya kike so nayi da Soyayyar Sadeeq da take dawai niya dani wallahi yanzu
haka daurewa nike yi rabo na dashi tun jiya ko awaya bai kirani ba".

"shiyasa nace ki kwantar da hankalin ki yanzu ki fara shawo kan Sadeeq din daga
baya sai musan yadda zamuyi da Abban naki".

"Mama kin San bamu da wannan lokacin kuma tabbas Abba da gaske yake dan naga bacin
ran sa da ban taba gani ba, wallahi ni ba wai Maheer din ne bana so ba tsoro nike
kada asiri na ya tonu a silar aure na da zaiyi".

"Da wannan dan wannan" Mama ta fada tana sa hannu ta goge gumin daya keto mata a
goshin ta , wani kallo Zuby ta bits dashi da ita kadai tasan ma'anar sa, kamin ta
tashi ba tare da tace komai ba tanufi dakin ta, wayar ta ta d'auka number Sadeeq ta
shiga nema har sau uku tana kiran sa amma bai dauka ba

Shi kuwa Sadeeq zaune yake a dakin sa yana kallon kiran ta amma sai yaki dauka
saboda ba karamin mamaki ta bashi jiyannan ba, gashi bata kirasa ba tun jiya bare
ta basa hakuri shine yanzu zata kira sa tai masa dadin baki dan ta mayar dashi dan
iska, Sam bazai dauka ba har sai tayi nadama yanda ko nan gaba baza ta maimaita
makamancin sa ba.

Turo kafar dakin a kayi ko sallama batai ba ta shiga, a dai dai lokacin kiran Zubyn
ya kara katsewa

Saida na turo dan karamin baki na nace "yaya gani yaya Farooq ne yace kana kira
na".

Ganin yadda nike cika nike batsewa naba wa yaya dariya sai da yai Murmushin sa mai
isar sa wanda yake kara baiyana ainihin kyawun sa yace "zo kiji magana zamuyi kika
zo daure da dan kwali a kugu sai kace wacce tazo filin daga".

Sai alokacin na tuna da dan kwalin da naci dan mara dashi ni kaina dariya abun
yabani saboda na dade ban yi hakan ba kwan cewa na shiga yi yaya yace "a a ki bar
abin ki ya miki kyau".

Dan nesa dashi ta zauna yace "ikon Allah wai ni kike gudu to bari ni nazo na same
ki na fada miki ba dukan ki zanyi ba magana ce zamuyi ". Ya karasa maganar a
lokacin da ya zauna kusa da ita hannayen ta ya kama gami da tallafo habar ta hada
ido sukai cikin sauri tayi kasa da nata ba wai dan tasan kunya ba amma sai taga ya
kara mata kwarjini bazata iya cigaba da kallon kwayar idon sa ba , shiko Sadeeq
tausayin Siddeeqan ne ya kama shi a karo na farko a cikin rayuwar sa tun bayan ta
fara tasowa, wallahi bai taba tunanin akwai ranar da zata zo yaji tausayin ta ba
sai gashi rana kwatsam wai tana bashi tausayi, bai san sanda ya rungume ta a kirjin
sa ba yana jin bai kyauta mata ba, Siddeeqah dai ta zama kamar mutum mutumi cikin
ta har ya duru ruwa tsoro ya kamata tasan yauma aljanin yayan nata sun kuma tashi,
tana so ta dago tana tsoro, saida ya gaji dan kansa ya sake ta yana shafa bayan ta
yace "dan Allah Siddeeqah kiyi min wannan alfarmar ki daure ki tafi wannan
makarantar wallahi saboda ina son ki ne nayi miki wannan gatan".

Da sauri Siddeeqah ta dakatar da shi ta hanyar fadin "ya isa haka yaya duk maganar
da zamuyi a tsakanin mu kada ka ambaci so domin babu shi a tsakanin mu har abada ka
fada min ba zaka taba sona ba kamar yadda nima ban taba jin sonka dai-dai da rana
daya a cikin zuciya ta ba, na yarda zan tafi idan har kayi alkawarin za kabi duk
wani sharadi da zan fada maka".

Bakin Sadeeq na rawa Yace "naji fada min zan bi duk abinda kika ce".

Ta cigaba da cewa "na yarda zan je idan har ka yi alkawarin zaka sake ni idan
nagama karatu lokacin na girma na kara wayau ta yadda zan samu irin mijin da nike
so na aura, amma ni wallahi Sam ban dace da kai ba yaya". Ta fada tana dago kan tu
suka hada ido tayi sauri tai kasa da nata saboda kwarjinin sa.

Yana mamakin Siddeeqah lokuta da dama idan tayi wata maganar ko babbar mace albarka
koda yake ba abin mamaki bane zamani ne dan ga yaran da basu kaita nan ba suna abin
da ba kowace babbar macen ba itama dan ta taso a kauye ne shiyasa take da wayan
kauye

yace "in dai wannan ne mai sauki ne zan sake ki tunda ke ce kika bukaci haka amma
me zaki cewa su Daddy da Momy idan suka bukaci sanin dalili?".

Sai da ta tashi daga inda take tayi tsallan murna tace "bani ce zan basu amsa ba
kaine ya dace da ka basu amsa ko dai ka fada musu gaskiyar bama son junan mu ne ko
kuma kayi musu karyar da har abada bazasu gane ka ba kaga sai ka je ka auri wacce
kake so, nima na auri wanda nike so".

"to". Kawai Sadeeq yace dan tafara gundurar sa da wannan maganganun nata da yake
daukar su kamar tatsuniya

Bai san ita kuwa siddeeqah har cikin ranta take fada masa wannan maganar ba

Tace "ko kaifa yaya hannu ta mika masa tace mu kulla abota yaya nayi maka alkawari
daga yau zan dunga jin maganar ka zanyi kokari na zama mai nutsuwa kamar yadda kake
so zan dunga yin duk abunda kace nayi ina son wannan abotar tamu ta fara daga yanzu
zuwa lokacin da zaka sake ni".

A tunanin Sadeeq Siddeeqah ce bata da wayau dan shi gani yake ya gama da ita
shiyasa komai tace yake yarda, yanzu ma ya yarda su kulla abota din har zuwa ranar
da zata kare secondary school din nata ya bata takardar ta

Hannun sa ta kama tace "yaya tashi muje falo ka fadawa su Daddy na yarda".

Mikewa yayi kamar yadda tace ta shiga jan hannun sa suka soma tafiya tana gaba yana
biye d a ita a baya a haka suka fara taka step suna saukowa, tuni suka fara daukar
hankalin wasu daga cikin mutanen falon da suka lura dasu kama daga Daddy Umar
Jiddah da Ummee banda Farooq da Khadija da suka zauna akan kujerar da tabawa step
din, Momy kuwa bata gurin tana bedroom taje daukowa Daddy wayoyin sa daya manta,
gaskiya sun burge sun bada sha'awa kuma sun dace da junan su

Ahaka suka karaso fuskokin su dauke da nishadi
Ba karamin mamaki Momy tayi ba alokacin da ta gan su, haka ma Daddy da sauran yaran
gidan

Koda suka karaso falon kan kujera Siddeeqah tai wa Sadeeq masauki inda itama ta
zauna kusa da shi hannun ta na sarke da nasa sai Murmushi take tana kara shige wa
jikin sa shi kuwa Sadeeq daure wa kawai yake dan bai saba da wannan sabon al'amarin
ba yana so yai mata tsawa yana tsoran ta birkece masa

Momy da Daddy kuwa addua suke acikin ran su Allah yasa lokacin haduwar kan yayan
sune yazo Allah yasa su d'aure ahaka

Comment
Share
Vote

NI DA YAYA SADEEQ

·٠•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬٠·˙

Chapter 28

______Shi kuwa Farooq tsabar mamaki sai mutsuka ido yake yana budewa gani yake
kamar a film yake kallon su.

can Daddy ya numfasa yace "dama kai niki jira yanzu nike cewa Umar yaje ya kira min
ku dan lokacin tafiya ta yayi".

"Siddeeqah". Daddy ya kira suna na cikin wata murya mai nuna ana jin tausayin wanda
akai wa ita".

"na'am" nima nace bayan na zare hannu na daga jikin yaya na daga kai muka hada ido
da shi

Ya cigaba da cewa "shin kin amince zaki tafi makarantar kwana?".

Ina wasa da yatsaun hannu na nace "eh na amince Daddy".

Sai alokacin Momy dake tsaye ta zauna tana fadin "Alhamdu lillah Allah yasa hakan
ne yafi alkairi".

Take yaya Sadeeq ya sauke ajiyar zuciyar da ko wannen mu sai da ya dago kai ya
kalle shi, ni kuwa takaici ne ya kamani ganin yadda yake murna zai rabu dani sai
kace zai rabu da musifa, lallai ma yaya tabbas zan nuna maka nima macace kuma zan
iya yin duk wani abu da mata suke yi wajen burge mazajen su, sosai nayi nisa cikin
tsara yadda abubuwa zasu kasan ce, fir gigit nai a dan tsorace na dawo hayyaci na
sakamakon tabani da kafa da yaya yai.

Daddy yace "Siddeeqah lafiya tunanin me kike yi haka? bayan na hana ki yin dogon
tunani irin wannan, kina yar karamar ki Ko so kike hawan jini ya kama ki? Ki mutu
tun kamin lokacin ki yayi?".

Baki na narawa nace "A a Daddy insha Allah na daina daga yanzu".

Yace "Masha Allah, Allah yai muku Albarka ni zan tafi ki kula da kanki banda kula
kwayen banza karatu ne ya kaiki shi zakiyi "

Nace "to Daddy nagode insha Allah bazan baku kunya ba".

Sai da ya sallami duka yaran gidan, dama Momy ya ruga ya sallame ta, kana yabi ko
waccen mu da kudi masu kauri, Gaba dayan mu muka dunguma zuwa harabar gidan saboda
muyiwa Daddy rakiya saida muka ga tafiyar shi sannan muka dawo gida, Momy ta daura
daga inda Daddy ya tsaya nasiha take min mai ratsa zuciya jiki na duk yai sanyi,
son Momy da kaunar ta yana dad'a ratsa ilahirn jiki da bargo na, saboda yadda take
kula dani, da nuna min so da kauna.

Bayan ta gama min nasihar tace "naje na kara shiryawa".

Kallon Ummi da Khadija nai muka hada ido naga jikin su yai sanyi Umar kuwa harda
kwalla, jiki na a sanyaye na mike na haura sama ba wani wankan na sake ba kaya
kawai na sauya i zuwa riga da sikel na atamfa dinkin bai min yawa ba kuma bai
kamani ba, sannan na dauko hijabi na nasaka ko da na sauko a tsaye na samu Yah
Sadeeq da Farooq da wani katon akwati a gaban shi, yana Murmushi yace "yauwa muje
ko, ke muke jira".

tuni kwalla ta fara wanke min fuska ta nace "amma yaya baka kira min Inna ba".

Shafa keyar sa yai yace "ai na manta gwara da kika tuna min".

Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar sa, amma sai ya rasa wa zai kira sanin Inna babu
waya a hannun ta dama da ta Farooq suke gaisawa "saida ya dan bata rai yace "kina
da rigima Siddeeqah sanin kanki ne Inna bata da waya"

Goshi na dan dafe, tuna cewar batada wayar.

Yace "amma dai ki bari zan san abin yi tunda ni yau zan koma zan baki number ta
idan kinje makarantar sai ki bama wata senior ta kirani sai na hada ku kuyi
magana".

"to" kawai nace

har bakin get su Momy suka rako ni, in rungume wannan in saki wannan haka dai nan
ta kuka Khadija da Ummi da Umar suna tayani, yayin da Momy ke bamu hakuri kamar kar
mu rabu da juna saboda sabon da mukayi, sabanin Jiddah da ko Allah ya kiyaye hanya
bata ce ba sai kallon banza da take bi na dashi, tana cika tana batsewa, yi nai
kamar ban gan ta ba saboda yanzu ba lokacin fada bane a gurina.

Da kyar yaya ya lallashe ni na shiga mota inajin raina babu dadi, tuni daman yah
Farooq ya shiga sannan shima sadeeq din ya shiga mai gadi ya wangale get muka fice,
su Momy nayi mana Allah ya sauke ku lafiya.

Yaya Farooq ne ke tukin yayin da Sadeeq ke kujerar me zaman banza ni kuma ina gidan
baya ji nike gabad'aya rayuwar ta dagule min tafiya ta fara yin nisa dan barci har
ya fara dauka ta

* * * * * * *

Zaune take kan dan madaidaicin gadon ta hannun ta rike da wayar ta sai cije lebe
take tana tsaki wai ita Sadeeq zaiki dagawa waya to wallahi bai isa ba tun da yace
yana son ta sai ya aure ta ta fada afili yayin da tayi kwafa.

Number Lubansy ta danna ta kira har tafara ringing sai kuma ta kashe saboda tasan
itama fushi take da ita baza ta d'auka ba idan tana son su shirya sai dai fa ta
shirya taje gidan su, gashi ita kuma yanzu bata jin zata iya fita saboda zuciyar ta
babu dadi, safa da marwa ta cigaba da yi gabad'aya ta rasa me zatai, can ta tuna da
group din su na madugo aran ta yltace "bari na dan hau online ko na samu na rage
damuwa" gefan gadon ta zauna kana ta dauko wayar ta shiga cikin whatsapp din nan ta
tarar da sakonni masu yawa amma duk bata tsaya bi ta kansu ba, abinda ya kaita
kawai shi take so tayi, bayan ta shiga cikin group din a hankali tafara karanta
sakonnin da akayi bata nan bata jima tana duba chart d'in ba ta fahimci cewa fada a
keyi sakamakon wata da tayi left cikin sauri da sauri ta cigaba da duba sakonnin
har zuwa inda aka tsaya da firar take ta fahimci Baddy ce tai left kuma ana
kyautata zaton yar leken asiri ce gabad'aya hankulun officials da members din gidan
a tashe yake saboda idan asiri ya tonu ba karamin yaki za ai ba, tuni Zuby ta shiga
cikin firan inda har take bada labarin tayi magana ma da yarinyar har take ce mata
"hajiya Tubalas ce ta kawo ta"

Hajiya Tubulas da jin an ambace ta, ta shiga auna ashar tana cewa "kada ayi mata
sharri ita yanzu ko wuqa a ka sa mata a wuya a kace ta siffan ta kammannin Baddy to
sai dai a yanka ta dan bata san ta ba".

Shugabar kungiyar madugo tace "ya kamata a hada meeting na gaggawa saboda a kawar
da wannan gagarumar matsalar".

Tubulas tace "gaskiya bazai yuyu ba saboda a cikin dokokin kungiya ba a meeting sai
ranar litinin din da tazo a cikin karshen wata, kuma kunga yau talata 28 ga wata,
nasan kunsan cewa karya doka daya ta wannan kungiyar dai dai yake da tonuwar
asirin mu gabaki daya".

Sai alokacin Turai ta tuna da wannan dokar kuma gaskiyar Tubulas ne karya daya daga
cikin dokokin kungiya babban laifi ne dan har gwara su dauwama a cikin wannan
tashin hankalin da suke ciki, amma abin dubawa anan shine wata uku da suka wuce
duka watan bai kare da litinin ba, kuma da alamar wannan ba ba da litinin zai kare
ba, tunda yau talata.

Duk kannin su sunyi na'am da batun Tubulas saboda haka suka ce a nemo wata mafitar
amma haka sukai ta fama duk inda suka bi sai suga babu hanya

Zuby dai gajiya tai ta sauka daga online din tana mamakin yadda Baddy ta ci amanar
su, tasan tabbas kungiya bazata bar ta a haka ba sai ta dauki mummunan mataki akan
ta.

Kofar dakin ta taji ana bugawa da sauri taje ta bude ba tare da ta tambayi wanda
yake buka kofar ba, koda ta bude Lubancy ce ta shigo tana wani shan kamshi bakin ta
dauke yake da chingom tana taunawa yana kara kas-kas haka dai tai ta yamutsa baki
tana yauki, bayan Zuby ta maida kofar ta rufe tazo ta rungume ta tana cewa "aminiya
nayi missing din ki". Lubancy taso sharewa amma saita kasa saboda a matse take tuni
itama ta rungumo ta tana sauke ajiyar zuciya, basu tsaya wata wata ba suka shiga
cire ma juna kaya suka fada kan gado suna nishi tuni suka fara shafe-shafen juna
suna sauke ajiyar zuciya.

idan kida ya sauya, rawa ma canza ta ake yi ganin abin yafi karfi na yasa na fito
daga dakin naja musu kofa, ina yi musu adduar Allah ya shirya su dan wannan dabiar
bata mutanen kwarai bace wace irin musifa ce wannan da mace take neman yar uwar ta
mace yayin da shima namiji yake neman dan uwan sa namiji, shiyasa annoba bazata
rabu damu ba saboda aduk lokacin da akasumu saukar annoba to sabon Allah ne yai
yawa akasa, kuma duk masu wannan dabiar a wuta zasu dauwama.

wa'iya zu billah.

* * * * * * * *

Yunwar da ta fara kwakular ciki nane ta tashe ni daga nannauyen baccin daya dauke
ni na manta a mota nike saboda haka nai mika gami da yin juyi, ai kuwa cikin rashin
sa'a na fada sakon mota inda ake saka kafafu, ihu na fara ina kiran sunan yaya da
duk ya bi ya gaji sai mita yake wai Farooq baya gudu ". Shi kuma Farooq na cewa" in
ba sama kake so na tashi ba ai wannan gudun ya isa ".

Ihu na ne ya katse musu firar su da sauri yaya ya juyo da kansa cikin motar yana
fadin "subhanallah garin yaya haka ta faru maza tashi". Ya karasa maganar yana zuro
da hannayen sa da kyar na iya temaka masa ya daga ni, bayan na gyara zama na akan
kujera nace "yaya wai har yanzu bamu kai ba ni na gaji yunwa nike ji". Na karasa
maganar cikin sigar shagwaba, nuna min Farooq yai yace "duk laifin shi ne kwata
kwata baya sauri tafiya yake kamar wanda yake tsoran taka kwalta".

Nace "to ni yaya yunwa nike ji"

Yace "to bari mu karasa can gurin ina kyauta ta zaton karamar kasuwa ce sai muje
baza'a rasa abin tabawa ba". Ya fad'a yana nuna min wani guri da nike hangan mutane

"To" Nace yayin da na hada kaina da gwuiwa ta

Ba mufi minti 7 ba muka karasa bakin gurin, kasuwa ce yar karama mata da maza sai
zurga zurga sukeyi, yara da manya Farooq yace "banda abinka Sadeeq me zamu samu
anan da zamu ci?".

Yace "mu fita ahaka ba zamu gane ba kuma can ma kamar masallaci ne mayi sallar
azahar gashi ma kamar ana kiran la'asar duka sai mu sauke nauyi,

Yah Sadeeq yace" ki zauna a mota bari mu fita mugani ko zamu samu abinci".

Ban bashi amsa ba suka fita harda rufe motar

Basu wani jima ba sai ga Yah Farooq ya dawo da kwano a hannun shi da kwarya, bayan
ya bude motar ya miko min na amsa, shi kuma ya juya

Koda na bude kwanon danbu ne na gani yaji gyada da zogale yayin da ita kuma kwaryar
fura ce acikin ta me rai da lafiya

Ba tare da nayi bismillah ba na shiga cin danbun, duk da yawan danbun saida na
kusan yin rabin shi saboda ina mutukar son danbu a rayuwa ta, bayan na koshi kuma
na dauki kwaryar fura itama na fara sha saida naji na cika cikina dam, har inaneman
gurin numfashi sannan na hakura ba don bakina ya koshi ba sai don cikina da ya
koshi

Gyatsa nike so nayi kozan dan ji dadin ciki na amma taki zuwa saboda haka nai ta
bude baki ina Jan iska

Can saiga su yaya nan sun dawo hannun Yah Sadeeq dauke da gorar ruwa bayan sun
zauna yace "kin rage dan bun?".

Nace "eh".

"yauwa miko wa Farooq danni bazan ci ba furar zan sha ai itama kin rage?"

"eh nace yayin da na miko mai kwanon danbun dana furar

A mota suka ci bayan sun gama suka je suka mayar da kwanon da kwaryar

Daka bisani muka kuma daukar hanya

" Nace yaya amma dai mun kusa zuwa ko?"

" eh mun kusa bai fi sauran mu 30 minutes ba mu karasa, ya nuna min wata katan ga
da muke ta shigewa yace "nan kinga duk makarantar ce, zaro ido nai nace" kai yaya
gari guda haka ".

Yace" eh har tafi haka girma bari muje ki gani".

Haka dai nai ta yiwa Sadeeq surutu yana biye min duk da fuskar sa babu wal-wala
amma duk tambayar da nai masa yana bani amsa, a raina nike cewa "nasan yana tsoron
nace na fasa ne shiyasa yake amsa min".

* * * * * * * * * * *

Aban garen Zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su tashi sukai suka shiga wanka
kamar kullum nan ma saida suka bata lokaci suna tsotse-tsotse kana suka fito
fiskokin su dauke da nishadi suka shirya cikin wata doguwar riga me ruwan kwai tana
da laushi matuka Lubancy tace "ina zamu yau?"

Zuby tace "gurin shakatawa man, yauwa naga baki hau online ba meyisa".

Lubancy tace "banida data ne, wani abun ya faru ?"

Zuby tace "kwarai ma kuwa ina wannan yarinyar da kika sameni ni da ita jiya?".

Tace "eh na tuna

Please Login or Register in order to submit comment