You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ɗan jima a bakin ƙofar, kafin Momy ta buɗe ta fito, "lah inna ke ce?
Bata jira amsar ta ba, ta ɗora da ina kwana hajiya".

cikin sakin fuska Inna ta amsawa surukar ta, kana tace ya baƙun ta?".

"Lafiya lau". Momy ta bata amsa.

"To alhamdu lillah".
A cewar Inna, ta ɗora da cewa "ki yaƙuri na tashe ki kina tsaka da bacci".

"Ayyah babu komai Inna" cewar Momy.

Inna ta cigaba da cewa "daman Garba ne wai a ban ɗaki, tun asuba gashi har yanzu
bai fito ba, Siddiƙa ma tace yau kamar gamo yayi, saboda yana tayin wasu abubuwa
irin na taɓaɓɓu, shine nace bari na tada ki muje bayin mugani ko lafiya".

Momy tace "Hajiya Inna badon karkice na raina ki ba da bazani ba tunda shi bayajin
magana".

Inna tace "Haƙuri zaki Aisha muje mugani ko lafiya, kinga da ya idar da sallar
asuba yake tafiya gurin aiki, amma yau shuru".

"To". Momy tace badon ranta yaso ba, tabi inna ban ɗakin.

Koda su Momy suka ƙarasa bakin bayin sunan shi Inna takira "Garba Garba". kamar
babu kowa a ciki, saboda bai amsa ba, saida Momy tace "Sadeeq wai lafiyar ka?".

Da wata iriyar murya yace "wallahi Momy nima ban sani ba".

Tace "au daman kana jin Hajiya na kiran ka kayi shuru, saboda ka raina mutane, ai
sai ka fito ka bawa mutane guri, saboda gari ya waye".

Yace "Momy bazan iya fitowa ba".

"Saboda me?". Ta tambaya

Momy wlh yau Ban san me ke shirin faruwa dani ba, ko nayi gamo ne tun nafito sallar
asuba na haɗu da bala'i ko sallar ma banyi ba". 🤣

Salati suka hauyi Inna natafa hannu kace "baka yi sallah ba, tom wai me kake yi a
cikin bayin ne haka?". Cewar inna

Cikin jin zafin tambayar da Inna tayi mai sadeeq yace "Wai baki ji nace ina cikin
bala'i bane, amma kike sake tamba ta".

Momy ce ta daka mai tsawa "rufe min baki anan gurin ko na ci maka mutun ci, kuma
kafito kabawa mutane guri suna son shiga bayan gida".

Sadeeq yace "Amma Momy...".
Katse shi tayi da "ko baka ji abinda nace maka bane".

"Naji". Ya faɗa a ta ƙaice,

Ɗan matsawa suka yi nesa da bayan gidan.

Ni kuwa da tun tuni nike zaman jiran fitowar sa, da naji Momy tace "ya fito". Sai
Na ƙara gyara zama na a kan kurer tsakar gida.

Saida ya ɗauki tsayin minti biyar kafin ya cire sakatar, ya buɗe ya fito, babu ko
riga a jikin sa, sai ɗan gajeran wando, basu Inna kaɗai ba hatta ni da niyi zaman
jiran fitowar sa, saida na tashi tsaye saboda yadda yayi wani iri, kamar ba yaya
sadeeq ɗan gayu da ƙwalisa ba, yayi wani wuji-wuji dashi, idanuwan sa sunyi jawur
se mutsuka su yake, ga jikin sa duk ya kar-karce sa da farce, harda shedan jini, ba
ƙaramin ciwuka yajiwa jikin sa saboda susa ba, hatta da fiskar sa bai bari ba
akwai alamun karta, duk ya faɗa fuskar nan yayi zuru zuru.

Mamaki ne kwance a kan fusko kin su Momy.

Momy tace "Wai sadeeq me ke damun ka haka kamar me borin jini?".

"Momy nima bansani ba". Ya bata amsa.

Yanzu yaji sauƙin ƙaiƙayin da jikin sa ke yi, sai dai raɗaɗin da fatar jikin sa ke
mai, da bala'in zugi.

"To ai saika je ko jallabiya kasa mutafi asbiti". Inji Inna.

"A a Inna ba sai kunje ba don asbitin gari zani kuma da nisa ku zauna a gida". Ya
faɗa yana tafiya.

ta kusa dani yazo wucewa, saida muka yi ido huɗu dashi na kwashe da dariya🤣

Kallan tsana yayi min, sannan ya nufoni, dagudu na miƙe, nanu fi bayan Momy ina
haki, biyoni yayi shima, da hannu Momy ta da katar dashi sannan tace "amma walahi
sadeeq kaji kunya kanwar kanwar ka itace abokiyar yinka, ba dole ta raina ka
ba,Wallahi ka bada maza wuce kabani guri, kamin kiƙam a gaba kamar wani soja, Ko
wannan iftila'in daka faɗa be isheka ishara karabu da yarinyar mutane ba". Ta ƙare
tana nuna mai hanya da hannu.

Badon yaso ba saidan yabi umarnin mahaifiyar sa.

Sake haɗa ido muka yi dashi, nayi masa gwalo ina ƙara yin dariya ciki ciki😄

Yace "Zan kamaki yarinya wallahi zakiyi bayani".

Inna tace"Ai gashinan alhakin tane wannan abin da ke faruwa da kai, saboda Allah ba
azzalimi ne ba sai dai bawa ya zalinci kansa".

"Kwarai ma kuwa". Momy tace

Jikin sa babu ƙwari ya wuce mu, tashi nayi nima nakoma ɗaki, saboda na gabatar da
sallar a subahi, sai a lokacin nayi sallar takwas saura, ina idar wa ko kan sallaya
ban sauka ba nahau rawa da juyi, saboda na rama a binda sadeeq yayi min, gado na
koma saboda yau bazan je 'yar kasuwa yin tsokanar safe ba bacci zan koma

♾️♾️♾️♾️♾️
Abangaren sadeeq kuwa koda yaje asbiti, kulawa ta musamman suke bashi saboda
asbitin su na 'yan sanda yaje, har gado aka bashi sannan aka saka mai ledar ƙarin
ruwa, saboda yana bukatar ruwa ajikin sa.

Harda allurar bacci a kamai saboda ya sami hutu.

♾️♾️♾️♾️♾️

Koda na farka daka bacci ƙarfe shaɗaya saura11:00am, naji dadin baccin sosai domin
ya ragemin damuwa.

Kamar yadda nasaba idan natashi bacci miƙa nayi babu ko salati, na sauka daga kan
gadon, na ɗauki brush ɗina na fito tsakar gida nayi, sannan nanufi falon hajiya,
acan na iske su Khadija suna cin waina da miya.

zama nayi kusa da Momy nace "ina kwana Momy".

"Lafiya lau". Tace min "kin tashi lafiya?".

Nace "eh Momy lafiya lau". Saboda ni bana son doguwar gaisuwa.

Tace "ba inda ke miki ciwo?".

kai na ɗaga mata
"madallah" ta ce masha Allah haka ake so.

Inna na kallah naga ta tasa kwaɗan zogale da kuli a gaban ta sai kaiwa baka
takeyi, ɗan Murmushi na sakar mata, ita ma ta maido min.

Kana na gyara zama, na saka hannu a kular wainar su Khadija, ina ci ina lumshe ido
saboda daɗi, Nace "Inn wai wannan wainar wane gida ce".

Tace "ta gidan su fulera ce matar ɗan tsoho".

"Haba koda naji". Nafaɗi haka yayin da nike kai lomar waina a baki na.

"Kice kinyi santi" Murmushi nayi kawai na cigaba da ai kawa cikina.

Umar ma cewa "yayi ni rabon da naci waina me daɗin wannan wallahi na manta".

"Umar duk santin ne haka". Inji Khadija.

Yace "ai kokema kinyi tunda naga kunnen ki ɗaya sai rawa yake".

Kowa a ɗakin saida ya dara

♾️♾️♾️♾️♾️

Bayan Sadeeq ya farko daga nannauyan baccin da ya ɗauke sa, jikin sa babu kwari
sam, a za filo yai a bayansa ya jingina, yana jin gabaɗaya jikin sa na mai ciwo, ga
wata yunwa da ke ad'dabar cikin sa, da kasala.

Likatan ne yazo ya zauna agaban shi dayike a bokin sa ne kuma shima ɗan sanda ne,
yace "wai sadeeq dame kai amfani ne?".

Ɗan shiru yayi kafin yace "nidai a binda nasani natashi da a suba lafiya ta ƙalau,
amma da bayan na ɗauki buta ta, naje bayi na dowo nafara jin yanayi na yana
sauyawa, koda na fara alwala ko fiska ban gama wan kewa ba, tsarkin da nayi yafara
damu na,
Sai nasa aka kai min ruwan wanka, to na ƙarƙare maka zance, daka zuba wannan ruwan
a jikina kiɗan ya sauya salo, sai azabar ta ƙaru bayan na sa a miƙo min sabulun
wanka, ba ba nasha wuya fa sosoi, tun asuba nike a cikin bayi nine har ƙarfe
takwas saura, wannan raunin duk ni najiwa kaina, saboda ƙyaiƙayin da jikina ke min,
idan ban sosa ba bana jin daɗi".

Dariya sosai Dr Farooq yake yi, Sadeeq yace "dr banason iskanci fa, nifa ban baka
labari don kayi min dariya ba, sai dan kayi aikin ka".

Dr Farooq yace "ba ba wallahi labarin naka ne gunin ban dariya, sai kace a cikin
shirin film".

Duka Sadeeq yakai wa Dr Farooq ɗin, amma sai ya kauce yana faɗin "shege ka samu
kenan, ɗazun kamar wani lagwani kana ta numfar fashi kamar baza ka kai aniji ma
ba".

Saukowa Sadeeq yayi daga kan gadon, Dr Farooq yai saurin miƙewa, ɗakin suka fara
zagayewa, Farooq ɗin yaƙi barin sadeeq ya kama sa, dan kansa Sadeeq ɗin da ya gaji
ya haƙura, ya janyo kujera ya zauna yana maida numfashi, ruwan sanyi Dr Farooq ya
ɗauko a ciki firiji ya miƙo masa, yana faɗin "maganin ɗan iska kenan gobe ma ka
ƙara".

Sadeeq ɗin amsa kawai yayi be kula sa ba
♾️♾️♾️♾️♾️♾️

𝑑𝑎𝑛 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑟𝑒𝑎𝑑𝑒𝑟𝑠 𝑘𝑢𝑦𝑎 ha𝑘𝑢𝑟𝑖 𝑎𝑏𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑦𝑎 𝑠𝑎𝑚𝑢 𝑦𝑎𝑢 𝑘𝑒𝑛𝑎𝑛 𝑏𝑎𝑏𝑢 𝑦𝑎𝑤𝑎


NI DA YAYA SADEEQ


‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Chapter 07

Ya ansa gorar ruwan ya fara sha, saida ya shanye ruwan tas sannan yace "malam kayi
min bayanin matsala ta nasan dai ba waccar matsalar bace".

"Eh ba ita bace" Farooq ya bashi amsa

"Amma a bisa binciken danayi, ya nuna kayi amfani da abu mai saka fatar jikin mutum
ƙaiƙayi acikin ruwan da kayi amfani dashi, sannan shima wannan raɗaɗin da kake ji
kayi amfani da abu mafi zafi ajikin fata, shiya sa yake maka wannan raɗaɗin". Dr
Farooq ne yayi wannan bayanin.

Shuru Sadeeq yay kamar meyin nazarin wani abu, be tuna komai ba, Dan haka ya taɓe
baki yace "Nidai nasan ban saka komai cikin buta ta ba amma zanyi bincike, saboda
abin da mamaki".

"Dadai yafi". Farooq ya bashi amsa ya kuma cewa "katashi muje akwai magun-gunan da
zan rubuta maka zasu temaka sosai, wajen rage maka raɗaɗin da kake ji".

♾️♾️♾️♾️♾️

Ina zauna a kan kujera a tsakar gidan mu, ina dakan kayan miya yamma ne lilis,
saiga Ladiyo kawata nan ta shigo jiki duk kwata, tun daka nesa nike ɗaga mata
hannu, saboda kada ta ƙaraso inda nake, bazan iya jure shakar warin kwatar da ke
jikin ta ba, ida nuwan ta jawur dasu, alamun taci kuka ta ƙoshi.

Saida nayi dariya mai isa ta sannan nace " ke Ladiyo garin ya kikayi wanka da kwata
a jikin ki kamar sabon shiga hauka?".
Takaici na ne ya ishi Ladiyo na dariyar da nike mata, ga tambayar rainin hankali
dana jefe ta dashi.

Cikin shash-sheƙar kuka take cemin "Ummata ce ta aike ni na kai mata niƙa, bayan
nakai annuƙo, akan hanyata ta dawo wa gida na haɗu da su Habibalo, itada Larai
sukai ta zagi na, naƙi kula su, nayi ƙoƙarin ganin na cigaba da tafiya ta, amma
suka hanani wuce wa, wai sai nayi dambe. can saiga Atinen Malam Bala nan Shine tace
"wa na kama wai jiya ni dake munwa ƙanwar ta duka, haƙuri na fara bata, amma suka
samin dariya, wai wallahi sai sun rama wa ƙanwarsu dukan da da kika yi mata, shine
suka haɗu sukai min dukan tsiya, sannan suka jefani a cikin kwata". Ta ƙarasa
maganar hawaye sabbi suna zubo mata ta ciga ba da faɗin "basu tsaya iya nan ba
saida Suka zubar da ƙullun wainar da na markaɗo".

Wata muguwar dariya ce ta ƙwace min ban san da zuwan ta ba, saida nayi mai isa ta.

Sannan nace mata "wallahi Ladiyo ke sakarya ce ki ka tsaya kamar kayan wanki suka
jibgeki,
🤣Baki iya koda mintsilun su ba, Hhmm ai da ni ce koda ya ƙushi da cizo saina rama,
kindai san halina, ni yanzu da ki kazo ki ka faɗa min inyi miki me? ai da zuwa gida
ma ki kayi Umman ki ta miki dukan da zata miki da tuni ya wu ce, amma a nan kina
ƙarawa kanki laifi ne a gun umman ki, kuma kin santa da jaraba".

Wani sabon kuka Ladiyo ta kuma fashe wa dashi,

Ni kuwa sai ƙyalƙyala dariya nikeyi harda rike ciki abin nema ya samu.

Dundun da naji an ɗuma min a bayana ne ya dawo da ni haiyaci na, Inna ce tsaye tana
huci.

Tsuke baki na nayi nace "Inna kin wai me nayi miki ne?".

Cikin jaraba irin ta tsofaffi Inna tace "ja ira ba ke kika ja mata du kan ba, amma
tana faɗa miki kina yi mata dariya".

Ta juya ta kalli inda Ladiyo take tace "kema ai da naki laifin, Ladiyo kina san
kiyi tsokana amma ba kida ƙarfi, kuma tsokana ta mara tsoro ce, tunda ba zaki iya
cire tsoro ba, sai kidena biye mata, idan ba haka ba wataran karyaki za ai".

Jin Inna tace za'a ɓalla Ladiyo yasa na ƙara kwashewa da dariya.

Cikin takaici na Ladiyo tace "ke ai sunce idan suka kama ki ɓaɓɓalla ki za suyi".

Wani ƙaton a shar nayi, Inna dake kusa dani tace "A'uzu billah".

Naci gaba da cewa "ke ma kin sani kaf ƙauyen nan, na ga gari uban kowa, na wuce ayi
min harara bare zagi, kinga ina za aje ga duka, ke dai da kike sakarya sai kita
tsayawa tunda sun gano lagwanki".

Momy dake jinmu tunsanda Ladiyo ta shigo gidan, tazo ta miƙo min kuɗi 1000k tace
"ungo miƙa mata ta kaiwa mamar ta".

Saida na amsa kuɗin sannan nace "wallahi Momy dan kece da bazan iya zuwa inda take
ba, ba kuji yadda gidan nanan yaɗau ka ba?".

Duka Inna taƙara kai min a karo na biyu, amma sai na kauce ina faɗin "ba zaki
ƙarasa ni tun kafin lokaci na yayi ba, da saura na wallahi".

"Shaƙiyiya har Talle ne zai yiwa audi gori?".
"Tab wai me kike nufi?". Nace da Inna "ni kika yadawa magana ko wa? Yo ai ko ke ba
zaki nuna min wanka ba bare Ladiyo".
Na ƙarisa faɗa ina murguɗa baki.

Hanci na na toshe da dan kwali na, sannan na nufi gurin da Ladiyo take a tsaye,
nesa kaɗan da ita natsaya nace "miƙo hannunki" miƙo hannun nata tayi, na saka mata
kuɗin nace "yau Allah ya ƙwace ki wajen Umman ki, da kinci duka biyu".

Godia Ladiyo tayi wa Momy sosai, zata wuce nace mata "mu haɗu a yar kasuwa anjima".
da "Tom" tabani amsa

Inna kuwa sai mita take wai Ladiyo bata da wayau, Momy na bata haƙuri tana cewa
"sha'anin yara kenan sai haƙuri".

♾️♾️♾️♾️♾️

A bangaren sadeeq kuwa yana dawowa gida ana kiran sallar magriba, ɗakin sa yabuɗe
ya ajiye ledar maganin da Dr Farooq ya rubuta mai shi kuma ya siyo, saboda ba suda
shi a abitin su kuma yace "zai rage masa zafin raɗaɗin da kaye ji".

Fitowa yayi daga gidan, yanufi masallaci, anan yayi alwala aka gabatar da sallar
magriba da shi, bayan an idar mutane sun fara raguwa ya miƙe, saboda ya biya bashin
sallolin da ake binsa, ai kuwa ya fara jero sallolin saida ya idar dasu kaf, ashe
a kwai wani mutum da ya lura da shi, tun sanda yafara sallar, ba ƙaramin mamaki
yayi ba da yaga matashi me jini ajika irin sadeeq ya tsaya yana haɗa sallah. Beyi
ƙasa a gwuiwa ba, yaje ya miƙa masa hannu saka yi musabaha, kana yace "yallaɓai
Allah yasa dai lafiya naga sai salloli kake jerowa kuma ga dukkan alamun ba nafila
bace farrila ce, saboda tun sanda ka fara nike lura da kai".

shiru sadeeq yayi, saida ya gama ƙarewa mutumin kallo tsaf dattijone dan gashin
kansa ma a kwai fur-fura, gwauran numfashi ya sauke, saboda bai san ya dattijan zai
ɗauki lamarin ba, amma zaifaɗa mai gaskiya tunda shi ya buƙaci jin dalili.

Bayani sadeeq ya shiga yimai dallah dallah, a kayi sa'a dattijan ya fahimce sa,
Fatan samun lafiya yayi masa, daga bisani ya miƙa masa hannu suka kuma yin sallama
dattijan ya tafi

♾️♾️♾️♾️♾️

Siddeeƙa kuwa bata samu fita daka gida ba sai bayan sallar Isha'i, koda Allah
yabani sa'a nafita daga gida, ina tafe a hanya ina tsokanar duk Wanda naci karo
dashi, raina fes saboda Izuwa yanzu nayi tsokana har ba a dadi, nafi tare masu yin
talla kuma nace "dole sai munyi dambe". Duk wanda yaƙi biye min, sai na zubar masa
da abin tallar na ruga da gudu ina dariya.

Hankali na kwance nike tsokana ta, yanzu haka wata me gyaɗa na tare, nayi nayi da
ita muyi dambe amma taƙi ta ce "ba abinda ya futo da Ita kenan ba". Saida nayi
shewa kamar ina gidan biki nace "yo ni abinda ya fito dani kenan ko kina so ko
bakya so sai munyi damben nan". Na ƙarasa faɗa ina ƙoƙarin kama tiren gyadar, ban
lura da kowa a gun ba ido na ya rufe, naji caraf an damƙe min hannu, koda na waigo
da kaina saboda nayi masifa, sai naga yayan yarinyar ne fuskar sa a murtuke babu
alamar wasa yace "yau me rabani da ke a gurin nan sai Allah, zakici ubanki daman
na daɗe ina Addu'ar irin wannan ranar, sai gashi kin kawo kanki har gida, saboda
kin addabe yaran unguwa ko ina yara labarin ki suke yi, kuma gaki 'yar ƙarama bare
nace jiki gareki kike tsorata su dashi".

Sai yanzu na ƙarewa layin kallo a she a ƙofar gidan su yarinyar nike.
Inada taurin kai bazan taɓa iya bashi haƙuri ba, ko da kuwa zai kashe ni, cikin
ƙarfin hali nace "dalla malam ka sakeni ko nayi maka sharri".

ɗaga hannun sa kenan da zummar ya mare ni, sai yaji ance "'kara mata".

Sai da gaba na yafaɗi, saboda me muryan ko a mafar ki naji yayi magana sai na gane,
bare kuma a zahiri.

Zauke hannu sa yayi, ya fasa mari na, ya maida duban sa izuwa inda yaji maganar,
saiga yah Sadeeq ya bayyana cikin takun sa na isa da ƙasaita.

Har inda muke ya ƙara so be tambayi ba'asi ba, yaciro belt ɗin wandon sa, ya cewa
matashin "ungo wannan kazane ta dashi nake ga kamar zaifi shigan ta, kuma hannunka
baze maka zafi ba".

A tsorace matashin ya kalli yah Sadeeq saboda ya shaida shi kuma yasan ni kanwar
sa ce.

Cikin in-inar magana matashin yace "yallaɓai nama haƙura tunda kayi magana". sai a
lokacin ya sakar min hannu.

Da alamar yah sadeeq ba haka yaso ba, so yayi a daka ni, dan yabuɗe baki zaiyi
magana kenan na falla da gudu ina cewa "Allah ya isa ban yafe ba ku duka ƙartan
banza, masu faɗa da 'yar cikin su". 😄

Duk kansu sunji a binda nace saboda na ɗaga murya ta sosai, kuma dama haka nike so,
shi dai matashin mamaki abun ya bashi, a cikin ransa yake cewa "yallaɓai guda nama
wannan rashin kunyar, tabbas tunda nawa yallaɓai babu wanda bazan mawa ba".

Yah sadeeq yanada Alheri, bashida rowa, yana so ya kyautatawa na ƙasa da shi,
saboda haka ya ciro kuɗi daga aljihun sa ya bawa matashin 'yan Naira Ashirin
sababbi gada gal.

Matashin ya ansa yana godiya .

Ban dawo gida ba sai 10:00 pm saura kamar dai jiya, bana kallon gaba na a guje na
shigo cikin gidan, yah Sadeeq da ɗauko kular a bincin sa kenan, na buge sa abinci
ya zube, koda na lura da abinda nayi ɗakina na shige aguje na saka sakata, ina
maida numfashi.

Su momy sunga abinda yafaru

Gurin Inna ya koma "Inna ina abincin yarinyar nan?". Ya tambaye ta

"Gayi can". Ta nuna masa wani kano dayike arufe cike da shinkafa da miya harda ɗan
naman kaza, ɗauka yayi zai fita, Momy tace mai "dawo mata da abincin ta kafin na
saɓa maka". Inna ce ta katse ta da faɗin "haba Aisha yanzu ai itace da laifi bakiga
yadda ta zubar mai da abincin sa ba, kuma idan ba natan ba mai zaici? kinsan Garba
baicin abincin waje, gashi dare yayi bare a sake girka masa wani". Ta cigaba da
cewa "mutumin ma da ba lafiya gare sa ba ma, yanzu fa yake ce mana sai da aka ƙara
masa ruwa da yaje asbiti, kuma ance saiya ci abinci sannan yasha magani,
tunda ba tajin magana ita ta kwana haka, yi tafiyar ka Garba kaje ka ci abin
cinka".
Yace "na gode Inna" ya fice daga falon.

khadija kuwa cewa tayi "wai Inna ina Siddiqa ke zuwa ne haka idan tafita sai dare
take dawowa kuma ba'a sanin sanda take fita".

"Ina kuwa zata in ban da yar kasuwa, ai nan take zuwa taita tsokanar mutane sam
bata san zaman gida, karatun ma yanzu taki shi kwata kwata, babu muhammadiya babu
na zamani".

"Allah ya kyauta" khadija tace "amma wallahi Sam Siddiƙa batawa kanta adalci ba
saboda a wannan zamanin ilimi shine kan gaba".

Momy ce tace "ai gobe Daddyn ku zai zo inaga da ita zamu tafi, Hajiya saidai kiyi
haƙuri, tunda bazaki bimu ba, ko yar aiki sai a ɗauko miki, amma karatun Siddiƙa
yana da mutuƙar muhimmanci, idan ba abar ta tayi ba, to nan gaba bazata gode mana
ba, zata ɗauke mu a matsayin azzalumai ne".

jin jina kai Inna tayi alamar gamsuwa tace "Allah yasa haka shine mafi alkairi".

Umar ne yazo ya buga min ƙofa daga ciki nace "waye anan?".
"Umar ne".

buɗe masa nai ya shigo na maida ƙofar na rufe, kamar dai jiya, yau ma tambaya ta
yayi labarin abinda yafaru, na kuwa bashi labari harda haɗuwa ta da yaya Sadeeq,
yayi dariya sosai, amma yace min "yayi fushi tunda ban nemeshi ba sanda zan tafi".

Haƙuri nashiga basa da cewa "nima ban san zanyi nisa ba naje siyo alewa ne, shine
nabiya ta an, naje da kai gobe".

Yace "uhm abinda gobe Daddy zaizo kuma gida zamu tafi.

Ji nayi gabana ya faɗi, amma saina daure nace "da gaske gobe Daddy zai zo?". Umar
yace "eh wallahi nima a bakin Momy naji". Nace "to Allah ya kawo sa lafiya".

"Ameen" Umar ya faɗa

"ina yaya Sadeeq?". na tambayi Umar

Yace "ya ɗauki a bincin ki ya tafi ɗakin sa, kin san baida lafiya".

ban san sanda dariya ta ƙwace min ba, saboda na manta da abinda yafaru, sai yanzu
da Umar ke fa ɗin baida lafiya na tuna.

"wai lafiyarki. Aunty Siddiƙa?".

Nace ƙalau Umar wani abu na tuna, shiyasa kaga ina dariya".

"Muje tunda wancan mugun benan ko Indomie na girka don yunwa nike ji".

𝐻𝑖𝑚𝑚 𝑡𝑢𝑟𝑘𝑎 𝑡𝑢𝑟𝑘𝑎, 𝑘𝑢𝑑𝑎𝑖 𝑘𝑢𝑐𝑖 𝑔𝑎𝑏𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎𝑠𝑎𝑛 𝑐𝑒𝑤𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑒 𝑑𝑎𝑛𝑖, 𝑑𝑜𝑛 𝑗𝑖𝑛 𝑚𝑎𝑦𝑒 𝑧𝑎𝑖
𝑓 𝑎𝑟 𝑢 𝑖𝑑𝑎 n 𝐷𝑎𝑑𝑑𝑦 𝑦𝑎𝑧𝑜 𝑎 𝑘𝑤𝑎𝑖 𝑑𝑟𝑎𝑚𝑎 𝑎𝑔𝑎𝑏𝑎


NI DA YAYA SADEEQ


‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Chapter 08

Yanayin tsarin ginin gidan 2 bedroom ne, amma a ko wani ɗaki anyi kofar da mutum
zai iya bi ba sai yabi ta falo ba, sai ɗakuna biyu da suke a tsakar gida ɗayan na
hanyar waje shine ɗakin yah Sadeeq,sai wanda idan su Momy sun zo suke sauka a ciki,
a kwai kitchen a tsakar gidan da bayi,
Inna bata son amfani da kitchen din ɗaki tafi sabawa da na waje.

Amma ni nakan yi amfani dashi idan zanyi jagwal-gwalo na.

Kitchen ɗin na shiga na buɗe dirowar da nasan muna ajiye Indomie, na dauki guda
ɗaya. Gas na kunna ruwa na fara tafasawa, kana nazuba Indomie ɗin, sannan nakawo
tarugu 1 nasaka nazuba mangyaɗa a ciki ina cikin juyawa, sai ga Khadija taleƙo,
cikin zolaya tace "ga yaya Sadeeq can afalo, yace mai kwatar ki yau sai Allah, Inna
tayi bacci tun ɗazu, Momy kuma ta tafi ɗaki, daga ni sai Umar ne a falo.

Hantar ciki na ce tafara kaɗawa, jikina yafara rawa na kasa magana, bani da tsoro
amma ina tsoran haɗuwa ta da shi, saboda ba da wasa yake min ba, amma duk da haka
idan rashin kunya ta, ta tashi ina yimasa

A kiɗime nace "bari na fasa ihu tun kamin yacinmin kinga su Momy za suji su zosu zo
su cece ni".

Saka tafin hannaye na nayi na toshe kunnuwa na, saboda inyi ƙarar iya karfi na, zan
ƙwallara kenan tayi saurin toshe min baki da tafin hannun ta, tana ƙyalƙyala
dariya, Ta ce "naɗauka keɗin jaruma ce, a she ba haka bane, kamar ba kece shekaran
jiya kika cemin sai kin rama dukan da ya miki ba, taya zaki rama kina wannan
tsoran?".

Sai alokacin nasaki ajiyar zuciya, nabi ta da duka ta fita tana dariya.

koda na duba Indomie na har ta dawu ta fara kamawa, kashe gas nayi, anan kitchen na
zauna, a cikin tukunyar naci, inaci ina santi saboda tayi daɗi kuma nayi mata
irin dahuwar da nikeso.

Bayan na gama ci, na buɗe baki na sosai na saki wata uwar gyatsa babu ko alhamdu
lillah
Na miƙe tsaye nayi miƙa.

Ɗaki na wuce inda natar da Khadija na sharar baccin ta hankalin ta kwance, kan
gadon nima na hau kusa da ita na kwanta ina jina wani iri kamar wani abu zai faru
dani.

Washe gari ban farka da asuba ba sai Misalin 8:9am Khadija babu irin tashin da bata
yi min da asuba ba, akan nayi sallah amma naƙi, sai ma ƙara gyara kwanciya ta da
nayi, Kamar yadda nasaba tashi haka nayi babu ko addu'ar tashi daga bacci, na sauka
a kan gadon, brush na ɗauka, ina tatsa makilin ne Khadija ta shigo fiskarta ɗauke
da murmushi, da ganin bakin ta a kwai magana, "au ashe kin tashi daman ke nazo
tasa wallahi". Ta faɗa tana matsowa kusa da ni.

"Eh tashi na kenan, wai yanaga kina ta murmushi ne?".

Tace "ba dole ba Daddy fa yazo, shine ma yace na taso ki saboda ya tambaye ni kina
ina". Nace kina bacci".

"Amma wannan karon yazo dawuri gaskiya". Nafad ina ajiye makilin ɗin hannu na.

Tace "Eh naji yana cewa Inna da karfe 2:pm jirgin su da zai wuce lagos zai tashi
shiyasa yayi sammakon zuwa".

Jin jina kai na nayi, alamar gamsuwa "to bari nayi sallah" nace tare muka futo ta
nufi ɗakin hajiya Inna, ni kuma na nufi rijiya na janyo ruwa, na zuba a bokitin
wanka, na kai bayi saida na fara yin wanka sannan na ɗaura al'wala.

Tawul na ɗauro ajiki na, amma irin 'katon nan ne, kuma na wanke kaina babu ko ɗan
kwali haka na

Please Login or Register in order to submit comment