You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na had'a d'a
da uwa idan ba haka ba mai...".

"ke sake ta kafin na tashi na 'babballaki". Sadeeq ya fad'a yana nufo inda nike ni
kuwa bil ha'k'ki naushin Jiddah nike abaki yanzu haka na fasa mata yana zubar jini

"Kada ka sake ka buge ta zan 'bata maka rai saboda tayi min dai-dai tunda ba da ita
ake yi ba ta ara ta yafa yanzu Khadija da Ummi da basu sa baki ba ai ba ayi dasu
ba". Momy ce tayi wannan maganar zaiyi magana Daddy yace "nima ai tayi min dai-dai
saboda haka ko kallon banza ban yarda kayi mata ba".

Khadija dai bazan ce taji dad'i ba saboda ita bata san fitina kana kallon fuskar ta
kasan ba a yanayin jin dad'i take ba Ummi kuwa saboda farin ciki bakin ta ko rufuwa
bai yi har kai naushi take kamar ita ke dukan saboda ba wani shiri take yi da
Jiddahn ba kasan cewar ta ba 'yar Momy ba yar yayan Momy ce wato kanwar Naseer da
ke 'kasar India karatu tun sanda mamar su ta rasu ta dawo gurin Momyn da zama a
lokacin tana da 7 year's old kuma ita ma sa'ar su Siddeeqahn ce a ran ta tace "da
jiya na biyema Jiddah da da ni za a fara" soboda sanda ta shiga kitchen ta tarar da
ita tana hada tea bata tanka mata ba ta hau fad'ar magan ganu kamar yadda ta saba

Umar har yafi Khadija damuwa saboda shi harda guntun hawayen

A lokacin da ya 'kara so inda muke caraf ya d'auke ni daga kan Jiddah zai aje ni
Momy tace "a a kasan fad'an Siddeeqah baya 'karewa indai aka taba ta to sai ta rama
kaita sama cikin dakin ka idan Jiddahn ta haura sama sai Siddeeqahn ta sauko".

Ina ji ina gani yaya ya haura dani sama ba dan raina yaso ba dan ni da so samu ne a
bar ni da ita na koya mata hankali saboda tana da raini da jin kai ni kuma bana
jure wa dan ko babba ba 'karamin nauyin sa ni keji ba idan har yaga yayi min ban
rama ba

Kamar yadda Momy tace bai dire ni a ko ina ba sa a cikin falon sa ya maida kofar ya
rufe da dan mukulli sannan ya zare ya saka a cikin al'jihun sa ya nemi kujera 2
cter ya kwanta ya lumshe ido
Sosoi bakin Jiddah ke zubar jini tuni Daddy ya wuce ban garen sa saboda yadda
Jiddahn ke rusa ihu kamar wacce aka aikoma sa'kon mutuwa

Khadija dur 'kushe gaban Jiddah cikin tausaya mata take mata sannu kana daga bisani
tace "sannu Little sister zaki iya tashi mu tafi asbiti saboda aduba lafiyar ki?".

Bata gama rufe baki ba Momy ta kara so daga tsaye tace ai daman ance jiki magayi
gobe sai ki kara, ke kuma kin zo sai faman sannu kike mata ba ita tajawa kan ta ba?
Maza d'auko mayafin ki kije ki" cewa "driver ya tada mota saboda ku kaita ayi mata
dressing din bakin ta".

"Wallahi Momy ko da ita ce da laifi bazan iya jure kallon ta cikin wani hali ba na
kyale Siddeeka ne kawai saboda itama 'yar uwa ta ce amma baki ji yadda zuciya ta ke
mini ba a lokacin da abin ke faruwa".

"Ai fa nan dama ke ki ka fi auki wajen son yan uwan ki nasan ko kanki baki masa
san da kike musu abu ne mai kyau amma ina baki shawarar da ki rage saboda kada wata
rana ya za me miki matsala".

Idanun Khadija ya kawo 'kwalla ta dubi Momy tace "idan har kuna raye kuna ci gaba
da samin albarka bazanyi da na sani akan 'yan uwa ba ba insha Allah ".

"to Allah yasa". Momy ta bata amsa tana barin gurin

Duban Umar Khadija tayi tace "kaje ka cewa Idi driver ya tada mota sannan idan ka
dawo ka dakko mini gyale na dana Jiddah".

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨

˙·٠•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬٠·˙

Chapter 16

______"To" Umar ya fad'a yana mai mi'ke wa jikin sa babu 'kwari
Khadija sai sannu take ma Jiddah da bakin ta ya kumbura yayi suntum sai zubar jini
yake
Umar bai wani jima ba ya dawo "Aunty Khadeeja na fad'a masa bari na haura sama na
d'auko muku mayafin"
"To" Umar khadija ta fad'a tana rungume 'yar uwar ta a 'kirji
A haka Umar yadawo ya iske ta ya mi'ka mata ta ansa ta yafa sannan ta yafa ma
Jiddah "zaka bimu ne?". "Eh zani". "To muje ko". Tafad'a tana d'aga Jiddah daga
jikin ta "sannu sister daure ki tashi na kama ki sai mutafi asbiti ayi miki
dressing kada abinda kike rainawa yazama babba da 'kyar Jiddah ta iya kama hannun
Khadeeja tana waiyo waiyo ta samu ta mi'ke kallo d'aya zaka yi mata ta baka tausayi
saboda yadda bakin ta ya kumbura da taimakon Allah da na Khadija suka fito falon a
lokacin Idi driver ya tada mota Habu mai gadi ne ya hango su cikin sauri ya 'kara
so inda suke ya bud'a masu 'kofa yana yiwa Jiddah sannu Umar kuma ya zagaya ta
d'ayan bangaren ahankali Jiddah ta shiga khadija ta mara mata baya Habu mai gadi ya
wangyale musu get suka fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tsaye Siddeeqah take ri'ke da kugun ta sai zum 'bure zum 'buren baki take yi a
cikin ran ta take fad'in "kai kuwa matar ka ta bani ayi mutum dun kum ba za ayi
fira da shi ba sai kace wani boss kullum fuska daure" "ke mai ki ka ce ina wasa
dake?". Abinda Siddeeqah bata sani ba ba acikin zuciyar ta tayi maganar ba sarai
sadeeq yaji mai tafad'a

'ko'korin tashi yake yazo ya cim mata sai wayar sa ta shiga naiman dauki da kamar
bazai duba ba saboda wannan yarinyar ta 'bata masa rai amma sai wata zuciyar tace
"ya duba dai yaga wake neman sa". Haka kuwa akayi dauko wayar yayi daga kan hannun
kujera My Baby shine sunan da yake yawo akan screen din nan take ya saki murmushi
harda d'an cije leban sa na 'kasa ya gyara kwanciyar sa da kyau
Baki bud'e Siddeeqah ke kallon sa a tunanin ta aljanin sa ne ya motsa
Amma sai taga ya d'aga wayar ya kara a kunne baiyi magana ba daga can 'ban garan
aka ce
_"Amincin Allah ya tabbata a gare ka ina fatan wanda nafi so da kauna a duk duniya
ya wayi gari lafiya koda yike naji a jiki na kana cikin koshin lafiya saboda inajin
duk wani yanayi da ka ke ciki a jiki na_".

Sadeeq kusan suman kwance yayi saboda shi a rayuwar sa yana son kula wa musamman a
bangaren soyayya zai iya 'bata lokaci mai yawa wajen tsara kalaman soyayya saboda
shi a yadda yake gani idan bai ba ma soyayya hakkin ta ba bai more rayuwar sa ba

Bakin sa washe kamar tana ganin sa yace _"gimbiya sarautar mata ina fatan amincin
tare dake"_
"Na gode My". Jiya na gaji ban san sanda bacci ya dauke ni ba dan Allah kaya kuri
ban kira naji yadda ka iso gida ba".

"Kada ki damu baby Allah ya kare miki ni da kariyar sa na zo gida lafiya kema fatan
dana baro ki babu abinda ya taba min ke".

Zuby na dariya tace "kana nufin har na kai a bani irin wannan kulawar sai kace wata
gimbiya?".

"Haba ke kuwa ai kin wuce gimbiya a gurina ko kin mata da auren ki nike so nayi?
Nan da kika ganni akan abinda nike so bani da sakaci ina basa kulawa ta musamman".

Cikin kissa da kisi sina Zuby tace "yanayin muryan ka ya nuna min baka karya ba
kana jin yunwa".

Sai alokacin Sadeeq ya tuna ashe bai karya ba
Siddeeqah kuwa duk sona da gulma dole na kyale ta saboda na kasa fahimtar yanayin
ta har yanzun a tsaye take idon ta akan Sadeeq kyam shi kuwa bai san tana yi ba ya
tafi duniyar masoya

Ya cigaba da ce wa "wallahi Baby na manta".
"My kaman ta fa kace yanzu fa 12:00 gaskiya ka daina barin mun kanka da yunwa
saboda ba kan ka ke bari ba ni kake bari idan kuma kanason na cutu ai shikenan".

"Haba Baby na na daina insha Allah zan dunga kula miki da kaina kamar kina gani na
dazun ma har zan karya sai wasu 'kannai na suka kama rigama har sukayi doke doken
juna to shine duk naji raina babu dadi".

"Ayyah my sorry kasan sha'anin yara sai ana hakuri da su amma gaskiya ka tashi ka
je ka ci abinci idan ka gama bayan sallar azahar saika kirani mu daura daga inda
muka tsaya".

"To ranki shidade na gode da kulawa I love you". 💖
"I love you too"
"By"
"okay by take care for me".
zuwa yanzu Siddeeqah ta nemi guri ta zauna amma wannan karan ba shi take kallo ba
da yatsun hannun ta take wasa saboda yadda take jin ranta babu dadi.
Shi kuwa Sadeeq har cikin zuciyar sa ya manta da wata Siddeeqah a d'akin sa shiyasa
ya saki baki ya yi ta suru tu

Kallon sa tayi tace "yaya zanyi fitsari" banza yayi da ita kamar bai ji mai tace ba

Can da taga fitsarin zai iya zubo mata tace "yaya yafa matse ni zai zubo".

Sai a alokacin ya dago kai suka had'a ido sai yanzu ya tuna ashe tana d'akin nasa,
bai kula ta ba ya tashi ya shiga bedroom din sa bai jima ba ya fito hannun sa rike
da mukkullin mota ya nufi 'kofar fita batare da yace mata komi ba ganin haka tayi
sauri ta mike kafar ta a matse ta soma tafiya alokacin shi har ya bude kofar ya
fice

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Kwance take akan gadon da ake kwantar da marasa lafiya anyi mata dressing din bakin
ta kuma an sa mata ledar 'karin ruwa ga dukkan alamu ma batasan wa ke kanta ba
saboda allurar baccin da aka mata Khadija na gefe tayi tagumi Umar ma haka kowa da
abinda yake sakawa a cikin ransa

_Na gaji da typing amma idan har naga ruwan comments zan kara yi muku wani typing
din anjima_
🙏
✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨

˙·٠•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬٠·˙

Chapter 17

_____Ringing din wayar Khadija ne ya katse shirun nasu bayan ta fiddo wayar Sunan
Momy ya bayyana akan screen d'in wayar da han zari Khadija ta d'auka ta kara a
kunne tace "Aslm Momy". Daga can 'ban garen Momy ta amsawa Khadeeja da "W/slm
Khadija naji ku shiru ne shine nace bari na kira naji ya ake ciki". "wallahi Momy
lafiya lau anyi mata dressing din bakin ta ne sai karin ruwa da aka sa mata".
"sai yaushe kenan zaku dawo?".
"dazaran ruwan da ake 'kara mata ya 'kare saboda nurse d'in tace zamu iya tafiya ba
wani ciwo bane kawai buguwan da tayi ne, saboda ce mata nayi fad'uwa tayi abayi ta
bige".
"yayi kyau". Momy ta bawa Khadija amsa daga haka suka yi sallama

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Da bibbiyu Sadeeq yake tsallake steps soboda yana son yaje wurin cin abinci kafin a
kira sallar azahar kici'bus yayi da Momy a dai dai lokacin da ya gama sauko wa daga
steps din cikin sakin fuska Momy tace "ah Sadeeq ga fa abin karya wan ka can fuskar
ka tayi zuru zuru nasan kuma yunwa ce kake ji".

"eh wallahi Momy yanzu haka saurin da ki ka ga inayi restaurant zani".

Kafin Momy ta ba Sadeeq amsa Siddeeqah ta sauko daga sama d'an kwalin ta rike a
hannun ta tana susur kanta d'ayan hannun ta kuma rike take da bakin zanin ta daya
kwance tayi wani iri da ita yayanayin ta ya nuna alamar tana cikin damuwa

Kallon ta Momy tayi na wasu 'yan da'kiku bayan ta gama nazarin ta tace "Mai gaskiya
lafiyan ki ki kayi zuru zuru dake ko kema yunwar ce".
"wallahi Momy nima haka kawai naji ni wani iri ina Ummi take?".
"Ummi tana sama tun da kuka haura tabi bayan ku kin san ta da bacci idan babu
makaran ta tana can tana sana'ar".
D'an ta'ba baki nayi nace to ina Khadeeja?".
"ta raka Jiddah asbiti ayi mata dressing d'in gurin da taji ciwo".
"To Momy nima bari naje na huta".
"ba dai ki huta ba kije ki shirya Sadeeq ya kaiki gurin gyaran kai saboda jibi ne
tafiya makarantar ki in Allah ya kaimu".
Jiki na ne yayi sanyi ni wallahi da zasuji ta tawa su 'kyale ni na cigaba da rayuwa
ta a haka saboda banga aibin ta ba
"Maza mana kije ki shirya Siddeeqah tunanin me kike yi haka". Momy ta tambaye ni
"babu komai". na fad'a ina haurawa sama
Maida duban ta tayi ga Sadeeq da yayi kicin kicin da rai kamar wanda akece ga ranar
mutuwar sa "ba sai kaje restaurant ba ga kayan da mukayi breakfast can na hana
suwaiba ta kwashe kaje ka karya saboda ka kai Siddeeqah wajen gyaran gashi kanta
yayi wani iri".

"Haba Momy asa idi driver ya kai ta mana ni inada uzurin da zanyi". ya 'karasa
fad'a kamar zai rushe da kuka
Saida Momy ta 'kare mai kallo sannan tace "lallai Sadeeq kana da aiki tana matsayin
matar ka ace sai wani driver ya kai ta gurin gyaran gyashi to kai maye amfanin ka
da bazaka kula da iyalin ka ba?".
Yana sosa 'keye ya ce "uhm Momy baza ki gane bane amma wallahi ba wani son yarinyar
nike ba kawai dai zan hakura ne saboda nayi muku biyayya".
Tabe baki Momy tayi kana tace "ina tausayin ka Sadeeq amma kaje kayi duniya ce"
Ba tare da yaji komai aran sa ba ya nufi dinning tebur
Momy ma d'akin ta wuce abin ta saboda Daddy yana gida

Zuciyar Sadeeq a cun kushe ya bud'e kular farfesun hanta ya zuba a filet kana yaja
kujera ya zauna ya d'auki cokali ya fara cin farfesun amma sai yaji kamar yana cin
magani saboda magan ganun da Momy tayi masa basu yi masa dadi ba saboda haka ya bar
cin abincin ya ciro wayar sa yad'an shafa screen d'in wayar ya danna number Farooq
saida Wayan ta fara ringing sanan ya kara a kunne ringing d'in farko Farooq d'in ya
daga yace "officer officer". Muyan Sadeeq a murtuke yace "kayi maganar makarantar
yarinyar nan kuwa?".
"d'an iska wai saurin me kake yi haka yaushe garin ya waye".
Sadeeq na jin amsar da Farooq ya bashi yayi saurin katse kiran yana Jan wani dogon
tsaki "mtssss".
Adai dai lokacin Siddeeqah ta sauko daga sama tayi fes da ita sanye take cikin
shigar doguwar riga 'yar dubai mai ruwan hanta ta yafe kanta da mayafin rigar duk
da ba kwalliya tayi ba amma tayi kyau abinka da farar mace mai siririyar fuskar da
ke d'auke da dogon hanci gaskiya tayi kyau ko ma'kiyi dole yace masha Allah saboda
kama take da larabawa

Gaban sa ta tsaya tace "yaya na shirya". Wani mugun kallo ya watsa mata gami da
cewa "dan uban ki ni sa'an ki ne zaki 'bace min dagani ko saina tashi na yi ball da
ke". Kafin Siddeeqah tayi wani yun 'kuri Momy ta fito daga part din ta. Tana
Murmushi ta 'karso gurin Siddeeqah ta kama hannun ta ta kalli fiskar ta tayi fayau
da ita masha Allah "gaskiya irin wannan kyau haka kamar zaki gasar kyau". Rufe
fuskar ta tayi da d'anyan hannun ta ce "Allah Momy banyi kyau ba ko hoda da kwalli
ban shafa ba".
"ai gwara da kika bar fuskar ki ahaka sai ainihin kyanki ya dad'a fitowa masha
Allah".
Tana Murmushi tace "Momy da gaske ina da kyau?".
"wata ta ta'ba kiran ki da mummuna ne?".
Waiga wa tayi inda yaya Sadeeq yake suka had'a ido ya balla mata harara Momy na
lura dasu idan ta fahimci Siddeeqah Sadeeq ne ke ce mata mummuna. Kafadar Siddeeqah
ta dafa tace "rabu dashi mai sunan manya kinfi shi kyau nesa ba kusa ba kishi yake
dake amma ko makaho ya shafa yasan kin fita daban kama da larabawa kike yi wallahi
da za a kwana yana fad'a ma wani ke hausa fulani ce bazai yadda ba har sai kinyi
magana yaji muryan ki".
Murmushi ne kwance akan fiskar Siddeeqah tace "Allah yabar mana ke Momyn mu ta bata
fek kiss a kumatu".
Kallan sa Momy tayi tace "tashi mana Sadeeq ka kai ta ta shirya kai take jira".
Kamar zaiyi kuka ya ce "yanzu sai a ganni da wannan abar rigi rigi zan kaita gurin
gyaran gashi ai abin kunya ne".
Momy na dariya tace "Sadeeq kenan wani lokaci idan kayi wani abu kamar sai ka dawo
kamar karamin yaro Siddeeqah ce zaka ce wannar abar? Allah ya shirya ka amma aga ni
na ganin ka tare da ita zai 'kara maka girma saboda iyalin ka ce".

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨

˙·٠•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬٠·˙

Chapter 18

______"haba Momy 'yar wannan abar ce zan fita da ita a matsayin iyali na?".
"Eh Ita d'in fa wallahi Sadeeq ka kiyaye ni ka raina ni ko? Duk abinda nike fad'a
maka abanza nike fad'i saboda baka d'auka".
"Momy dan Allah kiyakuri na daina ki ce mata ta wuce mu tafi".
"Au bakin ka ciwo yake da bazaka fad'a mata ba kai? Ko kafi 'karfi ne? Sadeeq ina
raba ka da kiwan kyalla kana shige wa kyallah ta haihu". Momy ta fad'i haka cikin
dakiya da tsitstsire sa da ido
Kame kame ya fara

Siddeeqah da taji haka tace "Momy sai mun dawo".

"to adawo lafiya 'yar albarka".

Harabar gidan ta fito taja ta d'an tsaya kamin yayan nata ya fito su wuce,

adai dai lokacin mlm Habu ya wangele get motar su Jiddah ta silalo ciki idi driver
ya samu guri yayi faking kana ya fito ya bude musu murfin motar Khadeeja ce ta fara
fitowa sai Umar ya fito saida Khadeeja ta zura kan ta da hannayen ta a cikin motar
ta kamo Jiddah da kyar Jiddahn ta iya fito wa tana cicci za le'be saboda yadda take
cin zuciyar ta na mata daci da radadi akan dukan da Siddeeqah ta mata ita kadai
tasan kalan tana jin cin mutuncin da tayiwa Siddeeqah

kallo daya Siddeeqah ta musu ta kawar da kan ta gefe tana dariya ciki ciki saboda
yadda taga bakin Jiddah ya yi sun tumeme
Sadeeq ne ya fito shima ganin Siddeeqah na dariya ita kad'ai abin ya bashi mamaki
yana shirin daka mata tsawa sai ya hangi Khadija rike da hannunan Jiddah Umar na
biye da su suna taho wa
Kallo na yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya yi gaba abin sa cikin sauri
nima na mara masa baya ba tare da na lura ba naji na ci karo da mutum a tsorace na
ja da baya ina yarfe hannu na, ganin Jiddah ce na bige "mttsssss" na ja wani dogon
tsaki naga sanda Khadija ta yi mata magana da alamar dai mantuwa tayi a mota saboda
naga cikin motar ta koma Idan jidda yayi 'kwala 'kwala murayan ta na rawa tace
"wallahi zaki san kin ta'ba ni yarinya zan nuna miki kalar nawa rashin mutuncin
banziya d'iyar shegu ke idan....".
"Tas tas". shine 'karan marin da Sadeeq ya wanke Jiddah da shi yana wuci yace "kada
na kara jin kin ce mata shegiya duk lalacewar naka naka ne saboda hannun ka bai
ru'bewa ka yan ke ka wurgar ita d'in jinjin ki ce nasan kin San da haka. 'bace min
dagani kafin na 'ba'b'ballaki".

Jiddah kusan suman tsaye tayi saboda yadda taji saukar marin batayi zata ba lura
Sadeeq yayi da Jiddahn bata cikin hayyacin ta d'an ta'be baki yayi ala mun ko a
jinkin sa, kana ya kallo ni nayi sauri nayi 'kasa da kai na zaki wuce mu tafi ko
sai na had'a dake munafuka kidinga yin abu sumi sumi to ki kaddara aure na dake...
".

Bai 'karasa maganar ba kira ya shigo a wayar sa laluba aljihun sa yayi ya fiddo
batare da ya kalli sunan mai kiran sa ba yayi picking call d'in gami da karawa a
kunnen sa sannan yayafito ni da hannu ya yi gaba. Sai a lokacin Khadeeja ta iso
kallo na take yi nima da kallon na bita yaya Sadeeq har ya shiga mota nima bu'de
gidan baya nayi na shiga na zauna sai Sadeeq d'in ya waigo fuskar sa a murtuke yace
"ke uban waye diraiban ki zaki dawo gaba ki zauna ko saina miki tsinannan duka".
"uhm" ta fad'a kana ta dawo gaban motar. Habu mai gadi ya buɗe masa get ya fice
daga gidan

Khadija na taba Jiddah tayi luuuuu zata zube a 'kasa cikin hanzari Khadeeja ta mai
do ta kirjin ta ta run gume ta mamaki kwance akan fuskar Umar yace "wai aunty
Khadija mai yasa meta ni ma yan zu na dawo kina tafiya nima naje gurin Habu mai
gadi". Cikin kuka Khadija tace "Umar wannan wace kalar rayuwa ce daga wannan sai
wannan gaskiya ni na gaji Zan roki Daddy ya barni na koma kaduna da zama wallahi
bana son tashin hankali, nasan ita da Siddeeqah ne ko yaya tunda ina zuwa suka bar
gurin". Ta 'karasa fad'a tana rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Tana kokarin kama Jiddah sai ga Daddy ya fito da alamar masallaci zai je soboda
ankira sallar Azahar, hannun sa d'auke da gorar ruwa ta faro, hango 'ya'yan sa daya
yi cikin wani hali yasa shi karasa wa gurin su da sauri

Allah sarki mahaifan mu ko mai zamuyi musu bazamu taba biyan su ba saidai muyi
musu adduar Allah ya yafe musu yayi musu sakaiya da gidan aljanna fiddausi 🙏

"Khadija mai yasa meta ne haka na gan ku cikin tashin hankali". Daddy ya tamabaye
ta

Murayan Khadeeja na rawa cikin kuka tace "Daddy wallahi nima ban sani ba bayan mun
dawo daga asbiti shine na barta anan na koma mota saboda na manta magun gunan da
aka bamu nan dai Khadija ta kwashe labarin abin da ta sani ta fad'awa Daddy gorar
ruwar hanun sa ya bude murfin ta ya zuba rawa a tafin hannun sa ya watsa wa Jiddah
a fuskar ta nan take taja dogon numfashi ta sauke 'kirjin ta na bugawa da sauri da
sauri kara rungume 'yar uwar ta tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin ta farfado
yasa daddy cewa "ku shiga daga ciki Umar zo mu tafi masallaci". "To Daddy".

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Aban garen Sadeeq kuwa wani 'katon plaza ya kai ni mai kyau da tsari bakin
Siddeeqah a sake take kallon gurin saboda ita tun da take bata ta'ba ganin kasuwa
mai kyau irin wannan ba badan taga basuyi tafiya mai nisa ba da sai tace kasar ya
bari da ita yana gaba tana bin sa a baya har suka isa daidai bakin wani 'katon
shago mai dauke da kofar gilas tafke ke irin wacce na ciki yake ganin na waje amma
shi na waje baya ganin na ciki

Wani abun Sadeeq ya danna a jikin bangon shagon can sai ga wata mata ta fito da
ganin ta ba bahaushiya bace saboda a kwai 'karin gashi a kanta kuma babu mayafi a
jikin ta rigar ta irin mara hanu ce sai wani d'an gajeren siket da take sanya dashi
da turan ci Sadeeq yayi mata magana itama ta mayar masa bayan sun gama naga ya ciro
kudade masu yawa ya mika mata ta amsa tana godiya yace "bita mana kika saki baki da
hanci kina kollo na kamar yau kika taba gani na".

Bayan sun shiga daga ciki Siddeeqah ta ga Mata a zazzaune akan kujeru masu kyau da
burge wa wasu kuma an saka musu kan su a cikin wani inji yana kara wuuuu haka dai
Siddeeqah tai tabin gurin da kallo kamin ta zauna a kan wata kujera da babu kowa a
kusa da ita tsoro ne fal a cikin ranta saboda yadda taga ana sa mutum cikin inji
gaskiya ita baza ta yarda a sata ba aje a fille mata kai ana zaune 'kalau da ido
matan gurin suke kallon ta ganin ta suke kamar balarabiya wata a cikin su ce tayi
karambani tace "sannu baiwar Allah".
Kallon ta Siddeeqah tayi sai taga babbar maca ce saboda a kalla zata kai shekara 30
a duniya
Adan dakile tace "yauwa sannu Aunty". Saida gaba daya matan gurin suka kalli junan
su saboda yadda suka ji muryan ta sanyi ga dadi haruffa suna fita dai dai kamar
koyan hausar tayi masha Allah

Saida aka gama ma wasu mata sannan layi yazo kaina mai saloon din ta dube ni
"kanwar oga taso ki zo layi yazo kanki".
A tsorace Siddeeqah ta tashi tace "amma ni dan Allah kada ku sani a cikin wancen
injin ku wanke mun kaina kawai haka".

"To bazamu saki ba tashi muje" mai saloon tace

Bayan wasu mintocin da basu haura talatin ba saiga shi Siddeeqah ta fito das da ita
an gyara mata kanta har kyalli yake bayan kamshin da yake tashi asalin kyanta ya
kara baiyayana masha Allah a gaban katon madubi ta saya tana kallon yadda aka gyara
mata gashin duk tsayin sa da cikar sa anmayar dashi guri daya anyi mata faking a
tsikayar kai sai shafa kan take tana mur mushi saboda ita kanta tasan tayi kyau.
Mai kula da gurin ce tazo tace "kan war oga ya dawo yace kizo ku tafi".
"to". Na ce na yafa mayafi na ta zuge min glass na futo

A jikin motar sa na hango sa hannayen sa dore akan kirjin sa ya zuba min idanu
kamar wani maye😅 da ni ke kallon sa haka da yace

Please Login or Register in order to submit comment