You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito daga cikin bayin.

Adai-dai lokacin yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, haɗa ido mukayi, saida ya ƙare
min kallo tsaf, sannan yaja dogon tsaki, shasha ya faɗa afili, kana ya wuce ya
shiga ciki.

Saida ya wuce sannan nima na wuce ɗaki, wata doguwar rigar atamfa na ciro mai
launin blue da ruwan hoda, baseline na shafa, sannan na saka atamfar, na ɗauki
hijabi na nasaka na gabatar da sallar asuba, bayan na idar na nufi falon hajiya,
ina jin gabana yana faɗuwa, narasa mai yisa amma tun jiya da Umar yace "Daddy zai
zo" gaba na ke faɗuwa, amman yanzu bugun zuciyar tawa yafi tsanan ta.

Daurewa nayi na kutsa kaina cikin falon baki na ɗauke da sallama, kowa ya hallara,
suna karyawa, Daddy da Inna da yaya Sadeeq a kwano ɗaya suna cin ɗan wake, Khadija
Momy Umar. Kuma waina suke ci.

Daddy ne ya dube ni yace "wa'alaikum'ssalamu ɗiya ta shigo ga wuri ki zauna, ya
nuna min tsakanin sa da na yaya Sadeeq, ƙarasawa nai na zauna, kana nace"ina kwana
Daddy".

"Lafiya lau".

"na same ku lafiya?".

"lafiya lau Daddy, ya hanya?".

"Al'hamdu lillah ". yace min, yana mi'ko min cokali yace "bimismilah
me sunan manya".

Ina lura da yanayin yah Sadeeq ya canza tun sanda na zauna, ya wani ɗaure fiska sai
mutsu mutsu yake yi, ina saka cokali na cikin kwanan yana cire nasa yamiƙe tsaye,
Daddy ne yakalle sa, yace masa "ya-ya ana cin abinci ka tashi?". Na ƙoshi ne
Daddy".

"Dawo ka zauna sai mun cinye da kai".

Badan ran Sadeeq yaso ba, haka ya dawo ya zauna ya maida cokalin sa, ina lura da
yadda yake cin ɗan waken kamar yana cin magani.

Misalin karfe goma 10:00am Daddy zaune a kan kujera Inna na kusa da shi Momy na 2
cter, ni da Khadija na zaune a ƙasa kusa da ƙafar Momy, yah Sadeeq kuma na gefen
Daddy zaune a ƙasa, kanshi a ƙasa yana danna wayar sa.

Daddy ne yai gyaran murya, kana yafara da cewa "da farko ina mai ƙara jad-dada
godiya ta ga Allah ma ɗaukakin sarki da yabin damar aiwatar da wannan ƙudirin nawa,
tsira da aminci ya tabbata ga fiyayyen halitta annabin mu Muhammad (S. A. W).
Bakomai ne yasa na taraku anan ba, saidan ke Siddiƙa me sunan manya, ya faɗa yana
nuna ni, ina san yau ɗin nan na ai'watar da ƙudirin mahaifiyar ki akan ki,
Ina fatan zaki yimana biyayya, nasan baki da matsala, saboda mun isa dake ne zamuyi
abinda mukesan yi yanzu, ina so kisan bakida Wanda ya fimu a kaf faɗin duniya,
bazamu taɓa cutar da ke ba".

Tun da Daddy ya fara magana gaba na ke faɗuwa, shin wani kalan ƙudiri ne wannan da
har Daddy ya ambace sa da ƙudirin mahaifiya ta?". Banida wannan amsar saboda haka
nacigaba da sauraran abinda Daddy ya cigaba da faɗa.

Daddy ya cigaba da cewa "naso ace sauran 'yan uwanku sunanan, amma duk da haka kuma
kun isa shaida, kuma akwai abokai na guda biyu wa'inda tare dasu zamu tafi lagos,
nayi magana dasu, saboda muhimmancin abinda zan tattauna daku zasu biyo tanan".
Kallon Hajiya Inna yayi yace "Hajiya ko akwai abinda ki ke san faɗa".

Tace "eh ina da abin faɗa". yace "to muna saura ranki".

Tace "Ƙarami". Haka Inna ke kiran Daddy da Ƙarami "ni abinda ke damu na yadda,
Garba ya tsani yarinyar nan , kamar ba ƙanwar sa ba, Kaf ƙauyen nan babu wanda bai
san da zaman ƙiyayyar da Garba yaiwa yarinyar nan ba, a gaban kowa nunawa yake, a
waje bai sarara mata ba, haka a gida, motsi kaɗan tayi sai duka".

Wani gwauran numfashi Daddy ya sauke, sannan ya fara yiwa Yaya Sadeeq faɗa, ta inda
yake shiga ba tanan yake fita ba, sosai Daddy yayi wa yaya Sadeeq fata fata.

Kana ya maida kallan sa ga Momy yace "Aisha fa kina da abin da zaki ce".

murmushi tayi irin na su na manya tace "ai kai da Hajiya kun gama faɗan duk abinda
zan faɗa, sai dai aƙara yiwa sadeeq faɗa a kuma ja mai kunne, sai muyi musa fatan
Allah yasa alkairi".

"Ameeen" Inna tace yayin da Daddy yace "alhamdu lillah".

Daddy yace "mai sunan manya matso nan kusa dani kinji". Jikina a sanyaye na matsa
kusa na zauna a ɗayan bangaren da ke kallon Sadeeq, sai bankamin harara yake a
sace, nayi kamar bansan yanayi ba.

Dafa kaina Daddy yayi yace "Allah yayi miki albarka". "ameen". Nace

Sannan ya cigaba da cewa "𝚂𝚒𝚍𝚍𝚒'𝚔𝚊 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚢𝚊𝚞 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒 𝚂𝚊𝚍𝚎𝚎𝚚 𝚣𝚊𝚒 𝚝𝚊𝚜𝚑𝚒 𝚍𝚊𝚐𝚊
𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒𝚗 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒 𝚣𝚊𝚒 𝚔𝚘𝚖𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒 𝚋𝚞𝚢𝚞, 𝚣𝚊𝚒 𝚍𝚞𝚗𝚐𝚊 𝚊𝚖𝚜𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚢𝚒𝚗 𝚖𝚒𝚓𝚒𝚗 𝚔𝚒 𝚍𝚊
𝚔𝚞𝚖𝚊 𝚢𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚔𝚒".

Wata muguwar faɗuwar gaba ne ya ziyarceni, a take naji na fara kyarma, jiki na sai
bari yake,
a tare nida shi muka miƙe tsaye, duk kannin mu idan mu a waje alamar rashin fahim
ta.

" Koma ku zauna" Daddy ya faɗa, jikin mu babu ƙwari haka muka koma muka zauna,
Khadija ma dake zaune mamaki ne yacika ta shiko Umar ko ajikin sa Inna kuwa da momy
daman sun san da batun.

"ƙwarai kuwa abinda kukaji nafaɗa hakane ba mafarki kuke yiba, domin wannan shine
burin ƙanwata Aminatu". 'Kwalla ce ta cika idonun sa yayin da ya kasa ƙarasa
maganar Handkerchief yaciro cikin aljihun sa yana share ƙwalla.

Da irin murayan Wanda yake son yayi kuka, Daddy ya cigaba da cewa "auren ki da
Sadeeq shine burin ta, bamu sani ba ko a raye take ko amace, kimanin shekaru goma
sha biyu da wasu yan wattani kenan, tun tana goyen ki". ya nunani "nasan kunsan
komai ba sai na ƙara tada muku da zancen ba, saboda bana son tada mana hankula".

tuni inna tafara shash-sheƙar kuka momy na faman bata haƙuri, da ƙyar dai aka shawo
kan ta tayi shuru.

Da gaske duka family an san labarin ɓatar mahaifiya ta, amma bamu san yadda
al'amarin ya faru ba

Daddy yacigaba da faɗin sai dai kiyi haƙuri, naje har gidan ku da ƙyar nasamu
ganin mahaifin ki, na je masa da batun auren ki, yace min shi babu ruwan sa yama
manta dake cikin 'ya 'yan sa, ba tun yauba ai ya faɗa mana ya bar mana ke, idan
yankaki zamu yi muyi, shi baya da matsala babu ruwan sa, ya 'kara da cewa ai tun
ranar da Amina tabar gidan nan na manta da duk wani abu daya shafeta, yanzu haka
abinda yasa bazan sa karnuka su fidda min kaiba saboda baka sani ba, amma yanzu
tunda kasani kada inƙara ganin ka akoafar gidan a, kai ba kai ba ko Siddiƙa ɗiyata
ce tazo sai nasa karnuka sunyi yaga yaga da naman jikinta, saboda haka Get out in
my house".

jiki na babu ƙwari Siddiƙa haka na fito daka gidan ku.

Ban taɓa jin tsanar mahaifina irin na yauba kuka nike sosai ina tir da halayen sa,
kowa a ɗakin jikin sa yayi sanyi dady ne ke shafa min kai yana bani hakuri

"Siddiƙa ki cigaba da haƙuri Allah zai miki canji da mafi alkairi, ki cigaba da kai
kukan ki gurin Allah saboda shi Allah baya barin zalinci, Kuma kamar yadda nace yau
za a ɗaura miki aure da sadeeq idan anyi sallar juma'a babu fashi".

SADEEQ ne zaiyi magana Daddy ya katse sa da faɗin "zan saɓa maka sadeeq, Ko na
tambaye ka ne?".

bazan iya musawa su Daddy ba, amma shin meye aure nashiga uku na, yayin da nike jin
bugun zuciya ta yana dad'a 'karuwa.

‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Page 09

Na shiga uku ni Siddiƙa Yahya ɗan ƙwambo, anya su Daddy suna ƙauna ta? nasan kaf
duniya babu wacce Sadeeq ya tsana kamar ni, amman wai yau ni ce zan zama matarshi.

"Kutashi kutafi Allah yayi muku albarka". Daddy ya faɗa.

Sadeeq yariga ni tashi, saboda ni duk jikina ya mutu babu kwari.

"ji mana Sadeeq, ka kira abokanan ka na kusa a waya ka shaida musu".

Murya acan cikin maƙogaro Sadeeq ya cewa Daddy "ba sai sun shaida ba". Yana gama
faɗar haka ya fice fuu.

A masallacin juma'an dake garin buruku aka ɗaura auran *SADEEQ ALIYU MAI GORO* da
amaryar sa *SIDDIƘA YAHYA ƊAN KWANBO* ɗumbin taron Al'umma sun shaida ɗaurin auren
duk da kasan cewar babu ango da abokanan sa, Daddy ne yayi wakilcin Siddiƙa, inda
ɗaya daga cikin abokan Daddy da suka hallar ci taron, mai suna Alhaji Imran yayi
wakilcin Sadeeq, auren da aka ɗaura abisa sadaki dubu tamanin, lakadan ba ajalan
ba, yayin da Alhaji Imran ne ya biya sadakin.

A kwai 'yan ƙauyen Dande da dama, da suka samu halartar zuwa masallacin, saboda su
gabatar da sallar juma'a, da yawan su mamaki suke saboda kowa yasan tsamar dake
tsakanin Sadeeq da Siddy amma wai yau ya zama mijin ta, ko dashike daman ance idan
zakayi ƙiyayya kada ka tsanan ta haka ma soyayyar, da haka taro ya watse koda Daddy
ya dawo gida annemi Sadeeq anra sa kuma an kira wayar sa a kashe.

Siddi'ka kuwa tun sanda ta shiga ɗaki take raira kuka, rarrashin duniya anyi mata
amma taƙi barin kukan kamar ma daɗa zuga ta suke yi, haka suka gaji da lallashin ta
suka zuba mata ido, saida Daddy ya faɗawa su Inna zai shigo dasu Alhaji Imran
Sannan yaje ya shigo dasu, a falon Hajiya Inna suka zauna daman su Hajiya Inna sun
girka shinkafa da miya Khadija ce keta hidama da baƙin Daddy Sai da suka ci suka
sha sannan Inna tazo suka gaisa, gami da yi mata Allah ya sanya alkairi, anan Daddy
yayi mata sallama yace su zasu wuce Abuja dan a can jirgin su zai tashi zuwa lagos.

"To bari na kira maka Aisha ɗin ko". Inna ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.
cikin sosa kai Daddy yace "ai na riga na sallame su, suma nan bada jimawa ba zasu
wuce" mamaki ne yakama Inna saboda ita dai bataga sanda ƙarami yayi magana da Aisha
ba, Hajiya Dady ya kira sunan ta "da mai sunan manya zasu tafi nayi maganar yar
aikin za a nemu miki nanda kwana biyu".

"Wace yar aiki! ƙarami duk yaran dake cikin ƙauyen Dande basu isa ba har sai an
nemo wata, ai ko Ladiyo ƙawar Siddiƙa na yiwa iyayen ta magana tunda yarinyar ta
iya aiki, bata da ƙinji irin na Siddeqan baza su ki ba, sai ta dunga zuwa tana
tayani ɗan wanke wanke da shara tama dunga ɗebe min kewar siddy ɗin, sai idan wata
ya kare ka dunga yi mata ɗan ihsani".

"babu damuwa" Daddy yace yana mai ciro kuɗi daga aljihun sa masu tarin yawa, 'yan
dubu dubu ya miƙa mata

"ƙarami kuɗin nan sunyi yawa, na wancen watan ma daka bani suna nan ban taba suba
saboda duk abinda nike so akwai a gidan, da ka barshi kawai a gurin ka Allah yama
albarka".

Hannun ta Daddy ya kamo yasa ka yan bandir ɗin 1000 guda biyu "haba hajiya ki karba
koda sadaka ne kinayi dasu idan ki ka ga mai buka ta".

Albarka taita sanya mai, tanayi mai addu'ar Allah yatsare, ya kare,

"Ina mai sunan manyan take ne Hajiya?". Daddy ya tambaya

"Ai tun sanda ka fita ta shiga ɗaki tana ta faman rusa kuka, gajiya mukai da
lallashi muka kyale ta".

"Wani ɗakin?".

"Na can karshe". Ta bashi amsa

Tashi yayi ya cewa abokan sa "minti biyar".

A kan gado ya same ni kwance nayi rufda ciki.

Siddiƙa Daddy ya kira suna na cikin dakusashshiyar murya, na amsa da "na'am Daddy
".

"Inaso kisan duk abinda haƙuri bai ba bawa ba a rayuwa ba, to rashin sa ma ba zai
ba da ba, kuma wannan shine burin mahaifiyar ki tin sanda aka haife ki tace "idan
Allah ya raya ki ɗan ta Sadeeq shine mijin ki ko bayan baran ta mu cika burin ta, A
halin yanzu bamu san awani hali Amina maman ki take ciki ba, zai iya yuyuwa tana
nan a raye nesa damu, zai kuma iya yuyuwa Allah ya ɗauki ranta, amma muna nan muna
addu'a idan har Amina tana a raye Allah ya bayyana mana ita, nayi hakanne a yanzu
saboda bani da tabbacin zan ƙara wasu shekarun nan gaba, nasan ko bayan babu raina
na cikawa kanwa ta burin ta za tayi alfahari dani, kiyi mana biyayya amatsayin mu
na iyayen ki bazamu taba cutar da ke ba zakiga ribar abun nan gaba".

Duk maganar da Daddy yayi na kasa ɗago kaina, Ko motsin kirki na kasa ina nan a
yadda ya shigo ya sameni, shirun da naji ne, yasa naji ajiki na ya fita daga ɗakin,
kaina na ɗago ina ƙarewa ɗakin kallo Bansan mai nike nazari ba amma inajin kamar
raina zai fita.

Umar ne yashigo hannun sa ɗauke da kular abinci har kan gadon ya hau yace "aunty
Siddy please kada kicemin a a don soyayyar da kikewa goggo Amina ki tashi kici
abincin nan, nasan dai kina mutuƙar santa kuma duk 'yar da aka ce tayi abu dan iya
yen ta to indai tana son su za tayi".
Jin Umar ya ambaci mahaifiya ta na tashi zaune, saboda babu 'yar da zataƙi mamar ta
" to mi ƙomin kular". Na faɗa murya a can ciki.

Koda na buɗe shinkafa ce da miya har da nama a ciki, cokali nasa na fara cin
abincin amma kwata kwata banjin daɗin shi, hasali ma ji nike kamar ina cin magani.

"Umar wai haka abincin nan yake". Na tambaye sa

"Me yayi?"

"Naga kan infara ci yana ta zuba ƙamshi, yanzu kuma da nike ci wallahi ji nayi
kamar inacin magani".

Kallo na yai cikin ido yace "aunty siddy inaga bakin ki ne domin kowa ya yaba
girkin nan yadda yake da kamshi haka yake da daɗi abaki ma".

"To iya magana". Na faɗa ina tura masa kular abincin.

"Kaddai har kin ƙoshi?". Yace yana kallo na

"Na ƙoshi mana tashi kasamomin ruwa".

"To" yace ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai gashi da ruwa a cup

yace "Momy" tace "kiyi wanka yanzu gata nan zuwa".

"To". nace

dama akwai bayi a ɗakin, amma tsabar neman rigama yasa bana shiga, kuma da sabo dan
munriga munsa ba da bayin tsakar gida tun kafin a maida mana gidan mu ginin zamani.

Yaukam ciki na shiga wanda nike tsokanar ko sunan sa ma bana son inji ankira min.

Ban wani daɗe ba a wankan na fito, kaya na tarar abakin gadon da alamar sababbi ne
harda bra da fnt.

Ina cikin mamaki saiga Khadija ta shigo fes da ita cikin wata tsaleliyar atamfa
"cikin zolaya tace min amarsu har yanzu baki shirya ba Koda yake daman shirin amare
ance yana da daɗe wa, sai kiyi kishir ya dan ke kaɗai muke jira".

a kwati na na nufa saboda na ɗauko kayan da zan saka,

da mamaki Khadija tace "Siddiƙa baga kayan ki nan ba akan gado, da Momy tace su
zaki saka".

Hau shin kowa nake ji cikin masifa nace wa Khadija "naji to sai ki ban guri".

Sai da ta ƙyalƙyale da dariya kana tace "haba amaryar mu naji ance, ba'a san a
ɓatawa amarya rai, musamman ranar ɗaurin auren ta, dan haka na barki lafiya, idan
ni baki buɗe min ba zaki buɗe ma yayana".

Khadija tagirme ni da 2 years nasan ba zata rasa sanin abinda ainihin aure ya ƙunsa
ba, tunda ita abirni take kuma tana zuwa makaran ta, saɓanin ni da nike yawan gaɗa
a dan dali.

Tana fita na rufo ƙofar, shirya nai tsaf, sannan na zauna a bakin gado, ina ta
zubaba ƙamshi, da alamar kan a kawo kayan sai da aka feshesu da turaruka masu ɗan
banzan ƙamshi da tsada.
buga ƙofar naji a nayi koda na buɗe Umar ne hannun sa ɗauke da jaka da takalmi da
gyale, "ungo ki sanya, Momy tace idan shirya ki fito mu tafi".

Karɓa nayi takalmin irin mai tsinin nan ne, Allah na gani ban iya tafiya da shi ba,
amma hakan nan na sanya, jakar tanada yar girma kalar dai ta amare,a kafaɗa na
rataya ta, gyalan ko ahannu na riƙe sa, saboda ban saba sawa ba, ai kuwa na soma
tafiya.

Umar sai dariya yake min wai ahannu zan rike jakar, ba ratayawa zanyi ba, ko takan
sa banbi na, danni yanzu haushin kowa nike ji.

A gaskiya ina son kwalliya a rayuwa ta, tafiya nike ina taku ɗaiɗai, duk da ban iya
tafiya da takalmin ba zuwa zuwa ina turguɗewa Amman hakan bai hana ni yin yanga ba.

Afalo nasami su Momy duk sun shirya

"Momy wai ina zamu haka?". Na faɗi haka sanda nike zama kusa da Inna.

"Abuja". Momy ta bani amsa

Zaro ido na nayi nace "Abuja kuma Momy shine zaku tafi da ni?".

"Eh" kawai tace min narai-narai nayi da ido, take ƙwalla ta fara zubo min, abinka
da mai neman kuka, dama koda nai wanka banyi kwalliya ba ko hoda ma ban shafa ba,
saboda haka na cigaba da raira kuka na ina share ƙwallar da bayan hannu na.

Inna ce ta kama hannu na tana matsar kwalla, ba tare da tace min komai ba

Cikin kuka nace "Inna kada kibari atafi dani mana, Inna idan na rabu da ke mutuwa
zanyi, nayi matuƙar sabo da ke, bazan iya rabuwa dake ba nasan wannan tafiyar ba
irin wacce na saba yi bane saboda haka jiki na ke bani, nidai gaskiya bazan je ba".

Cikin sanyin murya Inna tace "to ba gasu Khadija ba acan kuma akwai su bilkeesu
baki da damuwa zaki saba kuma duka 'yan uwan ki ne, inaso na inganta miki rayuwa
ne". saboda 'Karami yace min idan ban bar ki kinyi karatu ba nan gaba dani zakiyi
kuka".

Ina sharar Ƙwalla nace "Inna ni ba zanyi kuka dake ba ki yarda dani da iya gaskiya
ta nike magana".

Shiru tai min, nai ta mata magiya.

Momy ce ta kama hannu na ta yima Inna sallama ina kuka ina kallon Inna haka na baro
ta

daman driver mu yake jira a bakin ƙofar fita naci karo da Ladiyo data ke ƙoƙarin
shiga gidan mu.

A ɗan firgice ta kalleni sai tayi baya.

Bance mata komai ba nashi ga mota idan ta naga ya kawo ƙwalla kuma ta bani tau
sayi, a take jiki na yai sanyi, yafito ta nai da hannu, aikuwa da gudu tanufo ni

"Siddi'ka ina zaki haka ko sallama babu?".

"Birni mana".

"inda kike zuwa?".
kai kawai na ɗaga mata

"Amma shine wannan karan ko sallama babu?".

"Nima bansan da tafiyar bane ladiyo kuma karatu zanyi a can ɗin ba yanzu zan dawo
ba".

"Karatu fa kika ce Siddi'ka, mai zakiyi da makaran ta?".

"Nima bansan me zanyi da ita ba Ladiyo, amma dai an cemin tana da mutuƙar amfani,
kuma nan gaba zai taimake ni, zanji matuƙar daɗi, dan shi ilimi shine gishirun
rayuwa".

Cikin sanyin murya Ladiyo tace "to Allah ya bada sa'a Siddi'ka don Allah kada
kimanta dani".

Tabani tausayi sosai nasan kaf kauyen nan Ladiyo ba tadakama ta, kuma nima banida
kamar ta
Wata ran ma ni zanyi tsoka na amma sai inja mata duk da haka bai sa ta rabu dani
ba.

Nace "Bazan manta dake ba Ladiyo zan dawo gare ku Ina yi miki fatan alkairi kema".

"Ki shiga gurin Inna kice injini taba ki kayan sawa na ga baki ɗaya".

"To" tace tayi min godiya mukayi sallama ta shige gidan mu

A lokacin su Khadija sun shiga mota driver yaja muka ɗau hanya.

Comment
Share
Vote

NI DA YAYA SADEEQ


‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Chapter 10

GARIN ABUJA

Bamu wani tsaya akan hanya ba, Dan Momy tace duk mai uzuri yayi haƙuri, ya riƙe
har mu isa gida, saboda ance mata hanya babu kyau, Da misalin 'karfe 3:25pm muka
isa garin birnin tarayya Abuja, tun daga unguwar zaki san ba irin unguwar nan ce ta
kowa da kowa ba sai ɗan wane da wane tunda ga wajen gidan Daddy zaki san gidan
manya ne saboda ko fulawowin kansu da aka zagaye gidan dasu abin kallo ne, ba sai
ka shiga daga ciki ba, yawancin gidajen un'guwar ginin gidan sama ne, idan ki kaga
wannan sai kiga duk yafi kyau, amma kina ganin wani sai kice wancen bai kai wannan
ba, to haka dai gidajen unguwar suke, na wane yana wane na wane,

Ba yau na saba zuwa ba amma har yanzu na kasa riƙe sunan un'guwar Saboda ita kan
ta sunan un'guwar na 'yan gayu ce, kuma da turan ci ne 🤔
Gidan su Khadijan ma yana ɗaya daka cikin ƙerarrun gidajen saman dake un'guwar,
shiyasa nike son zuwa saboda ina son bene a rayuwa ta.

Driver yayi horn adaidai bakin ƙaton get din gidan
Me gadi ne ya leƙo ta ƙaramar ƙofa, ganin motar Momy ne yasa shi saurin wangale get
motar mu ta sulala ciki, mai gadi ya maida get ya rufe.

Daka bisani yazo da gudu ya buɗewa Momy ƙofa, cikin ladabi yake yi mata sannu ,
fuskar Momy a sake cike da annuri ta amsa masa "mun same ka lafiya?". "Lafiya lau
hajiya". Mai gadi ya faɗa yana sadda kansa ƙasa, alamun girmamawa "masha Allah babu
dai wata matsala ko?". Momy ta kuma tambayar Habu mai gadi, yace "eh Hajiya babu
wata matsala komi yana tafiya daidai".

"A kwai kayan mu a bayan mota kashigo mana dasu ciki kaida Idi". Da "to" suka amsa
su duka

A kasalan ce muka fito daka cikin motar muka shiga cikin falo, ko waccen mu tasan
ɗakin ta dan haka muna shiga ko wacce tayi inda tasan nan ne dakin ta yake.

A sama ɗakin danike sauka yake don haka na haura abina amma dana murɗa hannun ƙofar
sai naji a kulle yake gam.

ɗakin Khadija dake kallon nawa naje shima a kulle yake sai dai naji motsi da alamar
ita tuni tana ciki ƙwan-ƙwasa ƙofar na shiga yi, daga can ciki tace "wace".

"Siddy ce". nabata amsa

Jim kaɗan sai gashi ta buɗe, jikin ta ɗaure da tawul da alamar har ta cire kaya
wanka zata shiga

"Khadija mukullin ɗaki na nazo ki bani".

"To" tace ciki ta komo sai gashi ta fito hannun ta rike da mukullin na amsa nayi
gaba a bina.

"Cikin ɗaga murya ta ce" to matar yaya a huce gajiya lafiya". Ai kwa da gudu na
juyo dan na doke ta, amma sai tai sauri ta maida ƙofar ta rufe tana dariya

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

A bangaren sadeeq kuwa yana barin ɗakin Inna bai zarce ko ina ba sai gidan abokin
sa Farooq, bai kirasa a waya ba amma yayi sa'a saboda ya same sa ne yana ƙoƙari
fita, nan dai ya bashi hannu suka gaisa Farooq yace "yanayin ka ya nuna kamar kana
cikin damuwa, kuma ba ka saba zuwa gida na a irin wannan lokacin ba, kodai kai da
mutuniyar taka ce? Saboda nasan labarin gizo baya wuce na ƙo ƙi, da fita zanyi na
gaji da zaman gidan, amma tunda kazo mu shiga ciki ka faɗa min abinda ke tafe da
kai".

To bayan sadeeq ya shiga ciki, bedroom suka wuce, saboda yanayin tsarin gidan irin
me ciki da falo ne sai bayi da kitchen kuma duka haka gidajen kusa dashi suke
saboda duka manyan 'yan sanda ne wasu suna da 1 star wasu biyu wasu uku wasu kuma
igiya ce gare su, da dai sauran su kusan unguwa ce ta ma'aikatan 'yan sanda, shi
yasa da wuya kaji ance wani abu ya faru a cikin ta ko kamar ace anyi fashi ko an
sace wane, saboda a zagaye take da masu tsaro kamar barikin sojo ji shima Sadeeq
saboda ansan shine, dan ko bai nuna id card ba ana barin sa shiga.

Kan gado Sadeeq ya faɗa yana maida numfashi, Farooq ya zauna a kan wata kujera dake
bedroom ɗin yace "ba ba kaifa nike jira kace wani abu mana ka wani baje a kan gado
sai kace wata mace".

Tashi Sadeeq ɗin yayi ya zauna ya shiga jero ma abokin nasa ɗanyen hukuncin da su
Daddy suka yanke, Farooq ya san Sadeeq ba zai taɓa yi masa irin wasan nan ba,
musamman ma da yasan cewa Sadeeq da Siddi'ka babu jituwa a tsakanin su, saboda haka
ya gyara zama yace "Alhamdu lillah gaskiya naji daɗin wannan haɗin, kuma da kace
ɗanyrn aiki wallahi sunyi dai dai, Ko ba komai zaka daina tsangwamar yarinyar, kuma
shaƙuwa mai ƙarfi zata shiga tsakanin ku, saboda haka ka tashi muje a ɗaura auren
da mu, a kwai wata sabuwar shadda na da nasa aka ɗinka min da niyar yau in sata to
sai bayan na anso ta daga wurin taila na canza ra'ayi, kaga sai ka sanya ta".

Kwanciya Sadeeq ya gyara a kan gadon yace "ɗan iska mayen mata, to ai sai kaje in
yaso ɗaurin auren ma sai ayi da kai, amma ni nan daka ganni babu inda zani wallahi,
wai ni za'ama aure kamar wani ƙaramin yaro, arasa ma wa za a haɗa ni da ita sai
'yar ƙaramar yarinya wacce ko gama sanin inda yake mata ciwo batayi ba".

Dariya ce ta kama farooq saboda haka yay ta da rawa abin sa, saida ya gama ya fara
lallashin a bokin nasa akan ya tashi ya shirya suje ɗaurin auren, amma Sam Sadeeq
yace "bai san da maganar ba". Farooq yana ji yana gani dole ya ƙyale shi, amma ba
dan ransa yaso ba.



Wayar sadeeq ɗin ce ta hau ringing cikin hanzari ya zaro wayar daga aljihun sa,
ganin sunan Ha'sheem yana yawo akan screen ɗin yasa shi jan dogon tsaki yace
"kagani ko Farooq abinda nake gudu kenan, yanzu haka kira na yayi ya cemin ashe
nayi aure ko gayyata babu". Kiran ne ya katse, yayi saurin kashe wayar gabaki ɗayan
ta, wannan dalilin ne yasa da Daddy ya kira wayar Sadeeq ɗin yaji ta

Please Login or Register in order to submit comment