You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda yafaru tana kuka, gaskiya Sadeeƙ
bai kyauta ba.

A take na kira sa a waya nayi masa kaca-kaca, kuma nakira Daddyn ku a waya, na
faɗa masa, ya ce mu zauna anan Danden nan da kwana 2 zaizo.

Ina ƙaƙalo hawaye nacire hajabin jiki na, nace "Momy kalla kigani fa wallahi babu
abinda nayi masa yayi min wannan dukan, kuma har da cewa kaɗan ma yai min.

Salati Momy keyi tana tafa hannaye "yanzu Sadeeƙ ne yayi miki haka?". Momy ta faɗa
tana riƙe haɓar ta.

gyaɗa kaina nayi alamar eh.

ta ce "kiyi haƙuri Daddyn ku zai zo nan da kwana biyu insha Allah, zai kuma ɗauki
mummunan mataki yanda koda kuɗi a kace Sadeeƙ ya sake dukan ki bazai sake ba".

Khadija da tunda ta shigo ta aje kular hannun ta, ta sami gefan gado ta zauna, sai
alokacin tace min " sannu Siddeeƙa yajikin naki da sauki dai ko?".

"Babu laifi dai zance amma wallahi na daku gurin baƙin mugun".

"Ina ke miki ciwo yanzu to?". Khadija ta kuma tambaya na.

Nace "Babu sai ɗan abinda baza'a rasa ba".

"Alhamdu lillah". Momy tace

yayin da Umar yace "aunty Siddeeƙa yajikin naki?".
"Da sauki" itace amsar dana basa, ina miƙa mai hannu alamar yazo kusa dani, ai kuwa
ba musu yakama hannun nawa, zaunar dashi a ɗayan gefen gadon nayi suka sani a
tsakiya.

dayi ke lokacin da nike bacci ruwan da ake ƙara min ya ƙare nurse ɗin tazo ta cire
min.

zubamin abincin Khadija tayi, tana faɗin "sister Siddeeƙa daure dan Allah kici
wannan babu yawa, taliya ce fara da mai da yaji".

nace "naƙoshi fa".

da ƙyar Momy ta lallaɓani naci ɗan kaɗan, na ture kwanan.

nace "ni fa na ƙoshi Umar zo kacinye sauran".

Sai alokacin na lura babu Inna "ina Inna wai?". na tambaya ina kallon Khadija.

Ai takoma gida, driver nasa ya maida ta, nace zan zauna dake har sanda zasu sallame
mu, a cewar Momy.

"to Momy mu koma haka ai na warke". Nafada ina sauka daka kan gadon kamani khadija
tai tana faɗin "wannan wani irin ciwo ne Siddeeƙa?🤔
Koda yike ke daman haka kike ba kyason asbiti".

"haba khadija ai kwata kwata natsani asbiti, zaman asbiti ai sai dole, to inba dole
ba me mutum zaiyi" nabata amsa da haka.

"kinji momy kira driver ɗin kawai, Allah da gaske nike na warke".

Ta ce "bari a fara kiran likita idan tace zamu iya tafiya gida sai su baki
sallama, tunda kin matsa".

dariya ce taka mani sosai nike ƙyalƙyatawa.

"Lafiyan ki kuwa Siddeeƙa". Momy ta tambaya, cikin san sanin dalilin da yasa nike
dariya.

Ina dariyar na ce "ai kece ki ka bani dariya Momy, baki karewa asibitin kallo bane
halan? To wannan asbitin da ki ke gani ba a sallamar mutum,
idan aka kawo mutum yaji sauƙi kawai tafiya zai yi abun sa. Idan kaga dama ne ma
sai kace musu zaka tafi, basa saida wasu magunan kirki, kuma basa wani rubuta maka
koda zaka siya wani gurin idan su basu da shi, idan ma sun rubata to abu 2 ne kawai
fanadol sai farasitamol".🤣na ƙarasa faɗa ina ƙara ƙyalƙyala dariya.

Na cigaba da cewa "nifa momy wallahi a gani na duk basu san aikin su ba, gwara
gwara ma Aliya. wannan taɗan iya aikin, itace ma tasamin ruwa, idan fa aka kawo
mutum bata nan sunan shi sorry, ba ƙaramin jagwal-gwalo yake sha ba".

sosai khadija ke dariya tace "ai ni ban zata ma asbiti bane, domin sam baya kama da
asbiti".

"'kwarai ma kuwa". Na bata amsa

Nace "kefa da a ka kawo ni wata a ka sauke a kan gadon a ka ɗora ni, nason don
sunga yah Sadeeƙ ne, duk sanda ya kawo ni gado suke bani".

cikin mamaki momy tace "wata fa ki ka ce aka sauke".
"eh mana Momy" nabata amsa.

"to ina suka kaita?". Momy tayi tambayar.

Nace "wallahi Momy ban sani ba lokacin ina fama da kaina".

Cikin hanzari momy ta fara lalubar jakarta tana faɗin "da gaskiyar ki Siddieeƙa
bari na kira driver yazo ya kaimu gida kamin kema a sauke mana ke, tunda Sadeeq ɗin
ya tafi".

Ina dariya nace "uhm Momy da zamu shekara anan babu wanda zai sauke ni".

"saboda me? Yaya ko?". Khadija ta tambaye ni tana kallon idona.

Nace " eh, nifa mutane har mamaki suke bani, yadda naga suna tsoran shi kamar
wani mala'ika".

Momy tace "ni dai duk da haka gwara mu koma gida, ko wani asbitin na kudi a canza
miki, ban yarda da wannan ba za a iya bawa mutum maganin da bashi ya dace ba".

Nace "momy nifa na ma warke babu wani asbitin da zan sake komawa".

Ɗaukar wayar ta tayi ta latsa numbar Idi driver, bugu ɗaya ya ɗauki kiran
kamar tana gabansa cikin ladabi yace "Hajiya na na sauke Inna tun ɗazun".

Ta ce "yayi kyau muma kazo ka ɗauke mu ta sami sauƙi mara lafiyar".

Ya ce "to Hajiya".
sannan takatse kiran.

Ba a fi 15 minutes ba saiga Idi driver yazo.

Da yake ɗazun har dashi aka zo yasan asbitin har ɗakin da aka kwantar dani ya
shigo. ya kwashi tarkacen da khadija tazo dasu yayi gaba.

Sannan mumu muka fito, da Aliya muka ci karo A bakin fita asbitin tana Murmushi
tace "mara lafi sauki yasamu kenan?".

"Eh". Na ce

Ta ce "to ba zaku sai magani bane?".

"muna da irinsu dayawa agida" nace mata.

"To shekenan Allah ya ƙara sauƙi" ta faɗa yayin da takai duban ta ga Momy ta ce
"Hajiya ya mai jiki?".

Momy tace "mai jiki ta warware ". Daga haka muka mata sallama muka fito cikin
asbitin, muka shiga cikin mota Idi driver ya hau titi.

Umar ne ke bamu labarin ban dariya a mota sai ƙyal-ƙyalawa muke yi kamar wasu
zararru, Momy dai saidai tayi murmushi idan taji ya faɗi abin dariya.

yanxu ma wani labarin bafullatani yake bamu.

Yace " wai wani ba fullatani ne, ya siyo lemu, shine aka samai lemun aleda, sai
ya saka lemun a bayan keken shi koda ya fara tafiya a kan kwalta, sai ledar lemun
ta ɓule, lemu ɗaya yafaɗi a kan kwalta, koda bafullatani yaga abinda ke faruwa
lemun sa ya faɗi kan kwalta, amma se gudu yake yi, sai ya sauka a kan keken ya
tsaya ya kwance sauran lemun da suka rage a cikin ledar, ya watsar kan titi, ya ce
"a kin banza a she ku kuna ma tafiya kuke bani wahala, to muhaɗu a gida". 🤣

Comment
Shear
Vote

Sbeauty ce ✍️
NI DA YAYA SADEEQ

Love story

Na
Siddiqatulkhaireey Yahya
(S beauty ✍️)

*EWF*✍️
_________________________________

Page 04

‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

________Sosai muke dariya Khadija harda rike ciki, ni kuwa ba a magana don har
tsalle nikeyi, a haka muka iso gida cikin farin ciki da nishaɗi, a dalilin su
Khadija, sai na manta da wani yah Sadeeƙ.

Muna yin faking na kwasa da gudu cikin gidan "Inna Inna". Na shiga ina ƙwala mata
kira, but a ce rike a hannun ta, da alamar banɗaki zata, farincikin gani na yasa ta
saki butar, ta nufo ni, kan ta ƙaraso na isa gareta na
rungume ta, ina cewa, ya dai tsohuwa ko baki murna da gani na bane, "ja ira". Inna
tace tana jan dogon hanci na "banyi murna daganin kiba zaki ce nida nafi kowa san
kisamu lafiya".

"To ya jikin Siddeeƙa?"

"Jiki yayi sauki wallahi".

"Haka akeso wancen mugun kuma Allah zai saka miki".

"To". Nace yayin da nike nufar cikin falo, ina shiga na zauna a kan kujera ina
maida numfashi, kamar wacce tayi gudu saboda haka ɗabi'a ta take.

Ban wani jima da zama ba sai ga Khadija tashi go, "ke haka ake tarban baƙi?".

"Ina baƙin suke?". na tambaye ta da mamaki, saboda ni dai banga wasu baƙi ba.

"Gamu" tanuna kanta, duka nakai mata sannan nace "wai ɓaki, ku da gidan ku".

"Na ji amma wallahi ba kida kirki Siddeeƙa, ko da yiki na miki uzuri, saboda baki
da lafiya". ta ƙare maganar tana zama kan kuje rar danike kai.

Kamar na tambayi me nai na rashin kirkin, amma sai na basar.

Taɓe baki nai nace "kinsan wani abu khadija?".

"A a sai kin faɗa".

Na ɗora da cewa "wallahi yaya Sadeeƙ bai daki banza ba zan rama, domin kuwa bashi
yaci, saboda ni ba kanwar lasa bace".

Cikin zaro ido ta miƙe, kallo na take alamun son ta tabbatar da abinda taji, ba
tare da shayi ba na sake maimaita furici na da cin alwashi.

Dafe ƙirji tai kana ta ce "wai da gaske? ".

"Kina mamaki ne?"

"Eh ai dole nayi mamaki, saboda nasan ɗan tsako ya hayke wa shaho".

"Ai kuwa ki bari wannan karon zakiga ni, domin sai nasa shi kuka, muna nan dake".
Na ƙare ina fashewa da dariya.

Da ido ta bini da kollo irin bakida hankali yarinya.

Nima nabi ta da kallon naji dai.

"Can dai na ce,"wai ya kike min kallon mara wayau ne? Ko kuma wacce ta fita a
hayyacin ta? Amma bari, zan tabbatar miki da a cikin hayyacin na nike".

"Uhm". tace tana cire gyalen ta, gami da ajiye shi a hannun kujera.

Umar ne yashigo bakin sa da sweet yana tsotsa, "la! Umar zo kasanmin". Na faɗa ina
miƙa mai hannu".

"Za kisha ne?".

"Eh".

"To bari na kawo miki naki, yana ɗakin Inna".

Kamin nace to, har ya fice.

"Nima katawo min dashi". Cewar Khadija.

bai daɗe ba sai gashi ya kawo mana, nan ya zauna mukai ta shirme, muna ife-ife,
saboda idan muka hau a guri babu dama.

Ana idar da sallar magriba ina sulalewa nabar gidan, da fita ta 'yar kasuwa na
zarce, ina tafe ina gaɗa ni kaɗai, a haka har na isa, can na hango ƙawa ta Ladiyo.

Kaf ƙauyen Dande banida ƙawa sai Ladiyo, saboda nafi san a kullum nice shugaba, a
komai nafi son ace nice a gaba, sam bana son raini ko kaɗan, sauran duk nayi faɗa
dasu, saboda halin mu be zo ɗaya ba, itama Ladiyo tana da hakuri ne kuma kome zan
mata batayin fushi.

Ladiyo nakwala mata kira daka nesa, ganin bata ni ba yasa na sake, waige-waige
takeyi, har ta juyo ta inda nike, baki ta washe ganin nice, da sauri ta nifo ni,
tafawa mukai alamun munji daɗin haɗuwa da juna.

"Ai nazaci bazaki futo ba". Ladiyo tace.

"Caf me zai hana ni fitowa da lafiya ta". Nace mata

"Yo saboda abinda yayan ki yace ɗazun, wallahi na tsorata bazan ƙara zuwa gidan
kuba".

Wani dogon tsaki naja "mastsstt kefa sakarya ce, sam bakida wayau, inba sakarci ba
taya zaki yarda da maganar sa, shi ba mala'ika ba ba kowa ba, abinda ma yasa baki
ganni da wuri ba banida lafiya ne saida aka kaini asbitin bakin gari".

ta ce "baki da lafiya fa kika ce" ɗaga mata kai nayi alamar eh

"To meke damun ki? nidai banga alamar rashin lafiya atare dake ba".

"Ke Allah da gaske bani da lafiya, yah Sadeeƙ ne yaimin dukan mutuwa, ke har fa da
ƙarin ruwa akai min".

Ido tazoro waje tana dafe kirjin ta tace "dukan mutuwa fa kika ce".

Tsaki nayi nace "dube ki kamar ke a kaima dukan, duk kin bi kin firgice".

"To ba dole na firgi ce ba, ɗazu fa da yana min magana wallahi baƙara min tsoro
naji ba, tsabar tsorata dana bar gidan ku kafin inkai gidan mu har fitsari nayi,
gashi kuma ɗan sanda, mugunta babu wacce be iya ba saboda rannan tsallan kwaɗo naga
yasa wasu yara a layin ku, niya ta nazo gurin ki, zuwan da banyi ba kenan".

Taɓe baki nayi sannan nace "kin san bai daki banza ba ko, domin wallahi bashi yaci,
abinda ma yasa nafito kenan neman mafita domin yau ba tsoka na zanyi ba".

"Ai kuwa naji daɗin ganin ki, saboda kar kiga yadda su Mariya da Harira suke
tsokana ta, wai inayin magana zasuyi suyi min lis".

"Sakarya kuma kika tsaya kina kallon su". na tambayeta

"Ke! To me kike so nace?".

Kwafa nai, kana nace "bari na gama da yah Sadeeƙ, sai na juyo kansu".

"Yanzu nidai faɗa min me zan mai na huce".

Shiru Ladiyo tayi a lamun tana nazari can tacemin "a dake dai bazai dakun miki ba,
sai dai muyi masa mugunta dai-dai da dukan daya miki".

"To wace irin mugunta ce kike ganin zan mai na huce?".

"Eh, kawo kunnen ki kiji yadda zamuyi".

A kunne taraɗa mun aikuwa naji daɗin shawar ta, sosai na saki raina, nayi tsokana
son raina, sai gurin tara na koma gida, a ɗakin Inna nasame su, a nata fira da
sallama na shiga.

Da ido kowa ke bina, "wai Siddeeƙa daga ina kike ne haka, gurun mutane biyar suka
kawo ƙaranki, Aisha ke basu hakuri da ɗan kuɗi, take kashe bakin su". Inna ce ke
wannan maganar

cikin in'ina nace "Inna daman naje....".

"Daman me" tace min cikin tsawa.

"ina turo ɗan ƙaramin baki na nace, waye yakawo ƙarata ban sani ba". Dubana nakai
ga Momy nace "wai haka momy ankawo Kara ta".

"Kinci gidan ku, Hajiyan ƙarya zatai miki kenan? wai Siddeeƙa yaushe zaki girma ne
kiyi hankali, kina girma kina ƙara rashin wayau, Allah dai ya shiryaki".

"Ameen, ina abinci na Inna?".
"Yana kitchen a cikin kula kije ki ɗauka".

Umar yace "nima banci abincin ba, nace sai kin dawo muci".

"To yayi ɗauko mana muci, mai aka girka? na bukata.

Yace "fatan doya ne Momy ta girka".

Nace "yauwa maza je ka ɗauko mana ".
Bayan ya ɗauko mana munaci ina bashi labarin inda naje da kalar tsokanar da nayi,
sai cizon yatsa yake, yana faɗin wai meyisa baki min magana ba sanda zaki tafi?
wallahi da dani za'ayi, da yanzu ba labari kike bani ba saidai ni na bada.

"Yo ka yaƙuri ban san ai zaka ba, na ɗauka kai ma irin Khadija ne me tsoran tsiya".
wa ni? Umar yafaɗa yana nuna kansa, Allah ya kyauta ina namiji intsaya tsoro sai
kace mace".

Comment
Shear
Vote


NI DA YAYA SADEEQ


Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya
(S beauty ✍️)

EWF✍️
_________________________________

Page 05

Bayan gama cin a bincin mu da Umar na miƙe ina hamma alamar bacci nike ji.

Khadija ce ta kalle ni tace "ba dai bacci za kiyi ba". Nabata amasa da "eh kwanciya
zanyi".

"Dawuri haka" ta tambaye ni

Da "eh". Na bata amsa

"Yo in banda abinki khadija ai Allah kaɗai yasan inda Siddiƙa taje bayan fitar ta
gida, kinga ko dole ta kwanta da wuri". Inna ce dake kwance tace haka, taɓe baki na
nayi nace "Momy zan kwanta saida safe".

Wayarta ta kunna ta kalli a gogo ƙarfe goma saura na dare, kallon Khadija Momy tayi
tace "kitashi kibita dare yayi goma saura". Umar ma tashi yayi ze bimu amma Momy
tace, bata yarda ba tare da ita zai kwana saboda ita batasan kwana ita kaɗai".

Akwai ɗakin da idan sunzo suke sauka acikin sa, duk wani abun buƙata Daddy ya zuba
a ciki.

Sai da safe muka ƙara yimusu Khadija ta rigani yin gaba, ina cikin tafiya naji
kamar na taka ƙafar mutum dayike lungun ɗakin a kwai duhu, ƙauyen dande kuma ba
wuta, jannareto muke kunnawa zuwa ƙarfe goman dare a kashe, to yau yaya sadeeq be
kunna ba. Ban gama tabbatar da ƙafar mutum bace a gurin, hakan yasa na ƙara ɗora
kafata a kai na murza, 'yar ƙara naji anyi alamun mutum ne, koda na waiga inda nike
tsammanin zan sami Khadija wayam babu ita ba alamar ta, zaro ido na nayi da kyau
gabana ya soma dakan uku-uku, sakamakon tunawa da nai ba wani bane illah Sadeeq.

A ɗan tsorace nace "la! yaya". Ban ƙarasa maganar ba ta maƙale, sakamakon bige min
baki da yayi, gami da shaƙe min wuya,ya haɗani da jikin bango, Yana faɗin me hali
be fasa halin sa gwara na kasheki kowa ya huta, sa'anki ne ni zaki murje min yatsa
eye?.

Da iya ƙarfin sa ya shaƙemin wuyan, ina son inyi ihun neman ɗauki amma na kasa,
cikin ikon Allah saiga Momy da Umar, sunzo wucewa hannun ta ɗauke da hasken fitilar
wayar ta, tana haskawa, mai zata gani wani ƙara tasaki saida wayar ta yafaɗi a
ƙasa, Inna da khadija rige-rigen fitowa suka yi saboda ihun Momy da suka ji.

Umar tuni ya das-kare a gurin, jikake tas tas ƙaran marin da Momy ta wanke yaya
Sadeeq

Amma duk da haka yaƙi sakina, don haka ta ƙara mai wani saida tayi mai mari biyar
amma ko gezau, beyi ba dayike yah sadeeq namijin duniya ne, "to idan baza saketa ba
sadeeq zan cireka cikin 'ya'ya na". ta faɗi haka fiskar ta babu alamun wasa.

Jin wannan lafazin na Momy yasa Sadeeq yayi jifa dani, idanuwan sa jajur kamar
Wanda yasha wani abun, huci yake yi sosai

Kasa nafadi shirim jikina babu ƙwari, ina fitar da numfashin wahala Inna da Khadija
takaici ya hanasu magana, hawaye ne ke gangan garowa a cikin Idanuwan Momy, ta kasa
magana hannuna ta kama muka wuce ɗaki na, su Inna na biye da mu abaya, kan gado ta
ɗorani, na kwanta yaraf, ruwan fridge me sanyi khadija ta ɗibo min ta ɗaga kaina ta
bani nasha ina maida numfashi.

Babu Wanda ya tambayi me ya haɗamu, duk kuwa da cewa zuciyoyin su cike take da
tambayoyi, daga haka kowa ya tafi ma kwancin sa.

a raina kuwa saƙa yadda zan wulaƙan ta yaya sadeeq nikeyi, domin wallahi bashi yake
ci wani mugun tsanar sa naji ya ƙara da ɗuwa a zuciya ta.

da wannan tunanin bacci ɓarawo ya sace ni.

Kiran sallar asuban fari a kunne na akayi, banida nauyin bacci, tashi nayi na zauna
gaba ɗaya jikina ciwo yake min amma wuya na yafi min ciwo.

Tashi nayi tsaye ina miƙa ko salati banyi ba, ba kuma dan ban iyaba saidan tsabar
shagala, da wasa da yayi min yawa.

Tsakar gida nafito babu kowa ɗan Murmushi nayi saboda zanyi abinda zanyi babu wanda
zai ganni, a irin wannan lokacin ya Sadeeq ke fitowa yayi alwala, kamar yadda
Ladiyo ta tsara min haka nayi, a binda kuwa Ladiyo tace min a kunne shine. Na zuba
masa karara aruwan alwalar sa, da na wanka, nayi na'am da wannan shawarar da
tabani, saboda nasan tanan ne kawai zan iya ramawa.

saɗaɗawa nayi ɓangaren sa, inda yake ajiye butar sa na nufa, "Alhamdu lillah". na
faɗa yayin da na hangi butar sa, a jiye a gurin, da hanzari na ƙarasa gurin.

ɗaga rigata nayi na war-ware siketin jikina, na ciro ƙullun ledar karara da nasaka
Ladiyo ta sato min na Umman ta da take saidawa.

Murmushin mugunta nayi, yayin da na ɗaga butar naji ta cike da ruwa, buɗe murfin
butar nayi na zuba, kana na rufe, na maidata ma'ajin ta.
Yaya Sadeeq baya barin sai zaiyi anfani da abu yanema yana tanadar sa ne tun kamin
lokacin amfanin sa yazo, saboda bayason bata lokaci

A jiyar zuciya nayi nabaro lungun, a hankali nike tafiya kamar mara gaskiya, Inna
na hango idon ta akaina ƙyar da buta a gaban ta, da alamar alwala ta gama, Murmushi
nayi gami da ƙarasawa gaban ta nace "Inna kin fito kenan?".

"Eh na fito, daga ina ki ke?".ta tambaya.

"Daga waje leƙawa nayi, alwala na fito sai yanayin garin ya bani sha'awa shine na
leƙa" na faɗa mata haka kamar da gaske

"Amma mai yatada ki daga barci" Inna ta tamba yeni a karo na biyu.

Wallahi Inna baccin ne yaƙi zuwa min sai naji an kira sallah shine nace "bari nayi
sallar sai na kwanta".

Tace "to ya jikin naki?" nace Inna da ɗan sauƙi, amma na kasa bacci, dana rufe ido
sai na dunga ganin kamar zai zo ya shaƙeni, saboda yace saiya kasheni".

Inna na salati tace"yanzu Garban ne yace saiya kashe ki!?". Eh Inna shi fa, aiba
'karamin mugu bane". Naƙare maganar ina yin hanyar ban ɓaki. Na bar Inna da mamaki.

Banɗaki nashiga nayo fitsari, na fito nazau na a kan kujera, nafara alwala kenan
saiga Yaya Sadeeq nan, nayi kamar ban ganshi ba, na cigaba da yin Alwala ta, ta
gaba na yazo ya wuce, bayan shi nabi da kallo ina Murmushi, a cikin zuciya ta nace
"zaka bawa yan garin ku labari, zaka san kayi da 'yar halak".

Banɗaki yashiga yajima aciki, can saiga sa ya fito, a lokacin nagama Alwala ta amma
ban tashi a gurin ba,

Tashi nayi na koma ɗan nesa da inda ya tsugunna, Alwala yafara, ganin ya manta beyi
kus kuran baki ba naji sanyi a raina, ɗaki na koma na tsaya a bakin hundo, ina
kallon sa.

yana wanke fuska ne naga ya mike kamar wanda aka tsungula gabansa yakama yana
murzawa🤣 bansan sanda daria ya kwace minba can kuma yafara kifta ido se yanzu yake
tunani tabbas yaji ruwan wani iri lokacin dayeke shakar hanci, abinda yasa baiyi
wani tunani ba yaga butar sa ce shi kaɗai babu wanda yake amfani da ita, sosai yake
murza idonsa atishawa na biyo baya haka yaita fama 💃 ɗaya hannun rike da gaban sa
yana murzawa 🤣.

Dariya nike ina tsalle abin nema ya samu, sosai Yah Sadeeq yazama karamin mahaukaci
gashi har an shiga masallaci amma shi ko alwalar be samu ya gama ba.

Sosai abin ke damun sa musamman gabansa yafi sosa gurin, a haka Momy tafito ta same
sa, watsi tayi dashi kamar bata ganshi ba, jin motsin da yayi ne yasa ya ɗan buɗe
idon sa, saboda yaga waye, wata a zaba ce ta ƙara shigar masa ido, har saida ya
saki 'yar ƙara, tsaki Momy taja tagama abinda za tayi nan tabar sa tanai masa
kallon mahaukaci. 🤣

Khadija Khadija yah Sadeeq ne ke ƙwala mata kira, barci take yi, ganin yana kiran
ta nayi saurin zuwa bakin gadon ina dukan ta,da magagin bacci a idon ta "lafiya?".
Tace min 'yar dariya nayi nace "yah Sadeeq ke kiran ki". tashi tayi zaune tana zaro
ido kamar ba me magagin bacci ba "yana ina?". tace min "tsakar gida". na bata amsa

Nace "amma fa kiyi a hankali don naga kamar yasamu taɓin hankali"

Jin ya cigaba da ƙwala mata kira yasa ta faɗuwar gaba, babu shiri ta sakko daga kan
godon, tayo waje, yadda taga yaya sadeeq ɗin a tsakar gida ba ƙaramar kunya yabata
ba, gani Yaya tafaɗa sanda ta ƙarasa gunsa.

"Ɗauko bokiti a ɗaki na ki zuba min ruwan wanka, ki kai min ban ɗaki". ya faɗi
haka.

Da "To" tabi shi kamar yadda ya umarceta haka tayi, a binda khadija bata sani ba
ina laɓe lungun bayi tana aje ruwan nazuba mai karara nai fitowa ta, tsaye na ganta
gurin tana cemai "yaya na kai maka ruwan".

"Kama hannu na to" yace mata, hannun na sa takama har bayi ta kaisa, sannan tafito.
Har yanzu Idanun sa a rufe suke, cire jallabiyar jikin sa yayi, sannan ya laluba
yaji babu kwandon soson wanka, kiran sunan Khadija yafarayi nikuwa daman ina kusa
da bayin, khadija kuwa tayi alwala ta tafi ɗaki sallah, "kawo min sabulu". Yace

Daman Yah sadeeq bai wanka da so so ko kadan sai sabulu kawai, Murmushi nayi naje
na dauko mai sabulu wanda na badeshi da zallan tarugun dana ga Inna ta daka sa ta
shanya asama jiya.

hhhmmmm nace "ai wallahi tunda ka taɓani sai kasan kayi da 'ya, taka kujera nayi
naje fa mai sabuln cikin bayi.

Komawa gefe nayi na zauna inajin raina fes banida wata damuwa.

Har gari yafara wayewa babu sadeeq babu labarin shi nikuma naƙi tashi, domin ko
sallah ma banyi ba.

Ya sadeeq kuwa yazama abin tausayi cikin bayi yarasa wannan wani irin bala'i ne,
shida yayi wanka domin yasamu sauƙi amma sai a kasin haka, susar jikinsa yake iya
ƙarfin sa duk da idan yasosa yanajin wani mugun raɗaɗi a jinkin sa, amma bashi da
wani zabin da yawuce susar.

har 7 am be fito ba, Inna ce zata shiga bayin na kalle ta nace "Inna fa da mutum".

"Waye?" tace min "yah Sadiq ne" na bata amsa.

Inna tace "me yake yi agidan har yanzu da bai fita gurin aiki ba, naga da an idar
da sallar asuba yake tafiya".

Nace "to Inna kika sani ko anyi musu canji ne kinsan ana canza su ai".

"Haka ne" Inna tace, ɗan matsawa nayi kusa da ita, sannan nace "Inna amma fa yau
yah Sadeeq wallahi kamar mahaukaci, domin tun asuba yake abayin nan, kafin yashiga
ya daɗe anan tsakar gida yanayin wasu a bubuwa masu kama da na mahaukata". Zaro ido
inna tayi
na ɗaga mata gira, nace idan baki yarda ba kuma, Ki je ki tambayi Khadija ko Momy
saboda dukan su sun ganshi a cikin yanayin.

♾️♾️♾️♾️♾️
Nagaji da typing atara gobe in Allah ya kaimu domin jin yadda za a kwashe tsakanin
Sidda'ka da sadeeq kucigaba da bibiyata nikuma zancigaba da nishadantar daku
♾️♾️♾️♾️♾️

💋💋💋💋💋💋💋
ʏᴀ ᴀʟʟᴀʜ ɪɴᴀ ʀᴏᴋᴏɴᴋᴀ ᴋᴀʏɪᴡᴀ ᴍɪᴊɪɴᴀ ᴀʀᴢɪᴋɪ ᴅᴀᴋᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴀʀᴢɪᴋɪɴ ᴀɴɴᴀʙɪ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ sᴀᴡ
ᴋᴀᴡᴀᴅᴀ ᴛᴀsᴀ ᴅᴀɢᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴡᴀᴅᴀᴛᴀʀ sᴀʏʏɪᴅɪɴᴀ ʀᴀsᴜʟᴜʟʟᴀʜɪ sᴡᴀ ᴋᴀʜᴀɴᴀ ᴍɪᴊɪɴᴀ ʜᴀssᴀᴅᴀ ᴋᴀʀ
ʏᴀʏɪ ᴋᴀʀ ᴀʏɪ ᴍɪsʜɪ ʏᴀ ᴀʟʟᴀʜ ᴋᴀ ᴋᴀʀᴇᴍɪɴ ᴍʏ ᴅᴀɢᴀ ᴍᴜɢᴜɴ ᴊɪ ᴅᴀ ᴍᴜɢᴜɴ ɢᴀɴɪ sʜᴀʀʀɪɴ ᴍᴜᴛᴜᴍ
ᴅᴀ ᴀʟᴊᴀɴ ᴅᴀ ᴅᴜᴋ ᴡᴀɴɪ ᴍᴇ sʜᴀʀʀɪ
💋💋💋💋💋💋💋
NI DA YAYA SADEEQ


Page 06

‫بسم الله الرحمن الرحيم‬

Jinjina kai Inna tayi, sannan ta nufi hanyar ɗakin da Momy take, ƙwanƙwasa musu
kofa tai,

Please Login or Register in order to submit comment