You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko magana, to
bayan na warke na dawo hayyaci na ya tambaye ni ahali na ko suna ina, sai na tsinci
kaina da ce mai bani da kowa sai Allah sai kuma kai, to bayan kwana biyu yazo min
da maganar aure, nace masa ni da ba fita nike ba ina zan samu muji?" yace" indai
wannan ne bashida matsala zai samo min mijin aure na kirki wanda zai rike ni amana
"

Bayan sati guda ina zaune a daki na sai gashi yazo yake cemin" ya daura min aure,
yanzu haka tare da mijin nawa yazo kuma dani zai tafi saboda haka na tashi na
shirya "

Haka dai na baro gidan Mlm liman ba dan raina yaso ba nabi Alhaji Imran, wato baban
yarannan

Ammi ta fada tana nuna su Fadeela

TA dora da cewa, nayi zama na amana da margayi, yana yawan tambaya na Ahalina amma
sai nace" ni bani da kowa ".

Na rasa kuma dalilin da yasa nike cewa haka dan ko tunanin wani nawa ma banayi,
cikin ikon Allah na haifi yarana yan biyu mace da namiji masu kama da Daddyn su, ya
tambayeni shawara akan sunan da zamu sa musu nace" Asa min Aisha da Aliyu ".

Haka rayuwa ta cigaba bayan wasu shekaru ina zaune a office dina saiga Sadeeq da
Siddeeqah nan sun shigo, tunda na kalle su na fara tuno da iyali na kuma naji ina
kwadayin na sake haduwa dasu, tunda naga Sadeeq naji a jiki na dana ne haka itama
Siddeeqah, sai naja ta ajiki na ta yadda take yawan bani labarin ku, hakan yasa na
kara tabbatar da tabbas ita din jini na ce, amma sai ban taba nuna mata ba, nasha
tambayar ta ina mahaifiyar ta? " sai tace min" mahaifiyata ta bata tun ina yar
karama kuma har yanzu bamu san inda take ba " hakan yasa na kara jin kwarin gwuiwa
shine fa da akai hutu nace ta bari zan kai ta".

Ta numfasa tace "wannan shine takaitaccan abun da ya faru bayan rabuwa ta daku".

Inna tace" wannan fa?"

Fadeela take nufi

Ammi tace" marainiya ce mahaifiyar ta ta rasu wajan haihuwar ta, kuma yayar su
Easha ce da suke uba daya".

Daddy yace "naji kina cewa margayi yanzu shi Alhaji Imran din ya rasu?".

Wasu hawaye ne masu zafi suka zobo wa Ammi tace "eh ya rasu a sakamakon hadarin
mota da yai".

"Allah ya jikan sa su Daddy suka ce"

Wannan kenan

Bayan ko mai ya lafa Ammi da Momy suka tambayi inna abinda za'a sha ruwa dashi?

Tace su bari Garba ya siyo tunda yanzu yamma tayi, ga gajiyar mota

Bayan kwana biyu ya kama jajibari, mayafi na na saba nace "Inna zan fita" tace
"zuwa ina kuma keda ba kya iya zama a guri daya?"

"gidan Ladiyo man tun nazo ban leka ta ba fa".

"to a dawo lafiya" inna ta fada ni kuma na fice a buna

A soro naci karo da Yah Sadeeq, bayan ya kare mun kallo yace" ina zuwa?".

nace" gidan kawata Ladiyo zani ".

" kuma da izinin wa" ya jefo min tambayar

"inna mana" na fada a takaice

"to bazaki ba ki koma".

Kallon in ka isa na mai na fice a bi na

karasawa cikin gidan yai ransa a mutukar bace ya fara masifa saboda duk suna tsakar
gidan, fadi yake "wai Inna akan me zaki bama yarinyar nan dama ta dunga gantali, da
aure na a kanta".

Momy ce tai caraf tace "eh lalle ma Sadeeq, yanzu ne kasan da ita din matar ka ce
yanzu ne kaje jin haushin yawon da take yi? To tun wuri ka fita ido na bazaka
takura ma yarinya ba".
Ammi da ke wanke wakan da za'a kosai dashi tace "Haba Momyn yara ai da gaskiyar sa,
tunda shi ba sakaran na miji bane taya zai bar iyalin sa sakaka a gari? Ina goyan
bayan sa kuma bari ta dawo sai naci mutuncin ta, na kara ganin ta fita ba da izinin
sa ba

Please
Comment
Share

NI DA YAYA SADEEQ

•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬

No editing

Chapter 33

_______zaune nike a dakin Ladiyo muna firar mu gunin ban sha'awa sai wasa da dan ta
Mamman nike yi, tace "wai ke Siddeeqah yaushe zaki tare a dakin mijin ki ne?"

Nace "waya gaya miki zan tare? Nida nike jira ya bani takarda ta naje na auri wanda
yake kauna ta".

Bakin Ladiyo bude tace "amma dai baki da hankali, a wannan zamanin ka samu miji
irin yah Sadeeq ai ka more, ke sune fa irin mazan da ake bada labarin su a novel,
amma kike nema kiyi fatali da damar ki".

Nace "bazaki gane bane, mubar maganar kawai" bayan na bata kyautar kudi nai mata
sallama nace "taya kuri nazo mata da kaya sai na bude a kwati na zan kawo mata"

Gadiya tai min har bakin zaure ta rako ni

A hanya na hadu da wani mai naci tun na fara tafiya yake bina yana min magana amma
ban kula shi ba.

Har bakin kofar gida ya rako ni inda yah Sadeeq da Yah Mubarak ke zaune suna fira,
da gani na Sadeeq ya hade rai kamar ya hangi mutuwa, tasowa yai ya nufo mu kan ya
karaso na shige gida ban san ya ya kare da mai bin nawa ba.

Koda shiga na gida Ammi ta hau yin sababi Momy na kare min nan na barsu nai cikin
daki na inda na samu Fadeela na ta sharbar baccin ta. Jiddah na zaune na chat
Khadija kuma na ninke kaya.

Bayan na cire mayafina na zauna kusa da Khadija ina taya ta ninkin kayan

Jiddah ce ke cewa "yau fa aunty Bilkeesu zata zo".

Khadija tace "au haba na dauka sai ranar Sallah"

"A a yau ne" ta bata amsa

* * * * * * * * *
Yau take sallah bikin daya rana gidan mu cike yake da yan uwa da abokan arziki da
makota, anci ansha yara nata har kokin su. Wa'inda suka san inna da dadewa suna ta
taya ta murnar bayyanar diyar ta.

AUNTY balki sai tsokana ta take wai yayan su zai kamani.
Little Easha ce ta shigo tace "aunty Siddeeqah yah Sadeeq na kiran ki"

"To" nace amma ban tashi a lokacin ba sai da na gama shan kanshi na

Ina ta raba mutane har na wuto falon. Shima tsakar gidan cike yake da mutane suna
cin abinci gunin burgewa.

Dakin yah Sadeeq na nufa bayan nayi sallama ai min izinin shiga na shiga.

Tasowa yai ya maida kofar ya rufe kana ya kama hannu na ya zaunar dani bakin
katifar sa yace " na gaji ne shine na kira ki ki mun tausa".

Dago kai nai muka hada ido ya daga min gira gajeran wando ne a jikin sa sai rigar
shan iska wato bes fuskar sa kuwa dauke take da saje ga dan gemu ya aje gunin
burgewa.

Kwanciya yai yace " fara nana " ido na zaro waje nace "yaya me zan fara kuma?
Wallahi ban iya ba"

Tashi yai ya zauna yace "to shikenan bari na gwada miki inyaso sai ki min yadda nai
miki ".

Da sauri nace na iya ba sai ya min ba amma yace "Allahn kashe sa sai ya gwada min"

Ya na iya haka ya Sadeeq yai ta jagwalgwala ni, tun yana yi cikin hankalin sa har
ya fara fita hayyacin sa dan kokari yake ya rabani da kayan jiki na.

Kuka na sa masa ina magiya akan ya rabu dani " ganin haka yasa ya sauka daga kai na
yai gefe idon sa a rufe yana jin marar sa na murda masa, take ya fara juyi yana
kiran sunan Allah, yanzu na fahimci dalilin wannan ciwan na yah Sadeeq da tun ina
karama naga yana yi, amma gaskiya bazan iya basa kaina a wannan halin ba, ganin
ciwan nasa na kara tsanan ta yasa na mike da hanzari na fita daga dakin, a tsakar
gida na hadu da Ammi, ta ganni kamar bana cikin hayyaci na tace "lafiyan ki kuwa
duk kin sukurkuce?"

Nace "Ammi ba lafiya ba yah Sadeeq ne gayican a daki sai hankoran mutuwa yake".

Ban gama rufe baki ba Ammi ta nufi dakin sa da sauri.

Ni kuma cikin hanzari na karasa falo, lokacin mutane sun ragu sosai a falon Cikin
tashin hankali nace "Momy yah Sadeeq fa baida lafiya gayi can cikin wani hali".

Duk da tausayin Sadeeq ya kamata amma sai tace "shi ya sani ita babu ruwan ta "

Inna ce tai ta mata fada da kyar taje dakin sa, amma tana ganin sa taji yayi
bala'in bata tausayi.

Mubarak Ammi ta kira ya kama shi akasa a mota Ammi da aunty Balki suka shiga don su
kai shi asbiti. Suna zuwa aka amshe su cikin kulawa aka kai Sadeeq dakin da ake
duba mara lafiya kai ka ce baya numfashi ne, bayan komai ya lafa Likatan yazo inda
su Ammi ke zaune yace ta same shi a office.

Zaune take kan kujera likitan yai mata bayani kamar haka "Hajiya gaskiya idan ba so
kuke ku salwantar da rayuwar yaron ku ba to kuyi masa aure dan banga dalilin da
zaku aje matashi kamar wannan babu mata ba, ina tunanin ma ya girmeni, amma ni
yanzu haka ina da mata da yarana guda biyu, kuma ba wannan ne karo ne farko da yake
yin irin wannan ba, magunguna yake sha da zaran yaji irin yanayin, to ahalin yanzu
ya ruga ya kai makura wa'innan magungunan sun daina masa aiki, aurar dashi ne
mafita gaskiya ".
Kalaman dakta ba karamin rikita Ammi sukai ba, abinda yafi tsaya mata arai shine da
doktan yace" zasu iya rasa shi" tabbas dole ta dauki mataki dan bazata zura ido
haka ya faru ba, ta gama yanke hukuncin tana komawa gida zata kira Daddy ayi
maganar tarewa.

Haka kuwa akai Ammi na zuwa gida ta kira sa a waya ta sanar mishi, ba tare da kowa
ya sani ba yace "to shikenan zai shigo nan da kwana biyu su fara shirye shirye"

Bayan kwana biyu Sadeeq ya murmure sai dai ya dan fada kuma yayi wani iri dashi,
yasha aiko Samaheer ta kirani sai nai watsi dasu, dan badani za'a dunga tsanan cewa
ba

Yau ne Daddy zai zo sai shirye shiryen hada Abinci Ammi keyi Momy na taya ta.

Bayan Daddy yazo sun tsaida magana akan nan da sati buyu zan tare, sunce daga baya
a saka ranar bikin Khadijan, amma kuma Ammi ta roki Alfarma akan tanaso ta kaini
naga mahaifina kamin lokacin bikin, sosai Daddy yaji dadi kuma yayi farinciki da
kanwar sa tayi wannan tunanin.

Wata ranar Juma'a muka shirya, Ammi tace naje na fada ma Yah Sadeeq dan shi zai kai
mu, koda nagan sa ba karamin tausaya masa nai ba saboda yadda ya zama wani iri
kamar ba yah Sadeeq dan gayu da kwalisa ba, nesa dashi na tsaya nace "Ammi tace
idan ka shirya kazo ka kai mu"

Ban jira amsar sa ba nayo waje abi na

Unguwar barnawa a bakin wani katon farin get yah Sadeeq ke danna hon can mai gadi
ya leko ganin bakin fuska ya ce su waye anan, koda yaji Muryar Ammi tayi magana
tace "Nice Hajiya Amina ce" take ya shaida ta yana fadin "Allahu akbar Hajiya ashe
zamu sake haduwa".

Bude mana get din yai muka sulala ciki

A dai dai lokacin wani dattijon mutum mai sanye da manyan kaya ya fito daga motar
sa ganin bakuwar mota a cikin gidan sa yasa yai turus, Jim kadan ni da Ammi da
Sadeeq muka fito, ido na ya sauka akan kyakkyawan dattijon da nike kyauta ta zaton
shine mahaifina, nuna mu ya shiga yi yana daga hannu sai ya bude baki yai magana
sai ya kasa, addu'ar neman tsari yai ta karantawa a cikin zuciyarsa kamin ya ce
"Amina"

Ido cikin ido Ammi ta kallesa tace "Suleiman".

A kuma dai dai lokacin wata bushash-shiyar mata ta fito ganin mu tare da Abba na
yasa ta cire dan kwalin ta ta fara ihu tana kururuwa cewa take "ta shiga uku yau
asirin ta ya tonu Amina da Sulaiman sun hadu". kuma boka yace " muddin suka hadu to
fa asirin kanta zai koma haka dai tai ta simbatu sai yaran gidan duk gasu sun fito,
sunji uwar su na hauka.

Koda na daga kaina wa zan gani senior Jamlah ce rike da wannan me haukar tana daura
mata dan kwalin da ta kwance.

Kallon Abban mu nayi sai naga yana kama da Jamlah, a cikin zuciya ta nake cewa
"kenan Jamlah blood sister na ce shiyasa tun a makaranta naji na tsane ta, ashe ba
banza ba mamar su ce ta tarwatsa min farinciki na ta hanani tasowa a gaban iyaye
na"

Take Abban mu yai waya da masu kama mahaukata yace "an sumu a gidan sa".
Babu bata lokaci sai ga masu tafiyar da ita su zo, yaran ta guda biyar sai kuka
suke Abba yace "duk wanda zai bita ya bita ga hanya nan" yana gama fadar haka ya ce
"Amina kuzo mu shiga daga ciki "

NI DA YAYA SADEEQ kuwa kamar wa'inda ruwa ya cisu dan mamaki, wato dai inda ranka
baka daina kallon abun al'ajabi ba, kuma Allah ba Azzalumi bane sai dai bawan da ya
zalincin kansa.

A wani kayataccan falo muka zauna da ganin Abban mu yana cikin faran ciki dan ya
kasa zaune ya kasa tsaye.

Jamlah ce ta shigo da yan kannan ta na biye da ita sai kuka suke kamar wa'inda
akaiwa mutuwa, Abba ne ya daka musu tsawan yace "wai bana ce muku duk wanda bazai
zauna ba ya bita? abinda ta Shuka ne ya koma kanta, kunga dole ta girbe shi. kuma
dama ramin mugunta ka gina sa daidai da kai saboda wataran kaine zaka fada".

Sai a lokacin Jamlah ta lura dani, da alamar tayi mamakin gani na tace "Siddeeqah
kece"

Ban bata amsa ba Abba yace" kunsan Juna ne?"

Ammi tace" eh duka daliban mu ne a makarantar Jibya ".

Kallon Jamlah Abba yai yace" gata nan kanwar ku ce sa'ar Sajida ce ".

Da mamaki ta kalli Abban mu dan ita tun da take a cikin gidan nan bata taba jin
anyi labari ko makamancin wannan ba.

Ya nayin ta ya nuna bata fahimta ba don haka Abba ya gyara zama ya shiga basu
labarin duk abun da ya faru, sunji babu dadi kuma sunji mahaifiyar su bata kyauta
ba, hakuri suka shiga bawa Ammi harda Abba akan ta yafe musu tace "kada su damu
komai ya wuce".

ABBA ya bukaci yaji labarin abinda ya faru lokacin da yaga ta fito zata bar gidan.

Take Ammi ta shiga labarta masa bata boye masa komai ba har labarin auran ta da
Alhaji Imran ta basa.

Yaji babu dadi amma basu isa su gujema kaddarar ubangiji da tazo a rubuce ba .

Da zamu tafi Abba ya bukaci a barni amma nace "ni bazan zauna ba sai da Ammi na".

Abba yaji babu dadi hakan yasa yace "to shikenan Kuje zan zo da daddare insha Allah
"

Da daddare Abba na yazo kamar yadda yai alkawari, anan cikin baranda akai mai
shimfida ya zauna inda suke tattaunawa da Daddy yai ta basu hakuri akan abinda ya
faru, kuma Daddyn ya hakura saboda sun san ba halinshi bane kuma Ammi tai musu
bayanin abunda ya faru da ta dawo.

Bayan Inna tazo suka gaisa nan ma hakurin yai ta bata tace "babu komai ya wuce
tunda ba'a cikin yaiyacin sa yai ba".

Bayan Inna ta koma ciki Abba ya kara gyara zama yace "dama kuma alfarma nike so na
kuma roka"

Daddy yace "alfarma kuma Alhaji Suleiman ai ka wuce neman Alfarma fadi kawai kanka
tsaye"
"dama inaso na maida Amina dakin ta ne"

Daddy yace "madallah haka akeso naji dadi sosai, amma nan da yaushe kake so ka
maida ta?"

ABBA yace "ai ba wani lokaci za'a dauka ba nan da kwana biyu ma yayi, sai aiyi
bikin Siddeeqah tana dakin ta itama Siddeeqan nasan zatai farinciki matuka"

"dan dakata ina zuwa" Daddy ya fad'a kana ya Mike, wurin kanwar tasa yaje suka
shawarta kana ya dawo gurin Abba na suka Kare magana, a take a gurin Abba ya biya
Sadaki, aka tsaida daurin aure ranar litinin.

Da ranar litinin tazo aka daura auran Ammi da Abba kuma a ranar Ammi ta tare da
yaran ta, wato little Easha Dady karami Fadeela Jiddah dan ita ma tace Ammi zata bi
sai kuma ni.

Gidan Abba na gida ne mai girman gaske bangare-bangare ba ruwan wani da wani, bayan
wasu yan kwanaki a cikin gidan mun dan fahimci Juna da su Jamlah sukan zo bangaren
mu ayi fira, ga maganar biki na ta taso gadan gadan dan bai wuce saura kwana goma
ba. Sosai Ammi ke bani magun-guna ga wanka da lalle da ake min akai akai, ana saura
sati daya Momy ta aiko mubarak yazo ya tafi dani gurin wata Hajiya kamshi aka
kaini, kwana na uku a gurin ta ana gyara ni, kar kuso kuga yadda na koma, duk da
abubuwa sun zo min a kurarran lokaci, ban samu gyaran da ya dace aiwa amare
completeba amma na hadu in ka ganni bazaka gane ni ba, indai ba kamin farin sani
bane dan na hadu nayi kyau iya kyau fatar jiki na tayi laushi ga haske da sheki
gunin ban sha'awa.

Zaune nike da su Sadiya, magana suke akan dinner din da zasuyi ga kamu da Arabian
night ni dai duk jin su nike, saida suka gama tsaf na ce "kun gama?". Kanwata
Sajida ce ta daga min gira Alamar "eh".

Nace "lalle kam kuna ruwa danni wallahi babu wata bidi'ar da za'ai, idan bacci kuke
gwara ku farka, dan walima ce kawai za'a ita ma kuma sai bayan na tare".

Ina gama fadar haka na tashi na barsu suna ta surutu wai ban isa ba. Su wannan ka
kalan basu sanshi ba

Ana saura kwana biyu tarewa Yah Sadeeq yazo gidan mu, inda ya aiko kanwata Hannatu
da muke uba daya ta kira ni,
A falon saukar baki na same shi har yanzu bai gama murmurewa ba, tausayin sa ya
kamani, sai naji zan zauna dashi kuma zan masa biyayya ko dan farincikin iyayen mu
ya daure, bayan na gaishe shi na zauna dan nesa dashi.

tashi yai ya matso kusa dani yana cewa "ke wai dodo na koma miki ne kike gudu na?
dama nazo ne na tambaye ki naji ko akwai wani events da zakuyi".

Kai na a kasa nace "babu wata bidi'ar da zanyi, walima ce itama sai bayan an kaini
za'ia".

"to" yace yana mai jinjina wannan tsarin nawa.

Washe gari mai fulawa tazo ta mana amma ni ja nace ai min tayi kyau sosai abinka da
farar mace, kuma a daran ranar aka sani a lalle.

Wa shegari ta kama asabar kuma yaune tarewa ta gidan mu cike yake makil da jama'ar
Ammi har yan Katsina da suke mutunci da Ammi sunzo, haka dangin mahaifina suma
sunzo gidan dai ya cika makil masha Allah amma babu wani kida da akai kaya kuwa na
canza wannan na saka wancan ga sarkar gwal da Abba na ya siya min mai tsadar gaske,
biki yayi biki. Ammi ma sai shiga take tana fita, abun dai ba'a cewa komai sai
masha Allah anyi komai cikin tsari da burgewa. Harda yan makarantar mu sunzo, nayi
mamaki da na gansu harda senior din mu, ashe duk Aunty Jamlah ce ta gaiyato su.

Da dare yai da misalin karfe 8:2 pm durkushe nike gaban Abba da Ammi nasiha suke
min mai ratsa zuciya, kaina a lullube cikin alkabba mai ruwan danyan gwall kayan da
nasa na ciki kuma farin leshi ne mai kyau da tsadan gaske ga kamshi sai tashi yake
ni kaina nasan na hadu.

Bayan an gama min nasiha kannan Abba na da wasu kawayan Ammi suka tasani gaba sai
kerarran gidan Sadeeq da yake a nan cikin sabuwar unguwar mu'azu, ginin gidan na
zamani ne haka adon gidan ma. Ban gare ne guda buyu wato daya nasa daya nawa. Goggo
Abida tace "nayi bismillah na shiga da kafar dama "

Har bedroom room dina suka kaini wanda ya gaji da haduwa komai na cikin dakin pink
ne hatta da fentin dakin ma ga wasu akwatuna lodi lodi dana gani a here. wannan
pink guda goma sha biyu wannan ja guda shida wannan me ruwan kasan guda ba kawai,
nayi matukar mamaki dana gansu ko duk na waye?

Basu wani jima ba akace su fito a maida su dare na yi harda su Khadija aka tarkata
aka tafi ya rage sai ni kadai ji na nike wani iri,

Tambayar kaina na shiga yi, Wai yanzu sabuwar rayuwa ce zanyi fa da Wanda bai so na
da kauna ta, nasan bani yake so ba gangar jikina yake so, kuma nasan daya samu
abunda yake so zai rabu dani, hawaye ne masu zafi suke zubar min, tunanin maganar
sa ya fado min arai na cewa" na fara tunanin yadda zan rubuta littafi mai suna NI
DA YAYA SADEEQ aduk sanda na tsinci kaina a gidan sa" tabbas lokacin yayi yanzu
Allah yasa farinciki zan rubuta.

Comment
Vote
Share
NI DA YAYA SADEEQ

•●♥ ‫•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم‬

No editing

Chapter 34

_______bayan wasu shekaru. Zaman aure na nike mai kyau da tsafta da kuma tsantsar
so da kulawa da junan mu, alhamdu lillah na kammala secondary school di na , amma
ban samu na cigaba ba, saboda yah Sadeeq irin mazajannan ne masu bukatar iyalan su
a kusa dasu, kuma yace "mai zanyi da karatu mai zurfi indai zan karanta na rubuta
kuma na fadi a fahimta nima idan an fada min na fahimta ai shikenan" .

Mun samu fahimtar juna sosai tsakani na da yah Sadeeq zan iya cewa tundaga ranar da
aka kaini har kawo yanzu da nike magana baiyi abunda zai cusguna min da gangan ba,
saida bisa rashin sani da kuskure wanda dama dan Adam tara yake bai cika goma ba,
yah Sadeeq mutum ne mai saukin kai da tausayin na kasa dashi yanzu haka mun bude
gidauniyar da ake temakawa marayu da gajiyayyu. Ya rike mukamai da dama a bangaran
aikin sa yanzu haka shine kwamishinan yan sanda na nan jahar kaduna, mun haifi yara
yan biyu duka maza shekarun su uku yanzu, Sunan Abba da Daddy aka sa musu, saboda
haka muke kiran Abba da Sudais Daddy kuma muke ce mai Taufeeq

Anyi auran Khadija da Yah Mubarak inda suke da yara biyu duka mata, kuma sun koma
zama a Dubai, karkashin wani kamfani da suka dauke shi

Sai Ummi da ta auri wani ma'aikacin Jarida, itama ta haifi dan ta namiji
Fadeela kuwa yah Farooq take aure sun haifi yara uku maza biyu mace daya

Sai Jiddah da take auran Maheer wanda sun hadu ne a wajen bikin wata kawar Jiddan
yayin da Maheer din shine babban abokin ango sun haifi diya mace

Tsaye muke a filin buga ball din. NI DA YAYA SADEEQ ne sai yaran mu da muke ta guje
guje cikin so da kaunar junan mu yah Sadeeq na wurga ma kallon ya cafe da hannu
yana dariya ya iso gareni ya shiga raira min wakar "zan rayu da ke zan mutu dake a
abadan dani da ke zamu zauna" . ✍️

Comment
Vote
Follow
Share

* * * * * * * * * *

Tammat bi hamdulla Alhamdu lillah duka duka anan na kawo karshen littafi na mai
suna NI DA YAYA SADEEQ ina rokon Allah ya yafe min abunda na rubuta bisa kuskure
wanda kuma nayi dai-dai Allah ya bani lada

Domin yin korafi ko kuma sharhi ko yabawa marubuciyar ko kuma bata shawara za'a iya
yin magana da ita ta whatsapp only whatsapp ku TunTuben a wadannan numbobin.

Siddiqahtulkhaireey Yahya
+966591512794

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment