You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng KULSUM




3




Littafin


SUMAYYAHABDULKADIR
takorikabara@gmail.com



SADAUKARWA
Ga dukkan matan da ke fama da lalurar 'nocturnal enuresis'(fitsarin kwance) a gidan
aure.

GODIYA
Godiya ta musamman ga Nura Sada Nasimat sabida jimirinsa na bin rubutuna kafin
bugawa da bada shawarwari. Allah ya raya mana zuri’a rayuwa mai albarka.

JINJINA
Ga daukacin mambobin TAKORI'S ONLINE FORUM, littafin Kulsum ya jinjina muku, ni da
ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source
of inspiration.

GARGADI
Banyar da a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ba tare da iznina
ba, tun daga radio, facebook, whatsappp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya
doka ne, kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'I Wali.

KULSUM-3
Har tana tuntube, saura kadan ta fadi… ta samu ta rike marikin kofar ofishin ta
yunkura ta fice da mugun sauri. Ba ta tsaya a ko’ina ba sai a jikin motar Taufeeq.
Babu inda ba ya rawa a jikin ta, ta tabbata Turaki ne ta gani ba mai kama da shi
ba. Fatan ta a lokacin kawai shi ne ta hango fitowar Taufeeq su bar asibitin
gabadaya, amma har aka shafe mintuna goma babu Taufeeq ba mai kama da shi.
Sai can ta hango su su biyu suna tahowa a tare, da shi da Turakin, sai
waige-waige suke yi. Rasa inda za ta sa kanta ta yi, sai kawai ta daddage ta taka
da gudu ta boye a bayan wasu shuke-shuke. Daga inda ta ke tana iya hango su har
cikin motar Taufeeq suke dubawa, daga baya Turaki ya juya cikin tafiyar nan tasa ta
‘ya’yan saraki ya koma cikin asibitin, Taufeeq kuma ya dauko motar sa ya tuko a
hankali yana bin gefen hanya da idanunsa, tana iya hango tashin hankalin da ke
shimfide baro-baro a kan fuskar sa.
Sai da ta ga ficewar sa daga get din asibitin, sannan ta fito daga bayan shuke-
shuken ta zo bakin get domin ta fice ta tari taxi zuwa Victoria Island gidan
Sakeenah. Tana zuwa get masu gadin suka taso suka kulle get, suka koma gefe suka
fuske, suna kiraye-kirayen waya.
Wani mugun takaici ya kama Kulsum, ko kallon arziki ba su yi mata ba, amma sun
kulle kofa sun hana ta ficewa. Ba'a jima ba ta ga mota kirar Acura na fitowa daga
cikin asibitin zuwa inda suke. Tun daga nesa ta gane mai tukin nan cikin tsananin
nutsuwa kamar bai son taka kasa. TURAKI ne.
A wannan lokacin ba gilashi a idon sa, wannan ya ba ta damar gane shi sosai. Da
gane irin canjawar da ya yi. Juyawa ta yi ta karasa gaban masu gadin ta soma rokon
su su bude mata kofa. Ko daga ido su kalle ta ba su yi ba, har motar Turaki ta iso
ta yi parking a gaban ta kamar za ta take mata ‘yan yatsun kafar ta.
Zama ya yi cikin motar yana kare mata kallo. Ga wani makalallen murmushi a
gefen bakin sa. Ya bude motar ya fito gaba-gadi, rataye da falmaran din bakaken
suit din jikin shi a kafadun sa. Gaban ta ya zo ya tsaya suna fuskantar juna.
Kallon ta kawai yake da idanun nan nasa da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a
ido biyu. Yayin da ta yi kicin-kicin da fuska, za ka rantse da Allah bata taba
sanin fuskar da ke tsaye gaban ta ba a tsayin rayuwar ta.
“Malam lafiya?” Kulsum ta yi tambayar, muryar ta na rawa, tana mai dojewa
kallon tsakiyar lumsassun idanun sa.
“Na zo fita ka sa an tare ni, na ci bashin ku ban biya ba ne?”
Ba ta yi aune ba ta ji hannun ta cikin na Turaki, shidewa ta kusan yi na wucin
gadi, kafin ta tantance me ke faruwa, ya ja ta tana tirjewa ya bude motar shi ya
sanya ta, tare da rufe kofar da key din hannun sa. Ya zagaya ya shiga mazaunin sa
ya tashi motar. Masu gadin suka wangale masa kofa ya fice, suna daga masa hannu
cikin girmamawa.
Tafiya kawai yake bisa shimfidaddun titunan garin Lagos ba tare da Kulsum ta
san inda aka nufa da ita ba.
“Malam sace ni za ka yi? Malam ina ruwan ka da ni ne? A ina ka sanni? Malam ni
matar aure ce ko ba ka gan ni tare da miji na bane?”.
Tambayoyin Kulsum kenan ga Turaki, cikin rawar muryar da ke gab da rushewa da
kuka.
Idan stiyarin motar ya ba ta amsa, to mai tukin motar ma ya ba ta, inda ta ke
wannan bai kalla ba, sai sharara gudu yake, amma makalallen murmushin da ke kan
tattausar fatar bakin sa ya kasa bacewa.
Kulsum ta soma bugun gilashin motar da duka hannayen ta, fatan ta gilashin ya
fashe ko da zai yanke ta ne, ta yi ihun da mutane za su ji su kawo mata dauki. Amma
ta lura gilashin motar ko sound ba ya badawa kuma ko za ta shekara tana bugunsa ba
zai fashe ba.
Kawai sai ta fashe da kuka tana kiran Goggon ta da Baffan ta. Abin da ya yi
matukar bai wa Turaki dariya. Ya dube ta da lallausar murmushi ta gefen lumsassun
idanun sa, cikin rada ya ce,
“Saura Batulu da Umma!”.
Idanun ta cike da kuka, amma hararar shi ta ke, daidai lokacin da suka kawo
wani check-point na ‘yan sanda. Daga murya ta yi sosai tana kwarara ihu ba ta san
cewa murya ba ta fita daga gilashin ba. Sai ta daga hannuwa tana yi wa ‘yan sanda
alamar da ta sa daya daga cikin su ya zo jikin motar tare da kwankwasa gilassan,
Turaki ya sauke glass a hankali ya kuma nuna masa katin shaida (I.D card) na
shaidar aikin sa, nan da nan dan sandan ya yi baya yana daga masa hannu, ya yi sama
da gilassan motar da sauri ya sake shan round ya shiga unguwar Ikoyi.
Kulsumu ba ta bar kuka ba, don ta gane in ma sata ce Turaki ya gama sace ta.
Sun wuce kyawawan gidaje kamar guda biyar kafin su shiga wani kyakkyawan lodge mai
hawa daya. Maigadi ya zo ya bude, Turaki ta zura hancin motar sa cikin gidan.
Ya yi parking a rumfar adana motoci wadda ke dauke da wasu motocin guda biyu,
ya kashe motar tare da sakin ajiyar zuciya. Ya dubi Kulsumu wadda ta ki dagowa daga
cinyoyin ta balle ta san inda ya kawo ta. Sautin kukan ta kadai ka ke ji a motar,
kamar wadda aka gaya wa sakon mutuwar iyayen ta.
Kirjin sa ne kawai yake dagawa yana sauka da sauri-da-sauri. Wani lokacin
excitement zai iya haifar da bugun zuciya. Mutum ya fadi ya mutu farat daya. To
hakan ce ta faru ga Turaki, wanda ke ganin komai da ke faruwa da shi yau kamar a
mafarki… wai shi ne da Kulsumu a gabansa!
Idan mafarki yake yana rokon Allah kada ya farkar da shi daga wannan mafarkin,
har sai ya ga karshen sa, har sai ya gan shi tare da Kulsum matsayin ma’aurata a
karo na biyu.
Ashe duk mahaukacin neman nan da yake wa Kulsumu tana cikin kasar Nigeria, a
garin da yake yawan rayuwa? Allah shi ne shaida kan babu abinda ya wahalar da shi a
duniya irin neman da yai wa Kulsumu, shekaru dai-dai har guda hudu. Shi Allah da
yake Gafurur-Raheem ne, yau ga shi ya tankado keyar Kulsumu ya kawo mishi ita har
cikin ofishin sa. Shin shi wane irin wawa ne da zai yi saken da za ta sake kufce
masa???
“If you are done with the cry (idan kin gama kukan) ki wuce mu karasa ciki”.
A matukar fusace Kulsum ta dago ta dube shi, idanun ta a rufe sabida bacin rai,
ta ce,
“Da wacce hujja zan bi ka inda ban sani ba? Me ye hadin ka da ni? A ina ka san
ni, ko na yi maka kama da ‘yammatan da ake daukowa bisa titi a garin Legas a kawo
su guest house ne?”
Kyabe baki ya yi, ya ce, “Ni ma ban san me ye hadin nawa da ke ba, kuma ba ki
yi kama da ‘yammatan bisa titi ba, sannan nan ba guest house ba ne, gidan mutane
ne, hujja ta ta cewa ki bi ni ciki mu zauna mu yi magana ta nutsuwa ita ce; kin yi
min kama da matata ne, matar da ban saki ba har gobe, amma na neme ta na rasa”.
Ya karasa maganar da kasalallen murmushin sa na gefen baki.
“Ina so in tabbatar ne, I just want to confirm ko Kulsumu na ce wannan....I
just want to confirm idan matata UmmuKulsum da na rasa nake nema ce… I just want to
confirm idan reaction dinta saboda gani na a inda ba ta yi tsammani ba, yana nufin
itama ta gane ni ne take pretending....ko kuwa wani abin ne daban ya firgita ta ta
ke gudu tana neman mafaka…”.

Kafin ya rufe baki Kulsumu ta amsa, “ni ban gane ka ba, babu wani sani da na yi
maka. Ban sanka ba, ban taba ganin ka ba, sannan ni matar aure ce, kuma tare da
mijina ka gan ni, amma ka sa aka rufe min kofa saboda tozarci, saboda ka sato ni ka
kawo ni guest house. To tsakani na da kai Li’ilafi dubu”.
Turaki ya yi wani murmushi, wani tattausan murmushi da rabonsa da yin emotional
murmushi irin sa ba zai iya tunawa ba. He salute her courage! Yau ji yake babu
wanda ya kai shi sa’a a duniya, babu wanda ya kai shi samun cikar buri. Ashe zai ga
Kulsumu komai daren dadewa! Sai dai kuma watakila ganin nata ya zo at a wrong time,
idan har abin da ta ke fadi gaskiya ne na cewa (wanda suke tare mijin ta ne). Idan
har wannan ikirarin nata gaskiya ne, shi ya ya zai yi da rayuwar sa?
Saboda ita ne har yau bai kara aure ba. Saboda ita ne har yau babu diya macen
da ke burge shi. Saboda ita ne yake jin zai iya kare rayuwar sa single idan har bai
same ta ba. Ashe ita tuni ta manta shi, she have move on tare da wanin sa. A zahiri
bai kamata ya ga laifin ta ba, amma sai ya ji gabadaya duniyar na juya masa. Idan
har da gaske matar auren ce, ya san hatta wannan kebewar da ya yi da ita a cikin
motar sa haramun ne, sai dai ji yake in wannan shi ne haramun din da zai halaka
shi… ba zai bari ta sake kubuce masa ba.
“Look Ummukulsum, duka cikin mu nan ba yaro karami, ki yi ta pretending din ki
ba zan hana ki ba, amma in kin ga na barki kin bar gidan nan, to kin fito mun shiga
ciki ne, mun zauna mun yi magana, na fahimce ki kin fahimce ni".
Kulsumu cikin shesshekar kuka, ta ce, “Ta ya ya zan yarda in bi ka ba ni da
masaniyar ko za ka cutar da ni? Ta ya ya ka ke tunanin zan yarda in shiga inda daga
ni sai kai babu muharrami a tsakanin mu, alhalin na kasance matar aure?”
Turaki ya lumshe idon sa na sakan biyu ba tare da ya bude ba, kalmar auren nan
tata da take ambata ta kasa yi masa dadi, ta kasa zauna masa a rai, haka ta kasa
daina gasa zuciyar sa, sannan ya kasa yarda da ita, ya ce,
“ki sa a ranki cewa, kina cikin amana ta, ke da auren naki. Amanar da idan na
ci ta sai Allah ya saka miki. Ki yarda komai lalacewar duniya har gobe akwai sauran
masu amana da kokarin cika alkawari”.
Kulsumu ta ce, “babu ruwana da amanar ka, ko me za ka gaya min ka gaya min
yanzu ka sallame ni in tafi, ni dai na san ban san ka ba, ban taba ganin ka ba ko a
hanya. Kawai ka ga matar mutane a titi ka sako ta a mota ta karfi ka dauko ta,
wannan ai cin mutuncin aure da keta haddin dan Adam ne”.
Ba ta rufe baki ba Turaki ya bude motar ya fito, cikin zafin nama ya zagayo ya
bude tata kofar, kama duka hannayen ta yayi ya dunkule a cikin nasa. Sannan ya
janyo ta ta karfi daga motar.
“Ni ma ban ce ki ce kin san ni ba, mu je a ba ki san nin ba, ni ma ai ban sanki
ba Kulsum, amma dole mu yi magana ni da ke”.
A haka suka shiga falon gidan, falo ne tsararre english parlour, bata ankara ba
ta ga ya sa mukulli ya rufe kofar ya jefa mukullin cikin aljihun trouser din sa.
A tsaye Kulsumu ta tsaya ta ki zama, Turaki ya tako har gaban ta ya tsaya
hannayen sa duka biyu zube cikin aljihu kamar yadda yake a al'adar sa. Ya yi
kokarin kallon tsakiyar idanun ta ya sakar mata signal. Ta dauke kai, amma hatta
hantar cikin ta kadawa ta ke yi. Yana da wani irin effect (tasiri) a kan ta tun
zamanin kuruciyar ta. Ta yadda idan ya kasance a gaban ta, ko ya gifta ta gaban ta
hatta hantar cikin ta rawa take yi. Yau da ya kasance a gaban ta cikin wani sabon
yanayi da bata taba tsammata daga gare shi ba, babu inda ba ya rawrawa a jikin ta,
including tsokar zuciyar ta.
"Ummukulsum yaya rayuwa? Yaya bayan saduwa? What is special a bayan rabuwar
mu?"
Bata bashi amsa ba, illa sunkuyar da kan ta da ta yi. Kamshin one man show ya
cika hancin ta. Turaki ya kara takowa zuwa gaban ta, space din dake tsakanin su bai
fi taku biyu ba. Ya ce.
"Aka ce ba kya kasar? Aka yi ta wahalar da ni? Ashe kina cikin kasar nan
Kulsumu? Kin samu rayuwa yadda kike son ta kin manta da ni ko, ni ina can ina ta
wahalar neman ki lungu da sako, , Kulsum tell me about you ko dan yaya ne. I'm
extremely intrigued! Me ya kawo ki Lagos?"
Wannan karon ne ta dago kai ta dube shi cikin ido. Kai tsaye ta gatsine fuska
ta ce "AURE! Aure ne ya kawo ni, ba zan gaji da gaya maka cewa ni matar aure ba ce.
Ka mayar da ni inda ka dauko ni, tun kafin miji na yayi karar ka".
Zuba mata ido ya yi kamar ya hadiye ta. Hannayen ta duka biyu Turaki ya kama
kafin ayi haka ya rungume ta da wata irin azama, wata irin kyakkyawar runguma wadda
ta hade bugun zuciyar su wuri guda, yana sauke numfashi da sauri, yana barin dukkan
excitement din zuciyar sa ya na fita ta cikin numfashin sa.
"Ko waye ya aure ki yayi aure kan aure UmmuKulsumu, ni da baki na ban taba
sakin ki ba..... kuma har abada bazan yi ba! Kuma na rantse sai kin dawo gidan ki
da yardar Ubangijin sammai da kassai. I don't mind your pretendings.... ki cigaba
da yi, shekaru takwas da nayi ina dakon wahalar soyayya baza su tashi a banza
ba..... this is a promise (wannan alkawari ne)".
Kokari take ta zame daga jikin Turaki amma ya ki bata damar hakan. Kawai sai ta
saka masa wani gigitaccen kuka da yasa dolensa ya sake ta, amma bai saki hannun ta
ba, sunkuyawa yayi ya sumbaci goshin ta, karan hancin ta da saman bakin ta, abinda
ya kara gigita Kulsumu, ta fizge daga rikon sa da karfi ta ja da baya tana hararar
sa, tamkar idanun sa fado, murmushi ya yi, ya bude kofar falon suka fita. Bai sake
ce mata komai ba.
Shi da kan sa ya bude mata kofar motar ta shiga, shima ya zaga mazaunin sa ya
zauna, sai da ya kara bata lokaci yana kallon ta da murmushin da bata taba ganin
sa da shi ba. Gabadaya ta canza masa, ta koma masa sabuwar Kulsumu, ba 'yar ficikar
yarinyar da ya aura a kauye ya gudu ya bar ta ba, tana ta sharar hawayen dake gudu
a fuskar ta da gefen mayafin ta. Alamu ne dake nuna zuciyar ta na tono old
memeories masu daci a kan sa da ta dade da binnewa lokaci mai tsaho.
Ya kunna motar ya taka totur din ta, reverse ya yi ya fita daga ma’adanar
motocin ya doshi get cike da kuzari. Maigadi ya bude musu kofa ya hau bisa kwalta
yana jan motar tamkar tayoyin ta sun yi faci, sabida rashin gudun ta.

“Wace unguwa zan kai ki Ma’am?”

“Ka kai ni bus stop zan samu taxi zuwa gida”.
“Wannan ne kuma ba ki isa ba, sai na damka ki hannun solobiyon mijin ki, kamar
yadda na yi masa alkawari”.
Wayar sa ya dauko ya kira lamba ya sa a kunnen sa, tare da saka wayar a
handsfree, tarrr ta ji muryar Taufeeq yana fadin,
“Doctor kun gan ta? Ga mu nan duk hankali a tashe”.
Turaki ya ce, “security sun ganta, muna kan hanya yanzu haka. Fada min address
din naku”.
Tana ji Taufeeq na fadin lambar gidan Aunty Sakeenah da sunan unguwar Victoria
Island. A ranta ta ce, “Shi ke nan tawa ta kare!". Amma a fili ban da kukan bakin
cikin Turaki, ba abin da ta ke da rinannun idanun ta.
Suna sanyo motar cikin get din gidan Aunty Sakeenah gabadaya jama'ar gidan suka
nufo su har Engnr. Farouq. Shi ya bude side din da Kulsumu ke zaune, yayin da
Taufeeq ya bude wa Turaki. Tana fitowa Nasmah da Aunty Sakeenah suka yi kanta suna
kiran sunanta don tabbatar da lafiyar ta. Ba ta tsaya ba, wuce su ta yi dukkan su
ta yi cikin gida da gudu, Aunty Sakeenah ta bi bayanta hankali a tashe.
Taufeeq na bude masa kofar ya fito, inda Taufeeq din ya ba shi hannu, sannan
suka yi musabaha, Taufeeq na ta yi masa godiya, ya ce, “Amma anya Doctor do you
think she is okey?”
Murmushi Turaki ya yi, wanda ya fi kama da na rainin hankali, ya ce, “Lafiyar
ta kalau, na fi kyautata zaton akwai abinda ta gani ne wanda ya hargitsa ta. Amma
tunda kai mijin ta ne ai za ta gaya maka”.
Da haka suka yi sallama, Engnr. Farouq ma na ta yi masa godiya.
Gabadaya suka rufu zuwa cikin gidan, Mujaheed ya ja Nasmah gefe suna magana.
Tsayawa suka yi bakidaya a kanta, kowa da tambayar da yake jefo mata.
“Kulsumu lafiyar ki kalau?” Sakeenah ta fada.
“Ya ya za ki yi min haka Kulsumu? In kai ki asibiti mu shiga ofishin likita,
kawai sai in juyo in neme ki in rasa? Kin daga min hankali yadda ba kya zato, kadan
ya rage jini na ya hau, to ina ki ka shiga cikin asibitin da muka neme ki muka
rasa?” In ji Taufeeq.
“Ku yi mata a hankali, ba kwa ganin kuka ta ke ne? Duk mu kyale ta zuwa ta samu
nutsuwa, please, na tabbata ko mene ne za ta gaya muku”. Cewar Engnr. Farouq.
Da wannan duk suka watse suka bar ta da Taufeeq, ya zauna kusa da ita, ya kira
sunan ta a tausashe,
“Kulsum”.
Ba ta amsa ba, kamar yadda ba ta dago ta kalle shi ba.
Ya dora hannun sa bisa nata, ai da mugun sauri ta janye hannun ta. Abubuwan sun
mata yawa, har suna son fin karfin kwakwalwar ta.
“Wai me ke damunki ne? Are you okey?”
Maimakon ta ba shi amsa, sai ta mike ta nufi toilet, ta shige tare da rufe
kofar da mukulli, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Ya dade a zaune inda ta bar shi cikin matsananciyar damuwar da ya kasa gano ta
inda zai bullo mata.
“Ko dai Kulsum ta yi gamo da aljannu ne?” Wani bangare na zuciyar sa ya
tambaya, a karshe ya ga shawarar Engnr. ita ce abar bi, wato su ba ta lokaci ko
zuwa gobe ne. Yana so ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, amma bai san me zai ce
mata ba, tunda bai san abin da ke damun Kulsum din ba. Don haka ya tashi jikin sa a
sanyaye ya bar dakin zuwa falo, suka hadu dukkan su suna ta tattaunawa a kan
al’amarin, kowa da abin da yake fadi. Sakeenah ta dubi Nasmah kamar ta mare ta, ta
ce,
“Tun farko da izinin wa ki ka dauke ta ku ka fita? Ba ki san amarya taka tsan-
tsan ake da ita lokacin auren ta ba? Yanzu in gamo ta yi me ki ke so na gaya wa
Mum? Da ma ba da son ranta ta yarda ta barta ta zo ba, ta fi so ko mene ne a yi shi
a can Abuja da Gaya”.
Nasmah ta yi narai-narai da ido, “Wallahi Aunty Sakeenah ba ni da laifi, kin
gansu nan, su ne suka kira mu”. Ta fada tana nuna Taufeeq da Mujaheed.
Taufeeq ya dalla mata harara, ya tashi ya bar wurin.
Sakeenah ta ci gaba da yi wa Nasmah fada, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke
fita ba, kan don me za ta biye musu? Tunda ta san gyaran jiki ake mata kuma ba a
barin ango ya ga amarya har sai bayan daurin aure.
Nasmah dai ta karbi laifin ta, Mujaheed shi ne mai bada hakuri, don ya ce shi
Taufeeq tausayi ya ba shi, ya damu ya gan ta sosai, amma su kwantar da hankalin su
insha Allahu babu aljannu a tare da ita, kamar dai yadda likitan da ya kawo ta ya
ce ne, wani abin ta gani ya hargitsa ta.
Cikin dare Nasmah na barci, Kulsum ta tashi ta zauna dungurgur! Ya zama dole ta
nema wa kanta mafita. Mafita daga auren mashayi wanda ba za ta iya ba, ko ita ta fi
kowa halarci a duniya, da kuma kubucewa daga inda Turaki zai sake samun ta. Turaki
daga dukkan alamu bai zo gidan su don ya kawo ta kawai ba, sai don ya ga inda ta
ke. A yayin da ita kuma ba ta ga dalilin hakan ba. Duniyar sa ta riga ta kare a
tata duniyar, ba ta fatan wata mu’amala ta sake hada su ko da ta gaisuwa ce.
Ya riga ya gama playing duk wani game din sa cikin rayuwar ta. Ba ta jin a
yanzu za ta iya sake daukar wani komai kankantar sa. Allah da ya hada Ya riga ya
raba, don hakan ya zama alkhairi a gare ta. Alkhairin da ta ke zaton Taufeeq ne,
ashe shi ma nashi kalubalen har ya fi na Turaki. Shawara ta karshe da ta yanke wa
zuciyar ta shi ne, ta yi nisa da dukkan su, ta tanadi kalaman da Hajiya Nasara za
ta fahimce ta ranar da duk Allah ya sake hada su.
Mikewa ta

Please Login or Register in order to submit comment