You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

falon, sai garden daga wajen kitchen din, mai
shimfide da korran ciyayi daga sama har kasa sun yi wa gidan rumfa ruf, gidan
karami ne sosai kamar sauran gidajen Estate din, sai dai ya ishi dan Adam duk wasu
bukatu na rayuwar sa.
Kwanan su uku ba su je ko’ina ba suna ta fama da fitsarin Kulsumu. Fitsarin da
kamar jira yake su sauka a Reading ya kara ta’azzara. Hutawar da suka yi niyya duk
ba su same ta ba, soyayya an jingine ta a gefe saboda Kulsumun kwata-kwata ba ta
cikin hayyacin ta saboda damuwa da tashin hankali.
Ita babbar damuwarta shi ne Turaki zai tsane ta. Yayin da shi kuma damuwar sa
ita ce damuwar da ta ke jefa kanta a ciki, wadda yake tsananin tsoron kada ta taba
brain dinta, ta jawo wata matsala wadda ta fi ta fitsarin kwance.
Ya kira Dr. Ibrahim Takai kan appointment din su na ganin sa, ya ce za su hadu
a asibitin nasu Turaki, wato Royal Berkshire Hospital ya zo ziyarar aiki ne daga
Illinoise teaching hospital na watanni uku a asibitin koyarwa na garin Reading.

Kulsum ta yi tsai da idanun ta tana kallon Dr. I.M Takai, ta dauka za ta ga
mutum wanda ya manyan ta kamar likitan ta na Lagos, sai ta ga sardidin mijin na
Rayhanah Baban Asma’u matashi tamkar nata mijin. Sun dade suna magana shi da
Turaki, da turancin su mai accent wanda ba duka ta ke fahimta ba. Ya yi mata
tambayoyi masu yawa tana ba shi amsa. Ta kuma gaya masa sunayen magungunan da ta ke
sha a baya, da dukkan treatment din da ta karba daga hannun likitan ta na Lagos.
Dr. Ibrahim ya dube ta sosai, sannan ya ce, “Ina tsammanin kina da karamar
mafitsara ko blocked urethra (mafitsara tosasshiya), zan yi miki test har guda
hudu; na farkourinalysis, inda za mu dauki sample na fitsarinki mu duba infection
acikin sa ko sauran urinary tract infections. Test na biyu da za mu yi shi ne urine
culture, inda za mu tura sample na fitsarin ki zuwa lab don duba ko akwai bacteria
ko yeast a cikin fitsarin ki. Sai test na uku shi ne uroflowmetry, inda za ki yi
fitsari a cikin special funnel da za mu ba ki, mu auna yawan fitsarin da ki ke yi
and how quickly it flows out. Sai test na karshepost-void residual urine
measurement; wannan test din zai nuna yawan fitsarin da yake ragewa a mafitsarar ki
ba tare da ya fito ba duk lokacin da ki ka yi fitsari. Idan muka yi duk wadannan
gwaje-gwaje, za mu gane what are the possible causes na nocturnal enuresis din ki.
Za mu gane blocked urethra ne ko pelvic organ prolapse, ko kuma matsalar daga
structure din mafitsarar ki ta ke (wanda na fi tsammani), ko enlarge prostate ne ko
urinarytract stones ko infection na mafitsara.
Ki ci gaba da non-pharmacological treatment irin na baya, sannan inaso ki gaya
min abubuwa guda hudu.
Karfe nawa ki ke bed -wetting?
Yawan fitsarin da ki ke yi (kadan ne ko mai yawa)?
Yawan abin da ki ke sha kafin kwanciya barci?
Sauran alamomin da ke nuna za ki yi fitsari?
Kulsum ta fada masa duk abin da ya tambaye ta iya sanin ta. Doctor Takai ya ce,
“To yanzu za ki shiga toilet ki ba mu fitsarin ki, mu auna mu gani, sannan
akai lab, gobe sai ku dawo mu ga me result ya nuna”.

Washegari karfe goma na safe suna gaban Dr. Takai, nan ya gaya musu result din
gwaje-gwajensu ya nuna Kulsum na da karamar mafitsara. Za ta sha magunguna masu
karfi ba irin na baya ba na tsawon sati biyu, derifenacin (enablex), oxybutynin
(ditropan), tolterodine (detrol) da kuma trospium chloride. Idan ba ta daina
fitsari tsayin wata guda ba za su dawo. Dole sai an yi surgery. Sunan surgery din
da za'a yi “Bladder augmentation”.
Dr. Takai ya ce, “It’s an operation that makes your bladder larger, which
raises the amount of urine it can hold (aiki ne da ake yi wanda zai kara girman
mafitsarar ki, ya kara yawan fitsarin da za ta iya rikewa)”.
Da wannan suka baro gaban likita Takai bayan Turaki ya sayo duka magungunan da
aka rubuta musu.
Haka kawai Kulsum ke jin wata irin gamsuwa wannan karon da treatment din
gawurtaccen nephrologist Ibrahim Takai, domin kwata-kwata bai yi kusa da wanda ta
samu a Lagos ba. Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Magungunan sun fi na baya
karfi nesa ba kusa ba. Sai da ta yi sati daya ba ta yi fitsari ba ko sau daya da ta
fara shan su. Murna wurin Kulsum abin ba'a cewa komai, amma Turaki kallon ta kawai
yake. As a medical doctor jikin sa yana ba shi karshen ta dole sai an yi surgery
din nan.
Ya koma aikin sa tuni, don haka ita kadai ta ke wuni a gidan, Sajeedah da
Abdul’Ahad sun bar Reading sun koma Manchester inda aka yi wa Abdul’Ahad transfer.
Turaki ya mata alkawarin in hankalin su ya kwanta sun gama da asibiti za su je musu
har Manchester wajen su.
Ilai kuwa bayan kwana goma sai ga shi ta sake yin fitsari, wanda alama ce da ke
nuna cewa, karshen ta surgery zai tabbata. Turaki bai gaza ba wajen karfafa mata
gwiwa kan cewa yana tare da ita cikin kowanne hali, yana son ta a duk yadda ta ke.
Sati hudu suka cika suka koma gaban likita, ko a ranar ma sai da ta yi fitsari,
don haka Dr. Ibrahim Mansur Takai ya sa musu ranar surgery kwanaki biyar masu zuwa.

*****
Ana i gobe surgery din Kulsumu kasa barci ta yi, gani ta ke in ta shiga dakin
tiyata ba za ta fito da sauran numfashi ba. Turakin ta zai zama mallakin wata a
bayan ran ta. Ta yi kuka, ta yi kuka har ta ji babu dadi.
Ko da Turaki ya dawo aiki a ranar ya fahimci ta ci kuka ta gode Allah. Bai yi
kasa a gwiwa ba wajen wanke damuwar ta da nau’ikan soyayyar sa masu tsayawa a zuci.
Da ya fita sai ga shi ya dawo da sinkin adult diaper (pampers din manya) don su
huta da wankin zanin gado, duk da yanzu ba ya taba katifar su sabida water mattress
ce. Dr. Takai ne ya ba shi wannan shawarar ya ce, hakan zai fi musu sauki, after
intercourse din su ta sanya diaper idan non-pharmacological treatment ya ki aiki a
jikin ta.
Kulsum ba ta taba jin madaukakiyar kunya a duniya irin ta yau ba. Wane
embarrassment ne ya wuce miji ya sanya maka diaper? Ta jinjina wa Turaki a zuciyar
ta, ta amince samun kamar sa cikin maza dubu sai an tona. She is indeed among the
luckiest women on earth (tana daga cikin mata masu sa'a a duniya), amma shi din ko
a jikin sa, gaya mata ma yake,
“Ba shi ke nan mun huta da wankin bedsheets ba?”
Ita dai kunya ba ta barta ta ce komai ba. Da idanun sa yake lalubo idon ta
wanda ya cika taf da hawayen tausayin Turaki. Ta fi tausayin shi akan yadda ta ke
tausayawa kanta. Ita ke fitsari, amma shi ke cin wahalar sa. Da suka hada ido ya
daga mata gira, a hankali ta ce,
“Na gode Prince”.
Sai ta fashe da kukan tausayin kanta. Turaki ya janyo ta barin jikin sa yana
fadin.
“In dai diaper ce ta sa min mata kuka, sai a bar ta, babu dole”.
Kulsum ta shafe hawayen ta, a hankali ta ce, "Ba kukan diaper nake ba, kuka
nake don tausayin ka, ka auri wahala... Ka auri kazanta. Yet ba ka taba nuna min
gazawar ka ba. Ba ka taba nuna kyama a gare ni ba. Don Allah Prince ka kara aure...
Wallahi na amince, in ba haka ba sai alhakinka ya hana ni warkewa".
Murmushi Turaki ya yi, ya ce, "Well, mu bari after surgery in ba ki warke din
ba sai ki zabo min mata na aura. Amma ni ba ni da idon kallon mata. Mai fitsarin
kwancen kawai ido na yake iya hangowa".
Za ta iya cewa ba ta taba jin kalmar da ta yi mata dadi a rayuwar ta irin
wannan ba. Ko da kuwa Turaki ya fada ne don ya faranta mata kadai ba don haka abin
yake a zuciyar sa ba.
*****

Washegari aka shiga da Kulsum dakin tiyata. Bayan sun yi wata irin sallama da
mijin ta Turaki 'very emotional'. Ya sumbace ta a goshi da hanci. Ya ce, "Insha
Allah lafiya za ki tashi Kulsum, kuma da yardar Allah wannan shi ne karshen wahalar
ki".

*** *** ***
A rayuwar Dr. Ibrahim Takai, bai taba yin 'surgery' ko 'kidney transplant' an
samu kuskure ba, to haka ma a wannan karon yana kyautata zaton samun nasara a aikin
da ya yi wa Ummu Kulsum. Amma ba za a gane hakan ba sai nan da wata daya. Kulsum za
ta ci gaba da zama a gadon asibiti.
A wannan lokaci jinyar duk wata kulawa da soyayyah Kulsum ta same su daga mijin
ta Turaki. 'The one in million husband', wanda ta ke fatan har a lahira Allah ya
tashe su tare matsayin abokan rayuwar juna.
Bayan 'surgery' da jinyar wata guda, sun ci gaba da zuwa 'check up' a asibitin
'Royal Berkshire' hannun likitan da Dr. Ibrahim Takai ya yi 'referring' din su,
wato Dr. Kennedy baturen Worcaster, shi din 'kidney and bladder specialist' ne da
ake ji da shi a asibitin nasu. Yayin da Ibrahim Takai ya koma Illinoise wajen
Rayhanar sa,bayan ya gama aikin da ya kawo shi Reading.
A duk sanda suka zo 'check up' Dr. Kennedy na fada musu aiki ya yi kyau. Akwai
ci gaba sosai, da taimakon Ubangiji wannan karon Kulsum ta rabu da lalurar
'Nocturnal Enuresis'. Ranar 'check up' din su na karshe likitan ya yi murmushi ya
dube su.
"Congratulations Mr. and Mrs. Abubakar Turaki Abdullahi, your wife is finally
saved from bed-wetting". (Matar ka ta kubuta daga lalurar fitsarin kwance).
Ya kara murmusawa ya ce yana bai wa Dr. Abubakar shawarar ya dauki hutu domin
ya murmure daga jinyar nan da ya sha, su je garin Chelsea su huta.
Dariya Turaki ya yi ya dubi Kulsum, wadda ta sadda kai kasa, hawayen farin ciki
na zuba daga idanun ta. A haka Turaki ya kama hannunta suka bar gaban likita bayan
ya yi masa godiya sosai.

*** *** ***
"Shi ke nan yanzu kuma sai mu fara shirin zuwan amarya tunda uwargida ta
warke?" Turaki ya fada a lokacin da ya zura mukulli yana bude kofar 'apartment'
dinsu.
Kulsum ta yi gumm! Kamar ba ta ji shi ba.
Ya sake maimaita abin da ya fada, ta dauke kai ta shige dakin ta. Wanka ta yi,
ta yi kwalliya irin wadda tun zuwansu U.K ba ta taba yi ba saboda rashin kwanciyar
hankali. Ta yi alkawarin ingantawa Turaki daren yau da dukkan iyawar ta, domin nuna
masa godiyar ta ga dumbin lkhairin sa da soyayyarsa gare ta.
Wata irin doguwar riga ta saka mai bin jiki da aka yi da yadin 'velvet', ta bi
fatar jikin ta ta kwanta lambam. An tsaga ta tun daga idon sawu har zuwa gwiwa ta
yadda santala-santalan kafafunta suka fito 'freely' in tana tafiya. Ta feshe
jikinta da turaren nan na mata mai dadin kamshi COOL WATER (Davidoff). Gashin
kanta da ba wani yawa ne da shi ba sai salki da cika irin na fulanin Gaya ta raba
biyu ta tufke shi gefe-da-gefe. Ba ta taba shafa 'lip-stick' ba tun auren ta da
Turaki sai yau. Ta shafa shi kalar 'light pink' samfurin avon. Ta taje gassun idon
ta da girar idon ta da 'mascara' nan da nan fuskar ta ta zama 'cute' ta yi kyan da
ba ta taba yi ba.
A hankali Kulsum ta ke taku kamar a filin fashion-parade tana ta faman shige
da fice a gaban Turaki, wanda ya baza takardu a falo yana ta aiki cikin 'macbook'
din sa.
A hankali ya cira kai ya dube ta za ta wuce rike da robar 'ice-cream' a hannun
ta. Ya dan kara girman idanun sa yana kallonta sosai. Bai san sanda ya ce,
"...Come here baby...".
Ta rangwadar da kai, "Ba aiki ka ke ba Prince?"
Ya ture 'macbook' din gefe, ya ce,
"Na ce ki zo koh?"
Ta tako a hankali tana shan 'ice-cream' din ta debo kadan ta nufo bakin sa,
yayin da shi ba ta wannan yake ba, kokari yake don ganin ya zuge zib din rigarta
gabadaya, yana fadin.
"A duniya akwai mai hakuri iri na? Quite three months ba tare da mata ta
ba...".
Kulsum ta sakar masa komai, tare da inganta masa daren yadda ya kamata. Ita
kanta wani abun bata san ina ta koyo shi ba. Ta dai sa wa ran ta ne za ta yi komai
don ta faranta wa Turaki. Rayuwar ta kacokam fansa ce ga farin cikin sa.
Daren ya kasance musu tamkar a ranar suka taba kusantar juna, ya shige cikin
darare masu dumbin tarihi da suke adanawa a kundin rayuwar su.
Washegari suka shirya suka tafi Chelsea, kwanan su uku a 'hotel' din 'The
Chelsea Harbour Hotel' suna gwangwaje soyayyah zallah, ko wayoyin su kashewa suka
yi. Sai lahadi da daddare suka bi 'train' suka koma Reading.

Rayuwar auren Kulsum da Turaki kenan, rayuwa ce wadda aka gina bisa soyayyah,
kauna ta fisabilillahi da yarda zallah, wadda biro ya yi kadan ya bayyanata. Sun
gina rayuwar auren su ba don kyale-kyale na rayuwa ba. Babu sirrin junan su da ba
su sani ba. Yo mijin da ki ke yi wa fitsarin kwance ya wanke ai zance ya kare.
Turaki ba ya boye wa Kulsum komai da ya shafe shi, ko da a fannin aikin sa ne. Da
hankulan su suka natsa ne ya gane Kulsum na da matsala a ido. Sai lokacin ne ya
tuno zuwansu European Eye Hospital a Lagos ita da Taufeeq, ya tsare ta da tambaya
kan me ya kai ta ranar? A nan ne ya san matsalar idon Kulsum ta tun haihuwa. Mai
abu da abunsa, wani ma ya yi rawa bare dan makadi?
Tuni ya sa ta a gaba da bincike da gwaje-gwaje, a nan ya gano tana dauke da
matsalar da suke kira amblyopia (lazy eye), wanda magunguna na digawa (eye drops)
kadai zai magance shi ba sai ta saka gilashi ba. Tun daga ranar ya soma diga
mataeye drops masu kyau har suka washe.
*******
Ranar ta kasance juma'a, da wuri Turaki yake dawowa gida. Ya shigo a matukar
gajiye, Kulsum na zaune ta bararraje tana shan 'ya 'yan 'strawberries' in zai iya
tunawa yau wajen sati guda ke nan ba ta da abinci sai 'ya'yan 'strawberries'. Ta
kashe shi da murmushi, ya ce, "Kulsum are you alright? Cin wannan abun naki ya yi
yawa fa".
Ta yi narai-narai da ido, "In ban ji shi a baki na ba sai in ji saliva (miyau)
ya cika min baki".
Murmushi ya yi ya aje jakar hannun sa da falmaran din 'suit' din jikin sa akan
kujera.
"Then, you are subject to P-t (pregnancy test)".
Zaro ido ta yi abin dariya, "Haba Prince! 'yar yarinya ta da ni za ka yi min
wannan fatan?"
Dariya ya yi, ya iso gare ta ya mikar da ita tsaye. Ya jingina bayanta a jikin
sa ya daga rigarta da hannun damansa yana shafa shafaffen cikin ta cikin shauki.
"In mace ce, Batulu ce. In namiji ne Abdul'Ahad ne. Su suka taimaka min na same
ki 'for the second time', a lokacin da na riga na sa a raina na rasa ki, ciwon son
ki kuma shi ne zai yi ajali na. Sun ba ni 'support' din su dari bisa dari tare da
tabbatar min ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare. With Almighty Allah everything
is possible".
Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Ni dai ban fada maka ina da ciki ba".
Ya ce, "Amma kin iya sa miji a daki kina k......".
Da sauri ta kwace jikin ta daga nasa ta yi daki, tare da sa yatsun ta biyu ta
toshe kunnen ta. Turaki bai yi shiru ba sai da ya karasa mata. Ya kuma tabbata
zahiri Kulsum na da karamin ciki na watanni biyu, lokacin da Turakin ya gaji da
ciye-ciyen ta ya kai ta 'lab' aka auna fitsarin ta.
A wannan satin suka shirya zuwa Manchester wajen su Sajeedah. A 'train' suka
tafi zuwa Manchester. Sajeedah da Abdul'Ahad suka shirya musu tarba ta musamman za
su yi weekend (hutun karshen mako) tare da su. Amma kasancewar gidajen U.K kanana
ba 'spare room' dole sai a 'hotel' suka sauka.
Da safe wanka kawai suka yi suka shirya Abdul'Ahad ya zo ya dauke su zuwa gidan
su. A can suka yi 'breakfast', Kulsum da Sajeedah suka wuni hira, Sajeedah na kara
wayar mata da kai a kan rayuwar duniya gabadaya. Da yamma suka debe su a motar
Abdul'Ahad don su zaga da su cikin Manchester, inda suka ziyarci 'Greater
Manchester, Castle Field, National Football Meseum, Man City and Man United' da
suke jin labari. A karshe suka dire a 'university of Manchester' jami'a mai tsohon
tarihi. Sun rabu kamar kar su rabu, a lokacin cikin Sajeedah watanni bakwai. Burin
Sajeedah ya cika ta zama 'best friend' din Kulsum, abin da ba ta taba yi a rayuwar
ta ba (kawa) bayan Batulu.
Ba tare da shawara da ita ba Turaki ya cike mata 'application' na neman gurbin
karatu. Babu jimawa 'admission' dinta ya fito, ya kawo mata har kan cinyar ta.
Kulsum ta daga takardar tana karantawa a hankali. 'Admission letter' ce manne da
sunan ta KULSUM ABDULHADI YALLEMAN za ta karanci digiri a fannin aikin jinya (B.Sc
Nursing) na tsawon shekaru uku a jami'ar da Turaki yake wa aiki, kuma ya yi nasa
karatun, wato 'university of Reading'.
Da Kulsum ta buga wani tsalle sai ga ta makalkale a bayan Turaki. Da sauri ya
sa hannu ya riko ta.
"Kina da hankali kuwa? Wani abu ya samu cikin nan wallahi sai an fasa karatun".
"Na tuba na bi Allah na bi ka, Baban Batulu, angon Kulsum. Na rasa ta hanyar da
zan nuna godiya ta, ka gama cika min duk wani buri na, ka gama yi min duk wani
taimako a rayuwa. A lokacin da na fi bukatar taimako. Ka ba ni dukkan kauna da
kulawa ta yadda kullum nake kwana in wuni ina tunanin, ni da me zan saka maka
Prince?"
Tafiya ya hau yi dauke da ita a bayan sa zuwa dakin sa. Cewa yake, "Kin fi kowa
sanin da me ki ke saka min UmmuKulsum. Fata na ki cika min gida da 'ya'ya shi ne
kawai tukwicin da za ki yi min".
Cikin sa'a cikin nata ba mai tsarabe-tsarabe ba ne. Barta dai da ciye-ciye, ci
banza ci wofi don haka bai ba ta matsala sosai ba lokacin da ta fara zuwa
makaranta. Da farko ta sha wahala sosai kafin ta gane kan karatun nasu, amma da ta
likewa Turaki duk sanda yake gida tana gefensa rike da littafin ta, nan da nan
komai ya fara zauna mata. Domin koyarwar Turaki wanda ya kasance malamin jami'a,
kuma 'consultant' a kiwon lafiya ta sha bamban da ta dukkan malaman ta. Ta yarda
Turaki dan baiwa ne ba a fannin soyayyah kadai ba, Ubangiji ya ba shi baiwa a ilmin
kiwon lafiya.
Ko da watan haihuwarta ya kama Turaki cewa ya yi ba za ta je gida ba,
kasancewar suna tsakiyar karatu. Ta haifi kyakkyawar 'yar ta mace a asibitin 'Royal
Berkshire' ranar litinin. Turaki ya rungumi 'yar shi ta farko a duniya yana tsaye a
kan mahaifiyar ta da ake gyarawa. Tare da shi aka karbi haihuwar.
A wurin ya yi mata khutbah da sunan da ya tanadar mata tuntuni, wato Fatima-
Batulu.
Lokacin da Kulsum ta samu kanta, Turaki ya dauko babyn ya ajiye mata a kan
kirjin ta. Murmushi ta ke yi tana kallon yarinyar. Komi na Turaki ta kwashe, har
zara-zaran yatsun hannun sa. Ta karanta addu'ar kariya daga zina ta tofa mata a
al'aurarta, wato aya ta 11 cikin 'suratul Tahrim'.
(Wa Maryam ibnat Imranal-laty ahsanat farjaha fanafakhna fiihi min ruhina wa
sadaqat bikalimati rabbiha wa kutubihi wa kanat minal qaniteen) kafa 41, sannan ta
mika wa Turaki ita, wanda ya zauna a kusa da ita yana rada mata kalaman da suka
zamo sirri ne a tsakanin su.
Lokacin da Kulsum ta yi wa Batulu albishir da sunan da Turaki ya saka wa baby,
Batulu kuka ta saki don farin ciki. Tun ba su bar gadon asibitin ba kowa nasu da ke
Gaya ya samu labarin haihuwar, Turaki ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, ta ce da
man cikin satin nan za su shigo U.K ita da Daddy za su shigo Reading su ga baby.
Hakan kuwa aka yi, washegarin komawar su gida su Hajiya Nasara suka zo,
Sajeedah ma da danta Naufal duk sun zo. Duk da Turaki ya dauki nurse wadda za ta
kula da su a gida, Hajiya Nasara ita ta ke wa maijego wanka da tawul, ta kuma wanke
baby safe da yamma. Dole Turaki ya debi kayansa ya bar musu gidan don ya yi musu
kadan, daki ya je ya kama a 'hotel' na tsawon sati biyu da Hajiya Nasara za ta yi.
Umma ta yi fadan lallai ya dauko Kulsum da baby ya dawo mata da su, amma da ta
ji Hajiya Nasara na tare da su sai ta hakura, ta tabbatar za ta ba su kulawa yadda
ya kamata.
Jego na sosai Hajiya Nasara ta yi wa Kulsum, Sajeedah ce mai musu girki. Cikin
kwana bakwai sun murmure sun yi kyau. Turaki da Abdul'Ahad sai dai su zo su ci
abinci su tafi, don Abdul'Ahad din tare da Sajeedah da dan su Naufal suka zo. Ya yi
'weekend' tare da su ya koma Manchester ya bar su Sajeedah ita da Hajiya Nasara
suka ci gaba da kula da mai jegon da baby har tsayin sati biyu, inda Hajiya Nasara
ta soma shirin koma wa London inda ta baro Daddy, za su kara sati daya sannan su
wuce gida.
A bakin Hajiya Kulsumu ta ji labarin Taufeeq ya samu mata, diyar abokin Daddy
ce, nan da watanni uku za a yi bikin.
Ta nuna wa Mum farin cikin ta sosai tare da yin fatan alheri. A ranta ta ce, da
a ce tana da wata sana'a ko tana da kudi, da ta yi wa Taufeeq gudunmuwar lefe.
Kamar Turaki ya san abin da ke ranta, lokacin da Mum za ta koma ya dunkulo kudi
masu dama ya ba ta, ya ce ta hada wa kowa da ya dace tsaraba. Don haka ta rubuta wa
Sajeedah duk abin da ta ke so ta sayo da kudin. Goggo da Umma atamfofi Sharaton
turmi uku kowannen su, Baffa da Malam Hadi bandirin shadda excelcior, Maimartaba
turare mai daraja,

Please Login or Register in order to submit comment