You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai kamshi suke daga ita har shi. Tsakanin gidan
su da masarautar Gaya ba tafiya ce mai yawa ba, a kafa ma za a iya zuwa. Amma mota
suka hau, lokacin da suka isa Umma fada ta hau yi kan don me zai fiddo Kulsum ko
wata guda ba ta rufa ba, in gaisuwa ce ai tana aiko mata kullum. Shi dai hakuri
yake ba ta, bai gaya mata ba ya so ya fito ya baro Kulsum cikin damuwa ba ne.
Umma ta tambaye ta, “In ce ko babu matsala Kulsum?”
Kanta a kasa ta ce, “Babu Umma, muna godiya da dukkan dawainiyar ku. Allah ya
kara girma, Allah ya kara yawan rai”.
Umma ta ce, “Ko kina bukatar karin ma’aikata? An ce gidan naku da girma sosai”.
Kulsum ta ce, “Umma har sun yi yawa, Baba Laraba akwai zafin nama kamar ba
tsohuwa ba".
Umma ta yi murmushi, ta ce, “Ga iya girki kuma. Sannan tana son ki sosai”.
Kulsum ta ce, “Yaya labarin mutanen kaduna? Tun bayan biki babu labarin su”.
“To ke din ce ai babu waya, Turaki ya ya batun wayar Kulsum ne?”
Shi dai yana gefe kan shi a kan wayarsa ba sauraron su yake ba, sai da Umma ta
kira sunan shi ya dago, ta sake maimaitawa, ya ce, “Ina sane, ban samu shiga Kano
ba ne sai wajen jibi”.
Duka dakin matan gidan sai da Kulsum ta je ta gaishe su, inda ta tarar Fulani
wato kakar su Turaki tana kwance babu lafiya, likita ne ma a kanta ya daura mata
ruwa. Tsohuwar tana jin jikin ta, amma albarka ta ke sa wa Kulsumu, tana rokon ta
ta rike Turaki da amana, domin shi dan albarka ne, wanda duk gidan ba wanda ta ke
so irin sa.
Ba su koma gida ba sai wajen sha dayan dare. Kulsum ta sa a ranta sai dai
Turaki ya yi fushi da ita, amma ba za ta sake kwana daki daya da shi ba, hakan
cutarwa ne a gare shi, duk son da yake ikirarin yana yi mata in aka ci gaba da
tafiya a haka tana sharkaba masa fitsari a gado, watarana na zuwa da za ya tsane
ta, in ma bai hada da duka ba. Don haka ta lallaba ta shige dakin ta ta murza key,
ta jingina da kofar tana sakin ajiyar zuciyar tausayin kan ta.
Bugun duniya Turaki ya yi, kiran duniya da lallashin duniya amma Kulsum ta ki
budewa, don bacin rai kasa kwana a daki ya yi shikadai ya dawo falo ya sa filo a
kasa ya kwanta.
Washegari sabida farin cikin ba ta yi fitsari ba don ta bi system din nan na
non-pharmacological treatment, da kanta ta hada wa Turaki abin karin kumallo. Ta
koma dakin ta ta yi wanka ta zuba kwalliya mai sanyaya zuciyar maigida. Ta feshe
jikin ta da turaren fahrenheit ta doshi dakin Turaki.
Da sallama ta shiga, yana kwance daga shi sai kayan barcin jikin sa yayi filo
da hannayen sa yana fuskantar ceiling. Bai amsa sallamar ta a fili ba, amma ya amsa
a zuciyar sa. Bai kalle ta ba, balle kwalliyar da aka yi domin shi. Tana iya
karanto kwantaccen bacin rai a kan kyakkyawar fuskar sa. Ta karasa a hankali ta
zauna a daidai saitin kansa.
“Barka da safiya Prince”.
Shiru ya yi mata, ta rasa abin da yake mata dadi.
“Na shirya abinci, don Allah ka fito ka ci”.
A lokacin ne ya juyo gaba daya ya fuskance ta.
“Kulsum, yaushe raini ya gifta a tsakanin mu, da har za ki kulle min kofa? Ina
miki magana ki ka yi banza da ni kamar ba ki san ina yi ba?"
Hawaye suka zubo daga idon Kulsum, ta ce, "Ban yi don raini ba Prince, na yi ne
don gudun cutar da kai. Yau da gobe duk hakurin ka da kaunar ka gare ni, wallahi
sai ka tsane ni Prince”.
“Abin da ki ka yi min shi ne babbar cutarwa a gare ni. Kin sani ba ni da wata
matar bayan ke. Ni idan zan same ki a kullum ba ni da matsala da fitsarin ki. Don
dai barin garin za mu yi ne, amma tuni na yi mana odar water mattress har guda biyu
daga Amazon za su kai min gida na na Reading. In wadannan sun mutu babu damuwa”.
Kulsum couldn’t help it ban da ta fada jikin sa ta fashe da kuka, wani irin
kuka mai kara soyayyar da ta ke yi wa Turaki.
Ta ce, “Na gode Prince, don Allah ka yafe min bacin ran da na sa ka jiya”.
Ya ce yana mai tuje daurin da aka bata lokaci ana kalmasawa.
“Ai hakuri daya ne, ki biya ni bashina na jiyan".
Daga haka ya canza akalar hirar zuwa irin wadda ya fi so su yi.

Tun daga ranar Kulsum ba ta kara rufe wa Turaki kofa ba, ta yarda shi din mai
son ta ne, mai yawan kaunar ta da tausayin ta ne. Sai dai kuma ta daina barci,
kullum cikin non-pharmacological exercise, wato ta daina shan abu mai ruwa-ruwa da
shi ruwan kansa daga karfe shidda na yamma, sannan kafin ta kwanta sai ta tabbatar
ta yi fitsari, bayan saduwarta da mijin ta abu na farko da ta ke yi shi ne fitsari,
sannan ta saita alarm ta aje a saitin kanta tana tashi sau biyu cikin dare at
interval ta je ta yi, daga lokacin da suka yi sallar asubah sai ta koma dakin ta, a
can ta ke ramuwar barcin ta ta yi fitsarin ta son ranta, sai dai ta yi wata dabara,
spreedsheet na kan dining table wanda leda ce ta dauke ta shimfida a saman katifar
ta, ta lulluba zanin gado mara kauri a kai.
Turaki ya kara sayo su da yawa ya jibge mata, tana tashi za ta yaye su har
ledar ta wanke ta shanya a bandakinta, ba ta taba fitowa waje ta yi shanya ba.
Turaki ba karamin tausaya mata yake ba, sabida irin yadda ta ke wahala wajen
tsaftace kan ta da muhallin ta.
Aikin da da hali da ba zai barta ta yi shi da kanta ba, tunda suna da wadatar
masu aiki, shi ya sa sau tari yake zuwa ya wanke zannuwan gadon da kansa, idan ta
jika su a omo ta shiga wata sabgar. Ta yi ta yi ya bari ya ki, cewa yake.

“We are together in this difficulty (muna tare a cikin wannan wahalar)”.

A gefe kuma yana ta shirye-shiryen tafiyar su U.K.
Ya cika alkawari ya kawo mata dalleliyar waya, sai damuwar ta ta ragu. Kullum
in ba ya nan tana tare da ‘yan uwan ta a waya, sannan duk inda ya je Allah-Allah
yake ya dawo da wuri don kada kadaici ya jefa ta a damuwa. Ba ya son abin da ta ke
yawan fadi na cewa, ta tsani kanta. Ji yake me ya sa ma tun farko bai zama kidney
and bladder specialist ko Nephrologist ba? Da tuni ya bai wa Kulsum duk treatment
din da ya kamata ba wanda ya ji ba wanda ya gani.. Ganin kwanakin da Dr. Ibrahim
ya deba musu yake kamar shekaru uku.
Ya je Gombe ya kwana biyu don gudanar da wani private aiki na Sarkin Gombe,
wanda cikin ikon Allah aka yi nasara idanun Sarkin suka washe. A lokacin da ya samu
lafiya ne ya kira Turaki, wai ya zo ga ‘yar shi Siyama ya ba shi kyautar ta ko a
mata ta hudu ne, bayan iyayen kudin da ya tura masa wadanda sun ninninka kudin da
suka yi za'a biya shi.
Turaki ya yi dariya, ya ce da Maimartaba Sarkin Gombe, ya gode, amma ba zai
karba ba, sabida ko wata bai yi da yin aure ba.

Wannan labari Turaki ya zo yana bai wa Kulsum, bayan dawowar sa daga Gombe.
Kulsum ta lumshe idanun ta ta ce, “Ai da ka karba Prince, ka ga ni babu tabbas din
zan warke gabadaya, ko ba zan warke ba. A baya ne nake tsoron ka yi aure, amma
yanzu na yarda da kai dari bisa dari, na amince babu macen da za ta sa ka juya min
baya. Roko na gare ka shi ne, kada ka taba bari matar ka ta san ina da lalurar
urinary incontinence (bed -wetting)”.
Turaki ya harare ta son ran sa, ya ce,
“Wato Kulsum ba kya kishi na ko?”
Ta ce, “Kishi ba zai sa in kware ka ba, soyayyar da nake maka ita ce ta sanya
nake son ka samu cikakken farin ciki kamar kowanne namiji. Ina farin ciki da jin
dadi ga auren mai jika gado? Ai sai dai maneji, manejin ma sai irin miji na
(Turaki) masu babbar zuciya ta tausayi da jin kai”.
Fushi sosai Turaki ya yi, wai ta gasa magana kuma ba ta kishin sa. Wuni guda ya
ki dawowa gidan, da ya dawo din kuma ya ki yi mata magana. Ya zauna a falo yana
kallon football. Kulsum ta fito cikin kasaitacciyar kwalliya, ta zagaya ta bayan
kujerar da yake zaune ta zagaya hannayen ta a wuyan sa suka sauka a kirjin sa. Ta
sanya fuskar ta a masangalin wuyansa ta sumbace shi son ranta, sumba sosai, mai
tsayi da zurfi.
“Ina bada hakuri my Prince, ka je ka karata da mai fitsarin kwancen ka, ba zan
kara cewa ka yi aure ba”.
Duk halin fushin da yake ciki sai da ta ba shi dariya. Ya mika hannu ya zagayo
da ita gaban shi ya zaunar ta bisa laps din shi. Bakin ta da ya sha wet-lips ya hau
tsotsewa sannan ya dalle mata shi da karfi, sai da ta yi ‘yar kara.
“Matar tawa ki ke cewa mai fitsarin kwance?”
Don zafi sai da hawaye ya tsattsafo mata.
“Ka yi hakuri, na bi Allah na bi ka”.
Ya rungume ta sosai yana jin bugun zuciyar ta a kirjin sa. Sun dade a haka yana
gaya mata babban abin da ba ya so shi ne ta ce ya yi aure, sabida lalurar ta.
Kulsum ta ce a ran ta, tabbas da ta rasa Turaki, kamar yadda ta so yin wannan
babbar wauta, hakika da ta yi asara irin wacce ba a mayarwa! Zancen zuci ta ke, ba
ta san cewa ya fito fili ya shiga kunnen sa ba.
“What are you saying?” Turaki ya tambaya, don bai ji sosai ba.
“I said I love you”.
“And I love you more”.
“I can’t do without you”.
“I can’t be happy without you too”.
“Na gode Prince, once again, I love you with all my heart…”. Ita ce ta ke fadin
soyayyar tata in theory, yayin da shi practically ya soma bayyana mata tasa. Ta
gane cewa, tata soyayyar is underestimated. Ga masu soyayya in practice, wadanda ba
sa bata yawun bakin su wajen bayyana ta.

*** *** ***
Kwanakin da Turaki zai yi a Gaya suka cika, wato wata daya. Ya kama gobe za su
tashi zuwa U.K, visa din Kulsum wadda za ta je a matsayin matar aure ga ma'aikaci
ta kammala, don haka yau da yamma suka shiga cikin gida don yi wa Umma da
Maimartaba sallama, daga can kuma za su biya gidan su Kulsum.
Maryam ‘yar Yaya Hadiza da ta dawo hannun Umma tun bayan auren Batulu ce ta
sanar da su Umma na wurin Maimartaba, bayan sun gaida kowa sun gaida Fulani da jiki
sun yi mata sallama tana mai sa musu albarka, suka karasa bangaren Maimartaba din.
Kulsum da Turaki suka zube suka kwashi gaisuwa. Maimartaba sarkin Gaya kallonsu
yake cike da murmushi, shi dai haka nan yake son yarinya Kulsumu kamar ‘yar cikin
sa.
Ya ce, “Ummu Kulsum, ina fatan babu matsala, kina nan kina ta hakuri da mijin
ki?”
Murmushi ta yi, ta ce, “Ai shi ma yana hakuri da ni’.
Haka ya yi ta jan ta da hira kamar ba surukar sa ba.
Ya ce, “Za a tafi kasar Turawa a bar mu ko? Ni dai aikin nan na Turai bana son
sa Turaki, ba zan gaji da maimaita maka ba, kasar mu na bukatar likitoci irin ka,
sau biyu ke nan kana min alkawarin dawowa gida gabadaya, amma sai ka kalallame ni
ka kara komawa. Yanzu kuma Kulsumun ma za ka dauke ta, mu da ganin ku sai Baba-ta
gani”.
Turaki ya muskuta ya kara dukar da kan sa, ya ce, "Insha Allahu wannan karon
zan cika alkawari, shekaru uku za mu yi mu tattaro komai mu dawo gida. Allah ya
kara maka yawan rai, na yi alkawarin ni da iyali na ko birnin Kano ba za mu je ba,
a nan Gaya za mu kafa rayuwar mu har mutuwa. Ina da burin bude asibiti idan na
dawo, ga UmmuKulsum ma ma’aikaciyar jinya ce za ta taya ni kula da komai. Fatan mu
dai a bi mu da addu’a”.
Ran Maimartaba Sarkin Gaya ya yi fari tas! Ya ce, “Albarkar mu na tare da ku,
albarkar uwa da uba, ba za ku taba tabewa ba”.
Umma ma da ke gefe tana ta kallon su sun mata kyau a fuska, sun dace da juna.
Turaki ya yi aure wanda ta ke so, kuma hankalin ta ya kwanta da shi, don haka ba ta
da sauran damuwa a yanzu.
“Umma, ke ma ki sa mana albarka”. In ji Kulsum.
Umma ta yi murmushi, “Ai Maimartaba ya hada har da tawa, kada albarkar tamu ta
yi muku yawa”.
Kowa sai da ya murmusa.
Ta ce, “ku tashi ku je gidan su Kulsumu ku yi musu sallama kada dare ya yi
sosai”.
Suka mike a tare suna godiya.

“Goggo tana nan? Jibo na kiran ta a zaure”.
Kulsum ta make murya ta fada daga tsakar gida.
Goggo na lazimi ta jiyo ta, ta yi dariya da murmushi duka a tare. Baffa Jibo ne
ya fara fitowa daga dakin sa. Ya nunata da dan yatsa.
“Wannan Jibon dai ya fi karfin ki, in ma zawarcin sa ki ka zo”.
Ta ce, “Haba! Kayyasa! Wane mutum! Ina da sardidin likita na a gefe, me zan ci
da tsoho baki duk goro?”
Turaki ya sunkuyar da kai yana dariyar su. Goggo ta fito ta shimfida musu
tabarma, farin ciki ya cika ta, yau Kulsum ce tare da Turaki suna masu farin ciki
da juna. Ya Allah ya kara mata tsawon rai, ta dauki jikokin su. Addu’ar da ta ke yi
a zuciyar ta ke nan.
Ko da Kulsumu suka shiga daki da goggo, ba ta gaya mata fitsarin ta ya dawo ba.
A wannan gabar ta rayuwar su ta amince suna bukatar kwanciyar hankali. Ta kuma
kwana da sanin babban tashin hankalin su a rayuwa fitsarin kwancen ta ne.
Duk wani support da encouragement (karfin gwiwa) ta gama samun shi a mijin ta
abin kaunsr ta (Turaki). Ba abinda fada musun zai haifar sai tashin hankali a gare
su.
Kulsum ta kira Baban ta ta yi masa sallama, sabida Turaki ya ce gobe kafin su
wuce Abuja za su fara zuwa 'Yalleman su yi wa Baban sallama, nan Goggo ta ke gaya
mata ya kira ta dazu ya ce ba ya gari, ya je Maiduguri kan wata harka da ya samu.
Tausayin Baban ta ya cika ta, mutum ne shi mai kokarin neman na kansa don rufuwar
asirin iyalin sa. Ta roki Allah ya ara mata dama ko yaya ne watarana iyayen ta su
huta a karkashin inuwar ta. Duk da cewa ba cikin wahala suke ba.
Ta gaya wa Goggo, Turaki ya ce gobe ta Abuja za su tashi, don haka za ta biya
gidan Hajiyar ta.
Ba su bar gidan ba sai karfe sha daya na dare. Tunda suka koma gida suka fara
hada kayan su.
Washegari karfe shidda na safe suka dauki hanyar Abuja. Daga Kulsum sai Turaki
a motar. Yana tuki tana gefen sa, tana so ta yi barci don barcin ta na jiya ragagge
ne, ta kwana tana hada kayan su. Amma tana yaki da barcin don kada tsautsayi ya sa
ta fitsare masa mota. Da ma ta yo guzurin lipton din ta, shi ta yi ta sha har da su
nescape duk don su hana mata barci.
Turaki na tuki ba tare da ya juyo ba ya ce, “Wai wannan shan shayin na mene ne?
Ko dai…”. Ya ki karasawa yana murmushi. Kulsum da bata dago inda ya sa gaba ba ta
ce, “Ko dai me? Ni don ya korar min bacci nake shan sa”.
Da mamaki ya ce, “To a kan me ba za ki yi barci ba? Ana raba jikin dan Adam da
barci ne?”
“Uhm”. Kawai ta ce, ai it is embarrasing ta gaya masa tana tsoron jika masa
mota ne.
Hannun hagun sa ya mika ya kwantar mata da kujerar ta.
“Please sleep baby”. Yana iya hango fargabar ta cikin kyawawan idanun ta.
Ya kuma san me ta ke fargaba din.
“To Ummu Kulsum, mece ce mota? Barcin ki ya fi ta muhimmanci a waje na”.
Tana lumshe idanu cike da barci ta dube shi cikin shaukin so. Mutum kamar mai
gani har hanji? Ya daga mata gira tare da kashe ta da wani kyakkyawan murmushi da
ya ratsa har cikin ruhin ta.
“Help me and sleep” (taimakeni ki yi barci). Kulsum ta lumshe idanun ta, kafin
dan lokaci barci ya dauke ta.
Cikin taimakon Allah ba ta yin ba har suka shiga Abuja. Yana kokarin shiga da
su hotel din Rockview ta ce, “Prince, don Allah mu je in gaida Hajiya ta, ban yi
mata sallama ba”.
Ya ce, shi sai ya yi wanka da sallah ya huta. Kuma sai ta tabbatar saurayin ta
ba ya gidan sannan za su je. Ta yi narai-narai da ido.
“Ya ya za a yi in san yana gidan ko ba ya nan? Shi da gidan su?"
Ya yi fuska ya ce, “Ki kira ki tambaya".
Dariya ta yi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska.
“Da ma ka cire shi a ran ka, ni ban taba son sa ba, irin son da ka ke tunani.
Ina son sa ne a matsayin sa na dan uwa na na jini, kuma shi ma ya sani, ya sha fada
da bakin sa;
“Ki taimake ni kada ki kara ambaton Turaki a gabana, zuciya ta za ta buga
Kulsum”.
Turaki ya yi wani lallausar murmushi yana murza sitiyarin motar sa cikin gwanin
ta.
“Wato har zance na ki ke masa Kulsum? Ashe kina so na duk da laifuka na gare
ki?” Ya fada cikin sanyin murya.
Kulsum ta kare fuska da mayafin ta, “Hatta Hajiyar mu da Goggo, sun san irin
son da nake maka Prince".
Turaki ya mika hannun damansa ya kama nata ya matse shi sosai a cikin hannun
sa.
“To say I thank you… is not enough to express the feeling….....”.

Daidai lokacin da suka adana motar a parking lot. Ya mika hannu ya bude mata
kofa, jakar hannun ta kawai ta dauka. Turaki ya wuce gaba ya je ya kama musu daki.
Ta lifter suka bi zuwa dakin nasu. Duk abubuwan da ya lissafa sai da ya yi su;
wanka, sallah, hutawa sannan suka fito don tafiya (Brains&Hammers) wato gidan
Hajiya Nasara.
Hajiya Nasara kadai suka samu a gidan, karshen farin ciki ta yi shi da ganin
su. Ta sa Serah ta shirya musu abinci. Turaki duk ya kasa sakewa saboda surukuta,
amma haka ta matsa musu kan sai sun ci abinci. A dakin ta da Kulsum ta shiga domin
su gaisa sosai Hajiya Nasara ta kasa boye farin cikin ta, ta ce,
“Na ji dadin yanayin da na ganki ciki Kulsum, na kuma tabbata Turaki na kula da
ke yadda ya kamata. Madallah”.
Nan Kulsum ta ke gaya mata sallama ta zo ta yi mata za su wuce U.K can inda
Turaki ya ke zaune, ba ta san lokacin da za su dawo ba. Farin cikin Hajiya Nasara
ya karu, ta ce, “Ai kuwa zama bai gan ni ba, bari in tattara miki kayan girki, don
a can ba za ki samu irin su ba”.
A waya Hajiya Nasara ta kira Dr. Sakeenah da Nasmah duk ta gaya musu tafiyar
Kulsum. Nasma ta shiga EDD dinta, Taufeeq na Lagos, kayan amfani masu yawa Hajiya
Nasara ta hada mata. Ko da wasa Kulsumu ba ta yi zancen fitsarin ta ba, ba ta so ta
kara daga wa kowa hankali, wahalar da suka sha a baya Allah ne kadai zai biya su da
mafificin alherin sa.
Sai karfe goma suka bar gidan, domin hira ce sosai ta shiga tsakanin Turaki da
Hajiya Nasara, kasancewar su duka mazauna Birnin Sarauniya.
Hajiya ta ce, ta taba zuwa Reading Berkshire, kuma insha Allah ba da jimawa ba
in sun shigo London za su zo har Reading su gan su ita da Daddy.
Ko da suka koma hotel gajiya ba ta bar su sun tsinana komai ba. Amma Kulsum ta
ki yarda ta kwanta don kada ta yi fitsari. Ta hau kujera kwalli daya da ke dakin ta
kishingida tana faman daddanna wayar ta. Turaki ya kwace wayar, ya kuma kashe
fitila mai haske ya ce,
“Malama ki kwanta please, gobe asubanci za mu yi, is good ki samu barci ko yaya
ne”.
Ta bi umarnin sa ne kawai don ta san ko me za ta ce ba zai kyale ta ba. Suka
kwanta Kulsum kalmashe cikin jikin sa. Amma ko na sekon daya ba ta bari barci ya
dauke ta ba. Ta lafe a jikin Turaki tana sauraron yadda yake sauke numfashi a
hankali, ita ina ta ga wannan kwanciyar hankalin? Ta lura Turaki na jin dadin
barcin sa, don haka ba ta nuna wata alama da za ta nuna idanunta biyu ba, har
lokacin sallar asubahi ya yi.
Karfe shidda wanda zai kai su filin jirgi ya kuma tafi da motar Turaki ya zo,
wani abokin sa ne Dr. Habib mazaunin Abuja. Sun bata lokaci wajen screening da
zaman jiran jirgi ya daidaita. Karfe goma sha daya na safe jirgin su ya tashi zuwa
United Kingdom.

*** *** ***
A cikin jirgi ne Kulsum ta samu ta yi barci sosai a jikin Turaki. Tafiyar
awanni takwas a cikin jirgin British Air ta sauke su a birnin London. Inda daga nan
suka dauki taxi ta kai su tashar jirgin kasa, suka bi train zuwa garin Reading,
Berkshire.
Nisan da ke tsakanin babban birni (London) da garin Reading (37 miles) ne, wato
tafiyar mintuna arba’in da biyu a cikin jirgin kasa. Reading babban gari ne mai
tsohon tarihi a kan kasuwanci a yankin Berkshire (South-East England).
Gidan Turaki na cikin jerin gidajen malaman jami’ar Reading. Mai taxi din da ya
dauko su har kofar gidan ya sauke su. Gajiyar da ke tare da Kulsum ta sa ba ta gane
komai da ke cikin gidan ba sai washegari. Gida ne a cikin Estate duka gidajen iri
daya ne, masu dakuna ciki-biyu da falo, kowanne daki da toilet manne a cikin sa,
sai kicin wanda kofar sa ke cikin

Please Login or Register in order to submit comment