You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hatta yaya Hadiza da Batulu ta aika musu 'laces' masu kyau,
sannan ta sa Sajeedah ta saya mata takalma da jakunkuna set (24) bayan ta sa Nasmah
ta tambayo mata 'size' din kafar Fahima matar Taufeeq, ta shirga su cikin akwati ta
bai wa Mum ta ce a bai wa Taufeeq gudunmuwar ta.
Aka ce naka-naka ne, sai dai ka yi kara da kawaici. Hajiya Nasara ta yi farin
ciki sosai ba don ba ta da shi ba. Sai don alheri wa naka ko ya ya yake dadi ne da
shi.
Washegari ta koma wajen mijin ta suka fara shirin dawowa gida.

Taufeeq ya yi mamakin sakon da Kulsum ta aiko masa. Ya dauka ta yanke alaka da
shi kenan tunda ta samu dan Sarkin ta. Ko ba komai hakan ya rage kullacin da ya yi
mata. Har da Hajiya ta kira ta ya karbi wayar ya yi mata barka, wannan ya faranta
ran Hajiya Nasara sosai.
Su ma su Sajeedah washegarin tafiyar Hajiya Nasara suka koma Manchester.
A daren Turaki ya dawo daga balaguron 'hotel' dinsa, ya tadda iyalinsa cikin
koshin lafiya. Aka dora soyayya daga inda aka tsaya, musamman da ya kyalla ido ya
ga Kulsum na sallah. Kulsum har da kukanta kan cewa za'a sa ta yin kazamin jego, da
gwarne (rurrutsa). Duk sai ta bai wa Turaki dariya, ya ce yana mai tallafo kanta
cikin tafukansa, "Rurrutsa na taso na ga ana yi a gidanmu, kuma ban ga kowa ya mutu
ba. Mun rayu bi-da-bi cikin koshin lafiya. Ni in za ki haifa min yara duk karshen
wata ina so Kulsum, tunda Allah bai hana min yadda zan yi da su ba".
A yanayin da ya yi maganar ya karya zuciyar Kulsum. Ta ji cewa, ba
gwarne/rurrutsa ba, ko haihuwar kullum yake so za ta yi masa muddin hakan yake so.
Ta shige cikin jikin Turaki a hankali tana mai sallamawa dukkan bukatun sa. Idan ta
tsaya tana lissafo gudunmuwar Turaki cikin rayuwar ta, sai ta ga cewa ita ba ta
taba yi masa komai a duniya ba. Don haka kamar yadda ya ce din ne, da haihuwar
kawai za ta biya shi. Burin sa ya bude ido kullum ya ga 'ya'yan ta sun cika masa
gida. Wannan ne kadai martanin soyayyar da yake so daga gare ta.
Kafin Kulsum ta kammala B.Sc din ta 'ya'yan su biyu; Batulu da Iftihal. Zuwa
wannan lokacin Turaki ya yi murabus daga aiki a 'United Kingdom' ya tattaro tarin
kwalayen sa da experience din sa da iyalin sa sun soma shirin dawowa gida gabadaya.
Kulsum Abdulhadi, a matsayin cikakkiyar ma'aikaciyar jinya mai shaidar HND da B.Sc.
*****
MURFI
GAYA
Suka dawo mahaifar su kamar yadda suka barta shekaru uku a baya. Cikin iyayen su,
kakannin su da 'yan uwan su. Ba jimawa Turaki ya soma ginin asibitin sa a Gaya,
wanda ba ido kawai za a dinga dubawa ba. Don haka ya debo kwararru daga fannonin da
Kulsum ke so su bada taimakon su, musamman 'obstetrics and gynaecologists'. Da
taimakon Maimartaba Sarkin Gaya III tangamemen asibitin ya kammala cikin dan lokaci
kalilan. Wanda Turaki ya sanya wa suna GAYA SPECIALISTS HOSPITAL. Asibiti ne na
lalurorin mata da haihuwa da cututtukan kananan yara, sannan da matsalolin da suka
shafi ido, wanda ya samu lasisi daga hukumar lafiya ta kasa. A kyauta ake duba
marassa lafiya, magunguna kadai za su saya, domin akwai hannun gwamnati a cikin sa.
Kulsum ta hada kudaden ta da ta dade tana tarawa da dan aikin 'part-time' da ta
yi a U.K ta biya wa Baban ta Malam Hadi hajji shi da Baffa, sai Turaki ya biya wa
Goggo da Umma da yayar sa Hadiza, suka tashi gabadaya zuwa kasa mai tsarki.
A wannan tafiya Kulsum ta sha addu'a daga mahaifin ta da kakannin ta, wadanda
dukkan burinsu a duniya bai wuce ingantuwar rayuwar ta ba, da dorewar ta cikin
zaman lafiya a gidan auren ta.
Ta yi burin dora 'course' a kan 'perioperative' bayan dawowar su Gaya, amma
laulayin ciki na uku ya hana ta. Sannan ba za ta iya tafiya Yola shekara guda ta
bar Turaki ba shi ya sa ta tsaya haikan a kan asibitin su a matsayin 'Chief of
Nurses'. Sun tarar da rasuwar Fulani kakar su Turaki watanni kadan kafin dawowar
su.

Gudunmuwar Dr. Abubakar Turaki Gaya ga kiwon lafiya bai tsaya a garin su Gaya
kadai ba, ana daukar sa hayar aiki a fannin sa na 'Ophthalmology' a manyan
asibitocin idon nan na 'European Union' da ke Lagos, asibitoci masu zaman kansu da
manyan Asibitocin gwamnati. Duk inda Turaki ya je ya yi aiki garin su Gaya yake
dawowa cikin iyalinsa bai yi gida a kowanne gari cikin maraya ba.

Kulsum ta zauna ta yi tunanin ya kamata ta fito duniya ta yi 'creating
awareness' ga mata 'yan uwan ta masu fama da lalurar fitsarin kwance, domin da
yawan wadannan mata, wadanda mostly suna gidajen aure, ko gaban iyayen su sabida
zaman aure ya gagare su, a kan su fito su nemi 'medical help' a kan lalurar
'ENURESIS'. Yanzu zamani ya zo da sauyi na ci gaba da babu irin lalurar da ba a
magancewa a asibiti, maimakon su zauna cikin bakin cikin rayuwa. Ta kuma yi kira ga
maza kan su taimaka su kuma tausaya wa matan su masu lalurar fitsarin kwance. Nuna
kyama da wulakanci a gare su ko rabuwa da su babban kalubale ne ga rayuwar su.
Hakan zai jefa rayuwarsu cikin 'risk' na kamuwa da depression, self-hatred da
inferiority complex, wani lokacin har ya jawo tunanin kashe kai, wato (suicidal
thought) ga masu raunin imani.
Ta tattauna da mijin ta uban 'ya'yan ta Dr. Abubakar Turaki kan kudirin ta. Shi
kuma ya ba ta goyon baya dari bisa dari. Ta soma gabatar da makalar a media
(talabijin da radiyo) a manyan tasoshi da taimakon Turaki. Lakcoci ne ta ke
gabatarwa masu taken 'Enuresis in Adults; A way out in the medical
profession'(fitsarin kwance ga manya; mafitar sa a fannin kiwon lafiya). A wata
makalar kuma ta ce 'Psychological Trauma of Noctural Enuresis; ta kawo bayanin
yadda mata da yawa ke fama da shi a gidan aure. Yadda maza ke 'treating' dinsu da
kyama, hantara, wulakanci da raini, ta yi kira ga masu fama da wannan lalura kan
cewa lokaci ya yi da ya kamata su san cewa fitsarin kwance ba shi ne karshen
rayuwar su ba. Su mike su nemi magani, don tsira da martabar su a gidan aure.
Tun daga lokacin da aka fara sakin lakcocin Kulsum a 'social media' ta fara
karbar kira daga mata daban-daban inda suke tabbatar mata halin da suke ciki kenan,
da yanayin zaman su da mazajen su. Kulsum in ta ji wani abun, ta tuno Turaki da
nasa kalar 'treatment' din a gare ta, sai kuka ya kwace mata. Ta kara godewa
Ubangijin ta, ta amince Turaki daya ne cikin dubu, kuma Ubangiji ya so ta da rahma
ne da ya nufe ta da dawowa hannun sa.
*****

Baffa ne ba ya jin dadi, ta yi masa girki na musamman ta zuba yaran a mota suka
tafi don su duba shi. Goggo da Baffa wadanda tsufa ya dada kama su, amma shar suke
cike da koshin lafiya sabida kulawar da suke samu daga Kulsumu da Turaki, suka
shiga ina suka saka-ina-suka-aje da tattaba kunnensu masu kiriniya. Iftihal ta yi
tsalle ta haye wuyan Baffa tana fadin, "Baffan Goggo ka yi min doki irin wanda Baba
na yake mana".
Kulsum ta mako ta a fusace tana fadin, "Sai kin karya min Baffa na? Ki je Baban
naki ya yi miki amma wannan Kakana ne".
Iftihal ta bare bakin shagwabar ta tana kuka, Baffa ya jawo ta jikin sa yana
rarrashin ta.
"Kyale Mama, ni ma ba Baban ta ba ne, Baban ta yana 'Yalleman".
Goggo kuwa ta hau yi wa Kulsumu fadan saurin duka irin nata, fada ta ke,
"Ke wa ya doke ki? Akwai wanda ya kai ki hawa jikin mutane?"
Kulsum murmushi ta ke tana zubo wa Baffa dafuwar hanta da ganyen alayyahu da ta
kawo masa a faranti ta mika masa, ta zuba wa Goggo tana fadin, "Ku ci sosai ku
murmure, umarah za ku koma sati mai zuwa, a can za ku yi azumi gabadaya".
Baffa sai ya kasa cin abincin don farin ciki, a rayuwar sa ba abinda ya ke so
irin zuwa Makkah, ya dinga sanyawa Kulsum albarka, ba ya taba gajiya da ganin sa
gaban dakin Ka'abah mai alfarma.
Washegari kuma 'Yalleman suka tafi, boot din motar su shake da buhunhunan kayan
abinci da kayan masarufi. Direban Turaki ne ke jan su kasancewar Turaki ba ya gari,
ya je wani aiki a AKTH. Malam Hadi ya tarbi 'yan jikokin sa cike da farin cikin
ganin su, Lami sai hidima ta ke da su don yanzu tsakanin ta da Kulsum biyayya ce
irin ta ubangida da yaron sa, ta yarda Allah ya gama daukakata a kan 'ya'yan ta,
kuma ita ce marufar asirin su.
Ta gaya wa Malam Hadi sakon Turaki cewa, su samu wani gidan aro su koma sati
mai zuwa za a zo a rushe gidan a yi musu ginin zamani.
Malam Hadi ya ce, "Kulsumu kina dora wa mijin ki hidimar mu, wadda na tabbatar
ta fi karfin aljihun sa, a kan me? Gini fa Kulsumu! Ni ai gidan nan ya ishe ni a
hakan da yake in ganganda in karashe ‘yar ragowar rayuwa ta, hidimar da ku ke mana
kuwa Allah ne zai saka muku. Addu'o'in mu gare ku ba za su taba yankewa ba".
Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Baba, duk abin da ka ji ya ce zai yi, to zai iya
ne. Burin mu shi ne ku kasance cikin farin ciki ku yi ta sanya mana albarka".
Lokacin da suka dawo Gaya yamma ta yi sosai. Tun a harabar gidan ta ga motar
Turaki a ma'adanar adana motocin sa, tabbacin ya dawo kenan daga Kano. Wani sanyi
ya ratsa zuciyar ta. Kwanaki biyun da ba su sanya juna a idanun su ba, tamkar
shekaru biyu suke ganin su. Batulu da Iftihal suka bude motar suka fice da gudu
suna fadin.
"Our Daddy is back..." (Baban mu ya dawo).

A falon suka tadda shi, yana tsaye yana waya sanye cikin kaftan na danyar farar
shadda ga sajen nan nasa ya kwanta luf a saman fuskar sa ma'abociyar zati da
kamala.
"Kullum girma ya ke, shekarun sa turawa suke, amma kamar kullum kara masa
kuruciya ake!"
Kulsum ta fada a zuciyar ta.
Ya suri yaran su duka biyu a hannayen sa hagu da dama yana fadin, "Ina Mummy ta
kwashe min ku ta kai ku na dawo babu kowa a gidan?"
Batulu sarkin magana ta ce, "Ai 'Yalleman muka je, Grandpa yana gaishe ka".
Dariya ya yi ya ce, "To in ce kun kawo min tsarabar 'Yalleman?"
Iftihal ta mika masa katuwar gorubar da ke dunkule a hannun ta.
Ya sumbaci goshin yarinyar ya ce, "Dadi na da Ifty babu rowa, Batulu ke ina
taki?"
Ta shagwabe fuska ta ce, "Daddy na cinye, na yada kwallon".
Ita ma ya sumbace ta a kumatu ya ce yana kokarin sauke su kasa, "Maza ku je
Baba Laraba ta yi muku wanka ku huta, a bar ni in gaisa da Mummy sosai".

"I missed you Prince...".

Ta fada tana sakalo hannayen ta ta saman wuyan sa. Kallon ta yake kamar yau ya
soma ganin ta. Kullum Kulsum (sweet 16) ta ke kara komawa a idanun sa. Kulsumun da
ta dusar da hasken sauran mata daga idanun sa, ta cike masa gurbin da mata hudu da
kwarkwarori goma, ba za su iya cike masa ba. Kulsumun da ta dauke kuruciyar sa ta
ci gaba da gwagwarmaya da shi a shekarun girman sa. Kulsumun da ba zai iya hadawa
da kowacce mace ya yi adalci ba... Kulsumun da yake fata har a aljanna Allah ya
tashe su tare, matsayin shugabar duka hurul-eenin'sa!.
Daukanta ya yi gabadaya yana tafiya da ita a hannunsa zuwa katafaren dakin
barcin su. A lokaci guda yana gaya mata kalaman da suka fi karfin biro na ya
rubuta.

Wannan shi ne labarin KULSUM,....UMMUKULSUM ABDULHADI 'YALLEMAN.

Karshensa kenan ba shi da littafi na hudu.

Masha Allah laquwwata illa billah!!!

Kuskuren da ke ciki, ku taya ni rokon Allah ya yafe min. Alkhairin da ke ciki,
Allah ya raba mana ladan ni da ku bakidaya.
Sai mun hadu a sabon littafina.

YI WA KAI HISABI!!!
Tuna sunan;

YI WA KAI HISABI!!!
YI WA KAI HISABI!!!
Shima zai zo muku complete insha Allah nan ba da jimawa ba. And I promised you
a thrilled reading !

SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI ke cewa.

"Da fatan watarana Allah ya hada mu cikin ALHERInSa, amin".

Ga masu bukatar tsofaffin littatafaina softcopies ko hardcopies ku tuntubeni a
07030137870 (whtsp only).

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment