You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din ta.
Ya ce, “Good morning Ma'am, za mu je gaida Baffa ni da Abdul’Ahad, ko kina da sako
wajen Goggo? Sajeedah za'a rako ta yanzu, ba za ku gan mu ba sai dare, don yau ne
za mu yi kilisa”.
Ciki-ciki ta amsa, “Ba ni da sako, a gaida Goggo da Baffa". Amma har cikin
ranta ta ji dadi, tana son mijin auren ta ya zamo mai yawan gaida iyayen ta, ko da
ba zai ba su komai ba.
Laraba ce ta rako Sajeedah tare da faggon kayan ta tare da wata yarinya
budurwa, in kun tuna Laraba tsohuwar mai aikin Kulsum, Umma ta cika alkawari da ma
ta ce sai bayan sati daya za ta turo wa Kulsum masu aiki, don daga yau an daina
aiko musu da abinci daga can gida. Kulsum ta rungume Sajeedah tana mata barka da
zuwa. Da kyar ta gane Laraba sabida ta kara tsufa. Zo ki ga murna wajen Kulsum ta
rungume tsohuwar wadda ta ke hawayen farin cikin dawowar Kulsum. Sun yi zama na
kauna da amana.
Laraba ta gaya mata yarinyar jikar ta ce, sunanta Ladidi, su za su dinga yi
mata duk wasu aikace-aikace, in tana da aike wajen Umma ta aika Ladidi. Kulsum ta
raka su dakin da za su zauna, sannan ita da Sajeedah suka wuce nata.
Wuni guda Sajeedah tana kara wayarwa da Kulsum kai a kan yadda za ta zauna da
Turaki ta mallake zuciyar sa ita kadai, don ta fahimci Kulsum din har yau tana da
raunin wayewar kai. Tare suka yi girkin rana da na dare suka adana na su Turaki
wadanda ke can suna hawan angonci. Ba su shigo gidan ba sai bayan isha, Sajeedah ta
dubi mijin ta cikin kayan sarauta abin ya yi matukar burge ta, Kulsum kuwa makalewa
ta yi daga bayan labule tana leken Turaki cikin Royal Attire din sa, kayan da ba ta
taba ganin shi da su ba. Ya yi mata kyau da kwarjini har yadda ba za ta iya
kwatantawa ba. Ya fidda tuntumemen rawanin kansa ya dubi Sajeedah da ta rungume
Abdul’Ahad a gaban sa, ya ce,
“Ina Ummu Kulsum?”
Sajeedah ta hau waige-waige, don dai ita dai ta san tare suke a falon, ba ta
san yaushe ta shige ba.
“Ai kuwa muna tare, ban san ina ta yi ba”.
Turaki ne ya ga motsi a bayan labule, ya tafi kansa tsaye ya janyo ta suka
shige daki.
“Sai kin gaya min dalilin leke na, na yi kama da wannan raggon saurayin naki
dan Abuja ne?”
Kulsum ta yi kicin-kicin da fuska, ita a dole ba shi ta ke leke ba, hadi da
zumburo baki. Bakin da ta zumburo ya sa yatsansa ibham ya dalle shi da karfi. Ta
kai hannu ta dafe bakin ta hawaye suka ciko idon ta don zafi. Sai kuma ta ba shi
tausayi, ya tarairayo ta ya rungume yana shafa bayanta a hankali cikin lallashi.
“Kulsum ko wane irin laifi na yi miki ya kamata a ce zuwa yanzu kin hakura kin
yafe min, tunda na kawo kaina a matsayin mai neman afuwa. No one is above mistake,
Kulsum don Allah ki yafe mini mu shimfida rayuwar mu haka. Ko me ki ke so zan miki
in dai za ki daina fushin nan da ni. Amma don Allah kada ki ce za ki sake bari na a
karo na biyu…”.
Saura kalaman suka makale a makoshin sa sakamakon jin hannayen Kulsum sun
zagayo ta bayan sa sun rungume shi. Wani abu da bai taba zata ba a wannan lokacin,
don haka fadin halin da Turaki ya samu kansa unimaginable ne. It was kind of gentle
romance da biro na ba zai iya rubutawa ba. Yayin da Kulsum duk da ba ta cikin
hayyacin ta sabida yadda Turaki ke gigitata da nau'ikan soyayyar sa ba ta manta da
bakin su da ke falo ba.
A hankali ta zame da kyar ta tura Turaki baya, ya fada bisa gado da baya da
baya, dariya ta bashi ganin yadda duk ta sukurkuce, just daga kissing, ficewa ta yi
tana cewa, “Kai da Abdul’Ahad babu ruwana”.
Sanda ta fito Abdul’Ahad din da Sajeedah suna bisa dining suna cin abinci.
Sajeedah ta jefo mata kallon ko ke fa? Kulsum ta yi murmushi, ta ja kujerar kusa da
Turaki ta zauna, shi ta fara serving sanan ta zuba wa kanta. Shi da Abdul’Ahad suke
maganganun da suka shafe su. A ranar suka yi sallama da su don gobe za su wuce
Abuja su kwana, su bi British Airzuwa U.K.
Sosai Kulsum ta ke kewar Sajeedah, tunda Turaki ya fita tare da su bai dawo ba
sai sha dayan dare. Kulsum ta yi wanka ta fito tana shafa mai a kan stool gaban
madubin ta, Turaki ya murda kofar dakin ya shigo sanye da fararen Pajamas.
Tunda Kulsum ta kalle shi sau daya ta dukar da kai, ba ta kara iya hada ido da
shi ba. Turaki ya kara kunna fitila mai haske a dakin yana ta kallon Kulsum sosai,
ganin komai yake tamkar a mafarki. Tamkar idan ya rufe ido kafin ya bude za ta sake
kufce masa. Rayuwa ta koya masa darussa sosai. Ya kara fahimtar ka rike abin da ka
ke da shi da daraja, ranar da ya kubuce daga hannun ka za ka sha wuya kafin ka same
shi, idan ma ka yi sa'a ka same shin ke nan!
Sannan ya fahimci soyayya ta gaskiya ba ta faruwa a lokaci daya… ita wata irin
aba ce da ba ruwan ta da lokaci, ko lafiya da dangogin su. Abu ce wadda ke faruwa a
duk sanda ta so, ta gudanar da Tunani ta sarrafa gangar jiki (ALHERI-TAKORI). In
haka ne, ke nan shi a ra’ayinsa bai yarda da abin da bature ya kira love at first
sight ba, wannan infatuation ne.
Ya karaso a hankali gaban Kulsum wadda ko shafa man da ta ke yi ta kasa ci gaba
sakamakon idanun nan na Turaki masu kama da magnetism da hasken fitila da ya wadaci
dakin. Gaban ta ya iso tamkar mai counting steps dinsa (kirga takun sawun sa).
A hankali ya tsugunna a gaban ta ya dora hannun damansa a kan tafin kafar ta,
ya jima tsugunne kanshi bisa cinyoyin ta, kafin ya dauke ta gaba daya su fice dakin
zuwa turakar sa.
Komai ya faru ne ba yadda ta zata ba, komai ya faru ne cikin kauna da soyayyah.
Gently, softly, romantically, emotionally. Dare ne da al’amuran da suka faru cikin
sa suka shige cikin kundin tarihin rayuwar Ummu Kulsumu. Ta amince da soyayyar
mijin ta Turaki, ta yarda shi din ba wanda ta sani a baya ba ne, wani sabon Turaki
ne wannan. Loving and romantic. Sannan fassarori da yawa da ta yi masa abin ba haka
yake ba, shi dai bai shirya aure ba a wancan lokacin aka aura masa ita, amma ba
kinta yake ba. Bai taba kinta ba. Ta amshi soyayyar sa da hannu bibbiyu, ta maida
martani iyakar iyawar ta, suka dunkule suka zama abu daya a wannan dare mai dumbin
tarihi a cikin rayuwar su. Ba su suka samu suka runtsa ba sai misalin karfe uku na
sulusin dare.
Goshin asubahi, a lokacin masallatai sun fara kiran sallah, Prince Turaki, ya
muskuta manne da Kulsum a jikin sa, amma sai ya ji wani sururun sanyi na shigar sa
ta kasan sa. Ya sake gyara kwanciya har zuwa yanzu bai raba Kulsum da barin jikin
sa ba don kada ya tashe ta daga barcin hutun da ta samu. Jin sa ya yi male-male a
cikin damshi, tun daga samansa har kasan sa a jike yake yarab! Daga shi har
Kulsumun.
Cikin tsananin tu’ajjibi da mamaki har ma da tsoro ya raba Kulsum da jikin sa
ya mike zaune. Wannan ruwa daga ina haka? Motsin sa ne ya tada Kulsum, juyawar ta
da zaman ta suka ankarar da ita abin da ke faruwa.

“Ta yi fitsarin kwance!”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.
Kulsum ta ambata cikin tsananin tashin hankali. Kafin ta sunkuya ta fashe da
kuka, gigitaccen kuka mai nuna zurfin tashin hankalin da ta samu kan ta. Ta dauka
ya tafi, ta dauka sun yi sallama, ashe jira yake ta yi aure ya dawo ya sake raba ta
da farin ciki a rayuwar ta???
Shi dai Turaki har zuwa lokacin ya kasa gane komai. Kukan ta ne ya kidima shi,
ya kamata, ta yi sauri ta janye jiki a hankali daga gare shi, ta koma can karshen
gado ta ci gaba da kukan ta.
Ta san rabuwarta da Turaki ta zo, a lokacin da ta gama samun duk wani
contentment na rayuwa. Babu wani namijin da zai jure rayuwar aure da mai lalurar
fitsarin kwance, balle babban likita mai matsayin consultant, kuma dan Sarki kwaya
daya tal irin TURAKI.
Kukan ta ya tsananta, ya kara gigita Turaki, gabadaya ya rasa gane me ke
faruwa? Sai a lokacin kwakwalwar sa ta ankarar da shi. Shekarun baya ya tuna da
hirar da ya ji tsakanin ta da Laraba, ashe ba ta warke ba din har zuwa yanzu, har
tsayin zaman ta a hannun marikan ta? Fuskar sa expressionless (bata nuna komai ba)
ya bar dakin jagab da pajamas din shi sai yarari yake.
A toilet din dakin sa ya cire kayan, ya sakar wa kanshi shower. Ruwan na sauka
a jikin sa yana tunanin ta yadda zai taimaki matar sa Kulsum. Tausayin ta ya bi
ko’ina na jikin sa, ko kadan bai ji kyama ba, sai ma wata sabuwar soyayya da ta
kara manne masa a zuci da ruhi, wadda tausayi ke assassawa. Yana iya hasaso how
embarrasing ta ke jin kanta, shi ya sa ta ke wannan kukan tamkar na fitar rai. Ya
sa a ran sa da taimakon Allah sai ya zama silar da Kulsum za ta samu lafiya, idan
kuma wannan ita ce kaddarar ta, wato dauwama cikin lalurar fitsarin kwance, zai ci
gaba da zama da ita cikin so da kauna, hakan ba zai raunata komai na daga soyayyar
da yake yi mata ba.
Zai saya musuwater mattress, washing machine da zannuwan gado masu yawa, zai
taimaka mata ta dinga tsaftace kanta, a duk lokacin da lalurar ta same ta.

Kulsum bayan ta ci kukan ta ta koshi, ta yi tunanin kiran Dr. Sakeenah don ta
sanar da ita, ita ma ta san da laifin ta, likita bai ce ta daina shan magungunan ta
ba ta daina, tunda ta ga cewa ta samu lafiya. Ba za ta iya tuna lokaci na karshe da
ta sha maganin ba, sai dai kuma ta baro wayar ta ne a Lagos tun gigicewar ganin
Turaki.
Ta je ta yi wanka, hawaye na bulbula, fitowar ta ke da wuya ta sa mukulli ta
kulle kanta, ba za ta iya kara hada ido da Turaki ba. What an embarassment (wannan
abun kunya har ina). Sai daga baya ta yi tunanin to wa zai gyara masa gadon idan ba
ta je ba? Gara dai ta boye kanta ta ji da gundumemiyar kunyar ta da tozartar ta.
(Wannan ne halin da mata masu lalurar Enuresis ke fuskanta tsakanin su da
mazajen su, ga wasu mazajen wannan shi ne dalilin wulakanci a gare su. Ya jama’a mu
sani cewa, babu wanda yake sama da lalura duk matsayin sa duk ilmin sa, masu lalura
soyayya da tausayi suke bukata, musamman daga mazajen su, domin kaddara ba ta wuce
kan kowa ba. Allah ka kara mana lafiya da zama lafiya, amin- Takori).

Turaki da kansa ya yaye zanin gadon, ya je ya sa shi a famfo ya zuba Ariel da
hypo ya wanke. Ya rasa yadda zai yi da katifar dakin sa, sai ya kada omo a bokiti
ya zo ya sa tawul ya dinga gogewa. Da ya tabbatar ya fita, sai ya daga ta ya
shimfide a tsakar dakin ya sakar mata fanka da A.C.
A gurguje ya shirya don Maimartaba yana jiran sa, ya fito zuwa dakin Kulsum.
Murdawa ya yi ya ji ta rufe da mukulli, ya kira sunan ta a tausashe,
“Ummu Kulsum bude min kofa”.
Yana jiyo shesshekar kukan ta da ke tashi a hankali. Zuciyar sa ta kara
raunana, ya ce, “Kulsum… please…..”.
Cikin kuka ta ce, “I cannot face you…”.
Murmushi ya yi ya ce, “Na ji to, zan rufe idona yadda ba zan gan ki ba”.
Ta ce, “Ka yi alkawari?”
Ya ce, “It’s a promise…”.

Ta zo ta bude kofar tana rakubewa a bayan kofar. Ya janyo ta ya hada da jikin
sa, “Duk wannan kukan na fitsarin ne? Idan ya sanya miki zazzabi fa? Haka kawai ina
cikin amarci na a cuce ni?”
Duk halin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, murya abin tausayi ta ce,
“Wane amarci ga mai fitsarin kwance?”
Ya kara matse ta a jikin sa sosai, sassanyan kamshin jikin sa na ratsa ta, yana
haifar mata da wata irin nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta rasa.
Ya ce, “Kulsum ki sa a ranki, ba fitsarin kwance ba, ko yoyon fitsari ki ke yi,
I’m at the extent of loving you, intending to stay with you, and vowing to help
you… we will fight this problem together (ina kan kololuwar sonki, dauke da aniyar
ci gaba da zama da ke, da kuma alkawarin taimaka miki. Za mu yaki wannan matsalar
tare) insha Allahu. Just relax and pray. Yanzu zan je in ga Maimartaba akwai inda
za mu je sai dare zan dawo. Me ki ke so in taho miki da shi?"
Hawayen farin ciki suka zubo daga idanun Ummu Kulsum. Ba ta taba tsammanin
martanin da za ta samu daga Turaki ke nan ba. Ta kara gamsuwa da cewa....this is
not the previous Turaki… wannan wani sabon Turaki ne, mai dauke da kauna ta ban
mamaki a gare ta.
"Ba abin da nake so sai kai Prince dina”. Ta fada tana kwantar da kai a kirjin
sa. Kaso tamanin cikin dari na tashin hankalin ta ya kau. Ya dan bubbugi bayan ta,
ya ce,
“In dai Turaki ne kin samu, I’m only yours. Zan kawo miki waya sabida su Goggo,
amma ban yafe ba in ki ka yi magana da Taufeeq”.
Ta lumshe ido tana murmushi, ta ce, “Ko ka yafe ba zan yi ba. Bana neman komai
daga sauran maza, you are more than enough to me. Allah ya bar mu tare cikin
alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi”.
Sosai Turaki yake kissing din kowacce halitta ta fuskar Kulsumu, ido, hanci,
goshi, da baki sai da suka karbi rabon su na sassanyar passionate kiss daga Yarima
Abubakar Turaki. Sannan da kyar ya janye ya gyara zaman hular sa ya fice da gudu-
gudu sauri-sauri ganin sunan Maimartaba a kan fuskar wayar sa. Kulsum ta bi shi da
lallausar murmushi. Ji ta ke kamar su dauwama cikin wannan yanayin da ba ta taba
samun kanta a mai dadi da sanya nutsuwar sa ba.
Ko da ya dawo a ranar kin zuwa dakin sa ta yi, har yanzu kunyar ba ta sake ta
ba. Ta yi shirin kwanciya ke nan sai ga shi ya shigo, tun daga bakin kofa ya jefa
mata harara.
“Me ki ke nufi da ni ne matar nan? Ina ta jiran ki ki zo mu cike wasu takardu,
kin barni ni kadai? Shirin kwanciya ma ki ke yi abun ki alhalin ga turakar mijin
ki?”
Kulsum ta langabar da kai abin tausayi, ta ce kasa-kasa.
“Ina tsoron kada ya kara zuwa ne”.
Ya sa hannu ya dago habar ta, murmushi ya sakar mata wanda ya ratsa har cikin
ruhin ta. Sannan ya sumbaci bakin ta ya ce, “To sai me? Har na sayo mana injin
wanki da katon din hypo da na omo (Ariel). In mun yi sai mu wanke. Watarana sai
labari…..!”.
Da karfi Kulsum ta kankame shi tana wani irin kuka. Gabadaya ya daga ta suka
fice daga dakin. Cike takardu bai yiwu ba a wannan dare, domin ya kasance daren
rahma ga ma’auratan, sun raya shi har yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Amma a
karshe Kulsum ta ki yarda barci ya dauke ta, tana kallon Turaki yana barcin sa
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali irin wanda miji ke samu idan ya samu kyakkyawar
gamsuwa daga matar sa.
Sai zarya ta ke daga gadon zuwa toilet tana kakalo fitsari. Ba ita ta kwanta ba
sai da suka yi sallar asubahi, Turaki ya dube ta tana lazimi idanun ta sun yi luhu-
luhu. Ya daure fuska sosai ya ce, “Look, hau gado ki kwanta sai karfe goma na yarda
ki tashi daga barci. Wannan daura wa kai wahala har ina? Ina ce katifa dai tawa ce
ko? Zanin gadon ma nawa ne ba naki ba?”
Ta sunkuyar da kai tana murmushin maganar sa, soyayyarsa na karuwa a zuciyar
ta.
“Oya! Hau ki kwanta tun ban canza manufa ta ba”.
Ta gane me yake nufi, don haka ta ja jiki zuwa gadon ta kwanta a dofane, ya
jaquilt ya rufe ta da kansa. Tare da sunkuyawa ya sumbaci goshin ta.
Ta yi barci kuwa sosai, domin kuwa shi ba'a cin bashin sa. Sai dai kuma ta
tashi ne again cikin yanayin da ya fi na jiya. Turaki yana dining yana karyawa da
abincin da Laraba ta tanadar musu. Sai da ya gama ya dawo dakin, ya shiga toilet ya
yi wanka ya fito yana zaben kayan da zai sa ba tare da ya san halin da Kulsum ke
ciki ba. Ta sanya kanta karkashin filo tana kuka, wanda da hawaye kawai ta ke yin
sa babu sauti. Ba ta so yau ma ya yi aikin fitsari shi ya sa ta sa hannu ta toshe
bakin ta.
Sai da ya gama tsaf! Ya fesa turarensa one man show, sannan ya iso gabanta don
ya duba ko ta tashi. Filon da ta danne kanta da shi ya dauke, “Kina so ki danne
numfashin ki ne?”
Gani ya yi wajen ya jike sharkab da hawaye. Nan ya gane halin da ta ke ciki.
Fuskar sa ta nuna damuwa ya ce, “For God’s sake Kulsum, wannan kukan ne zai yi
maganin lalurar? Duk abin da na gaya miki bai shiga kunnen ki ba. In dai a kaina ne
ki ke shiga wannan halin ni kam kina zaluntata! Damuwar ki da fitar hawayen ki sune
manyan damuwa ta ba fitsari ba. Idan ‘depression’ ya kama ki ba zan yafe miki ba”.
Da kyar ta mike cikin tsananin jin kunya, ya taimaka mata ta hanyar kama hannun
ta ta mike ta shige toilet. Ya yaye zanin gadon, amma wannan katifar in ba ta sha
rana ba yau akwai matsala, domin ko an goge da omo sai ta yi warin damshi.
Tana fitowa ta same shi ya balle links din hannun rigar shi ya kwance botir din
wuyansa ya zage yana goge katifar. Kifa kai ta yi a jikin bango tana hawaye.
Turaki ya yi kwafa ya ce, “Ki yi abin da ki ke ganin shi zai fishsshe ki”.
Duk runtsi ba zai fidda katifar nan waje ba sabida ‘yan aikin su, balle Laraba
da yake da masaniyar ta san Kulsum na da lalurar. Ya rasa yadda za su yi da
katifar, ya dai sakar mata fanka ta sama da ta kasa. Ya canza kayan jikin sa ya je
ya shigowa da Kulsum abin da za ta ci. Da kyar ya samu ta iya cusa dankali biyu a
bakin ta. A ran ta ta yanke ba za ta kara kwana dakin Turaki ba duk abinda zai ce
mata gara ta je ta yi ta kazantar ta ita kadai a dakin ta.
“Tea din nan sai kin shanye shi, in har kina son zaman lafiya Kulsum".
“Ka yi hakuri Prince, ba ni da appetite, wallahi na tsani kaina!”.
Turaki ya tsura mata ido, kalaman rarrashi sun kare masa. A irin wannan stage
din ne mata da yawa ke haduwa da depression wanda zai iya yin sanadin suicidal
thought.
Ya ajiye kofin shayin ya matsa gare ta ya rungume ta. Ta kwantar da kai a kan
kirjinsa tana ta sharbar kuka.
Ya ce, “Is o.k Kulsum, na san abin da ki ke ji. Amma don Allah ki kwantar da
hankalin ki, wannan lalura ba kanki farau ba, mata da yawa suna fama da ita, wani
lokacin ma har maza. Tun jiya na yi magana da kwararren nephrologist din da zai
duba ki Dr. Ibraheem Mansur Takai (Rayuwar Rayhana). Za mu hadu da shi a U.K, zai
zo asibitin da nake daga Illinoise (Chicago) kan wani aiki da za mu yi tare. So
relax please, stop these waste of tears, ni ko ba ki warke ba ina sonki haka! Zan
kuma ci gaba da zama da ke cikin kowanne hali, to the very end”.
Kulsum ta shafe hawayen idanun ta, har yanzu kanta na bisa kirjin Turaki, ta
ce, “Watarana za ka gaza… watarana za ka auro wata… in ta gane zan wulakanta… zan
tozarta…”.
Hannu ya sa ya toshe mata baki.
“Ban yi miki alkawarin har abada ba zan kara aure ba, tunda Ba-sarake ne ni. Amma
Kulsum ko aure ya kama ni sai na tabbata kin warke. Ba dai in yi aure saboda
lalurar ki ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki”.
Kara shigewa jikin sa ta yi tana jin kanta tamkar a kan gajimare. Turaki ya
gama yi mata komai a rayuwa, Allah ya sa ya tabbata a hakan.
“Now, gaya min treatments din da ki ka taba karba a asibiti, in cike a wadannan
takardun zan tura wa Dr. Ibraheem…”.
Tiryan-tiryan ta soma gaya masa tun zuwanta Lagos gidan Aunty Sakeenah,
treatments din da ta karba; pharmacological and non-pharmacological. Result din da
treatments din suka bayar. Kwayoyin maganin da aka dora ta a kai, wato tricyclic
antidepressants, tofranil (imipremine) da kuma (desmopressin acetate) da ta jima
tana sha. Ta kuma daina sha ba tare da likita ya dakatar da ita ba, sai don a
tsammanin ta ya tafi ke nan.
Duka Turaki ya shigar da bayanan, sannan ya tura wa Dr. Ibrahim ta email din
sa. Ba jimawa response din sa ya shigo, inda ya ce ya amince zai ga Kulsum a U.K
sati uku masu zuwa.
Turaki yake gaya mata da ma hutun da ya dauka na aure na wata daya ne, don haka
za su koma a daidai lokacin da Dr. Takai ya diba musu. A nan ta ke ji ya zo Lagos
ne ziyarar aiki ba'a can yake ba dindindin. Yana aiki ne da asibitin koyarwa na
jami’ar Reading wato Royal Berkshire Hospital wanda reshe ne na NHS Foundation.
A nan ne ta san abubuwa da yawa game da Turaki wadanda a baya ba ta sani ba.
Har haduwar su a jami’ar Reading shi da Abdul’Ahad da irin abotar da ke tsakanin
su, da rawar da ya taka wajen taimaka mishi ya same ta. Ya dube ta ya yi murmushi,
“Shi ya sa na dame ki sosai kan ki karbi bakuncin su, they are your real
supporters”.
Yana kwance rigingine da laptop a kan kirjinsa yayin da kansa ke bisa cinyoyin
ta suke hirar, a lokaci guda yana processing visa dinta ta shiga U.K as his spouse.
In ka gan su sai sun ba ka sha’awa, yatsun ta cikin sumar kansa wai kitso ta ke
mishi cikin tarin kwantacciyar sumar sa duk ta duddunkule mishi gashi, ko kofar
gida yau bai fita ba, duk don kada ya fita Kulsum ta koma cikin damuwar ta.
Da magriba ne ya je ya yi sallah ya dawo, ya ce ta shirya su je ta gaida Umma
da sauran mutanen gida.
Sosai ta yi shiga ta alfarma

Please Login or Register in order to submit comment