You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ta dauko handbag din ta, ta duba return ticket din ta ta tabbatar
yana nan. Tana da kudi wajen dubu ashirin a jakar ta, ta tabbata za su ishe ta har
ma su yi canji. Allah-Allah ta ke a kira sallar asubahi, daidai lokacin da ta san
maigadin gidan Sakeenah na tafiya zuwa masallacin kusa da su.
Yadda Kulsum ta ga rana yau haka ta ga dare. A kan idonta da kunnen ta aka tada
sallar asubahi, ko kayan ta ba ta dauka ba ban da handbag, waya da hijabin sallarta
dogo har kasa. Sadaf! Sadaf! Ta fice daga dakin ta bar Nasmah na ta kirba minshari.
A zuciyar ta tana fadin, “Sai watarana Nasmah! Zan yi kewar ki ba ‘yar kadan ba”.
Ta kai bayan hannunta ta shafe hawayen idanun ta ta fice daga dakin.
Kofar falon wadda za ta fidda kai waje jam-lock aka saka mata ta ciki. A hakali
ta bude ta fice ta rufo kofar silently. Kanta tsaye ta doshi get inda cikin sa’a ta
tadda maigadi ya shiga masallaci kamar yadda ya saba. Sakatar kofar wucewar mutum
daya ta zare ta fice a hankali tare da rufo kofar.
Sauri ta ke ta yi kamar za ta tashi sama, sai da ta kai bakin titi ba ta ga
mota ko babur ba. Ta dan jima tsaye a titi tana waigen bayanta ko an biyo ta. Cikin
ikon Allah sai ga wani okada-rider ya zo zai gifta gabanta. Da saurin ta ta tare
shi, ta ce da shi cikin harshen Turanci ya kai ta airport na garin Lagos ko nawa
yake so za ta ba shi.
Mai okada har cikin airport ya shiga da ita, naira dubu biyu ya ce ta ba shi.
Ba musu ta kirgo ta ba shi, sannan ta karasa. Ba yau ta fara hawa jirgi daga Abuja
zuwa Lagos ba, don haka ba ta sha wahalar samun jirgin Abuja ba, amma sai karfe
takwas na safe zai tashi, lokacin bakwai ta kusa. Don haka ta soma neman inda za ta
buya, ta yadda ko su Taufeeq sun biyo bayan ta ba za su ganta ba. Cikin fasinjoji
ta kutsa ta shige, masu jiran lokacin tashin jirgi, ta ja hijabin ta ta rufe fuskar
ta.
Karfe bakwai jirginsu ya tashi daga Lagos zuwa Abuja. Tana sauka a Abuja ta
nemi taxi ta ce a kai ta Jabi Motor Park. Tana zuwa ta tambayi inda ake lodin Kano,
aka nuna mata. Ta biya kudin mota, cikin sa’a motar saura mutum daya ta cika, tana
shiga direban ya tada mota suka durfafi Kanon Dabo.
Sai wannan lokacin Kulsumu ta samu ta sauke ajiyar zuciya, at least she escaped
daga Taufeeq har Turaki. Ta san Baffa da Goggo za su fahimce ta, sannan ba za su
taba bari rayuwar ta ta tozarta da auren mashayin giya ba. Kamar yadda ba za su
kara bari azzalumi, mugu, mai son kansa, makiyin ta Turaki ya sake dawowa cikin
rayuwar ta ba. Ta sa a ranta ta gama zaman Abuja, ta gama zaman gidan Hajiya
Nasara, ta dawo gaban kakannin ta kenan har abada! Da ma karatu ta je yi, kuma
cikin yardar Allah ta yi ta gama. Za ta koma mahaifar ta ta gina sabuwar rayuwa, ba
za ta yarda ta wargaza rayuwar ta da sunan halarci ba don ko Ubangiji bai yarda da
wannan ba. Haka ba za ta yarda a karo na biyu Turaki ya sake zamowa barrier ga
farin cikin rayuwar ta ba.
Tafiyar awanni biyar ta kawo su Kanon-Dabo, inda daga nan ta hawo bus mai zuwa
garin GAYA. Bakin ta dauke da addu’o’i masu yawa na Allah ya sa Goggo da Baffa su
fahimce ta, su fahimci ta yi hakan ne ba don butulci ga Hajiya Nasara ba, sai don
ta gina wa kanta kyakkyawan future. Ba ta ji dadin auren kuruciya ba, ba ta fatan
ya kasance shi ma auren da ta yi cikin cikakken hankalin ta ya zo ya samu nakasu,
tunda kuwa zuciyar ta ba za ta iya juriyar zama da mashayin barasa ba.

*** *** ***
Baffa Jibo na gyare-gyare cikin dakin da yake jibge amfanin gonar sa, kafin ya
kai su kasuwa. Ya jiyo wata siririyar sallama kamar ta Kulsumu. Kwana biyu ke nan
da tafiyar Goggo Abuja, shi kadai ne a gidan, shi bai je ba don nan Gaya za a taho
daurin aure ranar asabar. Duk wanda ya kamata su gayyata sun gayyata, mutanen
'Yalleman gobe za su wuce Abuja, inda za su kwana biyu daga can za su taho bakidaya
ranar juma’a zuwa Gaya tare da Hajiya Nasara da jama’arsu, a yi daurin aure asabar,
su juya da amarya ranar lahadi.
To sai ga wata makalalliyar sallama yana ji kamar muryar Kulsumun. A cikin
muryar akwai jigata da alamun gajiya. Da sauri Baffa ya fito, ya kalle ta sanye da
zumbulelen hijabin ta har kasa idanuwan ta duk sun fada, ta yi zuru-zuru saboda
wahala da yunwa. Baffa ya bude baki ya ce,
“Kulsumu, ke ce? Ko kuwa mai kama da ke ce?”
Ai tana ganin Baffa, hawaye ya kece mata. Ta karasa da azama ta rike shi cikin
kuka, ta ce, “Ni ce Baffa”.
“Lafiya na gan ki yanzu? Ke da waye?”
“Ni kadai ce, tun daga Lagos na taho”.
Baffa ya yi salati, ya sallamewa Ubangiji, amma sai ya kama hannun ta suka
shiga dakin Goggo, sai da ya tabbatar ta kwanta a gadon Goggo ya juya yana fadin,
“Jira ni ina zuwa”.
Baffa bai fi minti goma sha biyar ba ya dawo rike da bakar leda guda biyu,
gasasshen balangu ne mai yawa da damammiyar fura a ciki, ya samu har zuwa lokacin
kuka ta ke yi kasa-kasa. Babban tashin hankalin ta shi ne, kada Baffa da Goggo su
kasa fahimtar ta sabida kunyar Hajiya Nasara. Ba ta da nufin tozarta Hajiya Nasara
ko shi Taufeeq din kansa, amma wannan aure ba za ta yi shi ba, domin ba ta son ta
kara yin aure ta sake fitowa, auren mashayi kuwa babu kwanciyar hankali a cikin sa,
sannan ‘ya’yan da za ta haifa watarana sai sun tuhume ta da zaba musu uba mashayin
giya tunda dai Allah da ya nufe ta da gani gabanin auren, ya nufe ta ne da rahamar
sa.
Ko da ma can ita ba damuwa ta yi da ta yi aure ba, sannan Taufeeq ba wai tana
masa mugun so ba ne, abubuwa ne da yawa suka taru suka yi dalilin amincewar ta da
auren sa.
Muhimmi shi ne, mahaifiyar sa da ‘yan uwan sa, sai kuma takurawar su Goggo a
kan ta yi auren. Amma ita tun daga kan auren Turaki ba ta kara marmarin aure a
rayuwar ta ba. Har yanzu ba ta daina tsoron maza ba. Ba ta daina tunanin dukkansu
halin su daya ne ba. Halin selfishness da heartlessness irin na TURAKI. Wadanda ba
su dauki mace a bakin komai ba.
Baffa ya ce, “Tashi maza ki ci wannan, ko kin samu karfin yin sallah”.
A halin da ta ke ciki ta manta da wani abu wai shi abinci. Duk wani kyakkyawan
tunanin ta ya ta’allaka ne a kan yadda za ta samar wa kanta mafita daga auren
Taufeeq, auren da sauran kwanaki uku a daura shi. Amma ta san in ba ta ci abincin
nan ba, ba za ta samu nutsuwar yi wa Baffa bayanin da zai fahimce ta ba. Don haka
ta sauko kafafun ta daga gadon karfen Goggo, ta karbi ledojin da Baffa ke mika
mata. Ya juya ya fita yana fadin,
“Ki ci ki yi wanka da sallah, sannan mu zauna in ji me ya faru kin ji Kulsumu?
Ki kwantar da hankalin ki, da raina da lafiya ta babu abin da zan kasa yi miki”.
Wadannan kalaman na Baffa su suka sanyaya mata zuciya. Har ta samu karfin
gwiwar cin naman sosai. Da ma tsakanin ta da balangu akwai kyakkyawan aminci. Ta
shanye furar gabadaya wadda ba'a cika mata sukari ba, sannan ta tashi ta je ta yi
wanka ta dauro alwala. Sai da ta rama duka sallolin da ke kanta, sannan ta ji
nutsuwa ta soma shigar ta.
Sai da Baffa ya dawo sallar isha sannan ya kira Kulsumu a dakin sa. Ta shigo
sanye da hijabi ta zauna ta rakube abin tausayi. Baffa ya ce, “Kulsumu?”
Ta ce, “Na’am Baffa”.
“Ina so ba tare da kin boye min komai ba, ki gaya min duk abin da ya faru. Mene
ne dalilin tahowar ki daga wajen marikan ki kwanaki uku kafin daurin auren ki ke
kadai tun daga Lagos?”
Kulsumu ta share hawaye, ta ce, “Baffa auren ne na fasa”.
Baffa ya hadiye fushin sa da razanar sa, ya ce, “A wane dalili, ko ko don ki
wulakanta dattakon mu, ki saka hairan da sharran?”
Hawaye suka zubo wa Kulsumu, ta ce, “ko daya Baffa, sai don in tserar da kaina
daga sake zawarci a shekarun girmana, bayan wanda na yi a shekarun kuruciya ta, in
zaba wa ‘ya’yana uba na gari, in kuma yi jihadin ceton tarbiyyar ‘ya’ya na a can
gaba”.
Baffa ya kasa fahimtar ta, sai ya ce, “kai tsaye ki gaya min, me ya faru?”
Kulsumu ta sunkuyar da kai.
“Baffa zan fi so a ce yana zaune zan fada, don kada ya samu damar cewa na yi
masa sharri. Sannan Hajiya da Daddy kada su zarge ni da munafuntar su”.
Baffa bai ce komai ba, sai ya yi shiru yana nazarin kalaman ta, amma hankalin
sa ya tashi sosai, don ya kasa cankar inda zancen ta ya sa gaba.
Kira ne ya shigo wayar Baffa a lokacin. Yana dagawa ya ce, “ga Nasaran nan ma”.
Ya amsa suka gaisa a mutunce yadda suka saba, sai dai ya ji muryar ta ba yadda ya
saba jin ta ba.
Ta ce, “Baffa, Kulsumu Gaya ta taho?”
Baffa ya dubi Kulsumu, sannan ya ce, “ga ta nan a gabana”.
Wata irin ajiyar zuciya Hajiya Nasara ta saki a fili, ta jero alhamdulillahi
sau uku. Ta juya ta ce da su Goggo,
“Kun ji Kulsumu na Gaya”.
Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, “Idona idon Kulsumu… wannan
yarinya ta dauki alhakin mu, ni Taufeeq na fi tausayawa, dubi yadda ya fita
hayyacin sa sabida neman ta, wannan sakarci da me ya yi kama? Ki kamo hanya tun
daga Legas ba tare da sanin kowa ba?”
Hajiya ta nisa, ta ce “Ku daina fadan nan Goggo, ni na tabbata Kulsum cikin
hankalin ta ta ke, akwai muhimmin abin da ke damun ta da ya sa ta aikata hakan. Da
ma gobe za mu tafi Gaya dukkan mu ko mene ne za mu hadu a yi maganin sa, Daddy sai
ranar daurin aure ya yi niyyar tafiya, amma gobe zan sa shi a gaba mu tafi tare
gabadaya har Taufeeq din”.
Hajiya Nasara ta kira Malam Hadi ta ce da shi, mutanen ‘Yalleman kada su zo
Abuja, su zarce Gaya su ma gobe can za su tafi, an fasa yin kamu da wunin a Abuja.
Taufeeq na shigowa ta gaya masa Kulsum na Gaya,. Zama ya yi jabar! A kan kujera ya
rasa abin da ke masa dadi. Me ke damun yarinyar nan ne tamkar mai motsuwar
kwakwalwa?
Hajiya Nasara ta dube shi ta kasan idanu kafin ta yi magana cikin bacin rai.
“In ma wani abun ne ka yi mata wanda har ta zabi ta koma wajen iyayen ta, kada
ka yi tunanin za ka yi amfani da ni ka cuce ta, ita din marainiya ce kuma amana a
hannuna. Zan yi adalci ne na gaskiya a tsakanin ku”.
A jigace Taufeeq ya dago ya dube ta, he is looking helpless tun tafiyar Kulsum,
tun jiya yake cikin tashin hankali da wahalar da Kulsum ta sabbaba masa. Shi kuwa
me zai yi wa Kulsum da har za ta zabi barin su? Babu komai cikin zuciyar sa a kanta
sai tsananin so da kaunar ta. Iyakar tunanin sa ya san bai yi mata komai ba. Ko dai
Kulsum ta fasa auren sa ne shi ya sa ta ke tsiro da wadannan bakin halayen? Wani
abu da shi kuma ba zai taba lamunta ba, ya yi saken da Kulsum za ta kubuce masa.
Shi kadai ya san wahalar da ya sha kafin ya samu kanta, ko me ta ke so zai yi mata…
amma ban da fasa aure!
Washegari tun asubah suka kamo hanyar Kano a cikin babbar (Land Cruiser) din
Daddy, Taufeeq ke jan motar, Daddy na gefensa, Hajiya Nasara da Goggo suna baya,
Nasmah ba ta biyo su ba sabida ba za ta iya jure tafiyar mota ba, za ta jira su har
su dawo tare da amarya in an dauro aure. Mujaheed sai goben zai bi su ya samu
daurin aure.
Karfe goma sha daya na safe suna cikin Kano, daga nan suka dauki hanyar Gaya.
Wajen karfe daya na rana Taufeeq ya kashe mota a kofar gidan Malam Jibo.

(Daga can nesa da su, wani gajeren saurayi ya fiddo waya jikin sa har rawa
yake, ya lalubo lamba ya kara a kunnen sa).

*** *** ***
Daga inda ta ke kwance a kan gadon karfen Goggo tana jiyo sallamar su daya
bayan daya. A hankali ta runtse ido tare da kiran sunan Allah. Goggo ce ta fara
shigowa dakin ta haska ta da tocilan kasancewar dakin ba haske. Kwafa ta yi tare da
cewa,
“Kin kyauta abin da ki ka yi. Shin Kulsumu ke karamar yarinya ce, ko ko goyon
ki ake yi? Kin bi kin daga wa bayin Allah hankali babu gaira babu sabar. Yanzu ga
shi kin taso su bagatatan, wai kina cikin hankalin ki kuwa?”
Kulsumu ta gyara kwanciyar ta ba ta ce wa Goggo komai ba. Ta yi bambamin fadan
ta har ta gaji, Kulsumu ba ta tanka mata ba. Hajiya Nasara ce ta shigo ta bude
tagogin dakin da Kulsumu ta rurrufe, haske ya wadaci dakin.
Ta ce, “Fadan nan ya isa haka Goggo, ki bari su Daddy su dawo sallah sai mu
zauna da ita mu ji damuwar ta. Na san Kulsumu ba za ta yi abubuwan da ta ke yi haka
kawai ba”. Sannan ne Kulsumu ta samu lafiya daga sababin Goggo, ta sauko ta yi wa
Hajiya Nasara barka da zuwa, tare da tambayar Nasmah.
Hajiya Nasara kallon ta kawai ta ke tana mamakin yadda ta zabge cikin kwana
biyu kacal. Ta ce, “Nasmahn da ki ka kusa sa wa nakuda lokacin ta bai yi ba. Ki ka
jefa su a tashin hankali, ai ba ki da guts na tambayar ta. Amma Kulsum ko ma mene
ne ki tsallake ni ki taho tun daga Lagos har Gaya ke kadai? Gaskiya ban ji dadi ba.
Na dauka ni ce mutum ta farko da za ki fara dosa da kowacce damuwar ki?”
Kulsum ta yi kasa da kai, ta ce, “Ki yi hakuri, ba zan sake ba Mum”. Iya abin
da ta fada ke nan. Don bata da kalaman kare kan ta.
Bayan kowa ya yi sallah mazan sun dawo daga masallaci, Baffa ya yi musu
shimfida a falon sa. Tunda suka shigo Taufeeq ke raba idon ganin Kulsumu amma ko
inuwar ta bai gani ba. Har sai da Baffa ya yi wa Goggo umarnin a kirawo Kulsumu.
Daddy na zaune kusa da Baffa, Taufeeq a kusa da shi, sai Hajiya da Goggo daga
kusa da kofar dakin. Kulsumu ta yi sallama ta shigo kanta a kasa, ta ja mayafi ta
rufe fuskar ta. Daga kusa da Hajiya ta zauna ta ki yarda ta kalli bangaren da
Taufeeq yake, wanda ke cikin dukkan damuwar duniyar nan, ya rasa abin da ke damun
ta. Ya bi ta da kallo har ta nemi wuri ta zauna.
Baffa ne ya bude taron da addu’a, sannan ya ce, “Na ji dadi da ku ka zo
bakidayan ku, domin na yi-na yi da Kulsumu ta fada min abin da ya taso da ita haka
afujajan tun daga Lagos har Gaya ita kadai, ta ki gaya min. Ta ce sai Taufeeq yana
zaune”.
Ya gaya musu a halin da ta zo masa jiya na jigata da fita hayyaci, sannan ya
dube ta, ya ce, “To Kulsumu, ga Taufeeq ga iyayen sa, ga kuma mu kakannin ki
wadanda ba ki da wanda ya fi su, muna so ki gaya mana abin da ke damun ki, ko
hankalin wadannan bayin Allah ya kwanta a ci gaba da shirin daurin aure”.
Kulsumu ta muskuta, ta ga cewa wannan ita ce damar ta ta karshe, idan ta yi
shiru Baffa ya fusata da ita, ko ta zo daga baya ta fada ba zai saurare ta ba. A
cikin ranta kuma sai ta ji tausayin Taufeeq ya darsu mata, don ita ta san irin
masifaffen son da yake mata. Amma dole ta fadi abubuwan da idanun ta suka gane
mata, ko da a ce zai musanta hakan. In ba haka ba hankalin ta ba zai taba kwanciya
da shi ba.
“Ke muke saurare Kulsumu, duka wajen nan babu bare, kamar yadda babu abokin
wasan ki, idan ba ki da damuwa ki fada mana mu kama abubuwan da ke gaban mu”. In ji
Goggo.
A hankali muryar Kulsumu ta fito, ta ratsa kunnuwan su.
“Baffa, na fasa auren Taufeeq, ku yi hakuri”.
Goggo ta yi shiru tana mamakin karfin halin Kulsumu, shi kuwa Taufeeq dagowa ya
yi a firgice ya dube ta. Duk da bai yi sa’ar ganin fuskar ta ba. Daddy ya hadiyi
miyau da kyar, Hajiya Nasara kuwa a ranta cewa ta yi, ta san za a rina, don tuntuni
ta yi zargin Taufeeq shi ne matsalar Kulsumu.
Baffa ya ce, “Ko za ki fadi dalilin ki, tunda Allah ya hana hukuncin da babu
hujja?”
Kulsumu ta yi shiru, Daddy ya ce, “Kulsumu feel free to talk, we are all here
for you. Idan mun amince da hujjojin ki ba za a daura auren nan ba”.
Tausayin iyayen Taufeeq ya kama Kulsumu, amma haka ta rufe ido ta fadi abubuwan
da ta gani a cikin firij din sa. Ta kare da cewa, “Ina tsoron auren ko da mashayin
wiwi ne, balle giya. Ina tsoron halin da zan fada a gaba, da kuma ranar da
‘ya’yanmu za su gane dabi'ar mahaifin su, su zarge ni da zaba musu mai wannan
dabi’a. Amma in Yaya Taufeeq ya ce na yi masa karya, yana iya rantsewa ba haka ba
ne”.
Tsit! Ka ke ji a falon, yayin da Taufeeq ya sunkuyar da kai yana hada zufa. Bai
taba tozarta a rayuwar sa irin yau ba. Bai taba zato watarana asirin sa zai tonu ga
iyayen sa ba, bai taba zaton abin da Kulsumu ta gani kenan ba ya hargitsa ta haka.
Tun farko shi me ya kai shi kiran ta zuwa gidansa ya kasa hakurin a daura musu
aure? Yau ga abin da ya janyo wa kansa.
Hajiya da Daddy ne suka tsura masa ido, Daddy ya yi karfin halin cewa.
“Da gaske ne Taufeeq?”
Ya kara yin kasa da kansa kamar ya roki kasar ta tsage ya shige.
Hajiya Nasara ta ce, “Da gaske ta ke ko sharri ta yi maka?”
Cikin tsananin nadama Taufeeq ya ce, “Ba ta yi min sharri ba. Tabbas ta gani
din. Amma Mum don Allah ku yi min afuwa, wallahi ban dade da fara sha ba… a komawa
ta Lagos ne don in samu in rage tunanin ta, a lokacin da ki ka ce sai na jira ta
for some years… na ga cewa ba zan iya jiran ba, shi ne na nemi abin da zai yi
assisting dina, amma wallahi daga yau Mum na bari, na bari har abada, ba zan sake
ba. Tsautsayi ne”.
Goggo ta kawar da kai, jin hawaye na son zubo mata. Tausayin Nasara ya yi
bala’in kama ta ganin halin tashin hankalin da ta fada lokaci daya. Daddyn Taufeeq
kuwa kada ka so ka ga fuskar sa a lokacin sabida tsananin fushin da ke cikin ta.
Ya ce, “Taufeeq, sabida mace ka zabi ka sha GIYA, ka saba wa Ubangijin ka? Duk
tarbiyyar da uwarka ta yi maka? Ba ka sha giya a Turai ba sai a Nigeria Muhammad
Taufeeq?”
Hawaye Taufeeq ya soma, ya ce, “Daddy na yi kuskure, na yi nadama, zan yi
istigfari, amma don Allah kada ku hana ni auren Kulsum, wallahi daga yau na bar
giya har abada!”.
Hajiya Nasara ta mike hawaye fal idon ta, ta ce, “Maganar aure tsakanin ka da
Kulsumu babu ita, na soke ta har abada. This is your punishment, ka je ka yi
karatun-ta-nutsu. Don mai shan giya bai iya rikon aure sai dukan mata. Allah ya sa
hakan shi ne mafi alkhairi”.
Goggo ta ce, “Ku yi masa afuwa mana, don Allah ke Kulsumu ba kya afuwa? Da
Allah ba ya afuwa gare mu da tuni bai kifar da duniyar ba? Dukkan mu masu kuskure
ne, sai ake so in muka gane kuskuren mu a karbi hanzarin mu. Ki yi hakuri tunda ya
ce ya bari”.
Kulsumu ta girgiza kai tana hawaye.
“Ba zan iya ba Goggo, tunda Hajiya ta ce a yi hakuri, to a yi. Zan taya Yaya
Taufeeq addu’a Allah ya ba shi wadda ta fi ni”.
Daddy ya ce, “Goggo a bar maganar nan, Taufeeq has to be punished don gobe ya
gane ba duk abin da ka ke so sai ka same shi dole ba, a kuma lokacin da kake so. Ya
je ya yi karatun-ta-nutsu, ranar da ya tabbatar ya zama mutumin kirki ya dawo ya
auri Kulsumu, amma aure gobe babu shi”.
Ya mike shi ma ya fice.
Hawayen idon Taufeeq suka gangaro, ya ce, “Don Allah Baffa ku ba su hakuri, ina
son Kulsum ba zan iya hakura da rashin ta ba…”
Baffa ya ce, "Taufeeq yanzu sun dauki zafi, ka bari su huce. Ba za su saurare
mu ba. Ku tashi ku je, Allah ya yi muku albarka”.
Duk yadda Taufeeq ya yi don ya kebe da Kulsumu ya samu ya lallashe ta ta ki
fitowa daga dakin Goggo, har Daddy ya yi kiransa domin su tafi cikin Kano su kama
hotel su kwana, gobe su biyo su dauki Hajiya Nasara su wuce, don lokacin magriba ta
kusa ba za su iya kama hanya ba.
Haka Taufeeq ya bi bayan Daddy, yana mai jin karshen duniyar sa ya zo. Yana mai
hasaso yadda rayuwa za ta koma masa babu Kulsumu. Ya yi nadama sau ba adadi,
nadamar da ya tabbatar iyayen sa ba za su karbe ta a wannan lokacin da suke cikin
tsananin fushi da shi ba.
Sun idar da sallar isha, Hajiya Nasara na kwance a dakin Goggo, zazzabi ya rufe
ta, Goggon sai ba ta baki ta ke, tana cewa, ta dauki abin nan da sauki kada ciwon
zamani ya shige ta, yaran yanzu ai kowanne da matsalar sa, kuma Taufeeq ya yi
nadama tana da tabbacin in ya auri Kulsumu ba zai sake ba.
Daga kwancen da ta ke Hajiya Nasara ta ce, “Allah ya kiyaye in hada Kulsumu da
mai shan giya, kuma tunda sai ya samu Kulsumu ne zai bari ya je ya yi ta sha,
Kulsumu ta riga ta tsere masa’.
Sallamar yaro suka jiyo daga tsakar gida, Goggo ce ta fito tana amsawa.
Ya ce, “Wai ana sallama da Baffa”.
Goggo ta ce, “Tunda ya tafi sallah bai dawo ba…”.
Ba ta rufe bakin ta ba sai ga Baffan na shigowa, fadi yake, “Kai din bako ne da
za ka tsaya a waje kana sallama? Da can haka ka ke yi ba sallama

Please Login or Register in order to submit comment