You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ke yi kan ka
tsaye ka shigo ba?”
Ya shigo, bakon na biye bayan sa. Hasken farin wata ya haska wa Goggo fuskar
Yarima Turaki, gabadaya tsakar gidan su ya dauki kamshin sassanyan turaren sa, a
idanun Goggo har tsayi da girma ya kara, fatar sa sai sheki ta ke a cikin hasken
farin wata, ga wata shadda mai maiko da ya zuba sai walainiya ta ke (Excelcior), ya
dora hula wadda ta dace da shaddar jikin sa ruwan toka, hannayen sa biyu zube cikin
aljihu kamar yadda ya saba. Sai faman sunkuyar da kai yake, yana murmushin da da ka
gani ka san na rashin nutsuwa ne.
Dazun nan da safe yaron nan Sadi makwabcin su Kulsumu da ya sa ya dinga yi masa
dakon zuwan ta Gaya ya fada masa ta zo har da marikan nata, kuma ya ji kishin-
kishin gobe ne za a daura auren ta.
Duk abubuwan da ke gabansa haka ya zubar da su ya taho Gaya, bai samu jirgi da
wuri ba shi ya sa isowar sa Gaya ke nan ko gidan su bai shiga ba ya zarto nan, don
ya ga ko da abin da zuwan sa zai amfana masa.
Har gobe jikin shi yana ba shi zai samu Kulsum, zai dawo da ita cikin rayuwar
sa komai daren dadewa. Ganin ta da ya yi a Lagos ya kara tabbatar masa Ubangiji na
nufin wani babban al’amari a tsakanin su.
Goggo ta ce, “A’ah! Turaki ne tafe?”
Yayin da Baffa ya shimfida masa darduma ya zauna, Goggo ta shigo ta zauna a
gefe suna gaisawa. Baffa ya dube shi ya yi murmushi, ya ce, “To alhamdulillahi, da
ma yanzun nan da ka gan ni na dawo, gidan ku za ni wajen Maimartaba, in gaya masa
in har yanzu kana bisa ra’ayinka na neman komen Kulsumu, gobe ka kawo sadaki a
mayar maka da matar ka”.
Turaki ji ya yi tamkar zuciyar sa ta yi tsalle ta fito daga kirjin sa, sannan
ta kuma yin wani tsallen ta koma muhallin ta. Ya ji shi tamkar yana yawo a kan
gajimare, duk da haka bai gaskata kunnuwan sa ba, domin wani abu ne da ya zo masa
bagatatan tamkar saukar aradu, ya bugi zuciya da kwakwalwarsa a lokaci daya.
“Na’am Baffa… me ka ce?” Ya tambayi Baffa don dai ya samu wannan karon zuciyar
sa ta karbi tabbacin maganar.
Baffa ya sake maimaita masa, ya ce, “A da, gobe za a daura auren ta da dan
uwanta, to amma an samu matsalar da ta sa aka fasa, sabida haka in har yanzu kana
kan ra’ayin komen, ni a gobe zan yi wa Kulsumu aure, da ko ma waye, jama’ar da na
tara ba ni da bakin sallamar su”.
Baffa bai yi aune ba sai ganin Turaki ya yi ya fuskanci gabas ya yi sujjadah.
Murmushi Baffa ya yi don ya fi kowa sanin wahalar da yaron ke yi a kan neman komen
Kulsumu, ko sati daya ba a yi ba ya zo, amma bai gaya masa ta kusa aure ba, don ba
ya so ya karya masa zuciya. Ya yi musu hidima mai yawa ta kayan abinci kamar yadda
ya saba, Allah ya sani! Tun farko ya fi so Kulsumu ta koma wa Turaki, kunyar Hajiya
Nasara ce ta sa ya amince da zancen Taufeeq.
Bayan ya dago daga sujjadar Baffa gani ya yi hatta kyawun fuskarsa ya karu.
Ya ce, “Baffa "na gode" ta yi kadan ta bayyana godiya ta. Na gode Baffa, Allah
ya yi muku duk abin da ku ke so a duniya da lahira. Ya jikan mahaifa, ya ja kwanan
ku. Yanzun nan zan je na fada wa Maimartaba da Umma, kuma a daren nan ba sai gobe
ba za a kawo sadaki”.
Mikewa ya yi zai fita, jikinsa har rawa yake.
Baffa ya ce, “Bari a kirawo Kulsumun mana ko gaisawa ne ku yi”.
Turaki ya juyo daga bakin kofa gaban sa na faduwa, ya ce, “A’ah Baffa, kyale ta
za mu gaisa gobe. Yanzu dare ya yi”. A
zuciyarsa kuwa ya fadi hakan ne gudun rigimar Kulsumu kada ta ruguje wannan
maganar, amma kwarai zai so ya sake ganin ta. Bayan ganin da ya yi mata a Lagos,
wanda ya hana shi ko da runtsawa tsayin kwanaki biyun nan gabadaya.
A hankali yake tukin motar hawaye na sauka a kan kundukukin sa. Hawayen farin
ciki irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Kai tsaye cikin gida ya wuce da sassarfa, bangaren Umma ya nufa. Har dakin
barcin ta ya duba ba ta nan, sai ga Laraba za ta gifta ya tambaye ta Umma, ta ce
tana turakar Maimartaba, ita ce mai girki. Bai tsaya ya gama jin me ta ke cewa ba
ya wuce bangaren mahaifin nasa.
Sallama ya yi cikin kokarin daidaita nutsuwar sa, duk suka amsa mishi, Umma na
serving Maimartaba abinci. Murmushi ya yi lokacin da Turaki ya gurfana a gaban sa
yana gaisuwa. Ya amsa, sannan ya ce, “Yanzu da ma na ce Umman ka ta kira min kai a
waya, kwana biyu idanun nan nawa sun matsa min da kaikayi, ga wani hawaye da ke
yawan fitowa”.
Turaki ya yi kasa da kansa, ya ce, “Allah ya kara ma yawan rai, zan kawo
maganin da za a dinga digawa”. Sannan ba tare da ya jira amsar Maimartaba ba ya
dora abin da ke cin sa a zucci.
“Baffan Kulsumu ne ya aiko ni Allah ya kara maka lafiya, ya ce, in har yanzu
ina son komen Kulsumu in aika sadaki gobe a mayar da auren ta da zaa daura a
kaina”.
Umma ta saki cokalin da ke hannun ta, ta ce, “Kai Turaki bana son hauka, ko dai
soyayya ta sa ka fara kuncewa ne? Ya ya za su daura wa ‘yar su aure da dan uwanta
ka ce wai wani an ce da kai za a daura?”
Murmushi ya yi, ya ce, “Wallahi Umma babu shirme cikin magana ta, na je ne in
gaishe su kamar yadda na saba, sai yake cewa an samu matsala da wancan an fasa, in
zo a daura da ni”.
Maimartaba ya ce, “to ban da abinki rabon kwado yana hawa sama ne?”
Umma ta yi hamdala a fili, ta ce, “Ina ruwan Allah, abinda nake gaya maka
kullum ke nan Turaki, cewa ka fauwala wa Allah komai, idan da rabon sauran zama a
tsakanin ku Allah zai ba ka wannan damar”. Sai ga hawaye a idon ta. Ta kai hannu ta
goge ta sake cewa, “Allah na gode maKa da Ka nufi Kulsumu da dawowa gare mu”.
Maimartaba kuwa cewa ya yi, ya kirawo masa Galadima a waya. Nan da nan ya kira
ya hada su. Yana ji Maimartaba na bada umarnin a hada dukiyar aure da sadaki na
alfarma su je shi da Chiroma su karba wa Turaki auren matar sa ta baya.
Tuni Umma ta fice zuwa dakin ta. Batulu ta fara kira, sannan Yaya Hadiza da
Ramla ta ce, su yi kokari dukkan su su zo gobe, amma ba ta gaya musu makasudin
kiran nasu ba.
Nan kuma ta hada barorin ta da masu girkin bangaren ta ta soma bada umarnin
girke-girken da za a yi gobe, da abubuwan da ta ke so a tanada, Laraba kawai ta
gaya wa ko me ke nan, sai ga tsohuwar tana rawa tana juyawa.
A waya Baffa ya kira Daddyn Taufeeq wanda ke cikin Kano tare da Taufeeq din, ya
gaya masa hukuncin da ya yanke na maida Kulsumu ga mijinta don ba zai iya kyale ta
ta sake kwana a gabansa babu aure ba. Duk da Daddy ya ji ba dadi, don shi ya yi
hukuncin ne don in an kwana biyu Taufeeq ya sake nutsuwa a dawo da maganar auren.
Amma sai ya kasa fadin kudurin zuciyar tasa kada Baffa ya ga ya yi son kai, ya bi
bayan nasa. Ya sa albarka tare da cewa, insha Allahu da su za a daura auren Kulsumu
gobe kafin su wuce.
Bai gaya wa Taufeeq ba, don a lokacin ma yana gaban sa yana masa magiya da
hawaye, da zai amsa wayar Baffa sai ya kauce daga gaban sa don bai san me wayar
karfe goma na dare ta kunsa ba.
Karfe goma sha dayan dare Galadiman Gaya kanin Maimartaba da Chiroma da limamin
masallacin fadar Maimartaba Sarkin Gaya suka iso gidan Malam Jibo. Babu wanda za su
aika don haka Chiroma ne ya yi sallama da kansa. Baffa da ke yi wa Goggo da Hajiya
bayanin hukuncin da ya yanke a lokacin, ya fito don ganin masu sallama. Nan ya ga
manyan bakin dake tafe cikin dare daga fadar maimartaba Sarki. Komawa ya yi ya
sanar da su Goggo suka koma dakin Goggo ita da Hajiya Nasara, suna ta kakabin
al’amarin a zukatan su. Hajiya Nasara ba ta yi mamaki can-can ba, don ta san su
Baffa har gobe suna son Turaki.
Baffa ya shigo da bakin sa har dakinsa, nan aka yi magana ta gemu-da-gemu. Ya
ce, sadakin da suka kawo ya yi yawa, don Kulsumu ba yau za ta fara zuwa gidan su
ba, Galadima ya ce ai ba su da hurumin maida ko sisi ga maimartaba. Nan aka sa
lokacin daurin aure karfe goma sha daya na safe. Kuma a daren ranar duk wanda ya
kamata ya san zancen auren Turaki a masarautar Gaya sai da ya sani. Mata ne kawai
ba su da labari, su ma zuwa wayewar gari duk Laraba ta gama fesawa kowa labarin
dawowar uwardakin ta UmmuKulsumu. Nan aka fara hidimar girki wanda za a raba wa
jama’a bayan daurin aure. Daga nan kuma mata za su zarce da biki ne.
Kulsumu na kwance uwardakin Goggo a daren ranar, ba ta san wainar da ake toyawa
ba. Haka kawai ta ke fama da guilty conscience? Ta ke tuhumar kanta, anya hukuncin
da ta yanke a kan Taufeeq ta yi daidai? Me ya sa ba ta yi hakuri ta aure shi haka
ba? Ko don albarkacin iyayensa da ‘yan uwan sa, ta san son da Taufeeq ke mata idan
ta ce ya bar abu komai tsaurin sa za bari, in har za ta yi farin ciki. Yanzu ga shi
ta jefa iyayen sa cikin damuwa, ta hada su da dan su, anya hukuncin ta bai yi
tsauri ba, kuma bai yi kama da butulci ba?
Da wannan guilty conscience din ta kwana, tana jin kamar ta je ta samu Baffa ta
gaya masa ta janye hukuncinta. Amma lokacin karfe biyu ne na dare, Hajiya na falon
Goggo tana sallah, ta san shiriya ta ke roka wa Taufeeq a wurin Ubangiji. Ta san
halin Hajiya Nasara, duk wata matsala idan ta tunkaro ta, to ta daina barci ke nan
har sai ta ga karshen ta da karfin addu’a. Ta kara jin nadama ta lullube ta, ta sa
a ranta gobe in Allah ya tashe su lafiya the first thing in the morning (abu na
farko da zata yi da safe) shi ne gaya wa Baffa, Hajiya da Goggo ta janye hukuncin
ta, za ta auri dan uwanta Taufeeq cikin kowanne hali, ta taimaka masa ya yi yaki da
kowanne irin sabon Allah.
Da safe bayan sun idar da sallar asubahi duk su ukun ba ta tashi a wajen ba sai
da ta bude baki ta gaya wa Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, a ci gaba da
shirin daurin aure. Ba su ce mata komai ba sai ido da suka bi ta da shi suna
tunanin ko dai ta samu depression ne?
Baffa na shigowa daga masallaci, shi ma ta je ta gaya masa. Murmushi ya yi ya
janyo wata jaka ya tura mata gaban ta.
“Dauki wannan, sadakin ki ne. Amma ba da Taufeeq ba, da wanda Allah ya tsaga da
rabon sa”.
Kulsumu ta bi Baffa da kallo kamar za ta yi kuka.
“Baffa, sadakata ka bayar?”
Wani murmushin ya sake yi, ya ce, “Wace irin sadaka bayan ga sadaki irin wanda
duk garin nan babu ‘yar wanda ta taba samun rabin sa? Ni ba sadakar ki na bayar ba,
aure ne na na-gani-ina-so. Ba ki kara kwana daya gaba na sai da igiyar aure a
kanki, domin kin gama zaman Abuja”.
Hankali tashe Kulsumu ta bar gaban Baffa ta koma daki ta soma rusa kuka. Daga
Goggo har Hajiya babu wanda ya rarrashe ta. Gari na wayewa suka shiga hidimar da ke
gaban su kada jama’ar da suka gayyata su fara isowa ba su shirya komai ba.
Karfe goma sha daya na safe, dumbin jama’ar garin Gaya da wajenta suka sake
shaida daurin auren UMMUKULSUM ABDULHADI ‘YALLEMAN da YARIMA ABUBAKAR TURAKI
ABDULLAHI a kan sadaki lakadan ba ajalan ba. ‘Yan ‘Yalleman sai ana gab da daurin
aure suka iso. Daga nan ne kowanne bangare (gidan su amarya da gidan su ango) ya
zarce da wunin biki. Turaki dai ko ganin sa ba a yi saboda yawan jama’a, kai ka ce
an yi sati guda ana gayyatar su. Kodayake su su Goggo sun yi gayyatar haka duk
wadanda su Hajiya Nasara suka gayyato daga Abuja domin halartar auren dan su, sune
suka halarci daurin auren Kulsumu da Turaki a karo na biyu. Cikin mahalarta daurin
auren har da TAUFEEQ MUHAMMAD BELLO (tears).
Boye kansa ya yi bayan daurin aure a cikin sassan shi da ke cikin gidan, ya
gabatar da alwala ya sallaci walha (dhuha), sannan ya dora da sallar nafila raka’a
biyu ya yi godiya ga Allah da Ya cika masa buri na karshe a rayuwar sa. Duk wasu
burikansa Ubangiji ya cika masa su daya bayan daya, wanda yake gani a matsayin mafi
wahala (wato samun Kulsumu), yau ga shi Ubangiji ya cika mishi ba tare da kokari,
dabara ko iyawar sa ba.
Lallai ne shi Allah fa’a’alun lima yuridu ne (wato mai aikata abin da ya so) a
kuma lokacin da Ya ga dama.
Wayar sa ya lalubo daga cajin da ya sanyata tun jiya, mutum na farko da ya kira
shi ne, Dr. Abdul’Ahad Aminu Maikano, ya ce,
"Aboki, kana ina?”
Ya ce, “Ina Manchester, amma gobe insha Allah zan koma Reading”.
Ya ce, “To kunnen ka nawa?”
Murmushi ya yi mai sauti ta cikin wayar, ya san albishir din ba zai wuce a kan
Kulsumu ba, the only obstacle of Turaki. To ko dai ya samo ta ne? Ya ce, “Kunne na
goma sha biyu, plus na Turaki in an hada da nawa sun zama sha hudu kenan”.
Dariya ya yi, ya ce, “To kai komai sai ka sa wasa a ciki? I called to inform
you yau na zama angon UmmuKulsum for the very second time, cikin yardar Ubangiji da
amincewar sa”.
Dr. Abdul’Ahad ya ce, “Idan wasa ka ke min, to bana so mu yi magana ta
gaskiya”.
Turaki ya ce, “Na taba yi maka irin wannan wasan? Well, ba ni da lokacin ka
yanzu. Zan so ka zo Gaya, akwai hawan angonci na musamman da zan shirya next week
wanda ba a taba irinsa a Gaya ba. It''s a promise da na yi da dadewa cewa duk ranar
da zan yi auren soyayyah zan yi hawan angonci. Your Horse is reserved for you (an
ajiye maka Dokin ka)."
Zuwa yanzu Abdul’Ahad ya yarda Turaki da gaske yake. At last ya samu Kulsumu,
kowa zai samu lafiya. Ya ce cikin murmushi,

“Dole ne ma in zo, ko don in ga Kulsum, in ga shin me ta taka haka da ta
sukurkuta min aboki shekara da shekarusaura kadan yayi asarar likatancin sa a
kanta?”.
Murmushi Turaki ya yi, ya kashe wayar sa ba tare da ya ba shi amsa ba. Shi
kansa in za'a tsare shi ba zai iya fadar abu guda daya da yake son Kulsumu sabida
shi ba, ita din bakidayan ta yake so, the whole her. (Dukkanta).

*** *** ***
Umma ta aiko an gaya wa Goggo gobe lahadi da yamma za su dauki amarya, don haka
duk wani shirye-shiryen su daga yau zuwa gobe gare su. Hajiya Nasara ta sa Sakeenah
ta hado duka kayan dakin Kulsum da suka tanada ta taho da su Gaya a gobe-goben nan.
Ba ta gaya mata ko me ke nan ba, ta dai ce ta yi kokari ta zo tare da kayan, kuma
kada ta gaya wa Nasmah komai kada ta dage sai ta biyo ta ta zo tana haihuwa a kan
hanya.
Washegarin ranar Sakeenah ta iso da motocin kaya, Baffa ya bude dakin da ya
ajiye wadanda Maimartaba ya aiko wa Kulsumu tun ma kafin auren ya juye kan dansa.
Aka hada da wadanda su Hajiya Nasara suka yi wa Kulsum aka wuce da su gidan Sarkin
Gaya inda za a yi wa Kulsumu kafi. Amma sai Maimartaba ya ce, Turaki ba zai zauna
cikin gidan ba wannan karon, sassan ya yi musu kadan kuma ya tsufa, ya mallaka masa
sabon gidan sa da ya gama ginawa a bayan gari, don haka can aka wuce da kayan, aka
kuma yi wa su Hajiya Nasara da za su yi kafi jagora zuwa can.
Lokacin da su Batulu suka iso, Umma ta gaya musu kome ke nan. Batulu hawaye ta
dinga yi, farin ciki ya kai mata ya kawo. Ta ce a lokacin za ta tafi gidan su
Kulsumu, Ummah ta ce ba ta yarda ta je ta cikata da dumi ba, ta bari sai gobe su je
su dauko ta gabadaya.
Dr. Sakeenah ta ji abin da ya faru, ta yi bakin ciki sosai a kan Taufeeq, ta yi
fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi, Ya yi wa Taufeeq sauyin alheri.
Sun je sun yi kafi, suka dawo suna ta yaba tsaruwar gidan, Lami matar Malam
Hadi ta rangada wa Kulsumu guda aka ta ce,
“Allah ya sa kannen ki a damshin ki Kulsumu, gida kam na duniya kin yi shi,
Allah ya sa na lahira ya fi shi”.
Kulsumu wadda tun wayewar garin yau ta ke risgar kuka, damuwar ta shi ne,
wannan aure da Baffa ya yi mata mai kama da auren sadaka da mijin da ba ta san ko
waye ba. Duk maganganun da mutane ke yi a kan gidan wanda suka je kafi suka dawo ko
daya bai burge ta ba. za ta fi so a ce Baffa ya yi hakuri ya kara mata lokaci ta
kawo masa wani mijin, tunda ba su karbi nadamar ta a kan Taufeeq ba.
To shi wannan din an san nasa halin? Kada dai ta yi gudun gara ta tadda zago.
Kada garin neman gira ta rasa ido. Allah ya sa dai Baffa ba kudi ya gani ba, tunda
yana ikirarin sadakin ta duk Gaya ba ‘yar wanda ta samu kamar sa. Su kuma ga su sun
zo suna santin gida. Amma da ta tuna ko wane ne Baffan nata, ta san hakan ba za ta
taba faruwa da shi ba.
Ba ta samu kebewa da Babanta Malam Hadi ba sai da ya zo tafiya bayan daurin
aure, kasancewar shi ba zai kwana ba, amma su Lami duk suna nan sai sun raka
Kulsumu dakin ta.
A zauren farko suka tsaya sabida yadda gidan ke cike da jama’a. Ya dubi Kulsumu
wadda idon ta ya yi kozai-kozai don kuka, babu wata kwalliya ta amare a tare da
ita. Haushin kowa ta ke ji, musamman Baffa. Ko da Aunty Sakeenah ta yi mata magana
kan ta canza kayan jikin ta ko hoda ce ta shafa kuka ta fasa mata. Kukan da ya sa
dole ta kyale ta, don ita Sakeenah ba ta son kuka a rayuwar ta.
Malam Hadi ya ce, “Kulsumu komai ki ka ga ya faru da bawa, da ma rubutacce ne a
lauhul mahfuz, wani ba ya auren matar wani kamar yadda wata ba ta auren mijin wata.
Ki sa a ranki duk mijin da Allah ya zaba miki shi ne alherin ki. Na ji an fasa aure
da shi wannan yaron dan wajen marikiyar ki sabida wasu matsaloli da suka taso.
To dama ni tun farko na amsa ne sabida karamcin iyayen sa gare ki, amma
Kulsumu na fi so ki koma gidan tsohon mijin ki. Hausawa suka ce da sabon gini
gwanda yabe, su kam ai sun sanki ciki-da-bai din ki, babu wani abu naki da zai zame
musu sabo, ke ma kuma in kin nutsu kin kwantar da hankalin ki sai kin fi jin dadin
gidan Sarkin Gaya.
A hankali Kulsumu ke daga kumburarrun idanun ta tana bude su a kan Baban ta.
Wai me yake nufi ne da wannan zancen nasa? Ita ko alifun ba ta fahimta ba, ban da
sunan gidan SARKIN GAYA.
Har ya yi mata sallama ya sanya mata albarka tare da yi mata addu’o’I masu yawa
ya tafi, Kulsumu ba ta koma daidai daga razanar da ya sanya ta a ciki ba. Maganar
gidan Sarkin Gaya da ba ta fahimci musabbabin ta ba. Ga shi har ya wuce ya tafi ba
ta nemi karin bayani daga gare shi ba. Harshen ta kamar an daure mata shi, haka ta
ja jiki ta koma cikin gida kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Gadon Goggo ta hau ta kwanta, ta lumshe idanun ta tana sauke ajiyar zuciya.
Cikin dare ta kasa barci sai juyi a kan gadon karfen Goggo, ta tabbata ita din
yanzu matar aure ce, matar wanda ba ta sani ba, ta yi sallama da Taufeeq daga cikin
rayuwarta. Kwata-kwata kwakwalwar Kulsumu ta ki yarda ta karbi zancen gidan Sarkin
Gaya da malam Hadi ya yi mata, sabida tsabar ba ta kawo hakan a ranta ba. Ta fi sa
wa a ranta ya fada mata ra’ayin sa ne kawai na gidan da ya fi so ta yi zaman aure.
Ko mecece kaddarar ta tunda ita ta ki karbar Taufeeq ita ta ja wa kanta, dole
ta karbe ta da hannu bibbiyu. Amma ba ta taba lissafo wa da Turaki cikin kaddarorin
da ka iya samunta ba. Duk da haduwar su a Lagos ya bankado shafuka da yawa daga
karkashin zuciyar ta da ta dade da binnewa na ciwon abin da ya yi mata.
Wai "matarsa da ya rasa bai sake ta ba". Ta tuna statement din sa. Ita ta san
wannan ba Turaki ba ne, Turakin gaske bai taba son ta ba! Turakin da ta sani daban
yake da wanda ta gani, tunda ta aure shi har Allah ya raba su ba ta taba ganin
murmushi a fatar bakin sa ba. Amma haduwar su a Lagos Turaki har rungumar ta ya yi,
ya sumbace ta passionately, duk da ce masa da ta yi tana da aure, sannan ta ga
murmushin sa ya kai sau nawa, wanda ya kusa tafiya da sauran numfashin ta.
Tana wannan tunanin har aka yi kiran assalatu a kan kunnen ta. Har aka tada
sallah ta kasa motsawa, sai da Goggo ta bubbuge ta. Ko da ta yi sallah kasa komawa
barci ta yi, idon ta ya soye, zuciyar ta ma ta soye kamar soyayyar gyada marau-
marau, da tunanin yau ne rana ta biyu da za ta sake barin gaban iyayen ta zuwa
gidan aure. Akwai fargaba mai yawa a tattare da ita, wadda ta cika ruhin ta
sakamakon tunanin shi kuma wannan auren me za ta je ta tarar a cikin sa?
Idan lalurarta ta dawo fa? Tunda har gobe likita bai ba ta tabbacin warkewa
gabadaya ba? Babban abin da ya sa ta ke gudun aure ke nan, ba ta so ta kuma yinsa a
sake sako ta. Sannan ba ta son terere da bankada a kan lalurar da Allah ya dora
mata. Duk da jikin ta yana ba ta ta gama warkewa, Dr. Sakeenah ma na da tabbacin
hakan.
A haka barci mai nauyi ya dauke ta, a karshe ta bingire a kan sallayar tana yin
sa bilhakki, babu wanda ya tashe ta

Please Login or Register in order to submit comment