You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don sun lura kwanan ido biyu ta yi.
Washegari gidan aka tashi da hidimar tafiya kai amarya wanda za'ayi da yamma,
Dr. sakeenah ta ja hannunta suka shige dakin Baffa kasancewar ba ya nan ya fita.
Wani fulas ta jawo ta aje mata a gaban ta ta ce, ta cinye kazar ciki tas! Ta ba ta
kasusuwan, sannan ta ba ta wasu kwayoyin magani ta ce in ta gama ta hadiye su. Ta
dube ta cikin ido, ta ce,
“Na san Kulsumu ba za ki ki bin umarni na ba, na san kina girmama ni!”.
Bayan fitar Sakeenah ta dade kafin ta fara ci. Kasancewar da yunwa ta kwana,
sai naman ya yi mata dadi ta bude ciki ta ci sosai, ta hada mata kasusuwan kamar
yadda ta umarce ta. Ta kuma hadiye magungunan da ba ta san na mene ne ba.
Karfe biyar na yamma ‘yan daukar amarya suka zo, Dr. Sakeenah ta zabo mata wani
sabon lace din ta don Kulsumu ba ta zo da kaya ba, sannan ba wasu kayan aure da aka
kawo mata, Baffa ya sa an maida sauran ya ce, sadaki kawai zai karba kamar wancan
karon. Wadanda suka zo daukan amaryar dattijai ne su uku, cikin wata kosasshiyar
mota ta Maimartaba. Daya kanwarsa ce Goggo Hanna, daya yayar Umma ce da ta zo daga
Gombe, dayar kuwa matar Galadiman Gaya ce Hajiya Rabi.
A karo na biyu yau ma sai da Lami ta goya Kulsumu sannan suka iya tafiya da
ita. Ko nasiha Goggo ba ta samu ta yi mata ba sabida tsananin tausayin da Kulsumun
ta ba ta, ga ta cikin matsanancin kuka kamar na fitar rai. Abubuwa da yawa ne suka
damu Kulsumu, zuwa yanzu ba ta damu da sai ta san ko wane ne mijin da iyayen ta
suka zaba mata ba, domin ta sa a ranta wannan auren za ta je bautar Allah ne kawai
albarkacin ba za ta iya tozarta Baffa ba. Ba ruwan ta da ko waye mijin. Tausayin
Nasara da ‘ya’yanta shi ne babban abin da ya fi damun ta.
Ta yi nadamar kin Taufeeq da ta yi, domin an ce ko a lahira wani kan ci
albarkacin wani, amma ba ta duba hakan ba ta yi abin da zuciyar ta ta fi kwanciya
da shi, ga shi sakamakon hakan ya jawo mata auren wanda ba ta sani ba, ba ta san
shi kuma mene ne nashi nakasun ba.
Kugin da motar ta yi na karshe a kofar gidan Dr. Turaki ne, kyakkyawan gidan da
duk garin Gaya babu mai kyau da tsarin sa. Asali Maimartaba ya gina gidan ne don
hutawar sa ba da sunan Turaki ba, amma da ya ji kowa Turaki zai aura, ya tabbatar
Turaki da gaske yake ya karbi zabin da suka yi masa da hannu bibbiyu, kuma ya yi
damarar zaman aure ne yanzu da Kulsum, sannan kaunar sa ga yarinya UmmuKulsum wadda
ba ya wa Turaki sha’awar kowacce mace sai ita, sabida sun zauna da ita, sun san
halayen ta. Sannan sun amince da dattakon iyayen ta, da soyayyar da ta ke yi wa
Turaki. Da wannan zazzafan darasin da iyayenta suka koyar da shi, su suka hadu suka
faranta ransa har ya yi wa Turaki kyautar wannan dankareren gida.
Abin da ya janyo kishi karara daga sauran matan sa, amma ba su da ta cewa
tunda ba su da Da namijin da zai kara da Turaki, duk ‘ya’yan su mata ne a gidan
aure.
Su Batulu ai tun safe ana gidan amarya, da ita aka yi jere/kafi da komai. Ba ta
damu da ta ga Kulsumu ba tana cikin sabga sosai. Yaya Hadiza ce ta taro su lokacin
da suka iso, ta yi musu jagora zuwa dakin Kulsumun, wadda ke rufe ruf cikin
yalwataccen mayafin da Dr. Sakeenah ta lullube ta da shi. Hajiya Nasara ce rike da
ita, a kofar dakin ta gaya mata ta shiga da kafar dama, sannan da addu’ar da za ta
karanta. Batulu ba ta gidan, Umma ta kira ta don ta je su hada kayan sallamar masu
kafi da kawo amarya. Daga Yaya Hadiza sai Aunty Ramla da sauran sisters din Turaki
da suke uba daya.
Ko da wasa Kulsumu ba ta bude lullubin ta ba wai don ta ga inda aka kawo ta.
Kukanta ta ke bilhakki duk ta jika mayafin ta da hawaye. Lokacin da ta ji su Hajiya
Nasara na haramar tafiya sai ta rirrike ta, cikin kuka ta ce.

“Mum ki yafe mini, kin yi min komai a rayuwa, amma ni na ki Yaya Taufeeq a kan
ajizancin da babu wanda ya wuce shi. Mum daga baya na so in gyara kuskurena baffa
bai ba ni dama ba, wallahi Mum da wannan damuwar zan rayu har karshen rayuwa ta…”.
Ta fada jikin ta tana kuka mai nuna nadamarta.
Hajiya Nasara ta riko ta sosai a jikin ta, ta ce, “Kulsum kada in kara jin
wannan maganar a bakin ki, ke ‘yata ce kamar yadda Taufeeq yake dana. Ba Taufeeq ne
ya hada mu ba zumuncin Allah ne wanda Ubangiji ya yi mana umarni dole mu yi shi. Da
kin auri da na da ba ki aure shi ba, matsayin ki na ‘ya a gare ni ba zai taba
canzawa ba. Ba ki da wadda ta fi ni ke da Goggo, kamar yadda ba ni wadanda suka fi
ku. Ki sa a ranki Allah ne bai kaddara aure tsakaninki da Yayanki Taufeeq ba, ki
taya ni addu’a Allah ya yaye masa halin da ya jefa kansa ya samu mata nutsattsiya
kamar ki ya aura”.
Kulsum ta kara rungume Hajiya Nasara tana sakin wani sabon kukan, ta ce,
“Na gode, na gode Mum”.
Ta ce, “Ba kin gode ba, be happy with your marriage, ki yi wa mijin ki
biyayyah, shi din mai son ki ne. Ina da tabbacin wannan karon sai kin fi kowa farin
ciki da zaman aure. Daina kukan nan in mun tafi ki dauro alwalla ki yi nafila
raka’a hudu ki roki Ubangiji Ya dorar da farin ciki a rayuwar auren ki”.
Tana ji tana gani duk suka shige motoci suka tafi babu wanda ya rage a gidan.
Hatta masu aiki Umma ta ce sai bayan kwana bakwai za a kai mata.
Ta yi kukanta ma’ishi, a karshe ta yanke bin shawarar Hajiya Nasara, wato ta yi
sallahr nafila. Mikewa ta yi ta warware mayafin da ke jikinta ta ajiye, idanun ta
suka hango mata kyakkyawan dakin nata, wanda ya ji rantsattsun furnitures tafiyayyu
tun daga China. Ta san wannan aikin Hajiya Nasara ne, ta yi mata tanadin rayuwa da
danta, amma a karshe gidan wani suka shigo. Ta girgiza kai a hankali, ta doshi
kofar da ta tabbatar toilet ne.
Tana murda kofar toilet don fitowa, Turaki na turo kofar dakin don shigowa.
Sanye yake da wani irin tattausan yadin filtex fari sol, dinkin tazarce. Kansa babu
hula, sumar nan baka wuluk da ya tara a U.K ta kwanta luf a kansa, sai sheki ta ke
yi, hade da lallausar sajen fuskar sa wanda a lokacin samartakar sa bashi da shi.
A hankali ta daga idanu ta dube shi. It was a sudden shock irin wanda zai iya
haifar da bugun zuciya a lokaci guda. Fuskar ta kuma ba ta boye halin shock na ba-
zata da ta shiga ba, sai ta tsaya standstill rike da hannun kofa. Ta rasa mafarki
ta ke yi ko idonta biyu? Ya fi kama da mafarki, wanda kusan kullum ba ta rabo da
yin irin sa,. Seeing Turaki a matsayin mijin ta!!!
Wani tattausan murmushi ya yi, wanda ya nuna fahimtar sa ga halin firgicin da
ta samu kan ta, ya kuma gane ba ta san kan shi Baffa ya maida auren ba. Wannan abu
ya kara yi masa dadi ba kadan ba. Takowa ya yi a hankali zuwa gaban ta. Ya mika
hannu da nufin ya kamo hannunta. Da wani mugun zafin nama ta ja da baya, sannan ta
daddage ta fasa wani firgitaccen kuka tare da durkushewa a kasa tana ta gunza shi
kamar za ta fasa dakin.
Wannan abu ya matukar bai wa Turaki dariya, waje ya samu gefen gadon ta ya
zauna, ya zuba mata ido, daga baya sai ya kishingide ya dauko wayar shi ya shiga
danne-danne, ba da sanin ta ba vedio yake yi mata.
Cikin gunjin kuka ta ke fadin,
“Na shiga uku na lalace ni Kulsum, abin da Baffa ya yi min ke nan???”
Wannan karon dariyar Turaki ta kasa boyuwa. Ya ce, “Ummukulsumun Turaki, this
is the best decision ever, ki gode wa Baffa saboda ya taimake ki. Ya dawo da ke
inda kike so ake son ki. Ina amfanin badi ba rai? Ina amfanin ki je gidan Taufeeq
alhalin kina da mijin ki a gefe? To ki je ki kai masa me? Bayan Turaki ya kwashe
komai tun Kulsum na kwailar ta? Ai da muguwar rawa gwanda kin tashi”. Ya karasa da
wani mischievous smile (murmushin keta) a siririyar fatar bakin sa.
Kulsum ta yi sak! Daga kukan fitar ran da ta ke yi tana nazarin kalaman sa,
kafin wani dan lokaci ta gane me yake nufi. Wata zuciyar na cewa ta rufe shi da
duka ko ta ji dadi, wata na cewa ta fice ta bar masa dakin. Ta je ta yi jinyar abin
da ya same ta ita kadai.
Kamar Turaki ya san tunanin da ta ke yi, ya mike kamar zai fita, kawai sai ya
murza wa dakin key, ya tako ya iso har gaban ta ya durkusa. For the first time a
rayuwar sa da ya samu kansa durkushe gaban mace, sannan da niyyar lallashin ta.
Kulsumu ta yi wuf za ta mike, ya riko ta da kyakkyawan rikon da ba za ta iya
kubucewa ba. Sannan a hankali ya mike shi ma suka fuskanci juna, kirjin ta na
heaving faster and faster tamkar mai ciwon asthma, yayin da zuciyar Turaki ke wani
irin circulating tana haifar masa da abubuwan da bai taba ji a rayuwar sa ba akan
diya mace. Kulsum ba ta gama tantance halin da ta ke ciki ba ta ji Turaki ya
rungume ta da wata irin kyakkyawar runguma (tight hug) yadda jikin sa ya ratsa
ko'ina na jikin ta. Bugun zuciyar ta ya karu, kamar yadda nasa ke yi, suka koma
bugawa a tare, kamar zuciyar su za ta ballo allon kirazan su ta fito.
Kokari yake ya lalubo bakin ta, amma Kulsum ta ki ba shi damar hakan. Sai faman
cusa kai yake a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta yana kissing iya abinda zai
iya samu. Zamewa ta yi ta kasan hannayen sa ta koma toilet da gudu ta banko kofa ta
murza key. Ta koma ta jingina da kofar bandakin tana sauke ajiyar zuciya. Gara ta
kwana a toilet da ta kwana tana ganin Turaki a gaban ta, kuma wai a matsayin mijin
ta na sunna a karo na biyu.
Tana jin shi yana mata magana a daidai kofar bandakin, “It’s okey, ni ba bakon
zafi ba ne. Na bar miki dakin ki, ki kwana cikin aminci UmmuKulsumun Turaki. And
dreamt of our twin babies masu zuwa nan da watanni tara”.
Ya yi murmushin da har ta ji tashin sautin sa, ya sake cewa “Allah na tuba wane
dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daren mutuwar sa. Mutumin da ya yi hakurin
shekara takwas ai ba zai gaza yin na dare daya ba”.
Ita dai ba ta ce komai ba. Ya sake cewa,
“Na barki lafiya Princess”.
Tana jin fitar sa da rufo kofar sa, amma ba ta fito ba sai da ta tabbatar ya
fita din. Tana fitowa ta murza wa dakin makulli. Kasa tada sallar ta yi, sai ta
zauna a bakin gado tana tunanin rayuwar ta mai abun mamaki. Turaki as her husband
for the second time, tare da wasu mabambanta halaye da suka barranta da nasa.
Ba ta da zuciyar da za ta kara yarda da Turaki, kamar yadda ba ta taba shirya
wa ranta sake rayuwa da shi ba. Zai sha mamaki kuwa, idan har yana zaton wannan
karon ma zai ci galaba a kan ta, kamar yadda ya ci a baya, idan zaton sa karamar
yarinya Kulsumun da, ita ce a cikin gidan sa yanzu.
Sai yanzu ta gane maganganun da Baban ta Malam Hadi ke yi a kan gidan Sarkin
Gaya, ashe-ashe nufin sa can za ta sake komawa. To me ya sa Baffa ya boye mata? Ba
shakka don ya san ba za ta amince ba ne.
Hawaye suka zubo mata, how could she forget his wickedness (ta ya ya za ta
manta muguntar sa?) Shi ne yanzu ya zo yana ‘yar murya don ta tashi daga Kulsumu
‘yar kauye, mai fitsarin kwance? Ta koma yadda yake son ganin mace? Ko ta rasa miji
me za ta dawo ta dauka a gidan Turaki? Gara masa ya maida ita inda ya dauko ta ko
ya shirya zama cikin bakin ciki da tashin hankali, ba za ta taba zaman lafiya da
shi ba har karshen rayuwar ta.
A wannan daren, duk iya sata irin na barci da kyar ya iya sace UmmuKulsumu,
tana kitsawa tana warwarewa, amma ta kasa gano hanyar da za ta bi ta tserar da
kanta daga auren Turaki. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Ta yi kuka, ta yi kuka
har ta gode Allah. A rayuwa Baffa bai taba bakanta mata irin wannan lokacin ba,
shin ko sun manta wane ne Turaki ne?
Turakin da ya bula musu kasa a ido, ta koma sunan karamar Bazawara a dalilin
sa, har ta yi zaman gidan sa ta kare ba ta taba ganin murmushin sa ba, kalma ta
arziki bata taba hada su ba, bai taba daga ido ya kalle ta ba, sabida a baya bai
dauke ta mutum ba, yanzu ne ta ke mutum, sabida ba ta fitsarin kwance, kuma ta yi
ilmi ta goge?
Zai sha mamaki kuwa, don ba don shi ta dage ta canza rayuwar ta ba. Ta canza ne
don amfanin kan ta. Tabbas za ta aro rigar rashin mutunci wanda ba halin ta ba ne
ta saka a zama da Turaki, sai ya maida ita inda ya dauko ta yana so ko ba ya so. Da
wannan tunanin barci ya samu nasarar sace ta goshin asubahi.
Turaki a nasa dakin bayan ya rage kayan jikin sa zuwa na barci, komawa ya yi
falo ya yi waya da Abdul’Ahad, yana bukatar raba farin cikin da yake ciki tare da
aminin nasa.
Ya ce, “Aboki, ga ni ga Kulsum a cikin gida na, matsayin matata for the second
time, wace irin godiya ya kamata na yi wa Ubangiji?”
Abdul’Ahad ya ce, “ka yi sadaka ga mabukata, ka ziyarci marassa lafiya a
asibiti, ka yi musu ihsani. Sannan ka yi damarar rike matar ka tsakani da Allah,
don ba dabararmu ce ta sa Ubangiji ya dube mu Ya yaye mana damuwar mu ba. Rahamarsa
ce da Gafarar sa gare mu”.
Turaki ya gamsu da maganganun Abdul’Ahad, ya yi niyyar bin duk abin da ya ce da
zuciya daya. Nan ya ce, “Amma wani hanzari ba gudu ba, Kulsum matukar fushi ta ke
da ni Aboki, don ba ta ma san da ni aka daura mata aure ba. Fushin da ban san yadda
zan yi in rarrashe ta ba”.
Murmushi Abdul’Ahad ya yi, ya ce, “Turaki kada ka bada maza mana, ai kawai
rikidewa za ka yi daga likitan ido ka koma Romeo, ka yi hakuri da duk abin da za ta
yi, za ta gaji ta bari ne tunda bakin alkalami ya bushe”.
Turaki ya kyabe baki, ya ce, “ni fa ba zan yi abin da zai jawo min raini ba
Malam, idan ta kawo ni bango dauke ta zan yi mu bar garin, mu tafi inda ba mu da
kowa, in yaso ta tsire ni ta huta”.
Dariya Abdul’Ahad ya yi, ya ce, “Sanda za ka zama Romeo din ai ba gaya min za
ka yi ba. Ina nan isowa jibi insha Allahu, da ni za a yi kilisa”.
A yau ya san ya yi barci irin wanda tsawon shekaru takwas da doriya rabon sa da
yin irin sa. Duk wani tension ya kau. Duk wani migraine ya tabbata daga yau babu
shi; Kulsum cikin gidan sa, matsayin matar sa ta sunnah! Babu wani kwanciyar
hankali da contentment din da ya fi wannan a gare shi.
Da asubahi ya so ya je ya buga mata kofa, sai kuma ya yi tunanin ya kyale ta, a
sanin da ya yi mata sallar asubah ba ta wuce ta ba tare da wani ya tashe ta ba.
Domin lokacin ne ta ke aikin wankin kayan fitsarin ta.
Ta dade da tashi kuwa kamar yadda ya yi hasashe, ta yi wanka, amma babu kayan
da za ta canza. Tana cikin gyaran gado ta ga wata jakar bacco a gefe, da ta bude
sai ta tarar da kayan sawa ne na Dr. Sakeenah, ta santa da kayan a jikin ta, ta
gane ajiye mata ta yi don ta yi amfani da su kafin a tattaro kayan ta daga Abuja a
kawo mata. Kaunar Sakeenah da ganin girman ta suka kara cika ranta. Ta zabi wata
shudiyar super holland riga da zani da dankwalin su ta sanya, ta lullube jikin ta
da mayafin kayan kamar mai shirin fita unguwa, lotion kawai ta shafa, ko hoda ta ki
shafawa kada Turaki ya dauka kwalliya ta yi masa.
Tunanin sa kawai ya janyo mata wani irin bacin rai. Daidai lokacin da ta ji ana
buga kofar ta. Dole ta je ta bude don rana har ta soma fitowa.
Wa za ta gani? Batulu!
Wani irin rungume juna suka yi, Batulu na fadin, “Kulsumu na, ashe zan sake
ganin ki?”
Ta ce, “Batulu kudurar Allah ai ta fi gaban haka”.
Tare suka wuce zuwa tangamemen falon wanda ya sha tsari da tsadaddun kaya kamar
a Turai. Batulu ta ce, “In na ce wa Yaya Turaki ya kwantar da hankalin sa, idan
Kulsumu matar sa ce babu makawa sai ya same ta, sai ya ga kamar na fada masa karya,
yau Allah cikin hikimar sa ga Kulsumun mu ta dawo mana cikin yardar Ubangiji”.
Nan suka fara labarin bayan rabo, Kulsum ta ce, ina yaran ta? Ta ce suna wajen
Ummah.
Suna zaune kamar sa hadiye juna don kauna da aminci, kowacce na labarta wa ‘yar
uwarta yadda rayuwa ta kasance mata bayan rabuwar su, Batulu na ba ta labarin irin
bilinbituwar da suka sha ita da Turaki wajen neman komen auren ta. A cikin ran ta
ta yi mamaki sosai, mamaki ba dan kadan ba, in ta ce mamaki tana nufin mamaki, sai
dai wannan bai ishe ta ta yarda yanzu Turaki na matukar son ta ba ne, yana dai da
hujjar sa, watakila don ya samu cikar wani burin nasa ne. Sai dai ba ta ce da
Batulu komai ba, ganin yadda ta ke jaddada mata kaunar Yayan ta gare ta.
To da ma ita soyayyar kan shiga farat daya ne bayan kiyayyah? Don dai ita a
gabadaya sanin da ta yi wa Turaki kiyayya yake mata ba soyayya ba, don haka ba za
ta yarda da wannan campaign din na Batulu ba, a dai yi sha’ani kawai wai kaza ta so
tsegumi.
Gyaran muryar Turaki ya sa Batulu ta nutsu, ya shigo dakin cikin shirin fita,
kamshin sassanyan turaren sa one man show ya mamaye su. Ya dubi Batulu ya ce,
“Ke kuma haka ake zuwa gidan mutane da sassafe? Mutanen ma amare sabon aure?”
Dariya ta yi, ta ce, “wadannan ai tsofaffin amare ne. Yaya Turaki na kasa
hakurin yamma ta yi ban ga Kulsumu ba. Ka san tun tafiyar ta ba mu sake haduwa ba”.
“I can relate”. In ji Turaki.
Ya maida duban sa ga Kulsum, “Ummukulsum zan fita, ko kina da sako wajen su
Baffa?”
Dauke kanta ta yi gefe ba ta amsa ba.
Sai da Turaki ya yi da na sanin kula ta, ga shi ta dizga shi a gaban kanwar sa
da ke matukar ganin girman sa.
Yana fita Batulu ta ce, “Wai fushi ki ke da Yaya Turaki Kulsumu? Ki yi wa Allah
ki yi wa Yaya Turaki adalci mana, ya sha wahala a kan ki, ya sha matukar wuya kafin
ya same ki. Ya yi nadama!”.
Murmushi kawai ta yi, ai Yayan ta ne da ta ke so, uwar su daya uban su daya, ba
abin da ba za ta ce ba don kafa gwamnatin sa. Ita kuma ta sha wahalar soyayya idan
shi wahalar neman ta ya sha, shekara da shekaru tana dawainiya da soyayyar sa,
wadda ba ta ga ranar da ta yi mata ba.
Batulu ta bar zancen don ta san ba hurumin ta ba ne. Ta ce su je su zagaya ta
ga gidan nata sosai. Ba inda ba su shiga ba, har ran ta ta yaba da gidan, sai dai
farin cikin ta ragagge ne duk da kasancewar ta mallakin sa, tunda da Turaki za ta
yi rayuwa a cikin sa, wanda ba shi da gurbi ko kankani a zuciyar ta yanzu. Ko son
ganin sa ba ta yi.
Umma ta aiko musu da abincin karin kumallo a manyan warmers, suka zauna suka ci
ita da Batulu. A lokacin ne baki suka soma zuwa ‘yan ganin daki da ‘yan ganin kwaf!
‘Yan uwan Turaki da ‘ya’yan zuri’ar su duk sun zo. Wadanda ta saba da su a baya, da
wadanda sai yanzu ta san su. Har dare suna hidimar baki ita da Batulu, sai da aka
zo daukan Yayar su Magajiya ‘yar wajen Hajiya Saratu, sannan Batulu ta bi su suka
tafi da alkawarin gobe kafin ta koma Kaduna za ta biyo su yi sallama, ta kawo mata
Nurain da Zunnurain ‘ya’yanta ta gan su.

*** *** ***
Turaki bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare. A matukar gajiye yake, a kan
dining ya samu abinci cikin warmers, ya debi wanda zai iya ci, ya koma kujerar
tsakiyar falo ya yi zaman sa, ya kunna talabijin ya kamo tashar da yake so, wato
CNN, ya koma cikin kujera yana cin abinci yana sauraron labarai.
Bai damu da ya je inda ta ke ba, amma zuciyar sa da idanun sa so suke su gan
ta, ko da kuwa rikici za su yi, ba zai iya kwana bai san halin da ta ke ciki ba.
Mikewa ya yi zuwa dakin nata. Ya murda kofar ya ji ta a rufe. A hankali ya ce,
“Ummukulsum, bude min kofa”.
Banza ta yi da shi ta ci gaba da shimfidar gadon da ta ke yi. A ran ta ta ce,
“Yadda ka aure ni ba da sani da amincewa ta ba, haka za ka gaji da ni ka maida ni
inda ka dauko ni".
Ya sake tausasa murya, “Kulsum kada ki yi abin da zai fusata ni, idan na shigo
dakin nan...…”.
Sauri ta yi ta je ta maida mukullin jikin kofar, yadda ko ya zira nasa ba zai
budu ba, wato ya doke ta sannan ya hana ta kuka saboda zalunci? A lokacin da ta ke
neman jin kan sa, kulawar sa da soyayyar sa bata samu ba sai yanzu da ta daina
bukata?
Hakan kuwa ya yi, domin dakin sa ya koma ya dauko bunch of keys na gidan
gabadaya, ya zo ya yi ta gwadawa, amma ya ki shiga. Nan ya gane makullin ta bari a
jiki. Ya yi kwafa. Ya ce.
“Ni da gidana a ke rufe min kofa? Ki yi kina sani, ranar da zan rama tana nan
zuwa”.
Kulsum ta yi murmushi ta san ta shaka masa. A zuciyar ta ta ce, "da na ce
gidana ne? Dadin abin ba daga bola ka tsinto ni ba”.

Turaki kwana ya yi da wannan bacin ran, washegari ba ta fito ba sai da

Please Login or Register in order to submit comment