You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Batulu
ta zo yi mata sallama tare da yaran ta. Suka yi sallama cike da begen juna. Kuma a
ranar ne Malam Yusha’u ya kawo mata dukkan kayan ta na sawa da na amfani, da
takardun makaranta daga Abuja.
A daren ranar Turaki bai neme ta ba, ya sa a ran sa ya fita sabgar ta, don shi
duk wata hanya da za ta kawo raini tsakanin sa da kowa bai son ta. Balle iyalin
sa. Duk da hudubar da Abdul’Ahad ke ta yi masa na cewar, kwantar da kai zai yi,
girman kai ba nasa ba ne a halin yanzu, ya aje sarautar sa da mulkin sa a gefe ya
lallashi Kulsum, laifi har ba iyaka ya san ya yi mata, amma ya san shi ba zai iya
ba, yana tattalin girman sa sosai.
A tunanin sa in har zai samu su kebe cikin nutsuwa ya san ta duk hanyar da zai
bi ya wanke laifin sa a aikace, amma ba ta irin hanyar da Abdul’Ahad ke so ba. Shi
Ba-sarake ne, wanda ya gaji sarauta gaba-da-baya ba haye ya yi ba. Kulsum ta je ta
yi ta yi, ranar da ta gaji za ta bari ne. Domin wannan karon auren su na har gaban
abada ne, don haka tun ranar bai kara zuwa ya buga mata kofa ba, ita kuma ba ta
fasa shigewa tun yamma ta kulle kan ta ba. Da ma ita in ta ci abinci karfe shida na
yamma shi ke nan kuma ba ta kara ci sai breakfast din washegari.
A haka suka zauna ba mai shiga harkar dan uwan sa har tsayin kwana biyar, ya
kama washegari ne hawan angoncin da Turaki ya shirya da abokan sa da ‘yan uwansa
maza. Kuma a ranar ne Abdul’Ahad ya iso, abin mamaki tare da Sajeedah. Bai gaya
masa ba don ta ce surprise ta ke son yi musu. Ba za ta iya hakuri ta zauna ba ta zo
ta ga Kulsum din Dr. Abubakar ba. Ta zama kawar ta ta farko daga bangaren matan
abokan su.
Turaki da kansa ya raka su wajen Umma da wajen Maimartaba suka kwashi gaisuwa,
Umma ta dade tana jin labarin Abdul’Ahad a wajen Turaki. Ba karamar tarba tasa aka
yi musu ba, aka kai su guest house din Maimartaba, amma sai Sajeedah ta ce ita
Allahnbur wajen Kulsum za ta sauka. Abdul’Ahad ya harare ta, ya ce,
“kin taba jin inda aka yi masauki a dakin amaryar da ko sati ba ta rufa ba?”
Ta ce, “Dear, ni ba zan hana su amarci ba, akwai sakonnin da zan bata ne. And I
want to be her first friend from Reading”.
Turaki ya ce da Abdul’Ahad ya kyale ta, in sun yi wanka sun huta zai zo ya
dauke ta zuwa wajen Kulsum din, amma a can karkashin zuciyar sa cike yake da
zullumi da taraddadin tarbar da za ta samu daga Kulsum din, shi kansa a me yake
gare ta balle wani nasa? Gabadaya ta canza daga Kulsum din da ya santa, saliha mai
sanyin hali, ta rikide zuwa wata halittar daban. Kamar ba ta san girman hakkin
aure a kan ta ba.
Laifi ya san ya yi mata, amma ta ba shi da ma mana ya wanke kansa?, Ya ba ta
hakuri kamar yadda Abdul’Ahad ya ce, su fahimci juna su manta baya? Babu dan Adam
din da ba ya kuskure a rayuwar sa. Sai dai shi zaman nan da yake tare da Kulsum
cikin gidan sa, duk da babu wata alaka mai dadi a tsakanin su, ya fiye masa
gabadaya lokutan rayuwar sa a Reading dadi, sanin cewa ita din mallakin sa ce, kuma
tana cikin dakin auren sa, shi ne babban kwanciyar hankalin sa.
Bai aure ta don biyan bukatar gangar jiki ba, sai don ita din bakidayan ta yake
so. Fatan sa Allah ya nuna masa ranar da zai sake mallakar Kulsum a shimfidar sa,
ya wanke gabadaya laifukan sa na baya ta hanyar da shi kadai ya san ta, ta hanyar
da shi kansa ya san unexpressable ce. Shi ne kuma kadai maganin taurin kan Kulsum.
Da wannan tunanin ya iso gida, ya adana motar a inda ya saba adana ta. Cikin
rashin karsashi ya nufi dakin Kulsum. Cikin sa’a ba ta kai ga rufewa ba kamar yadda
ta saba, don a lokacin ta ke sallar la’asar ma. Yana shiga ya rufe dakin da
makullin da ke jiki ya zare shi, ya rufe toilet shi ma ya zare. Ya hada su duka ya
zuba a aljihun rigar sa.
Kulsum na sallah tana jin duk abin da yake yi. Gaban ta ya yi mummunar faduwa
da ba ta san dalili ba. Turaki ya kishingida a gefen gadon ta yana kallonta with
lingering emotion a zuciya da idanun sa. Rabon da ya sanya ta a idanun sa yau kwana
hudu ke nan. Haka kawai ta hana musu morar amarcin su da kuruciyar su, sabida wani
fushin ta wanda bai karewa.
Kin sallamewa ta yi, in ta sallame sai ta tada wata, bayan kuma ya san bayan
la’asar ne ba lokacin nafila ba ne. Wato dai wadannan sallolin don shi aka kirkire
su, ba don Allah ba. Murmushi ya yi ya mike ya saki labulayen dakin gabadaya, ya
kashe kwan lantar ki ya kunna A.C. Dakin ya bada wani irin dim, sanyi mai dadi ya
fara ratsawa a jikkunan su. Rigar voile din da ke jikin sa ya cire ya saura daga
shi sai singileti da wandon jikin sa, ya yi kwanciyar sa a gadon Kulsum, yana
fadin,
“Yau daga ni sai ke, sai Ubangijin da ya sanya min soyayyar ki. Ki kashe ni ki
huta Kulsum, ya fiye min wannan silent killer punishment din naki”.
Ya dau filo ya rungume, ya yi kwanciyar sa.
Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta, ta yi sallolin har kafafun ta sun gaza
daukar ta, sallolin da ta tabbatar babu lada a cikin su. Ba ta yi aune ba ta dan
zauna tana hutawa, sai jin ta ta yi a hannun Abubakar-Turaki. Gabadayan ta ya sure
ta ya haye gadon da ita, ya ja duvet mai laushi ya lullube su, bayan ya rungume ta
tsam-tsam a cikin kowacce kusurwa ta jikin sa yadda bazata iya kwacewa ba. Kafin ya
soma kissing din ta wholeheartedly ma'ana da dukkan zuciyar sa. Ya ja tunga da lips
dinsa cikin nata, amma duk da ta soma ficewa a hayyacin ta a dalilin deep kisses
din Turaki, ba ta fasa kokarin kwatar kanta ba. Ba abin da ta tuno a lokacin sai
ranar su ta farko, ranar da Turaki bai taba tausayin ta ba… ranar da ya tabbatar
mata ba ya son ta, ya tara da ita ne a bisa tilas. Nan da nan ta fara protest, wasu
hawaye masu zafi na bin gefen fuskar ta. Turaki ya ji dumin su a kan fuskar sa, ya
sassauta daga tsattsauran rikon da ya yi mata, ya sake kissing din tausasan
labbanta softly. Wadanda a lokacin suka koma kalar light pink.
A hankali ya kira sunan ta, ba ta amsa ba sai hawayen ta da suke kara gudu,
sassanyan kamshin jikin sa na sanya ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa,
ta daina kokawar da ta ke yi da shi duk jikin ta ya saki. Abin da yake so ke nan,
ta nutsu ta saurare shi.
Ya ce, “Ummu Kulsum ko mene ne a tsakanin mu, komai girman laifi na, ina rokon
ki darajar iyayen ki ba don ni ba, ki jingine shi a gefe zuwa kwanaki uku, ki karbi
bakuncin babban amini na da matar sa, wadanda suka taso takanas tun daga U.K,
saboda su taya mu murnar aure”.
Kulsum ta kwace jikinta daga nasa, ta juya masa baya. Har wata murna za a taya
a wannan auren na rashin adalci? Turaki ya kwantar da kai a bayan ta, ya shiga
magiya da rokon ta yayin da hannayensa ke shafa kwantaccen gashin kanta, abin da
bai taba tunanin zai iya ba a rayuwar sa. Amma Abdul’Ahad na da babban matsayi a
wurin sa, duk da ya san komai ba ya so ya tozarta a idanun Sajeedah kamar yadda ya
tozarta a gaban Batulu, domin ya lura da gaske ta ke son Kulsumun, dole ya nemi
hadin kanta kafin ya kawo ta.
Kulsumu sai ta sa masa kuka, ta ce, “Ni ina ruwana da abokin ka balle matar sa?
Ce musu ka yi auren soyayya ka yi da zan nuna musu ina son auren ka? Ai gara ma ka
fada musu gaskiya cewa, yaudara ta ka yi ka dawo da ni gidan ka”.
Ajiyar zuciya ya yi, ya ce, “Duk na amince, atleast forget everything sai sun
tafi, sai ki ci gaba da gasa ni yadda ki ke so, in ci arzikin su. Ko a lahira wani
kan ci albarkacin wani. Kada ki manta bakon ka Annabin ka”.

Ba ta ce komai ba, amma reaction din ta ya nuna sassauci, ya mike daga gadon ya
kunna fitila jin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba. Ta ja quilt din ta rufe har
kanta.
Ya yi kwafa, ya ce, “Lokacin ki ne, ki ci gaba da wulakanta ni son ran ki, ni
na jawo da na saka miki ido har zuwa yau. Da na bambanta miki da da yanzu, da ba ki
raina ni har haka ba”.
Kyabe baki ta yi a cikin quilt din, kamar yana ganin ta.
Ya ce, “Zan dauko su idan na yi sallah, Umma za ta aiko da duk abin da za su
ci. Don Allah Kulsum ki taimake ni, irin dan murmushin nan na mata da miji da
caring din da mace ke nuna wa mijin ta. Ni kuma na yi alkawarin in sun tafi duk
abin da ki ke so zan yi miki”.
Da sauri ta ce, “Ba abin da nake so illa ka daina shigo min daki. Ba za ka taba
samun yadda ka ke so a tare da ni ba. Me ya hana lokacin da ni ma nake bukatar
kulawar ka a baya ka kula da ni ka tausaya mun? Ka kaunace ni? Amma sai ka tsallake
ka bar ni? Sai yanzu don na zama mutum? Wallahi ba zan taba mantawa da ko wane ne
Turaki ba. The vicious… the selfish… the rapist…”. (Mugu, mai son kai, mai fyade).
Runtse idanun sa ya yi, ya ce, “Ummu Kulsum, ki san abin da ki ke fada min, I’m
your husband no matter what, ki tuna mala’iku suna tare da ke. Ashe da ma akwai
rape a cikin aure? Idan na ce miki nima a lokacin ban san yaya ake auratayyar bafa?
Abin da zan ce shi ne, ki yi hakuri ki hadiye komai just for three
days, ......please". Ya fada cikin roko.
Shiru ta yi tana kara boye kanta cikin quilt, ba ta son kallon wadannan idanun
na Turaki, wadanda ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu. Yau ga Turaki
ta samu, amma zuciyar ta ta kasa karbar sa.
“In je in taho da su Kulsum kin amince? Please Kulsum just for three days…”.
Ta gaji da magiyar sa, kamar ba Turaki ba, wannan Prince din mai ji da kan sa,
ciki-ciki ta ce,
“na amince”.
Sosai fuskarsa ta washe ba tare da sanin sa ba, ya yi murmushin nan nasa na
gefen baki.
“Inyaso in sun tafi sai a cigaba da gasa ni, ko a yi gunduwa-gunduwa da ni,
Allah Sarki ni Abubakar”.
Ya fice yana cewa,
“Ki tashi ki shirya yanzu za mu shigo”.
Ko amsa ba ta ba shi ba, ya bude mata toilet da kofa da ya rufe ya fice har
wata irin sassarfa yake don farin cikin ya fara samun kanta.

Masaukin su Abdul’Ahad ya koma ya samu duk sun kimtsa, shi suke jira. Sajeedah
ta dauko ‘yar trolly din da ta zuba kayanta suka tafi.
Tun fitar sa Kulsum ta mike daga gadon, wanka ta sake yi, ta fito ta shirya
sosai. Wata shadda Ghanilla ta saka mai babban dinki senegalese ruwan goro, ta sha
aiki daga sama har kasa. Ta kawo mayafin da ya dace da kayan ta yafa. Tana fitowa
falo ta tarar Umma ta aiko ‘yan aikin ta sun kawo abincin da bakin za su ci. Ta
jera komai a dining ta kunna turaren oud a burner, gidan gabadaya ya dau sanyin
kamshi. Tana kokarin kunna talabijin ta ji sallamar su.
Turaki ne a gaba, Abdul’Ahad ya biyo bayan sa. Sai wata kyakkyawar mace son
kowa, wadda kallo daya ta yi mata ta gane zubinta ba na matan Nigeria ba ne. Ta
amsa sallamar su, tare da karasawa ta karbi jakar hannun Sajeedah. Murmushi suka yi
wa juna ta yi musu jagora zuwa cikin falon, amma ta kasa hada ido da Turaki, balle
ta yi masa abin da yake so, don ita ba ta iya pretending a komai ba. Yanzu-yanzu
idanun ta zasu bada ita. Sai dai ta sa a ranta ba za ta yi abin da zai bata ran shi
ba, don ta lura kwarai yake ji da bakin nan nasa.
Sosai Sajeedah ta ke kallon Kulsum, ta yaba da nutsuwa da kamalar ta. Kyau kam
akwai shi, amma ba na tada hankali ba. Irin dai na fulanin Gaya. Farat daya ta ji
Kulsum ta shiga ran ta. Duk yadda Turaki ke son su hada ido ta ki yarda. Ta kai
kayan Sajeedah har bedroom din ta, ta dawo ta zauna a kusa da ita, sannan ta yi
musu tayin cin abinci.
Gabadayan su suka hau tebir ta yi serving kowa, making sure ta fara serving
Turaki first. Wannan abu ya yi masa dadi, har ya samu karfin gwiwar yi mata magana.
“Sajeedah ta ce a wajen ki za ta sauka”.
Ta yi fara’a sosai tana duban Sajeedah, “You are most welcome Aunty Sajeedah,
na gode sosai da wannan karramawa”. Ta fada da harshen Turanci, kasancewar ta gane
Sajeedah ba ta jin hausa.
Sajeedah ta ce, “Da fatan ba zan takura wa amarya da ango ba. ina so mu saba
ne, mu fahimci juna. Wannan ne karona na farko na zuwa kasar Nigeria. I’m
Eritrean”.
Dr. Abdul’Ahad ya ce, “To fadi ba a tambaye ki ba”.
Kulsum ta yi ‘yar dariya, tana son mutane irin Sajeedah, haka suke open minded,
sannan ba sa bakunta a duk inda suka samu kan su.
Mazan suka koma tsakiyar falo suna hirar da ta shafe su. Ta ja Sajeedah suka yi
dakin ta. Sajeedah ta ce, “Ni fa na sanki ba tun yau ba, labarin ki iri-iri babu
wanda ban sani ba”.
Mamaki ya kama Kulsum, ta ce, “ke kuwa a ina ki ka san labari na?”
Duk cikin harshen turanci suke magana. Sajeedah ta ce, “Duk wanda ya san Dr.
Abubakar farin sani ya san ki Kulsum, ki gode wa Allah ba karamin so mijin ki ke
miki ba. Har ya yi rayuwar dalibtaka zuwa ta aiki a jami’ar Reading Dr. Abubakar ba
shi da budurwa. You are his only love tun daga sanda ya rabu da ke har zuwa yau da
ya kara samun ki.
Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa na nace sai na sauka a wurin ki. To
babban dalilin shi ne, don in labarta miki yadda Turaki ya kwashe shekara da
shekaru a cikin soyayyar ki, da neman inda zai gan ki. Babban burin kowace diya
mace shi ne ta auri mijin da ke son ta, fiye da son da ta ke yi masa. In haka ne
kuwa ke kam Kulsum kin dace, sai in ce ki kara rike mijin ki da daraja, soyayya da
kauna don ki kara nesanta zuciyar sa daga sauran mata".
Idanun Kulsumu suka cicciko da kwallah, ta ce, “Sajeedah, Turaki ya yi min
laifi da yawa, laifin da zuciya ta ta kasa yafe masa….”. Ta labarta mata komai, na
rayuwar su ta farko, amma ban da zancen fitsarin kwancen ta. Da haduwar su a
Lagos, da yadda ta gan shi a matsayin mijin ta na biyu. Ta share hawayen ta, ta ce,
“In ke ce za ki yarda yanzun da gaske yake son ki? A lokacin da na so ya so ni,
zuciya ta ta ke matukar son sa duk bai so ni ba, sai lokacin da na yi yaki da ita
na fidda shi da komai nasa a rai na?”
Sajeedah ta dafa kafadun ta biyu, ta ce, “Na fahimta Kulsum, shi da ma aure na
hadin iyaye ai haka yake, soyayya ba ta zuwa farat daya, tana zuwa ne gradually
along the way a cikin rayuwar aure. So ki bude zuciyar ki ki karbi soyayyar mijin
ki a wannan karon, ku mori rayuwar ku tare. Ki manta da duk abin da ya faru a baya,
tabbas Turaki bai kyauta ba, amma ki dauki hakan as a system of understanding one
another ke da Turaki. Ki daina waiwayen abin da ya riga ya faru, just the present.
Ubangijin da ya halicce mu ma yana mana afuwa a bisa kurakuran mu in mun yi
nadama, mun yi alkawarin ba za mu sake aikata wannan laifin ba”.
Kulsum ta turo baki cikin shagwaba irin tata ta ce, “Aunty Sajeedah, Turaki ba
ya lallashi na, komai cikin gadara da sarautar sa yake yin shi…”.
Dariya Sajeedah ta yi, ta ce, “Ke kuma so ki ke ya kwantar da kai ya lallashe
ki ko?”
Kulsum ta kai hannu ta rufe fuskar ta kunyar duniya ta lullube ta. Sajeedah ta
yi dariya, ta ce, “To ai wannan aikin ki ne Kulsum, shi naturally haka yake ko
magana wahala ta ke masa. Amma a matsayin ki na mace za ki iya shaping behaviour
din sa zuwa duk irin yadda ki ke so ya koma. Don Allah ki manta da komai Kulsum,
Turaki needs your love, ki rungume mijin ki, ya sha wahala a kan ki yadda ba kya
zato, yanzu ne lokacin da ya dace ya samu hutu da farin ciki a rayuwar sa”.
Kulsumu ba ta ce komai ba, amma tabbas maganganun Sajeedah sun yi tasiri sosai
a gare ta, ta yadda za ta fara gina kyakkyawar mu’amala tsakanin ta da Turaki ne ba
ta sani ba. Akwai kunya sosai ta sauko da wuri haka. Sajeedah ba ta kyale ta ba ta
ci gaba da tausar zuciyar ta, da kalamai masu dadi da karfafa gwiwa, sannan ta ce,
“na zo miki da abin da zai kara mallaka miki Turaki, sirrin mu ne na matan
Eritrea”.
Ta dauko jakar ta ta dinga fiddo mata su, ta kuma takura mata ta sha a gaban
ta.
Sai wajen goma na dare Abdul’Ahad ya koma masaukin sa bayan sun yi sallama shi
da Sajeedah. Ta yi shirin bacci ta ga Kulsum na gyara daya barin ita ma za ta
kwanta.
Ta ce, “A’ah Kulsum ya ya haka? Duk abubuwan da na fada miki ba ki dauki ko
daya ba ke nan? Ai sai Turaki ya gan ni Yayar banza, na zo na makale masa mata a
daki. Maza dauki duk abin da za ki dauka ki tafi turakar mijin ki”.
Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta da wannan umarni na Aunty Sajeedah. Ta kai
kan ta turakar Turaki? To ta ce masa me? Me ya kawo ta?
Girgiza kai ta yi, za ta yi magana Sajeedah ta tare ta, “Kulsum, mazan da ki ka
sani a da, ba daya suke da na yanzu ba. Dole ki mike ki nemo aljannar ki, ba ruwan
Allah da fushin da ki ke da Turaki, auren Turaki da ke wuyan ki shi ne abin da
Ubangiji zai yi la’akari da shi ranar gobe kiyama. Don haka ki sa a ranki kin yafe
wa Turaki dukkan laifukan sa, kin yi damarar kyakkyawan zama da shi daga daren yau,
ki roki Ubangiji ya ba ki karfin gwiwa don na lura kina da riko’.
Murmushi ta yi, sai dai ga dukkan alamu maganganun Sajeedah sun shige ta. Hatta
ruwan da za ta yi wanka Sajeedah ce ta hada mata, ta zuba turaren su na mutanen
Eritrea a cikin ruwan wankan. Ko da ta fito ita ta zabar mata rigar barcin da za ta
saka. Ta ce,
“Na fasa kwana a gidan nan, masaukin mu zan koma, har na kira Turaki na fada
masa, yanzun nan zai maida ni”.
Ta dafa kafadun Kulsum da idanunta suka yi rau-rau.
“Enjoy the blessings of your marriage my dear. Sai da safen mu”.
A nan ta bar jakarta, sai handbag dinta kawai ta dauka.
Bayan fitar ta Kulsum kasa bin shawarar ta ta yi, ta yi kwanciyar ta a dakin
ta, a ranta tana fadin, “Mu Hausa/Fulani ne Sajeedah, ba kabilar mu daya ba, da
kunya da kamun kai aka haife mu”.
Tana jin dawowar Turaki daga maida Sajeedah wajen mijin ta, ya kashe fitilun
falo da kayan wuta ya wuce dakin sa.
Mikewa ta yi ta kashe wutar dakin. Ta yi addu’a ta kwanta. Rana ta farko da ba
ta sanya key a kofar ba. Amma har barci ya dauke ta babu Turaki babu ko inuwar sa.
Wai kuma sai ta ji duk ta damu, ko dai shawarar Sajeedah za ta bi ne? Yau ta
yarda ba ta taba daina son Turaki ba, daidai da dakika daya, fushi da bacin ran
abin da ya yi mata a zaman su na baya shi ne ya danne soyayyar. A yanzu sai bankado
kanta ta ke tana bude sababbin rassa tana zuba sabuwar yabanya. Musamman da ta ji
labarin nan daga bakin Sajeedah na yadda Turaki ya sha wahalar dawainiyar soyayyar
ta.
Sai dai duk kokarin ta na ta iya kai kanta turakar Turaki ta kasa. Haka ta
kwana tana juyi a gado, ga ciwon mara sabida magungunan da Sajeedah ta dankara mata
masu karfi ne. Amma ta daure komai don tsira da jan ajin ta.
A dakin Turaki kuma yana bisa na’ura mai kwakwalwa ne yana yin wani research a
kan wani aikin ido da zai yi wa Sarkin Gombe mai fama da lalurar glaucoma sati mai
zuwa. Aikin da ya kai shi har karfe biyu na dare. Da ya gama ya yi shirin kwanciya
bai leka Kulsum ba, ba ya son ya yi abin da zai tunzurata ta fasa kula masa da
bakin sa. Saidai kwarai yake son ganin ta ko dan fadan ne su yi kafin ya kwanta.
Amma ya taushi zuciyar sa ya kyale ta, sai dai fa tun dazu da ya yi kissing Kulsum
komai ya kwance masa, cikin karfin hali yake komai, amma al’amarin ya tado masa da
tunanin can baya. Watarana guda daya da ba zai taba mantawa ba tsakanin sa da
Kulsum, ranar da ta canza rayuwar sa da zuciyar sa akan ta, ranar da Kulsum ta
shige sukuf cikin ransa.
Washegari ba su hadu ba sai wajen karfe goma na safe, ita ta fito tana kara
kintsa falon kamin isowar bakin su, shi kuma ya fito cikin shirin fita. Yadin
filtex ne ruwan makuba mai shara-shara a jikinsa. Ta lura Turaki na son yadikan
filtex marassa nauyi, masu taushi haka. Ba ta juyo daga abin da ta ke yi ba, wato
karkade center table da duster duk da babu wata kura a jikin sa. Turaki ya iso gare
ta, ta bayanta ya rungume ta ya sanya kansa a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta,
wani irin qamshi ya ji da ya gigita shi (turaren Sajeedah). Ya juyo da ita
bakidayanta suka fuskanci juna, da azama ya kara rungume ta ya soma kissing idanun
ta, hancin ta da bakinta very softly. Ta yi kokarin janyewa, amma bai ba ta damar
hakan ba. Bugun da ake yi wa kofar shigowa ya sa dole ya janye daga gare ta ya je
ya bude kofar. Abincin karin kumallon su ne da na bakin su Umma ta aiko a kawo.
Hanya ya bai wa matan suka wuce zuwa ciki, shi kuma ya koma inda ya baro
Kulsum, ta gagara ci gaba da aikin da ta ke yi ta zauna a cikin kujera tana
regaining consciousness

Please Login or Register in order to submit comment