You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zato taga ya dago kanta dake kasa yana karewa fuskarta kallo

lokaci guda yayi kicin-kicin da fuska gabanshi na wata irin faduwa, Allah yasa kar zarginsa ya
tabbata



sakin fuskar tata yayi gami da cewa"zanyi tafiya zuwa America sai rana ita yau zan dawo ki kula
da kanki, bayan haka kuma na lura da abinda kike kunshewa kallo guda da nai miki sabida kafin
in dawo ki ki samawa kanki mafita sabida kin san bazan taba karbar dan da ba nawa ba"
bai saurari abinda zatace ba kawai ya sakai ya fice daga dakin.




Tana kwance tana binshi da kallo har ya kari maganarshi ya fice tana mamakin furucinsa
itama tafara zargin wani abu gabanya ya dinga dukan uku-uku da sauri ta diro daga bed din ta
nufi toliet ta dauko pt ta dauki fitsarinta ta fara kokarin gwadawa,Addu'a take Allah yasa kar
zarginta ya zama gaskiya




Aikuwa Allah bai amsa mata ba domin positive ya nuna mata,zaman dirshan tayi a toilet din
jikinta na kyarma,ranar da aka kawota gidan nan ranar tagama al'ada aranar tai wanka,kuma
ranar ta dauki ciki,innalillahi wa inna ilayi raji'un




Kuka ne ya kufce mata tanayi tana mai-mai ta innalilahi dama rabo ne ya kawota gidan Nasir
gashi ya fahimci ciki ne da ita tun ba aje ko ina ba, tasan sarai baya kaunar haihuwa ita kam ko
zama da kasa zata hade baza ta yadda ya zubar mata da ciki ba




nan ta karaci kuke kukenta ta mike tayi wanka tafito ta shirya tsaf, ta dauki aniyar yaqi da Nasir
duk abinda zai biyo baya zata dauka domin bazata yadda ya zubar mata da ciki ba.
[6/20, 16:21] Binta Umar Abbale: Tunda Nasir ya tafi basu hadu da Mubina ba ko wacce na
gurinta, yau kwananshi biyar saura kwana biyu ya dawo kenan,




Mubina suna waya dashi kullum in bai kirata ba ita zata kirashi wani lokacin in "yan
wulakancinsa suna kusa sai yaqi dagawa ku kuma yafara neman fada babu arziqi take masa
sallama,ta aje wayar.




Maryam ko jikinta yaqi dadi kullum cikin zazzabi take ga jiri babu damar ta dade a zaune in ta
mike tsaye sai jiri ya kusa kada ita, haka dai take daddafawa ta sha magunguna abin sai a
hankali
Misalin karfe hudu na safe na yamma jirginsu Nasir ya sauka a filin saukar jirage na Malam
Aminu dake kano,




Yaranshi Tony da giss suna hango fitowarshi daga jirgi suka nufeshi da sauri ko wanne fuskarsa
dauke da murmushi na murnar dawowar oga




rungumeshi sukai suna dariya,shima dariyar yake sannan suka nufi inda motarsu take,




Giss yace" Boss ina Abokinka ne,naga tare kuka tafi"



"yana can na barshi yana hado mana kaya mybe gobe ko jibi ka ganshi"




Tony yace"Boss ina muka nufa ne"




hutawa yake so yayi yasan in ya je gida yanzu Momy bazata barshi ba,kai tsaye yace mu wuce
can gest house dina idan na huta sai muje gurin Momy"



"Ok Boss"



lumshe idanshi yayi yana jin wani irin a jikinshi tsigar jikinshi sai tashi takeyi in ya tuno da wani
abu wanda shi kadai yasan ko menene shi
Tony da Giss ne suke ta faman yi masa hira wani ya amsa wani ya share shi kadai ya san
abinda yake damunshi tsawon kwanaki bakwai din nan da yayi dauriya kawai yake,amma bazai
je ya kashe kanshi ba,tunda shi dai ga yadda Allah ya halliceshi




"Boss mun karaso"
Giss yafada bayan ya bude mashi kofa




a hankali ya bude idanshi wadanda suka kada sukayi jajazir dasu ya fito daga cikin motar,Giss
yayi saurin yin gaba yaje ya bude mashi kofa yana jiran karasowarshi,
sai da ya shiga sannan ya bi bayanshi hannunshi rike da karamar jakarshi da ya tafi da ita
bayan ya aje jakar sai ya fito ya barshi domin yaji dadin hutawa




yana zama gefan gado wayarshi ta fara kara

wayar ya kalla ganin Momynshi ce yasa ya dauki wayar yana sauke ajiyar zuciya,

"Momah"
yafada muryarshi kasa-kasa




Itama ajiyar zuciyar ta sauke tace"Myson ya naji muryar ka kamar na mara lafiya,uhum? ina nan
zaune ina jiran karasowarka, kace karfe hudu zaku sauka ko"?




Gyara murya yayi ya san halin Momynshi yanzun nan sai ta tada hankalinta, yace"Momy mun
sauka, yanzu haka ina gesthouse dina,ina hutawa bayan sallahr magariba zan shigo"

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment