You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai-dai ba ,jikinshi na rawa ya shiga motar sosai
gami da dago ta ya rungume ta a jikinshi yana tunanin wane irin taimako zai mata a karo na
biyu

Wata zuciyar tace kayi mata irin Wanda kayi mata kwanaki baya

Batare da ya tsaya wani tunani ba kawai ya dago fuskarta ya sa bakinta a nasa yana hura mata
iskar dake bakinshi

Yafi minti goma yana abu daya sannan taja wata shegiyar a jiyar zuciyar numfashinta ya dawo
dai-dai idanunta a rumtse taki yadda ta budesu

Qirjinta ya kalla ganin yadda zuciyarta take bugawa fat!fat ,bai San sanda ya dora hannunshi a
kai ba yana dannawa

Maryam ta bude idonta da sauri jin kamar Hannun mutum a jikinta kuma a kan kirjinta,ido hudu
sukayi da Nasir Wanda ya zuba mata idonshi sosai yake kare mata kallo yau.

Saurin dauke kansa yayi daga kanta domin bayason yana kallon idonta da daddare,

Ta yunkura zata tashi takasa ,sabida yadda yayi mata rikon tsauri



Da kyar ta bude baki tace"ka sakar min jikina domin ni ba lalatarciya bace,kuma Allah ya isa
taba min jiki da kayi"



Shiru yayi na minti uku yana dai dai ta nutsuwarshi domin kusancinsu da ita ya tayar mai da
tsumammiyar sha'awarta ta shekaru da dama ,

Ya kwantar da ita sosai cikin kujera ,sannan ya fito ya maida kofar ya rufe ya zagaya
mazauninshi ya zauna ya kunna motar,



Kai tsaye gida ya nufa da ita



Da kyar ta samu ta mike zaune jikinta a mace sakamakon tafiyar kafa da tayi abinda bata saba
ba ,kallon hijab din ta tayi Wanda ya jike jagab da ruwa ,mamaki takeyi mai ya jika mata jiki
haka

Ta kalleshi ganin ya nufi gida da ita tace"ka maryar dani asibiti domin aunty tanacan tana
nemana nasani ko wannan hakki ma nasan Allah bazai barka dashi ba"



Babu abinda yace mata kawai ya cigaba da tukinshi batare da ya sauya hanya ba

Haka har suka je gida ,ya fito kawai ya kulle motar batare da ya kalli inda take zaune ba yayi
shigewarsa part dinshi



Tafi minti goma a cikin motar tana saqawa tana kwancewa, sannan tafito jikinta duk yayi mata
nauyi ta nufi part dinsu tana addu'ar Allah yasa kar taga Malam ya fito sallar dare domin yanzu
ne lokancin tashinsa,
[24/05/2019 12:04 PM] ®Binta Umar Abbale: A kuwa Malam Ya'u na tsugune a tsakar gida yana
daura alwala,Maryam ta shigo
Gabanta yafadi ,addu'ata bata karbu ba



Kallonta yakeyi cikin mamaki yace"Maryama kece da dadaranan ,Allah yasa lafia
Domin ya kawo ko Baban gida ne rai yayi halinsa



Cikin ina ina tace "e nice Baba, aunty ce lallai sai na bawa uncle hakuri wai nayi masa rashin
kunya,shine Na tawo gida nazo na bashi hakuri"

Cikin mamaki yake nazarinta yace"aunt taki ce tace"lallai kizo kibashi hakuri da daddaran nan,ai
a bari sai da safe"



Daga kai tayi ,yace "shikkenan ai wuce ciki,zamu hadu da ita"



Maryam ta shige simi simi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki

Malam ko ya dade yana tunanin abin ,daga bisani ya daura alwalarsa ya mike daga gurin



Maryam ko tana shiga dakinta toleit ta shiga tayi wanka da ruwan zafi ,sannan ta dauro alwala
tafito ta shirya tsaf ta hau kan dadduma ta tada sallah, tadade tana addu'oi a kan Allah ya kawo
musu dauki ita da iyayenta ,sannan ta kwanta, tana tunanin abinda ya faru da ita a wannan dare



Fuskar Nasir kawai take gani yana mata gizo lokacin da tafarka daga suman da tayi ta ganta a
kwance a jikinshi ga fuskarsa daf da tata, zuciyarta ra rinqa bugawa , tunda Allah ya hallice bata
taba son wani kamar yadda take sonsa ba ,amma ta bawar zuciyarta sabida ta naganin yafi
karfinta bayan haka kuma kwata-kwata bata sha'awar auran namiji manemin mata, sabida tana
da kishi sosai shiyasa tun lokacin da taganshi da "yan matansa takeji kamar takashe kanta ta
huta.



Babban abinda yake hadata dashi shine rashin ganin girman iyayenta da bayayi ita duk
mutumin da baya ganin darajar iyayenta to itama bazata ga girmanshi ba,shiyasa take ganin
girman Abdul sabida yadda yakeson ta yake ganin girman iyayenta baya gudun talaucinsu, duk
son da takewa uncle baza ta bari ya wulakan tamata iyaye ba,



Tun tana yarinyar "yar shekara bakwai baxata taba mantawa ba lokacin uncle din ya zo Hutu
daga da ya shiga gurinsu aunty take fada mata shine a uncle dinta to tunda ga lokacin takejin
wani Abu a zuciyarta a game dashi har yanzu tanajin abun ,sai dai taki yadda abin ya bayyana
ya fito fili sabida tasan Nasir din ba tsaranta bane
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: [25/05/2019 10:06 AM] ®Binta Umar Abbale: [25/05/2019
9:49 AM] ®Binta Umar Abbale: [25/05/2019 9:16 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*88*

To shima nasa bangaran tunanin da yakeyi kenan tun da ya taso a rayuwarsa yayi hulda da
mata iri -iri amma bai ta ba cin karo da yariyar da take caza masa kai ba kamar Maryam tunda
ya daura idansa a kanta a lokacin da yazo hutu lokacin tana shekara bakwai a duniya yakejin
wata muguwar tsanarta a zuciyarsa, haka kawai yaji baya son ganinta ko gilmawarta a guri
,dalili kuwa tun ranar ya fara mafarki da ita in har ya kwanta bacci, duk tsawon shekarun nan bai
fasa mafarkin taba, shiyasa yake kauce wa abinda zai hadasu guri guda, amma can kasan
zuciyarsa yana jin wani matsanan cin kishinta wanda yake sawa yaji kwata-kwata baya kaunar
ya bude ido ya ganta da wani namiji.



Haka yayi ta juye juye kan bed yana jin wani iri a jikinsa yarinyar ta tayar masa da sha'awa
wacce ta sanya masa kasala yaji ko Dan ya tsansa baya son ya daga, haka yayi ta taune
lebanshi na kasa idanshi yayi ja ya mike da kyar ya nufi toleit ya dinga zubawa kanshi ruwan
sanyi ko yaji sauqin abin amma abu yaci tura tamkar karawa kansa wata sha'awar yakeyi ,gashi
yayi alkwarin ba zai sake kusantar wata mace ba mutukar ba matarshi bace

Ya fito a daddafe ya fara laliban magani ya balli biyu ya sanya a bakinshi batare da ruwa ba
haka yake tsotsa ya fadi kan bed din rigif! Hannuwanshi dafe da mararshi

Wajan minti goma sha biyar abin ya fara lafa masa ,sai gumi yakeyi tamkar babu Ac a dakin a
haka bacci ya dauke shi na wahala.




Washe gari Maryam da wurwuri ta tashi tayi Wanka tsaf ta shiga kchin ta na hada abin karin
kumallo Malam ya leqo yace"kiyi sauri ki kammala mutafi ,dazu da'a suba aunty taki tayo waya
hankalinta a tashe ,wai an ne meki an rasa, nace mata ta kwantar da hankalinta gaki nan a
gida"



Gabanta ne ya fadi tana jin tsoran haduwarta da aunty ,sabida tasan dole sai tayi mata fada, tafi
jin tsoran aunty ta a kan Malam sabida shi bashi da zafi kamar aunty



Muryarta a sanyaye tace"to Baba yanzu zan gama insha Allahu"
Ficewa yayi daga kchin din hannunshi rike da carbi yana ja ya nufi bakin get din



Nasir ya fito jikinsa sanye da kayan motsa jiki , ya nufi bakin get din



Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya mikawa Malam hannu domin su gaisa kamar yadda suka
saba



Mamaki Malam yakeyi sabida Nasir din a kwanaki baya bashi hannu

Sai ya mika masa hannushi shima yace"Nasiru ka tashi lafia"



"Lafiya arrama "
Nasir din yafada yana kokarin zare hannusa

"To masha Allahu
Jiya kuma sai naga wannan yarinyar cikin dare wai aunty ta ce tazo ta Baja hakuri, Dan rashin
hankali, nace bata bari gari ya waye ba"
[25/05/2019 9:48 AM] ®Binta Umar Abbale: Gabanshi ne ya fadi kadan yana addu'ar Allah yasa
kar yarinyar ta fada masa abinda ya faru ita dashi



Sai ya gyara fuska yace"Owk ai ni bangan taba ma kwata kwata a jiya"

Cikin mamaki Malam yace"tace kuma tazo gurinka tabaka hakuri"

Girgiza kai yayi kai tsaye yace"batazo ba"

Kawai ya fice ya bar Malam tsaye a gurin yana binshi da kallo

Zama yayi kan bainci dake gurin yana al'ajabin wannan abu ,amma zai zaunar da Maryam din
ya tuhume ta yasan yarinyarsa tsarkakkiya ce kuma ba zatayi masa karya ba.



Nasir kuwa Can wani guri ya nufa cikin estet din nasu da suke motsa jiki yafara motsa jikinshi
babu abinda ya dameshi.



Tsaf tagama hada komai tafito jikinta sanye da katon hijab dinta kamar yadda ta saba,ta aje
kayan dake hannunta kusa da Malam tace"Baba bari inje mu gaisa da Momy ko"



"To babu Laifi "
Malam yafada yana bin ta da kallo



Kai tsaye part din Momy ta nufa

Momy na zaune kan kujarar daining ita dasu Nafi'u sun shirya tsaf , Uwani mai aikinta tana hada
musu breakfast ,Maryam tayi sallama



Momy ta amsa mata fuska a sake tace"Dota shigo mana kika tsaya nan"



Kanta a sunkuye ta shiga ciki farlo sosai ta karasa gurin Momy din ta durkusa har kasa tana
gaida ta



Momy tace"Nima yanzu nake cewa Nafi'u ya gama karyawa yaje ya kirawo min ke"

Murmushi tayi batace komai ba



"Ina fatan kin karya ko"
Momy tafada tana kallonta

"Eh Momy na karya ga abinci can ma nayiwa su aunty"



Momy tace"ai da baki bawa kanki wahala ba ,tuntuni nasa Uwani tayi musu"

"Laa Momy ai babu komai sai su hada da nawa"

Dariya Momy tayi tace"to shikkenan sai ki jiramu mu gama karyawa a nutse sai mu tafi"

"To Momy"
Maryam tafada gami da mikewa taje ta zauna cikin daya daga cikin kujerun farlo

Ko minti uku batayi da zama ba Nasir ya shigo farlo

Idansu ya tsarke guri guda
Da sauri ta dauke kai ta mayar kan kayuwat TV plasma dake manne a farlo din, ta cigaba da
kallonta



Fuska ya hade sosai yana namakin mai yakawo yarinyar nan da sanyi safiyar nan , zuciyarsa
yace mybe ko Momy ce ta jajibo ta yasan halin Momynsa da kwashe kwashe

Kai tsaye Tv ya je ya kashe batare da ya saurari gaisuwar da su Nafi'u suke masa ya shige
dakinsa dake farlon



Baki a sake Momy take binshi da kallo tana namakin abinda yake nufi, girgiza kai tayi kawai
tacigaba da cin abincin ta

Bai fi minti biyu da shiga ba sai gashi ya fito yana ya mutse fuska hannunshi rike da wayarsa
yana daddanawa ya tsaya daga bakin kofar dakinshi yana kallon Momy yace"Momy wai Dan
bana amfani da room din nan sosai shine ba'a gyara min, yanzu inaso in shiga toilet na tadda
ko ina kaca-kaca"




Hararasa Momy tayi tace "sannu Ubana kashigo ba ka kula kowa ba shine yanzu zakazo ka
titsiye ni da tambaya"
[25/05/2019 10:06 AM] ®Binta Umar Abbale: Please Momyna kisa a gyara min dan Allah
,Wanka nakeso inyi zan fita"

Yafada yana karasowa inda take zaune

Momy tace"ko jiya sai da nasa, Kyauta, mai yimin goge goge ta gyara maka dakin kai dai kawai
kace zakayi min iyayi"



Dariya yayi kadan abinda ya Dade bai yi mata ba ,yana kallonta yace"Momy kinsan halina
banason kazanta,wallahi tunda na shigo Farlon nan nakejin karni na tashi nake kamar zanyi
amai wallahi"
Ya karashe Maganar yana ya mutse fuska

Kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake ba Maryam kadai ba ita kanta Momy ta tsargu
da Nasir din domin tunda take dashi bai taba yi mata irin wannan maganar ba ,kasancewar a ko
da yaushe ko ina na gidan cikin kamshi yake sabida Allah da yayi Momy a kwai San kamshi.

Sai tayi shiru da bakinta domin bataso ta kara wata maganar Nasir din ya kwabo wata maganar
tasan zuciya batada kashi dole wata rana Maryam din tafara mai da martani kamar yadda tafara
ramawa jiya a asibiti



Minti biyu farlo yayi tsitt Maryam sai kokarin danne zuciyarta takeyi ,sabida yadda take jin kamar
ta tashi tabar gurin ,tana jin kunyar Momy ne kawai kuma tana ganin mutumcin ta, amma ranta
ya yi mugun baci da wulakancin da Nasir yake mata idanta ya Tara kwalla sai kokarin mayarwa
takeyi ,kawai tajiyo Muryar Momy tana cewa Maryam Dan Allah shiga ki gyara masa dakin kafin
mu gama kinji ko"

"Don Allah"
Tafada maganar cikin zuciyarta

Yanzu Momy ce take hadata da Allah

Allah sarki Momy ,albasa batayi halin ruwa ba

A nutse ta mike tsaye tana gyara hijab din ta juyo ,fuskarta a sake tace"to Momy karki damu
yanzu zanyi abinda kikace insha Allahu"
[25/05/2019 2:00 PM] ®Binta Umar Abbale: "Yawwa Dota Allah yayi miki albarka"
Momy tafada cikin farin ciki yarinyar tana burgeta sosai ,tanada hankali kwata-kwata bata
biyewa Nasir din da abinda yakeyi



Cikin nutsuwa ta nufi bed din ,Nasir ya dago kanshi dake sunkuye yana kallon wayarshi ya bita
da kallo yana ya mutse fuska ,yace"ke!"



Maryam ta juyo a nutse tana kallonsa

Yace "kar ki kuskura kiyi min binkice a daki domin a kwai muhiman abubuwana a ciki , duk
abinda na nema narasa to sai kin biya ni"



Shiru Maryam tayi a tsaye tana tunanin ta shiga ko tafasa tunda zargi ya shigo ciki

Momy tace"wai mai yasa kake hakane my Son mai Maryam tayi maka kuma kake mata wani
zargi na daban"



Shiru yayi baice komai ba ya cigaba da danne dannensa a waya babu abinda ya dameshi
Momy tayi kwafa kawai ranta a bace tace"Dota yi hakuri kinji ko ,kar ki dakata ta halinshi kiyi
domin ni"



Maryam tayi dariya mai ciwo race"Momy karki damu ai uncle yana da gaskiya , kar inje inga
wani abu nasa mai muhimanci in share ko in zubar, kwata-kwata raina bai baci ba"



Momy tasan Maryam din dannewa tayi kawai sabida kawaici irin nata,sai tace "to shikkenan
Maryam je kiyi sauri ki kammala muwuce ko"



Maryam ta wuce dakin ranta yana mata suya tarasa inda zata sa ranta sabida yadda takeji a
yanzu zata iya fito na fito da Nasir din ko dame yake taqama Kuwa




Babu wani datti a cikin dakin na kuzo mu gani ko ina tsaf in banda bedshit din da yayi datti
kadan kasancewarsa mai kalar haske ,cikin sauri ta dauke shi gami da zare rigunan filillikan
tabude sif ta Ciro wani sabo a ledarsa ,ta shimfida tsaf, sannan ta wuce toilet din shima babu
wani datti



Sai jirwayen sabulu na Wanka shima ba sosai ba asalima in banda kamshi babu abinda yake
tashi a ciki na irin kalolin sabulan da yake amfani dashi gurin Wanka da wanke sumarsa



Tsaf ta wanke ta sanya turaran wuta Na ban daki ,sannan tahada masa kananun wan dunanshi
da vest dinshi a cikin abin wanki ,afili tace "wallahi bazan wanke ba masa Dan iska kawai,Dan
rainin hankali"



Ta fito tana Jan tsaki kai tsaye kofa ta nufa domin fita daga dakin,suka ci karo dashi,zai shi go



Maryam tayi baya da sauri tana dafe goshinta sakamakon yadda suka gabza karo,ya shigo
dakin yana bin ta da wani mutsiyacin kallo Na kaskanci ya mayar da kofar ya rufe yana bin
dakin da kallo ,fuskarshi a hade




Bata kalleshi ba ta sanya hannunta a Karo na biyu tana kokarin bude kofar
Taji ta a kulle gam!

Sai ta waigo tana kallonshi fuskarta a murtuke

Kallon kallo sukeyi minti biyar tukkuna yace"kika kuskura kika fadama mahaifinki abinda yafaru
jiya wallahi sai na kaiki inda baza ki iya dawowa ba kin tafi kenan"



"Kashe ni zakiyi Kenan"?
Maryam tafada kai tsaye tana kallonshi babu kifta wa



"Yes"
Yafada yana zare mata ido

Dariya ce ta subuce mata bata shirya ba ,tace "wallahi da naji dadin haka kaga dana huta da
ganinka a duniyar nan domin bana kaunar in bude ido in ganka a rayuwata"



Shiru yayi yana bin ta da kallo Sam maganganunta basu bata masa rai ba so yakeyi ya kirkiri
abinda zai bakan ta mata rai yanzu

Zama yayi gefan gadon yana ya mutse fuska yace "Ke boyi boyi na zo nan Dan Ubanki ki fito
min da kayan da zansa yanzu nan"



Wani mugun shocking Maryam taji a jikinta lokacin da ya kirata da wannan Kalmar Boyi-Boyi
,har da zagin Ubanta,lallai yau zata nuna masa tasan darajar iyayenta
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*

*89*



Maryam ta juyo a nutse tana kallonsa fuskarta babu yabo babu fallasa,tace "Nasir inaso kasa ni,
ni Maryam wallahi nafi qarfin in zama boyi-boyin ka ,dukkanin abinda kaga ina yi maka ina yi
makane kawai sabida darajar Momynka,amma kasani cewar kudinka ko takamarka basu isa su
sa na yi maka bauta ba ,wallahi in har nice zan dauko maka kayan da zaka sa,to sai dai a
kwana a haka,amma kai baka isa kasani abinda banyi niyya ba"



Idanshi tsaye a kanta har ta kare maganar
Ranshi a bace yace"Na nawa kuma yarinya ,Wanda yayi silar zuwanki duniya ma gashi can
bakin get yana min gadi,ballantana ke!!"
Ya karashe maganar yana nunata da hannu cikin izgili

Kuka ne yakeso ya Kufcewa Maryam jin cin mutumcin ya shallake kanta ya dawo kan
Mahaifinta



Tace"tabbas kafadi gaskiya mahaifina ba komai bane ,kuma ba kowa bane a duniyar nan ,muna
nai man tsari da dukiyar da zata samu mu manta da Allah mu shagala da duniya murika sabon
Allah a cikinta"



"Ke kika sani dai yarinya na get out malama"
Yafada yana nuna mata kofa



Maryam ta bude kofa ta fice batare kawai tana girgiza kai cikin takaici wulakancinsa




Momy na tsaye da hijab a hannunta tana kokarin sawa tace"yawwa dama yanzu nake kokarin in
shiga in miki magana kifito mutafi naji shiru,nace Allah yasa bawani abin yayi miki ba"



Cikin kokarin danne abinda yake taso mata Na bacin rai tace "babu komai wallahi Momy nayi
duk abinda kika Sani"



"Yawwa Allah yayi miki albarka"
Momy tafada
Sannan suka fita a tare
Momy ta daukesu a motarta har Malam Ya'u suka nufi asibitin




Mikewa yayi bayan fitarta ya nufi tolirt a gurgije yayi Wanka ya fito ya nufi inda kananun
kayanshi ,ya kwana biyu bai sasu yau sai yaji yana sha'awarsu ,tsaf ya shirya cikin wani mugun
wando jins mai mutukar tsada blue colour shart din ma haka ta matse masa jiki sosai power
dinshi ya fito ya gyara sumarshi tsaf sannan ya dauki agogonshi ya daura,ya nufi inda
takalmanshi suke ,sai da ya sanya safa sannan ya saka wani mugun takalmi fadar kudinshi ma
aiki ne ,sosai Yayi bala'in kyau ,sabida yadda dressing din ya karbe shi ,sabida yadda ya yi qiba
jikinshi ya murje sosai ya fito ,ya nufi inda motarshi take shima babu inda yayiwa tsinke sai
hospital din yanaso yaje ya duba marasa lafiyarsa ,sannan ya wuce can gurin Abbas domin
cigaba da tsare tsarensu na bude sabon gurin shakatawa da zasuyi
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:51 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*90*

Alhamdullihi jikin Baban gida yayi sauki sosai ,yana zaune gefan gado su aunty a kusa dashi ,
su Momy sukayi sallama cikin dakin, Yaya Rabi ta amsa tana yiwa Momy sannu da zuwa, fuska
a sake Momy ta karasa cikin dakin tace"A'a lallai jiki yayi sauki Baban gida Allah ya kara afuwa"
"Alhamdullhi kam jiki ya samu wallahi"aunty tafada tana bawa Momy gurin zama Momy ta
zauna suna gaisawa da Yaya Rabi cikin mutumci , aunty ma suka gaisa cikin sakin fuska Yaya
Rabbi ta kalli Maryam dake tsaye jikinta a sanyaye tace"ke kuma abinda kikayi kin kyauta cikin
dare ki fita ,kisa mi ta nai manki ko duk kin daga mana hankali"

Maryam ta sunkuyar da kanta kasa ,domin bata da abin cewa,tasan in tafadi abinda ya faru ba
yadda zasuyi ba




Momy tace"subahanallahi kamar yaya tafita cikin dare"?



Aunty ta girgiza kai cikin bacin rai tana kallon Momy tace"wai daga cewa in uncle dinta ya shigo
taje tabashi hakuri kan irin rashin kunyar da tayi masa jiya,shine da ta fakaici idon mu taga
munyi bacci shine ta gudu gida ,sabida tana ganin kyashin ta tsaya tabashi hakuri"



Momy tayi murmushi tace "Laifin mai tayi da har zaki titsiyeta kice lallai sai tabashi hakuri ,waya
gaya miki anawa yara haka,? Ni sam banga laifin ta ba ,Dan yaro ya tsare kare martabar
iyayenshi sai ace yayi laifi ,karki kara yin haka Suwaibah wannan ba hukunci ba ne"



Malam Ya'u yana tsaye jikin gadon da Baban gida yake kwance ,ya sauke ajiyar zuciya yace"
nima abinda nakeso ince mata kenan abinda tayi bai yi dai-dai ba ,jiya misalin uku shaura Na
dare naganta ta shi go gidan a furgice,hankali na ya tashi sosai ,duk Na tambaye ta dalili shine
take fada min



Yaya Rabi tace"kwarai hakan ba dai-dai bane wallahi kar kiso kiga yadda hankalinmu ya tashi
jiya

Sai da asubah da nace ta kira Babanta ta sanar dashi halin da ake ciki ,shine fa yake cewa gata
a gida mu kwantar da hankalimu"
Momy tayi ajiyar zuciya tana kallon Maryam din tace "kar ki kara aikata irin haka,yanzu inda
wani Abu ya sameki Na tsautsayi kice mai,Allah ya kiyaye ameen"



Maryam tace"insha Allah Momy bazan karaba"

Momy tace"ga kayan kari nan Rabi"

Yaya Rabi tace" to angode Hajiya Allah yakara girma ya jikan magabata"

Nan Momy tasa a ka hadawa Baban gida abinci a kabashi sannan tabashi magani da
kanta,suna hira kadan kadan,Nasir ya shi go cikin dakin Dr Sofia na bayanshi hannunta rike da
wasu takkadu
[26/05/2019 10:18 AM] ®Binta Umar Abbale: Sama-sama ya gaida su aunty hankalinshi na kan
Baban gida,Dr Sofia kuwa babu wanda ta gaida a cikinsu sai Momy ,to Momy Sam bata kawo
komai ba , sabida tasan yarinyar dama can ba wani hausa takeji ba sai turanci amma dai duk
da haka inda mutumci yadda ta gaida ita ta gaida sauran da suke tare

Aunty ma jikinta ne yafara sanyi sabida ta lura da irin kallon raini da Dr Sofia take musu ita da
Yaya Rabi,amma sai ta daurewa zucuyarta tace ko Dan yarinyar ba musulma bace shiyasa
batasan darajar Dan adam ba.




Maryam ko taci alwashi sai ta ci mata mutumci ko da me take takama wallahi bazata raina mata
iyaye ba,tana addu'ar Allah yasa kafin su gama zaman asibitin wani abu ya hadasu da'ita sai ta
wulakantata
Dama gashi tana jin haushin yadda take wani shishshigewa Nasir din Dan wani lokacin tana
lura jikinsu har haduwa yakeyi



Ya karasa bakin gado yana duba shi sosai Ya kalli aunty kadan yace"anbashi magani ko"?



Aunty tace"eh yanzu Momy tabashi"

Shiru yayi kawai ,ya dauke idonshi daga kan Baban gida ya dora kan Momy ,fuskarshi kamar ko
da yaushe yace"Momy ina ganin zan sallameshi tunda ya dawo normal So sai ya cigaba da
karbar magani a gida ,sabida ni banaso ana cika min asibiti kullum"
Duk cikin turanci yake maganar in banda ita Momy din da Dr Sofia da Maryam babu Wanda ya
fahimci abinda yake fada
Cikin turancin Momy tace"Why My Son mai yasa kake haka ne suwaye mutane ,ni ko kuwa
iyalan wannan bawan Allah ,uhumm! Wulakanci fa babu kyau"



Ya mutse fuska yayi kadan yana duba a gogo yace" Momy bafa haka nake nufi ba please
kinsan komai nawa a tsare yake ,wallahi kwata kwata tunda suka shigo hospital din nan daga
jiya zuwa yau komai ya sauya,gwara kawai su koma gida ,sai in cigaba da kula dashi"

Dr Sofia tasa baki ita ma cikin ya mutse fuska cikin turancin ta tace"yes Bama bukatar hayaniya
a wannan guri Momy sabida duk yawanci marasa lafiya suna bukatar huto da kwanciyar
hankali"



"Momy tayi kwafa tana kallonta rai a bace tace" wato koya min yadda aikin asibiti yake zakuyi
ko kuwa tun kafin a haifeku nake wannan aiki"



"Sorry Mom ba haka bane , kiyi hakuri in maganar tayi miki ciwo ,in babu damuwa abar mana
Mara lafiyar shi kadai kawai bama bukatar "yan jiya ,sabida a kwai masu kula da..

"Ya'isa"! Maryam tafada a hasale tana nuna Dr Sofia da hannu cikin turanci tace"ko kunce ko
baku ce ba dole Baban gida zai bar asibitin nan tunda ba Ku zaku bashi lafia ba , ni nan na isa
in kula dashi tunda nima abinda na karanta kenan baku kadai Allah ya bawa ilimin ba,akin
banza aikin wofi ,sai anyi magana ki dinga yiwa mutane turamci banza da wofi da wani rubban
bakin ki da yagaji da shan giya da kayan maye"
[26/05/2019 12:07 PM] ®Binta Umar Abbale: Shiru dakin yayi duk sun zubawa Maryam ido



Momy taji dadin abinda Maryam tayiwa Dr Sofia ,sabida ta lura yarinyar tana da girman kai



Dr Sofia ta kalli Nasir ranta a bace tace"kaji abinda wannan yarin take cewa ko, kamar ni zata
dinga zagi tana fadawa magana ,ina kan aiki na"



Shiru yayi kawai baice mata komai amma ranshi yayi bala'in baci da abinda Maryam din tayi
,wato duk kokarin da yakeyi a kansu bata gani,ya lura zaqewarta tayi yawa amma zai taka mata
burki



Fita yayi daga dakin batare da kara magana ba Dr Sofia tabishi a baya itama ranta a bace , duk
suka bisu da kallo,



Maryam ta sauke ajiyar zuciya tanajin dadi ko babu komai ta'amayar da abinda yake damunta




Ko da Nasir ya fita ,kai tsaye bakin get ya nufa Dr Sofia Na bayanshi ya samu Sucurity ya kalle
ta cikin turanci yace"kuje tare dasu ki sasu su fito da wannan yarinyar ayi waje da ita ,ita kadai
nace kiyiwa haka banda sauran, zan fita ki kula da kowa ,sannan ki duba wannan takkadun da
suke hannunki duk Wanda kikaga ya cancan ci a dauke shi aiki sai ki dauki sunanshi ,ki kirashi
domin kiyi masa intervio"



Cikin jin dadin hukumcin da ya yanke tace" OK za'ayi duk abinda kace,sai kadawo"



Nasir ya shige motarshi ranshi a bace



Dr Sofia ita da Security din suka nufi cikin Asibitin



Suna zaune shiru kowa yana sakawa da kwancewa ,mussaman Malam Ya'u yana tunanin mai
nene mifita a rayuwarsu Suka ji an turo dakin an shi go



Cikin bada Umarni Dr Sofia ta nuna Maryam da hannu tamkar wacce tayi gagarimin laifi cikin
turanci tace "kuyi waje da ita"




Kafin Momy tayi magana tuni sunyi kan Maryam suna zare ido




Momy ta daka musu tsawa tace"kar Wanda ya kuskura ya taba ta wallahi ranku zai baci"



Daya daga cikinsu yace"Madam umarni ne daga oga"



"Ok Umarni ya baku Nasir din cewar kuzo Ku fita damu"?
Duk cikin turanci suke maganar.



Yace"No ita kadai yace mu fita da ita"



"To shikkenan Momy tafada rai

Please Login or Register in order to submit comment