You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya bayan ya aje wasu manya manyan
ledoji



Maryam ta mike ta biyo bayanshi suna tafiya suna hira har ya karaso kusa da motarshi, ya
shiga yana kokarin fita , Mai gadi ya bude get din Nasir motar Nasir ta shigo cikin gidan



Sai ya kashe motar kawai ya fito yana jiranshi Maryam na tsaye a gefanshi kanta a kasa,Sam
bataso ta hada ido da Nasir din




Giss ya bude masa kofa ya fito ,fuskarshi babu yabo ballasa ya mikawa Abdul hannu suka
gaisa



Abdul yace" yanzu nake zan can kada ma"

Fuskarshi ya saki yace" yaushe kadawo ne Alhaji"



"Yau kwana biyu da dawowa wallahi, nazo ganin amarya na"

"Ok andawo lafiya ya aiki"?
Nasir yafada yana binshi da wani kallo jin abinda yace
"Alhmdullhi wallahi komai normal"



Nasir ya zare hannunshi cikin gajiya yace"zan shiga ciki Abdul nima Na gaji ,gashi gobe nake
saran zan wuce america amma bazan dade ba"



"Allah ya kaimu da jirgin safe zaka bi ko na yamma"?

"Na yamma"
Nasir yafada yana kokarin barin gurin

Abdul yace "zan shigo da wuri insha Allahu a kwai alfarmar da nake nema a gurinka"



"Allah ya kaimu lafia"
Yafada yana wucewa Giss ya na take masa baya

Duk wannan abinda yake faruwa Maryam kanta a kasa tana jin duk irin share-sharen da Nasir
yakeyi shi kuma Abdul din sai wani binshi yakeyi lallai ta yadda Farin jini da daukaka a jininsa
take
[31/05/2019 9:17 AM] ®Binta Umar Abbale: Ita yanzu ta daina shiga sabgarsa ma kwata-kwata
sabida ta lura ba karamin dan iska bane



Abdul yayi mata sallama ya wuce ita kuma jiki a sanyaye ta wuce bangarqnsu




Momy na zaune cikin kujera tana kallo kuma tana jiran shigowar Nasir din sabida bayan fitarshi
dazu Alh Salisu yazo ya kare mata rashin mutumci wai itace take zigashi yakeyin duk abinda
yakeyi cikinsu babu Wanda yake gani da gashi ,sabida haka lallai in ya dawo ta ce masa yaje
yana naimanshi ,aura shi da Mubina babu fashi, tunda haka Mahaifinshi yace kafin rasuwarshi.



Momy ranta ya baci domin har kuka sai da tayi tunda take babu mutumin da ya taba tsayawa a
kanta yayi mata cin nutumcin da Alh Salisu yayi mata yau, sabida haka mutukar ita ta haifi Nasir
dole ne ya auri Mubina inyaso daga baya sai ya auri zabinshi.




Yayi Sallama ya shigo Momy ta bishi da kallo har ya karaso kusa da ita ya zauna, ita kanta
tausayinsa takeji ganin yadda girma ya hau kanshi da kananun shekarunshi amma da yake
*Yaron* yana da ilimi cikin nutsuwa yake tafi da komai



Yace"Momy na gaji wallahi"

Cikin tausayi ta kalleshi ,ta kasa cewa komai ma



Sai ya dago kai yana kallonta jin har ya shigo yayi magana Momy bata tanka mashi
Lallai akwai wani Abu



Ya gyara zamanshi sosai yace"Momy menene,? Bafa nasan in ganki cikin damuwa, uhmm
lafiya lau Na fita na barki"




"Myson lafia ba lafiya ba"
Momy tafada tana gyara zama sosai tana fuskartansa



"Tell me"
"Momy fada min ko manene kinji"



"Dazu bayan fitarka Kawunka yazo har cikin falon nan ya karemin zagi sosai wai lallai sai ka
auri diyarshi ,sabida haka mutukar nice Na haifeka dole ne ka aureta domin mu samu kwanciyar
hankali"



Ranshi ya baci mutuka jin abinda Momy take fada masa



Yace"Momy kikace "uncle Salisu yazo gida ya zage ki to akan me"?



"Ga dalili nan na fada maka"
Momy tafada



"Ouk sabida a auri "yarshi yazo har gida ya zageki"
Yafada a zafafe sai huci yakeyi"
"Cam down My son, ban fada maka wannan magana ba fa domin ta daga maka hankali, kuma
bance in kaje kayi mishi rashin kirki ba, ni dai kawai ga umarnin da na baka"




Shiru yayi kawai ya koma ya kwanta hade da rimtse idonsa lallai dole yayiwa tufkar hanci domin
kuwa babu shegan da ya'isa yazo ya runka tadaga mahaifiyarshi hankali wallahi ,sabida a halin
yanzu ita kadai ce ta rage masa
[31/05/2019 9:28 AM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"kayi shiru ba kace komai ba My son don
Allah ka fitar dani kunya, wallahi nagaji da wannan cin mutumci"



Da kyar ya dago kanshi ya zuba mata idonshi wadanda suka sauya kala yace"Momy kinaso in
auri Mubina ko"?



"Inaso mai My son"

"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu zan aureta tunda kinaso"



Momy ta saki fuska sosai tace"Allah yayi maka Albarka My son Ubangiji ya shiga al'amarinka,
yadda kake bina kaima In sha Allahu naka yaran zasu bika"



Mikewa tsaye yayi yace"Momy nagode da addu'a, zan shiga ciki"



"Ba zakaci abinci ba ne"?
Momy ta tambayeshi



Shiru yayi yana Dan murmushi

Itama Murmushin tayi tace"OK zakayi halin naka ko"

Sai ya saki dariya kawai yace" Momy ni tun a motana na cika cikina,in kinason saura in dauko
miki"



"A'a rabani da kayan zaqi nan"
Momy tafada tana tabe baki
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [31/05/2019 4:58 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*100*

Murmushi yayi kawai ya wuce dakinsa, zuciyarsa sai zafi take yi, shi yarasa mai yasa mutane
sukeyin haka, amma dole zai tari Uncle dinsa, ya kiyaye zuwa gurin Momynshi yana bata mata
rai duk abinda ya dameshi yafi mutumci ya tunkareshi da maganar
Amma Sam! Bazai yadda da bacin ran Momynshi ba.




Karfe goma shaura Abdul latif ya shigo gidan yayi parking din motarshi Nasir din ya kira a waya
"hello Abdul din yafada bayan yaji andauki wayar

"Kashigo ne"?
Nasir din ya fada

"Eh kana part dinka ko kana gurin Momy"?

"Kashigo gurin Momy kawai"

"Ok"
Abdul yafada ya kashe wayar



Momy Na zaune cikin kwalliya kamar ko da yaushe, suka gaisa da Abdul cikin sakin fuska tana
tambayarshi mutan gida

"Lafiya kalau Momy"

"To masha Allahu"

Nasir yana zaune kan kujera cin abinci ,hannunshi rike da waya yana latsawa Abdul ya karasa
inda yake ya zauna kujara guda, gami da mika masa hannu
"Ya a kayi ne Alhaji"
Nasir yafada hannushi rike da hannun Abdul din



"Normal Alhaji"
Abdul yafada yana dariya



Yace"ya shirye-shirye"?
"Na kammala sai tafiya kawai"

"OK kasan abinda ya kawoni gurin ka"?

"Sai kafada"
Nasir ya fada yana danna waya



"Zan kawo maka takkadun Maryam ka duba don Allah ka dauke ta aiki a hospital dinka ,kasan a
nan zan barta cikin Estet din mu Na family kafin in kammala ginina ,in kuma nasamu gurin zama
zan dauketa mu tafi tare"



Ba tare da ya kalleshi ba yace"wacece Maryam"?



Abdul ya sha kunu yace"bana son iskanci fa"



Fuskarshi ya hade yace"ban fahimci wace Maryam kake nufi ba,ai shiyasa na tambayeka"

"Ok My wife dina yarinyar gidan nan"
Abdul yafada babu wasa a fuskarshi



Nasir ya dago kanshi yana kallonsa tsawon minti uku bai ce komai ba, ya saki Murmushi gami
da cewa "a yanzu dai bama bukatar ma'aikata, in ma muna bukata to batayi ilimin da zata yi aiki
a wannan asibitin ba"



"Mai kake nufi"?
Abdul yafada rai a bace



"Bana nufin komai"
Yafada hankalinshi Na kan wayarshi



"Look Nasir ka tsaya kayi min maganar da zan fahimta bafa na son wulakancin ka Wanda ka
saba"
Abdul yafada ranshi a mugun bace
Momy ta waiwayo da sauri ganin yadda Abdul din yake daga murya tace"lafiya wai naji kuna
magana Sama-sama"?
[31/05/2019 5:21 PM] ®Binta Umar Abbale: "Momy wai sabida yaron nan bai da kirki nace
masa, ya dauki yarinyar nan aiki a asibitinsa, shine yake fada min magana"



Momy ta kalleshi tana murmushi tace"duk abin ai ba Na zafi bane Abdul wace yarinya kake
magana a kai"



"Momy Maryam nake miki magana fa"



"Ok Dota wai"?

"Eh Momy"?
Abdul ya fada yana mikewa tsaye ranshi a bace



Momy ta kalli Nasir yana zaune har'ila yau hankalinshi na kan wayarshi



Tace"Myson Dan Allah ina Neman alfarma nima ka dauketa aiki,wai maiye duniyar ne ,tunda dai
Abdul din ya amince tayi ai shikkenan , Wanda ya taimaki wani shima Allah zai tai makeshi"



"Momy ki rabu dashi don Allah kar Allah yasa ya dauketa zan cigaba da nema mata"



"A'a duk baza ayi haka ba , ka koma ka zauna mu kashe magana"
Momy tafada tana kallon Abdul din

A gogo ya kalla yace"Momy wucewa zanyi wallahi banason abin bacin rai , zamu iya rigima
dashi yanzu"



Cikin mamaki Momy tace"akan mace zakuyi rigima da Dan uwanka Abdul"?



Kunya ta kamashi sai ya sunkuyar da kanshi kawai



Momy tace"koma ka zauna"
Ya koma ya zauna kawai gami da dauke kanshi yaki yadda ya kalli Nasir din

Shi kuwa babu abinda ya dameshi



Momy tace"Myson "mai kace a kan maganar"?



Tafi minti biyu kafin yayi magana, daga bisani yace"Momy ni a yanzu bani da lokaci amma zata
iya zuwa gurin Dr Sofia tayi mata intervio shikkenan sai ta ajeta a matsayin da ya dace"




"To ai babu matsala sai taje din"
Momy tafada,ta cigaba da cewa kai Abdul kaji abinda yace"



"Momy babu komai ai sai taje tunda naima takeyi,Allah ya rufa asiri"



"Ameen ameen"
Momy tafada ta cigaba da cewa dan Allah kar Ku yadda wata mace ta farraqa tsakaninku kunji
ko"



"Momy kar kidamu insha'Allah"
Abdul din yafada yana mikewa da niyyar tafiya yayiwa Momy sallama




Bayan fitarshi Momy tace"don Allah my son ka rage girman kan nan gami da izza domin babu
inda zata kai ka"




Dariya yayi sosai har sai da habarshi ta lo6a yana kallon Momy din yace" Momy yaya ake
girman kai don Allah mutane da dama suna fadin haka a gareni , basu San cewar ni haka
nuture dina ne ba"
"E ai duk da haka my son kana karawa da wani ni dai nace ka daina"



"Insha Allahu Momy kiyi min addu'a"



Momy ta zauna suka cigaba da hira cikin so da kaunar juna.
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [01/06/2019 5:11 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*101*
Nasir bai tafi America ba sai da yaje gurin kawunshi Salisu, sabida yadda yaga Hankalin Momy
shi ya tashi a kan al'amari, nan uncle Salisu ya rika kwantar da kanshi yana rarrashinsa, da yayi
hakuri ya auri Mubina, Nasir yayi mamaki ganin yadda yake kwantar masa da kai sai kawai ya
basar , yace" magana ta wuce amma don Allah kar ka kara tayarmin da hankalin Momy domin
abinda kayi mata ya daga mata hankali, zan wuce america, sati biyu zanyi zan dawo in yaso sai
muyi maganar, Abin mamaki Dadyn Mubina ya dinga washe baki yana shi wa Nasir albarka nan
Nasir ya tafi ya barshi sai mamakinshi yake,lallai mutane basu da kirki, wato in kana da kudi
komai kafada dai-dai ne ,shi kanshi yasan ba don Allah uncle din nashi yakeso ya hadashi aure
da diyarshi ba.



****
Yau satin daya da tafiyar Nasir ,Abdul ma ya tafi bayan ya kammala komai na maganar aure
rana kawai ake jira,cikin so da kaunar juna sukayi sallama da Maryam.



Momy kadaici duk ya dameta sai ta fito harbar gidan ta zauna kan kujera kawai nan su Nafi'u
suke zama da'ita suna hira Maryam ma sai ta samu gurin zuwa , siyi ta hira cikin fahimta




Ranar Momy ta tashi ta shiga ciki sai ta bar wayarta kan kujera Maryam na zaune suna chating
da Abdul sai Murmushi takeyi kawai da'alama hirar tana mata dadi



Wayar Momy tafara kara da sauri ta kalli fuskar wayar, Myson ta gani yana yawo a fuskar
wayar.



Gabanta ya fadi tayi kamar ta dauka wata zuciyar tace kar ki dauka, wayar ta katse kafin ta
farga wani kiran ya kara shigowa,
Sai da takusa katsewa sannan ta daga batare da tace uffan ba



Ajiyar zuciya taji yana saukewa kafin taji wani irin voice da ya kusa sumar da ita a zaune
Momynahhh"
Taji ya fada yana ajiye numfashi




Shiru babu magana

"Please Momy kiyi min magana mana yinin yau banji muryarki ba ayyuka sun dame ni"



Maryam tana ta kokawa da zuciyarta, jikinta yayi bala'in daukar dumi domin Nasir ya gama
kashe mata gangar jiki, gaskiya tana bala'in kaunar Nasir




"Momy"
Maryam taji yafada da ainihin muryarsa ,sai taji kamar ma acikin damuwa yake

Sai tayi saurin kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya daki-dai
[01/06/2019 5:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Momy ta dawo gurin, ta kalli Maryam dake zaune
tace"Dota na barki ke kadai ko"



Maryam tayi murmushi tace"A'a Momy chating nakeyi ma"




Wani kiran ne ya kara shigowa wayar Momy a karo na uku



Momy tayi saurin daukar wayar tana dariya



Tace"Myson yau nayi fushi ,nayi ta tsammanin kiranka tun da safe naji shiru nace Allah yasa
lafiya"



Ajiyar zuciya ya sauke yace"Momy ina ta magana shine kika shareni ko"
Cikin mamaki tace"yaushe akayi haka, My son"?



"Yanzu Momy na kira sau biyu ina ta magana naji shiru"



Momy tayi murmushi tana kallon Maryam tace"ba nice na daga wayar ba Myson Dota ce wallahi
ni Na shiga cikin gida"



Shiru yayi na minti biyu sannan yace"Momy mun gama magana da uncle ,in nadawo za mu
tsayar da magana ina fatan haka yayi miki"



"Yayi dai-dai Allah yayi maka albarka"



"Ameen ameen Momyna"

Sukayi shira sama-sama sannan yayi mata sallama dama a cikin busy yake yanzu ma free ya
samu shiyasa ya kirata sabida duk abinda yakeyi hankalinshi na kanta.




Bayan Momy ta aje waya ta kalli Maryam cikin murmushi tace"Dota Son'ya kira waya kinki
magana mai yasa"?




Maryam tayi murmushi tana tunanin abinda zata ce ,da kyar dai tace "Momy kafin inyi magana
ya kashe wayar shiyasa"



Dariya tayi tace"ina fatan dai kinje anyi miki intarvio kamar yadda ya fada"



"Momy ban je ba"



"Mai yasa Dota"

Shiru tayi kanta a kasa domin tun lokacin da Abdul ya fada mata ga yadda sukayi da Nasir wai
lallai taje asibitinsa gurin wannan matar da ta tsana taji kwata-kwata aikin ya fice mata a rai
sabida in har Sofia ce zata mata intervio sai dai ta hakura da aikin




Momy tace"ban sanki da haka ba Dota kije kinji ko tunda dai yace ki je babu matsala"




"Shikkenan Momy zanje insha Allahu gobe"



"Yawwa Dota Allah yayi miki albarka, kema na kusa yin missing dinki ko"?




Maryam ta rufe fuskarta da gyale tana murmushi



Momy ta rinka dariya tace"ke kam kin fiye kunya wallahi"



Da sauri Maryam ta mike ta bar gurin fuskarta a rufe




Momy ta bita da kallo tana dariya kawai tana girgiza kai Yarinyar tana burgeta sosai
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [01/06/2019 6:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*102*

Lokaci yana ta matsowa Malam Ya'u yayi shirye-shiryensa aunty ma ba'a barta a baya ba tana
ta gyara "yar ta Maryam kuwa ganin lokaci ya matso jikinta duk yayi sanyi komai take kokari
takeyi soyyayar Nasir tanata sasakar zuciyarta tarasa yadda zatayi da komai bata jin dadinshi,
saura kwana uku daurin aure Nasir ya dawo gada america, Momy ta rinka murna tare suka
shirya masa abinci mai rai da lafiya ita da Maryam, shiyasa suna kammalawa Maryam ta gudu
sabida Sam! Bata so yazo ya tadda ta ya ci mata mutumci

Momy ta rinka shi mata albarka

Wanka tayi ta kimtsa jikinta domin sunyi waya da Abdul yace gashi nan zuwa
Shi kuwa Nasir yana zaune Momy ta tisa shi a gaba tana lallabashi lallai sai yaci abinci shi
kuma yana botsarewa



Momy ta kalleshi tana shan kunu tace" yanzu zamuyi fada dakai wallahi dube ka fa duk ka yi
Dan wuya nasan baka cin abincin kirki ko a can sai ciye-ciyen da kasa ba"



Shagwaba yake mata sosai kamar wani yaro kankani

Ita ko kamar ta bashi abincin a baki haka takeji sabida yadda taga duk yayi rama sati biyu kacal
shiyasa kwata-kwata bata kaunar taga yayi wata dugowar tafiya



Sai da yagama sangartarshi sannan ya fara cin abincin



Momy tace"ni har fargabar kayi aure nake sabida ban San matar taka ko zata tsaya ta kula da
kai ba"



Murmushi kawai yake mata yana kara jin so da kaunarta cikin zuciyarsa



Bayan ya kammala ya goge bakinshi , ya maida hankalinshi kanta yace"Momy a wannan satin
zan fitar da zakka, zanje can birnin kudu zanyi musu a can"



"Masha Allah my Son Allah ya kara albarka"



"Ameen Momy"
Nasir yafada yana mikewa yace"zanje inyi Wanka in kwanta in huta Momy"



Momy tace "Allah ya huce gajiya sai ka fito"



Dakinshi ya nufa komai tsaf-tsaf dashi sai qamshin turaran wuta yakeyi sai ya zube tarkacan
dake hannunshi ya nufi toilet domin ya Dan watsa ruwa ko jikinshi ya warware dama wayoyinshi
duk ya kashesu sabida yasan yanzu, za'aita damunshi a hanashi hutawa da Abbas kawai
sukayi waya
Bayan ya fito ya sanye wando 3Q sai kawai ya kwanta kan bed dinshi yayi rigin gine gami da
dafe kanshi da duk hannunwanshi, shi kadai yasan abinda yake damun zuciyarsa
[01/06/2019 7:30 PM] ®Binta Umar Abbale: Kullum abin kara kaimi yakeyi mutukar zai kwanta
bacci babu dare babu rana sai yayi wannan masifaffaen mafarki wai gashi yana yin sex da
yarinyar da yai wa muguwar tsana a rayuwarshi.



In ya farka kuka ne kawai baya yi sabida tsabar bakin ciki da bacin rai jikinshi kaca-kaca yake
tashi dole komai dare yaje yayi Wanka ko da yaje america ma bata canza zani ba, sabida abin
ma ya kara qaimi sabida yadda"yan matanshi na can suka matsa masa kullum sai sunzo sun
dameshi, sai tayi da gaske yake tsallake kai dinsu domin yayi alkawari bazai kara kusantar zina
ba ,shima romance din da yakeyi so yake Allah ya yaye masa




Da kyar bacci ya dauke shi mai dauke mafarkai kamar ko da yaushe yau ma haka ya tashi
jikinshi kaca-kaca yayi ta jan tsaki dole ya sake wani wankan ya fito yanajin nauyin jikinshi
sabida baccin magariba dama haka yake sawa jikin mutum duk ya mace



Momy ya samu zaune a farlo bayan yadawo daga sallah magariba sai kawai ya zube gabanta
yana rike cikinshi




Momy tace "Lafiya My son"



"Momy marana ta dameni da ciwa wallahi"
Yafada yana rimtse idonsa



Kallonsa Momy tayi tana nazarinshi kadan ta dauke fuskarta tace" mai ya jawo maka ciwon
Mara"?



"Momy ban sani ba nima"
Yafada yana kokarin bagarar da maganar
Momy tace"shiyasa banaso kake shaye-shayen kayan zaqin nan mybe sune suke haddasa
maka ciwon"
Momy tafada tana kauda kanta sabida ta Riga ta gama fahimtar abinda yake damunshi.
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [02/06/2019 6:54 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*103*

Shima bai sake cewa komai ba, kawai sai ya lumshe idonshi gami gyara kwanciya kan kujera
Momy ta rika satar kallonshi tana nazarinshi, dole ne ta matsa masa yayi aure ,sabida duk ta
gama fahimtar abinda yake damunshi, ta sauke ajiyar zuciya kana tace"Myson " bude idonshi
yayi ya zuba mata su, tace"Yaushe kuka tsayar da maganar daurin auran"?
Zakudawa yayi yana ciccije bakinshi yace"zamuyi waya in anjima" Momy tace"mai zai hana a
hada dana Abdul, nan da sati biyu masu zuwa" gabanshi ne ya fadi jin abinda Momy tace,
amma sai ya gwada mata halin nashi



Yace"Momy waye Abdul kuma"

Girgiza kai kawai tayi sabida ta San halin kayanta



"Abdul latif na kawunka Muktar"

Yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi

"Kayi shiru baka ce komai ba"

"Wane date ne"?

"Ai lokaci yayi nan da sati biyu masu zuwa"

Gabanshi ya rika wani irin bugawa fat!fat!fat , ta tabbata kenan Abdul zai auri ta batare da ya
kawar da wannan muguwar sha'awar tata dake damunsa ba

Jikinshi yayi bala'in sanyi sosai da sosai

Yace"shikkenan Momy Allah ya nuna mana sai ayi yanda kikace"



"Allah yayi maka albarka,My son"
Momy tafada
"Ameen ameen Momy"

"Yanzu wane shirye-shirye kakeyi, yau tilas kaje gurin Mubina ku gaisa"



"To Momy za'ayi"
Yafada idansa a lumshe



Momy taga duk yayi sanyi tace" naga jikinka yayi sanyi My son ko Na takura maka ne"?



"A'a Momy ina da damuwa ne"



Ita ma jikinta tayi sanyi Yaron ta yana cikin damuwa lallai itama tana cikinta




"Kafadi min abinda duk yake damunka"?
Momy tafada babu alamun wasa a tartare da ita,gaba daya ta maida hankalinta kanshi



Shiru yayi yana da wurwurar abin cikin zuciyarsa yana jin ya fada mata ko kar ya fada mata.




Momy ta kara maimai tamasa tambayarta.



A jiyar zuciya ya sauke gami da bude idonshi sannan ya gyara zamanshi yana kallonta
yace"Momy wani mafarki nakeyi Wanda yake damun zuciyata kuma ba da kowa nakeyi ba sai
da wannan yarinyar ta cikin gidan nan, shiyasa nace miki mayu ne, kinki yadda Momy yarinyar
ta rike wuta a kaina kullum sai tazo cikin bacci Na ta takura min babu dare babu rana Momy ina
cikin musiba"
Ya karashe maganar gwanin tausayi, domin shi abin ma tsoro yake bashi
[02/06/2019 9:11 AM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"wane irin mafarki ne wannan My son"?



Shiru yayi

"Tambayarka nake fa"
"Momy mubar maganar"

"Naqi bari"
Momy tafada kai tsaye idanta tsaye a kanshi



Murmushi yake shima ya zuba ma ido

Momy tsaf ta fahimci abinda yake damunsa

Tace"My son fitinar ka yawa gareta,Allah ya rufa asiri"

Dariya ce ta subuce masa ya dinga yi



Momy itama dariya take tana girgiza kai

Yace"yau hutawa zanyi Momy babu inda zani"



"Gwara ka huta ai,amma dai dole da yamma kaje gurin Mubina ko"



"Eh Momy yanzu ma sabida ita na kashe wayana sabida tun ina jirgi take takuramin"



Dariya Momy tayi tace"soyayarku a ta mussaman ce"



"Wane irin ta mussaman Momy nifa Sam bata yi min ba wallahi Dan dai kawai Na faranta miki
rai ne"



"Nima nasani Myson yarinyar tarbiya bata isheta ba ,amma in dai tana sonka zaka iya juyata
kayi mata tarbiya"




Tabe baki yayi yace"wani babban abin haushi ma ,Hanifa kanwarta tana tan tana tada
hankalinta sai faman shirme take min a waya wai yaya zanyi mata haka"



"Wace Hanifa kake magana"
Momy tafada cikin mamaki



"Kanwarta, itama wai sona take Mtsss



Momy tayi dariya tace"to Allah ya sawaqe,Allah ya kawomu wani zamani ni "yasu"




"Momy shashanci ne da iskanci kawai babu maganar zamani anan"

"Allah ya kyauta"
Momy tafada

Nan dai suka zauna hira sama -sama har wajejan sha biyu Na dare ,sannan Momy tace yaje ya
kwanta



Yana shiga dakinshi ya kunna wayoyinshi nan da nan sakkoni suka rika shigowa, ko sauraron
wayar baiyi ba sai da yayi Wanka yayi shirin bacci sannan ya fara duba sakkonin



Message din Mubina sun fi goma tsaki ya ja yafara duba sakkonin mutanenshi, wayarshi tafara
kara sunan Mubina yana yawo kan fuskar wayar

Kin dagawa yayi har ta katse , ta kara kira a karo na biyu nan ma saura kiris ta katse ya daga
batare da yace komai ba.
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [03/06/2019 1:18 PM] ®Binta Umar Abbale: [03/06/2019
9:22 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*104*

Mubina kamar ta fashe da kuka tace"Yanzu Nasir ni kake wulakantawa, nafi sati daya ina
kiranka a waya Dan wulakanci kaki dagawa sai yanzu ka gadama"
Tsaki yaja yace"kinga Malam karki dameni, tunda dai na amince shikkenan kuma mai kikeso
nayi miki ku so kike in aje aiki in tsaya dan kin kira waya ina sauraron shirme da shiri ririta, karki
kara yimin makamanciyar magana irin wannan ya karashe maganar yana Jan tsaki a karo na
biyu



Jikinta ne yayi sanyi sosai dama tasan za'ayi haka dashi

Itama sai tau fada tace" kasan bazan jure wannan rashin mutumcin naka ba wallahi
[03/06/2019 1:17 PM] ®Binta Umar Abbale: Kashe wayar yayi kawai bai tsaya sauraronta ba
zuciyarsa sai zafi takeyi ,sakkonin yake dudduba wani kiran ya kara shigowa wannan baby ce
katse kiran yayi nan ma ya cigaba da abinda yakeyi , sai da yaga duba sakkonin sannan ya kira
Sofia a waya cikin turanci suke magana, nan ya ke tambayarta yaya aiki dafatan komai babu
matsala.
Basu jima suna magana ya kashe waya,



Ya dade kafin bacci ya dauke shi, biyar saura Na asubah ya tashi har an idar da sallahr asubah
duk jikinshi a mace yakeyin komai, tun jiya da Momy tafada mishi labarin auran Abdul da
Yarinyar jikinshi yayi sanyi nan falo ya zauna yana Jan carbi Momy na sama bata sakko ba Har
bacci ya dauke shi bacci mai tartare da damuwa da wahala gami da gajiya




Momy ta sakko kamar ko daushe cikin kwalliya, ta tsaya suna magana da Uwani mai aiki,
Uwani tace" naga uban gidana yana bacci a farlo ,Momy ta cikin sauri ta juya tana kallon farlon
Nasir ta hango kwance cikin kujera bacci yake sosai da sosai




Wani irin tausayinsa ne ya kama Momy sai ta zauna kusa da kafafunsa tana kallonsa cikin
tausayi da kauna irin ta uwa da danta , shi kam bai San ma abinda yake faruwa bacci mai nauyi
ne ya daukeshi.
[03/06/2019 2:21 PM] ®Binta Umar Abbale: Sai wajan karfe tara da rabi ya tashi , yana bude
idonshi ya saukesu kan Momy, cikin mamaki ya mike zaune yana mika ya kalleta gami da cewa
"Momy bacci nayi anan"?




"Bacci kayi sosai Myson" Momy tafada tana kallonshi



Agogon hannunshi ya kalla yana mamakin yaya Akayi bacci ya daukeshi a nan batare da ya
shirya ba




"Momy bari in yi wanka " yafada yana mikewa
"Sai ka fito My son"



"Ok Momyna"



Cikin sauri ya kammala komai ya fito ,Momy tace"kazo ka karya yau nasa Uwani tayi maka
kunun gyada gashinan yaji madara"




"Ok Momy"
Kai tsaye daining din ya nufa Momy ts hada mishi yaji madara sosai tace"ko in zuba maka
abinci ne"?



"A'a Momy kunun ma ya isa"

"Kadaure kaci ko yaya ne"

"Momy wannan ma ya'isa kinsan yanayin cikina yanzu sai ya rikice



"Amma dai yau karkayi ciye-ciyen kayan zaqin nan don Allah"
Momy tafada gwanin tausayi



Dariya yake yace"insha Allah Momyna"

Mikewa yayi yana gyara links din hannunsa, yace"zan wuce Momy amma kafin in tafi zan shiga
asibitin in ga abinda yake faruwa"




Momy tace"to Allah ya kiyaye hanya a gaida "yan uwa da abokan arziqi, har waje ta rakoshi
Giss yana tsaye yana jiran fitowarsa,



Yayi sauri ya karbi wata karamar dake hannun Nasir din , ya bi bayanshi inda motarshi take
Momy sai addu'a take ta zabga masa , Tony ya bude masa motar ya shiga da Sauri ya rufe ya
zagaya ya bude mazauninshi ya zauna gami da kunna mota suka fice daga gidan
Maryam ce take bin titi a nutse tana sanye cikin atamfa riga da zani mai kalar ja tayi amfani da
mayafi kalar atamfar, takalmin dake sanye a kafarta mai tsine ne sosai sabida haka a nutse take
tafiya, Maryam najin takaicin tafiyar nan sabida kafin ta fita babban titi akwai tafiya , sosai
yawanci dama duk da motoci suke fita in ba lalura ba babu Wanda zaka gani yana tafiya da
kafa cikin Estet din tunda guri ne Na wane da wane, so take ta fita babban titi domin ta samu
Napep , tayiwa Momy Alkwari zataje yau hospital din, amma in taga da wulakanci bazata jura
ba
[06/06, 01:51] +234

Please Login or Register in order to submit comment