You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ruqa
bawa dady hakuri yana tausar zuciyarsa ganin yadda ya hasala,sai fada yakeyi.



Nasir na tsaye kanshi ,a kasa yayin da ya zube hannunwanshi cikin aljihun wandan dake jikinshi
3 qutar ,ranshi yana masa zafi mutuka ,tunda yake da dadynshi bai taba fudda hannu ya
mareshi ba tun korociyarshi,kawo wa girmanshi, amma yau in baiyi qarya ba, yau ya mareshi
sau uku a kan yarinyar da bai San asalinta ba,



Fuskarshi a murtuke ya ke kallon dady dake ta balbala masa fada,yace"dady ,kasan bana karya
,bana boye abinda yake zuciyata, nace kar ka kulla wannan lamari ,ok kai ne a ciki ,duk abinda
ya biyo baya kar ka tambaye ni yana gama fada yayi nufin barin dakin ranshi a mugun bace.




Dady ya bishi yana zagi,yace "duk abinda zakayi kaje kayi,aure kai da Maryam babu fashi,na
fada maka,idan andaura auran ka kasheta ,kagani in ban sa an kasheka ba kai ma, zanga
abinda kake taqama dashi,ka lalata yarinya ,daga baya ka kawowa mutane maganar
banz.....kuka Maryam ne ya katsewa dady Fadanshi,ya waigo a fusace,gami da cewa"Maryam
in dai ina raye bazaki wulakanta, zan cika Alkawarin da na daukarwa mahaifinki tun bakizo
duniya ba




Da rarrafe ta karasa kusa da dady din ta ruqumqume kakafunshi tana gursheken kuka,
tace"dady please ka janye wannan maganar da kafada a kai na da Uncle, dady ka dai na
zaginshi kana ai batashi, dady uncle yafi mu gaskiya, fa tun da yace bayaso kar kayi masa dole"
Ya buga mata tsawa gami da cewa"rufe min baki shashashar yarinya ,kawai ,kema tsoro yake
baki,ya cuceki ,kina rufa masa asiri,baxan janye ba,duk abinda zakuyi kuyi,kinji na fada miki"

Maryam na kuka tana rokan dady a kan irin zagin Nasir din da yakeyi ,tace"dady Uncle bai yi
min komai ba asali ma yaje taimakona ne, lokacin da wannan can yayi nufin cutar dani a
motarshi,tafadi maganar tana nuna Anwar da hannunta .



Dady ya buga mata tsawa a karo na biyu yace" ki kiyaye ni nafada miki ,ni zaki fadama halinshi,
Anwar bazai yi masa sharri ba, sabida yasan halinshi,idan kema zaki bijeremin kamar yadda
yayi min shikkenan,nasan dai tarbiyarki ba irin tashi bace,



Tausayi dady ya lullube ta sosai tace"dady kayi hakuri bazan bijirewa umarninka ba,Amma ina
rokan alfarma ka janye maganar hadamu da Ancle nayi maka,alkwarin yi maka biyyaya ga duk
namijin da kazaba min ,amma ba Nasir ba.



Dady yaji babu dadi da jin furucin Maryam zuciyarshi tace"wata kila itama yarinyar tana gudun
mugun halin danka ne,shiyasa take kuka,kar ka shiga hakkinta,
Jiki a sanyaye ya kalleta yace"ok naji maganarki Maryam, kiyi shiru kin jiko bazan cutar da ke
ba domin jin ki nake tamkar yar da na haifa a jikina, kiyi min alfarmar auran Nasir kinji ko,
zuciyata tana bani a kwai alkairi a auranku sosai,kece zaki zama silar kintsuwarshi"
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*



*70*



Maryam ta mike tsaye tana share hawaye ,tace"dady kai ne zaka dinga yi masa addu'a dady ka
dai na yi masa mugun baki,domin bakinka yana da dafi a gareshi , kasan shiriya ta Allah ce"



'To
Maryama na dai na, kinji dama duk a kanki ne,abinda nakeso dake shine kifadamin gaskiyar
abinda ya afku a tsakaninku dashi,shin maganar da Abokinshi yafada haka take a kanki"?



Maryam bata iya karya ba,nan ta zayyanewa dady komai tun lokacin da tafito daga gida ,da
yunkurin cutar da ita da Nasir din yayi Allah ya taimaketa ta gudo,ta kare maganar da
cewa,amma Sam baiyi min fyade ba kamar yadda kake nufi dady"




Dady yace"na yadda da duk abinda kikace Maryam domin ba kya karya ke sabida haka na
janye maganar da nafada a kanki,ke da Nasir din ,bazan miki dole ba,kwanaki Abdul latif yaron
kanina yazo min damaganar yana son ya aure ki ,nace ya bari in sanarwa da mahaifinki
tukkuna ,Na lura dama ke dashi kuna shiri ko?




Maryam ta sunkuyar da kanta cikim jin kunya. Ta daga kai alamun haka ne dady yayi murmushi
yace"To masha Allah ,Allah ya nuna mana,ke kuma Allah yayi miki albarka"




Anwar ji yake tamkar ya kashe dady sabida tsabar bakinci ki yana iko da abinda banasa ba, ai
yarinyar ba"yarsa bace ,ba "yar waninsa ba ,da zai riqa yanke hukumci a kanta,Abdul din banza
da hofi,ko Nasir ne ya aureta ba yajin zai iya hakura batare da ya kashe ,shiryawar dake
damunsa ba
Ya zakuda ,yanawa dady wani irin kallo na raini,yace "haba! Dady wannan ba girmanka
bane,eh!! Yawa!! Fa kakeyi kakyale yarinya ta mori kuruciyarta,kai tsaye zakace zakayi mata
aure, gaskiya in hakane nine yafi dacewa in aureta ,sabida Nina fi Kowa sanin ta sabida haka
ka cire hannunka daga kanta ,tunda dai ba "yarka bace!

Cikin rashin kunya da rashin mutumchin da suka saba Anwar yakewa dady magana



Dady mamaki ya kasheshi yakasa furta komai ,Lallai dama hausawa sunce naka shike ba da
kai,yanzu inda Nasir na ganin girmanshi ,ai Anwar bazai sami kafar zaginshi ba, ranshi yayi
mugun baci,bai ce komai ba ya nufi hanyar fita daga dakin
Babu zato Anwar yaji saukar mari! A kuncinshi, Maryam ce
Sai huci! Take dama a kufule take dashi.

Ya dago kanshi ,cikin sauri yana mamakin ta ,idonta masu kama dana mage ta zuba masa tana
watsa masa wani mutsiyacin kallo.
Tace "ko da maza sun kare a duniya bazan taba auranka ba ,Dan iska macuci azzalimi ,ba
gwaramin Uncle din sau dubu ba a kanka, to bari kaji ,abinda bakasani ba dady yana da iko
dani ,ba kamar yadda kake zato ba, duk abinda ya zartar a kaina da ni da iyayena,daidai ne
sabida haka ,duk abinda ya umarce ni dashi ,shi zanyi,tana gama fadin haka,ta sakai ta bi
bayan dady din.




Anwar ko ya jima hannunshi dafe da kuncinshi ,yagaza tabuka komai ,tunani yakeyi ya'akayi har
ya tsaya yarinyar nan ta mareshi,lallai ta tarowa kanta bala'insa da sharrinsa sai ya kulla mata!!
Sai ta gwamace ba'a haife ta ba.




Babu motar Nasir a gurin tuntuni yayi tafiyarshi, sabida haka Nura drevar yana ganin fitowar
dady ,yayi sauri yaje ya bude masa mota ya shiga ,yana jin wani Bacin rai a jikinshi,yayi sanyi
da'alama hawan jininshi ne yakeso ya tashi Maryam ta shiga bayan motar itama dady yabawa
Nura umarnin tafiya,Nura yace",rankaya dade zan kai office ne"?



"Aa Nura muje gida kawai nafasa zuwa ,bana jin dadin jikina,baya gahaka ma lokaci ya
kure,mubarwa gobe, kawai"
Nura ya ja motar suka bar gurin yana mamakin abinda ya canja dady ,yanzu yanzu sabida ya
lura dashi ranshi a bace yake,



Maryam ma haka, sai ta rika bashi hakuri, tamkar ta fashe da kuka.



Yace"nayi hakuri Maryama karkiyi kuka kinji ko,muje gida ,ki huta ,Allah zai sakamiki duk
Wanda ya cuceiki




Maryam tafashe da kukan da take boyewa tace"Dady nifa nayafewa Uncle sabida dama babu
abinda yayi min Uncle ba ya taba laifi a gurina, don Allah ka daina fadar haka,komai ya wuce ka
kwantar da hankalinka"
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*



*71*



Haka suka sauka gida Maryam na tausar zuciyar dadi,da kalamai masu sanyi,ya riqa shi mata
albarka, Nura nayin parking ya fito da sauri yazo ya bude masa kofa ,dady ya yunkura ya fito
yanajin wata hajijiya a kanshi,kan kace kwabo ya yanke jiki yafadi a gurin ,yana fidda numfashi
sama sama,Malam Ya'u dake kokarin mayar da get ya rufe ya tawo da sauri,yana fadin
subahannallahi Alh" ya karaso gurin suka kama dady shida Nura ,suka shiga dashi gida,bai San
inda kansa yake ba,Maryam ko sai kuka takeyi sosai



*innalillahi wa'inna ilayi rajiun*
Shine abinda Malam Ya'u yake ta nanatawa ,sai gumi ne yake karyo masa
Momy na zaune cikin kujera tana duba wani littafi ,taga an shigo mata da dady ranga ranga,
hankalinta ya tashi ,ta mike da sauri,har littafin yana faduwa,kan fisu karaso ta karasa
,tace"Nura lafiya mai yasameshi,lafiya lau ya fita fa"



Nura yace"wallahi Hajiya kalau muka fita dashi kamar yadda kika fada sai yanzu kuma naga ya
fito daga asibitin da muka akai Anwar abokin Nasir hankalinshi a tashe"

Cikin gigita Momy tace"mai yasami Anwar din ,ina My Son ,ta na nufin Nasir,

Nan Nura ya warware mata komai da abinda yafaru,Momy ta fashe da kuka ,tana kallon
Maryam tace "yanzu da abinda zaku saka mana dashi kenan Malam Ya'u, yarinyar ka ta zame
mana annoba, yanzu a kwai abinda dady zai nema a gurinki ki kasa yi masa"



Malam Ya'u ya diri-ririce sabida bai fuskanci inda maganar tata ta dosa ba,yace Hajiya ban
fahimci maganarki ba"



Momy na kokarin hawa sama cikin tashin hankali tace"ai baza ka fahimci komai ba Malam Ya'u
mungode da wannan Abu"



Dady yana ta kokarin magana ya kasa sabida yadda bakinsa ya harde maganar bata fita sosai ,
Maryam takarasa kusa dashi tana kuka wai ko zataji mai yake cewa,duk da haka bata fahimchi
komai daga abinda yake fada ba.



Tana kuka ta rirruqe masa kafafu tace"dady ka yafemin in nice na bata maka rai ,wallahi zanyi
maka biyayya dai dai gwargwado,

Nan Malam Ya'u ya fahimchi Wato Maryam din ce dalilin bacin ran sa, bai yi wata-wata ba ya
gaura mata mari! Yace "wato kece kika haddasa masa tashin ciwonsa ko, abinda tun kafin kizo
duniya bai tashi ba,sai yanzu ta dalilinki ,mai kikayi masa wanda yasa ranshi ya baci wane
umarni ya baki ,da kika kasa bi,kin cika butulo Maryam ,mutumin da ya hana kowa fita nemanki
yace,shi zai je ,shine zaki saka masa da haka!



Maryam kuka take kamar ranta zai fita tanabawa Mahaifinta hakuri,shiko sai faman fada yake
Mata,tun da take dashi ,bai taba dukanta ba,ballantana ya yi mata fada,sai yau"

Cikin tsawa yace"kifadamin mai nene dalilin da ya haddasa masa wannan tashin hankalin"?
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*

*72*



Kafin Maryam tace komai Momy ta sauko daga sama hannunta ruqe da kwalayen magungunan
dady,ta mikawa Nura, tace bude ka bashi ko kallon inda Malam Ya'u yake ba tayi ba,taje ta
dauki wayarta ,tana neman number Nasir,hankalinta a tashe,



Fitowarshi kenan daga toilet ,ya ga kiran Mom din kin daga wayar yayi har ta katse wani kiran
ya kara shigowa nan ma yaqi dagawa sabida yasan dady ya fada mata duk abinda ya faru,a
tunaninshi ,za tayi masa fada ne,



A takaice dai sai da momy ta kira sau kusan biyar sannan ya daga wayar kafin yace komai
tace"ka kyaura Son" kaji ko wato ni zaka ki dagawa waya ,ko babu laifi, ina so duk inda kake
kazo yanzu,dadynka babu lafiya ciwonshi ya tashi,gashi nan bai San wanda yake kanshi ba"
Dama abinda nake ta gudu kenan"



Gabanshi ya fadi,! Amma sai ya share yace"mom kin manta ya kore ni a gidanshi ne,banaso
inzo wani Abu ya faru ni dashi,sabida dama dazu ba rabuwar kirki mukayi ni dashi ba"




Momy ta sanya kuka tace"wato har yanzu kanaan kan vakanka ko My Son,sai kace bakasan
halinshi ba,da fifita bare a kan nashi kayi hakuri kazo kaji ko"
"Owk Momy ki dai na kuka dan Allah ganinan zuwa kinji kar inzo kina kuka,yaya jikin nashi"?




"Yananan bai San wanda yake kansa ba kasan dama in ciwon nashi ya tashi haka yake masa"



Nasir ya kashe waya cikin sauri ya saka ,kayanshi ya fito ya shiga motarshi,bai nemi rakiyar su
Joy ba shi kadai ya tafi ,yana bala'in kaunar mahaifinshi sosai kawai halinshi ne ba ya so ,dady
n nashi fadanshi yayi yawa gami da shiga abinda babu ruwanshi shiyasa ,suke yawaita fada
dashi,



Masu tsaron gurin ne suka bude mass get din ya shiga yayi parking gurin a je motoci, ya fito
,yana amsa gaisuwarsu ,sama-sama ya shige ciki.




Dady ya gani kwance kashir6an kamar baya numfashi, duk sunyi tsaye a kanshi,yay in da
Maryam take gurfane kusa da kafa fun shi,ta rirruqe masa kafafau tana kuka,



Hankalinshi ya tashi ,da sauri ya karasa gurin,ya fincike Maryam din ya wurgar da ita gefe guda.
Yana zaginta da turanci yace"idan so kike ki kashe shi ai ba ta wannan hanyar ba ,sabida kowa
zai gane ki, Ke mayya ce,ubanki ne shi da zakizo ki rirriqe shi,ko kina da alaqa dashi,wallahi
duk maytarku kurwar dady daci gareta"!!
Maryam na kuka ta kara komawa kusa da dady domin Sam bata fahimci abinda Nasir din yake
nufi ba burinta kawai taga dady ya mike ,yana magana tafada masa cewar ta 'amince da auran
Nasir din,domin duk a ganinta ,ita ce dalilin da ta haddasawa dady tashin ciwonsa




Dady yana kallon Nasir yana motsa baki ,sabida tun lokacin da yaji muryarshi ya bude ido,
yanaso ya fada mashi ya dai na zaginta




Malam Ya'u kam hankalinshi ya tashi jin furucin Nasir din a kan Maryam shifa duk sunbi sun
rikitashi ya kasa fahimtar komai



Nasir ya kamo kafadun dadyn nashi idonshi jazir sai sauke ajiyar zuciya yakeyi ,ya sanya gefan
rigarshi yana goge masa gumi, ya kalli Nura wanda ke tsaye riqe da kwalayen magani,yace
"dauko min fresh milk a frij"

Da sauri Nura ya tafi,yaje ya dauko. Nasir ya balle Murfin ,ya fara kokarin sawa dady Abaki,
*innalilahi wa'ina laiyi raji'un*

Yadda yake saka masa fresh milk din haka yake dawo wa sam bayq zama a bakinshi ,ballanta a
saran zai zauna a cikinshi, Momy tuni ta karaya da dady sai kuka takeyi ,shima Nasir din
daurewa kawai yakeyi,



Dady ya kama hannun Nasir ya riqe tamau!! Yana kallonshi, shima nashi hannun ya riqe
,yace"dady please ka tashi muna bukatar ka,ga Momy na tana kuka,dady in nine na bata maka
rai kayi hakuri ,bazan kara kaji,yadda ya fadi maganar sai ka tausaya masa




Alamun tsayuwar motoci suka riqa ji ,dama Momy tuni tayiwa"yan uwanshi waya aiko sai ga su
sun shigo farlo din hankali a tashe, Mahaifin Hanifa ,ya bugawa Nasir tsawa yace"burinka ya
cika ,Nasir babu tamtama kai ne ka yi silar tashin ciwonshi ,kasan sarai ba ya San damuwa,in
ka kashe shi sai nayi shari'a da kai"!



Nasir da ba'a fada masa ya kyale ,ya kalli Uncle din nashi sheqeqe ,yace"in har dady ya mutu
,to kwananshi ne ya kare bawa bai isa ya kashe wani ba, in lokacin mutym yayi dole ya
mutu,sabida haka kar ka kuma dora min,ai ba Ku fini jin ciwonsa ba"
Dukkaninsu mamakinsa suka yi to amma dake sun San halinsa ,babu Wanda yakara cewa ufan
a cikinsu,suka kama Dan uwansu , da nufi tafiya asibiti
[06/06, 00:44] +234 808 996 5176: [15/05/2019 1:57 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*



*73*



Hankali a tashe Malam Ya'u ya karaso gurin da nufi kama Alh Huseen ,Nasir ya daka masa
wata muguwar tsawa tamkar bai san daga inda yake ba tace"karka kuskura ka ta bashi Malam
,duk wani surkule irin naku na fulani kaje ka kwance ,shi sabida dama na lura tun tuni kuka
asirce dady ,shiyasa kwata-kwata bayason Bacin ranku kai da iyalinka, sabida haka ka rubuta
ka aje ,zamanka a gidanan ya kare"



Mahaifin Hanifa yace"kayi min dai-dai Nasir dama nima tuntuni nake zargin haka, dole subar
gidan nan,ni ina zarginsa gurin rashin lafiyar dan uwanmu,dole ya bar gidan domin ba mu hada
zuri'a dashi ba ,



Malam Ya'u yayi tsamo-tsamo tamkar Wanda a ka watsawa ruwa a jiki ,sai gumi ne yake zuba a
jikinshi, lokaci guda ya muzanta,bakinshi yana rawa yace"ku fahimce Alh babu wannan abu mai
muni a tsakanina da Alhji Huseen sai alkairi,uba na dauke shi ,babu cutarwa tsakanina dashi
sabida yayi min abinda bazan taba mantawa ba a rayuwata"




"Rufe mana baki dattijon banza da Wofi"!! Nasir ya katseshi cikin tsageranci ,yana masa wani
banzan kallo"



Maryam ranta yayi mugun baci! A gabanta Nasir yake kiran Ubanta da dattijon banza Lallai
bazata lamunta ,dole a kwai ranar da zata amayarwa da uncle duk cin mutumchin da yake mata




Duk wannan abinda yake faruwa Dady ya naji ,ranshi yana mugun zafi,da irin rashin kunyar da
Nasir yakeyi,anrasa mai tsawatar masa ,a cikin "yan uwanshi,sabida sunajin tsoransa,wanan
yana nuna cewar ko mutuwa yayi haka zasu wofintar da jininsa,tabbas zumunci bai ce haka ba
tunda shi ba haka ya musu ba
[15/05/2019 2:18 PM] Binta U Abble: Tari! ne ya sarqe shi ya riqayi babu kakkautawa ,nan da
nan suka mayar dashi suka kwantar,Nasir ya nufi frji da sauri ya ciro ruwa mara sanyi sosai
yazo ya na sama a baki,



Dady ya ki karba ,idanunshi tsaye kan Malam Ya'u, yana kallonshi ,da kyar ya daga hannunshi
da yayi masa bala'in nauyi yayi masa alama yazo gareshi ,Malam Ya'u ya karasa kusa dashi
jikinshi a sanyaye,yace "sannu Alh Allah ya baka lafiya"



Dady ya bude baki da kyar yace"Malam Ya'u ko bayan babu raina ban amunce ka bar gidanan
ba ,shashen da kake ciki na mallaka maka shi ,halak malak, sannan , inaso kayi min wannan
alfarma ga amanar Nasir nan na damka maka ita a hannunka kar ka wofintar da shi,ka cigaba
da yi mishi addu'a Nasir naka ne dama can "

Malam Ya'u yace"na karbi Amana Alh ko da ranka ko babu jinnika ba abin gudu bane a
gareni,in sha Allahu zaka tashi ka cigaba da rayuwa, nagode da karamchin ka a gareni ubangiji
Allah ya biyaka da aljanar fiddausi"



Cikin zuciyarsa yace ameen,sannan ya kamo hannun mahaifin Abdul latif ya ruke gam! Yace"ni
Hussen in dai na isa da kai da abinda ka haifa ,ina so ko bayan babu raina ,ka daura auran
Abdul da Maryam,domin ina sha'awar hada zuri'a da ta Ya'u, da naso Nasir ne ya samu wannan
garabasa domin auran kamilar mace irin Yarinyar dace,dukkaninku baza Ku fahimchi haka ba
sai nan gaba, Nasir ya fadamin qeqe da qeqe ban isa dashi ba ,kuma bazai bi umarnina ba,
sabida haka da wannan bakin cikin zanmu a rayuwata ,Nasir nagode nagode, nagode, tari ya
rurnikeshi,!!



Hankalin Nasir yayi mugun tashi, kaddai ,dady ya sauki maganar su ta dazu da zafi haka,har ta
janyo masa tashin ciwonsa,shifa yafadi hakane kawai dan ya bata masa rai, amma
kwata-kwata-ba gaskiyar abinda yake zuciyarshi ba kenan,

Kafin ya dawo daga tunanin nashi,yaji Momy ta rusa ihu,yayi da Mahaifin Mubina,yake Fadin
*innalillahi wa'inna ilayi raji'un*
Dady ya amsa kiran Ubangiji
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 9:26 AM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*



*74*



Nasir ya fasa wani ihu yayi kan dadynsa ya ruqunqume shi,kuka ya kece masa ,cikin dimuwa da
fitar hayyaci ,yake fadin *innalillahi wa'ina ilayi raji'un*
Dady kar ka mutu, bakace ka yafe min ba, dady ka tashi in fada maka abinda yake zuciyata duk
kanin abinda nafada maka abaya ,karya nakeyi wallahi,dady ina mutukar kaunarta ,har a cikin
zuciyata,dady in kayi min haka ina zan sanya rayuwata pls dady karka yimin haka rayuwata
nima tazo karshe ban da amfani a duniyar nan,kafadamin mai kake bukata nayi maka shi
yanzu!!! Nasir kuka yake sosai da sosai ,duk ya gigice yafita hayyacinsa, in banda gumi babu
abinda yake zuba a jikinsa,yabi ya rungume gawar dady ya hana kowa ya kusance shi,da kyar!
Malam Ya'u ya karaso gurin gami da dafa kafadar Nasir din cikin dauriya da jajircewa ya ce"kayi
hakuri Nasiru Allah Ubangiji ya amshi Alh cikin aminci da yaddarsa, ya mutu yana kalamar
shahada,yanzu babu abinda yafi bukata da kai sai addu'a kaji"




Nasir ihu! Yakeyi yana sambatu da'alama kwakwalwarsa a lokacin ta daina aiki,domin kwata
kwata bai ji abinda Ya'u yake fada ba.




Maryam ko yanke jiki tayi tafadi, ta suma!!!



Kafin kace kwabo gidan ya hautsine da hayaniya, tuni Nura ya fita ya sanar da Sucurty da ke
waje abinda ke faruwa a cikin gida,




Aunty ko tana bangaransu duk wannan abin da yake faruwa bata sani ba tana kchin tana
hidimar Dora abincin rana,taga Malam ya shigo mata da yarinya ranga ranga,

Salati ta tafka tana tambayarsa abinda ya faru ,sabida dama tasan da batan da Maryam din tayi
na awanni biyar da suka wuce,Malam Ya'u yace"babu lafiya Suwaibah ,muna cikin tashin
hankali,Allah yayiwa Alh rasuwa



Gigicewa aunty tayi domin duk a zatonta mahaifinta yake nufi ,sabida tasan shima ba shi da
koshin lafiya.



Kuka ta fashe dashi tace "shikkenan baba wahala ta kare"



Ganin bata fahimci abinda yake nufi ba,yasa ya tsaya yayi mata bayanin komai,aunty ta rika
salati tana sanar da ubangiji,da gudu tayi dakin ta zaro hijab tana ,nanata innalilahi a fili,take
tambayar mai ya sameshi,shiru Malam yayi mata shi dai yana ta tasbihi cikin zuciyarsa, tare
suka shiga farlou, har yanzu Nasir na rungume da gawar Mahaifinshi ,yanzu. Ya dai na zubar da
hawayen sai kukan zuci yakeyi kwata kwata ya hana kowa kusantar gawar ,har Momy dinsa,
dake kusa dashi ,ita kuma a lokacin Allah ya sanya mata juriya,kwata kwata idanunta sun bushe
,babu hawaye ko days,amma kana kallonta kasan tana cikin dimuwa! Da tashin hankali
[16/05/2019 9:43 AM] Binta U Abble: Tace"My Son shiyasa kullum nake fada maka ka kiyaye
bacin ransa ,sabida kasan yana da lalura,kaki ji ,ko ka gani yanzu yazo ya tafi ya barmu mai
zakace min ,my son ,mai zakace min!!
Momy tafada muryar ta tana karkarwa,



Aunty tazo ta dafa kafadar Momy tana zubda hawaye tace"Hajiya Kiyi hakuri kinji,dama Allah ya
kaddara lokacin Alh yayi yanzu bawa bai ta kashe wani ba face sai lokacin sa yayi, kiyi hakuri
,kiyi mishi addu'a Allah ya jikanshi Hajiya Allah ya sanya mana hakurin jure rashinsa da mukayi.




Sai lokacin hawaye ya kecewa Momy ,tafadi a gurin ragwajb ,tana kuka, cikin tashin hankali da
damuwa take fad in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un




Aunty tazo ta dafa kafadar Nasir tace"dan gidan aunty kayi hakuri kaji ko ka fawwalawa Allah
kowa na hakane,don Allah ka saki kyale Alh ayi masa suttura ,duk wannan abinda kakeyi bazai
sa dawo mana dashi ba"



Nasir ya zubawa aunty ido yana kallonta ,bakinsa dai motsi yakeyi ,da kyar ya samu ya finciko
maganar ,yace"aunty dady ya mutu,!! Wancan yarinyar ,ce tayi sanadi ni babu ruwana,sabida
lafiya kalau na tafi na barshi da'ita,sabida haka ,duk yadda zanyi sai nayi gurin ganin na
wulakantata ,tunda tayi sanadin kashe min mahaifi.



Aunty Sam!! Bata fahimchi maganarsa ba ,ta lura kwata kwata baya cikin hankalinshi,tace"eh
nima Na amince Auncle ka dauki mataki kan wanda ya zalunce ka,amma yanzu abinda nakeso
dakai ka saki Alh ayi mishi suttura kaji ko"




Nasir yayi zakwado!! Yana bin dady dake rungume a jikinshi da kallo vakinshi sai motsi
yakeyi,yanzu wai da gaske ne dady shi ya mutu !! Ina karya ne!
Abinda ya fada kenan da karfi!! Sai ya fara Jan numfahi!! Da karfi ,kan kace kwabo ya afka kan
dady din nasa ya suma!!!
Guri ya hargitse da salati,Ya'u yazo ya janye Nasir ,daga kan dady,yayinda "yan Uwan dady din
suka samu damar janye dan uwansu,domin sutur tashi,
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 8:45 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*



*75*

Momy ta kidime tayi kan Nasir din tana kuka sosai ,tamkar wacce tasamu tabin hankali take
cewa "My son kai ma zaka tafi ka bar ni ne, ta kamashi sai jijjigashi takeyi tana kuka da sauri
Malam Ya'u yazo da ruwa mai sanyi cikin gora ya bude ya watsa wa Nasir din ,cikin zuciyarsa
yana ta nanata Kalmar innalilahi

Nasir ya mike a zabure!! yana dube dube babu dadynshi a gurin ya mike da sauri ,jiri! ya
debeshi ya yar kan kujere ,sai ya dafe kanshi da hannunshi guda,ya na furta,kalame "Ya Allah!!

Momy da aunty sai tausarsa sukeyi,kar ma dai aunty taji labari,shidai idanunshi suna
rufe,kwata-kwata hankalinshi da tunanunshi baya kansu,zuciyarsa take fada masa kayi rashin
mahaifinka har abada Nasir,sai ya karyar da wuyanshi jikin kujera ,hawaye yana zirarowa daga
idanunshi da suke rufe,




Kankace kwabo mutuwar Alh Huseen ta karade birni da kewaye sabida dukkanin wanda ya
kwana ya tashi a garin kano da kewaye babu Wanda bai sanshi ba idan ma baka taba ganinshi
ido da ido ba to za ka ganshi a jarida ko gidajan TV ko tashoshin yada labarai,sabida yadda
yayi suna gurin taimakon marayu da nakassasu gami da taimakon talakawa ,Sam dukiyarshi
bata rufe masa ido ba sabida haka ,kofar gidan damqam! Take da jama'a duk suna jira a fito
dashi domin suyi masa rakiya zuwa ma kwancinsa na gaskiya ,sai jaje sukewa juna suna ta
fadar alkairinsa, dayawa daga cikinsu hawaye suke sharewa domin sun gaza daurewa sabida
sunsan ba karamin rashi sukayi ba,




Addu'oi Ya'u ya dukkufa yana ta tofawa Nasir ,duk domin ya samu zuciyarsa ta sanyaya, cikin
hukumcin ubangiji ya bude idonshi ,ya na binsu da kallo daya bayan daya, kimanin minti biyu,ya
mike tsaye cikin nutsuwa ,aunty tayi saurin riko hannunshi,sai Malam Ya dakatar da ita ,yayi
mata alamar ta rabu dashi, kai tsaye dakinshi dake farlo ya nufa ,ya bude ya shiga gami da rufo
kofar,Momy tabishi da kallo zuciyarta ,tana tsinkewa
Toleit ya bude ya shiga ya dauro alwala ya fito ya kwabe kayan jikinshi, ta cire sarkokin da suke
wuyanshi,hade da barimar dake manne a fatar kunnenshi,ya bude katuwar siff dinshi,ya ciro
wata jallabiya fara kar da ita ya sanya a jikinshi bayan ya sanya gajeran wando,ya dauki carbi
mai ma dan nai



Lokacin da ya fito anfito da dady,"yan uwa suna ta yi mishi addu'a Momynshi na gurfane gaban
gawar tana kuka sosai da sosai, cikin jarumta yazo ya janyeta ya zaunar da ita kan kujera, bai
cewa kowa komai ba,yafara kokarin daukar dady,ganin haka yasa jama'ar da suke gurin suka
mike dama shi suke jira ya fito yayi masa addu'a ,sai suka kama masa makarar ya Dora a
kafarshi, suka fita bakinshi dauke da addu'oi iri-iri yana nai mawa dadynshi rahamar Allah.
[16/05/2019 9:05 PM] Binta U Abble: Nan Aunty ta zauna ita da saura jama'a suna ta tausar
Momy,kwata-kwata ta manta da Maryam da a ka kai mata ita ranga ranga,sai ganinta sukayi
tafado farlo din tamkar zautacciya sai zare ido takeyi dama ga su tubarkallah,



Ta rika bin ilahirin farlou n da kallo, cikin zuciyarta take fadin Allah mafarki takeyi ba gaske bane
abinda ta gani cikin mafarkin ta.



Mata tagani zazzaune ko wacce cikin hijabi ga carbi a hannu,da kyar! Ta samu ta furta,kalarmar
da ta fito daga bakinta, Tace"aunty wai da gaske dady ya mutu,wani mummunan mafarki nayi,



Kafin aunty tace komai,Momyn Mubina ta daka mata tsawa ,cikin tsantsan kyama tace" waye
sa'anki a gurin

Please Login or Register in order to submit comment