You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abace tace nice Mahaifiyarshi ,ba Maryam ya kora ba ni ya kora
kuma zan fita yanzu"



Dr Sofia tace"Mom kiyi hakuri , wan can yarinyar ya bada umarni a fitar masa ,ba ke ba please
mom



Momy tace "rufe min baki bana son zan can banza"



Malam Ya'u dake tsaya jikinsa a sanyaye duk da bayajin turanci amma ya fuskanci abinda yake
faruwa ba mai dadi bane ,gashi yaga ana nuna "yarshi da hannu Allah yasa bata wani laifi tayi
ba



Ya tari Momy wacce take ta faman fada da turanci,yace duk da dai bana fahimtar abinda kuke
cewa Hajiya ina ganin abin duk bai kai na daukar zafi haka ba,ina ganin tunda Baban gida
yasamu lafia zamu bar asibitin nan mungude da karamchi Allah ya kara girma"




Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "ai ko baka fada dole zamu bar asibitin nan yanzu, shi kuma
Nasir din zaizo ya same ni"




Abin mamaki duk da tsawar da Momy tayiwa Sucurty din ,ta kuma ce musu ita mahaifiyar Mai
asibitin ce ,hakan bai sa sun kauce daga kanta ba su tsaye kikam ! Suna jira ta tashi. Ita ko
Maryam Sam abin bai mata ciwo ba domin tasan Dan ya bata mata rai ya yanke wannan
hukunci, sai ta kalli Momy tace "kiyi hakuri Momy wallahi ni kaina narasa wace irin qiyyaya
uncle ke min amma babu komai"




Momy tace"ai ke zan bawa hakuri Maryam kinji ,babu komai zaizo ya same ni, tafada tana
mikewa tsaye tana gyara zaman hijab din ta
Su aunty ma mikewa sukayi ,Yaya Rabi tana kokarin tashin Mahaifin nata, Malam Ya karaso
gurin ya tasheshi ya mike jikinshi babu kwari sosai ,sai ya jin ginar dashi a kafarshi suka na
kokarin fita daga dakin

Suma suka biyo bayansu kowanne da rai a bace, Dr Sofia ko babu abinda ya dame ta, haka
wannan Sucurty suka tasasu a gaba har sai da sukaga sun fice daga asibitin sannan suka dai
na binsu sai kace wasu masu laifi.
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:16 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*91*

Wannan abu da Nasir yayi ya 6ata ran Momy sosai, tunda take dashi bai taba mata abinda ya
ta6a mata zuciya ba irin na yau,kwata-kwata ta lura Nasir bai san darajar dan'adam ba ko
kadan ,giyar kudi tana dibanshi ya nawa kowa kallon kaskanci,amma wannan karon dole ta
nuna masa bacin ranta, rai a bace suka karasa gida,dukkaninsu suka fito daga motar bayan
Momy tayi parking,kai tsaye part dinta ta nufa ,batare da ta tsaya a gurin ba domin wani irin
nauyi da kunyar mutanan takeji, gashi dai kullum Nasir din zai yi musu rashin mutumci amma
sabida karamci da dattako basa nuna wani bacin rai a tare dasu,

To bayan Momy ta wuce Malam ya shiga da Baban gida wajansa ,su aunty suka gyara masa ko
ina ,sannan suka fito,suka barshi tare da Malam Ya'u suna hira ,Baban gida ya kalli Ya'u
yace"dama a kwai maganar da nadade inaso muyi da kai"



Malam Ya'u ya gyara zama yana fuskanta Baban gida cikin girmamawa yace"ina sauraron ka
Baba"



Baban gida ya sauke ajiyar zuciya cikin alamu na marasa lafia yace"lokaci yayi da za'a ce ka
tsaya da kafarka ma'ana ka dai na ci a karkashin wani , tun lokacin da Marigayi Alh yana raye
naso ka karbi kasuwanci kamar yadda shi Alh ya so a lokacin ,kai ka nuna kafison ka zauna a
bakin get ko"



"Kwarai kuwa Baba ni kai na sai yanzu nasan na tafka babban kuskure wallahi"



Baban gida yace"dama ba wani abin ake gudu ba sai mutuwa"

"Kwarai kuwa Baba"
"Yanzu abinda za'ayi a kwai wata gona ta can garinmu albasu zan siyar da rabi sai in baka
kudin ka fara juyawa ko yaya kace"



"To madallah Allah ya saka da alkairi,wallahi nima tuntuni nake shawarwarin yaya za'ayi"

"Abinda za'ayi kenan ai "
Baban gida yafada yana gyara kwanciyarsa

Nan dai Malam Ya'u yayita godiya suka tsayar da maganar cewar zasuje can albasu garinsu
Baban gida domin a siyar da gonar sabida sauran "yan uwanshi duk suna can shine kawai
yafito nai man abinci cikin gari a wancan zamanin har ta kaishi da yin aure ya haifi su Yaya Rabi
da aunty Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu aunty da girmanta a lokacin Yaya Rabi a kayiwa aure
,to bayan rasuwar mahaifiyar tasu sai auntt ta cigaba da kula da mahaifinta har lokacin da ta
auri malam Ya'u




Malam Ya'u ya gyara masa kwanciya ya mike ya fito cikin farin ciki ya nufi bangaransu,



Ya na zuwa ya sanarwa da aunty halin da a ke ciki



Suma sun goyi da bayan haka sabida dama tun dazu abinda suke tattauna kenan



Maryam tana kicin tana aikin hada musu abinci ita ma taji dadin wannan lamari dama burinta
bai wuce ta dai na ci a karkashin Nasir ba ,Dan rainin hankali.
[26/05/2019 9:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Nasir kuwa sai wajan sha biyu na dare ya shigo
gida.

Kai tsaye part dinshi ya wuce domin yayi wanka ga wata irin yunwa yana ji



Momy tana falo tana jiran dawowarsa ,tana jin shiguwar motarsa ta mike ta nufi part din nasa.



Fitowarshi kenan daga toliet yana tsane kanshi,Momy ta tura kofar dakin nashi ta shiga da
sallama
Abin ya bashi mamaki ganin Momyn shi da daddaran nan ,sai ya tsaya yana kallonta ta karaso
ta zauna gefan gadonsa ita ma shi take kallo kamar yadda take kallonsa



Yace"Momyna lafiya dai ko"?

Tace "lafia lau tunda gani ka ganni Allah ya dawo dani gida bayan korar karan da kasa akai
mana"



Cikin namaki yaje ya zauna kusa da'ita yace"Momy waye yayi miki korar kare,ban fahimci
abinda kikecewa ba"



Tace"dazu bayan fitarka waye ya turo Sucurty suzo su wulakanta Maryam"



Momy"wacece Maryam"

" Ok zakayi min rainin hankalin da kasaba ko"?
Momy tafada a fusace!



Dauke kai yayi yana nazari na minti biyu yace"Momy please ban fahimci me kike nufi ba wallahi
, dazu dai nasan nasa Dr Sofia tasa ka Sucuty su fitar da yarinyar nan ganin tana nema tayi
mana katsaldan a kan aikinmu ,ba na son bacin rai shiyasa na yanke wannan hukunci"



Momy ta hararashi tace"wannan ba hukumci bane wulakanta mutum ne abinda kayi Sam Baka
kyauta ba, kamar ni ince musu ,su kyaleta suka qi ,ji sukayi mana tsaye a ka har sai da sukaga
mubar asibitin sannan suka dai na bin mu sai kace wanda mukayi gagarimin laifi"



Ranshi ya baci jin abinda Dr Sofia tayi kafin ya tafi sai da yafada mata ga yadda zata yi



Yace" Kiyi hakuri Momy ba laifinsu bane ,ni na isa in sa a kore ki Momy ke nake gani nake jin
sanyi a zuciyata Momy nayi missing din Dady Sosai ,kwalla ta taro a idanshi yana kokarin
mayar da ita,amma sai da ta fito ,ya sa Dan ya tsanshi daya yana daukewa



Ita ma Momy zuciyarta ce ta karye sabida Nasir ya fama mata mikin da yake cikin zuciyarta ,sai
tafara goge hawaye
"OK" "OK Momy yi shiru na dai na please ki dai na Dan Allah"
Nasir yafada yana marai rai cewa



Cikin kuka Momy tace"My Son Bakajin magana ko,ka manta wasiyyar dady din ka"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 1:19 PM] ®Binta Umar Abbale: [27/05/2019
10:35 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*92*

Momy ta cigaba cewa My son baka kewar mahaifinka, da ka kayi missing din nashi da gaske
da baza ka wofintar da wassiyar shi ba, nima kanaso ka dora hawan jini ,ko ka kasheni in na
mutu ka huta ai"Momy ta karashe maganar tana goge fuskarta.
Nasir hankalinshi ya tashi sai ya rungume ta sosai yake kokawa da zuciyarsa sabida bayason
hawayen da yake kokarin dannewa su zubo masa har Momyn ta gani hankalinta ta tashi,yace
"a'm Sorry Momy bazan karaba ki yafe min, ni kaina ,Wasu abubwan da nakeyi ba'a son raina
ba ,amma Momy kar kira zubar min da hawaye dan Allah"



Tausayinsa ya kamata ance tsakanin da da uwa sai Allah

Ta shafa kanshi kamar yaro tace"Na yafe maka ,amma Dan Allah kar kara wulakanta mutanan
,kaga mahaifinka har ya bar duniya tsakaninsa dasu mutumci ne,kuma duk Wanda ya taimaki
wani shima Allah zai taimakeshi"




"Momy ki kwantar da hankalinki insha'allahu zanyi kokarin ganin na faranta miki"



Momy tace"yawwa Allah yayi maka albarka"

"Ameen Momyna"

Tace"kaci abinci kuwa,domin jikina yana bani bakaci abinci ba"



"Uhum Uhumm Momy Wallahi banci ba yanzu hakama yunwa nakeji sosai"
Nasir yafada tamkar wani yaro karami



Momy ta Dan mari fuskarsa tana dariya tace"ai halinka zama da yunwa sai da kai tafaman cin
biscut sai kace wani yaro"

Dariya yayi har fararen hakoranshi suka bayyana ,kasan habarshi ya loba yana kanne mata ido
daya yace"Momy nifa har yanzu yaro ne a gurunki"



Momy ta girgiza kai kawai tana murmushi tana tuno hirarsu da dady kafin rasuwarsa inda yake
son yara kananu,

Ta kalleshi tace"Myson inaso ka haifa min yara da yawa kaji ko"



Shiru yayi fuskarshi dauke da murmushi yace"Momy ni a tsarina banason taron yara wallahi a
kwai damuwa"



Momy ta harareshi tace "albarkace damuwa my son"?

Yayi murmushi yace" Momy da gaske nake wallahi da daya ko biyu sun isheni"

"Baka isa ba"Momy tafada, tacigaba da cewa kai dai kawai ka nemi zabin Allah"



"Insha Allahu Momy,Allah ya kawo masu albarka"

"Ameen amee"

Tace"tashi ka kimtsa muje kaci abinci"

Ya mike tsaye yace" Momy muje kawai haka

Mikewa tayi itama suka fita.



Momy ta hada masa abinci sosai tasashi a gaba sai da yaci ya koshi sannan ta kyaleshi yaje
kwanta
[27/05/2019 10:56 AM] ®Binta Umar Abbale: Washe gari da wuri ya tashi ya kimtsa tsaf cikin
yanayin shigarshi irin ta jiya kwana biyu abin ya motsa mishi,ya fito ya tadda Momy zauna cikin
kujera tana duba wanni littafin turanci fuskarta manne da farin tabarau

Ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace"Kwana biyu kuma abin ya motsa maka ne"
Yayi murmushi gami da zama kusa da ita yana gyara wata katowar hula ta sanyi mai uban
tsada yawanci turawa ne suka fi amfani da ita mussaman da sanyi, yasanya ta a kanshi har sai
da rufe masa kunne , hannuwanshi ma safa ce kalar hular ,yace "Momy yau garin antashi da
sanyi wallahi kinsan banason wannan yanayi duk jina nake a takure"

Momy tace"shine ka jibga riguna a jikinka haka"



Dariya yayi yace"yeah Momy to ke ya kikaga wankan"?

Momy ta tabe baki tace"babu laifi dai"

Yana dariya yace" Momy in a America nake ,wannan dressing din nawa ,mai tsada ne sai
nasamu wanda zai'siya,



Momy tace"ai ban ce komai ba"

Yace"nan din ma bari kiga in fita ,yadda zan hada Gslow mussaman Na mata"



Dariya Momy tayi tace"baka da dama My son ,zan so inga Sirika ta,wai ko da Hanifa za'ayi ne
ko da Mubina wacce kazaba a cikinsu"



Nasir ya hade fuska yana turo baki kamar wani Yaro yace"Momy rabuda Wa "yan nan "yan
iskan yaran dan Allah"



"Yan uwanka ne "yan iska "? Momy tafada cikin mamaki

"Yes " Nasir yafada ya cigaba da cewa
Momy in ba iskanci ba wai a gurin taro Mubina ta mike ta kefadawa dady tana sona ko kunya ba
taji cikin jama'a"




"Laifi tayi kenan dan tace tana sonka"?



"Momy nifa a tsarina bana son in auri shashashar mace Mara kamun kai ,shiyasa ma har yanzu
ban fara dubawa cikin matanmu nan domin babu abinda suka iya sai shirme da kazanta gami
da shafa man bleecing"
Momy dariya take sosai ganin yadda Nasir ya hakikan iya gaskiyarshi



Shima yana dariya yace"Allah kuwa Momy inajin haushin "yan matan wannan zamani kiga sun
dage suna shafe shafen banza,karshe ya jawo musu cuta,nafison mace naturel "

Momy ta tabe baki tace "to ai sai kaje kauye ka nemo mata ina ganin can zai fi maka"
[27/05/2019 1:36 PM] ®Binta Umar Abbale: Ya mutse fuska yayi yace"haba Momy kauye fa
kikace,ni nayi kala da matan kauye yanzu"?



Momy tace "au matan kauyen kalarsu daban take da ta "yan birni,ashe bakasan sunfi tarbiya
ba, in ka amince sai insa Uwani ta duba maka a garinsu kaga Uwani kyakykyawa ce gata
bafulatana"



Dariya yayi kawai yana girgiza kai yace"Momy kenan indai zaki iya zama da'ita shikken ki
samomin"



Dariya tayi tana nunashi da hannu tace"dubeshi kamar gaske"



Cikin dariya dai ya mike ya nufi dainnig teble yace"da gaske ne mana"



Momy ma mikewa tayi tabi bayanshi tafara hada masa kalaci suna hira cikin so da kauna irin ta
uwa da danta,yace"Momy mun kammala komai fa Dan gane da bude Hotel dinmu ni da Abbas
yanzu kawai za mu tanadi ranar da zamuyi bikin budewa,bayan haka kuma munyi odar Motoci
Masu kyau Sosai da nagarta suna gareji ,kiyi mana addu'a Allah yasa mu fara a sa'a"



Momy tace"Allah ya dafa muku yayi riko da hannuwanku yasa Ku fara a sa'a"

"Ameen Momy"

Miftahu ne yayi Sallama ya shigo cikin falo, yana sanye jallabiya mai ruwan tuka kanshi da hula
irin ta Larabawa, yaron yafara girma yanzu yana shekara sha Uku zuwa sha hudu ,cikin
nutsuwa ya karaso yana gaida Momy
Momy ta amsa fuskarta a sake ,ya mikawa Nasir hannu gami da cewa "uncle barka da asubah"



Nasir ya bashi hannu sukai musabaha tace" ka tashi lafiya Boy"

Miftahu yayi dariya jin sunan da uncle din ya kirashi dashi yace"lafiya Lou uncle"

"Masha Allah"
Nasir yafada yana cire hannusa ya cigaba da cin abincinsa



Ya kalli Momy yace"Dama Baba ne yakeson yayi magana dake"



Momy tace" to kace ya shigo mana, in banda abin Malam Ya'u sai ya aiko ka, ai anzama daya"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 6:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*93*

Miftahu ya fita domin ya sanar da mahaifin nasa abinda Momy tace.
Tare suka shigo falo Momy ta mike daga kan kujerar cin abinci tace "Yanzu malam har sai ka
turo yaro yayi maka iso sannan zaka shigo"?
Tafada tana nuna masa gurin zama, Malam Ya'u ya zaune cikin kamala da dattako yana
murmushi yace"ai dole ne hakan domin haka shari'a tace" Momy tace"e kayi gaskiya Malam"

Malam Ya'u ya gyara zama sosai yana fuskantar Momy yace"Hajiya wata muhimiyar magana ce
nake tafe da ita"

Momy tace "To Allah yasa ta alkairi ce ,ina sauraronka"

"Hajiya inaso kiyi wa magana ta kyakykyawar fahimta wallahi ban shirya wannan Abu da wata
manufa ba,sai Dan ina ganin haka shine mafita a gare ni"

"Babu komai Malam ina sauraron ka"

"Dama na yanke shawarar cewar zan bar aiki anan zan shiga kasuwa in sha Allah"



Momy tayi shiru tana tunani a cikin zuciyarta,dama tasan wannan lokacin yana nan zuwa



Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa tace"Masha Allah arrama ,bazan hanaka ka fita nema ba
ubangija Allah yabada masu amfani"
Cikin farin ciki malam yace"ameen Hajiya nagode da fahimta ta da kikayi"

Momy tayi murmushi tace"ai nasan gaskiya Malam wallahi babu komai"

Duk wannan abin Nasir Na zaune yana cin abinci yana jin duk abinda suke cewa ,kala bai ce
musu ba,har Malam ya tashi yanawa Momy sallama sannan ne ya hangi Nasir din yace"A'a
Nasiru baka fita ashe"?



Nasir ya dago kai yana kallonshi babu yabo babu fallasa yace"e arrama yanzu dai nake kokarin
fita"

"To masha Allahu,Allah ya tsare"

"Ameen ameen Arrama"
Nasir yafada ya cigaba da cin abincinsa

bayan Momy tace "My son kana jin yadda mukayi da arrama ko"?

"Eh Momy inaji"

"Owk to yanzu kai mai zaka ce"?

"Momy mai zance kuwa ,ni banason takurawa mutum dama shine ya ga zai'iya ko yau ya bar
aiki zan samu get man, karki damu zan fitar da kudi in bashi hakkinshi,kuma dukkanin
dawainiyar da ake mishi ba za'a fasa ,sai dai in shine yace" baya bukata"



"Haka yayi Allah yayi maka albarka"

"Ameen" Nasir yace ya mike bayan ya gama karyawa yana duba agogo yace"Momy zan fita
kuma inaji sai dare zan shigo"

"To Allah ya tsare"

"Ameen Momyna"
Yafada yana kokarin fita




Kai tsaye motarshi ya nufa
Maryam na tsaye kusa da Baban gida dake zaune kan bainci ,jiki yayi karfi ,sai tsokanarsa
takeyi, ta hangi fitowar Nasir gabanta ya yanke ya fadi ,sai tayi saurin dauke kanta ta cigaba da
magana da Baban gida amma duk da haka gabanta sai dukan uku-uku yake ,sabida yadda taga
Uncle din yayi mata wani mugun kyau gaskiya kayan sun mishi kyau sosai
[27/05/2019 6:55 PM] ®Binta Umar Abbale: Gashi Malam baya guri ga get a rufe, ga Nasir ya
tawo da mota zai fita yaya kenan"?

Baban gida ya mike cikin rashin qarfin jiki yafara kokarin bude get din,



Maryam tayi sauri ta dakatar dashi ta hanyar mayar dashi ta zaunar kan bainci tace"haba tsoho
jikinka babu qwari ina kai ina iya bude kofa,ka kyalemu mu masu jini a jika, tafada tana dariya
Shima dariyar tayi yace"kaji ja'ira kamar wacce zata iya"




Kai tsaye gat din ta nufa cikin karsashi gami da jarumta tafara kici-kicin budewa,



Nasir tun kafin ya karaso ya hange ta tana kokarin budewa

Tsaki yaja kawai yana dariya domin shi dariya ma yarinyar tabashi gaskiya yana ganin karfin
halinta



Sai ya tsayar da motar gami da zuge glass din ta zuro kanshi dai-dai sai tin da Baban gida yake
zaune yace" Baban gida barka da asubah"

Baban gida ya fara kokarin mikewa yana amsawa Nasir yace"ba sai ka tashi ba ma, yaya karfi
jiki"

"Alhmdullhi Nasiru Allah yayi maka albarka,ya jikan alh Huseen ameen"



Nasir yace"ameen ameen" ya mayar da glass din motar yana dannawa Maryam Hon wacce ta
hakikance tana faman tura get amma kamar wacce take tura dutse kwata-kwata yaki motsi ,sai
gumi take yankawa.



Dariya kamar ta kashe Nasir a cikin mota ,yana sane yake ta faman danna Hon babu ji babu
gani
Maryam ta juyo a fusace tana danna masa harara taja tsaki ta cigaba da abinda takeyi,shiko
yana ganin abinda tayi sai ya kara danna hon da karfin gaske
Ya bude motar ya fito a fusace, ya nufi gurin , yana zuwa kawai ya buge hannunta daga jikin get
din yace"dallah matsa mana a guri kinsan baza ki'iya budewa kika batawa mutane lokaci idoit"

Maryam jikinta a sanyaye ta dinga kallonshi tana galla masa harara sai haki takeyi tsabar
gajiyar da tayi ga hannuwanta sunyi ja sabida yadda take tura kofar abinka da farar fata ,tafin
hannun yayi jajazir, a fusace ta wuceshi taje ta zauna kusa da Baban gida ,duk da haka bata
fasa hararsa ba



Ja da yayiwa get din duk irin raurinsa da nauyinshi kuwa ,ya bude nan take, sai a lokacin Malam
Ya'u ya karaso gurin, Nasir wuce yaje ya shiga motarshi ya fita daga gidan ranshi a bace
yace"ai ko ka bar aiki ko baka bari ba dole in samu wani Wanda zai dinga kula da aikinshi"
[06/06, 01:47] +234 808 996 5176: [28/05/2019 10:06 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*94*

Baban gida ya rika yiwa Maryam dariya bayan Nasir din ya fita,yace"kin cika raguwa da kika
kasa bude kofar can, nasan inda Nafi'u nasa ko Miftahu da tuni sun bude, ke kin tsaya shirme
dube ki sai nishi kikeyi kamar wacce tayi aikin karfi"

Itama dariya tasa tace"wallahi kuwa na dauka zan iya budewa ashe akin babba ne ,dubi hannun
fa"tafada tana nuna masa tafin hannunta, dariya kawai yake mata har Malam Ya'u yazo ya
zauna a gurin,
Yace "dazu naje na samu Hajiya nafada mata halin da ake ciki"
Baban gida yace"ai haka yafi gwara tasan komai da wuri"

Hakadai suka zauna suna tattauna maganar,

Maryam ta mike ta shiga gida tanajin wani farin ciki a zuciyarta ganin zata dai na rayuwa a
karkashin wani Wanda bai San darajar Dan Adam ba.



*****

Bangaran su Abdul latif kuwa lokacin da mahaifiyarsa taji abinda yake faruwa daga bakin Alh
Hassan wato mahaifin abdul cewar Dan uwanshi bar wassiyar ko bayan babu ranshi a daura
auran Abdul da Maryam, sai tayi tsalle ta dire tace"wallahi bata yadda ba danta bazai auri ,
wa"yanda ba'a san asalinsu ba ba'san daga inda suka fito ba sabuda haka indai ita ce ta haifi
Abdul to bata amince ba"
Alh Hassan yace"dama bama bukatar ki amince ,dole zan cikawa dan uwana burinshi kafin ya
mutu"

Rikici a ke sosai akan maganar inda Hajiya Zulai taja tunga tace bata amince ba,shi kuma yace
babu abinda zai fasa

Abdul ma yaji duk halin da ake ciki ,to duk da haka yana nan a kan bakanshi sai tausar zuciyar
Mahaifiyar tasa yake



Hajiya Zulai kuwa sai zugata akeyi cewar yarinyar "yar iska ce ,sabida kwanaki ma an nemeta
anrasa
[28/05/2019 12:11 PM] ®Binta Umar Abbale: Sabida haka ta tada hankalinta a kan maganar,
tace ita bada yawunta za'ayi wannan aure ba.




Misalin sha daya da rabi na dare Nasir ya shigo gida ,Malam Ya'u na zaune a bakin get har
yanzu bai shiga gida ba sabida Nasir bai shigo ba har yanzu radio ce a hannusa yana
sauraron tashar Ballo Dandago wato radio Kano kenan

Da sauri ya aje radio ya mike ya je ya budewa Nasir get, ya shigo da motar.

Yayi parking ya fito , kai tsaye bakin get din ya nufa Inda Malam Ya'u yake yana kokarin mayar
da kofar ya rufe.



Muryarshi Sama-sama yace"Arrama ina son magana da kai"

Malam ya juyo da sauri Dan bai tsammaci zuwanshi gurin ba



Yace"to to ai babu matsala Nasiru ina sauraronka

Nasir ya gyara tsayuwa sosai yana kallonsa yace"dazu Momy take fadamin maganar da kukayi
da ita, cewar zaka bar aiki a gidan nan ko"?

Cikin mamaki Malam ya dago kai yana kallon Nasir din yana Mamakin yadda ya tsareshi da
tambaya sai kace wani ubanshi,lallai Yaron yana ji da izza, amma sabida dattako irin na Ya'u
sai yace"kwarai kuwa Nasiru inaso in fara kasuwanci ne"
"Owk yanzu tsawon shekaru nawa kayi a gidan nan kana aiki ,inaso in biyaka hakki kane
kamar yadda shari'a tace"
Nasir yafadi maganar kai tsaye kuma da'alama haka abin yake har cikin zuciyarsa



Cikin dumbun mamaki gami da al'ajabi Malam yake kallon Nasir din, ya nuffasa gami da
cewa"kayi gaskiya Nasiru ni tun lokacin da marigayi ya dauke ni aiki a gidan nan ba muyi dashi
zai biyani domin ba nai masa gadi Dan ya biyani komai sabida haka babu wannan maganar a
tsakanina dashi har ya koma ga Allah"



Nasir ya sauke a jiyar zuciya, yace" ai nasan da haka, yanzu dai nine maigidan, kamar yadda
zan je in dauko wani get man din in biya shi hakkinshi ya zama dole in baka hakkin ka"



Arrama yace"bana bukatar komai Nasiru nagode sosai da kulawa"

Nasir ya bude Jakar dake hannusa ya fito da kudi kimanin dubu dari biyar yace"ga wannan ka
rike ka hada dasu gurin yin bussines din naka , Allah ya taimaka"



Cikin mamaki Malam ya karbi kudin shi kuma Nasir ya juya ya shige part dinsa



Da safe Malam ya fito da kudi yana nunawa aunty ,itama tayi mamaki sosai, sai tace kawai ya
hada dasu tunda dai shi bashi ya nema ba



Haka rayuwa take Malam Ya'u ya fara kasuwanci cikin sa'a sosai yake samun rufin asiri, yanzu
ya daina zaman get kwata-kwata da gari ya waye zai fita kasuwancinsa ,hakanan yanzu shine
yake dawainiya da yaranshi gurin biyan kudin makaranta,dama su Nafi'u ne ,Maryam tuntuni ta
kammala karatun ta, kafin mutuwar dady ya tsaya mata sai da tayi karatu sosai kuma
takkadunta sunyi kyau sosai shiyasa take so ta samu aiki ko a karamin asibiti ne domin ta
tsaya da kafafunta ita kam babu abinda zata ce da Alh Hussen kullum sai dai tayi mishi addu'a
samun Rahama gurin uban giji




Abdul yana Legos ya fara aiki yanzu sai dai su yi waya su sha soyyayrsu ,yace "in yadawo za'a
hado komai a kawo sai dai kawai a sanya ranar daurin aure.
Nasir kwata -kwata ta manta yau sharabon da su hadu ,sosai tayi bala'in kewarsa tun lokacin da
suka hadu a bakin get bata kara ganinshi ba.



Ban garansa kuwa abubuwa ne suka sha masa kai sosai domin yanzu harkoki sun bude masa
ba ya zama a gida sosai ko asibitinsa bai fiye zama ba in dai ba dole ba ,sabida yadda
kasuwancinsu ya bunkasa daga sunyi odar za ka nemeta karasa ta kare sabida kyawun
Motocin da suke shigo dasu da nagartarsu , kudi sosai suka yi suna shi da Abbas Nasir&Abbas
Motars sunan kamfanin nasu, Nasir yayi kudi na ban mamaki lokaci guda sunansu ya zagaye
kasashe ,a yanzu ma shirye shiryen da yakeyi zai tafi America domin a can ma suna so su bude
sabon company shi da wasu turawa.



Momy tayi tayi mishi addu'a , shiyasa yanzu kafin kaganshi sai kayi da gaske, sabida yawan
zirga -zirgar da yakeyi.
[06/06, 01:47] +234 808 996 5176: [29/05/2019 1:56 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*

*95*
Misalin bakwai na dare Nasir ya shigo gidan cikin wata sabuwar motarshi mai masifar kyau da
tsada ,yana kwance a bayan mota drevar shi Tony yana jan shi ,gefanshi kuma daya daga cikin
budy gard dinshi ne, a zaune , Tony yayi parking din motar a inda a ka tanada, Nasir ya fito
daga Motar hannushi rike da wayoyinshi, yayi wani haske sosai sabida yadda hutu ya zauna
yana sanye da kananun kaya as'usel kamar ko da yaushe kanshi sanye da wata person cape
mai uban tsada, kai tsaye part din Momy ya nufa , Giss ya bi bayanshi rike da jakarshi da wasu
takkadunsa ,kana ganin yadda yake tafiya kasan yayi bala'in gajiya, ga wata shegiyar yunwa
tana sasakar cikinsa tamkar zata cinye masa "ya"yan ciki, da kyar yayi sallama falon ya zube
kan kujera ,kusa da bakin kofa cikin gajiya ya ce "Ya Allah"!
Giss ya tsaya a kanshi yana zare ido, Nasir din ya waigo kawai ya mika mishi hannu batare da
yace komai ba.
Da sauri ya mika masa karamar jakar hade da takkadun hannunsa , kawai yayi mishi alama ya
tafi, ko da ya fita ma sai ya tsaya nan bakin kofa kawai yana bin harabar gurin da kallo



Momy ta sauko daga sama sabida jin motsi, Sam bata tsammaci shigowarsa ba yanzu, cikin
mamaki takaraso inda yake zaune tana kallonshi ,tace"My Son yau da wuri haka"?



Ajiyar zuciya ya sauke yana Dan ya mutse fuska yace"Wallahi Momy nagaji ne ,ayi ta abu daya
babu ji babu gani ,yau hutawa zanyi duk mai

Please Login or Register in order to submit comment