You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace"wallahi mutukar a ka
daura masa aure da Maryam sakinta zaiyi sabida haka maganin ayi kar a fara.




Hankali Alhaji Hassan yayi mugun tashi sai zufa ce take keto masa Abokanshi suka kewayeshi
suna tambayarshi ba'asi




Malam Ya'u yana zaune kanshi a kasa tunda wani abokinshi ya kawo mishi daya daga cikin
hotonan Maryam da suke yawo a cikin Jama'a sai kukan zucci yake yanzu wai diyarshi ce cikin
wani hali irin haka gashi kwata-kwata babu fuskar Anwar din sun rufe Dan kar a gani

Ya san Maryam tsarkakkiya ce Sam baza ta aikata ba yasan sharri ne




Wani Maroki ne ya dauki hotan guda ya na tafiya yana roko ya karasa har inda Nasir ke tsaye
kusa da dady Mubina suna mamakin Al'amarin.



Mika masa Hotan yayi yace"Yallabai mai zakace a kan wannan Abu"




Nasir ya kalli hotan hannunshi, gabanshi yayi muguwar faduwa, kamar yanzu abin ya faro hotan
Maryam ne da Anwar cikin mota kwanakin baya

*innalillahi wa'innailaihi raji'un*
[08/06, 19:50] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*110*

Da sauri ya karbi hotan ya yagashi gutsi-gutsi hankalinshi a mugun tashe ya shiga gida, ganin
yanayi da ya shiga yasa Hankalin Momy din yayi mugun tashi kafin ta ankara ya fadi bakin kofar
dakinshi sai wani irin nishi yakeyi tamkar zuciyarshi zatayi bindiga,

Da sauri Momy ya karaso gurin ta kamashi ta rike tana salati sai kokarin cire masa babbar rigar
jikinshi take ganin yadda yake ta zabga gumi, bakinshi sai karkarwa yakeyi ya gaza furta komai
gashi so yakeyi yayi magana amma ya kasa, Momy ta mike daga gurin hankali a tashe ta nufi
kofar fita da kyar ya jawo maganar daga bakinshi yace"Momyna"



Momy tadawo gurin da sauri ta kama hannunshi ta rike tamau suka mike tsaye a tare



Kujera suka nufa ta zaunar dashi sai kace wani yaro karama tace"wai meye ne My son naga
kashigo hankali a tashe"
Shiru yayi kawai yana wani tunani Wanda shi kadai ya Yankewa kanshi



"Momy wace irin wasiyya dady ya bari kafin rasuwarshi kan auran Abdul da Maryam"?




"Myson, banaso ana maimaita magana guda a gabanka fa komai ya faru, yanzu maiye ya faru
kake wannan tambayar"?




"Momy Abdul ya fito cikin jama'a yafa cewar ya fasa auran yarinyar ko an daura sai ya saketa"



"Subahannallahi"
Momy tafada hankali a tashe ta cigaba da cewa "duk mai ya jawo wannan abin Kuma"?
Momy tafada cikin mamaki




"Momy sai na daure Anwar har karshan numfashinsa, Momy ni Anwar zai tozarta a idan duniya"
Nasir yafada yana wani huci, kafin Momy tace"komai ya mike da sauri ba tare da ya mayar da
babbar rigar ba ya nufi kofa



Momy ta biyo bayanshi da sauri tana kiranshi , batare da ya waigo ba yace"Momy ki koma
akwai jama'a a waje kar kifito Dan Allah"



Momy ta tsaya kawai tana bin bayanshi da kallo har ya fice daga gidan
[08/06, 19:50] +234 808 996 5176: [08/06/2019 2:31 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*111*

Jama'a duk sun kewaye Alhaji Alhassan wanda yake cikin tsananin tashin hankali da damuwa,
wai shi Abdul zai tonawa asiri a idan duniya, shi yanzu wazai share masa hawaye gashi ya tara
mutane bai sai mai zai dasu ba, yana tsaka da wannan tunani yaji muryar maroki yana cewa
"Alhamdullahi Tabbas kai dan halak ne Dan gadon alkairi dan na gada ba Dan haye ba, Allah
yaja zamaninka Yaro mai halin manya, yanda, Ubangiji Allah ya tayaka roko, Maryama kin tsinci
dami akala, kukanki ya kare da izinin Allah, Nasuru ya karbi aurenki a madadin Abdul latif, Allah
yasanya alkairi ubangiji Allah ya tayaka roko jarimin Namiji"

Kankace kwabo guri ya hargitse da hayaniyar jama'a da ta maroka kowa da abinda yake cewa




Lokacin da Alhaji Alhassan ya tsinkayi abinda wannan marokin yake fada wani irin farin ciki ne
ya lullubeshi, lallai Nasir ya haifu cikin Dan uwanshi Alhussen, wai yau Dan da ya haifa shine ya
tozarta shi a idan duniya, kuma yaron da suka dauka a matsayin Mara kunya shine ya rufa
masa asiri, dama haka duniya take.




Dady Mubina yaji babu dadi a zuciyarsa ganin yadda al'amarin ya sauya amma da yake ya iya
allonshi ko a fuska bai nuna ba a kaci gaba da hada-hada dashi.




Malam Ya'u ma yaji wani iri lokacin da yaji daga bakin marokin, Sam abin bai kwanta masa
ba,domin yanzu shi lamarin masu kudin nan ya soma bashi tsoro.
[08/06/2019 3:11 PM] ®Binta Umar Abbale: Ba tare da bata lokaci ba limamai da wakilai suka
suka fara kasa goro da Alawa, cikin hukunci ubangija a ka fara daura auran Nasiru da Mubina
sannan a ka daura da Maryam.



Nasir ko ya sha yabo da roka gurin maroka photo kuwa babu adadi duk inda ya yi suna biye
dashi haka manyan mutane suka rika janshi suna photo dashi domin abin da yayi ya mutukar
burgesu sosai suka dinga ya ba masa




Hayaniyar gurin ce ta fara sashi ciwon kai da ya lura idanun mutane ya Dan dauke daga kanshi
kawai ya gudu gida




Yana shiga ya ga Momy a tsaye a harabar gidan fuskarta sai fitar da annuri takeyi, duk abinda
ya faro a kunnenta ya faro Nasir bai taba faran tamata irin yau ba
Tun kafin ya karaso inda take tsaye ta cimmasa sai kawai ta rungume shi tsam tsam! Shima ta
sanya duk hannuwanshi ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya




Momy tace"My son baka taba faranta min ba irin yau Allah yayi maka albarka Myson ubangiji
Allah ya tayaka riko, inama dady dinka yana raye ban san inda zai kai farin cikinsa ba, lallai ka
cika Dan halak Myson Allah yayi maka jagora"



Dago tayi yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta hawaye ya gani a kwarmin idonta sai ya sanya
ya stunsa biyu ya na goge mata




Fuskarshi babu yabo babu fallasa yace"Momyna a yanzu babu abinda zanyi in faranta ran dady
duk da baya raye a doran duniyar nan illa in kaunaci abinda yakeso Momy ni nasan irin kunci da
damuwar da nake shiga duk lokacin da na tuna a irin yanayin da muka rabu da dadyna, wallahi
ina shiga cikin matsanancinyar damuwa, bani da kowa Momy sai ke, nasan hakan da nayi kema
zai faranta ranki ko"?




Momy ta girgiza kai kawai hawayen da take kokarin boyewa ya zubo a fuskarta Nasir ya fama
mata wani miki a cikin zuciyarta




Tace"Myson ka Riga ka gama min komai a rayuwa ta, yanda kake min biyyaya in sha Allahu
kaima "yayanka sai sun bika wannan nauyi kuma da Allah ya Dora maka Ubangi ya baka ikon
yin rikeshi, insha Allahu Allah zai tsare maka rayuwarka da kai da zuri'arka, My son bazan taba
dai na yi maka addu'a ba.




"Momy nagode sosai Allah yakara girma"
Yafada fuskarshi cike da murmushi
Tare suka shiga falo Momy na rike dashi tamkar wani zai kwace shi sai tsokanrshi takeyi ango
babu babbar Riga




Ya zauna cikin kujera yana dafe kanshi yace"Momy in banda kin damu ni ina ruwana da wata
babbar riga, ko dazu ma da nasa damuna tayi wallahi




Tace"Yanzu dole ka rika sanyawa sabida girma ya hau kanka"




"Momy wane irin girma kuma"




"Na aure gashi kana da mata biyu"




"Momy ko mata hudu gareni babu abinda zai hanani sanya kananun kaya"
Yafada yana tabe baki



"Nasan bazaka fasa halinka ba ai"
Momy tafada tana kokarin mikewa tsaye
Tace"a kawo maka abinci ko"?



"A'a Momy ruwan tea zan sha ya isa"
Yafada yana kallonta sabida yasan dole sai tayi magana




Hararashi tayi tace "baka isa ba kaji nafada mak....
Sallamar su Alhaji Alhasan ce ta katse Momy, fuska a sake ta amsa tana musu barka da zuwa




Momy ta nuna musu kujeru tace bisimillah Ku zazzauna




Cikin mutumci suka gaigaisa da juna, Alhaji Alhassan yayi gyaran Murya yana kallon Momy
yace"tabbas Hajiya Aminatu kin haifu kuma kin haifi Dan halak, yafada yana nuna Nasir ya
cigaba da cewa Wannan yaro ya rufa min asiri a lokacin da Dan Uwanshi Abdul latif ya so ya
tona min a siri a cikin jama'a
[09/06, 00:18] +234 808 996 5176: [08/06/2019 7:23 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*112*
Alhaji Alhassan ya cigaba da cewa "Nasiru babu abinda zan ce dakai, ka rufa min asiri koma ka
cika Umarnin da mahaifinka ya bari ubangiji Allah ya tayaka riko yayi maka jagora, Allah ya rufa
maka asiri ya kareka daga sharrin masu sharri"



Fuska a sake Momy tace"wallahi babu komai Alhaji dama duk abinda kaga ya faru to dama
haka Allah ya hukunta Allah ya rubuta Maryam ba matar Abdul bace shiyasa haka tafaru kuma
dama mutum bai taba auran matar wani ba, ni dai abinda nakeso don Allah karkayiwa Abdul
baki ka qaddara cewar dama Allah bai nufa Maryam zata zama matarshi ba"




"Duk abinda ya faru ya wuce agurina Hajiya shi kuma abinda yayi kanshi ya cuta ba wani ba
gaba zaizo yana nadama, yayi nufin tozarta yarinyar mutane sai Allah ya rufa mata asiri dake
batada hakkinsa"




"Momy ta sauke ajiyar zuciya sannan tace"wallahi Alhaji banji dadi wannan abu ba

"Allah yasa haka shi yafi alkairi"




"Alkairin kenan ma ki kwantar da hankalinki"
Alhaji Alhassan yafada yana kokarin mikewa tare da jama'arsa




Nasir ya mike ya biyo bayansu,

Da sauri Momy ta dauko masa babar rigarsa ta biyosu a baya ta mika masa wai lallai sai yasa



Dole tasa ya karba yasa tare da sa bakin Alhji Alhassan yace"a kwai sauran jama'ata dole zaka
fito ku gaggaisa sosai domin dazu bansan lokacin daka gudo gida ba"




Momy tasa dariya gami da cewa"kamar ka manta halin Dan naka Alhaji kasan kwata-kwata
baya son jama'a fa"




Shima dariyar yasa yace" dole yanzu yayi hulda da jama'a yadda nauyi ya hau kanshi yanzu
yazama cikkaken mutum"

Momy tayi murmushi ita kadai tasan farin cikin da take ciki




Sai data ga ficewarsu sannan ta koma ciki




To ban garan su Maryam kuwa lokacin da labari iskesu, kasa katabus sukayi jikinsu yayi sanyi,
Aunty tafi minti ashirin tana jajanta abun , Nasir ne ya auri diyarta Maryam anya wannan Abu ya
hadu

Sai ta dinga tuhumar Nafi'u yadda a kaiyi haka tafaru, nan ya warware mata dukkanin abinda ya
faru

Maryam kamar ta mutu Dan bakin ciki kuka takeyi wiwi, babu Abinda zata cewa Anwar sai dai
tace "Allah yayi mata sakayya wannan tozarcin da yayi mata cikin jama'a
[08/06/2019 7:42 PM] ®Binta Umar Abbale: Shi kuma Abdul, ta barshi da Allah yadda yaci
amanarta bazata taba yafe masa ba, in ta tuno wai ita matar aure ce kuma matar Nasir sai
gabanta yayi ta mugun faduwa, Ya Rabi tayi tayi da ita tayi shiru abin ya gagara ,




Malam ya shigo yana sa6e babbar riga kana ganinshi kasan yana cikin tsantsan farin ciki




Kawai ya taddasu sunyi jingum jingum sai kace gidan makoki, ya bisu da kallo daya bayan daya
kana ya mayar kan Maryam wacce ke rakube gefan kujera tana shirgar kuka kamar wacce a kai
ma mutuwa




Ranshi ya baci ya daka mata tsawa gami da cewa"kukan mai kikeyi Maryamu"?




Ya Rabi tace"wallahi kuka take tun da taji labarin abinda ya faru, anyi anyi tayi shiru taki yi"




Zama yayi cikin kujera yana fuskantar ta yace" wani irin kuka zakiyi Maryamu ke da Allah ya
rufawa Asiri lokacin da a kaso a tona miki, tabbas nasan a kwai abinda Allah ya boye a wannan
al'amarin,
Abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankalinki kina tare da albarkamu insha Allahu zakiga
alkairi a rayuwarki mutukar kika yimana biyyaya, nine mahaifinki na kuma karbi sadakinki na
kuma bawa Nasiru Auranki a madadin Abdul"
Malam ya karashe maganar gami da zira hannu cikin aljihun malin malin din dake jikinshi ya ciro
kudi yace"ga kudin sadakin ki Maryamu Allah yayi miki albarka ya baki zuri'a tagari tare da "yar
uwarki abokinyar zamanki"

Maryam tana kuka ta sanya hannu bibbiyu ta karbi kudin dake hannun mahaifinta
[09/06, 19:26] +234 808 996 5176: [09/06/2019 2:23 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*113*
Da kyar Ya Rabi ta rarrashi Maryam ta bar kukan da takeyi ta sanyata tayi Wanka ta fito mata
da wani uban les blue colour yayi mugun yi mata kyau abinka da farar fata ta sata tayi kwalliya
dai-dai misali dama Maryam bata da matsalar gashi kullum cikin gyarashi take, dan haka Ya
Rabi ta kara gyara matashi sosai ta fito mata da mayafi pink colour hade da yari da sarka
fashion munti colour set din Takalmi da jaka iri daya masu bala'in kyau da tsada,kan kace
kwabo Maryam tafito Amarya sosai tayi kyau, haka "yan uwan mahaifiyarta suka sanya ta a
gaba suna ta bata baki kan ta godewa Allah akan sauyin da yayi mata, dama haka shi yafi
alkairi a rayuwarta




Lokacin da Mubina taji labarin abinda ya faru sai da takusa yin dan Karamin hauka, kamar ita
ace zatayi kishi da wannan yarinyar tasan tafita komai na rayuwa ilimi kudi wayewa nasaba uwa
uba kyau ita a ganinta tafi Maryam komai da komai sabida haka taci alwashin akan sai dai Nasir
ya zaba ita ko Maryam din domin bazata taba yin kishi da wannan jahilar ba.




Kwayenta sai zugata sukeyi kan in taje kar ta saurarwa Maryam kuma kar ta sake ta yadda su
zauna gida daya da ita domin babu aji.

Hanifa kuwa dariya take tana farin ciki a fili tafito tace"wallahi haukan bazan kike domin ko
makawo ne ya sha fa ki ya shafa kishiyarki yasan tafiki kyau, nesa ba kusa ba sabida haka ki
daina wani hura hanci"




Mubina ta rika zaginta kamar "yar maguzawa a kan me zatace Maryam tafita ita irin matan nan
ne masu San kansu komai sun fi kowa iyawa




A waya ta kira Nasir din tace masa ita Sam bazata zauna gida daya da wata wallahi kuma sai
dai ya zaba Ita ko Maryam




Lokacin yana tare da Momynsa kuma duk taji abinda Mubina tace hankalinta ya tashi, tun ba'aje
ko ina ba Mubina tafara shigo da tsirfa dama kwata kwata ita tasan Maryam ba zata damu ba
Mubina ce abin ji



Ganin Nasir din bai bata amsa ba ya kashe wayarsa tace"My son wane mataki zaka dauka ne
nifa banason rigima kuma ba nasan abinda zai daga maka hankali"
[09/06/2019 2:42 PM] ®Binta Umar Abbale: Tsaki yaja yace"Momy karki damu babu macan da
ta isa tasa na sauka daga kan ra'ayina , mutukar Mubina tana San zama dani dole tabi
umarnina, Momy bani da ra'ayin raba gida kuma bazan raba ba tare zasu zauna da juna
shikkean nagama magana"




"Myson ina ganin ka raba musu gidan kawai zaifi alkairi"



"Momy ki kyaleni Dan Allah wallahi Momy Mubina bata isa tasa ni nayi abinda banyi niyya ba,
kawai ki bar maganar,ke dai kawai ki cigaba da min addu'a"




"Toum shikkenan My son Allah ya taya riko ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu"




"Ameen Momyna abinda nake so inji kenan"

"Yanzu cikin Estet din zaka zauna ko zaka fita"?




A jiyar zuciya ta sauke gami da cewa "gidan Dady dake Tarauni nan nasa a gyara dazu munyi
waya da mai akin za'a mishi fanti ko wane part kowa zai dau daya tunda uku ne shikkenan
naraba gaddama babu wacce zata ga "yar uwarta sai taso"




"Kayi dabara Myson"
Momy tafada ta cigaba da cewa "yanzu ni kadai zaka bari a gidan nan ko"



Dariya yayi yace"Momy ko kinaso in zauna nan din"?



Itama dariya tasa tace"A'a babu ruwana ni bana son zama da sirika, Myson ina nan ina maku
fatan alkairi
Murmushi kawai yayi yana girgiza kai
Ya mike tsaye gami da cewa "zan shiga inyi Wanka in fito yanzu zan Dan fita a kwai wasu baki
da za muyi daga Fatkwat abinda ya hana Abbas halarta daurin auran kenan, gashi na kashe
wayoyina dole nasan zasu nemeni"




Momy tace" Yau dai daya su yi maka uziri yau ranar auranka ma sai ka fita My son"



Murmushi yayi yace"Momy kenan"
[11/06, 11:02] +234 808 996 5176: [10/06/2019 6:00 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*114*

Wanka yayi ya sanya wata shadda mai uban tsada wagambari fara kal ya sanya hula fara
takalmi mai gidan dan tsaya baki sai a goganshi na silver mai mugun tsada sosai dressing din
yayi mishi kyau kana ganinshi kasan ango ne hannushi rike da farin glass ya fito sai zabga
kamshi yake
Momy na zaune tana waya da mutananta tana fada musu yadda al'amarin ya kasance,
yace"Momy zan fita ni sai bayan isha'i zan dawo"




Momy ta mike ta biyo bayanshi tace"yanzu yaushe zasu tare iyalin naka"?



"Gobe insha Allahu
Za'ayi komai a gama"

"To Allah ya kaimu lafiya"
Momy tafada cikin farin ciki



Sai da ta ga fitarshi daga gidan sannan ta koma ciki



Ban garansu Mubina kuwa buki suke sosai da sosai babu yadda bata dayi da Nasir ba a kan ta
shirya party tanaso ya hallata amma yace mata babu inda zashi dan bashi ya sata ba, haka dai
tayi hidimar bikin ita da kawayenta
Wata kawar Ya Rabi ce tazo ta dauki Maryam ta kaita gidanta ta dauko mai mai kunshi gami da
gyaran jiki, kunshi yayi kyau sosai baki da ja daki guda ta sata ta turara mata jiki gami da
gyaran fata sai da fatar Maryam tayi mulmul sosai Hajiya Aisha ta shirya Maryam sosai sannan
ta dauketa a motarta suka nufi wani hadaddan boutique ta dinga jidar mata kananun kaya masu
kyau da tsada.




Hajiya Aisha tana dreving ta kalli Maryam dake kusa da ita tace"kinga wannan kananun kayan
da na sai mai ki in kinje gidan mijinki su zaki riqa amfani dasu, kar ki tsaya kunya kinji ko tunda
kinga kina da kishiya




Kiyi kokari ki kama mijinki a hannu tunda dai Allah ya qaddara wannan yaron Mijikin ne sai ki
godewa Allah, yanzu sauran yaki yana gareki
[10/06/2019 8:00 PM] Binta Umar Abbale: Hajiya Aisha ta dage tana koyar da Maryam dabarun
zama da miji da yadda a ke kula dashi tace "su mazan wannan zamani da kike ganinsu sai da
rarrashi da siyasa, sabida haka sai in zage damtse gurin ganin kin kama mijinki a hannu"




Maryam kuwa sunkuyar da kanta tayi tana jin kunya Hajiya Aisha jin irin abinda take fada ita
kam kunya take ji tana ganin bazata iya amfani da wadan nan kananun kayan ba




Sai daf da magariba suka shiga gida,

Ya Rabi taji dadin abinda kawarta kuma aminiyarta tayi mata ganin yadda Diyarta Maryam take
walwali ga wani mugun kamshi tana zabgawa duk inda ta gifta




Bayan sallah magariba Ya Rabi tace ai ya kamata su shiga bangaran Momy domin su gaisheta
kuma suyi mata godiya da fatan alkairi
Duk su ukun suka shiga gurin Momy ta karbe su cikin mutumci gami da kyautatawa



Ya Rabi tace" Hajiya sai mukaji wannan abin alkairi kuma"




Momy tayi dariya tace"ai haka Allah ya tsara dukkanin abinda Allah ya tsara babu mahalukin da
ya isa ya hana, Allah yayi Maryam matar Nasir ce"




"Wannan abu haka yake hajiya, Ubangiji Allah ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Allah ya
bashi ikon kyautata adalci a tsakaninsu"



"Ameen ya rabbi nagode sosai"
Momy tafada tana kallonsu cike da murmushi




Ta cigaba da cewa gobe insha Allahu zasu tare a gidanshi dake tarauni kar ku wahalar da
kanku komai an tanada a gidan, Maryam kadai muke bukata,insha Allah kayan lefanta ma
zataje ta tadda a can"




"Hajiya Allah ya saka da alkairi ubangiji Allah ya kara arzuqi da wata mukan babu Cabinda
zamuce daku wallahi"
Aunty tafada tana sunkuyar da kanta




Momy tace "nasan dai Dota bata da matsala yarinyar tana da nutsuwa amma dai sai a kara ja
mata kunne sabida ba ita kadai zasu zauna ba a kwai "yar uwarta duk abinda zata gani ta
kauda kanta wataran sai labari




"Insha Allahu za'a yi mata fada Hajiya duk da cewar Maryam bata da kwarfinaya da yawa,
amma yau da gobe ta wuce wasa
Hajiya Aisha tafada cikin nutsuwa da dattako



Hira suka cigaba da yi cikin fahimta gami da wayewa dake Hajiya Aisha wayayyiyar Mace ce
kuma "yar boko shine dalilin da yasa Momy ta ji hankalinta ya kwanta da ita
[11/06, 13:58] +234 808 996 5176: [10/06/2019 10:17 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA
KUDI*
*115*
Nan sukayi sallahr isha'i Momy ta sanya mai aikinta Uwani ta hada musu abinci dole babu
yadda suka iya suka zauna suna ci suna mamakin karamcin Momy




Karfe takwas na daran rabar Lahadi Maryam ce durkushe gaban mahaifinta tana kuka sosai shi
kuma yana mata fada kan ta kula da auranta kuma tayiwa mijinta biyyaya da dukkanin abunda
ya umarce ta.




Aunty ma tayi mata addu'a sosai sannan tayi mata nasiha irin tama ta mata yi nayi bari na bari



Yaya Rabi daman ita kullum Cokin yiwa Maryam din nasiha



Dake babu jama'a sosai sabida basu wuce su biyar ba sai Momy tacewa drevar ya dauki
babbar mota kawai ta isa



Haka Ya Rabi ta sanya Maryam cikin mota tana gursheken kuka kamar ranta zai fita wai yau ita
ce ta auri Wanda bataso Wanda yayi mata muguwar tsana a rayuwarshi
[11/06/2019 7:09 AM] Binta Umar Abbale: Momy ta rungume ta a jikinta tace "kiyi hakuri Dota ki
zauna da mijinki lafiya da "yar uwarki nice mahaifiyar Nasir nafi kowa sanin halinshi duk wani
abu da kike tunani zai faru babu shi sai alkairi, ni da kaina zan damka masa amanarki shine ki
kwantar da hankalinki in kika iya zama da Nasir zaki ji dadinshi sabida yana da saukin kai duk
ranar da kika ga ya tashi yana muskilanci to mybe da akwai abinda yake damunshi ke zaki
dinga bibibyarshi tunda shi zurfin ciki gareshi, dan Allah Maryam ga amanar Nasir nan Na
damkata a hannunki kamar yadda ba bashi taki amanar ki lura da cinsha da shansa domin Sam
baya son cin abinci sai na tsaya a kanshi sannan"




Wani irin tausayin Momy ne ya kama Maryam babu abinda Momy zata nema ta Gaza yi mata
shi a rayuwarta sabida haka tayi alkawarin ko da Nasiru zai yankata gunduwa gunduwa za ta
tsaya ta rike amanar da ta karba




Wani irin gida ne mai bala'in kyau da tsari plate ne mai dauke da part uku sai katowar haraba
gurin ajiye motaci ma na mussaman ne can gefe lambu ne an kewaye shi da wasu karafuna
sun sha ado gurin gress kafet ne a ko ina na gurin yanayin gidan kamar irin gina ginen
kasashan waje ko ina tsaf tsaf Ma'aikatan gidan sai kaiwa suke suna kawowa ko wanne da
aikinshi




Nura tayi parking din mota Momy ta fito hannuta rike da Maryam Ya Rabi da sauran jama'a suka
fito suna bin gidan da kallo cike da kauyanci sabida kalar faint gidan ma abin kallo ne Momy ta
fito da waya tana neman Nasir ta kira ya kai sau uku ba'a daga ba, gashi tana ring sai ta kashe
wayar tana tuna in wane part din ne na Maryam tana tsaka da tunani motoci suka fara shigowa
gidan dauke da amarya Mubina da ta wagarta, motoci sun kai goma




Kan kace kwabo gurin ya cika da hayaniya dangin Mubina suka dinga fitowa daga mota kamar
bazasu kare ba.
Wata yar Momynta ce ta hangi Momy tsaye jingene da mota ,abin ya bata mamaki yanzu yanzu
sukaje can gidanta domin su mikamata Mubina a matsayinta uwar miji ba ta nan abin mamaki
sai gata anan ko mai ya kawota oho




Har kusa da Momy ta karasa inda Momy take tace"Hajiya Aminatu ashe kina nan, yanzu yanzu
mukaje domin mu mika miki amarya kamar yadda al'ada ta gadar ba mu same ki ba"




Cikin nutsuwa da sakin fuska Momy tace"wallahi kuwa ai sabani mukayi domin bamu Dade da
fitowa daga gida ba nayi tunanin zan sameku anan, ai babu matsala ga "yar uwar tata ma yanzu
zan hadasu in yi musu nasiha"
Momy tafada tana kara damqe hannun Maryam




Hajiya Abu wato yayar Momyn Mubina ta dago kanta cikin mamaki tana kallon Momy kana ta
mayar da kallonta kan Maryam wacce sukayi kafada da kafada da Momy cikin zuciyarta tace
wato ita ce ta dauko ta ma lallai yarinyar tana da fada a gurin Momy




Sai ta hau yaqen karya tana danne abinda yake zuciyarta kamar gaske tace"Masha Allahu haka
yayi, bari mu bude part din Mubina sai mu shiga ciki tunda dai ita ce uwargida"




"To babu matsala"
Momy tafada cikin nutsuwa da dattako
Hajiya Abu ta kauce daga gurin cikin dinbun mamaki dole sai sun zage damtse kan Hajiya
Aminatu in ba haka ba burinsu baxai cika ba a kan Nasiru dole ne su ci arzigi su bar arziqi a
mazauninsa.
[11/06/2019 7:49 AM] Binta Umar Abbale: Momy taja tsaki abinda ba halinta ba tace"wallahi
wasu mutanen suna bani mamaki wai sai mutum yazo ya tadda mutane a guri ya kasa gaidashi
sabida girman kai Allah ya kyauta"




Ya Rabi tayi murmushi tace"Hajiya kenan aiko mutane kowa da irinshi sai hakuri"




"Allah ya sawaqe ameen"
Momy tafada tana kara kiran wayar Nasir din a karo na biyu
Gashi tana ring bai daga ba Momy jikinta ya bata babu lafiya amma ta barwa zuciyarta addu'a
kawai take masa




Hajiya Abu ta dawo gurin a karo na biyu tace"Hajiya Bisimilah"
Dukkaninsu suka rufa mata baya




Farlo a cike sai hayaniya suke Momy ta nufi wani bedrom dake falon tace"a shigo mata da
Mubina




Nan Hajiya Abu ta kamo Hannun Mubina wacce ke cikin kawayenta sai shewa sukeyi

Kwata-kwata babu kunya irin ta amare a tare da ita fuskarta tasha kwalliya kamar me ga wani
uban gashin ido da tsa in ta kalleka tamkar wata aljana mayafin dake jikinta ma figigi ne sai
taunar jingam takeyi abun dai babu arziqi
Cikin nutsuwa Momy take binta da kallo tana nazarinta tabbas Mubina bata da da'a ko kadan
tana zaune kan kujera har da Dora kafada daya kan daya babu abinda ya dameta




Momy ta sauke ajiyar zuciya tace"Mubina sauko kasa ki zauna kusa da "yar uwarki"




Sai da ta bata lokaci sannan ta sakko kasa tana wani ya mutse-ya mutse




"Alhmdullhi Allah kai ne abin godiya daka nuna min wannan rana da raina da lafiyata"
Momy tafada tana sauke ajiyar zuciya ta cigaba da cewa "Mubina ga kanwarki Maryam a
matsayinki na babba wacce

Please Login or Register in order to submit comment