You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/FTn1qlcoa83BAlCQEO7ZpH

*IYA RUWA...!*
(FID DA KAI)



BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


*First Class Writers*


Page 1



Yayin da tsinken agogo ya harba ƙarfe ɗaya na dare cif a daidai lokacin
Safiyya take safa da marwa a madaidaicin falonta cikin shirin kayan bacci,
matashiya ce wacce auren wuri ya sa dole ka kira ta da yarinyar mace, ƙara kallon
agogo ta yi a karo na babu adadi, kafin ta shiga ɗakin gado ta tofe yaranta biyu da
ke sharara bacci da addu'a, hijjabi ta saka har ƙasa ta fita zuciyarta cike da
fargabar yau kuma wane sabon shafin ne zai buɗe cikin littafin sauyin hali da
mijinta ya siyo kullum yake biya mata shi, tsayawa ta yi a tsakar gidan tana kallon
ko'ina kamar mai neman wani abu, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta doshi ɗakin da
yake mallakin mijin nata ta fara ƙwanƙwasawa tare da sallama.

Kamar yana jiran zuwan nata, cikin muryar da ke nuna ya fusata ya ce"Wane kuma
cikin daren nan!?".

Ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, sai da ta ajiye hijjabin ta zauna sannan ta aro
murmushi ta ɗora a fuskarta da sanyin murya ta ce"Abban Ni'ima wane ne zai shigo
maka ɗaki da tsohon daren nan idan ba matarka ba?"

Ya ɗauke kai yana haɗe gira, sannan ya ajiye wayar dake hannunsa, ya janyo babbar
wayarsa ta aiki ya fara taɓe-taɓe, suka yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce"Aiki
kake yi ne?"

"Aiki nake mene ne?" Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba.

Ta ce"Idan editing ne sai na taya ka ai, na ga dare ya yi, Abban Ni'ima kai ta
matse kanka da aiki, ka fita tun safe kana can kana aiki, dare ma kuma ba za ka
huta ba?"

Kamar mai jira, sai ya rufe wayar ya ce"Safiyya ke da 'ya'yanki ba tun safe kuke
cin abinci ba har dare? Ko kuna hutawa? Kin ga ba na so fa ki dinga ƙure ni, kar ki
kai ni bango!".

Ta ce"Allah Ya huci zuciyarka, ni ban faɗa da wata manufa ba". Sannan ta shiga
banɗakin da ke cikin ɗakin ta yi alwala ta yi sallah raka'a biyu, ta hau katifa ta
kwanta, sai dai sam babu bacci a idonta sai saƙa da warwara da ta yi ta yi a
zuciyarta, ba ta wani jima a kwance ba ta ga ya matsar da wayar ya ɗakko ɗaya wayar
wacce ita ce yake chart da sauran abubuwa, da alama chart yake yi domin ta ga yana
ta rubutu da murmushi a fuskarsa.

Har ya gama ya ajiye wayar, ya zo ya kwanta a gefenta bacci ya kwashe shi ita ba ta
runtsa ba, tunanin sauyin da ya ƙi yarda da ya sauya ɗin take yi, daga shi sai
'ya'yan da Allah Ya ba su take jin sanyi a tare da su, idan rayuwar auren su ta ci
gaba da tafiya a haka tana da tabbacin watan shiga ƙuncinta ya kama, wanda babu mai
share mata hawaye sai shi amma ace yau shi yake son saka ta hawayen? Tabbas ruwa ba
ya tsami banza.

Washegari bayan ta yi sallar asuba ta koma ɗakinta bisa al'ada, ƙarfe bakwai da
rabi ta kammala abin da za su ci, saboda Abban Ni'ima ƙarfe takwas yake fita, su na
zaune a falo ita da yaran suna jiran shigowar shi, domin sun saba a tare suke cin
abincin, ya ɗaga labule ya leƙo cikin shirin fita, ya musu kallo ɗaya ya fice, ba
ta yi zaton gidan zai bari ba, sai da ta ji tashin babur ɗinsa, ta haɗiyi wani yawu
mai ɗaci, kafin ta ɗauki waya ta kira shi, amma bai ɗauka ba, abincin suka fara ci,
Ni'ima ƴar shekara huɗu ta tambaye ta "Yau ban da Abba?"

Ta ce"Ya ci na shi kuna bacci".

Ta gama duk aikin gidan wajen ƙarfe goma tana kwance tana duba wayarta, saƙon shi
ya shigo, ta buɗe sai ta ga gargaɗi ne yake yi mata a kan kada ta sake kiran shi
alhali ta san yana kan abun hawa, ko so take yi ya yi hatsari? Murmushi kawai ta yi
ta ci gaba da harkokinta, da wannan tunanin sauyin na shi ta wuni, a da tare suke
karin safe yana ba wa ƴaƴan shi a baki cike da nishaɗi, ya yi musu kyakkyawar
sallama bayan sun tsayar da abin da za a girka daga rana zuwa dare, sai ta faɗi
abin da take buƙata na cefane, shi kuma zai sa a kawo mata, dab da magriba yake
dawowa daga kasuwa, idan ya yi sallah ya ci abinci daga masallaci gidan
mahaifiyarsa yake wucewa, inda ƙarfe takwas da rabi ta yi ya dawo gida, wataran ma
ana idar da sallar isha'i, idan yara ba su yi bacci ba sai a yi ta wasa da su, idan
sun yi bacci sai su yi firar su, idan yana da editing ya ɗauko waya ya yi ta tsara
hotunan atamfa, less, shadda da sauran su, kasancewar sana'arsa kenan a kasuwa, da
ganin yadda yake yi kullum ita ma ta koya, wataran yana ba ta ta taya shi, daga nan
kuma sai su kwanta bacci. A tsarin gidan ɗakuna ne guda huɗu wadatattu sai kitchen
da banɗaki, ɗakin da take ciki ciki da falo ne, sai wani fallen ɗakin da banɗaki a
cikinsa, kusa da shi akwai kitchen da banɗakin tsakar gida, sannan ɗakinsa shi ma
falle ɗaya ne da banɗaki a ciki, akwai katifa da ƴan tsirarun kayansa a ɗakinsa,
amma ba ya kwana a ciki a ɗakinta suke kwana tare, sai da ya fara nuna mata wannan
canjin ne ya kwashe duka kayansa ya koma nashi ɗakin, sosai ta shiga damuwa saboda
ba ta son barin yaranta su kwana su biyu a ɗaki, duka-duka Ni'ima ce mai shekara
huɗu, Khausar biyu, amma da ya nuna dole sai dai ta zaɓi ɗaya ko shi ko ƴaƴanta sai
ta zaɓe shi saboda a zauna lafiya.

Da daddare haka ta yi ta zaman jiran shi, sai ƙarfe goma da rabi ya dawo, wani
abu da bai taɓa yi ba sai da babban dalili kuma bayyananne, a lokacin da ya shigo
tana ɗakinsa a zaune, saboda yau ɗin ta shirya tunkararsa don jin laifinta a gare
shi.

Sautin dariyarsa ta ji yana cewa"Kin ga yanzu dai na shigo gida, idan wannan
matar ba ta shigo min ba zan kira ki, sai ki ƙarasa mini ko?" Ya ƙarashe maganar
cikin wata matacciyar muryar da ya jima bai yi mata irinta ba.

'Wannan matar!' Ta jinjina kalmar a zuciyarta, lallai ba a shaidar miji, baban
Ni'ima da wataran idan ta ci kwalliya har ɗaukarta yake yi ya juya yana ce mata ƴar
budurwarsa ko ya ce mata Babynsa, har ce mata yake yi shekara biyar da aurensu amma
gani yake kamar har yau ita budurwa ce, ta ƙi ta girma, shi ne yau yake kiran ta da
kalmar matar nan? Lallai akwai matsala.

"Baby ke fa na lura sam ba kya so na yi bacci, yanzu bayan auren ma haka za kina
yi mini wannan dabaibayin duk ki kashe mini jiki ki hana ni aiki ko...?"

Bai ƙarasa ba, wayar ta suɓuce ta faɗi, sakamakon ƙarasa shigowa ɗakin da ya yi,
suka yi ido huɗu.
"A'uzubillahi! Subhanallah! Haba Safiyya wannan wane irin rashin mutunci ne haka za
ki firgita ni? Ko gyaran murya ai sai ki yi na san da mutum a ɗakin, wannan ai
wulaƙanci ne!" Ya ƙarasa maganar yana ɗaukar wayar ya yi kicin-kicin da fuska.

Ta yi jarumtar danne hawayeta, ta ƙirƙiri murmushin takaici ta ce"Ka yi haƙuri,
kuma ni dai ban ga wani abun firgita ba har da yar da waya, sai dai idan dama dai a
firgicen kake".

Sai kuwa ya zaburo"Ni kike cewa a firgice? Kina nufin ni mahaukaci ne fa kenan!
Bantan ubancan ni da gidana ki ce mini mahaukaci? A lallai Safiyya na yarda halinki
ya canza".

Ta ce"Duka dai magana ta ƙare, ga abincinka nan".

A fusace ya ce"Ba zan ci ba! Kuma daga yau kar ki sake shigo mini ɗaki sai idan ni
na neme ki"

Ta ce"To in sha Allah! Amma ina so mu yi magana kafin na tafin".

Ya zauna bai ce komai ba. Sai ta fara hawayen da take ta dannewa, ta ce"Abban
Ni'ima me na yi maka ka canza mini? Gabaɗaya kana nema ka juya mini baya, ka daina
ba ni kulawar da ka sabar mini da ita, hatta yaranka ka fara janye jikinka daga
garesu, alhali ka san ni da su ɗin ba mu da wanda ya fi ka a duniyar nan, wannan
sauyin naka ba ƙaramin barazana ba ne ga rayuwarmu, don Allah ka ƙaryata hasashena
kar ka rabu da ni saboda wani dalili ko laifin da ban san ina aikatawa ba".

Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba, har tsawon lokaci ita kuma tana kuka mai
shassheka, sannan ya ce"Tun da kina son jin dalili to za ki ji in sha Allah, gobe
idan Allah Ya kai mu su Yaya Fa'iza za su zo, su za su faɗa miki komai".

Daga haka ya shige banɗaki, ita kuma ta tashi ta koma ɗakinta, ta zauna tana ta
tunanin sabuwar rayuwar da take shirin tunkaro ta, daga wayar da ta ji yana yi
tabbas ta san wata macen ce ta bankaɗa labulen rayuwarsu take son shigowa, ita dai
ba za ta ga laifinsa ba don ya ƙara aure idan hakan ya tabbata amma wannan sauyin
nashi ne babbar damuwarta, domin alama ce dake nuna idan an yi auren ba lallai a
wanye lafiya ba, ita kuwa barinta gidan aurenta tamkar tonon asiri ne a gare ta, to
ina za ta nufa idan ta bar gidan? Da wannan tunanin ta kwana, tana fargabar wayewar
gari saboda zuwan ƴan'uwan mijin nata da ta tabbata ba ƙaunarta suke yi ba.

Bayan sallar la'asar ta gama aikinta tsaf ta yi kwalliyarta mai haske, tana ɗan
duba wayarta suna fira da yaranta jifa-jifa, ta ji sallamar ƴan'uwan mijin, gabanta
ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta, sai da ta haɗiyi wani yawu sannan ta je ta
buɗe musu ƙofa, dukan su da yayyunsa da ƙannensa su shida cif, bayan sun gaisa
yayarsa Fa'iza wacce ta fi kowa zafi da tsanarta ta miƙo mata ɗan ƙaramin kwalin
cingam ta ce"To Safiyya Allah Ya kawo abin da muke ta jira!".

Mariya ƙanwarsa ta ce"Ƙwarai kuwa lokaci ba na mutuwa ba, na tsantsar farincikin
samun ƙaruwa".

Ta karɓi cingam ɗin tana rarraba ido da alamar neman ƙarin bayani.

Fa'iza ta ce"Cingam ɗin saka ranar auren mijinki ne, an ɗan jima fa da saka ranar
ma shi ya ce kar a faɗa miki, ga shi abu har ya matso saura sati huɗu in sha
Allah!".

Ƙirjinta ya yi wata irin bugawa da ƙarfi, ta daure ta ce"To Allah Ya kaimu, ya kuma
sanya alkhairi".

Suka amsa da amin, sannan suka shiga firar budurwar, a yadda ta fahimta Anti Saude
ce ta haɗa shi da ita, har hotonta suka kunno suna ta yabonta, ita dai kamar ta ce
su nuna mata, sai dai ta yi shiru har suka tafi, suka barta cikin wani irin yanayi.

A halittarta ba mace ba ce mai zafin kishi, tana jin ko mata nawa zai auro za su
zauna lafiya matuƙar dai ba zai tauye mata haƙƙinta ba, ko a yanzun ma ba auren ne
damuwarta ba, sauyin halinsa ne kaɗai ya dame ta.

Da daddare bai shigo gidan da wuri ba, sai sha biyu, tana ɗakinta tana jiran shi,
duk da baccin da yake neman kwantar da ita, tana jin shigowarsa ta fito tsaye ta yi
a ƙofar ɗaki tana hango shi yana saka sakata.

"Safiyya me ya hana ki bacci?" Ya tambaye ta yana shirin shigewa ɗaki.

Sai ta bi bayansa tana faɗin"Ta ya zan yi bacci ban jira ka shigo na ga ka ci
abincinka ba?"

Ya yi dariya ya ce"Haba dai abinci yanzu sai ka ce dai mai yin sahur? Idan kika ga
na wuce ƙarfe tara a waje idan na dawo ba ma sai kin yi mini tayin abinci ba, indai
zan je gidan su yarinyar nan ba ta rasa cika min ciki da abubuwa".

"Yarinya?" Ta tambaya duk da ta san abin da yake nufi.

"Zancen kike so Safiyya, sai da safe". Ya faɗa zai shige ɗakin.

Ta yi saurin ƙarasawa ta ce"Ai bayan wannan ma har da maganar da nake so mu yi".

Ya ce"Tsakar daren nan sai ka ce wasu aljannu? Ai sai mu bar wa safiya ko?"

"Yanzu nake so!" Ta faɗa a ɗan hasale.

Ya ce"Da dai ba kya yi mini musu". Ya shiga ɗakin, ta mara basa baya.

Bayan sun zauna ta ce"Jiya na tambaye ka dalilin canjin halayenka, sai ka ce mini
yau su Yaya za su zo..."

"Ba su zo ba?" Ya katse ta.

Ta ce"Sun zo, amma maganar da suka zo da ita ba ta da nasaba da tambayar da na yi
maka".

Ya ce"Ikon Allah! Ba su faɗa miki zan yi aure ba?"

Ta ce"Sun faɗa mini, amma me ya haɗa ƙarin aurenka da zamanmu? Me ya haɗa ƙarin
aurenka da canzawar halinka? Idan za a ƙara auren juyawa ta gida baya ake yi, a
banzatar da 'ya'ya? Idan za a yi sabo sai a jefar da tsoho tun kafin sabon ya shigo
hannu a tabbatar da ingancinsa? Ka ba ni tsoro, na fara tunanin anya kuwa za ka yi
adalci a tsakaninmu?"

A hasale ya nuna mata ƙofa ya ce"Tashi ki fita! Na ce idan kin gama zagina ta shi
ki fita, Safiyya har ni yau za ki ce ba ni da adalci dama jiya kin ce mini a rikice
nake ba ni da hankali? To an barzatar da ku ɗin, sai ki ɗauki mataki!".

Ta ce"Baban Ni'ima babu buƙatar tsayawa yi maka bayanin ba haka nake nufi ba, domin
ka fi kowa sanin halina, ka san abin da zan yi da wanda ba zan yi ba, na gode da
komai, aure kuma Allah Ya nuna mana lokaci, ya kuma ba ku zaman lafiya. Ta yi
murmushin da ya fi kuka ciwo ta tashi ta bar ɗakin, tana tunanin ta inda za ta fara
toshe wannan ɓarakar da ta shigo rayuwarsu babu zato.

Tun daga ranar bai sake cin abincinta ba tsakaninta da shi ta gan shi da safe su
gaisa, wataran ma ba ta ganin ficewarsa da daddare kuma ko ta ji dawowarsa ba ta
fitowa, tu rungumi yaranta su yi bacci lafiya, har tsawon sati biyu, a lokacin
bikin ya rage sati biyu kenan. Ya ɗin tana son yi masa zancen makarantar Ni'ima da
yake ta cewa za a kaita, shi yasa ta jira shi har ya dawo ƙarfe goma da rabi, yana
shiga ɗaki ta ƙwanƙwasa tare da sallama, ba ta jira amsawar shi ba ta tura ta
shiga, tsaye ta same shi yana ta danna waya, ta zauna ta ce"Sannu".

Ya juyo ya ce"Ciwo nake? Ke ma sannu!".

Ta yi murmushi ta ce"Dama magana nake so mu yi, akan makarantar Ni'ima, ka ga
wannan hutun za a ɗauki sababbin ɗalibai, ya kamata a kai ta".

Ya ce"Wai Ni'ima nawa take da za ki matsa a kai ta makaranta? Ki bari sai wata
shekarar kawai".

Ta ce"Shekararta huɗu fa, ƴan shekara uku ma ana kai su, ba na son zamanta haka,
don Allah a kaita".

"Ni dai na ce sai wata shekarar, idan kuma kin ga za ki iya to ki kai ta, ko kin
manta aure zan yi nan da sati biyu ina ta shirin hidima kuma ki kawo min zancen
Ni'ima da makaranta?" Ya faɗa yana kwamciya.

Ranta ya ɓaci ta ce"To shi kenan, Allah Ya kaimu wata shekarar".

Tana shirin fita ya ce"Idan Allah Ya kaimu gobe za ki yi baƙi".

"Baƙi?" Ta tambaya da ɗan mamaki

Ya ce"E wallahi, yarinyar nan ce za ta zo za ta ga yanayin gidan, tun da a nan zan
ajiye ta, sai ta duba ɗakunan a san yadda za a tsara zaman".

Kai tsaye ta ce"Ɗakuna ai a tsare suke, ni dai ka san inda nake ciki da falo ne,
sai naka, sai kuma idan wancen ɗayan za ka ba ta ai ko?"

Ya ce"E to! Sai ta zo ɗin tukunna, za ta duba har nakin a gani!".

Ta ce"Abban Ni'ima iya ƙoƙarina na kau da kai a kan lamarin aurenka, don girman
Allah kada ka ƙure ni, ta ya za a ce buduruwarka ta zo har cikin ɗakina wai ta zo
duba yanayin gida? To ban amince ba, kar ta sake ta zo min, ku tsaya a iya inda za
ka ba ta!".

"Za ta zo!" Ya faɗa ko a jikinsa.

"Ba za ta zo ba!" Ta faɗa a fusace.

Ya ce"To Allah Ya kai mu goben, zan ga waye mai gidan tsakanin ni da ke".

Daga haka ta koma ɗaki ta kwanta, zuciyarta tana mata zafi, ta kuma ƙuduri niyyar
babu wata yarinyar da za ta shigo duba mata ɗaki.
[5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA...!*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


*First Class Writers*
Page 2


Washegari da safe suna cikin karyawa ita da yara, ya shigo ɗakin ya zauna, tuni
ta daina girki da shi, saboda ko ta yi asarar shi ake yi, bayan ta gaishe shi ta
tura masa plate ɗin indomin da take ci tare da kofin shayi, ya ɗauki kofin ya kurɓi
shayin ya ajiye ya yi gyaran murya ya ce"Safiyya ya muke ciki?"

Ta ce"Da me fa?"

Ya ce"Maganar zuwan ƙanwar taki dai".

Ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima na ce maka babu yadda zai yiwu buduruwarka ta
shigar min ɗaki".

Ya ce"Amma kin san nan gidana ne ko? Don haka ina da ikon shigo da duk wanda na yi
niyya!"

Ba ta so a ja maganar har ta zama babbar rigima, don haka ta yi shiru, ya ce"Yawwa!
Bayan sallar la'asar ƙawarta za ta rako ta, me za ki dafa a kawo cefane?"

Ta ce"Duk abin da ka zaɓa shi zan dafa".

Ya ce"To zan aiko, ko ke fa amma da kin tsaya kina wani cijewa ke ba tsohon babur
ba? Ki saki ranki don Allah, idan ban da abunki kwana nawa ne ma za ta shigo gidan
ku zama abu ɗaya? Ni gidana na zaman lafiya ne babu zancen fitina in dai kin so".

Har ya gama ya fice ba ta sake cewa komai ba, ƙarfe sha ɗaya ya aiko da cefane,
kayan miya mai uban yawa kamar za a yi girkin sabga, da manyan kaji har guda uku ga
kuma jan nama da yawa, kwakwa ƙwallo da madarar gwangwani, ta yi murmushi bayan ta
gama gani, ta hau aiki, soye kajin ta yi tsaf ta kwashi rabi ta yi jar miya ta zuba
su, jan nama kuwa ta soya ta kai ɗakinta ta adana, ta dafa farar shinkafa, ta ɗibi
kwakwar ta yi lemo ta zuba sauran a firji, ta haɗa komai ta kai ɗakinsa ta ajiye,
sannan ta tura yaranta gidan maƙociyarta Maman Affan, ta fita ta siyo sabon kwaɗo
guda biyu, ta zo ta rufe ƙofar ɗakinta ta rufe kitchen, ta zuba sauran abincin a
kula ta tafi gidan Maman Affan ɗin.

Sun baje suna cin abinci Maman Affan ta ce"Wai wannan uban kajin fa Maman
Ni'ima?"

Ta yi dariya ta ce"Albarkacin kaza ƙadangare ya sha ruwan kasko".

Maman Affan ta ce"Don Allah ki min bayani, yaushe rabon da ki yi irin drink ɗin
nan".

Da murmushi ta ce"Baƙi za a yi a gidan, nasu kason yana can na zuba musu, sai
la'asar za su ƙaraso".

Ta ce"Kuma za ki yi baƙin shi ne kika fito kika baje a nan? Su waye za su zo?"

Sai da ta shanye lemon ta ajiye kofin sannan ta gyara zama ta ce"Buduruwar baban
Ni'ima ce za ta zo ganin inda zai ajiye ta bayan auren".

Kafin ka ce kwabo Maman Affan ta ƙware da lemo, ta shiga tari babu ƙaƙƙautawa,
abun ya ba wa Safiyya dariya, don ta san Maman Affan da kishin masifa, ta danƙo
hannunta tana zazzare ido ta ce"Da gaske ko da wasa?"

Safiyya ta yi murmushin yaƙe ta ce"Wallahi da gaske nake Maman Affan, baban Ni'ima
aure zai yi zancen da nake yi miki ma saura sati biyi bikin, yau za ta zo ta ga
yanayin gidan wai".

Maman Affan ta buga kofin hannunta da ƙasa har ya fashe, a fusace ta ce"Da gaske
ita kika yi wa girkin nan kuma?"

Safiyya ta ce"Su na yi wa!".

Sai ta ƙura mata ido na ƴan sakanni, ta ce"Kenan kina maraba da zuwan nata ko dai
taku ne? Ko guba kika zuba a cikin abincin?"

Safiyya ta yi dariya ta ce"Ke dai Allah Ya yaye miki wannan masifar kishin, ina ni
ina zubawa mutum guba a abinci? Ya ce na yi girkin ya zan yi? Ta zo ta ga gida,
amma na kulle ɗakina da kitchen ɗina, tun da nan ba huruminta ba ne".

Maman Affan ta jijjiga kai ta ce"Kar Allah Ya kawo ranar da mijina zai yi aure,
don wallahi ba ƙaramar ta'asa za a yi ba, na tsani jin kalmar kishiya, ke kam Allah
Ya miki baiwar haƙuri, wallahi da ni ce da tuni na gama haɗa kayan aikina ina jiran
zuwan su, don wallahi shigo-shigo babu zurfi zan yi musu, sai na tara su a ɗaki na
fara hauka tuburan na bi duk na ragargaje ƙafafun shegu!"

Safiyya ta yi dariya ta ce"Ke dai Allah Ya yaye miki kishi, babu ruwana da su,
yadda yake rawar kan nan idan na dage komai zai iya faruwa, idan ya sake ni ina na
kama? Ke kuwa kina da gatanki, wani abun mai uwa a raye ne yake yi".

Maman Affan ta ce"Haba Maman Ni'ima, ke ma da gatanki muddin kin riƙe Allah, kada
ma ki saka a ranki namiji ne gatanki, don za ki ga wulaƙanci kala-kala, ki dogara
da Allah ki tsaya da ƙafafunki, yanzu rayuwar ta zama iya ruwa fid da kai, ita kuwa
kishiya muddin kika sake mata wallahi rana za ta kai ki! Gidanki ne fa, ita ya
kamata ta dinga fargabar shigowa ba ke za ki yi fargabar zuwanta ba".

Safiyya ta yi ajiyar zuciya ba dan ta gamsu ba, ta ce"To Allah Ya kawo komai da
sauƙi dai". Ba ta son faɗa mata canjin da suke fuskanta da mijin nata, saboda ba su
saba irin firar ba, sam babu wani saɓani ma da yake haɗa su da shi ɗin sai yanzun
da ya tashi auren, haka suka ci gaba da firar su har aka kira sallar la'asar.

Katangarsu ɗaya da Maman Affan, shi yasa indai aka taɓa ƙofar gidanta sai ta jiyo
ƙara, suna zaune a sallaya suna ƙara tattaunawa suka ji ana buga gidan Safiyyan,
Maman Affan ta ce"To ko dai sun ƙaraso?" Ba ta jira amsa ba ta tashi ta je ta leƙa,
ta dawo tana huci ta ce"Wallahi su ne, ga manyan mata nan su biyu da ƴan'mata biyu,
ɗayar har da niƙab ɗin gulma ina ga shegiyar ce".

Gaban Safiyya ya dinga bugu, da ƙyar ta haɗiyi yawu ta ɗauki mukullin gidan ta
miƙawa Maman Affan ta ce"Je ki buɗe musu su shiga".

Maman Affan ta tsorata da jin muryar Safiyya tana rawa kamar za ta yi kuka, ta
ce"Yau ga mugun abu! Maman Ni'ima ba dai kuka za ki yi wa kishiya ba tun yanzu? A
lallai zan sha kallo kenan, tashi mu je na raka ki don ba zan je ni kaɗai ba, ba
kuma zan bar ki ki je ke kaɗai ba, su miki duka tun da na lura ke saiwar sala ce".

Suka fito ta na ƙoƙarin saita kanta ita ta rufo gidan, saboda Mamam Affan ta yi
gaba, tana ce musu"Wa alaikumus salam!" Ganin wata lukutar mata ta zage iya
ƙarfinta tana ta buga gidan. Duka suka juyo suna kallon mu, ta yi gaba tana
kiciniyar buɗe gidan ta ce"Ai ga ma su gidan nan, sannunku".

Babu wanda ya amsa sai bin ta da kallo da suka yi, ta buɗe ta shige, Safiyya ta bi
bayanta sannan su ma suka shigo, ta shiga ɗakin da zai zama na amaryar ta shimfiɗa
tabarma ta ce"Ku shigo mana, Safiyya kawo musu ruwa da abinci".
Ta buɗe ɗakin baban Ni'ima ta ɗakko musu, don ita da a lissafinta can za ta kai
su, tun da baƙinsa ne, ta ajiye musu ta yi gefe, Maman Affan ta ce"Ku saki jikinku
fa, a ɗakin amaryar kuke".

Sannan ta ja hannun Safiyya da ke tsaye kamar ta haɗiyi taɓarya ta yi waje da ita,
a barandar ɗakin baban Ni'ima suka zauna babu wanda ya ce da kowa komai, babu
jimawa kuma baƙi suka fito.

Maman Affan ta ce"To har za ku tafi? Ku gai da gida".

Lukutar matat ta coge ta ce"Ina zancen mu gai da gida bayan ba mu yi abin da ya
kawo mu ba? Ko ce muku aka yi yunwa muke da za ku ba mu abinci ku ce mu gai da
gida?".

Safiyya ta ce"Zancen yunwa kuma sai dai ku tambayi mai gidan, tun da shi ne ya yi
cefane ya ce a muku girkin, kuma wannan ɗaki da kuka shiga shi ne rabon amaryar ai,
shi wannan nawa ne, wancen kuma na mai gida".

"Me kuke nufi da rabonta? Kenan a ɗaki ɗaya zai ajiye ta?" Wacce suke

Please Login or Register in order to submit comment