You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba mu
sani ba? To zan je da kaina na taka mata burki, Allah Ya sa dai ba ka bari ta raina
Ameerar ba, don yadda kake son wannan busasshiyar kamar ita kad'ai ce mace".

Ya ce"A'a Hajiya, babu wanu fad'a da suke yi, kuma Safiyya yanzu ai ta san
matsayinta, saboda ni ta ba ni mamaki wallahi, a yadda na tallafi yarinyar nan ko
wuta na ce ta shiga ai za ta shiga, amma sai ki ga akan abu k'alilan ta kafe kamar
tsohon babur tana musu da ni".

Hajiya ta ce"Ai abin da ake kokarin nuna maka kenan ka kasa ganewa, sai yanzu da ka
fara dawowa hayyacinka!".

Washegari Hajiya da kanta ta je gidan, wai ta zo gargad'in Safiyya, idan ta sake
ji ta b'atawa Ameera girki sai ta yi ta igiyar aurenta, Safiyya ta ba ta hak'uri
tana hawaye.

Da ya dawo ta dinga kuka ta ce"Baban Ni'ima me na yi maka za ka had'a ni da
Hajiya? Ameera ce ta ce maka ni nake b'ata mata girki? Mene ne ribata a cikin
hakan? Ina ruwana da rayuwarku?"

Jikinsa ya yi sanyi, ya ce"Ni fa ban ce kin b'ata mata girki ba, amma daga yau na
saka doka duk wacce ta sake cewa an mata wani abu a girki ko ta yi girkin da na
kasa ci gaskiya komai zai iya faruwa, ita ma zan fad'a mata, ya za ku saka kayan
abinci a gaba ku dinga b'arnarsa?"

Ya fice ita ma Ameera ya je ya yi mata gargad'i.
Tun daga ranar Safiyya ba ta sake sakawa Ameera komai a girki ba, amma ita Ameera
ta k'ara mata gishiri sau uku, sai dai ta zubar ta sake dafa wani, daga nan sai
take zama a kitchen d'in har sai ta kammala girkinta, sai ta zuba a kula ta kai
d'akinta. Daga nan kuma Ameera ta ci gaba da shigo mata d'aki haka kawai ta zauna
kuma ba za ta yi mata magana ba, sau biyu Maman Affan tana tarar da ita a d'akin,
idan ta shigo sai ta fita, har ta nunawa Safiyya ta hana ta, ta ce ta k'yale ta, da
ta samu sake ma sai ta ga Maman Affan din ta shigo, ita ma sai ta zo d'akin ta
zauna, ba za dai ta saka baki a firarsu ba, amma za ta zauna tana danna waya,
watarana suna zaune a hakan Maman Affan ta b'ata rai ta ce"Safiyya za mu yi
magana".

Safiyya ta kalli Ameera ta ce"Ko za ki ba mu wuri?"

"Ok!" Ta fad'a ta tashi ta fita, sai da ta koma d'aki abun ya dame ta sosai, tana
so ta san abin da za su tattauna, saboda ta tsani wannan matar ba ta yarda da ita,
kuma ta ga ko kallon kirki ba ta yi mata, kasa jurewa ta yi ta je k'ofar d'akin ta
lab'e, amma ba ta jiyo komai ba, don haka ta d'an bud'a labulen kad'an ta lek'a ko
za ta hango abin da ake yi, maman Affan da ta hango ta ta yi kamar ba ta ganta ba,
ta d'auki gorubar da Khausar suka gama kokowa da ita, cikin shammata ta wurga ta
jikin labulen, aikuwa ta samu Ameera amma ba ta samu idonta ba, da gudu ta shige
d'akinta, ita ma maman Affan ta fito da gudun ta ce"Ni'ima ban hana ki lek'e ba?"

Ni'ima da suke ta wasan su ba su san ma wainar da ake toyawa ba ta ce"Ba mu ba ne,
ba mu lek'o ba".

Ta d'aga murya ta ce"Duk munafukin da yake lek'e wataran sai na yi masa balaraben
ido kuwa!".

Safiyya ta yi dariya ta ce"Wallahi da kin k'yale ta, idan ta lek'o ma me za ta
gani? Zargi ne kawai".

A ranar da daddare baban Ni'ima ya kira Safiyya kamar abun arzik'i, ya ce"Safiyya
daga yau na kafa dokar da karyata zai iya jawo miki babbar matsala!".

Ta ce"Ina ji".

Ya ce"Daga yau kar Maman Affan ta sake shigo mini gida, domin duk wata fitina na
gano ita ce take haddasawa a gidana, wato bayan koya miki raina ni da taurin kai
yanzu har tsubbace-tsubbace za ta koya miki?"

K'irjin Safiyya ya yi wani irin bugu ta ce"Me kake nufi da tsubbace-tsubbace?"

Ya ce"Me kuka binne ke da ita d'azu da ta zo?"

A tsorace ta ce"A ina? Ni ce na binne wani abu?"

Ya ce"Tashi mu je" Ya kunna fitilar wayarsa, ta bi bayansa saitin kanta duk ya
kunce, gindin fanfo ya nufa wajen da suke da y'an shuke-sheke dama nan ne babu
siminti, suna zuwa ita ma kallo d'aya ta yi wa wajen ta ga alamar an yi tono, ya
ce"Tona ki ciro abinda kika binne da kanki!".

Jikinta ya fara karkarwa saboda tsananin bak'in ciki, ta ce"Wallahi baban
Ni'ima..."

"Ki tona!" Ya daka mata tsawar da ta saka ta fashewa da kuka.

Tana tonawa ba ta yi nisa ba ta ciro wani abu k'ulle a cikin tsumma, gabanta ya
tsananta fad'uwa ta jefar da abun cikin furgici ta ce"Wallahi ba ni na binne ba,
kuma ban san komai a kai ba".
Ameera ta saki murmushin samun nasara daga windo da take lek'ensu ta ce"Kad'an ma
kika fara gani".

Rai a matuk'ar b'ace ya ce"Kin ba ni mamaki Safiyya! Ina kika kai tarbiyyarki? Tun
da na k'ara auren nan da me na rage ki ke da yaranki da har sai kin kai ni wajen
bokaye saboda ki raba ni da matata ko? To wallahi wannan ya zama na k'arshe don ban
sani ba ko ba shi ne na farko ba, duk ranar da haka ta sake faruwa zan d'auki
mataki".

Ya wuce ya barta a wajen, ta fashe da kuka sosai, tana sake kallon k'ullin abun,
sai da ta ci kuka ta more sannan ta tashi ta shiga d'aki, har lokacin jikinta rawa
yake yi.

Ameera kuwa farin ciki ya lullub'e ta, indai wannan k'aramin abun zai fusata Salis
to kuwa tabbas watan barin Safiyya gidan nan ya tsaya cak, don a dabarun korarta da
ta shirya wannan k'aramin abu ne, kukar nera hamsin ce fa ta siyo ta tsinto tsumma
a hanya ta yaga ta juye ta ta k'ulle, duk a zaton ta ma abun ba wani tasiri zai yi
ba, sai yau ta gwada saboda ta ji haushin abin da maman Affan ta yi mata, ta ce
masa ya kula da maman Affan saboda tana lura da take-takenta, kuma yau ta ga suna
binne abu a gindin fanfo.



08028966015
[5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAK


FIRST CLASS WRITERS


Page 9


Da bak'in ciki sosai ta kwana, a ganinta ya kamata a ce ya tsaya ya saurare ta,
tun da a tsawon zamansu bai tab'a kama ta da makamancin haka ba. Da sassafe ta jiyo
shi yana k'wala mata kira daga tsakar gida, ta fito tana kallon shi yadda yake
had'e rai, kallon sakanni ya yi mata ya kau da kai, daga ganin idonta ta yi kuka,
har yanzu k'asan ransa yana son ta ba ya son ganinta cikin damuwa, haka indai ta yi
masa laifi ta bi shi da wannan marayan kallon nata sai ya ji mugun tausayinta, don
haka indai yana son hukuntata ba ya tsayawa kallon idonta.

"Ga ni". Ta katse shurun

Ya ce"Ki d'auki wannan k'ullin naki ki san yadda za ki yi da shi".

Hawaye ya kawo idonta ta ce"Wallahi ban san komai ba a kan wannan abun, Allah ne
shaidata".

"Ki d'auke!" Ya daka mata tsawa.

Sai ta d'auka ta je za ta saka a dustbin, ya ce"Ki fitar da shi daga gidan nan".

Ta sako hijjabi ta d'auka ta fita ta jefar a waje, ta dawo ta ce"Na jefar".
Ya juya ya shige d'aki, daidai lokacin da Ameera fito daga d'aki ta juya mata ido
ta ce"Sai ki kiyaye".

Safiyya ba ta ce komai ba ta shige d'aki, ko abun karyawa ba ta ba su ba, ta koma
ta kwanta tana hawaye.

MENE NE ALAK'AR SAFIYYA DA MIJINTA?

Briged Nasarawa local government Kano state.
Alhaji Muhammad d'an kasuwa ne da yake gudanar da kasuwancinsa a k'ofar Wambai,
suna cikin rufin asiri da matarsa Maryam y'a'yansu biyu, Aminu shi ne babba, kuma
daga kansa Allah bai kawo wata haihuwar ba sai da ya shekara goma sannan ta haifi
Safiyya, kasancewar tana koyawa Aminu aikin gida yana taya ta, sosai yake
taimakonta da rainon k'anwarsa idan aka tashi daga makaranta haka za su zo tare da
d'an mak'otansu Salisu wanda Allah Ya d'ora masa son yarinyar, kusan ma ya fi Aminu
iya rainon don haka Mama take yawan cewa ta ba shi ita, shi kuma sai ya yi dariya,
akwai lokacin da Salisu ya had'o kud'insa 'yan canji da yawa ya kawowa Mama ya ce a
siyawa Safiyya kayan sallah, abun ya ba ta mamaki da ya fad'a mata kud'in break
dinsa ne yake tarawa, ta saka hijjabi ta je gidansu bayan sun gaisa da Hajiya ta ba
ta wannan kud'in ta ba ta labari, Hajiya ta yi dariya ta ce"Haba ai ni ce ma nake
yi masa bankin, tun da dai kun ba shi ita ai gara ya fara sauke nauyi tun yanzu,
ana abu kamar wasa inda rabo sai ki ga ya tabbata, girman d'an mutum babu wuya".
Mama ta yi godiya ta tafi.

Tun daga nan fa Salisu komai ya samu na Safiyya ne, Safiyya tana shekara biyar a
duniya Mama ta sake samun ciki, sai dai wannan karon ya zo mata da laulayi mai
zafi, tana ta rashin lafiya, k'arshe dai abokin tafiya ne ta kusa haihuwa Allah Ya
yi mata rasuwa, a lokacin Safiyya ba ta san ciwon kanta ba, ballantana ta san zafin
rashin uwa, sosai Salis ya shiga damuwa da ya ji cewar Safiyya za ta koma can
Ungogo gidan kakarta, ya dinga rok'on mahaifiyarsa don Allah ta karb'i Safiyya ta
zauna a wajenta, har ta amince, sai dai Baban Safiyya da sauran y'an'uwa ba su
amince ba, haka ya hak'ura aka kai ta can d'in, duk sanda Safiyya ta zo sosai yake
shiga farin ciki, haka ita ma tana son Yaya Salis don yana kyautata mata fiye da
Yaya Aminu, shi ma kuma duk sanda Aminu zai je tare suke zuwa, don shi Aminu a
gidan yayan baban nasu aka bar shi bai je Ungogo ba, sai bayan shekara uku Allah Ya
yi wa kakar Safiyya rasuwa, sai a lokacin ne kuma Baba ya ga dacewar ya yi aure,
sai ya samu wata bazawara ya aure ta, ya d'akko Safiyya ya ba ta amanarta a lokacin
shekararta takwas.

Bayan shekara biyu.

Yarinya ce y'ar kimanin shekaru goma, tsugunne a bakin wuta tana ta fifitawa, sai
hayak'i take yi saboda yanayin damuna icen ba ya ci, da k'yar ta samu ta kama
sannan ta tashi ta koma ta ci gaba da wanke-wanken da take yi, sai dai hayak'in ya
taso mata da larurar idonta ta amosani, don haka k'aik'ayi ya addabe ta ta dinga
murza idon babu k'akkautawa.

Salis dake tsaye yana kallonta tun da take fifita wutar ya k'araso inda take ya yi
tafi ya ce"Ya isa haka".

Ta daina susar ta saki murmushi ta ce"Yaya".

Ya ce"Na'am k'anwar Yaya ki daina sosa idonki, kin ga sai k'ara k'ank'ancewa yake,
ya yi ja sosai".

Ta ce"To zan daina, amma damuna yake da k'aik'ayi shi yasa".

Ya ce"Yi hak'uri, ina fasa bankina zan kai ki asibiti, bari na taya ki".
"To!" Ta fad'a tana matsawa gefe, don dama ta gaji, ya ci gaba da wanke-wanken
suna fira. Umma ta lek'o daga d'aki tana ganin shi ta had'e rai cikin k'unk'uni ta
ce"Ana ji ana gani an d'aurewa yarinya k'ara gindi tana karuwanci a cikin gida, ka
yi magana a ce an ba shi ita, ai da an sani an d'aura auren tun yanzu.


*A yi hak'uri na san ya yi kad'an, Allah Ya kaimu gobe*🙏🏻
[5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAK


FIRST CLASS WRITERS


Page 10


"Tun da kin ba shi wanken-wanken ai sai ki yi shara" Suka ji muryarta. Safiyya
ta tashi ta share gidan, ya fifita wutar sannan ya ba ta ɗari da hamsin kud'in
littafin da ta ce za ta siya, sai uku Baba yana ba ta kuɗin Umma tana karɓewa, don
haka jiya ta tambayi Salis shi yasa yanzun yana ba ta ta ɓoye. Baban Safiyya irin
mazan nan ne da ba sa lura da gidansu sosai, ya yarda da matarsa saboda haka bai
taɓa bibiya ya tabbatar da Safiyya tana rayuwar ƴanci a gidan ko akasin haka ba, ya
wadata gidansa da komai amma Safiyya ba ta da ƴancin da za a kai mata wanki kuma ba
ta da damar ɗaukar omo ta yi da kanta sai lokacin da ta ga damar bata, sam ba ta
iya wankin ba jiƙa-jiƙa kawai take yi, sai kayanta duk suka dafe, Salis ya yi zaton
omo ne ba a samu saboda haka yake siyo mata, sai Umma ta dake ta ta ce tana roƙo
tana kai gulma a waje tana cewa ba a ba ta omo, kuma ta karɓe omon haka za ta yi ta
saka kaya da datti, ba ta faɗawa kowa shi kuma Yaya Aminu sam ba ya janta a jiki
ballantana ya san damuwarta, sai da abun ya dame ta ta faɗawa Salis, sai yake
karɓar kayan nata ya tafi da su gidansu ya wanke ya goge ya kawo mata a ɓoye, don
Umma ba ta taɓa sani ba. A lokacin shi yana da shekara ashirin, kuma yana aiki a
gidan biredi, kullum da safe sai ya jira ta a ƙofar gida shi yake raka ta
makaranta, ya ba ta kuɗin makaranta ya ba ta biredi tare da shayin da yake siyowa,
Umma ba ta taɓa sanin haka ba, sai da wata maƙociyarsu ƙawarta ta kai mata gulma, a
ranar ta ritsa Safiyya ta dinga dukanta don ce mata aka yi nama ne kullum yake ba
ta, ta ce daga yau ta daina cin abincin safe a gidan tun da saurayi yana ba ta, ta
raina wanda ubanta ya bayar, washegari sai ta hana ta zuwa makarantar ma, da safe
ta gama wanke-wanke da shara tana ɗaki ta ji sallamar shi, saboda ya daɗe a ƙofar
gidan yana jiranta, ya gaida Umma ya na tambayar Safiyya.

Ta ce"Tana ciki ai, jiya da zazzaɓi ta kwana".

Ya ce"Bari na ganta, ta sha magani?"

Ta ce"Ai kuwa yanzu na leƙa na ga tana bacci".

Jiki a sanyaye ya miƙa mata ledar ya ce"Ga wannan a ba ta idan ta tashi".

Ta ce"Yawwa Salisu dama baban Safiyya ya ce a faɗa maka ka daina ba wa Safiyya
abinci tana tafiya da shi makaranta, saboda ba ta rasa komai a gidan ba!".

Ya ce"To na daina".
Ya fice Umma ta bi bayansa da harara, sosai yaron yake ba ta haushi saboda a
ganinta zaƙewarsa ta yi yawa, ta buɗe ledar ta ga shayi da biredi da naira hamsin,
ta ce"Munafuka! Ashe har kuɗ'i yake ba ta".

Safiyya tana leƙen komai ta windo, sai da Umma ta cinye tas sannan ta ƙwala mata
kira, ta fito tana sosa ido, ta ce"Shirya ki tafi makaranta!".

Ta shiga ta shirya ta fito ta ce"Ban karya ba".

A fusace ta ce"Kuma ba za ki karya ɗin ba! Ba dai ke kin raina abin da ubanki ya
kawo ba? Ai kuwa kin yi biyu babu, babu na gidan ba na kwaɗayin".

Safiyya ta tafi ko kuɗin makarantar ba ta bata ba, kuma sai da aka yi mata dukan
latti. Da yamma Salis ya zo duba ta da lemo da kankana, sai ya ji ta tafi
islamiyya, Umma ta ce"Jikin ne na ji da sauƙi, ta ce ba ta so ta yi fashin
islamiyya". Ya ba ta kayan dubiyar ya tashi, a ƙofar gida ya zauna har ta dawo,
tana ganin shi ta ji sanyi a ranta tana murmushi ta ce"Yaya!"

Ya ce"Ƙanwar Yaya, ya jikin?"

Ta ce"Na ji sauƙi".

Ya ce"Me ya kawo zazzaɓin? Ko wanka kika yi da tuwan sanyi?"

Ta ce"A'a haka kawai ne".

Ya ce"Na siyo miki kankana da lemo, sai kuma me za ki ci?"

Ta ce"Ba komai".

Daidai lokacin Yaya Aminu ya zo shiga gidan, ya sakar mata ranƙwashi a kanta ya
ce"A nan za ki juye ladan makarantar ko?"

Salisu ya ranƙwashe shi ya ce"Aminu wallahi ka kiyaye ni".

Safiyya ta shige tana ɓata rai, idan da sabo ta saba, Yaya Aminu ba ya son ganinta
da abokin nasa. Ita dai har lokacin bacci ya yi ta kwanta ba a ce mata ga abin da
Salis ya kawo mata ba, washegari ya zo ya raka ta makaranta, amma bai ba ta komai
ba, haka a gida Umma ba ta ba ta abinci ba kuma ba ta bata kuɗin makaranta ba, sai
da aka yi sati ɗaya a haka, sannan watarana suna tafiya ta faɗa masa duk yadda aka
yi, kuma ta faɗa masa ba a ba ta abun karyawa, tun daga ranar sai ya daina zuwa
rakata makarantar sai dai ya jira ta a hanya, sai ya ba ta abun karyawa da kuɗin
makarantar.

Da haka suke gudanar da rayuwarsu cikin ƙauna da tausayi, har Salis ya samu wanda
ya ɗauke shi yaron kasuwa kuma yana samu daidai gwargwado, duk wani banki da zai yi
idan ya buɗe na Safiyya ne, ita yake yiwa hidima yayarsa ya sa ta tsaya a kan ciwon
idonta tana kai ta asibiti har sai da ta warke, Baba ya yi iya ƙoƙarinsa a kan idon
Safiyya, ya sha ba da kuɗin kai ta asibiti Umma ba ta kai ta sai ta cinye kuɗin,
don haka rana ɗaya ya ga ƴar tasa ta warke duk a zatonsa da kuɗinsa ne. Duk sallah
ɗinki kala biyu yake yi mata takalmi, mayafi da kuɗin barka da sallah, haka duk
sati sai ya ba ta kuɗin kitso, duk wata kuma shi yake siyo mata pad, sannan haka
kawai yana ba ta kuɗi ya ce ko za ta sayi wani abu, abin da Yaya Aminu bai taɓa yi
mata ba, kuma shi ma yana samun kuɗin don Baba ya ja shi kasuwa.

Lokacin da Safiyya ta kai shekara goma sha bakwai ta girma ta yi kyau sosai ƴar
farar burwa mai matsakaicin kyau, doguwa mara ƙiba, a kaf unguwar babu mai cewa
yana sonta don babu wanda bai san cewar matar Salis ba ce, a lokacin ta san wace ce
ita, ta san so kuma abu ɗaya da ta sani Salis shi ne mai sonta da shi ta saba da
shi kuma take burin gudanar da rayuwar aurenta har abada, sun yi wani mugun sabo da
shaƙuwa ta yadda take jin kusancin su kamar ya fi na Yaya Aminu, ba ta shakkar
tambayarsa duk abin da take buƙata, shi ma kuma ba ya ƙasa a gwiwa wurin faranta
masa, ankon ƴan'uwa da na ƴan unguwa duk aikinsa ne, haka har lokacin bai daina yi
mata wanki da guga ba.

To babban ƙalubalen da suka fara fuskanta shi ne da ɗan'uwan Umma ya ga Safiyya
rana tsaka ya ce yana son ta, Umma kuwa ta ce gida bai ƙoshi ba ba a kai wa dawa,
yayinda Safiyya ta yi tsalle da dire ta ce ba ta da miji sai Salis, suka kai ta kai
ruwa rana kafin Baba ya takawa abun burki ya ce tabbas Safiyya ba ta da miji sai
yayanta, haka aka haƙura sai dai Umma ta ƙara tsanar Safiyya da zangwamarta, wani
lokacin abinci ma ba ta bata sai dai idan tana jin yunwa sosai ta faɗawa Yayanta ya
kawo mata abin da za ta ci.

Ba a daɗe da saka aurensu ba Baba ya kwanta jinya, nan kuma wani abokin kasuwancin
su ya zo dubiya shi ma ya ga Safiyya ya ce yana so, Aminu kuma ya yi masa alƙawarin
zai same ta, yake ta karɓe ƴan kuɗaɗe a wajen mutumi, nan ya fara kushe Salis yana
faɗa mata dama fa ya yi shiru ne amma Salis yana shaye-shaye, kuma yana taɓa neman
mata, Safiyya ta yi tsalle ta dire ta ce ko me yake yi ta ji ta gani, akwai ranar
da Aminu har dukanta ya yi, shi a ganinsa tun da ga babban mutum mai kuɗi ya zo me
zai sa ta auri wani Salis, bai san cewa zuciya tana karkata bisa son wanda yake
kyautata mata ba, a yadda take son Salis a lokacin har gara Aminu ya mutu Salis ya
rayu.

Shi Baba yana jinya bai san abin da suke toyawa ba, Aminu ya zagaye ya ja wannan
Alhaji mai son Safiyya ya kai shi Ungogo ya dinga yi musu ɓarin kuɗi, nan ƴan'uwa
duk suka amince, aka ce ba za a biye ta Safiyya ba ita har yanzu ba ta mallaki
hankalin kanta ba, shi kuma Baba yana kwance kar a saka da shi ya zo ya shiga
damuwa, su suka kitsa komai dama kuɗin auren da Salis ya kawo yana wurin yayan
Baban, don haka suka ɗauka rana tsaka suka mayar gidan su Salis da sunan an fasa
auren, saboda sun ji labarin yaro ba shi da tarbiyya.

Sai da ran kowa ya ɓaci a dangin Salis, zance ya karaɗe unguwa ana cewa Safiyya da
iyayenta butulu ne sun ci amana, sosai hankalin Salis ya tashi, lokaci ɗaya ya fita
daga hayyacinsa, sassauci ɗaya da ya samu na ganin Safiyya har yanzu tana son shi
shi ya tsayar da shi a kan ƙafafunsa, don da tuni shi ya kwanta jinyar, wani irin
yanayi Safiyya da Salis suka shiga mara misali, kullum cikin damuwa suke, kaca-kaca
aka yi tsakanin Salis da Aminu, akan kuɗi aka yi fatali da abota tun ta ƙuruciya.
Kamar yadda Aminu da sauran dangin Safiyya suka tsani Salis ɗin da yake neman yi
musu katanga da haɗa jini da mai hannu da shuni haka su ma dangin Salis suka tsani
Safiyya, saboda zargin butulce wa wanda ya yi mata hidima tun tana yarinya.

Ƙarshe dai da ruguntsumin ya yi yawa a dole Baba da ke kwance ya ji komai, sosai ya
shiga baƙin ciki, jikinsa ya rikice ya ba da umarnin ko bayan ransa Salis ne mijin
Safiyya muddin shi ne ya haife ta, ba da son rai ba haka limamin unguwar ya tara su
don yin sulhu, aka ce Salis ya dawo da kuɗin aure, inda dangin Salis suka ce sun
fasa ba zai aure ta ba, shi kuwa ya yi tsalle ta dire ya ce ba shi da mata sai ita.
Ƙarshe dai da ƙyar aka sasanta, a ka tsai da ranar auren wata ɗaya a maimakon wata
biyar da ya yi saura, Baba ya ba da umarnin a ɗauki kuɗi a yi wa Safiyya komai na
aure, amma saboda baƙin cikin ta yi musu taurin kai suka ƙi yi mata komai, dangin
babarta dai sun haɗo mata kayan kitchen, don sai a na gobe ɗaurin auren aka san ma
ba a yi mata kayan ɗakin ba, ga shi rabin kayan lefenta Umma ta kwashe ta siyar
kuma suma dangin nasa sun rage kaya sosai kafin su kawo.

Dangin babarta sun nemi idan an ɗaura auren a ɗaga tarewar zuwa sati biyu, su
harhaɗa su mata kayan ɗaki, Aminu ya yi rantsuwar ana ɗaurawa ba za ta sake kwana a
gidan ba, haka ta faɗawa Salis tana ta kuka, shi ma ya ce ba za a ɗaga ba, ya
kwantar mata da hankali sosai, a ranar ɗaurin auren kuma ya siyo mata kujeru da
kayan gado, ai kuwa sosai ya sha faɗa a wajen Hajiyarsa ta ƙara tsanar Safiyya
sosai.

Haka aka kai ta gidan miji ƴan'uwanta suna fushi da ita, Aminu ko cokali mai siya
mata ba, ta tare rai babu daɗi. Amma dayake suna ƙaunar juna sai komai ya wuce
cikin ƙanƙanin lokaci, suka fara shimfiɗa rayuwa cike da nishaɗi, har ta kusa
haihuwar Ni'ima Aminu ba ya ɗaukar wayarta, haka sun yanke alaƙa da Salis, sai da
ya fara son ƙawarta Salma sannan ya nemi taimakonta ta kuma shige masa gaba har aka
yi auren dalilin shiryawar su kenan, Baba kuma ya samu lafiya ya ci gaba da
harkokinsa yana sakawa auren su albarka.

[5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAK


FIRST CLASS WRITERS


Page 11


Da daɗi da babu daɗi aka shafe wata uku da ƙarin auren Salis, ashe Ameera ta
samu ciki watansa biyu Safiyya ta yi tunanin hakan a lokacin da take laulayi, amma
Salis yake ta maimaita mata maleria ce take damunta, haka ta taɓa ji daga bakin
yayarta da ta zo dubiya tana cewa"Oh! Wannan malaria ta sako ki a gaba, Allah dai
Ya yaye". Su ma ƴan'uwan shi da suka zo dubiya ta ji suna zancen malaria, ita dai
ba ta ce komai ba, tana dai yi mata sannu, don amai take yi sosai, ga yawan zazzaɓi
da take yi, ko girki ba ta iya yi, dama sharar tsakar gida gyara kitchen da wankin
banɗaki tun da ta zo ba ta taɓa yi ba Safiyya ce take yi, da ta ga yadda take jin
jiki sai ta yanke shawarar ta dinga yin girki da ita, amma Salis ya ce Hajiya ta ce
za ta dinga aiko mata abinci, haka kuwa aka yi kullum sai ta aiko mata abincin rana
da na dare, da safe kuma shi da kansa yake haɗa mata shayi, ita dai ta ɗauki ido ta
zuba

Please Login or Register in order to submit comment