You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gara ta fara
zuwa wajen Kausar ɗin, ita da take hannu, don Hausawa sun ce ƙwai a baka ya fi kaza
a akurki. Hijjabi kawai ta zura ta ɗauki wayarta, sai kuma ta tuna ba ta san ma a
wane asibitin suke ba, ta kira shi ya ɗaga ta ce"Zan je ganin Kausar ɗin, suna wane
asibiti?"

Ya ce"Ni ma kin gan ni a gidan Hajiyar na zagayo na ji ko da wani labari, bari na
zo sai mu je".

Ya ɗan jima kafin ya ƙaraso, har ta ƙagauta, ta kira Baba ta yi masa bayani shi ma
hankalinsa ya tashi ya ce zai kira Salisun, tana ganin kiransa ta san ya ƙaraso ta
fita da sauri, ta hau babur ɗin suka tafi, a kallo ɗaya shi ma ya ba ta tausayi,
duk ya firgice, tsoro ta ji ma kar ya faɗi a babur ɗin, ba ta ce masa komai ba, sai
da suka fara nisa ya ce"Yanzu ma Yaya ta kira ni wai sai an kai takardar haihiwar
Kausar, kwanaki kin karɓa ko?"

Safiyya ta ce"E suna ɗakina".

Ya ce"To mu biya ta gidan mu ɗauka sai mu wuce". Ba ta ce komai ba suka ci gaba s
zuga gudu.

Tare suka shiga gidan bayan ya buɗe, yana kiciniyar shigar da babur ya ce"Kin san
yanzu ɓarayin babur sun ƙara ƙaimi da sun faki ido sai dai ki ji tiii har sun kai
ƙaraye". Ita dai ba ta kula shi ba, ya buɗe ɗakin nata, tare suka shiga, ta doshi
inda ta san ta ajiye kai tsaye ta fara dubawa, cak ta tsaya ganin ya cire riga ya
ajiye yana zare dogon wando, ta yi zaton kaya zai canza ta ce"Ha'a! Dama da kayanka
a ɗakin nan?"

Ya ce"Ga ki kuwa, ai ke ce manyan kayana, wannan da nake sawa sunansu tsumma" Yana
murmushi ya nemi katifa ya kwanta, ranta ya fara ɓaci da abin da yake yi, ta
ce"Haba don Allah! Wai me kake nufi ne?"

Ya lumshe ido ya ce"Zo ki ji mana ƴar ƙanwata".

Safiyya mamaki ya daskarar da ita, lokaci ɗaya takaici ya rufe ta, kenan buƙatarsa
ta fi zuwa asibiti duba ƴarsu, kuma a tunaninsa za ta dawo yau ne da har zai wane
tuɓe shi ga mai gida, ranta a ɓace ta ce"Wai me kake nufi!?"

Ya buɗe idanunsa masu cike da kewarta da kuma buƙatuwa ya ce"Ai kin gane".

Ta juya za ta fita, ya tashi da sauri ya ruƙota ya rungume ta ta baya yana ajiye
numfashi, a hankali ya ce"Ban yi tunanin zuwan ranar da ƙanwa za ta gaji da Yayanta
ba, Safiyya ina son ki, na yi kewarki, don Allah kar ki sake tafiya ki bar ni, ashe
ƙarya nake da na ce zan jure".

Jikinta ya yi sanyi lokaci ɗaya, ita ma ajiyar zuciyar ta sauke tana jin ashe
matuƙar kewarsa da kewar furucin da yake yi mata rungume da ita, hakan ya tuna mata
rayuwarsu ta baya, saukar hawayeta ya ji a hannunsa, ya juyo da ita suka kallon
juna, sai ta kauda kai tana ƙoƙarin dakatar da hawayen ta ce"Mu tafi asibitin kar
su jira ka".

Ya ce"Safiyya ke ce lafiyar Kausar, ke ce lafiyar Ni'ima haka ke ce lafiyar Salis
ɗinki, don haka Kausar ta samu lafiya, Ni'ima kuma an ganta cikin aminci, saura ni
ki saita ni".

Sai yanzu ta gane ainahin kan game ɗin, ta rasa taƙamaimai abin da take ji a
zuciyarta, ta zare hannunta daga na shi ta nufi hanyar barin ɗakin, ya dawo da ita
ta fizge da faɗa ta ce"Kar ka sake yi mini haka! Da bugar min da zuciya za ka
samawa kanka mafita? Duk wasan kwaikwayon da za ka yi kada ka sake saka ƴaƴana a
ciki, saboda bayan iyayena ba ni da wanda ya fi su, kar ka sake yi min haka, ka
ɗorawa ƴarka cutar ƙarya ka janyowa ƴarka musiba ka yi mata fatan ta ɓata? Saboda
ko me zai same su ba ka da asara ko?" Ta yi murmushin takaici ta ce"To dama me zai
dame ka tun da kana da magajinka? To su matan ni ban raina su ba, saboda haka sun
fi mini kowa, kar ka sake haɗa plan da su, gidanka kuma ba zan dawo ba!".

Ta juya za ta fita ya ruƙota, yana murmushi sam bai ji haushin maganarta ba, yau
wani burge shi take yi sosai, idan ya cire sabon halinta na faɗa sai ya ganta kamar
Safiyyarsa ta wancen shekarun ƴar ƙanwarsa, ya ce"Yaya bai kyauta ba, ƙanwar Yaya
ta yi haƙuri ko kuma ta yi masa hukunci amma kar ta sake barin shi, ta tuna
alƙawarin nan" Ya ƙarasa maganar kamar ƙaramin yaro, wanda hakan ba komai ya ƙara
mata ba sai jin haushin abin da ya yi da kuma wanda yake yi a gabanta.

Ta ƙara yunƙurin fita, ya saka sakata, ya janyo ta har katifar ya ce"Babu fa inda
za ki je Safiyya, kin dawo ɗakinki".

Tana hawaye ta ce"Yau da ka buƙace ni ko? Matarka ba ta yi tsarki ba har yanzu ko?"

Ya ce"Haba Safiyya me kike cewa ne? Kin san dai duk wacce zan so a bayanki take, ke
ɗin ce dai kuma wallahi ke ce gidan nan, ni na kasa ganewa kanki ne, tun da na yi
aure Safiyya kamar kin manta da yadda matsayinki yake a wajena, wallahi babu abin
da ya ragu, ko abin da kika ga ina yi miki wasu lokatan ni ma ba na jin daɗi a
raina, ni ina ga ma asiri aka yi mini wallahi, idan ba haka ba ta ya mace kamar ke
namijin da kansa babu wani motsi zai ce tafi gidanku? Ki yi tunani fa, wallahi
akwai ayar tambaya a lamarina, haka kwanaki fa na yi ta mafarkin wasu tsuntsye wai
ga su nan suna shawagi a kanki, idan na zo zan ɗauke ki sai su kawo min caki, ke
kuma kina kuka kina kiran Yayana, mafarkin nan ya firgita ni, shi yasa na ce gara
ki dawo don ban san halin da kike ciki a can ɗin ba..."

Ranta a ɓace ta ɗaga masa hannu, ta ce"Don Allah Ya isa haka, ai ni ina da fassarar
mafarkinka".

Ya nutsu ya ji me za ta ce, don shi babu wani mafarki da ya yi, kawai gyaran hanya
ne yake yi don ta zauna, ya ce"To ina sauraronki"

Ta ce"Zan faro maka ta ƙarshe, da ka ce ba ka san a wane hali nake ciki ba, to
zaman gidanmu ya fi mini daɗi a akan zaman gidan nan, saboda a can babu mai takura
mini, ƙalau nake rayuwata ban rasa komai ba, ba kamar yadda ka sani a baya ba,
yanzu komai ya canza, don haka kar ma ka sake tunanin ba zan ji daɗi a gidanmu ba".

Yana ta gyaɗa kai kamar ƙadangare, ta ce"Farkon mafarkinka kuma, su waɗan nan
tsuntsayen a zahiri maza ne, don kuwa ɗan zamana a gida suna ta inkiya suna kawo
hari saboda sun zata sakina ka yi, kai kuma da kake son ɗaukata suna cakinka to
inaga nan gaba idan ka rabu da ni za ka gane muhimmancina, sau ka dawo kana son
gyara kuskure lokaci ya ƙure tun da wasu sun yi min ƙawanya, kuma da ka tuna
mafarkin da kyau da ka ce ina kiranka gaskiya ba zai zama haka ba, sai dai idan
ƴaƴana nake kira".

Tun da ta ambaci maza fara'ar fuskarsa ta ɗauke, ya ji kamar ya buge bakinta har
sai ya yi jini, amma ya daure don ya ga gudun ruwanta, a fusace ya ce"Kenan Safiyya
maza kika je kike kulawa da aurena ko?"

Ta ce"Allah ne shaidata ban kula kowa ba, na dai fassara maka mafarkinka ne".

Ya tashi ya saka kayansa, ya fice daga ɗakin rai a ɓace, da mukulli ya rufe gidan
ya tafi gidan Hajiya zuciyarsa babu daɗi, lallai Safiyya ta gama canzawa, bai taɓa
zaton idan ya lallashe ta za ta cije ba, sai ga shi neman ƙure dauriyarsa ma take
yi, koma mene ne ba zai bari ta koma gida ba, haka kuma ba zai sake lallashinta ba,
su zauna a duk yadda ta zaɓa.

Ta ji sanda ya rufe gidan da mukulli, kuma da bai rufe ba ita ma ba ta da niyyar
komawa gidan, abin da bai gane ba yanzu ta gane matsayinta a wajen shi, ba zai ƙara
yi mata daɗin baki ta yarda ba, duk da ba wai ta daina jin ƙaunarsa ba ne, amma
wannan abun da ya yi mata yau rainin hankali ne mai zaman kansa, za ta zauna ko don
ƴaƴanta, amma sabon zama saboda ta miƙe ita ma babu wanda zai sake mayar da ita
karkatacciyar kuka.

Tana zaunen Baba ya kira ta, ta ɗaga ya ce"Ina ta kiran Salisu a kashe".

Ta haɗiyi yawun baƙin ciki ta ce"E ai yanzu ya fita daga gidan ma".

Ya ce"Nan gidan ya zo?"

Ta ce"Baba babu wanda ya ɓata fa, kawai saboda na dawo ya yi hakan".

Baba ya yi murmushi ya ce"Yanzu kina gidan nashi?"

Ta ce"E".

Ya ce"Ina yaran?"

Ta ce"Ina jin ɗakko su ya tafi".

Ya ce"To Allah Ya rufa asiri, ki yi haƙuri kin ji ko? Ku yafi juna".

Ta ce"To". Suka ajiye waya.

Yana zuwa gidan Hajiya ya tarar ba ta nan, ya yi sallama a maƙota inda take kai
ajiyar yaran, aka fito da su ya ɗora su a babur suka taho gida, yana ƙarasowa tun
kafin ya ajiye babur suka shige ɗakinsu cikin jin daɗi, Kausar ce ta yi kan Safiyya
ta zaunar da ita a cinya tana jin yadda ta yi kewar su, sannan ta kalli Ni'ima da
ta tsaya daga gefe kamar baƙuwa tana ɗan murmushi, ta miƙo mata hannu, ta zo ita ma
ta zauna, sai hawaye ya zubo mata tausayin yaran ya ƙara kama ta, ta ce"Na dawo, ba
zan sake tafiya na bar ku ba kun ji? Ko kun fi so na bar ku?" Suka girgiza kai
alamar a'a.

Ta tashi ta shimfiɗa musu tabarma a waje, ta hau gyaran ɗaki, kafin ta gama ya
fita ya yo cefane ya dawo ya zauna a gidan, da alama yau ba zai je kasuwar ba, tana
gamawa ta yi musu wanka ta canza musu kaya, sannan ta shiga ta gyara kitchen ɗin,
don shi ma ya yi ƙura, sai yamma sosai ta gama girkinta mai rai da lafiya, don kaji
biyu ya haɗo da su a cefanen, ita ma ta yi kewar dafa kalar abincin da take so,
gidan iyayenka ba gidanka ba ne, a gidanka ne kake da ƴancin dafa son ranka, gidan
iyaye kuma su ke da zaɓi tun da gidansu ne ba naka ba, a tare suka ci abinci da
yaran bayan ta kai masa nasa, babu wanda ya jira sai dare saboda dukansu ba su samu
nutsuwar cin abincin rana ba, har gara yaran sun sha garin kwaki a gidan da Hajiya
ta ajiye su.

Cikin yaranta ta kwanta suka yi bacci mai daɗi da sakewa sosai, ba ta je ɗakinsa
ba, shi ma bai neme ta ba. Washegari ta gaishe shi ta haɗa masa abun karyawa, ya ci
ya ƙoshi don ya yi kewar abincin gida, kullum sai dai ya ci wainar siyarwa ko shayi
a gidan Hajiya indai ba teburin mai shayi ya je ya ci indomi ba, bayan ta gyara
gida ta tsife musu kansu ta wanke tas ta tufke musu da niyyar gobe za ta tambaye
shi su je kitso.


LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL

2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[6/2, 6:12 PM] Sadiya Abdulrazak: 26

Washegari da safe sun gama karyawa ta ce masa za ta je kitso ya ce ba za ta je ba,
saboda fargaba yake yi har yanzu bai gama sakewa ba, gani yake kawai za ta iya
komawa gidan, ta ce"Haba don Allah, yaran nan kalli yadda kansu ya zama, ni ina ga
ma tun da na tafi ba a sake yi musu kitso ba. Ba ƙarya ta yi ba babu wanda ya musu
kitso har ta dawo, amma duk da haka sai da ya ji ransa ya ɓaci, saboda ta nuna
kamar Hajiyarsa ta gaza kenan ko kuma ba ta yi wa yaranta ruƙon da ya dace ba, ya
ce"E ba a yi musu kitso ba tun da kika tafi, ai har wanka da wanki ma babu wanda ya
yi musu, a haka su ka yi ta rayuwa, kin ga gobe ma kya sake barin su".

Ta yi murmushi ta ce"A lokacin ma ai kai ka ce na bar su, ba don haka ba babu abin
da zai sa na bar su".

Ya ce"Ƙwarai kuwa ni na ce ki bar su, kuma ko gobe idan za ki ƙara tafiya ƙofa a
buɗe take, amma babu inda za ki je da su, yara suna hannuna duk inda za ki je".

Suka yi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce"Baban Ni'ima kana ta ba ni mamaki
wallahi, lokaci ɗaya duk ka canza, kalli kalaman da kake yi min kamar ba kai ba".

Ya ce"Safiyya ke ba ku lura kin canza ba? Ko ba ki kula da irin rainin da kike yi
mini ba?"

Ta ce"Ni ban raina ka ba, idan ka ga raini ya shiga tsakani to namiji ne yake
rashin adalci, wani abun ina kafewa ne saboda na ga ka yi adalci, so ne ya kawo
hakan, duk mai son ka ba zai so ranar ƙiyama ka tashi rabin jikinka a shanye ba".

Ya yi shiru yana kallon hotuna a wayarsa. Ta ce"Ni na fi so idan na yi maka laifi
ka zaunar da ni ka ce Safiyya kin yi abu kaza me yasa kika yi? Idan na yi sai na
faɗa maka dalili, idan rashin fahimta ne na fahimtar da kai, idan kuma ba ni da
hujja sai na ba ka haƙuri na kiyayi gaba, idan ban yi ba na yi maka bayani, kai
kuma ka yi adalci ka saurare ni sai ka yi bincike kafin zartar da hukunci, amma kai
fa ba ka yin haka, duk abin da aka ce na yi kawai sai ka yarda".

Hankalinsa yana kan waya har lokacin, amma duk nutsuwarsa tana wajenta, ya ce"Ba
yarda nake yi ba wallahi wani abun na san ba ki yi ba, ina yarda kin yi ne saboda a
zauna lafiya, ko kuma umarnin uwa".

Ta ce"Kuma a ganinka kana yi min adalci kenan?"

Ya ce"To ai ya wuce".

Ta karɓi wayar hannunsa ta ajiye ta ce"Ni fa na fi so ka faɗa min mene ne sabbin
halayen da kake cewa na tsira? Ka ga sai na daina, ina so mu dawo kamar da mu zauna
lafiya".

Ya ce"To ni dai da ba ki da taurin kai, amma tun da na yi aure kika koya, yanzu ko
larurorin da su ka yi ta samun Ameera idan na ce ki mata girki ki duba ki ga yadda
kike yi mini, sai ki nuna ban isa ba, kuma dole a tafi a hakan, da idan muna zaune
kin ta ba ni labarai kala-kala wataran har na gaji, amma yanzu sai ki yi mini jugum
tun da na ƙara auren nan, da da wuri kike shiga ɗakina da daddare, amma yanzu
wataran sai na fara bacci ma zan farka na gan ki, kalli jiya abin da kika yi mini,
sai haka na kwana kamar mara gata, ɗan oyoyon nan kin daina, su ma yaran da suna
ganina za su taho a guje yanzu sun daina, to me na yi muku? Ɗan ƙunshin nan akai-
akai kina yi, yanzu Safiyya kin daina, da ke kike wanke min ƴan ƙananan kaya yanzu
kin daina, duk saboda na ƙara aure, kuma wannan abubuwan da na jero miki ita ma ba
yi min take ba, an ce mai mata biyu ɗan gata ni kuwa ɗan wahala ne, ana gasar
kyautatawa miji ku gasar wahalar da ni kuke yi da firgita ni, duk na rame a
maimakon ƙiba".

Safiyya ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima kenan! Ai kai da kanka ka rikita gidanka,
waɗan nan abubuwan da ka jero duk kai ka ja na daina, tun kafin ka yi auren nan
kake nuna mini wacce za ka aura ta fi ni, duk ka canza nan har yajin cin abinci ka
yi, ka ke zuwa kana ci a gidan su buduruwa, wannan ba zubar da mutunci ba ne? A ce
ba na ba ka abinci shi yasa za ka yi aure, ƙarshe ma cewa ka yi kar na sake shiga
ɗakinka sai ka neme ni, haka ɗin kuwa a ka yi, saboda za ka yi sabuwar amarya ka
gaji da tsohuwa, yanzu a ganinka zan manta abin da ka yi min na cire ni daga ɗakina
ka ba ta ka saka ni a ɗaki ɗaya? Ka ɗauki firji ka ba ta saboda kai ka siya, wannan
bai isa ya sa na janye jikina daga gareka ba na kama kaina?"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"To na ji, za a gyara in sha Allah!".

Ta ce"To ni ma zan gyara, in sha Allah".

Ya yi dariya ya ce"Oh! Ƙanwata ta zama ƴar rigima, wai har guduna take yi ma ina ji
ina gani, kuma Allah da gaske za ki iya rayuwar da babu ni a ciki?"

Ta miƙa masa wayarsa tana murmushi, ya riƙe hannunta ya ce"Ki faɗa min mana, yanzu
sai ki rabu da ni?"

Ta ce"Ai yanayi ne zai zo da hakan, kai ne ka fara furta zan bar gidan nan, komai
yana hannunka idan ka ce na zauna zan zauna, idan ka ce na tafi zan tafi".

Ya ce"Za mu zauna in sha Allah! Safiyya ai ke ce gidan nan idan na rabu da ke ban
yi muku adalci ba ke da ƴaƴanki, ƴan kwanakin nan da ba kya nan yaran sun zama abun
tausayi, ni ma fa na ɗan sha wahala ko ta ɓangaren abinci, ke ma ba za ki rasa wani
ƙalubalen ba, kin ga mu gyara mu zauna sai ya fi ko?"

Ta ce"Haka ne, ai dama kowa yana da ranarsa, ballantana zama ba yau ba ba jiya ba".

Ya ce"Yawwa bari na fita, ga shi sai ki yi har ƙunshi ko?" Ya faɗa yana miƙa mata
dubu biyu, ta karɓa ta yi godiya, shi kuma ya fita.

Daga ranar dai suka fara sabuwar rayuwa a nutse, ita da shi ɗin duk hankalinsu ya
kwanta, ya tabbatar Safiyya ita ce gidansa kuma nutsuwarsu shi da ƴaƴansa, suna yin
rayuwar farin ciki sosai a lokacin.

Bai faɗa mata Ameera za ta dawo ba, sai ganinta ta yi da safe ita da ƙanwarta,
lokacin Safiyya tana ƙofar ɗaki a zaune ita da yara, ta ɗan saki fuska ta ce"Maraba
da Sauban! Ashe yau za ku dawo".

Ameera ba ta san Safiyya ta dawo ba, don bai faɗa mata ba, ita kuma ba ta tambaye
shi ta sakankance ba ta nan kuma tana tunanin ba ma lallai ta dawo ba, sosai ta ji
haushin ganinta, ita dai a duniya ta tsani ta buɗe ido ta ga Safiyya da ƴaƴanta
suna shawagi a gidan nan, har ce masa ta yi ya canza mata gida ya kama mata haya
amma ya ce ba zai raba matansa ba.

Tana hura hanci ta ce"E Allah Ya dawo da mu".

Safiyya ta ce"Ma sha Allah! Wanka ya yi kyau, Allah Ya raya mana Sauban".

Ta ce"Amin". Safiyya ta shige ɗaki, su kuma suka shiga gyara ɗakin Ameera, can
Ameera ta shigo ɗakin Safiyya ta miƙa mata Sauban ta ce"Don Allah ga shi nan, ya
hana mu aiki".

Safiyya ta karɓe shi da bismillah tana yi masa wasa, Ameera ta koma ɗaki, babu
jimawa ma ya yi baccinsa, wajan sha biyu Safiyya ta fita ɗora girki bayan ta fito
da su Ni'ima saboda kar su taɓa shi, tana cikin girki ta ji kukansa, ta taho da
sauri sai dai kafin ta ƙarasa ta ja burki ganin Ameera riƙe da kunnen Ni'ima ta
murɗe shi tana faɗin"Don ubanki kashe shi za ki yi?" Ta hankaɗe ta da ƙarfi sai da
ta faɗi, ta fincikota ta dawo da ita, Safiyya ta ce"Ameera ya isa haka, me ya faru
ne?"

Ta ce"Kashe min ɗa taso yi, ina kawo kai na tarar tana toshe masa hanci, dama baƙin
ciki ake yi don Allah Ya ba ni namiji, idan ban da sun yi gadon baƙin hali Sauban
shi da yake namiji nan gaba ba shi ne gatansu ba? Ƴar iskar yarinya!".

Tass! Safiyya ta wanke Ameera da mari da iya ƙarfinta, zuciyarta tana tafasa ta
ce"Ba ki isa ba! Ke ba ki ma kai ba ballantana ki isa, kin yi ƙarya ki saka ƴaƴana
a cikin haukan kishinki na ƙyale ki, wannan yaran ba na ki ba ne nawa ne, saboda
haka ba ki da ƴancin ɗaga hannu ki dake su wallahi, yaran da ba ki taɓa yi musu
tsarki ba ta ina kika san wahalarsu da har za ki samu damar nuna iko akan su? To
wallahi wannan ya zama na ƙarshe, kar ki sake dukar mini ƴa!".

Ameera da ke dafe da kunci ta ce"Safiyya ni kika mara? Ni kika mara saboda na daki
ƴarki?"

Ta ce"Ƙwarai kuwa, zan ma iya yi miki fin hakan!".

Ameera ta ce"Wallahi ba ki mari banza ba, yau sai kin yi nadama!".

Safiyya ta ce"Ke ce za ki yi nadama, ke ba ki isa ki saka ni nadama ba, shi wanda
ya auro ki za ki saka nadama dama ya ce ya yi tun tuni".

Ameera ta shige ɗaki kamar kububuwa, ta ɗauki waya ta kira shi, yana ɗaukar waya
ta fashe da kuka, ya ce"Ameera lafiya, me ya faru?" Ta ci gaba da kukan ba ta yi
magana ba hankalinsa ya tashi ya ce"Ameera wai mene ne ki min bayani, ina Sauban
ɗin?"

Sai ta miƙawa ƙanwarta wayar ta karɓa ta ce"Baban Sauban Safiyya ce wallahi ta yi
mata duka ta tattakata, ta gwara kan Sauban da jikin ƙofa".

Salis ya miƙe tsaye cike da mamaki ya ce"Wace ce Safiyya kuma?" Don shi ma bai san
yau Ameera za ta dawo ba, ta dai ce masa a cikin satin nan, kuma da yake ba wani
marmarin dawowar tata yake ba sam bai saka abun a ransa ba, shi yasa ya yi mamakin
jin sunan Safiyya.

Nabila ta ce"Safiyya dai matarka!".

Ya ce"To a ina kuka haɗu?"

Ta ce"Ai mun dawo ɗazu, ina taya ta aiki..."

Ameera ta warce wayar ta kashe, don an zo inda ya kamata Nabila ta tsaya sauran
bayani nata ne. Salis ya sake kira ba ta ɗaga ba, ya yi tagumi zuciyarsa babu daɗi
yana shin Ameera ce musiba a gidansa ko kuwa kishin Safiyya ne? Daga dawowarta yau
har an fara? Shi kenan ƴar ƙibar nan dai sun rantse ba zai yi ta ba, watan
fargabarsa kuma ya tsaya, ya yi tsaki yana ajiye wayar, shi kam ba zai bar kasuwa
akan wannan halin nasu ba, idan ya koma ya ji komai, don idan ya biye musu kasuwar
ma sai ya rasa ta duka.

Safiyya ta ƙarasa girkinta, tana ta harkokinta a tsakar gida, jira kawai take
Ameera ta kawo mata raini wallahi babu abin da zai sa su dambatu a gaban ƴaƴansu.
Da daddare da ya dawo ɗakin Safiyya ya fara shiga, ta tsara masa duk yadda aka yi
amma ba ta ce ta mare ta ba, ta ce dai ta yi mata gargaɗin kar ta sake dukar mata
ƴa.

Da ya shiga ɗakin Ameera ya tarar da ita ta cika ta batse, ya ce"Ameera ashe kin
dawo, sannu da zuwa".

Ta ɓata rai sosai ba ta ko kalle shi ba.

Ya ce"Ameera me ya faru ne? Safiyya ta ce ba ta dake ki ba..."

"Bura'uban can! Ba ta dake ni ba? Kuma ka yarda ko?" Ta faɗa bayan ta miƙe tsaye.

Ya ce"Zauna Malama yanzu gidan nan ya gyaru an daina hayaniya, ki yi min bayani
kawai magana ce ta fatar baki". Ya faɗa yana haɗe gira amma cikin zuciyarsa a mugun
tsorace yake da ita.

Ta ce"Ba zan zauna ba! Ai dole ka ce haka tun da matarka ce ba ta da gaskiya, har
nan ta shigo ta karɓar min ɗa ta ce saboda na fi sakewa na yi aiki, ashe sun shirya
kashe shi ne, kawai na ji kukansa ina leƙawa na ga ƴarta tana toshe masa hanci, don
na ja kunnen yarinyar shi ne Safiyya ta dinga marina, ta hankaɗe ni har kan Sauban
ɗin sai da ya bugu, ta yi min duka ta tattakanni!".

Ya yi shiru yana kallonta, har ta dire sannan ya ce"Ita Safiyyar?"

A fusace ta ce"Ba ita ba uwarta!".

Ya ji maganar ta daki zuciyarsa don ji ya yi kamar ta ce uwarka, ya tashi a mugun
fusace ya ce"Ameera ni kike zagi? Ni kika zaga?"

Ta ce"Ni dai ban zage ka ba!".

Ya yi hanyar fita daga ɗakin, a fusace ta riƙo rigarsa ta ce"Kana nufin ta daki
banza kenan!?"

Ya fizge ya ce"Ta daki banza ta daki jaka!". Ya fice

Lokaci ɗaya Ameera ta yi wani tsalle ta dire ta ƙwalla ƙara ta fito a guje ta yi
kitchen tana wani ihu tana cewa wallahi ba ta daki banza ba, kan me uwa da wabi
yau, ko ni ko ku a cikin gidan nan!".

Salis yana jin haka ya yi ƙofar gida da gudu, sai kuma ya dawo da gudu ya shiga
ɗakinsa ya saka sakata yana leƙe ta windo. Ita kuwa Safiyya tun da ta ji ta ƙwalla
ƙara ta miƙe ta zira dogon wando, ta finciko wayar jikin TV dake saman sif, ta naɗe
ta a

Please Login or Register in order to submit comment