You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaton ƙawarta
ce ta faɗa tana wani jijjiga jiki, ita dai mai niƙab ɗin har yanzu ba ta ce komai
ba.

Ɗayar matar ta ce"Ai kuwa ba zai taɓa yiwu ba, wai an ba mai kaza ƙafa, yadda muka
yi da shi za mu shiga duka ɗakunan gidan mu duba Ameera ta zaɓi wanda ya yi mata a
bata, saboda haka ya zama dole a buɗe mana kowane ɗaki mu gani!".

"An zo daidai wajen!" Cewar Maman Affan tana rataye hijjabinta a kan igiya, sannan
ta ce"Ai kuwa ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ɗakin mai gidan za ku shiga ku ga
sirrin aure ko kuwa ɗakin matar gida za ku shiga ku gane mata sirrinta?"

Matar ta ce"Sirrin aure kuma na nawa? Abin da za ta shigo gidan nan da sati biyu
kowane sirri zai shigo hannunta? Ita kuma matar gidan har wace tsiyar ce a ɗakin
nata da za a gani a faɗa? Bayan kayan ɗakin ma shi ya yi mata!".

Tuni idon Safiyya ya kawo ruwa, ta fara karkarwa ta rasa abin cewa.

Maman Affan ta ce"Ba kayan ɗaki ba ko shi yake ba ta ci, sha da sutura tun tana
zanin goyo ba mu damu ba, domin ƙauna ce ta kawo hakan, kuma an yaba da tarbiyya ne
har ƙauna ta shigo ciki, ai wallahi duk wata ƙandararriyar yarinya da Salisu zai so
a bayan Safiyya take, kuma sauranta za ta a tarar, ɗaki dai ba za a buɗe ba, saboda
haka idan kun gama cin abincin ku yi waje! Wataƙil ya ga yunwar ne shi yasa ya
tashi baiwar Allah ta ɗora muku babbar tukunya".

Nan fa zagi da gore-gore ya kaure a tsakaninsu, sai ya zama ma faɗa ya bar zancen
Safiyya ya dawo kan Maman Affan, aka yi kaca-kaca, ƙarshe dai yarinya mai niƙab ɗin
ce ta janye ƴan'uwanta suka bar gidan.

Sannan Safiyya ta buɗe ɗakinta suka shiga, Maman Affan ta ɗauki lemo ta kwankwaɗa
tana sauke numfashi ta ce"Ɗaya kenan!".

Safiyya da damuwa a fuskarta ta ce"Me yasa za ki yi haka?"

Ta ce"Au lakwa-lakwa za ki mata kenan ta raina ki tun kafin ta shigo?"

Ta ce"Ba haka ba ne, amma yanzu kin san sai sun faɗa masa, kuma ban san matakin da
zai ɗauka ba".

Ta yi wani murmushi ta ce"Lallai Safiyya za ki sha wuyar zama da kishiya? Kenan
gaskiya za ki faɗa masa ki ce an yi hayaniyar! Tab".
Nan ta tsara mata komai ta ce kar ta sake ta ce masa an samu wata matsala, da suka
duba abincin ma suka ga ko taɓawa ba su yi ba, ga shi da yawa, Safiyya ta ce"Maman
Affan kwashi abincin nan kin ga ga wani a kitchen ya yi mana yawa!".

Ta ce"Ai mu gaba ta kaimu, yau ba sai na yi girkin dare ba". Da haka ta mata
sallama ta tafi, ita kuma ta cire kwaɗon ta ɓoye, tana ta ƙarfafa zuciyarta don kar
ya gane abin da ya faru idan ya dawo.

Ta idar da sallar magriba, suna zaune da yara tana koya musu karatu suka ji
dawowarsa, yaran suka tafi da gudu don tarar shi, saboda ya jima bai dawo da wuri
kamar yau ɗin ba, kamar yadda ta yi zato, kai tsaye ɗakinta ya shigo, kallo ɗaya ta
yi masa ta san sun tsara masa komai, tana murmushi ta yi masa sannu da zuwa. Yana
huci ya ce"Safiyya yau kin nuna min ban isa da gidana ba kenan!"

Ta yi alamun mamaki ta ce"Baban Ni'ima mene ne ya faru?"

A fusace ya ce"Ni za ki tambaya me ya faru saboda raini? Ya muka yi da ke akan
baƙin nan?"

Ta ce"Maganar baƙi ai mun daidaita, kuma sun zo sun ga gida sun tafi lafiya ƙalau".

"Kar ki raina mini hankali!" Ya faɗa yana mata mugun kallo.

Ta ce"Don Allah ka zauna, sai gumi kake dama wanka ka fara yi sai mu yi magana a
tsanake".

Ya ce"Ruwan kogi na zama ba gumi ba! Saboda wulaƙanci har ke za ki ɗakko hayar wata
mata ku haɗu ku ci wa mutane mutunci? Kuma ki kulle ɗakuna ki ce ba za su gani ba,
gidanki ne ko nawa?"

Ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan maganar kuma daga ina?"

Sai ya tsaya yana kallonta ya rasa abun cewa, don zuwa yanzu rainin hankalin nata
ya fara yawa.

Ta ce"Baban Ni'ima ka san halina, inda ban yarda da zuwan su ba ka san da zan tsaya
a kan bakana, kuma da ba zan musu girki ba, da gidan zan bari ba za su zo su tarar
da ni ba. Nan suka buga ƙofa na buɗe na tare su, suna ta ciccijewa, a ɗakina suka
zauna na ba su lemo da abinci suka ci suka ƙoshi, har ma ɗayar matar ta tafi da
sauran za ta kai wa yaranta, suka shiga ko'ina suka duba har banɗaki, sannan suka
tafi, to ban san me yake faruwa ba kuma".

Ya ce"Amma sun ce a wancen ɗakin kawai kika sauke su, kika ƙi buɗe sauran kuma kin
ɗakko wata mata har kuna musu gorin abinci".

Ta fara matsar ƙwalla ta ce"Shi kenan tun da abun arziƙi ya zama na sharri, amma ka
ba ni mamaki da ka yarda, a zatona kai za ka bawa wani labarin abin da zan iya da
wanda ba zan iya ba, sai ga shi kai za a faɗawa wani halina, ashe komai na yi da
dauriyar da na yi na tare duk ba zan tsira ba, shi yasa nake tsoron kaidin
kishiya".

Zuwa yanzu shi ma ya yarda ba ta yi ba, fitina ce kawai ta mata, ya ce"To wata
mata ce ta zo gidan?"

Ta ce"Babu wacce ta zo gidan nan yau, idan ban da Maman Affan da ta leƙo da safe,
ka fi kowa sanin da ita kaɗai nake mu'amula a unguwar nan".

Ya jinjina kai, tabbas ya san da ita kaɗai take mu'amula, kuma ya yarda da matar ya
san ba za ta taɓa aikata abin da Ameera ta faɗa ba.

Suka yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta tashi ta kawo masa abinci, ya ce ya ƙoshi.

Can kuma ya yi gyaran murya ya ce"Safiyya na rasa yadda zan yi, ɗazu mun yi magana
da ƙanwarki ta ce ɗaki ɗaya ba zai ishe ta ba, saboda kin ga ita amarya ce ba zai
yiwu kayanta su cinye ɗaki ɗaya ba".

Ta ce"To me zai hana ka haɗa mata da naka ɗakin?"

Ya ce"Ai yadda na riga na ji daɗin ware ɗakina gaskiya ba zan so na bar shi ba".

Ta ce"To ai sai ta yi haƙuri ta haƙura da ɗayan kafin Allah Ya hore maka a samu
mafita".

Ya ce"Safiyya ke ce babba, kuma kin san an ce babba juji, don haka ke za ki yi
haƙuri, ki bata wannan ciki da falon, ke ki koma guda ɗaya, shi kuma kitchen ki
kwashe rabin kayanki, don ita ma ta saɓu damar zuba nata".

Ta dinga yi masa wani kallo, ta rasa ma abin da za ta ce. Ya ce"Ki yi haƙuri mu
rufawa juna asiri".
[5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/FTn1qlcoa83BAlCQEO7ZpH

*IYA RUWA...!*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


*First Class Writers*


Page 3


Har ya fice daga ɗakin ba ta samu zarafin furta masa komai ba, saboda yadda ta
ji zuciyarta tana ƙuna ta san ba magana mai daɗi ce za ta fito daga bakinta ba, shi
yasa ta bari sai ta huce sai ta san ta yadda za ta masa bayanin da zai fahimta,
haka ta kwana tana tunanin lamarin, ta rasa da wa za ta yi shawara, a yadda ta taso
tun tana yarinya ba ta da abokin shawara sai shi, ba ta da wanda za ta kai wa
kukanta ya share mata hawaye sai shi, kuma shi ɗin ne dai yake saita mata duk wata
matsala da ta kutso rayuwarta, to yau ga shi shi ne yake yanko mata matsalar, ina
za ta kai kukanta kenan?

Washegari da safe tana kitchen ya shigo cikin shirin shi na fita, da yake ta
makara yau ɗin, ta gaishe shi ba tare da ta ɗauke ido daga kan doyar da take soyawa
ba, ya amsa, sannan ya ja turmi ya zauna ya ce"Safiyya ya aka yi ne, kin gama
tunani?"

Har yanzu ba ta kalle shi ba ta ce"Ni na ce maka ina tunani?"

Ya ce"Ai da na ga jiya ba ki yi magana na, sai na ba ki lokaci ki yi tunani, zancen
dai ɗakunan ne, kin ga dama kujerunki sun tsufa ina ta cewa zan canza miki Allah
bai yi ba, ni a shawarata kawai ki siyar da su, sai ki zuba kayan gadon a shi ɗakin
da za ki koma, idan Allah Ya hore mini na gina wannan filin nawa kin ga sai na sake
miki sababbi idan za mu tare ko?"
Ya tashi ya fara dudduba kitchen ɗin yana saita shi da hannu, ya ce"Kin ga nan".
Ta juyo ta kalle shi daidai lokacin da ta kashe gas ɗin, ya ce"Kin ga daga nan za
ki kwashe kin ga an raba daidai kenan, sai ta samu ta raɓa nata ita ma, zan sake
buga muku wasu kantocin, wannan lokokin ma ki kwashe kayanki daga ciki su sai su
zama store kawai".

Ta zuba doya a faranti ta miƙa masa, ya karɓa ya saka ɗaya a baki ya ce"Ai hakan
ya yi, ba a cuci kowa ba ko?"

Ta yi guntun murmushi ta ce"Ba ka taɓa cuta ta ba ai, ka yi haƙuri baban Ni'ima,
ina ga wannan ne karon farko da zan saɓa umarninka tun kafin aurenmu, gaskiya ban
amince da wannan tsarin ba, ba zan bar ɗakin da nake ciki ba, kuma ban amince na
raba kitchen da kowa ba".

Sai ya ajiye farantin ya haɗe gira ya ce"Safiyya ai ba amincewarki na nema ba, ina
yi miki bayani ne saboda kina da haƙƙi a kan abun, nan fa gidana ne sai yadda na
tsara, kuma dole ki bi matuƙar ba son barin gidan kike yi ba..."

"Me kake nufi?" Ta faɗa da wani irin firgici, tuni ƙirjinta ya fara lugude, ba ta
taɓa zaton jin kalmar rabuwa daga bakinsa ba, duk da tana kyautata zaton ya tauna
tsakuwa ne kawai don aya ta ji tsoro, don tana da yaƙinin shi ma ba zai iya rabuwa
da ita ba, kamar yadda ta yardarwa kanta ba za ta iya rayuwa babu shi ba.

Maganarsa ta katse mata tunani daidai inda yake cewa"Ƙwarai kuwa! Abin da kika ji
shi nake nufi, ba ki san dalilina na ƙara auren nan ba, don haka duk wanda ya yi
yunƙurin kawo mini cikas a sha'anin tuni zan rufe ido na tsinke igiyar alaƙarmu ko
shi wane ne!".

Daga haka ya fita ya bar ta a kitchen ɗin, ta zauna a kan turmi zuciyarta tana
mata zafi, ga wani abu mai ciwo da ya cushe mata maƙoshi, gefe guda kuma ta cika da
fargabar kalmar rabuwa da ya ambata, Salisun da ya ce ita ce mahaɗin rayuwar shi,
har ma yake roƙonta ko ƙaddara ta sa ta auri wani nsa kar ta yanke alaƙa da shi
saboda shi yayanta ne, kuma ƴan'uwa ba sa rabuwa yau shi ne yake nuna mata zai iya
rabuwa da ita saboda zai yi aure, ita kuwa wannan yarinyar mai suna Ameera da wani
laƙanin ta afko rayuwarsu, take shirin ruguza soyayyar ya da ƙanwarsa sahihiya tun
ta ƙuruciya? Ta share hawaye ta tashi ta haɗa abincin ta fito don ta sallami
yaranta, domin ita ta riga ta yi karinta da baƙinciki.

Bayan sallar la'asar Maman Affan ta shigo, kasa jurewa ta yi har sai da ta faɗa
mata halin da suke ciki na rabon gidan da za a yi, Maman Affan ta ce mata kar ta
sake ta yarda, ita da yara biyu za a bata ɗaki ɗaya wacce ba ta da yara ɗaki biyu?

Safiyya ta ce"Tsoro nake kar na dage daga baya na zo ina nadama".

Da mamaki ta ce mata"Nadama ta me?"

Ta ce"Kar ya rabu da ni, ina fargabar rabuwa da gidan aurena".

Maman Affan ta ce"Allah Mai iko! To a gaskiya Safiyya za ki sha wahalar rayuwa,
domin muddin kika cewa namiji sai da shi, tamkar kin ba shi sitiyarin farin cikinki
ne, haka zai ta juya ki yadda ya so, ban ce kar ki yi wa mijinki biyayya ba fa,
kuma ban ce kar ki ji tsoron rabuwa da shi ba, ai mutuwar aure ba ta da daɗi, kawai
dai ina nuna miki ke ma kina da ƴanci ne, kuma wasu mazan idan suka ja ke ma kika
ja sai ki ga saɓanin tunaninki, a maimakon su rabu da ke ɗin kamar yadda kike zato
sai su dawo su nutsu suna tarairaryarki, sai ki ga an zauna lafiya".

Safiyya ta ce"Kenan dai yanzu kina nufin na dage na ce ban yarda da rabon ba?"
Ta ce"Ƙwarai kuwa, amma fa ba da hayaniya ba, don ba mu san yarinyar nan ta wace
siga ta shigo rayuwarku ba, yanzu ki nuna masa ba zai yiwu ba, idan bai yarda ba to
ki je gidansu ki faɗawa iyayensa ki ji matakinsu".

Ta taɓe baki ta ce"Kin san yadda babarsa take jin haushina kuwa? Babu mamaki ma ita
ta tsara komai".

Ta ce"To ki tafi gidanku ki faɗawa babanki ki gani".

Ta ce"Hmmm! Zan gwada". Da haka suka bar firar suka shiga wata jikinsu duk a
sanyaye.

Sai da aka yi kwana huɗu bai sake yi mata zancen ba, a lokacin kuma auren ya rage
kwana takwas, ta faɗa masa za ta je gida ta kwana biyu ba ta je ba, kuma za ta
faɗawa Baba ƙarin auren ta san bai sani ba.

Ai kuwa ya ɓata rai ya ce"Au saboda zan yi aure shi ne za ki je ki kai ƙarata
kenan! Idan kika yi haƙuri ma ai zan sanar masa, tun da zan kai masa katin
gayyata".

Ta ce"Ni ba ƙararka zan kai ba, kawai dai zan faɗa masa ne wai ko da nasihar da zai
yi mini".

Ya ce"Wace nasiha kike nema bayan wacce kike yi wa kanki? Tun da muke da ke ban
taɓa ba ki umarni kin ƙi ba, kafin na aure ma ba ki kasa bin umarnina ba wai
Safiyya sai yanzu da har muka tara yara biyu, wallahi kin ba ni mamaki! Kuma bari
ki ji na faɗa miki ya zama dole ki kwashe kayanki daga nan zuwa jibi, don a satin
nan za su zo jere, su ma na kitchen ɗin ki san yadda za ki yi da su, don da ƙyar ma
ta yarda za ku haɗa kitchen ɗin, yanzu kayan da ta siya ma dole ta rage wasu, ke
kin ci amarcinki da gida wadatacce ita za ta yi komai a ƙuntace!".

Ranta ya ɓaci sosai, duk yadda ta so ta dake ta faɗa babu babu daɗi sai ta kasa,
saboda ba ta saba sa'insa da shi ba, kuma faɗa ba halinta ba ne, muryarta na rawa
ta ce"Ban yarda ba, kuma ba zan yarda ba, zan rage kayan kitchen, amma ba zan bar
ɗakina ba".

Ya ce"To mu zuba ni da ke, na ga wanda zai ci riba! Ga kuɗin mota nan, kuma kar ki
kai dare". Ya faɗa yana jefo mata ɗari biyar, ya fice.

Ta zauna ta fashe da kuka, yaranta da aka yi komai a gabansu suka zo suka raɓe a
jikinta, sai ta haɗa su ta rungume tana kukan ta ce"Allah ne gatanmu". Ta jima a
haka sannan ta tashi ta shirya yaran ita ma ta shirya, ba ta yi zaton ma zai bar ta
ta je gidan ba, ƙarfe goma suka bar gidan, da ta je ta tarar Baba yana shirin fita,
suka gaisa da Umma ta shiga ɗakin Baban, bayan sun gaisa ya ce"Gidan lafiya dai ko,
ya Salisun?"

Ta ce"Lafiya ƙalau".

Ya ce"Bari na fita, ai kuna nan har yamma ko?"

Ta ce"A'a ya ce kar na kai dare, dama Baba magana nake so mu yi".

Ya ce"To ina ji ki Ummi"

Ta ɗan yi jim sannan ta ce"Baban Ni'ima ne dama zai ƙara aure..." Ta tsagaita.

Baban ya ce"To aure kuma? Allah Ya sanya alkhairi, ban ji labari ba kuwa".

Ta ce"Ya ce zai kawo maka kati ai, saura sati ɗaya ma auren".
Ya ce"To Allah Ya nuna mana, ai dai babu wata matsalar ko?"

An zo wurin, don haka idonta ya kawo ruwa, ta ce"Baba akwai, ka ga ya ce dole na
kwashe kayana daga ɗakin, na koma ɗaki ɗaya ita amaryar kuma ta zauna a ciki da
falo, kuma kitchen ma wai rabawa za mu yi".

Ya ce"Subhanallah!".

Suka yi shiru na ɗan lokaci, can ya ce"Ki yi haƙuri, zan yi magana da shi na ji".

Ta gyaɗa kai.

Ya ce"Ki ƙara haƙuri kin ji, yayanki ne fa za mu yi magana in sha Allah za a
daidaita komai".

Ta ƙara gyaɗa kai, tana tausayin kanta da Baban, saboda a zaton shi har yanzu da
yayanta take tare, bai san tuni yaya ya tashi daga wannan matsayin ba yanzu ya zama
Salisu kuma mijinta, irin mijin da kuke haɗuwa da shi sama ta ka da haƙoranka cif a
baki, ya aureka ba tare da kun tantance ainahin zuciyar mutum ba, ya yi zaton har
yanzu yayanta ne mai tare mata rigima ya kuma rufa mata asiri.

"Ni zan fita, ku gaida gida". Ya faɗa yana ajiye mata dubu ɗaya, ta yi godiya
sannan ta fito.

Suna fira da Umma ita ma ta faɗa mata zancen auren, babu yabo babu fallasa ta ce
Allah Ya rufa asiri. Bayan azhar ta mata sallama ta tafi gidan yayanta dake ƙasan
layin, da yake sun saba da matarsa sosai, suka dinga fira ita ma ta faɗa mata ƙarin
auren ta dinga ba ta shawarwari, ta ce za su zo ranar tariyar, yayan nata ba ya
gari saboda haka bayan ta yi sallar la'asar ta fi gida, tana jin nauyin zuciyarta
ya ragu, kuma ta ji daɗi da Baba ya ce za su zauna da baban Ni'ima, ta san shi ma
bai goyi bayan tsarin nashi ba kenan.

Sai da ta leƙa gidan Maman Affan suka gaisa sannan ta shiga gidan dab da magriba.

Tana saka ƙafa a gidan taku ɗaya biyu ta yi ta tsaya cak, kamar yadda komai na ta
ma ya daina aiki na sakanni, sannan ta fara bin kayan da ta gani zube a tsakar
gidan da kallo, 'kenan har an kawo kayan amaryar?' Ta tambayi kanta, sannan ta
ɗauke kai daga kallonsu ta shige su Ni'ima da suke tambayarta kayan waye, sai dai
tana tura ƙofar ɗakin ta ji ta a buɗe, gabanta ya faɗi ganin ɗakin kamar an yi
shara babu komai a ciki, ta ƙarasa ɗakin gadon nan ma wayam, tamkar burodin da ya
tsumu a cikin shayi haka ta fito jiki a sake, sai yanzu ta lura da kayan gadonta ne
ashe har ma da katifarta, jagwab ta zauna a baranda hawaye suka mata sallama, tana
nan zaune har aka kira sallar magriba aka idar ta kasa tashi, sai da ta ji shigowar
shi sannan ta ɗago kai ta kalle shi, ƙure shi ta yi da kallo tana so ta gano wani
canji a tare da shi wanda zai ba ta tabbacin ba Salisunta ba ne yau ya yi mata
haka, amma ba ta ga komai ba sai mijinta yaya Salis ɗinta mai ƙaunarta da
tausayinta mai goyon bayanta.

Ta matso ƙwalla daidai lokacin da ya ƙaraso kusa da ita.

A dake ya ce"Safiyya ni na fito da kayanki, saboda ni ne mijin ke ce matar, kuma
gidana ne, don haka wannan ɗakin ɗayan shi na ba ki a shi za ki zauna, kayan
sawarku suna ciki, su wannan gobe zan shigar miki da su, kujerun kuma na ga idan
kika bar su a tsakar gida yanzu damuna ce za ta shigo sai su lalace, shi yass kawai
na siyar da su, dubu talatin aka siya, kuma da yake ban ƙarasa shirye-shirye na ari
kuɗin daga baya zan ba ki in sha Allah!".
[5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA...!*
(FID DA KAI)
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


*First Class Writers*


Page 4


Tun da ya fara magana kanta yana ƙasa tana hawaye har ya gama, suka yi shiru
na tsawon lokaci shi yana tsaye, yaran kuma suna ta wasansu suna ɗarewa kan katifa,
can dai ya sai ta ba shi tausayi ya sanyaya murya ya ce"Ki yi haƙuri don Allah!
Bari na shigar miki da katifar nan". Ya faɗa yana kiciniyar janyo katifar.

"Yayanaaa!" Ta kira shi cikin wata muryar da ya jima bai ji irinta ba, wannan
muryar tun ta ƙuruciya wacce take ba shi matuƙar tausayi, daɗin daɗawa ta daɗe ba
ta kira shi da wannan sunan ba, tun bayan aurensu ta canza masa suna take faɗa masa
na soyayya duk wanda ya zo bakinta, bayan haihuwar Ni'ima kuma sai ta saka masa
baban Ni'ima, tun daga nan indai ta ce masa Yaya to magana ce mai muhimmanci.

Yanzun ma jikinsa ne ya yi sanyi ƙalau, bai juyo ba har sai da ta ƙara "Yaya!"

A hankali ya ƙaraso ya zauna a gefenta, sai ta fara kuka ta ce"Yaya kai kaɗai nake
kai wa ƙara ka bi mini haƙƙina, amma ban sani ba ko yanzu ka zubar da wannan aminci
da ƙaunar da Allah Ya ƙulla".

A sanyaye ya ce"Ƙanwata ce ke har abada, hakan yana nufin ba zan zubar ba".

Ta ɗan ji daɗi kuma ta tabbatar da tabbas Yayan nata yana cikin hayyacinsa, ta
ce"Yaya ƙara na kawo maka, ƙarar mijina, a shekarun baya muna zaune lafiya amma tun
da ya fara zancen ƙara aure ya juya mini baya, ta kai yau ya fitar mini da kayana
waje saboda wata za ta maye gurbin ɗakunana, kuma ya hana ni kuɗin, ya zan yi
Yaya?"

Lokaci ɗaya ya tuna abubuwa da dama kuma masu nauyin da ya haddasa masa
cunkushewar ƙirji, sun jima a haka ya kasa cewa komai, ta saddaƙar ba shi da wata
magana, don haka ta tashi ta kama hannun yaranta suka yi hanyar fita daga gidan. Ya
tashi da sauri ya tare ta, ya ja hannunta ya dawo da ita ya zaunar, sannan ya ce"Ba
ki da gidan da ya fi nan, don haka ba za ki je ko'ina ba, za ki zauna da yayanki
har abada!".

Da ƙarfi ta fizge ta ce"A'a! Wannan ba yayana ba ne, mijina ne".

Ya ce"Yayanki ne kuma mijinki Safiyya, mijina bai kyauta miki ba, amma ki yi
haƙuri ki bi umarninsa ke ce da riba nan gaba in sha Allah, indai kina jin maganar
yayanki har yanzu to kar ki sake cewa komai, ki yi haƙuri kin ji ko?"

Ta ƙure shi da kallo, yayin da shi kuma kunya ta mamaye ilahirin jiki da
zuciyarsa, ya tashi don kallon waɗan nan idanun nata ji yake tamkar hukunta shi
take yi, tana zaune ya shiga da katifar, ya ɗauki tsawon ɗokaci yana ta gyara ɗakin
sannan ya fito ya ce"Ki yi haƙuri, bari na karɓo muku abinci ba sai kin yi girki
ba". Ya fice yana jin zuciyarsa babu daɗi.

Kiran sallar isha'i ne ya ankarar da ita ba ta yi magriba ba, don haka ta tashi
ta yi alwala ta shiga ɗakin da yaran tuni sun riga ta shiga, ta nemo sallaya ta
tada sallah, bayan ta idar ta shiga ƙarewa ɗakin kallo, har net ya ɗaura mata a
katifar, ɗakin babba ne don ya so ya fi falonta girma da banɗaki a ciki, yanzu ta
riga ta gane wannan yayan nata na wancen shekarun ya mutu babu shi a raye, gangar
jikinsa ne kawai a na Salis, don yayanta bai taɓa yi mata irin wannan hukuncin ba,
don haka ba za ta sake kiransa da Yaya ba ballanta ta kai masa kukanta, kamar yadda
ya faɗa ne ba ta inda ya fi nan ɗin don haka ta saka a ranta za ta yi haƙuri za ta
jure, kaza ya siyo musu da lemo, da kanshi ya juye musu a faranti, ya ɗakko kufuna
ya zuba musu lemon sannan ya fita daga gidan, yau sai ya kasa zuwa wurin Ameera, a
nan ƙofar gida ya zauna don yana tsoron kar ya yi nisa ta fice daga gidan, sai
wajan tara da mintina ya tuna da kiran da babanta ya yi masa, nan take ya tashi ya
tafi.

Bayan sun gaisa Baba ya ce"Salisu ashe aure za ka yi, ai ban ji labari ba sai ɗazu
da ta zo".

Cike da kunya ya ce"E wallahi Baba, dayake ba a buga katin gayyatar ba, dama zan
kawo maka ai".

Baba ya ce"Ma sha Allah! Gidan lafiya dai babu wata fitinar ko?"

Ya ce"Lafiya ƙalau Baba, babu komai wallahi".

Ya ce"Ai haka ake so, to sai dai ɗazu ƙabwar taka ta zo mini da zance a kan ɗakunan
gidan, wai ka ce sai ta kwashe kayanta daga ɗakuna biyu ta koma ɗaki ɗaya, su ɗaki
biyun ka saka amarya a ciki, me yake faruwa ne?"

Tun da ya fara magana gabansa ya fara faɗuwa, ya haɗiyi wani yawu don ba ya so ko
kaɗan Baba ya san da matsala a tsakaninsa da Safiyya, don shi kansa ya san a irin
halakcin da Baba ya masa idan ya ji ya cuci Safiyya ko bai yi masa magana ba shiru
ma sai ya hukunta shi, ya ce"E Baba, ba dai wata matsala ba ce, wallahi

Please Login or Register in order to submit comment