You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙarin auren
ne ya zo babu shiri, dayake umarni ne daga sama, e Mama ce ta ce sai na ƙara aure
to kuma akwai fili da na siya kwanan baya, amma ko bulo ɗaya ban fara sakawa ba,
sai na ga tun da da ɗan guri a gidan me zai hana na haɗa su lafin Allah Ya hore
mini? To dayake ita ƙanwar tawa dama kwanaki ta riga ta siyar da kujerunta ta fara
wani ɗan kasuwanci irin nasu na mata da kuɗin, sai na ga tun da iya kayan gado ne
me zai hana ta koma ɗaki ɗaya kawai, kafin a san yadda za a yi".

Baba ya yi shiru yana nazari, Salis ya ɗora da faɗin"Da farko ta ƙi yarda, amma
yanzu komawata gida mun sasanta ta yarda, yanzu ma muka gama zuba kayanta a ɗakin".

Baba ya ce"To ma sha Allah!". Sannan ya ɗauki waya ya kira ta, har lokacin tana
zaune a sallayar nan, tana kallo yaran suka gama cakalkala kazar nan suka yi bacci
ko wanke musu hannu ba ta yi ba, ta ɗakko wayar a jaka, tana ganin sunan Baba
jikinta ya ba ta Salis ɗin ya je kenan, ta ɗaga da sallama, suka gaisa ya
ce"Safiyya ya kuke ciki da zancen ɗakuna".

Ta sauke numfashi tana ƙara kallon ɗakin da shirgin kayanta, ta ce"Baba shi kenan
ai mun daidaita".

Baba ya ce"Ma sha Allah! Haka ake so, ki dinga haƙuri kin ji ko? Ya ce kin siyar
da kujerunki kin fara kasuwanci me kike siyarwa?"

Gaban Salis ya faɗi ya ji kamar ya tashi ya zura da gudu, amma hakan daidai yake
da fallasa kansa, don haka ya sunkuyar da kai yana ta salati a zuciyarsa.

Mamaki ya kashe Safiyya, ta runtse ido, tana buɗewa ta sauke su a kan shirgin
kayanta, idonta ya sauka a kan sabon zanin gadon da yayanta Aminu ya siya mata, kai
tsaye ta ce"E Baba, zannuwan gado ne nake siyarwa".

Baba ya ce"Ma sha Allah! Allah Ya sakawa abun albarka, ki ta haƙuri ibada kike yi".
Suka yi sallama ta ajiye waya, ta sani shi yayi ƙaryar nan, to idan ba ta amsa ba
za ta ƙaryata shi ne? Kafin ka hukunta mutum da sharrin da ya yi maka, ka tuna
alkhairin da ya yi maka, Salis ya yi mata halakci ya ba ta ruwa a lokacin da take
ƙishi, don haka za ta iya yafe masa komai.

Sai da ta yi wanka sannan ta kwanta, da safe bayan sun gama karyawa zama ta yi
tana ta tunani, har ya leƙo ɗakin, ya ce"Ni na fita, idan na dawo zan shiga da
kayan". Ba ta amsa ba har ya fice.

Ta ɗauki waya ta kira Maman Affan, suka gaisa sannan ta ce"Ki shigo gidana ki ga
ikon Allah!" Ba ta jira cewarta ba ta kashe wayar.

Babu jimawa kuwa ta shigo, a tsakar gida ta tsaya tana kallon kayan da mamaki,
Safiyya ta fito sai ta fara hawaye. Maman Affan ta ce"Me yake faruwa? Kar dai ki ce
min ya sake ki".

Ta share hawayen ta ce"Bai sake ni ba, ya dai fito min da kayana, ga shi har na
koma ɗakin".

Suka shiga ta ga ɗakin ta ce"To ina kujerun?"

Ta taɓe baki ta ce"Ya siyar wai ya ari kuɗin". Ta tafa hannuwa tana salati ta ce"Ya
ara kuma? Wannan wane irin rainin hankali ne haka?"

Safiyya ta yi murmushin takaici ta ce"Babu komai Maman Affan rayuwa ce, na haƙura
yanzu komai zai yi zan zuba masa ido, idan Allah Ya yi sai mun rabu ko ba na so sai
mun rabu, idan kuma addu'ata ta karɓu sai ki ga komai ya wuce kamar ba a yi ba".

Maman Affan ta sauke numfashi ta ce"Wannan gaskiya ne, ki ta addu'a, wannan
yarinyar idan ma sihiri ta yi masa Allah Ya sa ya tsaya a iya kan shi, ke dai ki ta
addu'a zihirin safiya da na maraice, ma dai mutum ba sai dai Allah! Akwai maganin
karya sihiri da yayata take haɗawa ko ba a yi maka ba idan ka yi amfani da shi
rigakafi ne, dole ki dinga karɓa duk sati kina yi Maman Ni'ima kar yarinyar nan ta
kasaara ki".

Safiyya ta ce"To na gode, yanzu mu shirya ɗakin nan na gaji da ganin shirgin nan".

Maman Affan ta yi ƙwafa ta ce"Yanzu haka za ki yi baƙi su dinga ganin gadonki?
Tsakani da Allah ɗakin gadonka ai sirrinka ne!".

Ta ce"To ya zan yi? Lokaci ne, indai Salis zai iya juya mini baya to tabbas babu
wata mace da zai aura ta tsira".

Sun haɗa gado, amma sun kasa shigar da sif ɗin, don haka ta kira shi ta faɗa masa,
sun daɗe suna jira sannan ya zo, don sai da Maman Affan ta je ta gama aikin gidanta
ta dawo musu da abinci suka karya su da yaran, suna zaune ya shigo shi da wani
yaronsa, da murmushi ya ce"Maman Affan ce a gidan? An tashi lafiya?"

Ta ce"Ni ce, ina fa aka tashi lafiya baban Ni'ima ka yanko mana aiki da sassafen
nan".

Yana dariya ya ce"A dai yi haƙuri maman Affan, kar ki jangwalo min ita".

Suka shigar da sif ɗin, suka rago kayan kitchen ɗin ma, sai ɗaki ya cunkushe filin
ɗan kaɗan ne, saboda gadonta babba ne, ga shirgi ta ko'ina.

"Ɗakin nan bai yi ba!" Safiyya ta faɗa kamar za ta saka kuka.

Maman Affan ta ce"Ni ma dai haka na gani, sam abun babu tsari babu kyaun gani".
Safiyya ta ce"Maman Affan kawai na siyar da gadon nan, na haƙura da iya katifar ina
ga ɗakin zai fi kyau".

Ta ce"Rashin sif fa babu daɗi".

Safiyya ta ce"Sai na sayi me biyu, wasu kuma na bar su a akwati".

Haka dai suka yanke shawara, nan take kuwa maman Affan ta sa ƙaninta ya zo da
dillali aka yi wa kaya kuɗi dubu sittin, suka siyar, sannan ta sa aka kawo mata sif
mai biyu mai kyau ta siya dubu goma, sai suka sake sabon shirya ɗaki, maman Affan
ta ba ta shawarar ta rago wasu kayan ta ajiye mata, sai ta ba ta manyan zannuwan
gadonta guda uku ne, da wasu kayan kitcken ɗin kuma ta fitar da kaya da yawa ta
bayar a maƙota, maman Affan tana ɗinki har na labulaye, ta je ta haɗe labule guda
biyar ta ɗinke ya zama babban, ta ɗaura igiya ta saka a kusa da katifar, sai ya
zama an yi wa katifar katanga ɗakin ya zama kamar ciki da falo sai ɗakin ya yi
kyau, sha biyu ta wuce don haka ta tafi gidanta, ita ma ta ɗora girki. Da daddare
da ya dawo ya shigo, ya ƙarewa ɗakin kallo ya buɗe labulen katifa ya ce"Mene ne
nan?" Sai ya yi wata dariya ya ce"Ikon Allah! Wato mata akwai hikima wallahi".

Ya zauna a kan san sallayar dake shimfiɗe ya ce"Ki yi haƙuri Safiyya, ba ga shi
ɗakinki ya yi kyau ba, wannan dai ko hasidin iza hasada ba shi da ta cewa wallahi,
amma Safiyya ina gadon yake?"

"Na siyar" Ta ba shi amsa ba tare da ta kalle shi ba.

Sai kuwa ya ɓata rai ya ce"Kin siyar fa!?"

Ta ce"E".

Ya ce"Dalili"

Ta ce"Ra'ayi".

Ya ce"Ni kike cewa ra'ayi ya sa kin siyar da gadonki? Kenan ni a banza kika ɗauke
ni da ba za ki yi shawara da ni ba kafin ki siyar da abu ko?"

Har yanzu ba ta kalle shi ba dai.

Ya ce"Ina kuɗin kuma nawa ne?"

Ta ce"Dubu hamsin ne kuma na tura account ɗin Baba ya ajiye mini". Ta yi wannan
ƙaryar, don maman Affan ta gargaɗe ta sosai a kan kada ta sake ta ba shi.

Ya haɗe gira ya ce"Saboda raini ko?"

"Duk yadda ka ɗauka haka ne" Ta faɗa tana tashi ta fita daga ɗakin ta shiga
kitchen, kafin ta fito ya fito zai bar gidan, tana riƙe da faranti ta ce"Abinci na
zubo maka".

Ko juyowa bai yi ba ya fice.

Washegari ya zo da kafinta aka buga wasu kantocin, sannan a ka gyara mukullan
lokokin da suka lalace, aka saka sababbi, maman Affan ce ta ce kar ta jera nata har
sai an gama bikin tukunna, don haka gas ɗinta ne kaɗai a ciki.

Ranar Lahadi ce ta kama ɗaurin aure, ranar Juma'a da safe yake faɗa mata yau za a
zo yin jere, a waya ta faɗawa maman Affan, ta ce mata ta kira wasu ƴan'uwan nata
kafin ta gama aiki ta shigo, amma ta samu masu zafi-zafi saboda tsaro, ta yi tsaye
da waya ta rasa wa za ta kira, Salma matar yaya Aminu kullum a chart sai sun yi
firar kishiyar nan tun da ta je gidan ta ba ta labari, ita ma masifaffiya ce, don
duk baƙin halin yaya Aminu ba ya iya yi mata, tana kiranta kuwa ta ce ga ta nan,
sannan ta kira ƙawarta Hafiza, ta yi sa'a ita ma ta ce za ta zo, kafin sha ɗaya duk
sun zo, baban Ni'ima ya aiko da cefane don a musu girki, Salma ta yi tsalle ta dire
ta ce ba za a yi ba, don dole Safiyya ta yarda, suka dafa iya nasu suka ci, aka
dinga fira ana ba wa Safiyya shawarwarin zama da kishiya, wasu ta ɗauka wasu kuma
ta san ba zai yiwu ta gwada ba.

Ƙarfe biyu suka ji tsayawar motar kawo kayan, suka yi sallama wata zabiya cikinsu
ta ce"Ga baƙin arziƙi idan an so".

Hafiza ta turo ɗankwali gaban goshi ta ce"Mu na tsiyar ma sai dai su shafa mana
lafiya!".

Matar ta ce"A'a yarinya mu fa alkhairi ne ya kawo mu, alkhairin haɗa raya sunnar
ma'aiki".

Wata ta ce"Ƙyale ta, ai kishi halak ne, ballantana wacce za a gallowa budurwa fil
a leda".

Maman Affan ta ce"Allah Ya sa ita ce budurcin ma, ai duk wani amarci a bayan na
Safiyya yake, ƴan matan yanzu ma da duk sanyi ya gama da su, ka ga budurwa tana
susa har ina budurcin yake? Allah Ya sa ma ba a barbaɗar a titi ba!".

Matar ta ce"Duk dai baƙin cikin tanda sai an ci waina, kuma zancen barbaɗa ai zama
ne zai nuna hakan, Salisu zai san yanzu ya yi aure!".

Haka suka dinga cacar bakin nan, suna jere suna yi har suka gama suka tafi, Hafiza
ta leƙa kitchen ɗin ta ce"Ai kun ga sun cike shi tsaf!".

Maman Affan ta ce"Dole su tattare ai tun da ba gidan ubansu ba ne!".

Sai magriba suka tafi, tana zaune a ɗaki ya dawo ya shiga ɗakinsa, ta tashi ta bi
shi ɗakin, ko sannu ba ta yi masa ba ta ce"Baban Ni'ima an yi jere, amma ka ga an
cike kitchen ɗin, ni ina zan jera nawa kenan?"

Ya ce"E ni na ce su jera duka, don ƙanwar babarta ce ta ƙi yarda ku haɗa kitchen
ɗin, kuma da na ga ba ki jera nakin ba na za ta duka ɗakinki ya cinye har na
kitchen ɗin".

Ta ce"Bai cinye ba, kuma ba zan bar mata ɗakuna na bar mata kitchen ba, saboda haka
a gyara!".

Ya ce"Gaskiya babu wanda zai saka mini ciwon kai, yanzu ana taɓa musu kaya wata
fitinar za ta iya tasowa, ki bari idan ta tare zan ce ta tattare".

"Ba zan bari ba, a yau zan tattare, fitina kuma zan iya musu ba sai ka shiga ba".
Ta fice daga ɗakin ta doshi kitchen ɗin.
[5/27, 11:32 AM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA...!*
(FID DA KAI)



BY
SADIYA ABDULRAZAK


*First Class Writers*
Page 5


"Safiyya! Ke Safiyya!" Ya kira ta a tsawace, amma hakan bai hana ta k'arasawa
kitchen din ba, tsaye ya same ta tana neman ta inda za ta fara, ya b'ata rai ya
ce"Na fad'a miki kada ki tab'a musu kaya!".

Ta ce"Ba fa dauka zan yi ba, matsarwa zan yi".

Ya ce"Ni dai na fad'a miki kar ki tab'a komai, idan ta tare za ta tattare su, shige
mu tafi". Ta coge tana huci ta kuma k'i ko motsi, suka d'auki lokaci a haka sannan
ta fita ta koma d'aki, babu jimawa ya shigo ya ce da ita"Ina mukullin kitchen din?"
Ta dakko ta ba shi, sai da safe tana fitowa ta ga gas dinta a k'ofar d'aki ya fito
mata da shi ya kulle kitchen din, ta jinjina kai ta shiga harkokinta zuciyarta
cunkushe da bak'inciki. A ranar Asabar d'in wacce ta kama saura kwana d'aya d'aurin
aure da yamma y'an'uwansa suka zo, kowacce fuskarta d'auke da walwala, wannan
tsohuwar k'iyayyar tun ta k'uruciya ita dai tana nan daram a idanunsu, bayan sun
gaisa Mariya ta ce"Ni Safiyya sai na ga duk kin k'are a tsaye".

Ta yi murmushin takaici ta ce"Ko dai idonki ne? Amma ni kam ko jiya baban Ni'ima
sai da ya ce mini sai k'iba kike kamar ba wacce za a yi wa kishiya ba, na ce to me
zai dame ni bayan na san mijina mai adalci ne?" Duk suka yi saroro don kuwa ba su
yi zaton jin haka daga bakinta ba, ita kanta da a da ne shuru za ta yi, amma yanzu
dayake tana ta d'aukar darasin da ake biya mata tana da amsar ba su, Anti Fa'iza ta
tab'e baki ta ce"Yo shi har ya yi wani zancen k'iba? Waye silar k'ibar tata?
Mutumin da tun tana yawo da guntun kashinta yake ci da ita, ballantana yanzu da ya
kawo ta gida ya rufe ake cin duniya".

Mariya ta ce"K'warai kuwa, amma yanzu ai Allah Ya taro shi, tun da ya dawo
hayyacinsa, sai ya yi auren nan zai gane a da goguwa ya yi ba angwanci ba, ai wani
abun sai Salisu, a ce ka yi hidimarka ka yi ta amarya? Ita kuwa wannan ko cokali
bai siya mata ba".

Haka suka yi ta firar su, tana bin su da kallon ko a jikina, har suka gama sannan
suka mik'o mata leda, wai ga kayan fad'ar kishiya. Ta fad'ad'a fara'arta ta karb'a
ta bud'e, atamfa ce guda d'aya da takalmi da mayafi, ta ce"Allah Ya amfana".

Fa'iza ta ce"Ga shi nan, iya abin da ya bayar kenan, ana yi da kai ya fi ba a yi
da kai, wai sarki ya zama mai unguwa".

Safiyya ta ce"Laa! Babu komai wallahi, ai ya yi mini bayani, ya ce ya samu matsala
ne a kwanan nan, amma daga baya zai yi mini akwatina, na ce ma ya hak'ura tun da a
gidan nan wane irin kaya ne ban saka ba, amna kin ga ya k'i, ya ce sai ya yi dai".
Ta k'arasa maganar da murmushi kamar babu damuwar komai a zuciyarta, wannan duk
cikin darasin da ta fara koya ne na kissa, kuma ta lura zai kai mata, domin kuwa
tashin farko ta ga fuskokinsu sun canza.

Daga k'arshe suka fad'a mata za a yi wuni gobe a gidansu idan za ta je, ta ce
Allah Ya kaimu.

Sai da suka tafi ta k'ara kallon kayan, atamfar ba wata babba ba ce, wai ita zai
bayar a kawo mata a matsayin kayan fad'ar kishiya, ta jinjina kai ta je ta adana,
don tuni ta ware kayan da za ta saka, akwai less guda biyu da ya d'inka mata ba ta
tab'a sakawa ba. Da daddare yana dawowa ya shigo d'akinta, a fusace ya ce"Safiyya a
kan me za ki had'a ni da uwata?"

Gabanta ya fad'i, ta ce"Subhanallah! Me na yi kuma?"
Ya ce"Yaushe muka yi da ke zan k'aro miki kayan fad'ar kishiya?"

Shaf ta manta da an yi haka sai yanzu ta tuna, ta kauda kai gefe ta yi murmushin
jin dad'i, ashe dai sosai ta cusa musu bak'iciki daurewa kawai suka yi.

"Ina magana kin juya mini kai saboda raini ko!?" Maganarsa ta dawo da ita daidai,
sai ta fara rawar murya ta ce"To baban Ni'ima mai zan ce maka? Indai shekarun da
muka yi da kai bai sa ka gane halina ba to ko na yi maka bayani ba za ka gane ba,
aure fa za ka yi, kishiya za ka yi mini, idan ba ka kwantar mini da hankali ba bai
kamata ta yar ba, akan me zan yi k'aryar za ka k'ara min kaya? Na tab'a yi maka
hakan? Me na yi wa y'an'uwanka ne? Meye laifina saboda kana sona?" Sai ta fashe da
kukan k'arya.

Jikinsa ya d'an yi sanyi domin ya san Safiyya ya san halinta, tabbas k'arya ba
halinta ba ne, don haka ya yarda makircin su y'an'uwansa ne kawai tun da ya san ba
sa son ta, ya jinjina kai sannan ya ce"Ke ba za ki yi taro ba ne? Na ga ba ki
tambaye ni kud'in da za ki yi wani abun ba".

Ta ce"To ai na ga ba sai na tambaya ba idan ka yi niyyar yi mini abu shi yasa na
zuba ido".

Ya ce"To zan ba ki dubu goma sai ku yi girki da bak'inki, don ba kud'i ne da ni ba,
duk na kashe kud'i a auren nan wallahi, jiya da na yi lissafi abun har haushi ya ba
ni".

Ta ce"Ikon Allah! Kai da ka cika umarnin uwa ai riba za ka k'irga in sha Allah,
kuma dama d'akko amarya ai ba a yi a araha ba".

"Hmm! Ke dai a yi sha'ani kawai Safiyya". Ya fad'a yana d'an kishingid'a.

Shuru na d'an lokaci sannan ta ce"baban Ni'ima ka kulle kitchen".

Ya ce"Don Allah kar ki sa mini ciwon kai, zan bud'e za ta tattare kayan ke ma ki
samu waje". Sai kuma ya yi tsaki ya tashi ya fice daga d'akin.

Washegari da ta kama d'aurin aure tun sassafe maman Affan ta shigo, ita ma matar
yaya Aminu ta yo sammako, suka yi cefane suka hau aikin abinci, k'arfe goma angon
Ameera, yayan Safiyya kuma mijinta ya fito fess cikin shirin tafiya d'aurin
aurensa, a lokacin tana d'akinta tana shirya su Ni'ima, ya shigo, ta d'ago ta kalle
shi ya yi mata murmushinsa wanda yake matuk'ar burge ta a shekarun baya, ita ma
murmushin ta yi, tana kallon yadda yi kyau sai k'amshi yake "To mu za mu tafi, kin
san goma ne, mun ma yi latti". Maganarsa ta katse ta daga kallonsa, ta sauke ajiyar
zuciya ta ce"Allah Ya sa a gama taro lafiya, Allah Ya ba ku zaman lafiya".

Ya washe baki ya ce"Amin Ya Allah! Ko ke fa, sai yanzu na tuna da Safiyyar yayanta,
amma da duk kin bi kin canza kin birkice mini, kin san fa ina son ki, amma bari dai
na dawo za mu tattauna". Ya fice, ta bi bayansa da kallo tana mamakin wai yau ita
ce mijinta zai mata kishiya, ashe da yake ta cewa ba zai iya had'a ta da wata ba
saboda gudun aikata rashin adalci duk dad'in baki ne, ta sauke ajiyar zuciya tana
tunanin kalar zaman da za su yi.

Babu laifi ta yi taro, mak'ota da d'aid'aikun y'an'uwan duk sun shigo, ana ta
raha ana dariya, har ta ji kamar ba ta da wata damuwa, sai da magriba ta yi gari ya
fara duhu aka kawo amarya, kowa ya sulalewa aka barta ita kad'ai sannan ta fara jin
babu dad'i, ta yi zaton ma yau d'in sai an dambatu da su maman Affan, amma sai aka
samu sauk'i, saboda habaicin y'an kawo amaryar da sauk'i, ko don sun ga idan sun yi
ba a bar musu ne oho.
Tana jin shigowar ango da abokansa, a lokacin tana d'aki shuru ita da yaranta,
tana ta jiyo shewarsu dayake akwai sauran k'awayenta da ba su tafi ba, babu jimawa
kuma suka yi sallama a k'ofar d'akinta, suka shigo da amarya lullub'e cikin mayafi
suka zaunar da ita, har wata k'awar tata tana cewa"Zauna a hankali k'asa ne, babu
kujera".

Wata zabiya a cikinsu ta ce"To Anti Safiyya ga amanar k'anwarki mun kawo, sai a
yi hak'uri Allah Ya kad'e hau".

Safiyya ta yi murmushi, tana ayyana kenan yara ne ma za su kawo amanar ba iyayenta
ba, duk da dai ba girmansu ta yi ba, amma ai ta ci girman uwar gida, ta ce"To Allah
Ya ba mu zaman lafiya, mu dai gidanmu na aminci ne, kuma karamci gadonsa muka yi".

Wata ta ce"Mu ma kam ba daga nan ba, za ku zauna lafiya da Ameera indai kin so".

Ta yi murmushi ta tashi ta d'akko kayan fad'ar kishiya da aka kawo mata, dama suna
nan a ledar ta ajiye a gaban amarya ta ce"Allah Ya had'a kanmu". Duk suka amsa da
amin, sun fito za su tafi baban Ni'ima ya ce su bar amaryar a d'akin, ya je ya raka
su ya dawo ya kulle gida, sannan ya shigo, a gefen katifa ya zauna yana wasa da
hannun Kausar ya ce"Ku ba ku yi bacci ba? Ga sabuwar Anti an kawo muku".

Ni'ima tana daga kwance ta ce"Abba a nan za ta kwana?"

Ya ce"E kullum ma a nan za ta kwana, kin ga d'akinta can, ita ma babarku ce, za
kuna shiga kuna yin wasanku". Sai ta yi shuru.

Ya yi gyaran murya ya ce"To Safiyya ga Ameera nan, k'anwarki ce duk da dai ta girme
ki a shekaru, don Allah ki ja girmanki, ba na son fitina kuma na san ba halinki ba
ne, ku rufa mini asiri ku zauna lafiya don na samu damar gudanar da adalci a
tsakaninku".

Safiyya ta ce"In sha Allah!".

Ya ce"Na gode, Ameera ku zauna lafiya don Allah ku had'a kanku saboda kan yaranku
ma ya had'u kin ji ko?"

Ta ce"To".

Sun tashi za su fita Safiyya ta ce"Baban Ni'ima zancen kitchen d'in, da ta shiga ta
tattare".

Kamar jira yake ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Safiyya yaushe kika zama
haka ne? Ameera wuce mu je".

Suka fice, ita kuma ta yi murmushi dama tana sane ta yi zancen, don Ameerar ta
d'an tada masa hargitsi ko banza amarcin ya rage armashi.

Bayan su Ni'ima sun yi bacci shiru ta yi, tana ta tuna rayuwarsu ta baya, da irin
yadda amarcinsu ya kasance cikin soyayya da sahihiyar k'aunar, cike da tausayin da
ta san Allah ne ya sakawa yayan nata domin kawo mata tallafi a baud'addiyar
rayuwarta ta baya. Ba ta san iya tsawon lokacin da ta d'auka tana tunani ba, ta dai
ji k'arar k'ofa alamar an bud'e k'ofar d'aki, babu jimawa kuma ta ji ana yin wanka,
aka dawo aka banka k'ofar d'aki da k'arfi, ta kalli agogo ta ga sha biyu da rabi,
can wajan d'aya da rabi ta k'ara jin an bud'e d'akin still an sake yin wanka, wanda
kamar da gayya ake shek'a ruwan, sai kuma ta ji tafiya an zo k'ofar d'akinta, ta
windonta ta ji wata murya ta ce"Second round!".

'Second round' Ta maimaita kalmar a zuciyarta, sai da ta yi tunani na sakanni
sannan ta gane abin da ake nufi, sai kuma ta ji an sake bud'e k'ofa an rufo, ta
sauke ajiyar zuciya ko za ta ji sauk'in abin da ya tokare mata k'irji, yanzu ita
ake fad'awa second round? Ita da suka shekara biyar da mijin, to kuma wane dare ne
jemage bai gani ba?




08028966015
[5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAK


FIRST CLASS WRITERS


Page 6


Sai ta fara tunanin to me ya hana ta wanka a d'akin nashi, sai ta zo band'akin
tsakar gida? Kuma ma k'ofar d'akinta ta ji ana bud'ewa da rufewa ba ta mai gidan
ba, kenan dai shi ya biyo ta d'akinta ya kwana. Ta sauke numfashi a ranta ta ce'ku
yi ku gama'.

Washegari sassafe ta fito, ta k'wank'wasa k'ofar d'akin shi "Baby ce? Shigo
mana".

Ta ce"A'a ba ita ba ce, wannan uwar Baby ce".

Sai kuwa ya fito ya hade rai ya ce"Safiyya rainin naki har ya kai haka? Ni kike
zagi?"

Ta yi murmushi ta ce"Ni fa ba da wata manufar na fad'a ba, tun da ni na tsufa na
wuce Baby, Khausar ai Baby ce, ita babynka ni kuwa guzuma uwar baby". Ta k'arashe
da y'ar dariya.

Ya had'e gira ya ce"Mene ne?"

Ta ce"Mukullin kitchen".

Ya ce"Safiyya don Allah me ya sa ba kya so mu dinga rufawa juna asiri?"

Ta ce"Na dinga rufa maka dai, ni nawa a rufe yake in sha Allah! Kawai ka ba ni
mukullin kitchen".

"Ameera!" Ya k'wala mata kira.

Ta fito tana wani yauk'i cikin kayan bacci ta ce"Honey".

Ya tsaya yana kallonta kamar ba tare suka kwana ba jiya, Safiyya ta kalle ta ta
ce"Mun tashi lafiya?"

"Lafiya k'alau" Ta amsa da gadara.

Safiyya ta ce"Ma sha Allah! Ya kwanan bak'unta?"
Sai ta yi dariya mai kama da ta rainin hankali ta ce"Ni da gidana ina zancen
bak'unta?"

Ta yi murmushi ta ce"Haka ne fa".

Ameera ta k'araso ta ce"Me ake yi ne Honey?"

Safiyya ta karb'e zancen ta ce"Wai mukullin kitchen zai ba ni, na gyara kayanki na
samu wurin zuba nawa, ke ma ko d'an ruwan zafi kin ga na dafa miki".

Ameera ta yi wa baban Ni'ima kallon tuhuma. Ya ce"Ki yi hak'uri Ameera ku biyu za
ku had'a kitchen d'in, dama cewa na yi idan kin tare sai ki gyara ta zuba nata".

Ta tab'e baki ta ce"Illar auren mijin wata kenan, kuma sai da na ce maka ka kama
mini gidan haya ka

Please Login or Register in order to submit comment