You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aiman ta tare ƙofa tana leƙen yaranta dake tsakar gida ta ce"Safiyya lafiya
kuwa?"

Safiyya ta ce"Lafiya lau, kitso muka zo ko za mu samu".

Da sauri ta ce"A'a ba za ku samu ba!" Ta banko ƙofarta ta bar Safiyya tsaye da
ɗumbin mamaki.

Ta ƙasara gidan Mariya, suka gaisa take faɗa mata kitso ta fito kuma duk ba ta samu
ba ma, a nan gidan ta yi sallar magriba saboda ba girkin dare za ta yi ba, suka ci
tuwo a gidan sannan suka koma gida.

Washegari ta tambaye shi zuwa gidan Salma ya barta, ta san sai dare za ta dawo
saboda haka ta ɗauko hijjabin Ni'ima da ya yage yau ɗin ta ba ta ta kai ɗinki a
maƙota, babu jimawa Ni'ima ta dawo da hijjabin ta ce wai an ce ba za a ɗinke ba,
Safiyya ta ɗauka shirme ta je ta yi kawai, saboda haka da suka shirya za su tafi ta
saka hijjabin a jaka suka fito, a ƙofar gida tana yaran mai ɗinkin suna wasa yara
biyu suka shige gida da gudu, Safiyya ta ciro hijjabin ta miƙawa ɗayan yaron da
yake zaune ta ce"Kai shiga ka bayar a ɗinke min wannan".

Har ya karɓa wani yaro da ya zo wucewa da almar tsoro ya ce"Kai Sadik ba an ce mu
daina kula wannan matar da ƴaƴanta ba, shi ne za ka je aikenta?" Ya tafi da sauri.

Yaron da sai yanzu ya tuna, ya saki hijjabin a ƙasa da mamaki Safiyya ta ce"Kai ba
za ka je ba ne!?"

Daidai lokacin da babarsu ta fito, fuska kicin-kicin ta ce"Safiyya me ya haɗa ki da
ƴaƴana? Me kike yi musu?"
Safiyya ta ce"Ikon Allah! Me zan yi musu? Ɗinkin hijjabin nan na ce ya miƙa miki
fa".

Matar ta ce"Ba zan ɗinke ba, kuma babu ruwanki da ƴaƴana, don duk abin da ya same
su ke ce!". Ta shige gida ta bar ta tsaye da mamaki. Ta saka hijjabin a jaka suka
tafi, har ta baro gidan Salma mamaki ya ƙi barinta jikinta duk ya yi sanyi.

Washegari da safe ta sallami yara sun tafi makaranta ta ji ana buga mata ƙofar
gida da mugun ƙarfi, a tsorace ta tambayi waye? Daga wajen ta ji muryar mata sun ce
su ne, ta sako hijjabi ta buɗe, tun kafin ta ce wani abu ta ga mai ɗinkin jiya ce,
da wata wacce ba ta santa ba.

Ɗayar matar ta ce"Wannan ce Safiyyar?"

Mai ɗinki ta ce"Ita ce".

Matar ta kalli Safiyya ta ce"Kin gan ni nan? Duk duniya babu shege ko shegiyar da
nake tsoro, wallahi ba maita ba ko tsafi sai dai ya gan ni ya ƙyale, saboda haka
salun alun shige mu je ki tsallake ɗan mutane ki sakar masa kurwa!".

Wata irin bugawa ƙirjin Safiyya ya yi, ta ce"Me kuke nufi?"

Ba ta ankara ba matar ta wanka mata mari, ta ce"Yaron da kika bawa hijjabi da
ƙaryar ya miƙa miki ɗinki, kika kame kurwarsa ga shi nan yau da zazzaɓi ya kwana!
Don haka dole sai kin tsallake shi, idan kuwa kika kashe shi babu abin da zai hana
mu kashe ki!".

Lokaci ɗaya Safiyya ta fara karkarwa muryarta tana rawa ta ce"Wai ni kuke zargi da
maita? Ni?"

Mai ɗinki ta ce"To a unguwar nan uban waye bai san ke mayya ba ce!? Ashe shi yasa
aka koro ki daga inda kika taso shi ne kika zo nan za ki lashe mu ɗaya bayan ɗaya!
To wallahi ki ci kowa ki kwana lafiya ban da kurwar ahalinmu!".

Hayaniyar da suke yi ce ta fito da matan maƙota daga gidajensu, kafin wani lokaci
an fara cika kowa yana tofa albarkacin bakinsa, babban abin da ya ba ta mamaki babu
mai goyon bayanta kowa ya yarda wai ita mayya ce.

Ana cikin haka sai ga Mariya wacce labari ya je mata, ta daɗe tana jin ƴan unguwar
suna raɗe-raɗin Safiyya mayya ce, sai dai ta faɗa musu ba haka ba ne, ba ta so ta
zaƙe a ce don matar yayanta ce, sai yau da maƙociyarta ta shigo take ce mata ta
fito kallo ga shi can Safiyya ta kame kurwar yaro daga ba shi hijjabi jiya ya taɓa
ya kwana da zazzaɓi, Mariya ta sako hijjabi ta fito a kiɗime, tana zuwa ta tarar
har an cika maƙil Safiyya sai kuka take, har da wanda suka fara janyota tana
fizgewa ga ciki abun ya bawa Mariya tausayi, nan ta fara tijara tana ƙaryata mutane
da cewar sai an shiga koto kowa sai ya bada shaidar inda aka ga ta yi maitar,
sannan ta ɗaga waya ta kira Salis, yana kallon kiran ya ƙi ɗagawa don ya yi zaton
Safiyya ce mai kiransa.

Ƙarshe dai mazan unguwar da ba su kai ga fita ba su suka kwantar da tarzomar, ta
hanyar cewa Safiyya ta kira babanta da mijinta su zo za a yi sulhu, Safiyya kai
tsaye lambar Yaya Aminu ta bayar, ta yi sa'a yana garin kuma yana gida a kwance,
tana kuka ta yi masa bayani, da mugun ɓacin rai ya duro daga kwancen da yake a
gado, ko bayani bai yi wa Salma ba ya fice zuciyarsa tana tafasa.

Tun kafin ya ƙaraso ya hango dandazon mutane a ƙofar gidan, hakan ya sa ya gane
kwatancen da ta yi masa, sosai ransa ya ƙara ɓaci, ya yi tsalle ya ɗare bishiyar
darbejiya ya karyo reshi ya tattare hannun riga ya taho a fusace, yana ƙarasowa ya
ce"Kowace shegiya ta bar wajen nan!" Ido ya koma kanshi, bai tsaya wata-wata ba ya
fara ɗaga ice yana zugawa duk wanda hannunsa ya kai kansa, kafin ka ce kabo ihu ya
kaure unguwar matan kowa ya yi nesa, mazan ne suka riƙe shi suna zaginsa yana
ramawa duk da wasu ma sun haife shi, amma idonsa ya rufe.

Da ƙyar ya nutsu aka tafi gidan mai unguwa tare da mai ɗinkin har da yaron da ba
shi da lafiyar, nan aka ce sai mijinta da babanta sun zo, Safiyya ta dinga kiran
Salis bai ɗauka ba Aminu ya ce"Ni nan ni ne a matsayin ubanta, shi kuma mijinta ɗan
iska ne shi da babu duk ɗaya, saboda haka a yi duk abin da za a yi kawai!".

Nan matar ta mai da magana, mai unguwa ya ce a ina ta ji cewar Safiyya mayya ce?
Ta ce a unguwa ta ji, sai da ta faɗi sunan matar da ta faɗa mata baki da baki aka
zo da ita, ita ma ta ce a gari ta ji, aka ce sai ta faɗi wacce ta faɗa mata, ita ma
ta faɗa, aka zo da matar, ƙarshe dai aka gano a bakin Hajara maganar ta samo toshe,
saboda haka aka tiso Hajara a gaba wacce mijinta ya biyo bayanta, aka ritsa ta aka
ce ta faɗi a inda ta ji, ta yi tsuru-tsuru tana ta kame-kame, sai da mijinta ya ce
idan ba ta faɗi gaskiya ba daga nan gidansu za ta wuce sannan tana kuka ta ce
kishiyarta Ameera ce ƙawarta, kuma ita ta ba ta dubu ashirin don ta ƙirƙiri
maganar, kowa ya yi mamaki, nan aka tisa ƙeyar Hajara aka tafi har gidan Ameera,
ashe Salis yana gidan ma bai fita ba zazzaɓi yake yi, aka yi sallama ya fito, ya bi
mutane da kallon mamaki, har da Aminu da bai taɓa zuwa gidansa ba, ga Safiyya kana
kallonta za ka san ta sha kuka, daga ciki suka shiga aka kira Ameera aka mai da
zance, dama Ameera tun da ta ga Hajara gabanta ya yanke ya faɗi, don ta san aiki ya
lalace, Salis ya kalli Ameera ya ce"Haka ne maganar da aka faɗa?"

Ta gyaɗa masa kai tana sharar hawaye. Salis ya ji ɓacin rai sosai ya ce da mutanen
da mai unguwa"Don Allah ku yi haƙuri, wannan maganar ta gida ce, za mu yi wa tufkar
hanci, a yi haƙuri don Allah!".

Nan aka yi wa Hajara faɗa sosai, da kuma cewa za ta bi duk gidan unguwar nan ta
faɗa musu buyanta aka yi ta yi mata sharri, ita ma Ameera aka yi mata nasiha, aka
bawa Safiyya haƙuri, sannan suka tafi suka bar Safiyya da Aminu.

Salis ya kalli Safiyya ya ce"Don Allah ki yi haƙuri, zauna a nan, bari na yi wanka
na raka ki gidan".

Ya juya zai tafi, Aminu ya janyo jallabiyarsa ya maido shi baya, Salis ya kalle shi
da mamaki, Aminu ya ce"Kai wa ka mayar ɗan iska tsakanin ni da Safiyya?"

Salis ya haɗe rai ya ce"Aminu ka san dai ina da ƴancin korarka daga gidana ko?
Saboda haka ka fi ce mini!".

Aminu ya ce"Kai ban da ƙaddara ta haɗa ƙanwata da kai ka isa ma na kalle ka
ballantana kejin gidanka? Safiyya tashi mu tafi!". Ya yi maganar yana kallonta.

Safiyya ta tashi, Salis ya ce"A matsayina na mijinki ban yi miki izinin fita ba!".

Aminu ya ce"Da gaske kake?"

Safiyya tana shirin fita Salis ya ce"Idan kika fita daga gidan nan kar ki sake ki
dawo!".

Ta ce"Me hakan yake nufi?"

Ya ce"Kawai dai na faɗa miki ne, sai dai ki bi shi ya ajiye ki a gidansa!".

Aminu ya ce"Za ta bi ni, kuma wallahi ba za ta dawo ba sai ranar da ka saka
gwiwarka a ƙasa ka ba ni haƙuri ka ce na dawo maka da ita".

Salis ya ce"Ko da hakan zai katse igiyar aurenta?"
Aminu ya ce"Wannan shi zai fi komai sauƙi ma".

Daga haka ya yi hanyar ficewa daga gidan, Safiyya ta bi bayansa, ko waiwaye babu,
suka fice suka bar Salis tsaye kamar an shuka shi.



LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL

2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[6/6, 9:15 AM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*Nationwide delivery*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin
farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅


36

Safiyya ta ce"Tsoro nake fa kar Baba ya yi faɗa".

Aminu ya ce"To faɗan me zai yi indai da adalci? Sai ki zauna mijinki da matarsa
suna juyi da rayuwarki, har ki zauna ana yi miki ƙazafin maita saboda tsabar raini,
yana cewa a yi sulhu a gida, yana kare matarsa kuma ki dinga tunanin za ki ci gaba
da rayuwa da shi? To mu tsaya tun daga hanya mu samu matsaya, ni na gaji da rayuwar
rashin ƴanci da kike yi, zan sama miki mafita ne, idan kina so yau zan tafi da ke
inda za ki huta ki zama mutum, idan kuma ba kya so to ki nunawa Salisu duniya ba ki
da wanda ya fi shi, ki juya ki koma ki zauna a inda ya ajiye ki, amma wallahi duk
ranar da kika sake kawo min ƙara ke ko ƙafarki na gani a gidana ko Salma ta ce na
ba ki wani abu Allah sai kin ga rashin mutunci!".

Safiyya kamar za ta yi kuka ta ce"Yaya Aminu ni fa ban ce ba na son ƴanci ba, Baba
nake gudun..."
"Dalla kyale shi! Shi ma daga baya zai san haƙurin da kika yi, yanzu dai za ki bi
ni?" Ya tambaye ta babu wasa a fuskarsa.

Ta ce"Yaya idan na je gidanka na tare ba zan takurawa Salma ba?"

Ya yi dogon tsaki ya ce"Allah wadaran naka ya lalace! To idan ba waɗɗamsul basiratu
ba Safiyya ina yi miki maganar ki yi nesa ki huta kina zancen gidana? Kina gidana
ai kamar kina gidan Salisu ne, mu je ki kwaso kayanki tukunna dai".

Suka hau adaidaita sahu, suka je gidan Safiyya ta haɗa akwati da duk abubuwanta
masu muhimmanci, sai da ta fito za su tafi ta fara kuka, da mamaki ya ce"Safiyya
idan fa kina son mijinki ki yi zamanki".

Ta ce"Yarana fa? Suna makaranta".

Aminu ya yi tsaki ya ce"Idan kin tafi da yara ta ya za a san muhimmancinki? Sai ya
kai wa matar tashi ko uwarsa!".

A sanyaye ta wuce suka tafi, gidansa suka je ta yi wanka ta ci abinci sannan Aminu
ya faɗawa Salma abin da ya faru, ya kalli Safiyya ya ce"Safiyya Baba bai nuna mana
muhimmancin dangin babarmu ba, su kuma duk maza ne kin ga ita kaɗai ce mace, ku
mata kun fi zumunci shi yasa duk su ma ba sa nemanmu, to kin ga ni daga baya na
neme su duk da sau ɗaya na taɓa zuwa, amma muna waya sosai da su, ina Baba Garba da
na ba ki lambarsa?"

Safiyya ta ce"Ina ga mun yi waya kamar sau uku".

Ya ce"To kin ga ina ta so dama na samu dama mu je tare, to tunani nake kar wannan
ɗan iskan mijin naki ya hana, shi yasa na ƙyale ki, ranar da na je gaskiya matarsa
tana da kirki sosai, don haka ina tunanin can gidan zan kai ki a Gombe ki yi
zamanki ki huta na wani lokaci, har sai kin dawo mutum, shi kuma idan ya yi hankali
ya neme ki sai na kora masa warning idan ma kuma mun samu abin da muke fata ya sake
ki shi kenan, ko ni zan samo miki wanda ya fi shi in sha Allah".

Safiyya ta yi na'am da wannan shawarar, don ita ma ta gaji tana so ta yi nesa da
gidan Salis ɗin, amma tunanin ƴaƴanta duk ya sanyaya mata jiki. Salma da ita ma
abun ya dame ta ta ce"Amma Love ba ka ganin Baba zai shiga damuwa? Kuma idan ya san
kai ne ka ɗauki Safiyya anya ba zai yi fushi da kai ba?"

A fusace ya ce"To Salma tashi ki je ki faɗa masa tun kafin mu tafi! Je ki faɗa masa
ya biya ki abin da kike nema a duniya, me ma ya zaunar da ke a nan wai muna
sirrinmu?"

Ta tashi tsam ta ce"Ku yi haƙuri rabon ayi ne ya zaunar da ni". Ta fice daga ɗakin,
sai ya bi ta da kallo ya yi murmushi, halinsa ne faɗa shi yasa har ita yake yi
mata, sai dai idan ta yi fushi ya san yadda zai yi ya gyarota, don sosai yake son
Salma da farin cikinta, musamman da ba ta taɓa haihuwa ba, sai yake ganinta kullum
kamar yarinya take ƙara zama.

Sai da suka yi sallar azhar sannan suka fito suka ɗauki hanyar tafiya Gombe, bayan
ta faɗawa mai babur ɗin su Ni'ima ya kai yaran gidan Hajiya, a mota ana fara nisa
da tafiya Safiyya ta ji iska tana shigarta har zuciyarta, wanda hakan ya ƙara mata
sanyin jiki, fata take a ranta Allah Ya zama gatan ƴaƴanta, kuma Ya sa wannan
tafiyar ta zame mata alkhairi.

A gidan Salis kuwa Aminu yana tafiya da Safiyya ya shiga ɗakin Ameera da take
zaune dirshan a ƙasa abun duniya da kunya sun yi mata yawa, a fusace ya shigo yana
huci ya ce"Ameera burinki dai ki tozarta Safiyya ko? Burinki na sake ta ki zauna da
ni ke kaɗai ko, yanzu har ke za ki je ki biya kuɗi a ɓata mata suna? Inda ba a yi
sulhu ba an shiga koto ya za ki yi? Ko kina tunanin ni zan fito da ke ne? To
wallahi ba ki isa ba dai a nan gidan ba, wallahi wannan ƙarin auren bai yi mini
rana ba, tun da na aure ki ban huta ba, matata ba ta huta ba, duk na birkice sai
ƙarewa nake a tsaye kamar kuɗin guzuri, to ki shiga hankalinki wannan ya zama na
ƙarshe da za ki shiga harkar Safiyya, kuma burinki ba zai cika ba! Ba zan saki
Safiyya ba, ba zan sake ta ba, wallahi ba zan sake ta ba!".

Ameera ta yi kukan kura ta miƙe tsaye ta yi tsalle ta dire a gabanshi kamar za ta
shige jikinsa, cikin ƙaraji ta ce"Kar ka sake ta ɗin! Na ce Salisu kar ka sake ta!
Kuma wallahi yau sai mun yi takife a gidan nan!" Ta fita da gudu ta yi kitchen, sai
ga ta ta fito da taɓarya, cikin dakiya ya tsaya yana muzurai saboda abokinsa da ya
ba shi shawarar ya daina tsoron matansa don sun tada aljanu, duk da zuciyarsa bugu
take yi amma ya dake ya ce"Bisimillah Ameera ƙwala min, ina jiranki!" Sai ta yi
mamaki, kuma ta kasa ƙwala masa ta tsaya tana ta huci kamar zakanya, hakan ya
ƙarfafawa Salisu gwiwa ya shiga ɗakinsa da gudu, ita kuwa da ta ga hakan ta mara
basa baya tana faɗin"Ka tsaya mana! Ka tsaya mu ga ƙarshen ƙaryarka, mu za ka
rainawa hankali?"

Salisu da dama abun duka ya shiga nema da bai samu ba ya fito ya shiga ɗakinta,
wayar TV ya fizgo, ita ma da take ta binsa tana shigowa ya shiga zumbuɗa mata yana
faɗin"A'uzubillahi minash shaiɗanirrajim!" Idan ya faɗa sai ya zabga mata wayar ya
tofa mata yawu, da ta yi yunƙurin tashi ya taɗe ƙafarta ta koma, kuma shi
tsakaninsa da Allah duk aljanu yake duka, don haka abokinsa ya faɗa masa irin
wannan ba mutum kake duka ba, indai kana ta maimaita a'uzubillahi ba su isa su yi
maka komai ba, don haka ya ƙara zage damtse yake ta zane ta yana a'uziyya.

Ameera da ta jigata a wahale ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, za mu tafi, mun tafi ba
za mu sake ba!".

Salisu da yau yake jinsa kamar wani jan wuya kuma ya cika jarumin jarumai ƙara
shauɗa mata wayar ya yi yana cewa"Da uban me yasa kuka shiga jikin matata? Me ya
kawo ku kuka hargitsa min gida?"

Ya ɗaga bulala zai ƙara mata ta ce"Don Allah Salisu ka yi haƙuri, wallahi Safiyya
ce ta turo mu, kuma ita take hargitsa maka gida".

Ya ƙara shimfiɗa mata bulala ya ce"Kenan ba za ku daina sharri ba!". Sai kuwa ya
cire jaɗɗabiya ya ajiye a gefe, ya ɗauki waya yana gyara ta zai shiga sabon zagon,
Ameera ganin da gaske kasheta yake son yi da sauri ta fara jero atishawar ƙarya
tana cewa"Mun fita, wallahi mun fita, attishawa! Ga matarka ta dawo mun bar ta har
abada!".

Salisu ya ce"Ni za ku rainawa hankali? Kun fita kuma kuke magana daga jikinta?
Lallai ba ku daku ba ashe" Ya ɗaga ya sake zabga mata.

Ta fara kuka sosai ta ce"Ameera ce ba aljanu ba Honey don Allah ka yi haƙuri,
wallahi ni ce, kashe ni za ka yi? Dama ƙarya nake, ba ni da aljanu, Safiyya ba ta
yi min turen komai ba na ƙarya ne wallahi!".

Salisu ya ce"Ameera".

Ta ce"Na'am!"

Ya ce"Ameera ke ce?"

A wahale ta ce"E wallahi ni ce, maman Sauban ce Babynka ce".

Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna yana haki, ashe ga magani a gonar yaro sai rashin
sani, ai bai san da gaske ana zane aljanu a zauna lafiya ba sai yau ɗin, ya ce"To
tun da sun tafi mu dawo maganarmu! Me ya sa kika yiwa Safiyya sharrin maita?"

Tana kuka ta ce"Wallahi babu komai, tsautsayi ne kawai da sharrin shaiɗan".

Ya ce"To ba zan lamunta ba, don haka yanzun nan ki haɗa kayanki ki tafi gidanku sai
na neme ki".

Ta ce"To!" Ta tashi da sauri, don wani mugun tsoronsa take ji, kar ta yi maganar da
zai yi zaton aljanun ba su tafi ba, ta haɗa akwati, ta goya Sauban da take ta
bacci, ta saka hijjabi ta tafi, tana jin ilahirin jikinta yanda yake mata zugi, sai
karkarwa take yi, ko karyawa ba ta yi ba, ta karya da masifa.

Tana tafiya ya yi wanka ya tafi kasuwa, ya san zai samu kira daga Hajiya, amma
wannan karon ba ya jin zai iya sauraron kowa akan abin da Ameera take yi masa, haka
sai ya ga ta gaji da zaman gidan zai neme ta. Shi kuma Aminu idan bai fita daga
hanyarsa ba zai shayar da shi giyar mamaki, domin a yanzu ya fishi iko da Safiyya
tun da matarsa shi, ya san Aminu bai ƙi ya saki Safiyya, to kuwa sai dai ya mutu
don auren shi da Safiyya babu saki ko da kuwa ƙiyayyar da yake ji akanta za ta yi
ajalinsa, ita ma alƙwari ya yi ba zai neme ta ba, sai dai ta dawo da ƙafarta, don
ya san Baba ma ba zai bar ta ta zauna ba ai, da haka ya shiga harkokin shi na
kasuwa.

Sai sha biyu Hajiya ta kira shi, ya ɗaga suka gaisa ta ce"Salisu me ya faru ne na
ga yaranka an kawo su da unifom wai babarsu ce ta ce a kawo su ba ta nan?"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Hajiya su zauna a nan ɗin, idan na dawo zan yi miki
bayani".

Ta ce"To gaskiya ni dai ba za ka min na wancen karon ba, ka ajiye min yara na yi ta
fama ni ba lafiya ba, kuma ka dinga iyayin ba na kula da su, don haka ka zo ka
kwashe su, ka kaiwa Ameerar, meye amfanin matan biyun? Ai ana ƙara aure ne don idan
dama ta ƙiya a koma hagu!".

Ya ce"Yi haƙuri Hajiya sai na zo ɗin". Suka ajiye waya, ta zuba musu abinci suka
ci, haka suka wuni da unifom a jikinsu tun da babu kayan da za su saka.

Ameera tana shiga gida ba ta bi ta kan Ummanta da ke bin ta da kallo ba, ganin
yadda ta shigo a birkice ga idonta kana kallo ka san ta sha kuka, ta shige ɗaki, ta
sauke Sauban, ta cire hijjabi ta cire riga ta yi ɗaurin ƙirji ta kwanta ta saki
wani marayan kuka, Umma da ta biyo ta burki ta ja tana kallon jikin ƴar tata da ya
yi ruɗu-ruɗu da shatin bulala, ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah Ya
raba mu da mugun ji da gani, Ameera me zan gani haka, wane shegen ne ya yi miki
wannan ɗanyen aikin? Waye ya yi miki dukan da ko ni ban taɓa yi miki irinsa ba?"

Ganin Ameera ta ƙi ko motsi sai ma sautin kukan da ta ƙara, ta ce"Ke tashi don
ubanki ki yi min bayani, wane isasshen ne ya dake ki haka?"

Ameera ta ce"Shi ne fa, Salisu ne".

Sai jikin Umma ya ɗan yi sanyi ta zauna ta ce"Kama ki ya yi kin ɗauki kuɗi?" Ta
girgiza mata alamar a'a.

Ta ce"To uban me kika yi masa?"

Ameera duk ta yi mata bayani tun daga farko har ƙarshe, Umma ta yi tagumi ta cire
ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ke me ya kai ki yiwa mutum sharrin maita? Kin san kuwa
shari'ar maita ba ta mutuwa? Yau idan suka kai mu kotu ya za mu yi? To bari ki ji
ko gidan nan da muke ciki za mu siyar sai kuɗin sun ƙare a kotu, gaskiya ba ki da
tunani, ni dai na haifi raguwa lusara, ashe ke ba ki san rayuwar nan ta zama iya
ruwa fid da kai ba? Ke har yau ba ki san kissa ba? Tun farko me ya hana ki tsalle
ki ce ita Hajara sharri ta yi miki? Me yasa kika amsa kin aikata? Allah na tuba ko
kisan kai na yi indai daga ni sai gawar zan amsa ne? Ke kam an yi shashasha! Shi
kuma zai zo ya same ni, wallahi sai ya san ya yi miki wannan dukan, na rantse da
Allah har Hajiyar yau sai ta san ba a taɓa min ƴa a taɓa banza, idan ma ta kama a
raba auren sai ya sake ki, ki zo ki yi idda ki samu wani, ai ba kwantai kika yi ba,
na ɗauka na ba shi!".

Ameera ta ce"Umma ni fa ban ce ina so ya sake ni ba, kuma da kike cewa na zo na
zauna a nan, na ga omon wanki ma daga gidana nake tara miki, haka kawai na zo na
zauna nama ma sai na shekara tab!".

Umma ta ce"To mayya don ubanki ki koma, ki koma ki ci nama, idan ba ki ci ba ai shi
ya cinye ki, wannan ai wulaƙanci ne har ya saka bulala ya dake ki wai ruƙiyya? Kuma
ma ban ce kar ki sake yin aljanun nan ba dama?"

Ta ce"Tsautsayi ne, kuma don na ga da yana tsoro ne, abun yana kai min idan na yi,
amma ba zan sake yi ba".

Umma ta ce"To tashi ki yi wanka ga ruwan zafi nan a wuta, kawo kuɗi idan akwai sai
a siyo miki madara ki sha shayi, a samo miki magani ki shafa a jikinki".

Ta ɗakko jakarta ta miƙa mata dubu ɗaya, Umma ta karɓa ta ce"Wanke ƙafata zan yi na
je gidan Hajiyar ta zo ta ga halin da kike ciki".

Ameera ta ce"A'a Umma ki ƙyale su, za su zo da ƙafarsu, don wallahi ba zan koma ba
sai sun ɗanɗana rashina sosai, sai ya sha wuya kafin na koma". Umma ta fita ta haɗa
mata ruwan wanka, kafin ta gama ta siyo madara da maganin shafawa, tana shan shayi
tana shafa mata, tana ta zagin Salisu har danginsa.


Dab da magriba Safiyya da Aminu suka sauka a Gombe, jikinta a sanyaye Aminu riƙe
da akwati suka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, duk da ya ga a buɗe

Please Login or Register in order to submit comment