You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsakaninta da Allah
so ne irin na ba ka so ka ga an fi ɗanka a komai. Da daddare Salis ya zo za su
tafi, Umma ta ce"To ga ta nan sai a lallaɓa Allah Ya ba ta lafiya, don Allah sai a
guji ɓacin ranta saboda kasan masu matsalarta da ransu ya ɓaci sai su taso, mun
gode Allah Ya haɗa kanku".

Salis ya ce"In sha Allah za a kiyaye Umma Allah dai Ya yaye mata".

Ta amsa da amin sannan suka tafi. Suna hanya, cikin yanayin nuna ta yi kewarsa ta
kwantar da kanta a bayansa, ƙirjinsa ya yi wata irin bugawa, saura kaɗan su faɗi,
ya ce"Ameera lafiya?"

Ita ma da ta tsorata saboda gargadar da babur ɗin ya yi ta ce"Mene ne?"
Ya ce"Ai na ji kin kwanta a jikina, na ce to ko jikin ne?"

Ta ce"A'a fa ka san fa na yi kewarka sosai".

Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, saboda har ga Allah tsoronta ya fara yi, shi tunani ma
yake yadda za su kwana waje ɗaya, yadda ya ji an ce tana buge-buge tana zubar da
mutane, idan suka motsa yanzu ya zai yi da ita? Da wannan zulumin suka ƙarasa
gidan.

Safiyya ba ta san yau za ta dawo ba, tana kwance a ɗakinta tana chart ta ji
shigowarsu, dariyar Ameerar ce ankarar da ita tare suka dawo gabanta ya faɗi ta yi
addu'ar neman tsari daga masifa, tsakani da Allah sati biyun nan da ba ta nan ta fi
ji daɗin rayuwar gidanta, haka su ma yaran ta lura sun fi sakewa su yi wasansu a
tsakar gida, shi yasa idan ta tuna za ta dawo sai ranta ya ɓaci.

Ɗakinta suka wuce ya buɗe mata, ta shiga ta fara gyara shi daga ƙurar da ya yi, shi
kuma ya shiga ɗakin Safiyya, bai zauna ba ya ce"Kin ga yau Ameera ta dawo, ta ji
sauƙi".

Safiyya ta ce"An yi ƙaiƙayin kenan?"

Ya ce"Ba a yi ba, tun da sun lafa kuma ai shikenan".

Ta ce"Ko tsoro na ji to na sa suka lafa?"

Ya ce"Kayya Safiyya a bar zancen haka don Allah! Allah dai Ya rufa asiri, akwai
abinci?"

Ta ce"Akwai mana".

Ya ce"Da ɗan yawa?"

Sarai ta san inda ya dosa, ta ce"Akwai mana daidai yadda kake ci".

Ya ce"Ai wai da na ga yau ga Ameera ban sani ba ko ba ta tsaya ta ci a gidan ba".

Ta ce"Ikon Allah! Ba ga kitchen ma, ai ina ga na rage kayan miya, kuma ma akwai
barkono".

Ya ce"Haba Safiyya ta ya za ta yi girki daga dawowarta?"

Sai ta tashi ta shiga kitchen ta fito masa da abincinsa ta kawo ba ta sake bi ta
kansa ba, ya gama tsayuwarsa ya ɗauki abincin ya shiga ɗakinta, daidai ta gama
sharar tana kunna turaren tsinke ya ce"Sannu daga zuwa kin hau aiki, ga abinci".

Ta ce"Kai mana ɗakinka kawai, gani nan zuwa".

Ya je ya kai ya zauna yana jiranta, sai da ta sake yin wanka ta shirya cikin kayan
bacci sannan ta shiga ɗakin, yana kallonta ya ji ta burge shi, amma da ya tuna
mutanen kanta sai tsoro ya kama shi, ya haɗiyi wani yawun fargaba, ya buɗe kular,
jollop ɗin shinkafa ce da ta ji kayan lambu, ya zuba ya matsa kusa da ita ya ɗiba
ya kai mata baki, tana ci ta yamutse fuska, ya ce"Lafiya?"

Ta ce"Ba na son ƙamshin, kamar zan yi amai".

Ya ce"Subhanallah! Ya za a yi kenan?"

Ta ce"Da zan samu doya da miya ita nake sha'awa".
Ya ɗan ji fargaba don ya san ba lallai Safiyya ta dafa ba, amma ya dake ya ce"To
bari sai a dafa miki, ina zuwa". Ya fita

Ta janyo farantin ta yi cokali biyar ƙwarara ta sha ruwa ta ture shi yadda yake,
don dama kawai so take Safiyya ta san ta dawo. Yana shiga ɗakin Safiyya ya ce"Maman
Ni'ima ba a yi bacci ba?"

Ta ce"Tukunna dai".

Ya ce"Dama kin ga wallahi Ameera ce wai ta kasa cin abincin, ta ce doya take
sha'awa da ƴar miya, shi ne na ce don Allah ko za ki dafa mata?"

Daga ganin yadda yake maganar ta san dole ce ta kawo shi, ya ba ta tausayi amma
hakan ba zai sa ta yi wa matarsa girki ba, ta ce"Doya da miya da daren nan? To ai
da ka siyo mata, ba akwai a bakin titi ba?"

Ya ce"Ai dayake kin san mai ciki ita ta fi so a miyar a ɗan saka alayyahu haka don
inganta lafiya".

Bai san maganar cikin haushi ta ba ta ba, ta ce"Ai kuwa ka ga babu alayyahu a
gidan".

Sai yanzu ya ga ashe ya kwafsa ya ce"Dama fa alayyahun cewata ne, dafa mata haka
ɗin ma".

Ta ce"Baban Ni'ima yanzu kai za ka yarda Ameera ta ci abun hannuna? Ni da nake son
illata ta, ai kamata ya yi ta kiyaye ni".

Ya ce"Haba Safiyya magana ba ta wuce ba kuma?"

Ta ce"Ba ta wuce ba, babu yadda za a yi na sake bawa matarka abuna, ya muka ƙarke
akan kunu?"

Ya sani tun da ta kafe ba za ta dafa ba, don haka ya fice daga gidan, ya je ya siyo
doyar dama yana da niyyar siyo mata kaza sai ya taho da ita da lemuka masu sanyi,
da ya kawo ya juye mata a plate ta ce"Wai siyowa ka yi?"

Ya ce"Ai Baby tunani na yi kar a sake maimaita yadda aka yi a kunu shi yasa, har ta
tashi za ta dafa na tuna na ce ta bar shi".

Ba ta ce komai ba ta fara cin doya, shi kuma yana cinkafa, suka gama suna cikin cin
kaza Safiyya ta yi sallama, Salis ya amsa ba ta jira izini ba ta shiga, zaune a
cinyarsa ta tad da ita yana ba ta kazar a baki, Safiyya ta tsallake su ta nemi waje
a katifa ta yi kwanciyarta.

Salis mamaki ya kashe shi ya ce"Safiyya lafiya dai ko?"

Ta ce"Me ka gani?"

Ya ce"Wane irin wulaƙanci ne haka kin zo kin haye katifa ranar kwananta?"

Ta ce"Lissafa dai, yau ai ranar kwanana ne".

Ameera cikin fusata ta ce"Kin yi sati biyu da mijin kuma yanzu ki ce wai ranar
kwananki!?"

Safiyya ta ce"Ke bar ni na yi da shi, ke ba ki kai na yi da ke ba tukunna".

Ta ce da shi"Da ta tafi ka ce min ga yadda za a yi da kwana? Ba ka ga ina fashi ba?
To ranar kwananta ce nake tsallakewa, ka lissafa ka gani yau ranar kwanana ce gobe
zan fita daga girki".

Ya yi shiru, can dai ya ce"Ameera haka ne, ƙyale ta gobe sai ki zo".

Ameera ta kumbura tana huci, ya tashi ya ja ta ɗaki ya ba ta haƙuri don ba ya son
ɓacin ranta musamman a yanzu da ta zama a lallaɓa auren zamani, a can suka ƙarasa
cin kazar sai da ta kwanta sanna ya fito ya rufo mata ƙofa, ya koma ɗakinsa.

"Safiyya kar ki sake yi mini haka! Wannan ai raini ne, me yasa tun ɗazu ba ki min
bayani ba?" Ya faɗa a fusace

Ta yi kamar ba ta ji sa ba, ya fice daga ɗakin, har bacci ya ɗauke ta bai dawo ba,
sai wajan ƙarfe biyu ta farka ta kura har yanzu bai dawo ba, baƙin ciki ya turnuƙe
ta don ta san Ameera ya bi ɗakinta suka kwana kenan ita ya barta da katifa, tashi
ta yi ta koma ɗakinta, tana zuwa ta same shi kwance a kusa da ƴaƴan shi yana
baccinsa hankali kwance, ta yi murmushi ta yi shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, sannan
bacci mai cike da nutsuwa ya ɗauke ta.

Bayan sati ɗaya da dawowar Ameera, watarana da sade Safiyya ta shiga kitchen za
ta ɗora girki Ameerar ta shigo tana wani zazzare ido ta ce da Safiyya"Baiwar Allah
fita za mu yi girki!".

Safiyya ta yi mamaki ta ce"Ƴar aiki ta fita saboda matar gida za ta yi girki ko?"

Ta ƙaraso dab da Safiyya ta daka mata wata tsawa cikin ƙarajin da har Salis sai da
ya jiyo ta ta ce"Ki fita muka ce!!!".

Safiyya ta ce"Ba zan fita ba don kutumar ubanku!".

Tass! Ameera ta wanka mata mari, daidai shigowar Salis ita ma Safiyya ta zage ta
fesawa Ameera mari, Salis ya ce"Innalillahi! Haba Safiyya ba ki..."

Kafin ya ƙarasa Ameera ta yi kukan kura ta faɗa kan Safiyya ta rufe ta da duka,
Safiyya da ranta ya gama ɓaci, zuciya ta ciyo ta ta rufe ido ita ma tana kai wa
Ameera duka ta ko'ina, nan da nan kayan kitchen suka fara fareti komai yana ta
kansa, don ma ba ta kunna gas ba.

Salis ganin Safiyya ta fi jibgar Ameera a ruɗe ya ce"Safiyya ciki ne da ita fa,
kuma ba ita ba ce aljanu ne, kin san fa aikin mai aljanu!".

Safiyya cikin ƙaraji ta ce"Ni ma ai ina da su, ni masarauta ce a kaina don kaza-
kazar uban na kan nata!".

Ta ja ta ƙiii ta kai ta jikin bango ta maƙure ta, shi kuma Salis tsoron aljanu ya
hana shi ƙarasawa ya raba su, har sai da Ameera ta sulale ƙasa tana wani farfar da
ido, ya ɗora hannu biyu aka ya ce"Shiken Safiyya kin kashe ta, kin kashe mai
ciki!".

Safiyya a haukace ta wawuro taɓarya ta yo kanta idonta ya rufe, Ameera tana ganin
halaka ta tashi ta yi kan Salis da gudu, amma ina kafin ta ƙaraso ya kwasa a guje
ya yi ɗakinsa ya danna sakata, sau ta afka ɗakinta ta kullo ƙofa.


LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL

2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank
KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: PAID PAGE
16

Safiyya ya yi jifa da taɓaryar tana huci, duk iskancin Ameera ba ta taɓa zaton za
ta iya saka hannu ta dake ta ba, wato za ta fake da aljanu ta dinga dukanta tana
cin bulus, ta saka a ranta ko aljanun gasken ne ba za ta zuba ido ba sai dai idan
ta ga abun ya fi ƙarfinta. Ta koma kitchen ɗin ta gyara kayanta da suka zubo wasu
har sun fashe ta ɗora girkinta har lokacin jikinta bai daina tsuma ba. Shi kuwa
Salis zaune ya yi a ɗaki yana tunanin dama ita ma Safiyya tana da aljanu ashe, kuma
da alama ma har sun fi na Ameera, shi yanzu ya zai yi da su kenan, don muddin aka
ce za su dinga wannan damben shi kam zai ma iya bar musu gidan su cinye kansu, babu
wacce za ta illata shi don ya san tunkarar mai aljanu sai wanda ya shirya, ta windo
yake leƙe har Safiyya ta gama girkinta ta fito daga kitchen ɗin. Ita kuwa Ameera
tana ɗakinta kwance girjinta sai bugu yake, ta daku duk da dai ita ma babu laifi ta
jibgi Safiyyar, ta yi mamaki ƙwarai don ba ta yi zaton Safiyya tana da ƙarfi ba,
ita ta yi zaton za ta ji tsoronta ne sai ta dinga fakewa da aljanun tana ɗan saita
mata hanya ko da mari ne, ashe ba zai yiwu ba, wannan plan ɗin bai yi ba dole a
haƙura da shi ko wataran reshe ya juye da mujiya, tana nan kwance tsawon lokaci ta
ji ƙarar wayarta ta ɗakko tana dubawa ta ga Salis ne, ta ɗaga, ya sauke ajiyar
zuciya ya ce"Yawwa, Baby ya jiki?"

Cikin takaici ta ce"Kai ɗin kana ina?"

Ya ce"Ina kasuwa!".

Ta ce"Amma kana kallon halin da nake ciki shi ne ka fita ko ka duba ni?"

Ya ce"Ba haka ba ne, na ƙwanƙwasa a hankali saboda ban sani ba ko bacci kike yi kar
na tashe ki".

Ta ce"Jikina duk ciwo yake yi, yanzu me zan ci?"

Ya ce"A ki dafa wani abun mana".

Ta ce"Na ce maka ban da lafiya!"

Ya ce"To bari na aiko miki, don Allah kar ki sake kula ta, idan babu dama ki tafi
gidan Hajiya ki wuni".

Ta yi harara kamar yana kallonta ta ce"Babu inda zan je!".

Ya aiko mata da abinci, ta ci tana so ta fito ta yi wanka ta kasa saboda har
kunyar Safiyya take ji. Shi kuwa Salis kiran Safiyya ya yi ya ce"Safiyya ya jikin?"

Ta ce"To! Dama ba ni da lafiya ban sani ba?"

Ya ce"To Safiyya ina lafiya ta ishe ku? Allah dai Ya yaye kawai, don Allah ki tafi
gida ki ɗan wuni mana".

Ta ce"Me kake nufi?"

Ya ce"Babu komai kawai saboda na ga kin kwana biyu ba ki je ba shi yasa".

Ta ce"To, zan biya har gidan Yaya Aminu ma".
Ya ce"A dawo lafiya". Suka yi sallama ta yi murmushi da ta lura Salis ɗin da gaske
tsoron mai aljanu yake yi, ta shirya suka tafi, ba ta samu Baba a gida ba don haka
ba ta daɗe ba ta da suka gaisa da Umma ta tafi gidan Yaya Aminu, kaf ta kwashe
labari ta bawa Salma suka ci dariya sosai, Safiyya ta ji daɗin firar su ta yaye
mata damuwa, sai dab da magriba ta koma gidansu suka gaisa da Baba, saboda Salis ne
zai zo ya ɗauke ta.

A ɓangaren Ameera ta ji daɗin fitar Safiyya, don haka ta tashi ta shiga kitcen duk
rabin kayan abinci ta kwashe hatta mai da magi ba ta bar su ba, ta yi wa Umma waya
ta aiko ƙanwarta ta tafi da su, kuma ta bawa Umma labarin badaƙalar da suka karya
da ita yau ɗin, Umma ta ce to kar ta sake gwadawa tun da dai abun bai karɓe ta ba.

Safiyya tana dawowa ta ga kamar an mata bincike a ɗaki, sai kuma ta ga wayam babu
firjinta, gabanta ya faɗi ta tafi ɗakinsa yana shirin shiga wanka ta ce"Baban
Ni'ima ko dai yau an shigo mana gida?"

Ya ce"Kin ga babu firjinki ko?"

Cike da mamakin yadda aka yi ya sani ta ce"Ƙwarai kuwa ashe ka sani ma".

Ya ce"Ki yi haƙuri wallahi Ameera ce tun da ta gamu da wannan larura take yawan
shan ruwan sanyi, shi ne na ce to tunda dama ɗakin naki a matse yake kawai bari na
ba ta firjin idan ya so daga baya na siyo miki ƙarami".

Ta ji baƙin ciki ya rufe ta, ta ce"Kenan dama saboda ka ɗauki firjin ka ce na tafi
gida!"

Ya haɗe rai ya ce"Ba fa na son raini! Idan na yi niyyar ɗauka ban isa na ɗauka a
gabanki ba ne?"

Ta ce"Ka isa, tun da kai ne ka siya dama don ka ƙwace me zai dame ni?" Ta fice daga
ɗakin ranta a ɓace.

Daga ranar tana ji tana gani Ameera ta mallake firjinta, sai kuma ta tsiri sarar
jone wutar ɗakin Safiyya, ga shi ana tsananin zafi, haka kawai tsakar dare sai ta
fito ta cire wata waya, wutar ɗakin Safiyya ta ɗauke, haka za ta kwana cikin zafi,
sai washegari a nemo mai gyara kuma babu wanda ya gane, ƙarshe Salis da ya gaji ya
ce shi ya daina gyaran nan ta yi haƙuri idan ya samu kuɗi zai canza waryar wajen
kawai, haka tana ji tana gani ta rasa wutar nefa.

Daga nan Ameera ta shiga kwasar kayan abinci babu kama hannun yaro, da ta faki
idon Safiyya wuf sai ta kwaso wani abun ta kawo ɗaki, ƙanwarta ta zo ta saka a
hijjabi ta fice, har Safiyya ta fara zargi don ta ga nan da nan kayan abinci sun
ƙare sai an ƙaro wanda suke ɗakinsa, wataran Safiyya za ta kwaso na ɗakinsa, da
mamaki ya ce"Safiyya ba shekaran jiya aka ɗibi kayan abinci ba?"

Ta ce"Wallahi ni ma ina ta mamaki, ka ga babu komai a kitchen ɗin".

Ya ce"To wane irin girki kuke yi haka?"

Ta ce"Ni dai yadda nake yi da haka nake yi har yanzu, ban sani ba ko ita".

Daga nan ya fae faɗa akan saurin ƙarewar kayan abinci, kuma iya Safiyya kawai yake
yiwa, bai taɓa yi wa Ameera faɗa ba, da Safiyya ta gaji ta ce masa a raba kayan
abincin ya dinga bawa kowa tana, sai a gane ta inda abun yake, shi ma ya gamsu da
wannan shawarar don haka ya yi wa Ameera bayani, aka fara raba kayan abinci, kowa
da lokar da yake zuba nasa, sai Ameera ta ce idan kun san wata ba ku san wata ba,
ba ta yin girki sai ta ga Safiyya ta gama, idan ta shiga sai ta kwashe kayan
abincin Safiyya ta dafa, nata kuma ta aika gida, bayan kwana biyu aka gane kayan
abincin Safiyya ne yake saurin ƙarewa don haka Salis ya dinga yi mata faɗa, abun ya
dame ta ta rasa gane me yake faruwa.

Watarana ta zo yin girki, ta san ta bar taliya ɗaya loka amma ta ga wayam babu, ta
buɗe lokar Ameera don ta ɗauki wacce za ta dafa, kasancewar shi ya daina barin
mukulli a gida, tana buɗewa ta ga babbar leda a ƙulle, ta kunce kawai ta ga taliya,
macaroni, shinkafa, har da mai wajen kwalba biyu, ta shika da mamakin me yasa
Ameera ta ƙulle su da ban, ai kuwa ta mayar mata ta ƙulle, ta ɗauki taliya ta dafa.

Ta saka ido sosai a shige da ficen Ameera don haka ta ga lokacin da ta ɗakko ledar
ta dawo da ita ɗakinta Safiyya tana ta mamaki, da yamma ta ga ƙanwarta ta zo wacce
take yawan zuwa don har ta fara mamakin zuwan nata, ba ta daɗe ba ta fito za ta
tafi hannunta da abu a hijjabi, Ameera ta rako ta.

Safiyya ta yi wuf ta tashi ta ƙarasa wajensu ta kira sunan yarinyar kamar yadda ta
ji Ameerar tana faɗa ta ce"Nabila ɗan tsaya".

Duk suka juyo suna kallonta, Ameera ta haɗe rai ta ce"Lafiya dai ko?"

Safiyya ta ce"Ita ta kawo hakan".

Ta ce da Nabila"Fito da abun hijjabinki zan ɗan gani".

Ita da Ameera duk gabansu ya faɗi, Ameera ta ce"Ban gane ba fa!"

Safiyya ta ce"Ai so nake ki gane ɗin".

Ta fincuko hijjabin yarinyar ta warci leda, leda ta fashe sai ga kayan da ta gani
ɗazu sun tarwatse a ƙasa har da ƙullin madara,milo da suga, ta ce"Ikon Allah ke
kuma yunwa ake yi a gidan naku? Kina ji Salis yana cigiyar inda ake kai masa abinci
kika ƙi yi masa bayani! Ni'ima maza miƙo min wayata".

Jikin Ameera ya yi wani irin sanyi, amma saboda ƙarfin hali ba ta nuna ba ta
ce"Babu ruwanki da duk abin da zan yi, yadda yake mijinki haka ni ma mijina ne kuma
gidana ne, ta kai hannu za ta tattare Safiyya ta doke hannun ta ce"Don gidan
mijinji ne sai ki dinga yi masa sata kina ci da gidanku?"

Daidai lokacin da ta karɓi wayar da Ni'ima ta miƙo mata, ta yiwa kayan vedio har ma
ta hasko Ameera dake tsaye cikin borin kunya da rashin abun yi, ta kuma hasko
Nabila, ta wuce ta bar wajen ta shige ɗaki, ta kunna data ta turawa Salis tare da
rubutu ta ce ka zo fa ana fati a gidanka.

Babu jimawa Ameera ta shigo ɗakin Safiyya a sanyaye ta zauna, Safiyya ta
ce"Lafiya? Me ya kawo ki ɗakina?"

Ameera ta ce"Babu komai".

Safiyya ta nuna mata hanya ta ce"To tashi ki fita!".

Ta ce"Maman Ni'ima, na mayar da kayan don Allah ki yi haƙuri kar ki faɗa masa".

Safiyya ta da wayarta ke hannunta ta kunna recording sannan ta ce"Me kika ce?"

Ameera ta ce"Kayan abincin na ce na mayar da su don Allah kar ki faɗa, ba don
halina ba".

Safiyya ta ce"Amma ke tsakaninki da Allah tun yaushe kike fitar masa da kayan
abinci? Yunwa ake a gidanku?"
Ameera ta shaƙa sosai na wulaƙancin da Safiyya take son yi mata, ita za ta cewa ana
yunwa a gidansu? Amma tun da rufin asiri take nema dole ta jure, ta ce"A'a kawai
dai kyautatawa ce".

Ta ce"Kyautatawa da abin da ba naki ba? A ina ake yin haka? Kuma tun yaushe kike
ɗiba?"

Ta ce"Yau ne na farko".

Safiyya ta ce"Wallahi ƙarya kike, dama duk ƙoarafin kayan abinci da ake yi yana
saurin ƙarewa ashe ke ce kike kwashewa, ke yanzu da ɗan rufin asirin mijinki za ki
na ci da gidanku? Irin wannan ai farantawa miji za ki yi sai ya farantawa iyayenki,
ke ma ya dinga yi miki kyautar kuɗi".

Ameera dai ta yi shiru zuciyarta na ƙuna, amma ta saka a ranta sai ta rama

Safiyya ta ce"Tashi ki fice min, ni na riga na faɗa masa fa!".

Ameera ta miƙe tsaye ta ce"Bura'uba! Kin faɗa masa!?"

Safiyya ta ce"Ƙwarai kuwa!".

Ta ce"Ai kin yi a banza, don kuwa yau za ki san ke ɗaliba ce a fagen kissa, sai kin
yi nadamar shiga gonata!" Ta fice fuuu tana huci, ta ɗakko kayan abincin ta kai
ƙofar ɗakin Salis ta ajiye.



LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL

2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[6/1, 11:49 AM] Sadiya Abdulrazak: 17
Ko da Salis ya ga saƙon Safiyya ya dai yi mamaki da ya ga kayan abinci ga kuma
ƙanwar Ameera, amma ya share bai ce komai ba, kuma bai sa a ransa zai zo ɗin ba,
haka kawai ba zai bar kasuwa ba yanzu haka dambe suke yi shi kuwa ba zai iya raba
su ba, don yanzu duk sun fara ba shi tsoro har gara ma Safiyya. Sai dare ya dawo a
ɗakin Ameera yake, don haka can ya fara shiga, sai ya ga ta kasa sakewa kamar tana
cikin damuwa. Ya ce"Baby lafiya? Na ga ba ki da walwala,ko kun ui faɗan ne?".

Ta ce"Idan faɗa ne ai da sauƙi akan makircin da Safiyya take son ƙulla mini, kuma
na san dole ma ka yarda".

Ya ce"Me ya faru?"

Ta ce"Ba ta ce maka na yi komai ba?"

Ya ce"Tabbas ta tura min video kuma har da ƙanwarki a ciki da kuma kayan abinci".

Ameera kamar za ta yi kuka ta ce"Na zo raka Nabila za ta tafi gida na tarar da su
ita da Maman Affan ta miƙa mata leda tana cewa ta kai wa Idi mai kanti sun gama
magana da shi, shi ne na ce wallahi sai na faɗa maka, sai Maman Affan ta ce ai kuwa
sai dai reshe ya juye da mujiya, ta sa Safiyya ta yi wannan videon wai a ce ni ce
na ɗebo kayan zan ba Nabila ta kai gida..." Ta fashe da kuka
Hankalinsa ya tashi da kukanta, tsoronsa kar mutanenta su tashi, ya ce"Kin ga ya
isa haka, bari na je na ji". Ya tashi ya fita daga ɗakin.

Ya shiga ɗakin Safiyya, ya haɗe rai sosai ya ce"Safiyya ashe ba ki rabu da matar
nan ba ko? Wai Maman Affan ce take aurenki?"

Da mamaki sosai ta ce"Haba Baban Ni'ima, me kuma ya dawo da abin da ya wuce? Tun da
ka raba mu ba magana ta ƙare ba?"

Ya ce"Me ya kawo ta gidan nan yau da har kika ba ta kayan abincina ta kaiwa Idi mai
kanti?"

Ta yi murmushi ta ce"Au abin da ta tsara maka kenan? To bari ka ga shaidata".

A fusace ya ce"Me ta tsara min!? Babu wani abu da zan gani, na faɗa miki ki fita
daga harkar matar nan, wannan shi ne karo na ƙarshe da zan sake jin an ganki da
ita!"

Ta ce"Ameera ce fa take kwashe duk kayan abincin gidan na da kake zancen tana
ƙarewa da wuri, ashe gidansu take..."

Ya ce"Don Allah Safiyya ya isa haka! Ni zancen da nake da ban, shi kuma abinci na
san yadda zan yi! Wannan wane irin abu ne haka ba za ku bar ni hankalina ya kwanta
ba? Na yi aure saboda na ƙara samun hutu da nutsuwa amma sai akasin haka ne yake ta
faruwa, kai Allah Ya raba bawa da wahala!". Ya yi ficewarsa ya shiga ɗaki ya yi
shiru yana ta tuna rayuwar gidansa ta baya nutsattsiya mai cike da farinciki, amma
yanzu komai ya jagule idan yana kasuwa suka kira shi har fargabar ɗagawa yake yi.
Waya ya ɗaga ya kira kowaccen su, suka nemi wuri suka zauna, ya ce"Safiyya, Ameera
na gaji da abubuwan da suke faruwa, don Allah tun da ba za ku iya haɗa kanku ba to
kowa ya fita daga harkar kowa, kowa ya yi rayuwarsa, akan kayan abinci kuma gobe
zan kawo in sha Allah, zan raba Safiyya ke da ƴaƴanki ki saka naki a ɗaki ki adana,
ke ma Ameera ki adana naki a ɗakinki, ya kasance tukwane da gas ne kawai a kitchen
ɗin, daga nan a ga wacce nata zai ƙare da wuri".

Ameera da wannan tsarin ya ƙona mata rai sosai, a tsiwace ta ce"To ka ce Safiyya da
ƴaƴanta, kenan nata zai fi yawa?"

Ya ce"Idan ma nata ya fi yawa ai ban ɓata ba, tun da ga yara biyu".

Ameera ta ce"Ni ma ai ga ciki, kuma ka san mai ciki da cin abinci, sannan na fi ta
yin baƙi, ƴan'uwanka ma idan suka zo a nan suke sauka".

Ya ce"To babu damuwa, zan ware miki na ɗan cikinki, zan ware na baƙi a ɗakina, duk
wacce za ta yi baƙi sai ta faɗa".

Da wannan aka samu maslaha akan satar abincin da Ameera take yi, daga nan kuma sai
hanyar samu ta toshe mata, ɗan abin da take samu duk ranar da taje asibiti ba yawa
ne da shi ba, shi kuma haka kawai ba ya baka kuɗi, idan ƙaryar biki ko sunan
ƴan'uwa ta yi masa abin da yake ba ta a ya yi wuta dubu biyu, ko kuɗin anko ba ya
bata, ga Umma ta matsa mata da zancen

Please Login or Register in order to submit comment