You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ba haka ba, ga shi daga zuwana jiya zan fara shak'ar
takaici!". Ta shige d'akinta a fusace, shi kuma ya bi ta.

Safiyya ta shiga d'akin nasa don rainin hankalin ya ishe ta haka, ta bud'e loka
inda yake ajiye mukullai ta d'auki na kitchen d'in, ta je ta bud'e, ta hau kwasar
kaya tana jibge su a gefe wasu kan wasu, ta juyo za ta fito don kwaso nata ta ga
Ameerar tsaye ta rik'e k'ugu tana kallonta, ta rab'e ta ta wuce ta kwaso nata
kayan, ta kusa shigowa ta ji k'arar fashewar abu, dinner ne guda biyu Ameerar ta
fasa su, sai dai ba ta sani ba tana sane ko tsautsayi ne, ta ga dai ta fice fuu
kamar kububuwa, ita kuwa ta shiga jera kayanta, babu jimawa sai ga ta nan ita da
shi, a fusace ya ce"Wannan wane irin bak'in hali kika koya ne Safiyya, ta ya za ki
d'aki farantanta kina sane ki sake su a tsaye? Kuma sai da na ce miki ki bari za ta
kwashe da kanta, amma saboda kin taki mugunta kika fasa mata!"

"Wallahi sai an biya ni!" Cewar Amerar tana kumbura.

Ya ce"Ai ya zama dole, kuma ita ce za ta biya wallahi, a cikin kud'inki zan zari
na wannan farantan".

Safiyya ta yi murmushi ta ce"Babu damuwa, na gode".

Suka fita ita kuma ta k'arasa gyaranta, ta dafa abun karyawa ta fice. Suna zaune
da yara ya shigo ya ce"Ina abincinmu?"

Ta ce"Abincinku?"

Ya ce"Shi".

Ta ce"Ban dafa da ku ba, tun da ba ni da wannan hurumin, ka kawo ta ne na dinga yi
mata girki? Kai ma sai ranar kwanana zan ba ka abinci ai ko?"

Ya ce"Amma da na ga ita amarya ce ga gajiyar biki tun da kina nan bai kamata ta
fara shiga kitchen yau ba ai".

Ta ce"E to! Da wannan ma, ga wahalar daren amarci watak'il ma ten raound".

Ya yi murmushi ya ce"Kash! Safiyya wane irin ten round sai ka ce wani taure, ita
jiya ma tana d'akinta ina nawa, dayake ba ta da lafiya, kuma kin san..."

"Ni ban ce ka fad'a mini sirrin aurenku ba" Ta katse shi.

Ya sosa kai ya ce"Daure don Allah ko indomi da k'wai ki sama mana, ki dafa wannan
shayin naki mai kayan k'amshin nan".
Ta yi murmushi ta ce"Baban Ni'ima kenan, na ga nan ka daina karyawa a gida kake
tsallake shayin ka tafi teburin mai shayi".

Ya ce"Assha! Wallahi ban je wajen mai shayi ba, ita Ameera ce fa kullum sai ta aika
mini abun karyawa a kasuwa".

Safiyya ta had'iyi wani yawun takaici ta ce"Ai ka ga ta kwana gidan sauk'i, tun da
ga ta a gida dad'in ciyar da kai kenan, sai ta fito ta dafa".

Ya ce"Haba Safiyya, tsakaninki da Allah ke washegarinki a gidana kin yi girki?"

Ta ce"Ban yi ba, amma babu wacce ta yi mini, fita ka yi ka siyo".

Ya ce"Ita ma na siyo mata kenan!".

Ta yi shiru, ya gama tsayuwarsa ya fice, da kan shi ya shiga kitchen d'in ya had'a
musu abun karyawa, Safiyya ta ce"Kad'an ma ka gani!".

Bayan ya fita, ta fito k'ofar d'aki ta zauna, tana kallo Ameera ta fito ta shiga
wanka, ita kuma ta tashi ta shiga kitchen, da hanzari ta d'akko flask d'in shayi
guda biyu ne babba da k'arami, a k'aramin suka sha shayi, babban a kwali ta ciro
shi, ta had'a shi da bango ta gwara ya ce tushhh! Ta d'auki k'aramin ma ta fasa,
sannan ta mai da babban kwalinsa ta fito a ranta ta ce, 'dama farantai biyu kika
fasa, bari na bar ki haka'.

Sha biyu ta gama girkinta, lokacin gidan cike yake da bak'in amarya, ta zuba a
madaidaiciyar kula ta aiki Ni'ima ta kai wa Ameera, babu jimawa Ni'ima ta dawo mata
da abincin, ta karb'a ta ajiye, tana idar da sallar azhar kiran Salis d'in ya shigo
wayarta, sai da ta shafa addu'a sannan ta d'auka da sallama, ya amsa ya ce"Safiyya
me yasa kike haka ne?"

Ta ce"Me kuma na yi?"

Ya ce"Ameera ta ce kin zuba mata abinci d'an kad'an ita da bak'inta".

Ta sauke numfashi ta ce"Ikon Allah! Ni fa na zuba mata ne saboda hakkin
mak'obtaka, ni zan yi wa bak'inta girki?"

Ya ce"Ai sai ki duba ki gani tana ta fama da bak'i yaushe za ta fita d'ora girki?
Kuma ma na manta ban zuba mata gas d'in ba, yi hak'uri ko taliya ce ki dafa musu ko
leda uku ce".

Ta ce"Ni ma gas d'in nawa ya k'are k'araf, don a gidan maman Affan ma na k'arasa
girkin, kuma na bar shi a can, idan mai babur d'inta ya zo zai zubo min".

"Subhanallah! To bari na aiko a zuba natan sai ki dafa don Allah!".

Ta ce"Ka yi hak'uri baban Ni'ima, kaina tun safe yake ciwo, nawa ma da k'yar na
yi". Ba ta jira cewarsa ba ta kashe wayar duka, ta kwanta.

K'arshe y'an'uwan Ameera ne suka yi girkin, shi kuma da ya dawo duk fad'an da ya
yi ba ta ce komai ba. Ya dawo da kayan abinci da yawa, don haka ya kira su
d'akinsa, ya fara bayani "Ga kayan abinci nan za a bar su a nan ku kwashi wanda zai
kwana biyu ku kai kitchen, tun da babu fili a kitchen d'in, sannan duk wacce take
da kwana ita za ta yi girki, a dafa wadatacce kowa ya d'ibi Wanda zai ishe shi,
amma na safe kowa ya yi nashi".

Duk suka amince. Daga nan bai sake cewa ta yi mata girki ba gar suka gama satin
amarci ya dawo d'akin Safiyya, a satin nan kullum sai Safiyya ta ji wannan k'arar
wankan, yanzu dariya ma abun yake ba ta.

A ranar da ta karb'i girki da rana Ameera ta yi bak'i su biyar, ita kuma ba ta dafa
da su ba, ta kira shi ta sa ya ce wa Safiyya idan wata ta yi bak'i a ranar girkinka
dole ka yi musu girki, dama tana da yaji ai kuwa ta dafa musu farar taliya, tana ji
suna mitar sun ci mai da yaji a gidan amarya, abun ya b'atawa Ameera rai ta fad'a
masa da ya dawo ya yi wa Safiyya fad'a sosai, ta yi shiru, amma ta saka a ranta
babu bak'in da za ta b'ata lokaci wajen yi musu girki.

Yadda ta lura duk ranar girkin Ameera cefane ya fi yawa da kyau, da ta yi masa
magana sai ya ce ai ita kullum cikin yin bak'i take shi yasa, haka ta yi shiru ta
k'yale.

Sai kuma ta lura duk ranar girkinta shi yake zab'ar abin da za a dafa, kullum da
rana shinkafa da wake mai da yaji, da daddare tuwo, sai dai ta dinga canza miya,
saboda haka babu wani cefane da ake kawo mata, sab'anin Ameera da ba ta tab'a yin
tuwo ba ko mai da yaji.

Yau ma kaji take dafawa tana kallon sanda aka kawo mata ta fara aikinsu, indai ta
dafa kaza ko k'afa ba ta ba Safiyya tata ce ita da Ango, abun yana damun Safiyya,
don haka Ameera tana fitowa daga kitchen d'in Safiyya ta yi wuf ta shiga, a zaninta
ta fito da abu a leda ta bud'e tukunyar ta zazzage shi duka ta juya ta yi sauri ta
fice, tana cewa"Yau sai dai ki ci ke kad'ai, shi ma sai idan ke mayya ce!".



08028966015
[5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAK


FIRST CLASS WRITERS


Page 7


Safiyya tana zaune a k'ofar d'aki ta fara jiyo k'auri da yaji, ta yi murmushin
jin dad'i, sai ga Ameera ta fito da gudu ta shiga kitchen d'in, tana shiga ta fara
tari kitchen d'in ya turnuk'e da yaji ta yi sauri ta kashe gas d'in, tana ta mamaki
don ta ga ba ta cika attaruhu a kazar ba, sanda ta d'and'ana romon gabanta ya fad'i
da ta ji wani uban yaji ya kaure mata baki, ta ci gaba da tari tana mamaki, haka
dai ta juye kaza a flask ta ajiye. Da daddare baban Ni'ima yana dawowa ta kwaso
abinci ta kai masa, ana ta fira cikin nishad'i da zumudin amarya, ta zuba masa
jollof d'in shinkafa, ta zuba kaza a palate, kazar ya fara ci, ya yaga ya kai baki,
nan take fara'ar fuskarsa ta d'auke ya ce"Baby wannan wane irin yaji ne haka?"

Ta ce"Wallahi na rasa yadda aka yi na cika yajin nan".

"Gaskiya ba zan iya ci ba" Ya fad'a yana tashi zai fita.

Ta b'ata rai sosai ta ce"Amma inda wannan matar ce ta yi ko me ka ji haka za ka ci,
shi kenan!" Ta tashi ta shige d'aki.

Ya san ta yi fushi sosai, shi kuwa sam ba ya k'aunar fushinta, tsakani da Allah
har jiran ranar kwananta yake yi, saboda haka ba zai so abin da zai shiga
tsakaninsa da samun nutsuwarsa ba, don sosai yake jin dad'in y'ar Babyn tasa, da
sauri ya bi ta, ya rik'o hannunta ya dawo da ita ya zaunar, ya ce"Haba Love! Idan
kika yi fushi da ni ina zan kama? Kaza ce ko?"

Ta d'aga masa kai alamar e.

Ya ce"To sakko mu ci".

Ta sakko, ya ja plate ya fara ci, sai da ya daure sosai sannan ya had'iye, wani
azababben yaji yake ji a mak'oshinsa, harshensa kamar zai tsage saboda zugi, ji
yake yajin kamar har cikin idonsa, amma haka ya daure yake ta ci saboda
farincikinta, yana zuk'ar iska ya ce"Babyyy ke ba za ki ci ba ne?"

"Na ci tun d'azu" Ta yi masa k'arya.

Ya ce"Don Allah ki k'ara, ni ko y'ar k'ibar nan ban ga kin fara ba, kin san fa kaza
ce mai saka mutum k'iba, shi yasa nake siyo miki".

Ta ce"Haba Honey ni me zan yi da wata k'iba?"

Ya ja yaji ya ce"Kaii! Ashe ma ba ki san mijinki ba kenan, ai ni wallahi ina son
mace mai k'iba sosai, kin ga ita dai Safiyya jikin ne a haka a bushe shi yasa ma na
daina asarar siya mata kaza".

Ta ce"Ba fa zan iya cin kazar nan ba, ina da olser".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya fad'a jin cikinsa kamar an kunna wuta

Ta ce"Mene ne?"

"Yaji mana!" Ya fad'a kamar an tsikare shi.

Ta yi murmushi ta ce"Haka dai za ka hak'ura ka cinye".

Sai da ya ci rabin kazar nan a wahalce sannan ya mik'e ya ce"Ke yasin ba zai yiwu
ba, na k'oshi haka".

Bai ma jira cewarta ba ya fice daga d'akin, kitchen ya shiga ya d'auki madarar ruwa
ya kwankwad'e, amma duk da haka bai ji daidai ba, ya fad'a d'akin Safiyya a zabure
yana ta shan yaji, Ni'ima ta ce"Abba sannu da zuwa".

Ya ce"Yauwa Ni'ima ba ni biskit ko alawa".

Ta ce"Abba babu".

Ya ce"Safiyya akwai biskit ko wani d'an abun tab'awa?"

Tun da ya shigo take danne dariyarta, duk da ta tausaya masa don kuwa muddin mutum
ya ci kaza da wannan uban barkonon da ta zuba dole rayuwarsa ta shiga yanayi.

"Safiyya ya ina magana kin juya kai? Wannan ai raini ne, biskit na ce ki ban".

Ta ce"Ikon Allah! Biskit sai ka ce wani d'an yaye? Ai ka zauna mu gaisa ko? Ya
kasuwar".

Cikin jin haushi ya ce"Subhanallah! Idan ba za ki ban ba na yi gaba".

Ta ce"Yaushe rabon da ka siyowa yara alawa da biskit, inda akwai ai a kitchen za ka
gani..."

Bai ma jira ta gama ba ya fice daga gidan, shago ya je ya siyo alawowi ya yi ta
taunawa, kafin ya zo gida ya d'an ji sauk'in abun, haka ya shiga d'akinsa ya kwanta
yana tsotsar alawa, ya so cin shinkafar nan k'warai amma yaji ya riga ya rud'a
cikin, ya tuna da Safiyya ce ta yi wannan girkin yau da sai ya kusa kwana yana
mita, amma wannan sabuwa ce babu dama, amma tabbas sai ya yi mata kyakkyawan
gargad'i akan saka yaji a abinci, sai ka ce makauniya? Murd'awar da cikinsa ya yi
ne ya katse masa tunanin, ciki ya k'ulle yana rugugi tamkar ana yak'i a ciki, ya
rik'e cikin yana cije baki, da gudu-gudu ya afka band'aki nan take ya b'arke da
gudawa, a daren sai da ya yi sau uku sannan ya ji sauk'i, haka ya kwana ciki babu
dad'i, ko ta kan Baby bai bi ba, don juya mata baya ma ya yi.

Bayan an kwana biyu Safiyya ta gaji da rainin hankalin da ake yi mata na zab'ar
girki, yau ma kamar kullum ya ce mata shinkafa da wake da rana tuwo miyar kub'ewa
da daddare. Ai kuwa da ta tashi ta dafa taliya da miya da daddare ta yi sunasir da
miyar agushi don ta san yana so sosai, da kud'inta ma ta siyi kifi ta saka a miyar,
da ta gama ta zuba masa nashi ta saka kifin ta tsame sauran, don kar Ameera ta zo
zubawa ta saka kifin.

Abin da Safiyya ba ta sani ba, Ameera ce ta tsarawa mai gidan wannan dafa shinkafa
da wake da tuwon, saboda ta cusawa Safiyyar takaici, ita ta yi ta canza girki miji
yana jin dad'i ita kuma ta yi ta tuwo ta san dole zai fi marmarin ranar girkinta,
amma ita ma ba gwanar cin tuwo ba ce daurewa kawai take ta ci, wataran ma ba ta ci,
don haka yau ta cika da mamakin dalilin da yasa Safiyya ta canza girki.

Yana dawowa ya shiga d'akin Safiyya, ta kawo masa abinci, yana bud'ewa ya ga
sunasir ya ji dad'in, don ya dad'e bai ci ba "Yau sunasir kika yi? Ma sha Allah!".

Kafin ta yi magana wayarsa ta yi k'ara, a tare suka kalli wayar da sunan my Sugar
ya bayyana a screen, Safiyya ta kau da kai tana zuba masa a plate, ya d'auki wayar
ya ce"Baby".

Ameera ta ce"Ina kiranka yanzu".

Ya tashi ya ce da Safiyya"Ina zuwa".

Yana shiga ya ga Ameera ta had'e fuska, ga kular sunasir a gabanta, ya zauna ya
ce"Babyna ya dai?"

Ta ce"Me yasa ba a yi tuwo ba yau?"

Ya ce"Shi ne abun b'acin rai? Wallahi ni kaina shiru na yi saboda farin cikinki,
amma na gaji da cin tuwon nan".

Ta ce"Gaskiya ni indai ban ci tuwo sau uku ko hud'u ba a sati ba na jin dad'i".

Ya ce"To Baby ki dinga yi ranar girkinki mana".

Ta ce"Aikinsa wahala yake ba ni, ita tun da ta saba ai sai ta dinga yi".

Ya ce"To ki yi hak'uri zan yi mata magana".

Ta ce"Yanzu me zan ci kenan? Ni ba cin sunasir nake ba".

Ya ce"To me zan siyo miki?"

Ta ce"Siyan abinci kuma? Ta dai dafa min wani abun".
Ya ce"To ina zuwa". Ya fice.

Ameera ta bi bayansa da harara, tana son sunasir, don sai da ta ci guda biyu, kawai
so take ta nunawa Safiyya ta fi ta fada a wajen miji shi yasa ta yi hakan.

Ya shiga d'akin Safiyya ya ce"Safiyya me yasa yau ba ki yi tuwo ba?"

Ta ce"Baban Ni'ima na gaji da cin tuwon wallahi, kuma tuwon nan sai ranar girkina
ake yin shi, na kasa ganewa".

Ya ce"Ni kaina na gaji! Ameera ce take so shi yasa, ga shi yanzu ma ta kasa cin
sunasir ashe ba ta ci, sai ki yi hak'uri ko taliya ce ki dafa mata".

Safiyya ta ji takaici ya rufe ta, ta ce"Yanzu dama umarninta nake bi nake yin tuwo
da garau-garau kullum? Ai kuwa wallahi ta ci na k'arshe! Kuma ba ta isa na tashi na
mata sabon girki ba, wannan ai rainin hankali ne!".

Ya ce"A'a Safiyya rufe ni za ki yi da duka kawai, to yaushe za ki tsaya kina
zagina, ai dukan sai ya fi".

Ta ce"Ni ban zage ka ba!"

Ya ce"Umarnina kika bi ba nata ba, don haka ni za ki fad'awa na ci tuwon k'arshe,
kuma ki zab'i d'aya ko ki wuce ki sama mata abin da za ta ci, ko ni na shiga na
dafa mata".

Ba ta ce komai ba ta fice, akwai sauran taliyar rana y'ar kad'an, da wacce su
Ni'ima suka jagalgala suka barta, sai ta had'e su, ta d'auraye da ruwan d'umi ta
tace, ta saka miya, ta nemi waje ta zauna a kitchen d'in, babu zato ta ji k'walla
ta zubo mata, tana zaune k'alau da mijinta cikin nishad'i rana d'aya wata ta
wargaza mata gidan da ba a san da yadda ta tsara shi ba, ko mai zai faru sai dai ya
faru, amma ta saka a ranta ba za ta yi saken da za a raba ta da gidan da take jinsa
kamar kabarinta ba.

Tashi tayi ta fito, a tsaye ta tadda shi yana safa da marwa, ta ajiye farantin ta
ce"Na dafa mata taliya baban Ni'ima saura me zan yi mata?"

Sai ta ba shi tausayi, ya dake bai ce komai ba, ya d'auka ya fice, ya kai mata
tana kwance a kujera tana danna waya, ya d'an yi murmushi ya ce"Ga taliya ta dafa
miki tashi ki ci".

Ta tashi a tsiwace ta ce"Taliya kuma? To wallahi ta rana ce, ita fa muka ci da
rana!".

Ya ce"Wallahi a gabana ta dafa, kuma idan ma laifi ne ni na yi saboda ni na ce ta
dafa taliyar".

Ta ce"To gaskiya ba zan ci ba".

Ransa ya b'aci, ya ce"Amma kin san ba zan kuma saka ta aiki ba ko?"

Ta ce"Ko siyo mini ne ka yi".

Sai ya ji kunyar mai da taliyar nan Safiyya ta ga ba a ci ba, don haka ya zauna ya
cinye ta ya sha ruwa, sannan ya koma d'akin Safiyya, ya so ya ci sunasir din da
yawa, amma saboda ya ci taliya sai kad'an ya ci ya fita siyo mata wani abun.


Washegari wajan goma na safe Ameera ta yi sallama a d'akin Safiyya, ta amsa sai ta
shigo ta d'auki sallaya ta shimfid'a ta zauna ta mik'e k'afa tana danna waya,
Safiyya ta yi mamaki, saboda ko gaisuwa ba ta had'a su, kuma tun ranar da aka kawo
ta gidan ba ta sake shigowa d'akinta ba, ta kwashi mintuna ba ta ce komai ba kanta
a kan waya.

Safiyya ta ce"Ameera lafiya dai ko?"

Ba ta kalle ta ba ta ce"K'alau".

Safiyya ta d'auke kai, suna fira da yaranta, sha biyu ta yi Ameera ba ta da niyyar
fita, ita kuwa Safiyya ba za ta iya barinta a d'aki ta tafi kitchen ba, don ba ta
yarda da ita ba, don haka ta ce"Ameera zan shiga kitchen".

Ta ce"To a fito lafiya".

Ta ce"Dayake turare zan kunna sai na rufo k'ofar d'akin".

"Ok!" Ta fad'a, sannan ta tashi ta fita.

Safiyya ta bi ta da kallon ni ma a shirye nake, sannan suka fito da yaran sai da ta
saka mukulli ta kulle d'akin sannan ta shiga kitchen.



08028966015
[5/30, 3:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *IYA RUWA*
(FID DA KAI)


BY
SADIYA ABDULRAZAK


FIRST CLASS WRITERS


Page 8

Tana shiga ta nemi kayan miya ta rasa, duk da jiya ta ga da saura da yawa, da za
ta siya da kud'inta sai kuma ta fasa ta d'auki waya ta kira shi ta ce ya aiko kayan
miya.

Ya ce"Safiyya yau ma ba shinkafa da waken za ki yi ba?"

Ta ce"E".

Ya ce"To shi kenan, zan aiko".

Ya aiko har da nama ta yi girkinta had'add'e, da daddare ma haka. Bayan ya gama
cin abinci suna tab'a fira kamar gaske, ya ce bari ya shiga ya ga Ameera yau da
wuri zai kwanta, yana shiga ya tarar da ita a falo tana kallo a TV, ta yi masa
sannu ya amsa yana cewa"Y'an mata ya garin ne?"

Ta ce"Ni dai gaskiya ana yi mini abin da aka ga dama a gidan nan".

Cikin k'osawa ya ce"Me kuma ya faru?"

Ta ce"Ka ce ta daina yin tuwo, yanzu shinkafa da waken ma ta daina? Bayan kasan shi
ne favorite food dina".
Ya ce"Ikon Allah! To gaskiya zan samar da maslaha a kan maganar girkin nan".

Ya d'auki waya ya kira Safiyya, tana d'agawa ya ce"Ki shigo d'akin Ameera".

Ta ce"Da dai ku d'in kun shigo nan". Ba ta jira cewarsa ba ta katse wayar, saboda
ba za ta shiga ba d'in.

Ya ce"Ameera taho d'akina". Sannan ya lek'a d'akin Safiyya ya ce ta shigo nashi
d'akin.

Suka zauna, ya ce"To Assalamu alaikum".

Kafin su amsa ya d'ora"Wato Safiyya na fara gajiya da yadda kike neman kawo mini
fitina saboda girki, idan na ce ga abin da za ki dafa sai ki k'i, saboda dama kin
riga kin raina ni, to don haka na raba girkin nan, kowa ya dinga yin girkinsa, kowa
ya dafa son ransa idan kashi mutum yake so ya dafa idan yaso in mutum ya dafa abin
da ba na ci sai na siyo wani a waje, ko idan mutum ya yi kwab'a a girkin sai na yi
ta kaina don ba za a kashe ni kwanana bai k'are ba".

Safiyya ta ji dad'in hakan sosai, ta ce"Hakan ya yi, mun gode.

Ya ce"Ameera ke fa?" Ta k'ara had'e fuska tana d'auke kai.

Safiyya ta tashi ta fice, sannan Ameera ma ta tashi za ta fita, sai ya rik'o
hannunta, ta ce"Malam sake ni! Ka gama ci mini mutunci a gabanta me kuma za ka ce
mini?"

Ya ce"Subhanallah! Mene ne na cin mutunci a nan? A ganina hakan zai fi ai, ke ki
dafa abin da kike son ci ita ma haka".

Ta ce"Amma ai da ka ce za a kasheka da ranka da ni kake, saboda rana d'aya an samu
matsala da dafa kaza".

Ya ce"Ba haka nake nufi ba, ita Safiyya ai ta san da ita nake, ko ba ki ji yanayin
girkinta ba, duk ba ta iya ba? Wallahi ba da ke nake ba".

Ta ji dad'i har sai da ta murmusa sannan ta bar d'akin. Da haka aka samu maslaha
kowa yake yin girkinsa kuma yana mata cefane daidai gwargwado, bayan an kwana biyu
watarana Safiyya ta je unguwa ba ta dawo da wuri ba, sai bayan isha'i, ba ta wani
damu ba saboda ba ranar girkinta ba ce, tana shiga d'akinta ta gan shi a hargitse,
kamar an yi mata bincike, ta kasa hak'uri har sai da ta tambayi mai gidan ko ya
nemi wani abu a d'akinta ya ce bai shiga ba, ta nutsu ta duba tsaf ba ta ga alamar
an d'auki komai ba, amma duk ta kamu da tsoron d'akin.

Wata rana da safe tana had'a abun karyawa, ta kad'a k'wai tana jira doya ta dahu
sai ta tafi yi wa Khausar tsarki, Ameera ta yi wuf ta fad'a kitchen ta dumbuzo
gishiri ta zuba a cikin k'wan ta fice, Safiyya sauri take ta gama ta sallami mai
gida shi yasa ba ta lura da tsinkewar k'wan ba, ballantana ta gane magi yayi yawa,
sai da ta gama ta zuba masa, yana ci ya ji bakinsa fau! Da k'yar ya had'iye, ya
tashi ya fice bai ce komai ba saboda takaici, sai da ta ci ta ji sannan ta
fahimcesa, ta girgiza kai don ta san Ameera ce, saboda ita ba ta cika amfani da
gishiri ba ma.

Da rana Ameera ta karbi girki, tana ta iyayi tana girki, sai da ya kusa tsotsewa
Safiyya ita ma da take kitchen d'in tana nata girkin ta d'akko ruwan kanwa da ta
jik'a shi tun safe mai yawa ta juye a girkin Ameera, ta juya ta rufe mata, ta ci
gaba da nata girkin, tana kallo ta gama ta juye a kula ta fice.
Sai da daddare Mai gida ya dawo ta zuba musu za su ci don ko d'and'anawa ba ta yi
ba, yana yin cokali d'aya, ya guntse baki yana rarraba ido, ya tashi ya fita waje
ya tofar ya dawo ya sha ruwa ransa a b'ace, Ameera da ba ta fahimci komai ba, ta
kai cokali d'aya bakinta, gabanta fa yad'i, ta kalle shi tana sosa kai, da k'yar ta
daure ta cinye cokali d'ayan, ta ture palate d'in.

Ya ce"Ya kika matsar da shi, ki ci mana!".

Ta ce"Ban san yadda aka yi ya yi haka ba wallahi".

Ya ce"Ni kuma k'addarata a girki za ta k'are kenan, ita da safe ta cika gishiri
kamar makauniya, ke kuma yanzu na rasa ma me kika cika, abun dai ba a cewa komai".

Ta b'ata rai ta juya kai gefe, a zuciyarsa ya ce'Wallahi ko fashewa za ki yi ba zan
ci ba, haka kawai wancen karon na you gudawa wannan watak'il na mutu ma' Ya tashi
ya fice, kai tsaye gidansu ya tafi, a can ya ci abinci, Hajiyarsa ta ce"Wai kai
Salisu ya aka yi da matanka biyu ka zo nan ka zage kana cin abinci?"

Ya ce"Babu komai Hajiya, wulak'anci kawai suke ji, yau idan wannan ta cika yaji
gobe sai wannan ta cika gishiri to ba sai na hak'ura na bar musu ba, idan kuma na
gaji wallahi wacce ta k'ware a girki zan auro".

Hajiya ta had'e rai ta ce"Yau d'in Safiyya ce ta yi girkin?"

Ya ce"Ina fa! Ameera ce wallahi, wani abinci babu fasali na rasa ma mene ne ya yi
yawa".

Hajiya ta tsuke fuska ta ce"To makircin Safiyya ne wallahi, ita ce take saka mata
wani abun".

Ya ce"Ai ita ma Safiyyar d'azu gishiri rangad'ad'au a doya".

Hajiya ta ce"A haf! Ai kissa ce, saboda kar a zarge ta, mu wata irin kissa ce

Please Login or Register in order to submit comment