You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda za ka
yi ka dawo da matarka, yo wane wulaƙanci ne za su riƙe ta su ce sai ta haihu a can?
Mu za a faɗawa gata, gatan banza da wofi wanda tana ƙuruciya da kashinta a ɗuwawu
ba a nuna mata ba sai yanzu da ta zama mutum, gata ai kai ka yi mata, idan ma raba
ku suke son yi sun yi na banza, tun da dai babu abin da wani shege zai faɗa maka a
kan Safiyya!".

Shiru ya yi sai da ta gama tsaf, sannan ya ce"To ki yi haƙuri Hajiya, kuma ma ai
kamar yau ne za ta haihun, duk ba wannan ba ma, Sauban ne ba shi da lafiya muna
asibiti duk ya galabaita".

Ta yi gyatsine ta ce"Sauban ɗin ɗan waye?"

Ya ce"Haba Hajiya, ɗana Sauban mana".

Ta ce"Ni uwarsa nake tambaya".

Ya daure ya ce"Ɗan Ameerarki ne mana".

Hajiya ta ce"O'o! Allah Ya raba bawa da wahala, ni dai kar ka sake jona ni da
ahalin ɓeraye, wallahi ban san wata Ameera take ko Nafisa, can ta matse maka". Ta
kashe wayarta ta ajiye tana cewa"Ni me zai sake haɗa ni da yarinya mara tarbiyya
kuma? Ta yi yamma na yi gabas". Sannan ta zubawa Kausar duka a baya da take wasan
ruwa da buta ashe har ta jiƙe Hajiyar ba ta ji ba saboda tana masifa.

Kausar ta matsa gefe ta fasa kuka, Hajiya ta ɗauki mafici ta jefa mata ta ce"Duk za
ku ci ubanku, daga ku har uban naku, sai ka ce Salisu ne kaɗai ɗana shi da matansa
da ƴaƴansa sun hana ni sakat!".

Ɗakin ya koma ya ja kujera ya zauna, yana kallon yaron da yake bacci, ya kalli
Ameera ta sunkuyar da kai, ya ce"Wai ɗana ne haka ko wanka ba ya samu!".

Mitar ta fara isarta, ta kauda kai ta ce"Ta ya za a ƙi yi masa wanka? Kunu aka gama
ba shi fa ka zo".

Ya taɓe baki ya ce"Yanzu wannan rayuwar kika zaɓar muku ke da shi ɗin?"

Murya a tausashe ta ce"Ai kai ne ka zaɓar mana, ka ce mu tafi sai ka neme ni, kuma
ba ka neme ni ba tukunna ko?"

Ya ce"Ai Ameera abin da kika yi ne idan na tuna har yau sai raina ya ɓaci, ta ya za
ki ƙalawa matata sharrin maita? Ki zo ki same ta a gidanta da mijinta da ƴaƴanta
amma kullum burinki ki muzguna mata! Tun ina biye miki har na gane ba ki da niyyar
alkhairi akan Safiyya".

Hawaye ya zubo mata ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, in sha Allah ba zai sake faruwa
ba, kuma ma zan je har gidan na ba ta haƙuri".
Ya taɓe baki ya ce"Ita tana Gombe, sai ta haihu za ta dawo ma".

Ta ce"Allah Ya sauke ta lafiya". Ya amsa da amin.

Sannan ya ce"Akwai gyara da zan yi a gidan, ɗakunan da kike ciki za ki bar su ki
koma ɗakin Safiyya, za a toshe ƙofar ciki a yi wata ta waje, falonki ya zama naku
ku biyu".

Ta ji maganar ta dake ta sosai, amma babu damar tijara, ta ce"Amma ta ya za mu haɗa
falo mu biyu?"

Ya haɗe gira ya ce"Ta yadda kuka haɗa miji ɗaya ku biyu! Ameera na ɗaura ɗamarar
gyara gidana fa, saboda haka ke ko ita duk wanda ya kawo mini wargi gidansu zai
koma da zama gabaɗaya, ban ga dalilin da zai sa ku yi ta gara ni ba, ni da gidana
ban isa da ku ba, daga na ɗinke nan ku farke can, idan na yinƙura zan ɗauki mataki
kuma ku fara tada aljanu, kodayake aljanu yanzu na san maganinsu!". Ya girgiza kai.

Ameera ta ce"Shi kenan, ni dai ban ce komai ba, Allah Ya b mu zaman lafiya, amma
kenan kujeruna su kowa zai ta dirza?"

Ya ce"Babu wanda zai kashe miki kujeru, kiran da na yi miki ɗazu dama faɗa miki zan
yi ki aiko a kwashe su, saboda yau na so fara aikin, sai kuma kika kawo min zancen
rashin lafiya, ni zan sayi kujeru na zuba zan sayi kayan kallo da firji kowa ya
mora".

Ameera ta ce"To shi kenan, yaushe zan dawo kenan?"

Ya ce"Da bari zan yi sai Safiyya za ta dawo, sai ku dawo tare, amma idan kin ga kin
matsu idan na gama gyaran sai ki dawo".

Ta ce"To zan dawo ɗin idan ka gama, ai bai kamata a tsaya jiranta, ita da za ta
haihu ta shiga jego kuma, wataƙil ma sai ta yi arba'in za ta dawo, kana ta zaune
babu mace a gidan, wai ya kake yi da abinci ma?"

Ya ce"Wannan ai ke zan tambaya, kalli yadda ɗana ya rame, ke ma duk kin wane motse,
wani irin kunu kike ba shi ma?"

Ta ce"Na tsamiya ne ake siyo masa a maƙota".

Ya yi tsaki ya ce"Allah Ya kyauta!".

Kwanansa ɗaya aka sallame su, a hanya ya tsaya ya siyo musu kayan shayi, sannan ya
ba ta dubu ashirin ya ce ta haɗa masa kunun gyaɗa ko na alkama, kar ta sake ba shi
tsamiya a lalata masa cikin yaro, ita dai kawai binsa take yi da to, a zaure ta
tsaya ta zare dubu goma ta maƙe a jikinta sannan ta yi sallama ta shiga, ƙaninta
kawai ta tarar a gidan Umma ba ta nan, ta ji daɗin hakan sai ta juya ta shiga
maƙota ta aiki wata yarinya kasuwa ta siyo mata kayan haɗin garin kunu, sannan ta
dawo gidan, sai azhar Umma ta dawo, tun da ta hango ɗakinta a buɗe ta fara mamaki,
ta yi zaton baƙi ta yi, ta shigo da sallama, Ameera ta amsa tana mazewa daga tsoron
da take ji.

Umma riƙe da labule ta ce"Wannan kuma fa? Me ya dawo dake, ko har ya ƙara koro ki?
Yanzu ke Ameera har ni za uwarki za ki watsa wa ƙasa a ido ki rungume miji? Ai kuwa
kar ki manta duk wacce ta ɗauki miji uba ta mutu marainiya, ni fa ban ce kar ki bi
mijinki ba amma duk wani faɗi tashi da nake yi akan lamarin aurenki wallahi saboda
na sama miki ƴanci ne, tun da ba kya so ai shi kenan!".

Ta saki labulen ta baje a tsakar gida, tana cewa"Me kika dafa?"
Ameera ta fito ta ce"Ban yi girki ba ai, a asibiti fa muka kwana Umma, ga wannan ya
ce na yi wa Sauban kunu, har ma na yo cefanen" Ta miƙa mata sauran kuɗin da kayan
shayin.

Umma ta karɓi kuɗin tana rogon da ta siyo a hanya ta ce"Allah Ya amfana".

Sannan Ameera ta faɗa mata duk yadda suka yi da shi, da gyaran gidan da za a yi.
Umma ta ce"Ai idan zaure ma zai kai ki babu komai tun da kin ji kin gani, ni dai
tun da ya raina ni ban kai ya shigo ya gaishe ni ba babu komai, ko ma mene ne ke ce
kika ja min".

Ameera ta ce"Umma ba haka ba ne, cewa ya yi fa kunyarki yake ji".

Ta ce"Dalla rufe min baki!".

Da yamma aka aika aka kwaso kujerunta, sauran kayan kuma aka shigar da su ɗakin
gado, tun daga ranar kuma suke waya da Salis wataran ma yana zuwa ya gan su, shi
kansa sai a yanzu ya ƙara samun nutsuwa da suka shirya da matan nasa, cikin satin
Ameerar ta koma da rakiyar ƴan'uwanta wanda suka taya ta kwashe kaya ta mayar ɗakin
Safiyya, falo kuma wayam yake babu komai don kulle shi ma ya yi, ya ce sai ya gama
hidimar gabansa zai zuba kaya, zaman su lafiya lau don tana takatsantsan da ɓata
masa rai.


LITTAFIN IYA RUWA NA KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL

2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[6/13, 6:13 PM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*Nationwide delivery*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin
farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

Satin Ameera uku da komawa Allah Ya sauki Safiyya lafiya, ta haifo ƴarta mace,
washegari Salis ya je Gombe, can ya gano Safiyya da ƴarsa waɗanda suke cikin kulawa
da gata ta ko'ina, ya yi mata huɗuba da sunan Mama wato Maryam, suna ce mata Ihsan,
duk wani kuɗin da za a buƙata a asibiti dama ya riga ya bayar tun kafin haihuwar,
da ya tambaye ta abin da suke buƙata ma ta ce komai akwai, saboda haka kuɗi kawai
ya bata don ƙaro wa ƴar kaya da kuma nata ɗinkunan, ya tafi cike da kewarsu. Da ya
faɗa wa Hajiya babu yabo babu fallasa ta yi masa barka, ya kira Safiyya a waya ta
yi mata barka, Ameera ma ta karɓi lambar Safiyya a wajensa ta kira ta sun gaisa ta
yi mata barka, ana gobe suna ya zauna da ƴan'uwan don ya ji su waye za su je suna?
Duk suka ce ba za su je ba, sai Mariya ce ta ce za ta je, sai da Hajiya ta nusar da
su muhimmancin zuwan nasu, saboda a gano yanayin da Safiyya take ciki sannan
yayarsa Saude ta ce za ta je, sai suka tafi Saude, Mariya, su Ni'ima, Salma sai
kuma Ameera wacce Salis ɗin ya ɓata rai ya ce ta shirya su tafi. Kuɗin ragon suna
ma tura musu ya yi aka siya, sannan Baba ma ya yanka mata wani aka haɗa biyu, bayan
ƙaurin da suka yi mata tun washegarin haihuwar.

A can gidan Mama Hajara aka yi taron sunan, saboda ya fi girma, don haka su ma a
nan suka sauka, tun daga ganin yanayin irin gidan da Safiyya take Saude ta sha
jinin jikinta, Ameera kuwa kafin a gama taron sunan nan bindiga ce kawai ba ta yi
ba, ganin yadda Safiyya ta yi mugun kyau tun kafin ma a zo kan suturar da dinga
canzawa, ita kuwa Safiyya ganin ƴaƴanta ne ya dawwamar da farin ciki a fuskarta,
don haka ta kasance a cikin fara'a da walwala har suka tafi, babu ƙarya an yi taro
na kece raini, wanda ita kanta Safiyya ta yi mamakin yadda suka nuna mata ƙauna,
haka ta samu alkhairi sosai, a nan gidan ta yi zamanta Mama Hajara ta ci gaba da
kulawa da su ita da ƴarta.

Safiyya ma ba ta jira komai ba, ta yi wa Hajiya Surayya magana, inda ta fara da yi
mata dahuwar kazar mai jego mai masifar kyau, ta haɗa mata da garin daka, da tsumi
wanda da su ta yi zaman kwana arba'in ɗin suka bi jikinta a tsanake, kafin a haɗo
mata parckage ɗin mai jego wanda ya haɗar da komai har da ingantattun magungunan
matsi wanda ba sa cutarwa, ita kanta ta san ta gama haɗuwa ta wannan fannin, saboda
haka ta bar shi haka, ta koma gyara fatarta, cikin sati biyu ta yi wani sihirtaccen
kyau, haskenta ya ƙara fitowa, ga wani ƙamshi mai kama duk inda ta zauna da
suturarta, hutu ya sa ta yi ɓulɓul da ita.

Sai da ta yi wata biyu da haihuwa sannan ta fara shirin komawa, wata uku ma ta so
yi, amma yadda Salis ya matse lamba ya sa suka ce ta haƙura ta koma kawai, shi ta
sa ya siyar mata da duka kayan ɗakinta, ta turo masa kuɗi ya siyo mata kayan
gadonta masu kyau, kujeru kuma da ya nuna mata kalar wanda zai siya ta ce ba su yi
mata ba, ta ƙara masa kuɗi a ka sayi kalar wanda take so, haka kayan adon falo ma
duk ita ce ta siya, firji ne ya sayi sabo babba da kayan kallo, Ameera kawai sai
gani ta yi ana shigo da kayan ɗaki, aka jere na falo, tana kallo aka shigar da na
Safiyya ɗakinta, ba ta gama sarewa ba ma sai da ta ga Salis ɗin ya zo da kayan
kichen sababbi ya ce ta matsar da kayanta kamar yadda suka yi a da, haka aka jere
kayan Safiyya har da Gas ɗinta babba mai oven, ɗaki ta shige ta share hawayen baƙin
ciki, haka ta wuni tana kumbura, yana ankare da ita ya ba wa banza ajiyarta.

Da daddare kasa jurewa ta yi, bayan ya gama cin abinci kamar za ta yi kuka ta
ce"Amma baban Sauban ba ka yi min adalci a wasu abubuwan".

Da mamaki ya ce"To kamar me kenan?"

Ta ce"Ka san bai kamata ka canza mata kayan ɗaki ni ba ka canza min ba, kuma ka ƙi
saka komai a falon nan sai yanzu da za ta dawo, sannan yanzun ma ka rufe shi kana
jira sai ta dawo tukunna, kenan komai nata ne, kuma kalli gas ɗin da ka siya mata
ba irin nawa ba, ka canza mata komai ni ko cokali ba ka siya min ba, wannan adalci
ne?"

Salis ya yi murmushi ya ce"Dama don haka kike ta ɓata rai? To ni ban yi mata komai
ba, duka da kuɗinta ta yi, nera biyar ɗita babu a kayan gadonta da na kitchen, kuma
zancen falo da kike yi, kuɗi muka haɗa ta bada rabi na bada rabi aka sayi kujerun
nan, sannan da kuɗinta aka sayi kayan adon ɗakin da aka saka, firji da kayan kallo
ne kaɗai ni ne na siya, abin da ya sa na rufe kuwa saboda ya kamata a ce ta zo ta
gani tukunna kafin a fara amfani da kayan, ko da za ta ce ba su yi ba kin ga dole a
canzo, wannan shi ne dalili".

Ta ce"Ko da kuɗinta ne, ai dai a aljihunka ta tatso kuɗin! Don haka naka ne".

Ya ce"Haram! Wallahi Safiyya ba ta taɓa min satar kuɗi a aljihuna ba, yo ina take
gidan ma ballantana ta ɗauka?"

Ta yi huci mai zafi, ganin bai gane hausarta ba, kawai ta bar zancen.

Ya ce"Ameera ita fa Safiyya sana'a take yi take ta ƙirga ribarta, saboda haka duk
wani abu da za ki ga ta siya ko ƴaƴanta kar ki zarge ni da rashin adalci, guminta
ne, ni kuwa ba zan hana ta yi wa kanta abu ba saboda tsoron kar ki ce ni ne na yi
mata, idan kin so ke ma ki tashi ki nemi naki, ban hana ki ba!". Ya fice ya barta
da zafin zuciya.

Ashe wannan ma duk sharar fage ce, sai da Safiyya ta dawo sannan ta gane lallai
ruwa ba sa'an kwando ba ne, don kuwa wani kyau, aji, nutsuwa da wayewa da ta ga
Safiyyar ta ƙaro, abun har razana Ameera ya yi, Safiyya sai wani ɗaukar ido take
yi, tana ƙamshi ga sababbin sutura kullum da kalar da za ta saka, babban abin da
yake ƙara mata takaici bai wuce yadda duk ranar girkin Ameerar Salis yake rawar
jiki ba, don shi kaɗai ya san romon demokraɗiyyar da suke sharɓa na sabon salon
soyayyar da Safiyya take tsiro da shi kashi-kashi, ya rasa tsakanin satin amarcinsu
da kuma yadda ta koma a yanzu wanne ya fi ba shi nutsuwa? Saboda Safiyya ta riƙe
saiwowin Hajiya Surayya ba ta wasa da su, ga kasuwar magungunan sai ƙara haɓɓaka
take yi, saboda duk wanda ya siya sai ya dawo, Maman Affan ma tuni ta zama dila a
harkar maganin, saboda ingancinsa, Salma ma da infection ne ya hana ta haihuwa, sai
da ta rungumi saiwowin nan na ingantaccen maganin sanyi sai ga shi mararta ta samu
lafiya, cikin ƙanƙanin lokaci Allah Ya ba ta rabon samun ciki, haka kayan gyaran
jiki kullum cikin aikin yinsu take, amma da ta yi ba sa taɓa kwana biyu an wawashe
ta adana ribarta cass, Salis ganin Safiyyar kamar hidimar haɗa kayan ta fara yi
mata yawa ga rainon Ihsan sai ya bawa Ameera shawarar ta dinga taya ta, shi da
kansa zai dinga biyanta, Ameera ta ce Allah Ya kiyaye, ita ma Safiyya ta maze ko
ƴar hodar gumin hammata ba ta taɓa sammata ba.

Gidan Salis ya fuskanci alƙibla, falo ya zama kamar na Safiyya ita kaɗai, don
Ameera idan ta zo ta zauna Safiyya tana shigowa cikin suturarta da ƙamshinta ta
hakimce a kujera tana ta waya da abokan kasuwanci tana ambatar kuɗaɗe sai baƙin
ciki ya turnuƙe Ameera, haka a gabanta Safiyya take bada kuɗi a siyo kayan ruwa
masu daɗi a zuba a firji, don haka Ameera ta yi zuciya ta daina kula firjin, tsohon
nata da yake cikin ɗakin gadonta a shi take zuba ruwa ta sha, tana ji tana gani
Safiyya ta sayi sola mai fankoki uku ta saka ɗaya a ɗakinta ɗaya a ɗakin Salis ɗaya
a falonta, don tuni Ameerar ta bar mata, ta koma rayuwar ɗaki ko ƙofar ɗaki, to
bangaren abinci ma haka duk ranar girkin Safiyya sai ta ƙara cefane akan wanda
Salis yake aikowa, saboda haka kullum haɗaɗɗen girki take yi duk ranar girkinta
haka za su bajekolinsu tana kallo, sai dai Safiyya ta zubawa Sauban, wanda idan
Ameera ta hana shi ci ya yi ta zunduma ihu, har Salis ya gane ya tsawar mata, ya ce
babu mai raba masa kan ƴaƴansa.

Safiyya ta karɓe mijinta kamar yadda ta karɓe gidanta, don shi kansa bai san
lokacin da ya fara bin umarninta ba, tun da babu shirme a cikin shawarwarinta, haka
ta koyi yi masa kyautar kayan sakawa, takalma, hula, da ƙananun kaya, haka kawai
sai ta canza masa gajerun wanduna da singlet, ta kuma cusa kanta a wajen Hajiya da
kyautata, duk yadda take gwasale ta ba ta damuwa yanzu kullum da kular abincin
Hajiya, ga yawan kyautar atamfa da take yi mata, haka duk ranar Juma'a sai ta sayi
goro mai kyau ta yi wa Hajiyar miya haɗaɗɗiya ta haɗa kan ƴaƴanta su je su gaishe
ta, wanda hakan ya sanyaya gwiwar Hajiyar tun tana cijewa har ta saki jiki da ita,
don duk yadda ta kao ga haɗe ranta babu ruwan Safiyya wuni take a gidan, don haka
yanzu sun gyara komai tsakaninsu, ganin hakan ne su ma sauran ƴan'uwan kowa ya
sakko, Safiyya ta sa kowa ya fuskanci alƙibla.

Haka da Ramadan ta saka shi raba musu kayan abinci wanda da ba ya yi, ita kuma da
sallah ta bi su da atamfofi su da ƴaƴansu, haɗaɗɗiyar shadda ta siya suka yi ɗinki
dukansu ita da yaran da shi uban gayyar, ta ɗora masa hula mai kyau da ta sa aka
saƙa masa, ta siya masa takalmi da agogo da turare, ana gobe idi ta ba shi, har da
na Sauban da ɗinkinsu iri ɗaya, Salis ya yi ta farin ciki yana ƙara jin ƙaunarta a
zuciyarsa.

Ranar Idi da safe Ameera ta ga Safiyya da ƴaƴanta sun fito tsaf cikin kalar
shaddar da Salis ya kawowa Sauban jiya, wani malolo ya zo ya tsaya mata a wuya, ta
yi zaton sauran ɗinkin nashi ne ya yi wa Sauban ɗin, don haka yau da taƙamarta ta
saka masa, don su gani su san ita ke da magaji ga shi za su yi ango da babansa, sai
ta ga saɓanin hakan, kenan ita Salisu zai wulaƙanta ya ɗinkawa Safiyya da yaranta
shadda ita bai yi mata ba sai Sauban kaɗai? Ba ta gama tsinkewa ba sai da gogan
nasu ya fito yana baza babbar riga cikin irin ƙamshin turaren Safiyyar, sai washe
baki yake yi, Safiyya ta ce"Wow! Ka ganka kuwa? Anya yau ba za ka ƙaro mana ta uku
ba?"

Yana dariya ya ce"Ai ke kika fito da ni, Allah dai ya shi albarka, ku wuce mu
tafi".

Dukansu suka wuce, shi har ga Allah Ya manta da Ameera wacce ke tsaye cikin sabuwar
atamfar da ya siya mata da hijjabinta, riƙe da ɗanta da sallaya, sai da suka fito
ya ga bai ganta ba, sannan ya koma, a ɗakinta ya same ta ta kifa kai a gado tana ta
kukan baƙin ciki, da mamaki ya ce"Suhanallah! Ameera me ya faru? Ba za ki
masallacin ba?"

"Ba za ni ba!" Ta faɗa a fusace kamar za ta dake shi.

Ya ɗauki Sauban da yake ta kukan ganin an dawo da shi ɗaki sauran ƴan'uwansa sun
tafi, ya fice da shi, suka tafi idi. Tun a hanyar dawowa Safiyya ta yi status ɗin
hotunan da suka yi a masallaci, wanda Ameera tana gani gudun hawayenta ya ƙaru,
haka aka gama bikin sallar nan tana kallon kayan da ya ɗinka mata kamar tsumma akan
wanda Safiyya take shiga ita da ƴaƴanta, idan ta yi magana ya ce sana'a take da
kuɗinta take yi.

To da babbar sallah ma, saniya ya yanka aka raba gida uku kowa ɗaya har Hajiya,
Safiyya ta yanka rago da kuɗinta, nan ma Ameera ta shaƙi takaici. Haka rayuwar take
ta tafiya Ameera girman kai ya hana ta sakko ta haɗa kai da Safiyya ko ta samu
alkhairi, kuma ta ƙi sana'ar komai don kar ace ta kwaikwayi kishiya.


BAYAN WASU SHEKARU

Salis kasuwar shi ta ƙara albarka, ya zama babban ɗan kasuwa, magidanci mai kula
da lamarin gidansa da iyalansa, ya sayi babban fili ya gida daidai da tsarinsa,
babban falo ne na kowa da kowa da dining, sai ɗakinsa da bandaƙi a ciki, ɗakin
Safiyya ciki da falo, kitchen da banɗaki, na Ameera ma haka, sai ɗakin yara ciki da
falo, ɗakin Sauban magajin gida ɗaki ɗaya, ɗakin Hajiya da ta dawo gidan ita ma
ciki da falo da banɗaki, Safiyya ta ƙara haifar wasu har huɗu duka matan, Ameera ma
huɗun ta ƙara duka mata, ƴaƴan gidan yanzu su goma sha biyu ne, Kausar da Ni'ima
sun yi aure, kuma kowaccensu tana sana'a a ɗakin mijinta, Ihsan ce ta yi karatu
sosai yanzu haka Nurse ce, tana kula da lafiyar Hajiya sosai wacce ta tsufa ta gaji
da duniya in ji Sauban, wanda shi ne ɗan ɗakinta, don a falonta yake kwana, shi
kasuwa Salis ya saka shi amma asha ruwan tsuntsaye yake yi, don duk gidan shi ya
fita zakka ba ya jin magana sosai.

Yau Ihsan dawowarta daga aiki kenan ta zarce ɓangaren Hajiya, kusan cin karo suka
yi da Sauban wanda Hajiya ta biyo shi da mafici cike da ƙarfin hali take
faɗin"Wallahi yau sai Salisu ya zo ya raba ni da kai, fitinannen yaro ko goro ba ka
siya min amma idan ka ga kuɗina sai ka gwada min ƙuruciyar matashin ɓera!".

Ihsan ta girgiza kai don babu wanda bai saba da diramarsu ba, ta ciro dubu ɗaya a
jakarta ta miƙa masa ta ce"Don Allah ka mayar mata da kuɗinta, wuni za ta yi tana
mana mita".

Ya karɓa ya fice yana yi wa Hajiyar gwalo, ta koma ɗaki ta zauna tana cewa"Oh! Ni
dai an cuce ni a ce wai wannan yaron ne jikana, ku matan duka kun fi shi hankali,
ni dama ku Salisu ya kai kasuwar da ya fi ganin daidai.

Zaman Ameera da Safiyya lafiya lau, yanzu komai ya zama tarihi don da Ameera ta ga
wankin hula zai kai ta dare, ga shi babarta ta rasu, ba ta da wani sauran mai ɗaure
mata gindi, sai ta yi ladab, ta haɗa kai da Safiyya tana tallata mata kasuwarta
tana biyanta, Safiyya ta ba wa Salis kuɗi yana juya mata, duk wata haka zai ƙirgo
ribarta ya bata Ameera tana ji tana gani, sai idan ya ji tausayinta ya yi mata
ihsani.


ALHAMDULILLAH! A NAN LABARIN IYA RUWA FID DA KAI YA ƘARE, DON GYARA, SHAWARA,
SUKA KO KUMA JINJINA ZA KU IYA TUNTUƁATA KAI TSAYE

08028966015

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment