You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi fushi."
hannun sa ta ruko tana faɗin "Toho muje kayi wanka."
ta janyo hannun sa sukashi ge cikin wani kayataccen bedroom, suna shiya da kanta ta tuɓe masa kayan jikin sa, boxes kaɗai ta bari takuma janyo hannun nasa sukayi cikin bathroom.
Ta taimaka masa yayi wanka suka fito ɗaure da towel a kugun sa.
lokacin an fara kiraye-kirayen sallar azaha jallabiya ya zura ya jasu sallah nan cikin ɗakin,
ko da suka idar, zaman sa ya gyara ya jingina da jikin bayan sa da jikin garu-bango yana lazumi, ido taɗan tsura masa kana sai kuma ta mike ta fita jim kaɗan ta dawo ɗauke da tray mai girma a hannun ta, a gaban sa ta dire, kana tashiga buɗe kulolin da suke kan tray'n har guda uku,
wani daddaɗan kamshi ne suka fara tashi daga cikin kulolin, nan da nan ɗakin ya kaure da kamshin lafiyayyun girkin.
tazuba cikin plt tare da saka cokula guda biyu, ta gyara zaman ta da kyau ta maso gaban sa, in da ta saka plt ɗin a tsakiyar su, suka rika cin abincin gwanin ban sha'awa
sunayi suna ɗan taɓa hira da zolayar junan su, a haka har suka kammala, takwashe kayakin ta mai da su kitchen,
ko da ta dawo ta taddashi ya koma gado, yana ɗan danne-danne a waya.
kimsa in da suka ɓatan tayi kana tazo bakin gadon ta zauna, dai-dai in da kansa yake, ta gyara zaman ta da kyau ta ɗago kansa ta ɗaura kan cinyar ta, yayin da ta cusa hannunta cikin sumar kansa tana ɗan yamutsa shi cikin tsalon sa mutum yayi bacci.
aje wayar dake rike a hannun sa yayi, kana yayi sama da
hannun sa ya shafi gefen fuskar ta, a hankali cikin muryar jin baccin da yafara ziyar tar sa, ta sanadiyyar abun da take masa, ya ce
"Kawa nayi bacci kenan?."
kai ta gyaɗa tare da faɗin
"Eh nasan ka gaji."
numfashi ya sauke kana yayi kasa da hannun sa yadaɗa gyara kwanciyar sa da kyau a hankali yashiga sauke numfashi.
batare da ɓata lokaci ba bacci yayi gaba da shi da taimakon yan da take sarrafa gashin kansa da wasu sassa na jikin sa.
sai da ta tabbatar da baccin nasa yayi nisa, sannan ta ɗaga kansa a hankali ta janyo pillow ta saka masa kana ta mike tafita, domin sanya ido kan aikin da masu aiki suke
gudanar wa a gidan...


Da misalin karfe uku da rabi ya farka bathroom ya faɗa can yafito ruwa na ɗiga daga jikin sa da alama wanka yakuma,
gaban wardrobe ya tsaya yaciro kaya wani dakakken yadi ne wan da daganin sa ma kasan bana wasa bane sai dai manyan kam.
bayan ya saka ya isa gaban mirror
turo kofar a kayi daga cikin mirror yazubawa kofar ido, lallausan murmushi ya sake wan da sai da kumatun sa suka lotsa, lokacin da suka haɗa ido da ita tacikin mirror,
baki ta ɗan turo gaba kana ta tako zuwa in da yake,
ta ɗaura hannun ta kan hannun sa daya ɗaura kan turare yana kokarin ɗauka, ta amshi turaren sannan ta dube shi tare da faɗin
"Shine zaka yi wanka baka neme ni na taya ka bako?."
kai yaɗan langwaɓar sannan ya ce
"Nayafe miki ai nasan kin sha wuya wajen sani yin bacci."
turaren ta ɗago tafara fesa masa a jiki sannan tace
"Babu wani wuya gun ai kin lada ni dai wayo kayi min ka hanani samin wannan ladar."
"Kinfa tara ladan nan da yawa amma rabawa zamuyi ko?."
yayi maganar cikin tsigar zolaya yana kuma jan kuma tun ta.
kafaɗa ta make ta ce
"Naki wayon naka yafi nawa yawa ai."
dariya suka sakar wa junan su.
sai da ta fisa masa turaruka wajen kala uku kana ta gyara masa zaman hular kansa, ta ce
"Kafito sosai fa."
"Haba original mirror ai ba ma sai naga wannan jebun ba."
yafaɗa yana nuna mirror.
murmushi tayi kana taɗan tsura masa ido sai kuma ta ce
"Aboki me ke damun ka?." tayi masa tambayar cikin nuna tsantsar kulawa.
da sauri ya ce "Wani abun kika gani ne, to ni kuma me zai dame ni bayan ina da ke."
ya kai bakin sa kan goshin ta tare da mannan mata kiss.
numfashi ta sauke tare da ɗan yin shiru tana nazartar yanayin sa, kana ta ce "To shike nan muje na rakaka katafi masallacin gashi ana kan kiran sallah."

Hannun ta ya damke cikin nasa cikin son kawar mata da shakkon dake hangowa kan fuskar ta ya ce
"Babu komai fa." da sauri ta katse shi da faɗin
"Ban kuma cewa komai ba fa muje katafi masallaci......"!








Mommyn Twin ce



10





Tun da yatafi masallaci bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha, dan tun san da aka idar da sallar zai koma ciki, yayi ba'i dan haka yasa akayi musu masauki a parlour'n ba'i,
basu kuma bar gidan ba sai daf magriba, dan haka masallaci ya zarce sai yanzu bayan sallar isha ya shigo.
ko da yashigo parlour'n babu kowa, sai sanyi me fidda daddaɗan kamshi ke tashi cikin parlour'n.
direct bedroom ɗin sa ya wuce, hular kansa ya cire ya ɗaura saman bedside, kana yatafi a hankali zuwa bakin gado ya zauna, a hankali yakai bayan sa ga katifa ya kwanta rigingine, yayi pillow da hannayen sa kafar sa na kasa yana ɗan lilo da shi.
shiru yayi yayin da ya kurawa pop'n ɗakin ido, kamar mai karantar wani abu a jiki.
a hankali ta turo kofar ta shigo da sallama, ido ta kura masa na ƴan dakikai kana a sannu ta taka zuwa bakin gadon,
sai ta faɗa jikin sa gaba ɗaya ta sake nauyin ta a kansa,
ido ya waro tare da faɗin
"Wash zata karya ni, Kawa kin kara nauyi fa."
cikin muryar dariya ta ce
"Allah Aboki babu wani nauyin dana ƙara in da nake da haka nake yanzu ma."
"Tap waya faɗa miki ke baki ganki kwana biyu sai daɗa zama duma-duma kike ba, niko sai tatse ni kike."
kwanciyar ta tadaɗa gyara wa a kansa cike da shauki tace
"Kai Aboki kai ma fa baka ganka bane kayi kiba kwana biyun nan."
dariya yayi yana dai-dai ta fuskar su a hankali ya manna mata kiss kan laɓɓanta.
yan da suke yiwa junan su idan ka gani zaka fagimci santsar kauna soyayya shakuwa yarda a saka nin su.
cike da shauki ya mirgino ta yadawo da ita kasa shi ya haye kanta,
nauyin sa shima ya sake mata, yana faɗin
"A hakan kike cewa nayi kiba jini fa babu ko nauyi kamar pepa kullum kina tsotse ni, kullum sai na tsame wani abu daga jikina na zuba shi jikin ki, taya bazaki daɗa kara zama wata duma-duma ba."
ƴar karamar kara ta sake tana faɗin
"Allah Aboki kayi nauyi wash Aboki na tuba ɗaga ni."
ƴar dariya yayi tare da shafa sumar kanta yana nan a kanta.
ƴan wasan ni suka cigaba da yi sakanin su me cike da zallar shauki da kauna,
zallar soyayya da ɗin bin kauna kake hangowa tsagwaran ta a tattare da su.

Cikin yanayin da suke ta dube shi tana faɗin
"Aboki ka rama ɗaga ni na tashi, idan ka kara yafi haka nima sai na rama."
tayi maganar tana ture shi.
ƴar dariya yayi mata tare da mirginawa ya koma gefe yakwanta rigingine tare da yin pillow da hannayen sa biyu, ta mirgina tayi pillow da damtsen hannun sa, sai kuma ta ɗago tasaka hannun ta a kumatun ta, yazamana da guiwar hannun nata najikin katafi, in da da kyau take iya kallon fuskar sa, duban sa tayi da kyau naƴan sakanni kana a hankali taso ma magana
"Meke da mun ka aboki?." tayi maganar idanunta cikin nashi. idanun sa ya lumshe tare da buɗe wa yaɗan ja numfashi kana yace.
"Tambayar ɗazu kuma har lau, to me kika gani yanzu bacci nake ji."
murmushi tayi kana ta shafa gefen fuskar sa sannan ta ce
"Bacci kuma him Aboki kenan,
adalilin yin baccin ka na rana zaka kuma yin wani baccin ne da misalin karfe 12 na dare, yanzu karfe 8:30 saura akwa uku da rabi lokacin baccin ka yayi, sam karya baya yi maka kyau sabo da rashin iya shi da bakayi ba shi yasa ko kayi ake saurin gane ka."
kokarin kawar da maganar yayi ta hanyar janyo ta jikin sa, kana ya shiga wasa da wasu sassan jikin ta,
a hankali ya furta
"Kawa ke baki ga in da idona sukayi ba bacci ne a cikin su, da alama dai baccin da ɗazu kika sani bai ishe ni ba."
ta ce "Him wai ni yau ake ɓoyin wani abun, Aboki yaushe ka fara ɓoye min damuwar ka, yaushe ka fara sanya hijabi sakanin sirri na da naka, duk faɗin da kake ni da kai abu guda ne ashe ba haka bane??, shin da ma ashe akwai wata ranar da zaka ɓoye min damuwar ka, ni ce fa wacce muke tauna matsalolin mu mu magance sa batare da wani ya sani ba, ashe dama faɗin mu tsirrin junan mu ne da kake abun ba haka yake ba, ban taɓa tunanin zuwan wannan ranar ba."
ɗan sakai ta maganar nata tayi tare da mike wa zaune ta tankwashe kafafun ta takuma duban sa da kyau, nan take sai ga hawaye yacika idon ta, hannun sa ta ruko ta kankame shi cikin nata, ta ce
"Tabbas akwai abun da yake damun ka
da ma ai ni na sani akwai ranar da zatazo irin haka."
hannun sa ta daɗa kankamewa cikin nata, taci gaba da faɗin
"Kayi hakuri amma ka sani nafika jin damuwa fiye da kai, ni na riga da nasa ni, dama kana hana ni damuwar ne kai kana yi,
idan da a ce mutum shi yake ba kan sa abu da karfin dukiya WALLAHI dana sadaukar da dukiya, WALLAHI idan dana san in da zanje na sami maganin da zansha yazamo silar haihuwa dana tafi ko da bangon duniya ce,domin samin farin cikin ka, nagaza baka ɗa kayi hakuri kayi hakuri kayi hakuri!!."
takuma nanata kalmar hakuri yayin da tuni hawayen idon ta suka fara zuba.

Da sauri yamike zaune tare da janyo ta jikin sa yana faɗin
"Ke meya kawo wannan maganar?, banace kada nasake jin wannan maganar a bakin ki ba?,meye na yin ta meya kawo ta yanzu kuma?,
Okay so kike ki kawar da farin cikin da ke nan ko?,
hauhuwa dama ashe mutum shi yake bawa kansa haihuwa?, okay kin mance cewa Allah shi yake bai wa bayin sa haihuwa?, so kike kiyi tsaɓo to kiyi gaggawan tuba, maza yanzu."
yayi maganar yana share mata hawaye.
kana yaci gaba da faɗin "Dai na kunan kada na sake jin wannan maganar a bakin ki, kada na sake ji idan kuma so kike ki koyi yan da zaki rika ɓata min rai to ki kara yin ta,
na ce miki ina son haihuwa Allah bai nufa na samu bane, idan yaso sai ya bamu bare ma muna da su ƴaƴan da muke yi musu hidima kama daga gidan marayu makarantu da dai sauran su suɗin ba namu bane, suma ƴaƴan mu ne, mai da hawayen kinji Fara ƴar duma-duma ta." "
kai ta shiga girgiza wa tana faɗin
"Nayi shiru bazan sake ba ka yafe min."
kai ya jinjina kana ya koma yajin gina bayan sa da jikin gado, ita ko zaman ta tagyara suna fuskantar juna ya ce
"Ko ke fa fara ƴar duma-duma ta to na yafe."
dariya tayi kana taɗan langwaɓar da kanta cikin muryar shagwaɓa a hankali ta ce
"Na yar da ba abun da na faɗa yanzu ke damin ka ba amma na tabbata akwai wani abun, zuciya ta baza ta sami sukuni ba har idan ban za mo silar kawar da damuwar ka ba, amma babu damuwa tun da ka nuna baka so na sani, yau rana ta farko daka taɓa ɓoye min damuwar ka, ban taɓa tunanin akwai ranar da zata zo ka ɓoye min damuwar ka ba, damuwar ka tawa ce kamar yan da yake tawa takace,
ai ban san cewa haka yanzu ka ɗauke ni ba shike nan babu damuwa."
tayi maganar tana kokarin sauka a gadon.
dakatar da ita yayi ta hanyar rike hannun ta kana yaɗan ja numfashi sannan ya ce
"Abar shi kawai faɗar shi ma bashi da wani amfani."
ido ta kura masa sannan tace
"Haka kace abar shi yaci gaba da damun ka da cin ka a rai ko?, kada ka mance nafi kowa sanin ko kai waye tun sati biyu da suka wuce na fara fahimtar akwai wani abun da ke damun ka, ban daɗa gaskata hakan ba sai yau da ka shigo gida, rungumar ka da nayi jikin ka da zuciyar ka suka tabbatar min da haka, dakuma tabbacin damuwar naka yakaru a yau,
tanbayar ka danayi ɗazu da zaka tafi masallaci yakuma bani amsar abun da nake zargi, babu halin da zaka shiga koda dai-dai na second 1 ne ban gane shiba."

Ganin yan da ta hakikan ce tanuna damuwar ta matuka a kanshi takuma nuna ɓacin ranta nakin faɗa mata da yayi wan da ada ba haka asakanin su.
sai ya janyo ta jikin sa ya rungume,
tabbas ita wata sashi ce a rayuwar sa da bazai iya ɓoye mata komai na rayuwar sa ba, kamar yan da tun fari suka gina rayuwar su ta hanyar faɗawa junan su sirrukan su,
bata ɓoye masa komai kamar yan da shima baya ɓoye mata, ko a yanzu dayake ta kokarin barin abun cikin zuciyarsa shi kaɗai yana ta shan fama da ɗawai niya da zuciyar sa dan bai saba ba sam.
numfashi ya ja kana a hankali yasoma magana
"Akwai wani abun da ke damu na amma sam banso na fitar ba naso nayi jarumtar iya barin sa a raina dan faɗar sa sam bashi da amfani."
wani numfashi yakuma saukewa kana a hankali ya cigaba da magana
"Kiyi hakuri da abun da naketa ɓoye shi a zuciya ta ni kaɗai, wan da nagaza iya dan neshi sabo da ban saba da irin saba, yabani wuya sosai a zuciya ta, kiyi hakuri yanzu da zakiji shi a kan laɓɓana, tabbas da gaske bazan iya ɓoye miki sirri na ba kokarin yin haka dana yi kuwa dan cigaba da ganin kwanciyar hankalin ki yabani wuya sosai a zuciya,
nayi ta kokarin danni shi cikin zuciya ta hakan ya garara gashi bugun farko kin gano da akwai abun da yake dami na."
hannun ta ya damke cikin nasa kana yaja numfashi ya sauke sannan yaci gaba da faɗin
"Wata ranar da Company na ya tura kayan bukata izuwa wata makarantar yara, kamar da yan da kika sani a ka saba,
lokacin da motar Company ya isa aka shai da min da isar sa, sai na tashi da kai na naje makarantar domin ganewa ido na kalar farin cikin da yara zasuyi kan kayan da aka kai musu wan da yawan ci kayakin wasa ne irin na yara,sai sabbin kujeru, dan nima naji daɗi, duk da kuwa makarantar bana Gwamnati bane, makaranta ne ma irin na ƴaƴan masu kuɗi,
lokacin da na shiga makarantar nayi arba da wasu yara guda biyu, sunata wasanni da kayakin wasan da aka kai musu, duk da yara dayawa agurin amma nafi ganin farin cikin waɗan nan yara guda biyun sosai cikin matukar farin ciki da kuma jin daɗi suke ta wasa da kayan da motar Company na ta sauke,
naji daɗi matuka ganin farin ciki a fuska da zukatan ɗaliban, amma sai dai hankali na yafi karkata kan farin cikin da ke baiyana ga waɗan nan yara guda biyu,
kasan cewar lokacin tashi yayi nan ɗalibai suka fara watsewa, wasu diraibobin su suka zo suka kwashe su wasu kuma motar makaranta ta kaisu, haka yara sukayi ta watsewa.
ina nan a cikin makarantar muna magana da shugaban makarantar bayan mun gama maganar na fito, lokacin tuni students sun watse, a bakin get na tadda waɗan nan yara guda biyun, da lokacin da na shigo makarantar su na fara ganin su da ɗin bin farin ciki kan fuskokinsu, tare da mai gadin makarantar suna zaune a bakin get.
ko da na iso gurin su kan su na shafa tare da duban mai ganin na ce,
yaya su ba'a zo ɗaukar su bane kokuma motar makaranta zasu bi kuma naga ɗalibai duk sun watse.
mai gadin ya ce
Ba motar makaranta zasubi ba direban su ne zai zo ya ɗauke su ko mai akayi dai yanzu yana hanya, yau an ɗan makara ne wajen zuwa ɗau kar su.
kan su na daɗa shafawa sai nayi waje cike da jin sha'awar yaran, ina fita kuwa sai suka biyo ni a baya, sai na tsaya naruko hannun su ina tanbayar su yaya sunan su,
kai yaya sunan ka nafara tambayar na mijin sai yace min sunan sa Naseem, ita kuma macen tace min sunan ta Nasmah,
nafahimci wayo sosai tattare da yaran duk da kuwa ƙarancin shekarun su, dan bazasu wuce shekaru uku zuwa uku da rabi ba,
bayan nayi musu tambayar sai suma suka mai da min tambayar.
to kai ma yaya sunan ka, wayon yaran ya burge ni sosai jin yan da suma suka iya mai da min tambayar,
Sai nace musu sunana Daddy, kin san wani irin yanayi nagani a tare da su lokacin da nace musu suna na Daddy?."

Dan sakai ta maganar yayi tare da daɗa matse hannun ta cikin nasa kana yaci gaba da faɗin
"Ihun murna suka sake haɗe da tsalle suka rungume ni suna faɗin laa kai Daddy ne irin Daddy'n su Aeeman,ɗin class ɗin mu, to kai Daddy'n su waye ne?, maganar yaran yasa Ni shiga wani yanayi, sai dai farin cikin danake hango wa tare da su da kuma fahimtar da nayi kalmar sunan Daddy dana furta musu yazo mu su a sabon abu ko makamancin haka,
Sai na ce musu Daddy'n ku.
kin san me yaran sukayi?."
nan ma hannun ta yakuma damke wa cikin nashi kana yaci gaba da faɗin.
"Da ɗa rungume ni sukayi suna ta tsallen murna da nanata kalmar sunan Daddy,
wani irin abu naji acikin jiki na da zuciya ta, a duk san da suka furta kalmar Daddy a gare ni, sai naji wani irin farin ciki da jin daɗi mara misaltuwa a gare ni, cikin kan kanin lokaci naji yaran sun shige cikin zuciya ta,
har nake ji tamkar ƴaƴan da na haifa ne a gaba na suke kira na da wannan suna,
abun da na daɗa lura da yaran a lokacin sosai na ke hango jin daɗi irin na samun sabon abu a tare da mutum, sai suka ce min
Daddy kai ma zaka bamu chocolate irin wan da Daddy'n Aeeman yake bashi. na ce musu kwarai kuwa, to lokacin akwai ragowar Chocolate a mota wan da nake baiwa yara a gidan marayu idan naje,
sai na ruko hannun su nace muje na basu chocolate yana mota ma kuwa.
lokacin da muka nufi gun mota, a dai-dai lokacin wata yarin ya ta iso gurin a cikin mota."

Sai kuma yayi shiru batare da yaci gaba da Maganar ba.
ita ko zaman ta tagyara sosai wannan karon ita ta mai da tafin hannun sa cikin nata tasar kafe yatsun su guri guda, kana ta sanya idanun ta cikin nashi, cikin daɗa karfafa shi da bashi kwarin guiwar gama fidda damuwar da take ganin tamkar ta yaye masa, tagyaɗa masa kai cike da bashi kwarin guiwar yaci gaba da da fidda damuwar da take yi masa kallon cuta ce barin sa a ransa.
A hankali kuwa yaci gaba da maganar yayin da ya daɗa sarkafe hannun nasu sosai,
ya ce "Kawa kin san me naji?, wani abun mamaki naji wan da ban san mene ne shi ba,
bayan da yarin yar ta ɗauke su ta tafi da su,
sai na tsinci kai na cikin wani irin yanayi mai ka ma da da muwa,
mai kama da son in sake ganin su, amma nafi alakanta son in sake ganin yaran ne,
bayan kwana biyu sai naji tunanin nawa yanata rikiɗa, madadin tunanin yaran su biyu sai ya dawo uku, zuwa lokacin na gama fihimtar har da ita yarin yar nake son sake gani.
nayi mamakin kai na matuka,
wata rana dana fita muka kuma haɗuwa da su a kan hanya ta ta zuwa mittin,
a tunani na ganin da nayi musu wannan rana shike nan zuciya ta zata huta da tunanin abun da bai shafe ta ba, amma ina bayan rabuwar mu da su sai naji tamkar kara min ake.
Bayan wasu kwana biyun sai nasa ayi min bincike a kan su wato ita da yaran dana ke yi musu kallon kannen ta ne,
nayi mamaki matuka lokacin da labarin su ya iso min, dajin waɗan nan yara nata ne ma ana ita ta haife su.
mamaki na shi ne ganin ta kara ma sosai, nasamu cikakken labarin su, da duk kanin bayanan tarihin rayuwar su..."
shiru yayi tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya ce
"Labarin su mai cike da ban tausayi na girgiza da jin lamarin, sai dai a yanzu su ba abin tausayi bane, dan Ubangiji ya zartar da ikon sa gare su..."

A hankali yashiga bata labarin su kamar yan da aka kawo mishi cikakken tarihin su, bai ɓoye ko rage mata komai ba kamar yadda baiyi da farko ba, bayan gama shaida masa abin da aka sanar masa a kan su sai ya cigaba da faɗin
"Kin san wace ce wannan yarin yar?."
kai ta girgiza jiki a sanyaye yayin da idanun ta suka cika da ƙwalla tap suna shirin zubowa.
taji bala in tausayin su da jin labarin su jikin ta yayi matukar sanyi.
ya ce "I ta ce mai Company *HAM'NAS*."
ido ta waro ta ce "Mai Company *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Nigeria Limited?."
"Kwarai kuwa ita ce."
kai ta jinjina tare da faɗin
"Allah mai iko wan nan shine sakayyar da mafificin rahama yayi mata sakamakon cin jarabawar da ya ɗaura mata tabbas labarin rayuwar ta abun a tausaya ne, a da yanzu kam Allah yayi mata sauyi da mafificin rahamar sa."
sai gata tana hawaye cikin matsanancin tausayin labarin rayuwar HAMDAH da taji, har da jan sheshshe ka.
ta kai hannun ta share hawayen ta tare da faɗin
"Allah kayi mana mai kyau kasa mu dace duniya da kiyama."
ya ce "Amin." sai ya saki hannun ta yakoma ya kwamta tare da lumshe idanun sa.
a sannu ta gyara ita ma sai ta kwanta gefen sa tare da yin pillow da damtsen hannun sa, a hankali takai hannun ta kan fuskar sa, a sannu tashiga shafa gefen fuskar sa, in da kayataccen saje ke kwance a gurin lub-lub gwanin ban sha'awa.
duban sa tayi da kyau cikin kulawa a hankali ta ce
"Aboki." idanun sa da suke lumshe yaɗan buɗe su a kanta sannan ya amsa da
"Na'am." in da ya am sa can cikin kasan mako shin sa, laɓɓan sa ne suka motsa tanan ta fahinci ya amsa kiran nata.
idanun ta cikin nashi, sannan tace
"Aboki bayan sanin labarin ta kuma sai me baka karasa bani labarin ba."
idanun sa ya lumshi cikin son kawar da zancen ya ce
"Wani labarin kuma ai na gama baki labarin."
murmushi tayi tare da faɗin
"Baka kara sa ba da saura dan acikin duk kanin labarin da ka bani baka bani asalin gundarin labarin ba, kawai dai ka ce min kana
jin wani abu a kanta mene ne shi?."
"Ba ko mai fa." yafaɗa a takaice yana gyara kwanciyar sa, tare da juya wa ya fuskanci jikin garu, yana faɗin
"Zanyi bacci ki tai maka min kisa yayi daɗi."
hannun ta ta cusa karkashin gashin kansa ta bayan keyar sa, yana jin haka da sauri ya juyo dan yasan jan masa sumar zatayi da karfi bawai tayi masa yan da zaiyi baccin ba.
dariya tayi tana faɗin
"Ai da baka juyo ba Aboki yau aski zan maka."
ido yaɗan waro ya ce "Aski da hannu."
farr tayi da ido ta ce "Zan nimo abin yin askin ai taɓawa nake naji ta in da zan fara."
ya ce "Faɗi gaskiya dai ƴar guntun muguntar ce ta motsa."
dariya takuma in da shi kuma ya murmusa yana kokarin mai da idanun sa ya lumshi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar faɗin
"Me zaka ɓoye min ne iye sai fa ka karasa bani labarin nan dan baka gama bani ba."
shiru yayi bai ce komai ba,
Murmushi tayi tare da faɗin
"To ni bazan karasa baka labarin, tun da yau ka aro hijabi ka sakata sakanin mu, zan yaye ta yanzu dan babu ita sakanin mu har gaba da abadan."
ɗan numfashi ta ja tare da cigaba da faɗin
"Tun da ka sanya ido kanta Ubangiji yayi ikon sa,ya datsa maka sonta, a lokacin da baka taɓa sammanin a kwai ranar da hakan zata kasan ce da kai ba, dan kai a tunanin ka ni kaɗai ce Ubangiji ya dasa

Please Login or Register in order to submit comment