You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta keta azalzala ta ji nake idan naci gaba da jan numfashi acikin garinnan tabbas zuwa anjima numfashi'n kwacewa zaiyi yatafi abun sa.
maganar da naji kusa da nine yasani ɗagowa wani ɗan yuniyon ne tsaye a kanmu yana faɗin
"Yauwa motar ku yanzu kam yacika kowa ya kawo kuɗin sa".
gafen da nake ya kalla kana yace
"Ƴan mata ke ma a wannan motar kike?".
tsintar kaina nayi da gyaɗa masa kai,yace
"To kawo kuɗin ki mota ta cika".
idanuna na mai da kan akwatin da ke gaba na tabbas nasan bana da ko sisi dan ban fita da ko biyar daga gida ba, hasali ma babu abun da na iya ɗauka in ba wannan akwatin ba,ganin yanata amsar kuɗin mutane sai na kai hannuna kan zip ɗin bayan akwatin ina ɗan wasa da shi a raina nake faɗin
"To ko ince masa yakarɓi akwatin a bakin kuɗin motar ne, Ni har da kayan cikin ma in dai zasu ɗauke Ni suraba ni da garin nan".
yadda nake wasa da zip ɗin sai yana ɗan zugewa da mamaki nakurawa aljuhun jakar ido ganin bakin kuɗi ya baiyana, da sauri na idda zuge zip ɗin nazaro kuɗin ina juyashi a hannuna naira dubu biyu sabbi dar.
tunanin ta yadda akayi kuɗin yashigo cikin a kwatin nake,
nan take na tuno lokacin rasuwar Inna ina zaune a cikin bedroom ɗin Ummi taciro kuɗi cikin wardrobe zatayi aika kasuwa daga cikin kuɗaɗen dubu biyu suka zubo,nakwashe ina mika mata tafita da sauri tana faɗin na ajiye bari tazo,a lokacin kuwa kasan cewar ina zaune ne kusa da akwatin sai naja zip ɗin a kwatin nasaka ciki kan cewar in tashigo zan cire na bata,gaba ɗaya nagama mance wa a she dai ban bata ba..

Numfashi na sauke a hankali na furta
"Alhamdulillah".
dai-dai lokacin kuwa ɗan yuniyon ɗin yake faɗin
"Kawo nake".
duka kuɗin na mika masa sai naga ya zare dubu ɗaya yakai hannu aljuhu yazaro ɗari biyu sai ya haɗa da dubu ɗayan nan ya mika min dubu ɗaya da ɗari biyu kenan.
karɓa nayi ina juya kuɗin a hannuna "Wato kuɗin motar garin da zasu ɗari takwas kenan?".
nayi tan bayar a raina,
ganin duk wan da yabada kuɗi sai ya shige cikin motar dake gaban mu sai nima na mike nashige cikin motar ina rungume da akwatina.
Ina alla-alla motar ta tashi duk da kuwa bansan motar wani gari zata ba ban kuma da mu da duk inda zaije ba ni dai burina nafita a cikin garin nan, bana kaunar na buɗe idanuna nakuma ganina cikin garin bana kaunar narika shakar iskar garin naji na tsani garin gaba ɗayan ta.
numfashi na sauke tare da yin hamdala lokacin da motar ta hau kan titin taɗau hanyar fita daga cikin garin......★

★★★


A nan cikin garin Bauchi kuwa,
kan kace me labarin abun da ya faru yakaraɗe ƴan uwa,
su Aunty Jaleela duk sun taho gidan cikin tashin hankali,
Aunty Rafee'at da yanzu isowar su ita da Dr Farooq ko jiran ya dai-dai ta parking batayi ba tafito cikin tsananin tashin hankali tanufi ciki.
Nan ta iske ƴan gidan dukan su zaune cikin parlour'n Ummi har da wasu ƴan uwan su,
da sauri tashigo cikin parlour'n cikin muguwar tashin hankali tana faɗin
"Ummi ina HAMDAH tatafi ina tasani batasan ko ina ba".
Ummi da har lokacin kwalla basu dai na zuba a idon taba takai hannu ta share wasu zafafan hawaye,bata iya ce komai ba
sai kwallar da ta cigaba da sharewa.
cikin share kwalla goggo Hauwa tace
"Tatafi bamu san in da ta tafi ba".
tafaɗa tana sharce hanci.
Kuka Aunty Rafee'at ta sake da karfi cikin muryar kuka sosai tace
"Wlh cikin Ya SALEEM ne wlh cikin sane wlh na shaida HAMDAH bazata taɓa ai kata abun da ake zargin ta ai kata ba".
da sauri
tayi gun Dr Farooq da yanzu yashigo tariko hannunsa tare da faɗin
"Wlh Allah cikin nan na Ya SALEEM ne Abba'n Adeel kai shai da ne".
sai kuma tasaki hannunsa tayi gun goggo Hauwa tace
"Goggo Hauwa kema shai da ce Ya SALEEM shine mutum na farko da ya taɓa sanin ta ɗiya mace,wlh na rantse HAMDAH bata ai kata abun da ake zargi ba wlh sharri a ke mata".
takarasa maganar cikin shashsheka..
Aunty Jaleela ma nagefen Ummi takasa cewa komai sai kwallar da take ta share wa,
parlour'n yayi shiru cike da jimami da sautin kukan Aunty Rafee'at......★


Ido na zuba wa hanyar da bansan na wani gari bane,duk tafiyar da motar yake gani nake baya sauri,
munyi tafiyar da yakai na a wa 2,wata matar da take gefe na tabuɗe murya tace
"Direba nakusa sauka ni a Narkuta zan sauka".
direban ya amsa mata da to.
tafiya kaɗan muka kara muka iso wani gari mai kyau da tsaruwa a dai-dai farkon shiga garin motar ta tsaya direban yace
"Mun iso masu sauka a Narkuta".
kasan cewar Ni ina ta bakin kofa ne yasa dole sai da na sauka kafin matar tafita,
maganar direban naji a sama
"Ƴan mata kema a nan zaki sauka ne".
firgigit na dawo daga tunani da natafi sai kawai na sinci kai na da gyaɗa masa kai,
"No wahala"
yafaɗa tare da jan motar sa yayi gaba.

ido na baza kan titin kowa na ta harkokin gaban sa,
a sannu na masa gefe kan wani kwalbati da ya kasan ce hanyar shiga wani layi na zau na, tare da aje akwati na a gabana,
yayin da masu a dai-dai ta da mashina suke ta tsayuwa suna tan bayana ina zani,wasu nace musu babu wasu kuma nayi musu shiru.
najima sosai zaune a gurin.
Har guri yafara rufawa yayin da ababen hawa suka yawaita kowa yana kokarin konawa gida,
Ina nan zaune a kan kwalbatin,
shafa cikina da naji yana ɗan motsa wa nayi yanzu kam naji ina jin yunwa akasin ɗazu da banajin ko ɗigon yunwa,duk da wunin yau bansa ko ruwa a baki na ba, dan ko breakfast banyi ba.
a hankali na mike nanufi gurin wata mai sai da abinci da nake hango ta can gefen titin,kuɗi na mika mata nace
"Abani abinci".
sai kuma na dubawa kuɗin da nake mika mata ido da mamaki ganin naira ɗari biyu ne bayan nasan dubu ɗaya da ɗari biyu ne a hannuna,
waige-waigen gefe da gefe na nayi ko dubu ɗayan yafaɗi kasa ne amma babu ko alamar sa.
maganar
matar naji tana faɗin
"Babu abincin 200".
nace "To abani drink".
ta miko min gora na amsa na juya a hankali hanyar da na bi nabaza ido ko zanga kuɗin amma har na'isa in da akwatina yake babu alamar sa,
kurɓa uku zuwa huɗu nayi wa drink ɗin sai naji cikina na murɗa ni sai na rufe gorar,
A sannu na ɗago jin karar mota ta tsaya daf da Ni dai-dai lokacin aka zuge glass ɗin motar kasa, wani matashi ne zaune a cikin motar sai busa sigari yake,yayin da wani ke zaune a gefen sa,kai na na kawar da sauri jin hayakin sigarin yana isoni, matashin ya dubi abokin tafiyar nasa yace
"Maye wannan fa ta haɗu musala zata rage mana dare sosai".
Kai ya gyaɗa cikin cakewa da kayan mayen da yake ta shaka.
matashin ya dubeni yace
"Ya ƴanmata shigo muje mana mubaki masau ki muhuta kihuta sosai".
yafaɗa yana latso laɓɓan sa,
nan take maganganu Inna da tarika yimin lokacin tana kwance a gadon asibiti suka fara yimin yawo a ƙwaƙwalwa ta.
rumtse idonuna nayi da karfi,sai na
kuma kawar da kai na batare da nako kalle in da suke ba bare na furta wani abun.
ɗayan dake zaune gefen mai zaman banza yaleko tare da ɗaga murya yace
"Zazzafa ce fa nawa za'a biya ki?".
nan ma banko juyo ba dan na fahimci ƴan iska ne inajin ɗayan yana faɗin
"Muje gaba akwai irin su, biyu zamu ɗiba dan mu huta sosai".
ɗayan kuma yace
"Ta haɗu fa duk da tana cikin hijabi".
"Shiyasa take taja mana aji manya masu zaren take so muje kawai".
haka sukayi ta magan ganunsu sukaja motar su sukayi gaba.
numfashi na sauke tare da cigaba da ambaton sunan Allah azuciya ta da nake,
tafiyar su dakamar 5mn wata mota takuma tsayuwa gefe na wannan karon sai da naji gaban kirji na ya faɗi,da sauri na juyo jin muryar wan da yake cikin matar
"Shigo na sauke ki a gida mana da alama dai kin rasa abun hawa ne".
saurayi ne shima sai dai baiyi kama da irin waɗan can da suka wucen ba yana zaune cikin kamala, murmushi yayi min kana yakuma faɗin
"Naga kin jima zaune a nan da alama dai jira kike azo daga gida a ɗauke ki in bazaki damu ba muje na sau keki a gidan".
da sauri na girgiza kaina tare da faɗin
"A'a Nagode kaje kawai".
kai ya jinjina yadube ni da kyau tare da faɗin
"To in ma bazaki shiga motata ba to ina mai baki shawara daki nimi mai abun hawa kihau ki tafi gida".
murmushi yayi cikin maganar da yake kana yaci gaba
"Duk wani wanda yagan ki zaune a nan to zai yi miki kallo irin kallon da waɗan can samarin da suka yi miki yanzu suka wuce,gashi dai duk mai tunani idan ya ganki bakiyi kama da irin mata masu tallen kansu ba duk da dai basa da kama,
bai kamata kici gaba da jira a kan wannan hanyar ba dan yana da haɗari sosai,
akwai matasa marasa ɗa'a su basa jiran amincewar mace ko kotaso ko kar taso zasu ɗauke ta da karfi su kai ta ɗaki su kulle idan suka gama kwanakin da zasu yi dake suje su yasar da ke,a irin wannan lokaci suke fitowa, babu kuma wan da ya isa ya dakatar da su domin ƴaƴan manya ne,zai fi miki kyau kitari abin hawa kitafi gida".
ido na waro ina kallon sa har yakai karshen maganar yayin da tsoro ya lulluɓeni sai nashiga gyaɗa masa masa kai,shiko murmushi yakuma kana yace
"Ko za'a bani aron number?".
mikewa tsaye nayi
cike da jin tsoron da ya ɗarsa min a zuciya na bashi baya ina ta ɗan kalle-kalle.
ina jin sa yakuma maimaita tan bayar sa ganin bani da niyyar amsa shi sai yaja motar sa yayi gaba.

ido na kurawa cikin layin da nake tsaye a mashigar sa, matasa da magidan ta kowa yana ta haramar tafiya masallaci sallar magriba. Da sauri na sunkuya na janyo akwati na nasoma takawa cikin layin da sauri sosai dan ba karamin tsorata nayi da jin abun da mutumin nan yafaɗa min ba,sai dai ina soma tafiyar naji cikina yayi min wani irin murɗa yayin da kai na yake mugun sara min.
Na yi tafiya mai ɗan nisa sai na zauna kan dakalin kofar wani gida,tare da tafe kai na dake matsa nancin tsaramin, da hannuna ɗaya ɗaya hannun kuma na dafe cikina, tausayin kai na ya kamani sai kawai na fashe da kuka mara sauti.
cikin muryar kuka nake faɗin
"Wayyo Allah cikina kai na wayyo Allah na, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un²".
wani sabon kuka ne yakuma zuwa min Allah sarki Inna banki a yanzu Allah ya ɗauki raina kamar yan da yaɗauki nata ba yafiye min wan nan rayuwar.


nayima ina kuka mai matukar kona zuciya kukun da naɗau lokaci mai tsawo batare da nasan lokacin yakure har haka ba,guri yayi shiru bakajin motsin komai sai haushin karnuka da kukan wasu tsuntsaye, na rakuɓe jikin garo na cusa fuskata sakankanin cinyoyi na,an ce bacci ɓarawo ne to ni dai na tabbata duk iya satan sa bazai iya sace ni a wannan irin lokacin ba,ta ya zai sami narasar saceni bayan ina tangare a dandamalin guri wan da a iya ƴan shekaru na ban taɓa mafarkin kasan tuwa a irin hakaba,ban taɓa rayuwa cikin bakin duhu irin haka ba,ina zaune a haka gari yawaye..
nayi al'wala a panpon da ke jikin gidan da nakwana a kofar gidan nayi sallah.
Koda gari yayi haske jama'a suka fara zirga-zirga a kan hanyar duk wan da yazo wucewa sai ya kalleni ganin na zame wa mutane abun kallo dai na mike naja akwati na,
a sannu narika kusawa cikin unguwar haka na rika zaga cikin unguwar idan na gaji sai na sami guri na zauna in na huta sai na mike nacigaba da tafiyar da ban san in da zani ba.
ranar wuni zubur nayi ina haka yunwa kishin ruwa zafin rana sune abokan rayuwata...

Yau kwana na uku a kan layi nake kwana idan nayi ta yawo har dare ya riskeni sai na sami kofar wani gida na rakuɓe gefe a haka zan kwana a zaune,batun yunwa kuwa tarigada ta shiga jikina har ya zamana bana jinta sai dai cikina sai yayi ta murɗeni abun cikina yayi ta motsawa,idan naji kishin kuwa sai na bazama yawon niman kofar gida mai panpo na tara da hannuna nashi,
ina sha kuwa sai nayi hawaye sabo da murɗan da cikina zai yi ta min...
Zaune nake akofar wani gidan da nake tunanin a nan yau zan kwana dan yamma tayi sosai ana daf da kiran magriba,
kishin ruwa ne ya dameni tun ɗazu sai dai nayi yawo a layin da nashigo yau ban sami wani gida mai panpo a kofar gidan ba,sai dai na fuskanci wannan unguwar na marasa karfi ne dan gine-ginen su ma kaɗai kagani zakasan unguwar talakawa ne.
a hankali na mike na janyo akwakina nacigaba da tafiya ko zan sami ruwa dan ina jin kishin sosai,
ina sharar wata kwana can na hango rijiya mutane na tsaye a kansa anata jan ruwa a cikin sa,
da sauri na nufi gurin dan ruwan da nafi muradi kenan,ina isa gurin na tsaya gefe da wata ƴar dattijuwar mata nace
"Dan Allah a sammin ruwa".
matar ta juyo kana tace
"Sha zakiyi ne?".
kai na gyaɗa mata tace "Ai ho". wani ɗan kara min roba ta janyo ruwan ta zuba ciki tace
"Ɗauka kisha".
To nace da sauri na ɗauka nasoma sha nasha sosai sai da naji cikina ya cika sannan na aje robar tare da yi mata godiya,ta ɗau ruwan ta tatafi a hankali naji cikina na ɗan murɗa min sai dai ba kamar na duk lokacin da na sha ruwan panpo ba,a hankali nasoma tafiya naɗan yi nisa da rijiyar kaɗan sai na zauna kan wani bulo dake gefen ciyawa jin cikin bai dai na yimin murɗa ba.
kai na na cusa sakankanin cinyoyi na inajin yan da cikin ke ci gaba da murɗa ni,
da sauri na ɗago kai na jin abu na tafi a kafata,wani irin waro ido nayi cikin firgici da razana ganin maciji a saman kafata,cikin zafin nama na mike tsaye tare da kwalla kara na yarfe kafar da karfi macijin ya faɗi can gefe yashige cikin ciyayin dake gurin,
da iya karfina nake ihun ina yarfe kafar....


"Wane ne waye a nan?".
naji murya daga can ana tan baya,cigaba da tan bayar a kayi ana motsawa in da nake,niko sai ihun nake ina tsalle da yarfe ƙafan,
jin an dafa kafaɗa na ana faɗin
"Subhanallahi ƴar nan menene?".
da sauri narike hannun matar da naji tana tan baya na da karfi cikin sananin tsoro nace
"Maciji maciji maciji".
nafaɗa da karfi ina cigaba da yarfe kafar,
a kiɗime matar tace
"Ya cije ki ko au da ma kece? me yazaunar dake a nan tun da kinsha ruwan basai kiyi azamar tafiya gida ba, kyazo gidan macizai kizau na ba'azo in da suke Bama ana tare-tare dasu acikin gida bare kinzo nan cikin su,maza zo muje a samiki magani tun kan dafin ya haura miki,wani irin zuwa unguwa ne har guri ya rufa baza'a koma gida ba".
tafaɗa tana janyo hannuna,sai lokacin na gane matar itace wacce na roketa ruwa ta bani nasha ɗazun nan.
ta janyo hannuna ina ɗangala kafar, tana cigaba da faɗin
"Dage kiyi sauri muje tun kafin dafin ya haura miki,waɗan nan abu ai sai a hankali har gida suke shiga mana dan ma yanzu da sauki muna saka musu magani shine suke ɗan yin nesa da gidajen mu".
dai-dai lokacin muka isa kofar wani gida muka shige ciki, murya ta buɗe tashiga kwaɗa sallama tare da faɗin
"Zainabu zainabu matar gidan nan tana nan kuwa".
wata mata tafito daga cikin ɗaki tana amsa sallamar tace
"Ina nan, a'a Mama mai awara kece tafe".
Matar da muke tare da ita tace
"Eh,malam Musa na nan kuwa ko har yatafi masallaci?".
Zainabu tace
"Yana nan yanzu yake shirin fita yazaga ne, yauwa gashi ma yafito".
tafaɗa tana kallon hanyar bayi,
mutumin da a ka kira da malam Musa ya dube mu yana faɗin
"Sannu Mama mai awara ku ne da yammacin nan".
tace
"Eh wlh malam Musa maciji ne ya cije ta dan Allah a sa mata magani kafin ya haura mata".
ya dube ni da har lokacin ina masar kwalla
yace
"To subhanallah garin yaya?".
Mama mai awara tace "Can gefen fadama tabi kasan kuwa kamar gidan su ne".
"Kwarai kuwa Allah yasa ba mugayen bane".
yafaɗa yana shige wa cikin ɗaki mama mai awara tace
"Amin dai". ni dai ina nan itana masar kwalla ban iya cewa komai ba, matar malam Musa wato Zainabu tashiga tafito da taburma ta shin fiɗa tace muzauna,ba jimawa kuwa malam Musa yafi ɗauke da wata ƴar karamar jaka ya zauna gefen taburman kana yadube Ni yace na miko kafar da yaga ina ta girgiza shi,na mika masa yazuge zip ɗin jakar yaciro kayakin magungunar sa ya zaro wani farin gyale ya gyara zaman sa da kyau ya ɗaura ƙyallen saman kafata kana yaɗauko wani magani acikin kwalba yaɗan ɗiga kan ƙyallen dake kan kafar tawa.
yazubawa ƙyallen ido
sai kuma ya ɗago ya dube ni yace
"An ya nan ne kuwa".
kai na gyaɗa da sauri cikin matsar kwalla nace
"Allah nan ɗin yahau".
nafaɗa ina daɗa girgiza kafar dan ji nake kamar har lokacin yana kan kafata,
Maganin yadaɗa ɗigawa kan gyallen kana ya dubi mama mai awara
yace
"Babu wani alamun dafin maciji a tare da ita gashi nan dai kina gani".
sai ya mai da dubansa gare ni yace
"Amma yaya kikaji da ya sare kin?".
nace "Ganin sa nayi a kan kafata kawai ban san yan da akayi yahau ba".
kai malam Musa ya jinjina kana yayi murmushi da faɗin
"Allah ya tai make ki wata kila wucewa zaiyi ke kuma kika tsaya masa takan hanya yabi takafar ki yawuce batare da yasan kina ma gurin ba da taimakon Allah".
mama mai awara ta sauke numfashi da karfi tace
"To Allah ya taimaka ina gama macijiya ce dan su matan basu fiye yin saraba sai sunji matsi".
Zainabu dake gefe tace "Haka ne kam Allah dai ya daɗa karewa".
suka amsa da amin nidai ido naketa cirewa cike da tsoro.
mama mai awara ta mike tana yiwa malam Musa godiya tayi wa zainabu sallama tayi waje nabi bayan ta.


Muna fita ta dube ni tace
"Allah ya kare mugayen basu cije kiba,ai wannan mai maganin har wasu garuruwa suna kawo masa jin yan sarar maciji dan shi gada yayi tun iyaye da kakani,idan maciji ya cije ka to da wannan kyallen yake gane kalar macijin da ya sare ka,sai ya baka magani,idan yasaka kyallen dai-dai in da maciji yazuba dafin sa to kyallen zai canza kala yakoma kalar jikin macijin,kinga ai yan da yaɗau ra kyallen a fari a farin sa ya ɗaga,babu rabon wahala Allah ya kare,
Maza kiyi gida yanzun nan muje na nuna miki hanya mai sauki da zaki fita bakin hanya,jirani a nan na ɗauko miki jakar ki".
kai kawai na gyaɗa mata yayin da naji wasu zafafan hawaye sun zubo min,yanayin yan da matar take magana yasa ni tuno da Inna ta,
"Allah sarki Inna na tabbata in da kina numfashi bazan taɓa hofanta ba".
Kwalla na kuma share wa lokacin da matar tadawo gaba na tana mika min a kwatina,
tace
"Maza ki tafi gida dare yayi ke bakya tsoron kije gida iyayen ki su miki faɗa, Allah ma ya takai ta ai da sai dai a kai ki gida da raunin maciji,
yi sauri muje na nuna miki kinga har na makara markaɗen awara nafito ɗauka wa shine na jiyo kururuwar ki da yanzu na dafashi har na tsane".

Duk abun da take faɗa sama-sama nake jinta wani irin kuna da raɗaɗi zuciya ta ke min sai sharar kwalla nake.
muna fita gaban rijiyar nan da hannu ta nuna min hanya tace
"Ki mike nan hanyar ta ɓulle har titi Allah bamu alheri".
kai na gyaɗa kana a hankali nasoma tafiya,ita kuma tabi ta wani hanyar.
A hankali nake tafiyar idanuna a kasa sai gani nake kamar zan ɗaura kafar kan wani macijin,duk da kuwa guri yafara yin duhu lokacin........!★





Mommyn twins ce




*Masha Allah yau Allah yayi ikon sa na dawo Nagode da addu'o'in ku sosai*🥰





Ina ganin shige war matar cikin wani gida sai na rakuɓe kofar gidan da na iso yanzu,
hawayen tsoro ne suka shiga zuba min a ido shike nan Ni nasan rayuwa ta ta kare yau maciji shi zai yi saniyyar barina duni,tun da kuwa garin su nazo,
wani sassanyar kuka na sake mara sauti nasadakar ma kawai macijin yacije ni na mutu ko zan huta da wannan rayuwar kunci da bakin cikin.
Ji nayi an gasko min toci da sauri na ɗago kai na tare da kare fuskata da hannuna sabo da hasken tocin dake haska min ido.
da sauri takaraso in da nake rike da roba mai ɗauke da kullun waken awara a ciki,salati ta doka tana faɗin
"Yau naga ikon Allah ƴar nan ashe baki tafi gida ba,kuma zama anan kikayi,hanyar koma wa gida ne ta ɓace miki kokuwa wani laifin kikayi kike tsoron komawa,in ba haka ba mai zaisa kiki komawa gida,ki zauna kina ta rabuɓe-rakuɓe a nan,
yaran zamani ga iya laifi ga tsoron hukunci,tun da kana tsoron hukunci ai sai ka riƙa gujewa ai kata lai fi,to baki tsoron ki karawa kanki wani laifin ni sam banason yaro irin haka to menene am fanin fitowa a gidan da har zaki ki koma wa gidan ki rakuɓe a nan kinata koke-koke, to in bugun naki za ayi bagara ki koma a bige ki ya wuce miki ba, ka zauna ka karawa kanka laifi,ɗauki jakar maza kizo nan".
tafaɗa tana dubana.


Tana gaba ina biye da ita muka shige cikin wani ɗan ma dai-dai cin gida mai ɗauke da ɗaki ciki biyu sai kitchen da Kuma banɗaki a gefe,
da kaga kidan kasan na talakawa ne sosai sai dai a tsaftace yake babu kazanta ko datti a cikin ɗan ma dai-dai cin tsakar gidan.
tanuna min ɗaya daga cikin ɗakunan tace nashiga,
a kasa kan taburman dake malale cikin ɗakin na zauna,
babu jimawa tashigo ɗauke da kwano ta direshi gaba na tana faɗin
"Ci yanzu muje na rakaki bakin titi kihau abun hawa ki koma gida,
in ban da rashin hankali niyyar guduwa kikayi gaba ɗaya a gidan da kika ɗau jaka?,
Akul karki kuma wan nan ba ta'adar ɗan kirki bane ci maza muje".
wasu zafafan hawaye na share kana da sauri har hannuna na rawa na buɗe kwanon,
tuwon jan dawa ne miyar bushashiyar kuɓaiwa,sai tashi da kamshin daddawa yake,
da sauri na sa hannu na soma ci.
ta fita ta kuma dawowa da kofin ruwa ta aje min,kana ta fita taje tasoma tatar kullun da ta ɗauko markaɗen sa.
cin tuwan nake tamkar na sami nama,yau kwana uku da wuni ɗaya kenan rabun da nasa wani abu mai gishiri a bakina.
naci tuwon sosai dan har nakusa cinye wa kana na kara da ruwa,
bayana na jingina da jikin garu tare da yiwa Ubangiji godiya,
a hankali narka jin murɗar da cikina keyi min yana ɗan raguwa, yayin da abun cikina da tun jiya da cikin ya murɗa ni sai shima naji ya motsa sai ya sauka kasan marana ya dunkule guri guda bai kuma motsawa ba sai yanzu naji yana ɗan motsawa da harbawa a hankali...
can an jima matar taɗa go labule tace
"Zo kiyi sallah kafin awara ta ta dafu sai muje na rakaki".
"Tom". nace na mike nafito rike da lanta da ke cikin ɗakin kasan cewar guri yayi duhu sosai,cikin ɗar-ɗar nashiga bayin nayi sarki nafito kana nayi al'wala na koma ɗakin na gabatar da sallar isha,
bayan na idar ina zaune kan sallaya tashigo,ganin da al'wala tare da ita sai na mike nabata sallayar na koma gefe.

Bayan ta idar ta mike ta dube Ni tana faɗin
"Taso muje ga dare nata yi ki tabbatar kin koma gida kuma kada kisa ke yin haka
kinaso kishiga fushin iyaye ne fushin su musufa ce yana jefa mutum cikin halaka".
wasu hawaye ne naji sun kuma zubomin
"innalillahi wa'inna'ilaihirra'un".
nashiga nanatawa a raina,shin nima haka zan tabbata da fushin iyaye,shin meyasa iyaye na zasuyi fushi da ni kan abun da ban ai kata ba,me yasa zasu yanke min hukunci kan abun da bana da masaniya a kansa??.
maganar ta naji a sama
"Yau kitashi muje kin tsaya kuka ne,ai har gida zansa mai abun hawan yakai ki, tukunna ma inane gidan ku a wani unguwa kike? dan gobe zanje na tabbatar da kin koma ko baki koma ba,kada ki sake ki kuma laifi kice zaki gudu ni bani son

Please Login or Register in order to submit comment