You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alkawarin bamu kariya da tsaro, suka tattari ƴan ta'addan suka saka su cikin mota, Ahmad ya ɗaga wannan makiyayin namu yatura shi cikin mota,
nan wasu daga cikin sojojin suka tafi da ƴan ta'addan suka bar motan soja guda.
ranar acikin rugar mu suka kwana suna bamu tsaro kwanan su uku kafin suka tafi,
Ahmad kuwa bai bar rugar ba har sai da yagina mana makaranta da asibiti yazuba mana malaman asibiti dana makaranta, makarantar ne ma Fatu take ciki, tun daga lokacin muke samin tsaro sosai, munyi matukar farin ciki da zuwan Ahmad cikin mu dan kuwa ya tallafawa rayuwar mu kwarai da gaske, har rana mai kamar ta yau ba'a kuma shiga rugar mu da sunan sata ba."

Numfashi na sauke cike da alhinin labarin da Bappa ke bani nace
"Ikon Allah to shi wannan makiyayin naku yaya iyayen sa sukayi dajin shima ɗan fashin ne, yanzu ku duk zaman ku da shi bakusan shi ma ɗan fashi bane?".
yace "Sam bamusan ɗan fashi bane, to ai shi asalinsa ma ba bafulatani bane, zuwa yayi rugarmu tun yana yaro yace zai rika yi mana kiwo muna biyan sa, shekaru 16 muna tare da shi, muka bashi duk wani yar da ashe macuci ne bamu sani ba, yana ha'intar mu, har sai da Allah ya turo mana Ahmad Tijjani Sabil."
kai na jinjina cike da mamaki ina faɗin
"Tab lallai to shi ya akayi yasan ɗan fashi ne shi da yazo bai jima ba, ku da kukayi shekara da shekaru da shi baku sani ba?."
Bappa yace "Wlh duk kanin mu kowa abun da yayi ta faɗa kenan bayan komai ya lafa, sai dai bamu sami amsar tambayar ba, dan ko shi Ahmad ɗin da muka tambaye shi bamu sami wani kwakkwaran amsa ba, sai muma muka bar shi bamu tsanan ta masa tambayar ba, munji daɗi da farin cikin da Allah ya nufa shi zai zame mana karshen matsalar mu."
Bappa yana maganar ne cikin nuna tsantsar farin ciki da jin daɗi...
na ce "Lallai kam to Allah ya tsare na gaba."
ya am sa da amin amin kana yamike yana faɗin "Bari na shiga ciki."
yana tafiya naruko hannun su muka haura sama...

Yauma kamar kullum narako su Naseem ina tsaye har sai da naga fitar su,
kana na koma ciki, wanka nayi ina gama kimsawa nayi breakfast, wan da nasa Zulai takawo min shi cikin ɗaki,
ina gama breakfast ɗin nahaye gado dan bacci ne a idanuna
ban farka ba, sai wajen karfe shabiyu saura ƴan mintina dabasu fi 20 ba, wayata na janyo na kira Number Yakubu, kasan cewar yau juma'a da wuri ake tashin su, bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga, nace
"Kayi maza kaje ka ɗauko su Nasmah." yace "To Hajiya da ma nima yanzu ina kan goge motar kenan yanzu zan tafi."
"Kabar wani goge mota katafi kaje ka ɗauko su." nayi maganar tare da kashe wayar, mikewa nayi nashige bathroom nayi wanka tare da dauro al'wala, ina fita na sauya kaya. ganin lokacin salla da saura sai na nufi kofa nafita kasa na sauka.
Talatu da Zulai duk suna parlour'n suna ganina sukayi min sannu da fitowa,na amsa ina yi musu yaya aiki, suka ce alhmdllh, an tsaftace gurin ko ina yayi tsaf sai kamshe ke tashi.
ina jin matukar daɗin zama da su sabo da suna baiwa aikin su kulawa sosai.
a ɗaya daga cikin kujerun parlour'n na zauna, tare da saka idanuna kan TV ganin shirin da ake.
zamata baifi da minti 10 ba najiyo muryar su Naseem daga kofa ta waje suna kwaɗa sallama, kallon kofar nayi da murmushi akan fuska ta, suka turo kofar da gudu suka shigo suna faɗin
"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."
faɗaɗa murmushi na nayi tare da faɗin
"To sannun ku da dawowa."
in da nake suka taho da gudu na buɗe hannuna suka faɗo ciki na rungume su, ina dariya da faɗin
"An yi karatu sosai dai ko?."
kai Naseem ya gyaɗa. nace "To madallah." na dubi Nasmah nace "Likita na anyi karatu sosai ko?." itama kai ta gyaɗa tana washe baki, Naseem ko baki ya turo yace "Mommy ni baki ce min tojan ki ba."
cikin muryar dariya nace "Oh soja na."
shima dariyar yayi cike da jin daɗin sunan dana kira sa da shi.
Nasmah ko mikewa tayi a jikina tarike kugu tare da jujjuya idanun ta tace
"Ai nafi Naseem yin kayatu da yawa yana ta wasa da wani yayo, ni nayi kayatu da yawa dan yika yima mutane ayyuya kuma."
ido na waro yan da take yi da ido ya bani dariya nace
"A.a.a Naseem ɗin wato wasa kaje ka zauna kake yi ba karatu ba ko?".
nayi maganar tare da rike haɓa ina kallon sa, yace
"Hum kaiya ne take yi, nayi kayatu da yawa kuma Daddy yace nayi kayatu da yawa idan nayi da yawa da yawa, yace dai jo ya auke mu a gida."
Nasmah tace "Um ai Daddy yace ni ne dai jo ya auke ni nafika kayatu da yawa, ai nayi mishi kayatu da yawa ma yau kuma."
Naseem yayi kamar zai ture ta yana faɗin
"Ai nima nayi ma Daddy kayatu da yawa."
ido na waro da mamakin kin sunan da suke ambata sunan da nayi ta musu barazana kan kuma faɗar sa, nace
"Kai kurafa min baki, wani Daddy'n."
nayi maganar cikin tsawa dan ni a tunani na ma wani ne daban ba wancan mutumin da na kwaɓe su da shi ba.
Yakubu da yashigo rike da school bag ɗin su yakaraso ciki Talatu ta amshi jakar tayi cikin bedroom ɗin su da shi, ya washe baki da faɗin
"Ai Hajiya Ahmad Tijjani Sabil suke nufi, ai ina isa na iske su tare da shi abakin get din makarantar su tare da shi, naji yana tambayar su karatu suna ta zuba masa karatun da aka musu, nace kai ashe fa yaran nan za'ayi masu ilimi ne anan wlh kuwa."
yayi maganar yana mai cigaba da washe baki.
fuska na tsuke sosai tare da mai da dubana kan yaran kana na mike tsaye na ruko hannun su na janyo su muka haura sama,
muna shiga ɗaki na sake su ina faɗin "Ni ƴasu yazan yi da yaran nan wato ku bakwa ji, duk abun da zanyi ta faɗa muku bazaku jiba shi wannan Ahmad yake ko wane wlh dole na ɗau mataki a kansa, idan bana ɗau mataki akan lamarin ba zai rushe min ginin danake ta gina shi,
yana ta kokarin rushewa ya haka ne kam, ina ruwan shi da su meye haɗin shi da su da zai rika sanya musu wani ra'ayi a cikin zukatan su."

Duban yaran nayi nama rasa wani irin masifa zan musu, ko da na musu ma abanza gobe zasu kuma,
zubewa nayi bakin gado da tunanin yan da zanyi na ɓullo wa lamarin, yazama dole na ɗauki mataki kan lamarin idan ba hakaba, to kuwa tabbas ginin da nake ta kokarin gina shi domin yayi karko to kuwa zai iya rusa min shi, tabbas zan ɗauki mataki kansa, "Amma mene ne mafita?. nayi wa kai na tambayar ina gyara zama ta,
"Mafitar kenan kawai ki canza musu makaranta."
zuciya ta ta bani amsa, kai na jinjina da gaskata abun da zuciya ta ta faɗa min, hakanne kawai mafita ta yadda zasuyi nesa da shi, idan kuma ba haka ba to kuwa abun da nake ta kokarin cire masu kwaɗai tar sa a zukatan su shine zai faru, dan kuwa in har hakan yaci gaba da faruwa zasu tashi da sanin wani mahaifi a ransu wan da bana son su san haka, nice nan uwa kuma uba a rayuwar su, sam bana son su tashi da jin cewa zasu sa mi uba ni zasu cigaba da jina uwa kuma uba a rayuwar su.
bana so su sanyawa ransu abun da baza su samu ba a rayuwar su, to mene ne amfanin sanya wa ransu hakan,
gara kawai su san cewa ba su da uba, su ji a ransu ni ce uban nasu kuma ni ce uwan su.
wannan kaɗai shine mafita in sauya musu makaranta in nesan tar da su daga gare shi, in ma koyarwa yake a makarantar imma mene ne baya sake ganin su bare ya cigaba da cusa musu wani ra'ayin, ai dai sun rabu bashi basu, bazai sake ganin suba suma haka bare su sake kiran shi da wani Daddy,
"Ɗan rainin wayo har da cewa surika ce masa wani Daddy, sai kace wani uban su ko meye gamin sa da su oho."
naja dogon tsaki tare da yin kwafa kana na mike, nashiga tuɓe musu uniform ɗin su, ina faɗin
"Ku da shi ɗin duk zanyi maganin ku."
bathroom na jasu da kai na nayi musu wanka yau, muka fito na saka musu wasu daga cikin kayan su da yake bedroom ɗina, sai da na nagabatar da sallar azahar kana na janyo su muka sauka kasa.
dinning area muka zarce bayan munci abinci najasu muka tafi part ɗin su Inna wuro, nan muka tarar da Faty ita ma dawowar ta daga school kenan, nan muka yada zango mukata hira...
da yammacin ranar zaune nake a parlour'n sama na ɗago wayata na laluɓo number shugaban makarantar su Naseem.....!





Mommyn Twins ce







8





Nan nake shai da masa bukata ta nakan canza su Naseem makaranta.
shugaban makarantar nasu yace "To ba bubu da muwa amma dan Allah muna so musan dalilin da yasa ake son sauya musu makarantar ko kuma makarantar tamu babu koyo ne yan da ya kamata?".
nace "Ko kaɗan ba haka bane ba kawai dai ina so ne na canza musu makarantar ba wai kodun rashin koyo ba, ai ba za'a ce makarantar ku babu koyo ba, yara suna fahimta sosai, kawai dai yaɗan yi nisa ne."
yace "To in dai kuwa haka ne to dan Allah kada a ciresu a makarantar gaba ɗaya, akwai ɗaya makarantar mu dake wata unguwa mafi kusa da ku in dai kina so sai a maida su can ɗin, ranar Monday idan suka zo sai ayi transfer ɗin su can ɗin."
shiru na ɗan yi cike da nazarin maganar sa, sai kuma nace
"To shi kenan a mai dasu can ɗin."
har munyi sallama zan kashe wayar yayi saurin cewa
"Dan Allah Madam a daure a kawo su sai a kaisu wancan makarantar, idan akace an cire su gaba ɗaya kokon to zai shiga zukatan iyayen yara zasuyi zaton ko wani matsala ce mai girma aka samu cikin makarantar, tun da bawai barin garin zakuyi ba,
zamu iya samun dakilewar customer, adai duba lamarin da kyau Hajiya."
"Babu damuwa in sha Allah za'a kawo su sai a kai su wan can ɗin."
godiya yashiga yi min kana mukayi sallama na kashe wayar.

Ina sauke wayar number Ukhtee na kira yayi ta ringing ba'a ɗaga ba,nakuma mai da kiran shima har yakusa yanke wa kafin ta ɗaga, da sallama.
na amsa cikin harshen larabci nace
"Oh kai Ukhtee ina kika aje wayar haka ina ta kiranki baki ɗaga ba?, ko yanga kike min an ce miki ni saurayin kine."
dariya tayi tare da faɗin
"Saurayi kuma haba dai kedai wayar tana bedroom ne nikuma ina parlour, nama shigo ɗaukar abune cikin ɗakin naji wayar tana ring, ai da haka zaki ta kira ma ban sani ba, ya kuke ina yarana suke?."
"Lafiya lau duk muna lafiya, yaran ki suna can gurin Bappa sunki biyo ni suna can suna damin sa da surutu, ni nagaji da hirar ne nadawo side ɗina naɗan huta suna can."
larabcin nake ina ta haryaɗa shi.
dariya tayi jin yan da nake ta kwamusa larabcin, tace
"Oh kin dawo kasar ku yaren kasar ku yana so ya korar miki da yaren kasar muko?."
nima dariyar nayi tare da faɗin
"Ashe kin gane inata yi da kyar amma fa su Naseem sunanan da shi a bakin su domin makarantar isilamiyyar su larabci zalla ake, shi yasa yake nan zaune a bakin su."
tace "Kai naji daɗi wlh gara ai su zauna da larabcin a bakin su, ke kizauna da yaren kasar ku tun da shi kika zaɓa."
nace "To ya zanyi mahaifa ta dole naso yare na ke ma ba kina son yaren kiba?."
tace "Sosai ma."
"Oh to shine nima baki so naso nawa yaren."
mukayi dariya. hira kukayi tayi sosai da Ukhtee wani maganar idan nayi ita zata gyara min shi dan larabcin bai gama nuna baki na ba.
sai can da jinawa mukayi sallama.

Yau Monday kamar yan da nasa ba na rako su Nasmah gun mota, Yakubu dake goge motar yayi saurin buɗe motar nasaka su ciki,bayani na yiwa yakubu kamar yan da mukayi da shugaban makarantar su idan sun je za'a haɗa su da wani domin yayi musu jagora zuwa ɗaya makarantar.
ina tsaye ina ɗaga musu hannu har suka fita...

Kai tsaye Yakubu yaɗau hanyar makarantar, kamar koda yaushe hira yake da yaran yanata washewa da dariya kamar yan da suma suke ta washe baki.
suna isa bakin get ɗin makarantar yayi parking yafito, kana ya buɗe musu suka fito, suna fita suka shige cikin makarantar direct office suka nufa daga nan aka haɗa su da wani malami da zai kai su ɗaya makarantar, suka fito tare.
suna fita bakin get ɗin school ɗin,
wata lafiyayyi zazzafar mota tayi parking a gefe, tun kan motar ta kakarasa parking Naseem yafara murna yana faɗin
"Laa ga Daddy yazo laa ga Daddy yazo."
Nasmah ma kuwa ihun murna ta sake tare da sa gudu sukayi gurin motar.
da sauri ya buɗe motar ya fito yaware hannayen sa ai ko da gudu suka shige jikin sa ya rungume su, duk suka saki dariya har dashi, kana ya mike yashiga ɗaga su yana cillasu sama sai kya-kya ta dariya suke.
sai da yayi wa kowannen su haka har sau uku kana yadire su kasa,
Yakubu ya karaso in da suke yana washe baki da faɗin
"Ranka shi daɗi barka da war haka."
amsa wa yayi fuska a sake sai dai gaba ɗaya hankalin sa na kan su Nasnah da suke ta zuba masa surutu.
shima wannan malamin da aka haɗo su da shi ya karaso yana faɗin
"Barka da zuwa yellaɓoi."
yace "Yau wa, yaya ji da ɗaliban?."
malamin yawashe baki tare da faɗin
"Muna kai kam."
yace "Masha Allah."
malamin ne ya dubi yakubu da kuma yaran yace
"To muje ko."
yayi maganar yana duban motar su.
sai a lokacin Ahmad ya ɗago da kallon sa kan yaran yadawo da shi kan su Yakubu kana yace
"Ina kuma za'a je ba makaranta za'a shiga ba?".
yayi maganar yana shafa kan su Naseem.
malamin yace "A'a zamu tafi da sune ɗaya makarantar mu."
duban sa Ahmad ya kuma da alamun tabbayoyi ɗauke a fuskar sa,
kana yace "Wacce makarantar kuma?."
yace "Ɗaya daga cikin makarantar mu ne za'a mai da su."
da fuskantar mamaki Ahmad yace
"Har sun gama wannan makarantar ne da za'a tura su wata makarantar daban?."
kai malamin ya girgiza tare da faɗin
"A'a ai za'a sauya musu makarantar ne anyi musu transfer can ne."
ɗan shiru Ahmad yayi kana yace
"Malam ɗin yana ciki?."
kai malamin ya gyaɗa tare da faɗin
"Eh yana ciki." yace
"Okay to muna zuwa." yafaɗa tare da gyara rukon Naseem da Nasmah a kowani hannun sa guda, ya janyo su suka shige cikin makarantar.

Malamin ya dubi Yakubu dake ta washe baki yace
"Wai nikam da ma ƴaƴan Ahmad Tijjaji Sabil ne kake kawowa makaranta?."
Yakubu ya daɗa washe baki yace "A'a ƴaƴan me *HAM'NAS* Company ne fa."
"Au ƴaƴan mai *HAM'NAS* Company ne to shi Ahmad Sabil dangin su ne? lallai Allah mai yin yan da yaso yahaɗa family guda da tarin dukiya."
Yakubu yace "Eh ƴan uwa ne."
yafaɗi hakan ne kawai dan bashi da amsar bashi, dan shi kansa bai isa yace suna da dangan taka ko basu da shi ba, a matsayin sa na mai ai kin gidan ba lallai dole yasan dan gin gidan ba, san nan kuma baya so ya disga kan sa gaban malamin, ko ba komai shi ma za'a rika yi masa kallon wani...
suna nan tsaye
zuwa can Ahmad yafito shi kaɗai batare da yaran ba.
ido suka zuba masa ganin yafito shi kaɗai, yakaraso in da suke, duban malamin yayi tare da faɗin
"Ka koma kacigaba da koyar da ɗaliban ka, kai kuma ka koma gida ka dawo da wuri ka ɗau ke su."
yakara she maganar da duban Yakubu.
Yakubu yace
"Ranka shi daɗe hajiya tace na tsaya sai mun kai su kafin na komo gida."

Yace "Kar ka damu kaje ka abin ka."
yace To. yashiga mota in da tuni malamin ma yakoma cikin makarantar.
shiko Ahmad a hankali ya isa jikin motar sa ya shige ciki...

Da misalin karfe 12
a hankali na mike na shige bayi wanka nayi haɗe da ɗauro al'wala nafito,nashirya cikin wani doguwar rigar atamfa pauda da man lip kawai na goga sai turare dana fesa a jikina,
a hankali na isa jikin window labulen window'n naɗan janye shi gefe tare da zuge glass.
ido na kurawa furannin da suke ta kaɗa wa gwanin ban shawa,
idanuna na sauke can bakin get jin karar buɗe get ɗin, da murmushi nake kallon kofar,
dan nasan su Naseem ne suka dawo, ɗan gimtse annurin fuska ta nayi ganin ba motar kai su makaranta bane wata motar ne daban ta shigo.
a sannu motar ta isa ta gyara parking a gefen farfajiyar gidan,
an ɗau tsawon minti 10 kafin aka buɗe motar,
ido na waro cikin tsananin mamaki da shiga shoc ganin wan da yafito daga cikin motar, cikin matukar kufula nake kallon sa yayin da yazaga ɗaya gefen ya buɗe, sai ganin Naseem da Nasmah nayi sun fito daga cikin motar suna ta washe ba ki.
"What! me nake gani haka, yaran da nasa a canza musu makaranta domin sa wai bin su yakuma yi?."
cikin matukar ɓacin rai nasaki labulen da sauri na juya nafita a ɗakin na nufi kasa,
da sauri na ke sauka har ina haɗa step cikin hanzari nakarasa sauka nayi waje da sauri.

Suna tsate jikin mota sai zuba masa surutu suke shiko sai binsu da murmushi mai haɗe da dariya yake,
tun kan na karaso in da suke nashiga faɗin
"Kai malam wai meye hakan ne, wai meye gamin ka da yaran nan ne kam?!."
dai-dai lokacin na iso in da suke, kugu na rike cikin masifa nacigaba da faɗin
"Meye da lilin ka na wani shishige musu da kake kana ta wani cusa musu
wani ra'ayi meye nufin ka da su?."
maganar nake a tsai-tsaiye kuma cikin ɗaga murya cikin masifa nakuma faɗin
"Bana bukatar wani ya raɓe su da manufa irin naka kagane ko malam?."
tun da na fara maganar ido kawai ya zuba min batare da yace komai ba, idanun sa kan lip ɗina, a sannu yaɗan yi baya ya jin gina bayan sa jikin mota hannayen sa ya sarkafe a kirjin sa, harshen sa yaɗan zuro waje yalashi pink lip ɗin sa,
har lokacin fuskar sa na ɗauke da murmushi wan da dimple suka daɗa kawata annurin fuskar sa.
cikin kuma ɗaga murya na dubi su Naseem nace
"Idan baku wuce kun shiga ciki ba na rantse sai na ɓaɓɓala yaro anan gurin ku wuce mutafi nace!."
nafaɗa ina nuna musu hanya.
Nasmah tace "Mommy ja mu jo."
ido na waro wato ma na jira su kenan sai sun gama abun da suke.
shiko wani murmuahi yakuma sakewa.
tsayuwar sa ya gyara tare da duban yaran kana ya mai da duban sa kai na sannan yafara magana
"Zaki ɓalla su?."
ya faɗa tare da kuma sakin wani murmushi kana ya ɗan sun kuya yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran ya dubi ko wannen su yace
"Kuje ciki ayi muku wanka kuci abinci ku kwanta ku huta kuyi bacci idan kun tashi kuyi karatu gobe zan tambaye ku karan tun da kukayi kun ji ko?."
kai suka gyaɗa masa suna faɗin
"Tom." yace "Yauwa to maza a je ciki."
Naseem yace "Daddy dakajo anjima?."
kai yagyaɗa yana mai cigaba da wannan murmishi wan da kamar da shi aka gina fuskar sa yace
"Sosai ma zan zo mana."

Cikin hatsala haɗe da ɓacin ran ganin yau ma kamar na ranar da na same su tare da shi a kofar makarantar su, ina nayi musu magana sukayi kamar basu san ni ba,
sai shi da suke ta biye masa suna bashi amsar duk abun da yace musu,
bugu da karin bacin raina kiransa da sunan dana hane su a gabana.
cikin tsawa nace
"Kai Naseem me nace maka waye Daddy'n ka wato bakaji ba ko, ban ce muku kada ku kuma cewa wani Daddy ba, wato duk maganar da nake muku aban za bakwa ji ko, idan naji kasake cewa wani Daddy sai na fasa maka baki,wuce mutafi nace!."
ko da nake masifar harlau idanunsa a kai na, sai ya saki wani murmushin gefen baki yayin da gefen kumatun sa na dama ya lotsa, har kuma lokacin yana rike da kafaɗar su.
a sannu yaɗan sun kuyo yadubi Naseem kana yakuma dubi Nasmah kana yakuma sakin wani murmushin sannan yace
"Naseem Nasmah mene ne ma suna na?."
suka haɗa baki wajen cewa "Daddy Daddy tunan ka."
yace "Kai yaran nan to Allah yayi muku albar ka, to maza ku tafi ciki ayi muku wanka kuci abinci maza kuje."
ya faɗa yana tura keyar su.
ai ko da gudu suka yi ciki suna dariya, ganin rainin wayon nasu da yawa yake wato umurnin sa ma zasubi ba nawa ba. nadube shi tare da rike kugu nace
"Kai malam kana ji ko, kada ka sake zuwa in da yara na suke kada ka sake kasake zuwa in da suke, kada ka sake cusa musu ra'ayin cewa wai kai Daddy'n su ne, kai ba Daddy'n su bane basuma san ka ba, ni ban gayyaci wani acikin lamarin ƴaƴana ba,karabu da harkar yara na idan kuma ba haka ba wlh zan ɗauki tsatstsauran mataki a kanka, kada ka kuskura ka sake zuwa in da yara na suke, kada ka sake yi musu karya kan abun da ba haka bane, bana kara kan haka dan ƴaƴana nice kaɗai uwan su kuma uban su,
dan Allah malam kada ka sake cusawa ƴaƴana wannan gurguwar ra'ayin, ka gane ko?!."
na karashe maganar da nuna masa yatsa haɗe da murguɗa masa baki, na juya a hatsale ganin duk maganar da nake madadin ya shiga taitayin sa sai ma daɗa sakin wannan murmushin nashi yake.
tafiya na soma cikin fushi dan nalashi takwabin yau sai na zane yaran nan tun da har ni zasu gwadan wani yafi ni muhimmanci agurin su har zasu ji maganar sa akan nawa.
sai jin maganar sa nayi daf dani
"Kece uwan su kuma uban su to ya akayi kenan hakan ta faru, ke kika ba kan ki cikin kenan,faɗa min da ma a she mace tana bawa kanta ciki da kanta, dama a she uwa tana bawa kanta ciki ita kaɗai batare da uba ba??."
wani irin juyi nayi jin sautin sa kusa dani batare da zato ko sammani ba, maganar yashige ni tamkar shigar shoc cikin jini na, wani irin mugun kallo na watsa masa tare da jan dogon tsaki, najuya na nufi kofar side ɗina da sauri...
shiko bayana yabi da wannan murmushin kana ya juya yashige motar sa yaja yabar gidan.

Koda na shiga banbi takan su Naseem ba dan nasan koda na yi musu hukuncin danayi niyyar ma bashi zai sa su dai na abun da na hanasun ba,
sai kawai nashige ɗaki nazube bakin gado, kamar an zabure ni kuma na mike na isa gaban mirror in da wayoyi na suke ajiye, number Yakubu na kira, nafara zazzage masa masifa
"Wato Yakubu dana ce kaje ka ɗauko su shine bakaje ba kabar wannan ɗan rainin wayon mutumin wai Ahmad yake ko wa yaje ya ɗau ko su ko?,
idan ka gaji ne kafaɗa sai a sallame ka."
da sauri yatari numfashi na da faɗin
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh yanzu haka ina hanyar dadowa ne ina ma kokarin kiran ki kenan sanar miki sai ga kiran ki, naje makarantar aka ce min yazo ya ɗauke su, ai Hajiya baki sani bama ɗazu da zamu kai su sabon makarantar yazo ya mai da su cikin makarantar yace mutafi mu barsu anan."
ido na waro da ɗinbin mamaki mai haɗe da mugun ɓacin rai,
ban san san da na dakawa Yakubu tsawa ba nace
"Dalla malam ya isa ni da kai na nace ayi abu kan ƴaƴana sannan wani can daban yazo yace ba hakaba kai kuma ka yarda, umurnin sa kabi kenan? ok to ka wuce gidan sa daga nan kaje can yacigaba da baka umurnin!."
nakashe wayar rai ɓace,
"Lallai ma wato ashe ma ba'a kai su makarantar ba shike nan ya hana ko me?."

Afusace na danna number shugaban makarantar yana ɗagawa nace
"Malama ya zan ce ga abun da nake so sannan kuma wani yazo ya hana kuma ku amin ce, to gaskiya daga yau bazama su sake zuwa makarantar ba ma sun fita kenan."
da sauri yace
"Ranki shidaɗe mahaifin su ne yazo yace kada a canza musu

Please Login or Register in order to submit comment