You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin sarki ya hau sarauta ya"

"auri uwarsu Hajiya Hadiza, sun rabu tun shekaru da dama."

"Yanda ta ba ni labari ba ta san abin da ya haWa su ba, amma Sarki baya son ko sunan yaran a ambata, ba"

"ma uwarsu ba, wannan dalili ne ma yasa jama'a da dama sun yi zaton Yarima ne babban Wan Sarki Jafar."

"Uwarsu Abdul Rahman tafiya ta yi da su hannunta tun suna ™anana, sai dai in sun ga dama suna zuwa"

"gaishe shi, shi ma sai a yi shekaru basu zo ba, yanda ta bani labarin, yanzun haka Hajiya Asabe tana Ibadan tana auran wani mai kuWi Alhaji Alabi."

"Shi kuwa Abdul Rahman yana Scotland zaune da matarsa baturiya (Vivian), yanda Mama take nuna mini"

"kamar Sarki ya yafe su ™wata-™wata, kenan ya barwa uwarsu su, sai dai ta ce ya kan aika masu da kuWin makaranta da na abinci da suna yara, yanzun kuwa ko maganarsu ma baya son a tayar."

"Asalinsu Mama kuma iyayenta ´an barikin Ladi ta nan Jahar Plateau,tun da daWewa a garin Jos,´an"

"™auyukan garin ke zuwa karatu, wato Makarantar ™wana ta gaba da Primary,anan suka haWe da Sarki a"

"lokacin bai ma hau gadon sarauta ba, daga baya ne ma da ya hau mulki ya ™ara auran Hajiya Kilishi."

"Yanzun haka iyayen Mama suna nan da ransu a garin Aboko, da sauran danginta. Yarima kuwa shi ne"

"Wan ta na farko, sai Salimat, sannan Idris, daga su kuwa ba ta ™ara ba. Hajiya Kilishi kuwa anan Jos ya"

"aure ta,Wiyar hakimin Bukuro ce ta nan ™aramar hukumar Plateau."

"Saboda rashin ganin hanya a ranar da muka zo gaishe da iyayen Yarima, shi yasa ban gane cikin gari suke"

"zaune ba,a unguwar Dogon Agogo,wai wannan rukunin da nake gani har wajen ba™wai a gidan Yarima,wai na farko fada ce in Sarki ya zo kenan dai gidansa ne na hutawa,ko kawo ba™i na musamman."

"Sai masallaci a li™e da shi, ragowar rukunin kuwa kamar namu ne,gidana da na Yarima, sai na su Idris da"

"Ahmad,wai in sun yi aure, amma kowanne da kalar yanda aka tsara nasa ginin, amma tsananin kowanne gida zuwa wani gida, sai an shiga mota,in ba motsa jini za'a yi ba, saboda ko da Asuba ko ragowar sallolin"

nan an kai Yarima a mota.

*** **** ****

"Tsugunne muke gaban Sarki ni da Yarima a ™aton falonsa, na cikin gida,kawunanmu kuwa a sunkuye"

suke da gani ka san gaban manya muke.

"""Yau ne matarka za ta koma gidanta wacce ta samu tsayin ™wanaki arba'in da biyu a hannunmu, dalilin"

da sakacin da ka yi da ita har ta faWa haWarin saran maciji.

"Bayani ya same ni na irin zaman da ka yi da ita a baya, zaman ko in kula da banzatar da ita. Wannan dalili"

"ne ma ya janyo mata faWawa rayuwa ™untatacciya, na gode,ka yi mini daidai ashe ni ina ta™ama da ina da Wa mai biyayya, ashe ban sani ba,™arya zuciyata ke gaya mini."

"Ka bani mamaki,a ce ita mace na je na nemo auranta ga iyayenta, suka amince suka ba ka ita, alhalin ba"

"ta san ka ba, kuma suna da wanda ke jiransu su aura masa ´arsu, ita ma tana da wanda zuciyarta ke so, amma ta ha™ura ta yi biyayya ga iyayenta, kai kuwa ban isa ba."""

"""Baba. "" Yarima ya faWa cikin sanyin murya."

"""Kada ka ce mini komai, kai ne da bakin ka ka gaya mini da ka amince in zaSa maka wacce na ga ta dace"

"da kai, tun daga ranar na baza mutane a kan su gano mini matar da ta dace da Wana wanda nake mugun"

"™auna a zuciyata, Allah ya ba ni ya kuma ba da sa'ar aka samu ´ar gidan manyan mutane masu mutunci."

"Ka tuna,bakina da naka muka yi wannan maganar ba fa aike na yi maka ba,ka tuna,kiranka na yi ka faWa"

"mini wacce yarinya ka gani ta ™wanta maka a yi maganar auranku,ka tuna, kai da bakinka ka ce mini"

babu.

"Yanzun na yanke hukunci zan raba auranku, amma na baka tsayin ™wanaki biyar ka zo mini da"

"rubutacciyar takardar sakinta. """

"""Baba. """

"""Bana son jin komai daga gare ka,ka bani haushi,ka Sata mini raina matu™a."""

"Ya mi™e tsaye, ""Šiyata ina ™aunarki da Wana, amma ki je kiyi ha™uri, sannan ki yafe ni da na sa aka raba ki"

"da wanda ke son ki,saboda son kai irin nawa. Zan aiko a yi kiranki."" Ya juya ya tafi."

"Yana ™ulewa a inda har ya ™ule, Yarima na Baba,Baba cikin girmamawa, amma bai ko juyo ba,ni kuwa na"

waigo a sanyaye na kalli Yarima inda ya koma ya ™arasa zama a ™asa.

"""Tashi mu tafi."" Na faWa cikin muryar da zata ™ara karyar da zuciya."

"""Kin ji abin da Sarki ya ce fa Yasmin."""

Na Wan yi murmushin da ™ago shi kawai na yi.

"""Kana da magani?"" Ya girgiza kai. Na mi™e na bar shi a wajen zaune,gudun kada ya karyar mini da"

zuciyata.

"Ina jiyo su daga falo,suna cikin Wakin Mama yana gaya mata, amsar da ta bashi ce nima ta Wan firgita ni."

"""Gara haka,ai ni har naji daWi, tun da baka son ´ar mutane a dinga ajiyarta a gidanka,™wanaki nawa kuka"

"Wauka da ita ba ka ji kana son ta ba,sai yanzu ?"""

"""Mama zan iya yi miki rantsuwa da Al™ur'ani akan ina son ta, Mama duk laifinta ne. """

"""Laifintan wa? Kusan kullum sai mun yi waya in har baka zo ba,in dinga ™watanta maka cewa don tana"

"mace,kai ya kamata ka dinga shishshige mata,yau da gobe za ta saki jiki da kai."""

"""Wallahi Mama, ina yi mata, ita da wanda take so,wai shi ANWAR."""

"""Shi kenan ka ga yanzu ka yi wa kanka, ita kuwa tana da wani."""

"""Mama yanzu ya zan yi? Wallahi ina son Yasmin,ni dama can ina son ta."""

"""˜arya ka ke yi, da kana son ta da baka tsaya yi mata mulki da kuma ˜ASAITA ba, haka ka ga muna zaune"

da mahaifinka?

"Mulkinsa da ™asaitarsa a waje suke, sai kuwa idan ya shigo gida ya ga barorinsa, wannan dole ya yi,kana"

kallo wata rana da kansa zai le™o ya kira wacce yake son yin magana da ita a cikinmu.

"Ko an ce maka jakadiyar da aka sa a tsakaninku, Addini ne ya shinfiWa ta?"""

"""Mama matsalar, Mama, Yasmin ba ta sona ™wata-™wata,ni kawai ke sonta."""

"""A yanzu ko kai ma?"""

"""Mama ki tuna ranar da na fara ganinta daga can sai nan fa nazo na gaya miki na ga yarinyar da nake"

"so,amma ban san ko ´ar waye ba, har ki ka ce sai in je in ta nema, wallahi Mama ita ce nake gaya miki,"

"don dai haWuwarmu ta zo ne da saSani shi ya sanya. """

"""SaSani ko dai ka nuna mata kai ka isa, dole ne ta ji tsoron zama da kai yanzun."""

"""Mama duk ki bar wannan maganar,a yanzu na ajiye duk wata ˜ASAITA in dai ina tare da Yasmin kamar"

"yanda nake miki Mama."""

"""Yanzun ko?"""

"""Mama,ki taimaka,in Sarki ya ha™ura ma zamu Greece Honeymoon da ita."""

"""In tana son ka ko, na san zai sa a tambaye ta,in ta nuna a'a, to kai ka sani."""

"""Mama zan yi ™o™arin da Yasmin zata so ni, wallahi na yi miki rantsuwa da Allah."""

"""To na ji kayi ta addu'a ka san halin Sarki, baya tayar da magana in dai har ya furta ta da bakinsa,ka san"

"dai ba sabon abu ba ne ba wannan. Yanzun da ™afar ´ar mutane ta lalace ya za mu cewa iyayenta?"""

"""Mama shi kenan mu zamu tafi, zan dinga zuwa."""

"Ta yi dariya, ""Dama ni ce Yasmin in ce sai Anwar "" Ta cigaba da dariya. Suka fito,ni kuwa sai ma na nuna"

ban san abin da suke yi ba.

"""³an gidan tun daga nesa na hango su tsaye ana ta murna,kai har da mazajen sashen gidan Yarima, Allah"

"Sarki, Mansura har da kuka,yarinyar nan ta shiga raina nima,ko don yadda take nuna mini ™auna,wai sai da muka kusan wajen sannan aka ™ara sakin labulan nan ba™i, duk da dama gilashin motar ma ba™i ne,"

sai dai ka ga mutum amma shi baya ganin ka.

"Ya juyo sosai ya ri™e hannuna, ""A tanadar mini abinci,yau gidanki zan yi hira, saboda in taya ki zama."" Na"

rausayar da idanuwana na yi murmushin da na san gefen kumatuna suna lotsawa.

"""Ka fi ™arfina."" Ya yi saurin matsowa. ""Kada ki ™ara faWar haka, har kin janyo ma ba zan iya wucewa"

"gidana ba,naki gidan zan sauka."""

"Ka rufa mini asiri."""

"Sai na ga ya yi saurin sakin hannuna ya matsa baya, wacce ta yi daidai da buWe ™ofar motar da muke ciki."

"Mun gaisa da jama'a da dama, sannan muka haye sama Wakina, sai na ji na kasa komai. Wannan yasa na dinga haWa shi da Allah ya tafi Wakinsa,an jima da dare ya dawo hirar sannan ya amince."

"˜wana uku yana zuwa taya ni hira, sai sha biyun dare yake tafiya, a ranar na huWun da goma na dare na ji"

"wayar hannuna ta yi ™ara, na Wauka a tunanina Aunty ce, sai na ji muryar Yariman da na gaji da jira, na yi"

"™walliyata mai ™yau, saboda shi amma shiru, wanda na kasa zaune na kasa tsaye saboda rashin"

"zuwansa,ni kuma na kasa zuwa inda yake in dubo ko lafiya."

"A hankali yake magana cikin muryar da zata iya tayar maka da hankali, idan ka ji ta, saboda tafi yanayi da"

"ta marasa lafiya,a take kuwa na ji hankalina ya tashi."

"""Yasmin na kasa zuwa wajanki."""

"Cikin yanayin tashin hankali na tambaye shi, ""Ba ka da lafiya ne?"""

"""Eh, to ni ya zan ce miki, zaki iya zuwa gare ni yanzu? Yasmin forget the fast please."""

"""Zan yi tunani."""

"""Please Yasmin."""

"""Okey,na ji."""

"Ya kashe wayar, na mi™e tsaye daga zaunawar da na yi a gado, na nufi madubina, na ™ara feshe jikina da"

"turare, na kalli kaina irin kayan da ke jikina, riga da siket ne na Turawa amma buWaWWen siket ne, ga shi"

"da tsayi har zuwa ™waurina,bulu ne mai haske (light blue)."

"Sai ruwan ja amma mai haske light pink mai dogon hannuwa ce, amma daga ™arshen hannun buWaWWu"

"ne, sai buWaWWan wuya, wanda ya nuna sashen bayana a buWe yake, haka gaban rigar (roundneck) , zagayayyen wuya ne, da wasu zarirrika biyu a gaban rigar waWanda an yi su don ™walliya kawai."

"Takalmin ™afata masu Wan tsini ne,kalar rigar jikina, amma Wan mayafin da aka sakowa kayan irinsu Waya"

"da siket Win,bulu mai haske kenan, sai da na feshe gashin kaina da turaran shi, sannan na mayar da mayafi na yafa kalar rigar jikina,alkyabbar da na rufa a sama, ita ma pink ce, sai da na kuskura man ™amshin baki mai ™amshin (mouth wash,rinse), sannan na rataye wayata mai ruwan alkyabbar a"

hannuna.

"Na murWa ™ofa na shiga,™asan ba kowa sai fitilar nan Waya da aka saba bari duk dare na Ubangiji, na haye"

"matattakalar bene,domin in isa Wakinsa."

"Falon sama na same shi ™wance cikin kujerar hutawa farar shirt ce da wando a jikinsa, amma ya Salle"

"maSallan gaban rigar, sai farar singilet ce ta rufe fatar naman jikinsa."

"Wayar hannu ita ce a saman ™irjinsa, wacce kalar jikinta fari ne daga ™wancen ya juyo ya kalleni."

"""Yasmin."""

"Shi kaWai ya faWa, amma bai tashi ba, na iso na tsugunna gabansa."

"""Ba ka da lafiya ne?"" Na dafa saman goshinsa, ya lumshe idanuwansa."

"""A'a."""

"""Yana ga jikinka ya yi laushi?"""

"""Ke ce."""

"""Me ya faru kuma?"""

"""Gobe ne fa Sarki ya yanka mini."""

"Ya yi shiru nima sai na ji gabana ya faWi. ""Na yi waya da Mama yanzun kafin in yi miki, amma ta ce Sarki"

"yana nan a kan abin da ya faWa."""

*˜ASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 3

"""To me ye na damuwa?"""

"""Na san halin Sarki ba tayar da magana."""

"""Shi ne na ce me ye na damuwa? Iyaka ka auro wacce ka ke so,dama ni ma takura ka aka yi ka au. """

Ya tashi zaune tamkar tashin wanda ba shi da lafiya.

"""Me ye abin damuwa Yasmin? Ni ke ce abin damuwata."""

"Na mi™e tsaye na ja baya tare da dafa goshina, na juya kamar zan tafi."

"""Yasmin,No! No!! No!!! I love you. Na juyo da kaina na gan shi a tsaye yana kallona, na girgiza kaina na"

juya zan tafi.

"""Please, Yasmin."""

"Na tsaya cak a lokacin da na ji wani abu yana yi mini yawo a cikin jikina, wanda ba zan iya faWar yanda"

"yake ba, na mayar da idanuwana na lumshe tare da fitar da numfashi sama-sama,shin me ye wannan? Ban kai ga tunanin amsar ba, na ji an rungume ni ta baya."

"Ajiyar zuciya uku ce ta fito gaba Waya a cikin sakan Waya, kafin in yi tunanin ya zan yi in ™wace jikina daga"

"Yarima, sai na ji ya zame alkyabbar da ke sanye a jikina zuwa bayana, madadin buWe bakin da na yi inyi magana, sai dai bakin ne ya tsaya a buWe sakamakon sumbata da ya kai a buWaWWan bayana, wanda riga"

ba ta ™arasa rufe shi ba.

"Madadin inji ya sake ni, sai na ji ya cigaba da sumbatar wuyana zuwa bayana. Me ye wannan ke yi mini"

"yawo a jikina? Lallai ba zan iya gano ko me ye ba,saboda ya fi ™arfin in iya faWarsa, jin alkyabbata ta faWi"

"™asa, ita ta dawo da hankalina a jikina, wanda na ji sam ba shi da ™arfin komai."

"Ba zan iya wata magana ba, sai dai na yi Wan ™o™arin da bai wuce na mirginawar marar lafiya ba, na zame"

"jikina, ina girgiza kaina, idanuwansa a lumshe suke inda yake saukar da numfashi sama-sama kamar mai asma farkon tashi."

"Numfashin haWe yake da faWar, ""No! No!! No!!!"" Wacce ba zan iya ™irga ko nawa ce take fita daga"

"bakinsa ba, wannan ne ya ba ni damar jan jikina in tafi gidana, wanda ko alkyabbar ban tsaya Wauka ba."

"Sai da na tsaya jikin ™arfen matattakalar bene na Wan huta,don ™arfi ya samu a jikina, sannan na samu na"

"iya gangarewa ™asa, har na kai ™ofa na murWa na juyo muryarshi."

"""Yasmin."" Na waigo na kalleshi tsaye yake a ™ofar benen ri™e da alkyabbata a hannunsa, na mayar da"

"kaina na sunkuya a inda ya iso, ya tsaya gabana tare da mi™o mini alkyabbata,na karSa muna kallon-kallo da shi."

"Sannan na murWa ™ofa zan fita, ya juyar da kai tare da Wan asirtaccen murmushi, wanda da gani tare"

"yake da takaici, saboda fitowar da ya yi tare da numfashi, sai da ya yi irinsa ya kai sau ba™wai, sannan ya"

"ja baya na buWe ™ofar, ya yi saurin ri™o hannuna."

"""Yasmin stay with me."" Na girgiza kai, na saSula hannuna na yi gaba, sai dai na jiyo shi yana kiran. No!"

"No!! No!!!"" Šinsa da ya saba kira,ko waigowa ban yi ba."

"Da gudu na haye saman Wakina, ina zuwa na faWa gadona, sai da na mayar da numfashi ya fi talatin"

"kamar wacce asma ta taso mata, ga idanuwana a lumshe, sannan na ji tunani ya zo mini."

"Shin ko wannan shi ne SO? Na girgiza kai,ba zan so Yarima ba. To me ye wannan? Oho, abin da zuciyata"

"ke faWa kenan,nan take ta juya linzamin tunaninta ga abin da ya faru ´an mintuna da ba su wuce goma"

ba da suka wuce.

"Jikina na ji ya kama rawa shi kaWai, na yi sauri na mi™e tsaye, sai na ji kamar jiri na shirin kada ni, na yi"

"saurin zama, na cire mayafin kaina na jefar da shi ™asa, na juyar da kaina, kamar wacce ta rasa abin da ke"

"yi mata ciwo a jikinta, na sunkuyar da kaina, gashin kaina ya zubo a fuskata,a inda na tura hannuwana"

duk biyun cikin gashina.

"Na samu mintuna goma sha biyu a haka, sannan na ji kamar an sumbaci bayana, na yi saurin Wagowa,"

"amma ban ga kowa ba, na yi murmushi na mi™e na nufi banWaki. A banWaki na cire kayana duka na shiga ruwan wanka mai Wumin gaske,wai ko abin da nake ji ya sake ni. Tsayin mintuna biyar na yi kawai na mi™e da sauri, saboda tunanin da ya faWo mini a lokaci Waya."

"Na Waura tawul na fito da saurina,wai ji nayi kamar an bugo mini waya,ba abin da ya faWo mini kuwa sai"

maganar Sarki.

"""Zan turo a kira mini ke kin ji."""

"Hankalina ya tashi matu™a, gobe, gobe lallai zan shiga damuwa kenan in an rabani da Yarima."

"Na yi saurin tunano Anwar a zuciyata, take sai na ji bana son tunaninsa,na fi son tunanin Yarima,shin ina"

"son Yarima? Ba amsa, na Wauki rigar bacci ta da su Mansura suka ajiye mini na zura a jikina, da ™yar na iya Waga ™afata na zura Wan diras Win da ke kusa da ita, na isa ga madubi na taje kaina tare da ™ara gyare shi."

"Rigar baccin doguwar shimi ce har ™asa, orange colour da ´an hannuwanta guda bibbiyu a kowanne"

"Sangare sai Wan leshi da ya ratsa saman ™irjinta, ruwan lemo ce mai santsin gaske. Na feshe jikina da"

"turare madadin in haye gadona sai na ji na kasa, buWe ™ofar barandar gaban gidan na yi na fita."

"Kamar yanda na saba a kullum yau ma haka na yi, shi ne in ware hannayena duk biyun,yau ma kuwa na"

"samu sa'ar garin yana fitar da iska mai sanyin gaske, wadda ta taimaka da wasa da gashin kaina, idanuwana kuwa a lumshe suke, amma na kasa tunanin komai a yau."

"Cikin wani sanyin jiki da sanyin zuciya, na ji tunanin Yarima ya faWo mini a zuciyata a iya nawa tunanin,"

"sai na ji dama Yarima ya iso yanzu,can Wayan gefen na zuciyata kuwa, sai ya dinga karanto ni a jikin Yarima,a cikin tunanina ne na ji kamar an bi nawa hannayen a hankali, wani daWi ya dirar mini a zuciya."

"Cikin tunanin kuwa na ji an haWe ´an yatsun hannuna da nashi waje Waya an runtse su, cikin ™wanciyar"

"hankali ya rungume bayana a ™irjinsa, sumbatar da ya kaiwa wuyana shi yasa na saukar da ajiyar zuciya"

mai fitar da sauti.

"Hankalina gaba Waya na ji ya Wauke har ya zamo na manta mai nake ji a jikina, ™wa™walwata ta fara"

karanto mini da in buWe idanuwana da suka yi nauyi in ga ko zan ga Yarima a barandarsa.

"Cikin sakan biyar na ji hankalina ya dawo a jikina, madadin in jini ni kaWai ina tunanina, sai kawai na tsinci"

"kaina da jin Wumin mutum a jikina, gaske ne,ko dai har yanzun mafarkin tunanin ne nake yi,jin sautin numfashi na tashi a kunnuwana yasa na buWe idanuwana da sauri."

"Na razana, na tsorata, duk a lokaci Waya da na ji bakina ana Yarima, na yi Wan gaggawar fizge jikina na ja"

"baya, kenan mafarkin tunanin da nake yi da gaske ne, na girgiza kai tare da Sata fuska."

"""Me ke damun ka haka? Bana son abin da ka ke yi mini,ba na..."""

"""Yasmin ya isa haka nan,don Allah, na san na yi miki laifi a baya, ya kamata ki zamo mai yafe mini."""

"Ya matso ya tallabo fuskata Wacce gashi ya rufe ta, yasa hunnunsa ya gyara gashin zuwa baya."

"""Yasmin."""

"""Ni fa ba zan..."""

"""Yasmin kada ki faWi abin da zai ™ara tayar mini da hankali."""

"""Ka manta gobe ne ranar ™arshena da kai,ka ga ba zancen wani gyara a nan."""

"""Na sani Yasmin,ki yi tunani kada kiyi tunanin ko yaudara ce tsakanina da ke, wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!"

"Tun a ranar da na gan ki a titin Ahmadu Bello Waya, har zuwa yau ban taSa daina tunaninki ba, matsalar da na samu shi ne ban san gidanku ba, ina shirin in bincika Allah ya haWa ni da ke a wajen fati,a ranar na"

"so mu daidaita sai ma ta ™arasa ™waSe mana."""

"Ya Wan tsaya ya mayar da numfashi, ya saki fuskata, ya dur™usa a gabana. ""Please Yasmin ki taimakeni,ki"

"zauna da ni."" Na tsugunno nima na fara magana a hankali, kamar yanda yake yin tasa."

"""Ba zai yiwu ba Yarima,ba zan iya zama da kai a wannan matsayin naka na mulki ba,ko tari na yi duk"

"gidan nan an sani, har zuwa gidanku."" Na mi™e na koma Waki na zauna gefen gadona."

Mintuna ba™wai da zamana ya shigo Wakin shi ma ya iso gaban gadon ya tsaya.

"""Ba zan taSa cewa na ha™ura da ke ba, ba kuma zan gaji da baki ha™uri ba, ba zan taSa mantawa da cewa"

"ina son ki ba, Allah ya gani, na yi miki abubuwa ne domin ki so ni, nima amma na yi kuskure."" Ya juya ya"

tafi ya ja mini ™ofar da har sai da na Wan tsorata.

"Na koma na ™wanta a rigingine, na dafe kaina da hannayena na yi tsaki, na juya na tashi zaune, na mayar"

"da numfashi na tashi na je na rufe ™ofar gaba, na koma na kulle ™ofar Wakina, na zare makullin na kashe dukkan fitilun Wakin, na Waga filo na saka makullan, na koma na shige bargona, kaina ne kawai a waje, inda idanuwana ke kallon duhuwar Wakina, duk da hasken da ke shigowa ta kafar labulaye ya Wan"

taimakawa Wakin da rage duhu sosai.

"""Yarima!"" Shi na faWa a fili, na tuna da maganar Sarki, na tunano Mama da ta ce Sarki ba ya magana ya"

"tayar da ita, hawaye na ji sun gangaro mini,wata zuciya ta tambaye ni, ""Shin ko ina son Yarima Faysal ne?"""

"Anwar shi ne mutumin da ya fara saka ni hanyar soyayya, mutumin da ya shayar da ni WanWanonta."

"Anwar Mutum ne wanda ya rigaya ya karanci halayyata, har ta zamo ba ta Sata masa rai."

"Anwar ba wai ™yakkyawa ba ne, sai dai sam ba ya layin munana,kalar fatar jikinsa kuwa mai Wan duhu ce,"

"amma da ganinsa ka san yana cikin hutu. Anwar babban ma'aikaci ne shi, wanda har ya kai matsayin babba a ofishin da yake (Cooporate Affairs Commission)."

"Mahaifinshi ya tsufa, mahaifiyarshi ce mai Wan jini a jika, wanda gidansu su huWu ne kacal,yayyansa biyu,"

"mace da namiji, sai kuwa ™aninsa namiji Waya. Ni kaina na san ina son Anwar, Mutumin da muka shekara"

"uku da shi muna (Friending), amma rashin auranmu da shi tun a baya, na san laifina ne, tare da ™addarar"

auran Yarima Faysal.

"Iyayensa ´an asalin Kano ne, aiki ya kawo mahaifinsa na Likitan dabbobi, suna da arzi™insu daidai"

"gwargwado, ga shi mutum ne mai tausayin gaske ni kaina na san Anwar na matu™ar ™aunata."

**** **** ****

"Wazirin Sarki,Galadima,Tafida, Talba da DurSi,su ne a tebirin shawarar Sarki, wanda Sarki Jafar Sada ya"

"tarasu ne a kan hukuncin da ya yanke a raba auran Yarima Faysal da Gimbiya Yasmin,saboda su ne mutanen da suka fi kowa kasanci da shi fiye da kowa."

"An Wauki Wan tsayin lokacin da za'a iya ba shi sa'a Waya (awa Waya), ana mahawara a kan maganar,"

"wanda a ™arshe magana ta koma ta basuyi na'am da hukuncin da Sarki ya yanke ba, saboda dalilai da"

"suka kawo irin nasu na manya, kamar dalilin waziri."

"Ya Kawo dalilinsa ne a kan nan gaba idan suka nemi aure za'a iya hana su, saboda za'a ga ba sa ri™e aure"

"da daraja, dalilinsa na biyu kuwa shi ne,a bar yaran da kansu su zo su ce basa son junansu,in sun zo da zancen haka, ina ga in an raba su ba za'ayi laifi ba wajen kowa."

"Galadima kuwa cewa ya yi a kan samu haka a tsakanin ma'auratan da aka haWa aure, ma'ana waWanda"

ba su suka zaSi junansu ba. Shi kuwa Tafida cewa ya yi abin kunya ne a garesu a ce sun yi wa Wansu aure

"wanda suka tara jama'a ba iyaka daga garuruwa, jahohi, ™asashe, amma a ce ™wanakin da ba su wuce arba'in ba aure ya rabu, alhalin muna ta™ama da cewa shi ne magajin Sarkinmu a nan gaba."

"Shi kuwa DurSi cewa ya yi anyi daidai da aka ja masu kunne aka tsorata su, amma maganar rabuwa ma"

"bata taso ba,a kira su dai a ™ara ba su lokaci, idan har ba su sasanta kansu ba, to sai a haWu da iyayen yarinya a ™ara tattaunawa, daga nan sai a nemi shawarar da ta fi cancanta, sannan yana mai baiwa Sarki shawarar ya je ya samu iyalinsa ya lalubi wani abu daga gare su na game da yaran, saboda su mata ne za"

su fi mu samun labarinsu.

*˜ASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 4

A nan dai suka tashi saboda ganin juma'a ce za'a fita Masallaci da wuri. Sarki ya shiga ya kira

"iyalansa,Mama Mariya ita ce mahaifiyar Yarima, sai kuwa Hajiya Kilishi wacce take mahaifiyarsu Ahmad ga ta amarya."

"Ya gaya masu shawarar da ya yanke a kansu Yarima, amma yana mai tambayarsu shawarar ya suka gani."

"Hajiya Kilishi ita ta fara magana,haba Shugaba ya za'a yi a ji irin wannan maganar daga bakinka, alhalin"

"ku ne manyan da ku ke yankewa ™anana hukunci,haba mai girma,ai ka san auran haWi dama ya gaji haka"

"kafin ma'auratan su saba. Ka tuna kanka mana,watana nawa a gidan nan ban saba ba, yanzu fa ka ga a sai mutuwa kawai ta rage mini a cikin gidanka."

"Ni a shawarata mai girma a sa masu ido, tun da an Wan tsorata su, balle ma yanda naga shi Yarima na"

"yawan zuwa gidan nan,a lokacin da aka dawo da

Please Login or Register in order to submit comment