You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juyawa na kalle shi ba, duk da dama"

jingine yake a jikin ™ofar shigowa ya harWe hannayensa saman ™irjinsa.

"""In kin gama ina sama."""

Ban amsa ba ni dai na ™agu in gama in koma in ™wanta.

"˜arfe sha biyu da mintuna goma na kammala komai, cikin tangarayen nan nasu na sarauta a ciki na haWa"

"masa haWin salat Win, na jera a wani ™yak™yawan faranti."

"Ina shiga Wakin nasa yana ™wance a ™asa kamar yanda na same shi da rana, na iso kusa da shi na ajiye"

"kayan, ya tashi zaune."

"""Za ki ci?"" Na girgiza kaina."

"""To na gode, shi kenan dama,mu je in rakaki."""

"Na mi™e na fara yin gaba, zuciyata ta cika dam da daWi. Ina tafe yana biye da ni har ™ofar gida ta ™asa, na"

juya na kalle shi.

"""Mu je in kai ki gida ko,ko ba™ya jin tsoro?"""

Ban dai samu yin magana ba.

"Yana bakin ™ofata ya dafa ta,ni kuwa ina daga cikin gida na ri™e ™ofar alamar zan rufe, ganin yana"

murmushi yasa na tsaya ina kallonsa.

"""Na gode Yasmin,sai da safe kin kawo mini karin kumallo (Break fast)."""

"""Nima ba ni nake yin karin kumallo ba, yi mini ake yi."""

"""Ina son ci haka nan."" Sai naga yana le™en bayana, na ga ya ™ara zare idanuwansa."

"""Me ye?"" Na tambaye shi da sauri."

"""Kamar wani abu ne tafe a bayanki."""

"Sai na yi saurin sakin ™ofa na fito da niyyar in waiga in ga ko meye, sai na ga ya yi ´ar dariya."

"""Ba komai zolayarki nake yi, saboda kin ™i yin fara'a."""

"Na Wan yi murmushin dole, na koma cikin gida, sannan ya juya ya tafi,ni kuwa na kasa rufe ™ofar da take"

"ri™e a hannuna, ina ta bin shi da kallon mamaki."

"Har sai da ya juyo ya Wago mini hannu, sannan na mayar da ™ofa na kulle da gudu na haye sama saboda"

"tsoro. Ina isa madadin in ™wanta sai na cire kayan saman rigar baccina, na buWe ™ofar gaban gidan na fita"

baranda na runtse idanuwana na ware hannayena duk biyun iska na Waukan gashina a hankali.

"Babu wanda ke zuciyata sai Anwar,son shi da ™aunarshi suka dawo mini sabo a wannan daren,shin ko dai"

dama yaudara ce Yarima ya yi mini yanzu gashi nan ya tunasar da ni masoyina. Na tuna wata rana da

"Anwar ya zo gidanmu zai tafi, na yi masa rakiya, har ya zauna kujerar motarsa sai na ga ya mi™e tsaye,"

"mamadin ya yi magana, sai na ga ya matso kusa da ni sosai."

"A hankali ya ce, ""Kalli ki ga yanda bishiyoyin nan ke rausayar jin daWi, saboda sun samu ni'imtaccen"

"wajen ™wanciya."""

"Ya kawo hancinsa gab da nawa, sai na ji ya ce, ""Haka muma wani daren za mu samu ni'imtaccen"

"ma™wanci."""

"Idanuwana a lumshe ina ji ya sumbaci wuyana, yanda tsigar jikina ta tashi a wancan lokacin, haka na ji ni"

a yanzu.

"Mamadin inji farin ciki, sai na ji lemar hawaye na gangaro mini,saboda tunaninmu ya zama mafarki,ko a"

"wane hali yake ciki yanzu? Tunanin da nake so in kawar a zuciyata,amma sai nema yake ya haye mini,wai"

tunanin Yariman da yake babban ma™iyina na yi tsaki a daidai lokacin da na tuno ni bayana ™wance a ™irjinsa.

"""Allah ya saka mini."" Na faWa tare da buWe idanuwana, na shige cikin gida, har na kama ™ofar gidan zan"

"rufe, sai na hango Yarima a barandarsa yasa hannuwa a aljihu yana kallon sama, na yi saurin mayar da"

"™ofata na kulle. Abin ka ga ™ofa mai gilashi ce, sai na Waga labulan na le™o yanda na barshi haka yake, na yi tsaki na wuce na yi ™wanciyata."

"Bacci zo mana, amma kamar an busar mini da idanuwana,ko me ye dalili? Oho, na mutstsuke idanuwana"

"tare da runtse su na yi lamo, amma babu alamar bacci a idanuwana. Ni kuma na kasa sanin me ya hana"

"ni yin sa,a zuciyata na ji ina so na ™ara le™awa in ga yarima ya shiga Wakinsa ko kuwa yana nan a tsaye."

"Shin dama haka yake yi ko kuwa yau ne kawai? Na mi™e na je na Waga labulan ™ofata,yana nan a tsaye,"

"amma yanzu ya Wan sunkuya ya dafa Wan abin barandar wato gilashi mai zagayen nan. TaSe baki na yi na koma, meye dalilinsa na ™urawa dakina idanuwa,ko yana nufin nima irin sa ce mai tsayuwar dare, haka na faWa gadona na tura kaina a ™ar™ashin filo, sannan na Wan samu nutsuwa."

˜arfe goma na safiya na samu na farka daga saman gadona. Baccin bayan sallar Asubahi da na samu na

"yi ta da ™yar, shi ma na san saboda kiran sallar masallacin cikin gidan shi yasa, wanda ake yin shi tamkar a ™ofar taga ta."

"Na samu tsayin awa Waya, sannan na fito falon ™asa,wayata da ke rataye a hannuna ita ce ta Wauki ™ara,"

"ina karawa a kunnena, sai na ji an ce."

"""Ina jiran Gimbiya in ta tashi,abincina nake son ci."" Sai a lokacin na tuna da ya ce yana cin abincin gidan"

"na safe, na taSe baki a lokacin da na isa Sangaren da nake yin karin kumallo."

"Su Musulma na zazzaune suna jirana, da sauri suka mi™e suka mi™a gaisuwarsu,a inda na zauna na"

"bubbuWe abin da su Asiya suka girka mini,kunun gyaWa ne mai Wauke da lafiyayyar madara, tare da"

"farfesun dagwargwajajjan naman kaza, wanda babu ™ashi ko Waya a jikinsa, gefe Waya kuma biredi ne wanda aka yi shi da faWi, tamkar an yayyankashi."

"Ban da kunun aya wanda mutumina ne,ni na ce kullum ina bu™atar a dinga yi mini shi, amma mai kaurin"

"gaske, cikin wata tangaran doguwa kuma tsire ne ya sha kayan haWinsa sai Waukan ido da hanci yake, gefe Waya kuwa sinasir ne shishshimfiWe a ™wanan tangaran."

"Na umarci su Mansura da su samo farantai su shirya su,su kai gidan Yarima su ce ga ni nan zuwa, haka"

"aka yi. Ina shiga na same shi a sashen cin abinci ya kishingiWa,siket da riga ne na atamfa ´ar Holand a"

"jikina, Winkin mai shaf ne (fitted), amma buWaWWan wuya da dogon hannu ne, sai mayafi ™arami da na"

lulluSe kaina da shi.

"Atamfar Koriya ce da Wishi-Wishin zane baki a jikinta, wanda takalma masu tsini ne a ™afata,su kuma"

"ba™a™e, haka mayafin saman kaina. Daga kishingiWan nan da yake bai tashi ba, har sai da na zauna tukunna ya tashi ya zauna."

"""Barka da Asuba."" Na ce masa."

"""Kin tashi lafiya?"""

"Na yi murmushi, ""ga ni kuwa kaga alama."""

"""Ya jikin naki?"""

"""Ya warware."""

"Na Wan yi shiru, ""Ka yi ha™uri don Allah na manta ne da tuni an kawo maka,ni kuma ban tashi da wuri"

"ba."""

"""Ba damuwa,ni ma ban daWe da tashi ba,yau da ™yar na je masallaci sallah saboda bacci, throughout jiya"

ban samu bacci ba na rasa abin da ya hana ni bacci.

"""Jin daWi."" Na bashi amsa. Ya yi Wan murmushi, ""ina fa jin daWi ga wanda ba shi da mata."" Ya faWa a"

"daidai lokacin da ya rage sautin muryarsa, na Wago kai muka haWa ido da shi, sai na ga ya yi murmushi tare da lumshe idanuwansa tare da buWe su."

"""Ko zaki amince ki zama matata,ki kawo mini jin daWin?"""

"Na girgiza kaina tare da mi™ewa tsaye. ""Zan tafi ni."" Na faWa, amma sai na tsinci kaina da canjawar murya."

"""Kayan abincin jiya na Waki,ko za ki fito da su,dama ni mai gata ne, da an gyara mini Wakin nawa yau Waya"

"dai."""

Ban ce masa komai ba na wuce abina.

"""Šinkin ya yi miki ™yau."" Na ji ya faWa a lokacin da na juya na tafi,a zuciyata na ce ka ™ari kinibibinka ni"

"dai ba zan taSa zama tare da kai ba,mayaudari,in ji da kunnena ka ce ba ka sona, sai yanzun don an hana"

"ka zuwa wajen ´a´an turawa, shi ne za ka dinga kashe mini muryar kinibibi. Na gangaro na ajiye kayan"

"kicin na yi gaba, zuwa gidana."

"An samu ™wanaki shida kenan yanayi mini ire-iren waWannan tsirfar, ban da kallo da yake bina da shi,"

"idan ina zaune a saman dutsen da nake hutawa, amma ko da wasa ban damu da abubuwan da yake yi ba, wani lokacin ma haushinsa nake ji, sai dai kuma abu Waya da ban gane shi ba, shi ne idan ina tare da shi"

"duk jikina sai ya yi sanyi,ko magana ba na son yi."

"Kuma idan na san yana waje a zaune, zan ga ina yawaitar kallon wajen,ko me ye haka kuma? Ni dai na"

"san ina yawan tunanin Anwar wanda nake ta mafarkin ya zama angona,shekaru huWu kenan, amma yau rana Waya mafarkina ya zama dirama."

"Na wayi gari da safe, ranar cikon kwanaki ta™was, wanda ya zamo daran jiya muna tare da Yarima har"

"™arfe Waya na dare,wai dole sai na tayashi hira,a irin zaman da muke yi ne a falo talabijin na ta aikin yin hidimominta, wanda hasken da ke fitowa ta jikinta shi ne kawai hasken falon saman da muke zaune."

Cikin mintuna biyar hankalinmu ya koma ga wani fim da suke yi wanda yaro da yarinyar fim Win suke

"zaune suna hirarsu, kamar dai mu sai naga yaron ya mi™e ya iso inda take zaune ya tsugunna daga nan ya yi mata wata magana wacce ta ™unshi aure."

"""Za ki aure ni, Please."" Sai na ga yarinyar ta Waga kanta tare da ri™e hannunsa ta tashi tsaye da sauri."

"Abin ka ga marasa kunya sai suka kama tsotsan bakin juna, ta wutsiyar ido na ga Yarima ya ™ura mini ido."

"Šan minti Wayan nan da na yi ina kallon Yarima ta wutsiyar ido, sai kawai na ji takun kiWan talabijin Win ya"

"canja kallon farko ban ™ara maimaitawa ba, na mi™e jikina na rawa ko sallama babu na sauko da saurina,"

"sai gidana. Ina isa gadona na faWa sai kuka. Anwar na dinga kira da ™arfi, saboda shi ne mutumin da yake ™wance a zuciyata."

"Ko da wasa ban yi zaton Yarima zai biyo bayana ba, asali ma ban ji ya shigo Wakina ba, sai dai jin an zauna"

"gefen gadona na ji anyi, na Wago da sauri,dama fitilar gefen gadona ™waya Waya ita ke kunne,ido muka haWa da shi."

"""Wa ye Anwar Yasmin? Ina ™o™arin in ga na mallaki zuciyarki da gangar jikinki gaba ki Waya, ashe duk ban"

"sani ba da wanda zuciyarki ke ™auna, na yi da na sani a yanzun da nine na fara sakar miki jikina, saboda samun ™wanciyar hankalin junanmu."""

"Ya mi™e tsaye yasa hannuwansa a aljihun wandonshi, wanda dama T.shirt ce a jikinsa, tsayuwar da ya yi"

"zata kai ta mintuna ta™was, sannan ya juya ya tafi. Tabbas ban ji daWi ba, ban kuma so a ce yajini ina ambaton sunan masoyina ba."

"_To masu karatu sai mun hadu a littafi na biyu, wanda tare suka fito._"

_Taku har kullum: Maryam Kabir Mashi_







*˜ASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 1

"˜wana na yi ina juyi gudun kada ya je ya sanar a gidanmu, saboda na ga alama ba shi da kunyar kai ™ara,"

tun da ya kai ™ara ta ga Aunty.

"Ganin an wayi gari lafiya, shi ne na yi wanka na saka kayana doguwar riga ce mai ruSi biyu, ´ar Saudiyya"

za mu iya kiranta ko Dubai. Na fito daga gidan ko Wankwali babu kaina na nufi bakin dutsen da nake hutawa na yi tsaye.

"Lokacin kuwa ya nuna ™arfe ta™was na safe kawai wanda na ce na yafewa su Mansura rakiyata,ko kalaci"

"ban tsaya yi ba. Ina tsaye nan ina ta sa™a abubuwan da na san ba zan samu ba,wato Yarima ya ji haushin"

"maganar jiya ya ce ya sauwa™e mini inje in auri Anwar, na Waga kaina jikin barandar Wakinsa, sai na hango shi zaune a kujera ya Wora ™afafunsa a saman tebir Win gabansa."

"Na juya abina, sai ma na tattaka na haye dutsen, tsayin minti sha biyar na yi sai na ji ina sha'awar shiga"

"™oramar nan,ta hanyar tattaka duwatsun da aka jera layi da su, waWanda suka yi cikin Wan dajin inda ruwa nan ke nufa,su kuwa duwatsun babu ruwanka da taSa ruwa idan dai har ka sa ™afarka a kansu."

"Nan take na saSule takalman da ke ™afata, na sulala cikin ruwan inda na dinga taka duwatsun a hankali,"

"na yi tsaye a wurin ina ta waiwaigawa sai na hango barandar Faysal,ai kuwa juyawar da zan yi ina tsaki,"

"sai na ga wani ™aton miciji ya nufo inda nake tsaye, ta cikin ruwan nan kanshi a buWe yana ta huci ban"

san lokacin da na yi baya da sauri ba ina ™walla ihu. Cikin ™an™anin lokaci ya tari gabana babu zancan iya

motsi a yanda na ga yana hucin.

"Runtse idanuwana na yi na dinga ™ara,tun ina ™arar har ya kaini ga kiran Yarima. Saman ™afata ya kai wa"

"sara, sai dai naji gab,na yi wata irin ™ara, na buWe idanuwana, sai kuwa na hango Yarima Faysal a guje shi da wasu a bayansa."

"Sai na dinga cewa, ""Maciji! Maciji!! Bai wani tsaya tattaka duwatsun nan ba sai dai kawai na ganshi da"

"gudu a cikin ruwan, wanda ganin da nake masa dishi-dishi ne, daga nan kuwa sai dai na dinga jin maganganun mutane sama-sama, sai kuwa ji na yi ana jijjiga ni da kiran sunana da nake jin ana yi."

"Ina jin ™asa na juyawa da ni, sannan ina ji sama-sama Yarima na daka masu tsawa zan iya cewa Waukata"

"ya yi cak ya koma gudu, amma daga nan ban ™ara sanin komai ba."

"A hankali na dinga motsa idanuwana,alamar ina son buWe su, ina cikin haka na ji Yarima na kiran sunana."

"""Yasmin! Yasmin!!"" Sai na ji yana dafa goshina."

"""Ta motsa?"" Na ji an tambaya."

"""Eh,tana motsa idanuwanta."""

"Na samu tsayin minti biyar a haka, amma na kasa buWe idanuwana, amma ina jin abin da ake faWa. Jin"

"abu mai sanyi a goshina, shi ya ™ara taimaka mini na ji hular idanuwana ta saki daga nauyin da ta yi mini, idanuwana Faysal suka fara gani zaune gefen gado,yana Wora mini abin nan mai sanyi da nake ji, sai na ga ya yi saurin jefar da shi ya Wago kaina ya rungume a ™irjinsa, ya yi wata irin ajiyar zuciya. Sannan na ji ya ce, ""Ta tashi."" Ya mayar da ni ya ™ara gyara mini ™wanciya,sannan ya sumbaci goshina, bayan nan"

"kuwa mutane suka dinga le™owa suna yi mini sannu, idanuwansu kuwa jajir kamar suna ciwon idon Afolo."

"Da WaiWaya duk na fara gane fuskokinsu, amma matan,mazan ban san kowa ba,gwara ma ´an na kusa da"

"shi da ba su fi Biyar ba, ´a´an Wakina kuwa har wannan lokacin kuka sukeyi."

"Bayan kamar minti sha biyar duk suka fita,a inda Yarima ya mi™e shi ma ya Wauki wayar hannu, ya fara"

daddannawa.

"""Barka da yamma,eh, yanzun za ta yi minti ashirin, Eh, tana gane mutane, a'a ban duba ba, to yanzun"

"zan duba. To sai kun zo,Mama da wuri don Allah yanzun ko, to zataji."" Ya juyo ya yi mini murmushi."

"Sannan na ga ya cigaba, ""Barka da yamma, eh, Yarima ne. Eh,Mamee, yanzu ta yi minti ashirin da Waya,a"

"cewa Daddy ya zo yanzun ta gan shi. To Mamee ai kamawa ta yi,to, to zataji, to sai kun iso, to a huta"

"lafiya, eh tana ™asa, eh, na san yanzun zata hayo,kin san ™wana biyu bacci ina jin bacci ne ya Wauke ta,a"

"Wakin ™asa, to za'a taso ta, mungode."""

"Ya dawo ya zauna gefena ya matso kusa da ni sosai, sannan yasa hannunsa ya shafa gashin kaina, ya ™ara"

"gyara mini gashina zuwa gefe, ""Sannu."" Ya ga dai ban amsa ba, sai na ga ya juyo sosai."

"""Yasmin,kina jina? Yasmin?"" Sai na Waga masa kai, sai na ga ya Wan mayar da numfashi tare da lumshe"

"idanuwa, ya yi saurin kai min sumbata a kumatuna."

"Ya tashi a hankali sai na ga ya buWe bargon da yake lulluSe da ™afa ta, sai a lokacin na tuna da cewa fa"

"Maciji ya sare ni, nayi ™o™arin motsa ™afar, na ji ta kamar dutse, ina kallo ya Waga ™afar tawa a hankali,"

yasa hannu ya Wan shafe ta.

"""˜afar ta mutu ko Yarima?"" Na faWa da muryata irin ta marasa lafiya."

"Ya rufe ya zagayo ya kama hannuna tare da zaunawa a gefena, wanda ™afarshi Waya ya Wago ta duka ya"

lan™washe ta har sai da gwiwarsa ma ta Wan hau saman cikina.

"""Bata mutu ba,za ki warke sosai ma."" Ya sumbaci hannun nawa,a take sai na ji tausayinsa ya kama ni."

"""A kawo miki abinci za ki iya ci?"" Na girgiza kai."

"""A'a,zaki Wan ci ko yaya ne,ko abu mai ruwa ne."" Ya mi™e."

"""Bari inyi miki burush(Brush)."""

"Da saurinsa ya fito daga banWaki da burushi na a hannunsa wanda saman shi ke cike da makilin, da ruwa"

"a ™aton kofi da wata silba a hannunsa, ya ajiye su gefen gado, sannan ya hayo gadon gaba Wayansa, ya"

"Waga ni ya jera filallika guda uku a bayana, na Wago sosai, ya janye bargon jikina ya mayar da shi iya"

"™uguna, ya gyara shi sosai, sannan ya sauka ya Wauko kayan ya Wora silbar a cinyata."

"Ya kanga mini kofin a bakina, ""Kuskure bakin tukunna."" Na kurSa, ya yi saurin ajiye ruwan a durowar"

"gefen gadon, sannan ya Wago silbar."

"""Zuba a nan."" Na zuba sai na ga jajawur yawun bakina, ga Woyi yana yi, kunya ta kamani, amma na ga shi"

"bai nuna alamar ™yan™yamina ba, ya ™ara bani ruwan na kurSa, na ™ara kuskurewa ya Wago na juye."

"Ya Wauko burushin na Wago hannuna na ri™e, ""Zan iya."""

"""A'a, kada ki wahala fa."""

"Bazan wahala ba."""

"Ya ™ura mini idanuwa,sai ya lumshe su tare da yin murmushinsa, ya buWe idanuwan tare da girgiza kai."

"""No Yasmin, jikinki ba ™arfi, ki yi ha™uri in kula da ke har ki warke,kina ga ya dace in bar yaran can su"

"dinga kula da ke, alhalin ™asa suke da ni, amma su ga wani Sangare na sirrin matata? No,no,is not possible."""

"""Wallahi zan iya."""

Ya mi™o mini burushin.

"""Na amince da ke."""

"A hankali na dinga gogawa, saboda jikina babu ™arfi sosai, amma duk da haka sai da naji na gaji sai da na"

"Wan tsaya hutawa, ya yi murmushi ya karSa ya ™arasa mini."

"""Ya sunan Waya daga cikin yaran gidanki?"""

"""Mansura ko Muslum."""

"Ya mi™e da hanzari ya ajiye kayan a ™asa ya le™a barandar cikin falo, ya kira Mansura, da gudu ta hayo,a"

inda shi kuma ya dawo ya zauna.

"Ya umarce ta da ta Wauko masa mango juice a firji,ta tafi cikin saurinta, shi kuma ya shiga banWaki da"

kayan ™azantar wanke bakina a hannunsa.

"Ko fitowa bai yi ba, sai ga Aunty ta ce, ""Lah! Ina Yarima, bari in gaya masa kin tashi."""

"Sai ga shi ya fito. ""Ta tashi?"""

"""Ta Wan jima, abin da yasa ban ce a taso ki ba,ganin kin samu bacci shi yasa."""

Ta iso ta zauna gefen gado.

"""Ya jiki Yasmin?"""

"""Da sau™i."""

"Nan suka ci gaba da zama ita da Yarima, har sai da ya ga nasha mango juice Win nan sannan Aunty ta"

"matsanta masa da ya je ya yi koda wanka ne, da ™yar ya amince."

"Bai fi mintuna goma da tafiya ba, sai ga Mama ta iso, cewa take, ""Barkanmu, barkanmu Yasmin,tare da"

"Sarki muke yana ™asa,kin san abun mata, shi ne na hayo in ga yanda ku ke tukunna."" Ta juya ta yi baya,"

sai ga su sun shigo tare da Sarki tun da ya shigo na ga fuskarsa cike da walwala.

"Sarki ne har gefen gadona,yana ta jinjina abin da ya faru, Mama ta Waga bargon da suka lulluSe ™afata,"

suka kalli ™afar.

"""She will be alright."" Sai ga yarima da saurinsa. Doguwar riga ce a jikinsa har ™asa ta ´an Saudiyya, wacce"

ta sha aiki tun daga samanta har ™asa da wandonta da hula kalar ruwan madara da takalman ™afarshi

kalar hular.

"Yana shigowa ya zauna har ™asa ya gaishe da Sarki, da mahaifiyarsa,yana sunkuyar da kai irin na"

"girmamawa, amma sai na ga Sarki ya Wan Waure fuska,Yarima na Wagowa, sai na ga ya yi mini"

"™yau,wanda ban taSa gani ba a fuskarshi, na ™ara kallonsa, sai na ga fuskarshi tana ™ara she™i. Na juyar"

"da fuskata gefe, saboda tunanin ko shaiWan ne ya ™ara ™ayata mini fuskarsa."

"Ranar kam naga jama'a, sai yiwa Yarima barka ake yi, madadin a yi mini. Su Mamee ma da aka zo,ai ta"

"Yarima ake yi bata ni ba,ni kuwa madadin inji yana ba ni haushi kamar baya, sai na ji ina jin daWi yadda"

"yake nuna ai ya shiga tashin hankali, a inda yake baiwa masu zuwa labarin ™wanana biyu kenan da suma"

haka ban farfaWo ba sai yau.

"Anan na samu labarin ashe har ™wanaki na yi a ™wance,lallai dole bakina ya yi Woyi. ˜wanana huWu a"

"™wancan nan, amma duk wata kulawa da ake nema, tabbas Yarima na ba ni ita, har ma wacce ta fita,a"

inda tunda ™wana biyu ya ce Aunty ta tafi gidanta ta ™wana ta ji da yaranta.

"Tun ban Waukar abin da Yarima ke mini da sunan so, har zuciyata ta amince lallai ya kamu da ciwon sona,"

"ciwon da na lura ya riga ya yi masa katanga a zuciya,ni dai bana cewa ina son Yarima, amma tsanar da nake nuna masa a baya, yanzun bana iya yi masa ita."

"Da la'asar wacce ta cika ™wana huWun sai ga Mama, bayan gaisawarmu ne, na ga sun fita falon sama da"

"yake labulan shara-shara ne tsakanin ™ofata da falon, shi ya bani damar ganin abin da ke faruwa a"

tsakanin Yarima da Mama.

"Shi ne na ga ya dur™usa ™asa yana yi mata magana, amma bana jin maganar, sun Wan Wauki mintuna sha"

biyar sannan ya shigo.

"""Yasmin can gida zan tafi da ke domin yi miki magani sosai,kin ga can an fi samun magani,a yanzun haka"

"ma Sarki ya tura a Wauko wani mai magani a ™auyen Bukuru."""

"Na washe baki alamar na ji daWin maganar da ta faWa, amma sai na ji jikina kamar bai amince ba, sai dai"

"kuma ba zancen gardama a tsakaninmu,Waga kaina da nayi na hango Yarima jingine a jikin bangon shigowa Wakina, shi yasa na ji tausayinsa ya kama ni. Ya iso wajen Mama jiki a sanyaye, ya dur™usa ™asa ya kama hannuwanta."

"""Mama, wallahi ina kulawa da ita,ki tambaye ta ki ji, Yasmin ba ina kulawa da ke ba? Mama a nan fa"

"nake ™wana a wajenta, Mama ki bar ta wallahi zan kula da ita sosai, zan fi dama."""

"""Wai kai meye na damun kanka ne a kanta, kai ka ce mini baka son """

"""Mama kada ki faWa, wannan a da ne,shin ba cewa na yi ™wata-™wata ba."""

"""Ka ga an gama magana, sai dai ka yi ha™uri."""

Ta juya ta kalleni.

"""Zan tafi da ke yanzun,su wa za'a kira su shirya miki kayanki?"""

"""Mansura."" Na bata amsa."

"Ta kalleshi, ""Kirawo Mansura a falo babba."" Ya ce to, ya mi™e ya tafi."

"Saman kujera doguwa yake zaune a babban falo, ya ™wanta jikinta sosai, da gani ka san cikin damuwa"

"yake, ya Wago ya kalleni a daidai lokacin da ake saukowa da ni sai na ga ya yi murmushi."

"""Ina nan zuwa anjima."" Haka kawai ya faWa,mu kuwa muka wuce."

"**** **** ***"""

"Lallai kam na ga gata, na tabbatar da cewa iyayen mijina na ™aunar Wan su, shi yasa ™aunar ta shafe ni,a"

"nan na ™ara yarda da cewa sarauta abin ™auna ce, ga wanda bai shige ta ba ne yake ganin tamkar aikin"

bauta ake a cikinta.

"Yanzun kam ni da kaina zuciyata da sauran jikina suna ™aunar sarauta, saboda ganin yanda take tafiya"

cikin tsari da nunawa jama'a ™auna ta gaske. A wannan zaman ne ma na san wa ye Yarima da iyayensa.

**** **** ****

"Yarima fari ne,™yak™yawan gaske wanda dirin jikinsa na cikakken namijin da ya amsa sunansa, wanda"

"gashin bakin fuskarsa ya ™ara ™awata fuskar tasa, amma shi farin shi ja ne, tamkar na Turawa,"

"idanuwansa kuwa sun Wan yi girma kaWan, tamkar na Salman Khan Wan ™asar Indiya."

"Sai dai shi zamu iya kiran ™irar jikinsa irin ta Turawa, da ganinsa dai ka ga (Handsome). Tabbas ya"

"cancanci sunansa, wato FAYSAL."

"Su biyar ne kaWai ´a´an Sarki. Yarima shi ne babba, sai ™annansa huWu, amma mace ke bi masa Salimat,"

"ita ce matar Wan Sarkin Wasai, wato ™aramar hukuma ce a Jos,sunan mai bi mata Idris,saurayi ne yana karatu a London, sai Sauda wacce take aure a Mina,sai autansu Ahmad. Yarima za a iya kiransa Wan shekara talatin da biyar, ya yi karatunsa ne a Greece tun yana Wan Sakandire aka kai shi ya karanci hulWa"

da jama'a Public Relations.

"Ba wai domin ya yi aiki ba, a'a don dai ya iya zama da jama'a da ri™e gari, idan ya zamana ya hau mulki."

"Matan Sarki biyu ne, amma mahaifiyarsu Yarima Hajiya Mariya, ita ta haifesu su uku, shi da ™annansa, da"

"Idris da Salimat, amma Sauda ´ar Wakin Hajiya Khilishi ce ita da Ahmad wanda yanzu yake makarantar gaba da Primary."

*˜ASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 2

"Ko a ido ka ga yanda ake wa Yarima,ka san ana ji da shi, sannan kuma sam ba ka gane cewa ba Wakinsu"

"Waya da ragowar ™annansa ba,ni kaina sai da na zauna gidan sannan na gane da kaina."

"Amma Mama ta ce mini, Yarima ba shi ne Wan Sarki na farko ba,yana da yayyansa biyu mace ce babbar"

"gidan ™wata-™wata Hajiya Asabe, sai ™annanta Abdul Rahman, amma tun

Please Login or Register in order to submit comment