You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ran Sarki,a wancan zamanin,kin san kowacce"

"masarauta a wancan zamanin da irin hikimar da ake amfani domin fitar da Magaji,wato wanda zai gaji sarauta. A zamanin da zaki ga wata masarautar su kan sa yaransu su yi tafiya mai nisa domin Wauko wani abu ko samo wani abu. To su kuwa wannan masarautar ta haka suke ganewa. Ina son ki yi murna kuma"

ki godewa Allah da yasa ki ka samu kanki a wannan matsayi.

*˜ASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 10

"Tsaya in baki wani labarin da ba wanda ya san shi daga ni sai Mai Martaba, sai kuwa ita wacce abin ya"

sama sai kuwa Allah.

"Kin ga wannan abin da ya faru da ke a yau, to shi ne ya haddasa tsana mai tsanani tsakanin Sarki da"

"matarsa ta farko, Hajiya uwarsu Abdulrahman, da na taSa ba ki labarinta. Mai martaba ya bani labari cewa, lokacin da aka kawo ta tana amarya ita ce ta dinga nuna masa ya zo gareta,kin san yanda auran"

"sarauta yake da wuya a bar ka ka auri wacce ka ke so, sai dai a zaSa maka."

"To wannan ne yasa ba so a tsakaninsu, lokacin wata ´ar barga yake so, wato irin ´a´an masu aikin"

"gidansu, aka hana shi auranta aka aura masa Hajiya Asabe. Ranar da Allah yasa za su haWu da ita a matsayin miji da mata, sai ga shi ya sameta ba yanda ake so ba, wato ta taSa sanin wani bayan shi."

"Tun a daren ya kira jakadiya ya sanar da ita, jakadiya ita ta kawo shawarar a samo kaza a yanka ta,jininta"

"a zuba shi a shinfiWarsu, wannan dabara ita aka yi, balle a wancan lokacin jakadiyarsa mai himma ce da wayo, ita ta yi masa wannan dabarar har ya samu ya haye a matsayin zai gaji sarauta."

"Tun daga wannan lokacin ya tsani Hajiya Asabe, har ya zama yana zarginta da fita waje in ta fita unguwa."

"Ke a ™arshe dai sai da suka rabu hankalinsa ya ™wanta. Ke ki godewa Allah ko in ce mu godewa Allah, wallahi ni ma nan da ki ka gani sai da aka yi mini wannan taron,ki yi ha™uri ki zauna da mijinki lafiya. Mu"

"dama tuni abin da muke son ji kenan, saboda duk wani masoyin Yarima zai so a ce ya ji wannan ranar, ta"

zo kuma yanda ake son ta.

"To ni zan koma sai kun zo mana sallama ko, Allah ya yi muku albarka, kira shi ki ce ni zan koma."""

"Abin ka da falon sama muke dama sai kawai na shiga Waki, ina shiga ya Wago kai ya kalleni daga inda yake"

"™wance,bai tashi ba har na iso gabansa."

"""Mama na kira."" Na samu na faWa,a inda na juya na koma wajenta."

"Sallama kawai ta yi da mu ta yi tafiyarta,iyakata bakin ™ofar falo, Yarima kuwa shi ne Wan doguwar rakiya."

"Kafin Yarima ya dawo ni kuwa har na saka rigar baccina na haye gadona, saboda ba zan iya cigaba da haWa ido da Yarima ba. Ina kallon shigowarsa, ta ™yallin idona Waya, ya zo ya tsaya a gabana kallona kawai ya dinga yi yana murmushi."

"Ya yi tsayin mintuna biyu a haka, sannan ya shige ciki, kenan ya koma ta bayana,ni ga shi babu damar in"

juya in kalli me zai yi ba. Ina jin shi ya shigo cikin bargon da nake ™udundune sannan ya hayo ta saman

jikina ya Wauki makunnin kashe fitilar Wakin.

"Me ya manta? Na faWa a zuciyata, saboda jin ya sauka daga saman gadona,™yallin idona Waya na ™ara"

"buWewa a nan ne na ga ya isa ga ™ofa yasa makullintaa ya kulle, cikin bargon ya koma tare da kashe fitilar Wakin gaba Wayanta, ina jin shi ya zare Wan abun Wane gashin da na sa na Waure gashina (band) cikin"

"ruwan sanyi na saukar da ajiyar zuciya jin ya sumbaci bayana, tare da rungume ni jikinsa ta bayana."

"""Na san kina ji na ki kayi shiru, because you hate me Yasmin,har abada ba zan taSa yaudarar ki"

"ba,sona,™aunata, mulkina,˜ASAITA, duk naki ne,in har babu ke a tare da ni na san zan iya zama ba ko Waya a cikin abubuwan da na lissafa,ni na san ˜ASAITa ta biya ni, tunda ta hana mata da yawa yi wa"

rayuwata katsalandan.

"Ki yi tunani, da ni mutum ne mai sakin fuska da mata nawa ne zasu dinga neman cin fuskarki, saboda"

"suna kishi da ke. Ke kaWai na fara sakarwa fuskata, da jikina baki Waya, kuma na yi imanin ke ce ™arshe."

"Please Yasmin ki saki jiki da ni saboda ke special ce a gare ni, kamar yanda sunanki ya ke special a wajen"

jama'a.

"Ki so ni,zaki sameni mai sau™in kai, komai ki kaga na yi na mulki a baya, saboda tsare mutuncin kaina"

"ne."""

Ya kama ni ya juyo ni a jikinsa sosai kumatuna ne ya ™wanta a ™irjinsa ya yi Wan saurin Wago kaina na san

dalilin Waga ni haka.

"""What? What? Yasmin, still you hate me."" Na koma na ™wanta a ™irjinsa mai ni'imtaccen gashi, ina jinsa"

ya yi ajiyar zuciya ya ™ara rungume ni gam a jikinsa.

"Gashin kaina yasa hannu yana Wan shafa shi a fuskata, ban iya buWe idanuwana ba, amma nasa hannuna"

na ri™o gashin tare da yin murmushina.

"""Zan je sallah ne masallaci ki tashi ki yi taki sallar, saboda yau zamu Wan fita zuwa wani Wan lokaci, amma"

"™asar Greece za mu fara zuwa,a can nayi karatuna, sai in nuna miki wuraren dana sani, ragowar ™asashe"

"uku ke ce za ki zaSa."""

"""Ni ba zan je ba."""

"Ya sa ha™oranshi ya cije laSSana duk biyun, har sai da na Wan yi ™ara kaWan, na samu na ™wace na cusa"

fuskata a ™irjinsa.

"""Zane ki zan yi da tsintsiyar ™wa™wa na ga alama."""

"Nasa yatsuna na Wan ja gashin da ke ™wance a ™irjinsa, yasa ™ara kaWan tare da ´ar kokawar ™wace"

jikinsa ya mirgina ya tashi yana dariya ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna.

"""Zan rama ne, gudu nake kada na makara da kin faWa."""

"Ni kuwa na ™udundune kaina a filo, ina ´ar dariyar murmushi ina jin shi har ya kammala alwalla ya fito"

"daga banWaki, saboda jan faWa har da buWe ™afata ya yayyafa mini ruwa."

"""Tashi."""

Na yi saurin jan ™afata shi kuwa ina jin dariyarsa a hankali har ya fice daga Wakin. Fitarsa zan iya cewa

"jinkirin minti Waya na yi na mi™e da tsallen murna, na sauka daga gadona, jin ™uguna ya Wan amsa, shi ya tuna mini ashe fa ba na jin daWin jikina, na yi murmushi na shige banWaki tare da tunanin na zama ta Yarima Faisal."

**** **** *****

"˜asar Greece,nan muka sauka FIVE STAR HOTEL,shi ne masaukinmu, wanda Wakinmu shi ne Waki na Wari"

"da goma sha biyu (112) , ya kama kuma hawa na uku kenan. Bai fi mintuna biyar ba da shigowar mu"

"Wakin ba wata ´ar ™ararrawa ta kaWa cikin sauri na ga Yarima ya fita falon da muka baro,mu kuwa muna"

Waki Yarima na Wan shirya mana kayanmu.

"Jin an Wauki ´an mintuna yasa na fito falon da Wan saurina, fararan mutane ne biyu Turawa, sanye da"

"farar rigar shirt da bulu Win wando, sai ba™a™en takalma a ™afarsu, wannan ne ya nuna mini alamun su"

ne ma'aikatan hotel Win da muka sauka.

"Baki Wayan hankalinsu ya dawo gare ni,ni kaina sai na ji kunya ta kama ni kallon da na ga suna yi mini,"

cikin Wan ™an™anin lokaci Yarima ya nufo inda nake.

"""Shiga ciki."" Ya faWa a daidai lokacin da ya iso gareni. Na shiga ciki ina Wan murmushina na mamakin"

yanda Yarima ya nuna kishinsa a fili.

"Wajen yammarsu, wacce a tamu yamman za mu iya kiranta ™arfe biyar da wasu mintuna na yamma. A"

"lokacin ne muka gama komai muna zaune a falonmu mu dai ga mu nan, ba ka cewa ™iyayya ba kuma za"

"ka kira mu masoya ba, tunda kowa a kujerarsa yake a zaune,ni zan iya cewa kishingiWe nake a tawa kujerar duk maganar da ya yi idan ta amsa ce in bashi amsarta,in naji zan iya."

"Ana cikin haka hankalina ya kai ga talabijin Win da ke ta aiki ita kaWai, na yi saurin tashi zaune har da Wan"

salatina.

"""Me ye?"" Ya tambaye ni."

"Har sai na ji na Wan ji kunya, ""Wa ye wannan? Šan uwanku ne?"""

"""A'a. Ya naga kina ta murnar ganinsa?"" ""Šan wasa ne na finafinan Indiya."" Ya gyara zama sosai."

"""Ya sunansa?"""

"Na ce, ""Sharukhan."""

"""Haka nan ki ke son ganinsa?"""

"""Ina bala'in son shi ne, ya iya acting."""

"""Me kika ce?"""

"""Cewa na yi ina son shi."""

Ya yi murmushi mai fitar da sauti.

"""Ko wajensa za ki koma?"""

"Nan take na juyo na kalli fuskarshi,ko kallona ma bai yi ba, balle ya bani wata amsa, na mi™e na nufi cikin"

"Wakina na ™wanta,bai fi mintuna sha biyar ba sai gashi ya shigo, ya iso ya zauna gefena."

"""Ban fahimci abin da ki ke nufi da tasowa ki ™wanta ba, daga na yi miki maganar mutumin da ba"

"muharramin ki ba?"" Ya juyo sosai ya sumbaci kumatuna."

"""Ki yi ha™uri in kin ji ba daWi."" Na Wan yi murmushi."

"""Ban ji komai ba, na dai zo na ™wanta ne kawai."""

"""To taso mu sauka ™asa ki ga mutane kafin gobe in kai ki wurare da dama waWanda na sani."""

"Na yi murmushi na tashi zaune, da niyyar in tashi mu tafi, ya ri™e hannuna."

"""Kisa doguwar suit Winki,saboda jama'a."""

"Yau ™wananmu huWu a ™asar Greece,a ™wanakin ukun da muka fara fita ba inda Yarima bai kai ni ba,"

"wuraren wasansu na yara, amma su manya ma na zuwa,a nan ma ya ga na fara sakin jiki da shi, balle da aka Wora ni wata mota mai sa jiri ina saukowa na kasa tafiya, sai dai Yarima ne ya ™wantar da ni saman"

kafaWarsa muka samu wajen zama yana yi mini dariya.

"Wani abin burgewa irin na ™asar Turawa, shi ne ba wanda ya damu da abin da ka ke ciki, balle a tsaya"

"kallonka, shi kansa Yarima sai yanzun na ™ara gane cewa dogarawan da ke bin shi a baya suke ™ara masa"

"girman kai, amma yanzun ba ki gane shi ko Wan waye."

A ™wanakin nan huWu kuwa ba wata alama da Yarima ya nuna mini sai ma Wan tilasta ni in yawaita shiga

"ruwan Wumi cikin hikima irin tasa. Tabbas Yarima na sona,ni kaina na amince da hakan,ni kuwa zuciyata"

"har yanzun tana ba™unta da shi, shi ne ta kasa tsayawa ta saki jikinta da shi, har ta gano irin son da take"

yi masa.

"Yanda nake ™wance a gadon da ke bakin ramin wanka,in ka hango ni ba ni da maraba da Turawa, saboda"

"kayan jikina,siket ne ba™i da farar riga a jikina, wanda gilashi ne manne a idanuwana, irin Waurin Wan™walin Turawa nima shi na yi, shi ne ka Waure gefe-gefe amma tsakiya a baje saman baya."

"Kaina ™wance yake gefe, ina kallon cikin ramin wankan,babu inda idanuwana suke sai kan Yarima da ke"

"ta wasan wanka a cikin ruwan, duk da duk Wan lokaci ya zo bakin ruwan ya Wan watso mini shi kaWan,in"

"Wan yi ´ar ™arar ™issa, shi kuwa ya yi ´ar dariya ya ™ara komawa sosai cikin ruwan."

"Ganin inda ya nutsa kansa ya tsaya cak ruwan baya motsi irin ana wanka da shi, shi yasa na Wan Waga"

"kaina sosai ko zan ™ara hango shi, amma ba na ganin sa ko kaWan, cikin sakan Waya sai na ji kamar kaina"

"ya sara, irin na tashin hankalin nan, ban san lokacin da na mi™e tsaye ba, isowa na yi bakin ruwan na"

"tsugunna duk gwiwa biyu ina jira,in ga Wagowar Yarima."

"Tun ina ganin kamar wasa, har na ga ya ™washe mintuna,nan take na ji kamar kaina ya fara juyawa, na"

"waiga ban hango wani wanda ya yi kama da Wan Afrika ba, ballantana in kirawo shi, abin ka ga ™asar"

"Turawa, kowa da tashi hidimar ba ma wanda hankalinsa yake a kaina."

"Juyowar da zan yi sai na hango Yarima ™wance saman ruwa, amma ta bayansa kenan kanshi da cikinsa"

"duk a ruwan suke, na mi™e tsaye na yi kamar in yi ihu, to wa zan yi wa,ni kuwa dalilina na ™ara ruWewa a"

irin ´an fina-finan da nake kallo na san in an ga mutum a saman ruwa to ya mutu kenan.

Ganin ba zan iya zuwa cikin hotel Win ba in kira ma'aikatan yasa na ji wani ™arfi ya zo mini ban san lokacin

"da na shiga cikin ruwan nan ba sai dai gani na nayi ina kokawa da gangar jikin Yarima,manufata in juyo fuskarshi ta kalleni ta hakan zan gane ko yana da rai."

"Duk cikin mintin da bai wuce Waya ba na yi haka,babu wani alamar rai a jikin Yarima a lokacin da na juyo"

"shi nan take na ji zazzafan gumi na tsiyayo mini ta saman gashina, ban da mugayen hawayen da ke"

shatata ba tare da an rera masu wa™ar kuka ba.

"˜arfi na ji ya ™ara zo mini cikin rawar jiki na ji na janyo shi zuwa bakin ruwan, sannan na yi ta maza na"

"Wora shi saman gefen ruwan, da rawar jikina na zagaya na fita daga ruwan. Sannan na janyo shi."

*˜ASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 11

"Amma ina namiji ba mace ba sai ma ya ™ara komawa cikin ruwan nan, take na sa ™ara mai tsanani, na"

"ruga a guje ina cewa a taimaka mini da harshen Turanci, ma'ana."

"""Please help me! Help me!! "

"Nan da nan aka zagaye shi ni kuwa gani nake duk ba su isa ba, tunda ba ma'aikatan hotel Win, da gudu na"

"isa falon da ake fara karSar ba™i (Reception) da harshen Turanci na yi masu bayani, kafin minti biyu har sun riga ni isa inda yake, ina isa na cakume shi, cewa nake, ""Yarima ka tashi! Tashi!!... har sai da suka Wan ri™e ni, sannan aka danna ™irjinsa da cikinsa sai ruwa ya Wan fito ta bakinsa."

"Na fizge na zo na ™ara kama shi,a ta™aice dai ban ™ara sanin abubuwan da na dinga faWa ba har aka kawo"

"Wan wani gado aka Wora shi, sannan aka tambaye ni lambar Wakinmu da ™yar na iya faWa,saman gado aka ™wantar da shi na warware bargo na rufa masa, sannan na ga an yi masa wata allura a jijiya, cikin sakan biyu na ji ya yi wani tari, na ™ara ri™e hannunsa gam, cewa nake."

"""Tashi! Tashi!! Tashi!!! Yarima kada ka mutu."""

"Sun gaya mini da harshen Turanci, zai tashi amma in dinga murza tafin hannunsa, da ™yar na amsa da to."

"Sannan duk suka fita na kuwa dage goga hannuwansa duk biyun in na yi wa Waya in saki in kama Waya,kai sai gani har da busa bakinsa,ni sam na ma manta da wani haWa baki muke yi da shi, wani ihu bayan hari zan ce, saboda wai sai a yanzun na ji ina mugun son Yarima, amma kuma ga shi a saman gado ya zame"

min ™ila wa ™ala.

"Na samu wajen minti talatin a haka, wanda hakan yasa na ji na karaya, sai kawai na ™wanta saman"

"™irjinsa na dinga kuka. Kuka mai tsananin gaske, amma ba wanda ake ihu ba, wanda gangar jikinka duka ke motsawa."

Sama da mintuna ashirin ina haka wanda tuni har tunanina ya bani in bugawa Aunty waya in ce a zo a

tafi da mu. Hannu na ji an sa an shafi gashin kaina Wan motsi da numfashi su suka sa na yi saurin Waga

"kaina saboda in ga mai taSa mini gashina. Yarima ne ke kallona yana murmushi, na yi wata sassanyar ajiyar zuciya na dinga murmushin daWi don ma ina jin kunyarsa da tuni na yi tsalle."

Na tashi da sauri na dawo saman gadon na faWa jikinsa ya mayar da hannuwansa ya rungume ni ina jin

"shi yana ta shafa gashin kaina, alamar lallashi ina jinsa yana ™o™arin ya Wago ni amma na rungume shi tamau, ina jinsa ya faWi kalmomin nan da harshen Turanci."

"""Yasmin do you love me now? Zaki iya sakin jiki da ni?"""

Na Waga kaina wanda ke ™wance a tsokar naman kafaWarsa.

"Tabbas murnar Yarima ta fito fili,dana amsa masa ina son shi, ya Wauke ni baki Waya ya Wora ni a gadon"

"da yake ™wance, ya mayar da ni ya ™wantar a ™irjinsa ya janyo bargo ya lulluSe mu a ciki, fuskokinmu kawai ke waje, na Wago na ce masa."

"""Ka samu sau™i?"""

"Ya yi murmushin da yasa na ji sabuwar kunyarsa ta dirar mini sannan ya Waga kai alamar eh, wanda jin"

Waga kan kawai nayi saboda ni tuni na mayar da kaina a ™irjinsa na ™wantar.

"Lallai yanzu zuciyata da gangar jikina sun amince mini da ina son Yarima,su ma kansu son Yarima ya cika"

"su dama. Na yi sauri na Wan yi alamar zan tashi ya ru™o gashina ta bayana, na juyo da sauri har da ´ar ™ara da ido da kai ya tambaye ni ina zani? Na sunkuyar da kaina ina murmushin da yake fita tare da ´an ragowar hawayen idanuwana."

"""Magani zan Wauko maka, likita ne ya ce da ka tashi na baka."""

"Da kai ya nuna mini cewa inje na Wauko, ina murmushin mamaki na cikin zuciya kenan bai fito fili ba,"

saboda mamakin yanda Yarima ya ™ware da maganar kai ko da yake ba mamaki idan na yi la'akari da

farkon haWuwata da shi yanda ya yi wa dogarawansa magana da gilashin hannunsa.

Bayan na kama shi ya tashi zaune na taimaka masa na jingina shi jikin kan gado wanda nasa filo a

"bayansa sannan na zauna kusa da shi na mi™a masa maganin da ruwa a kofi, maganin ™waya Waya ne Wan ™arami, sannan na ™ara janyo kujerar da na Wora Wan farantin da kofin maganin na ajiye kofin sannan na"

mi™a masa kofin ruwan madara ya shanye.

"Saboda magriba ta kawo jiki,in na yi la'akari kamar a ce ™arfe shida na Nigeriya kenan, wannan yasa na"

"ce ya yi ™o™ari ya je ya shiga ruwan Wumi a banWaki ko ya samu ™arfin jikinsa sosai,bai yi mini gardama ba ya mi™e abinka ga namiji sai na ga baya ko irin Wan tangaWin nan na marasa lafiya."

"Ina zaune ni kuwa na rabka uban tagumi a gefen gado ina jiran ya fito, wanda tuni na tafi duniyar"

"tunanina, na da Yarima ya mutu da ya zan yi? Ba don komai ba sai don yanda zuciyata ta fara nutsuwa wajen son zama da shi a matsayin mijin aurena,wai don shirme sai na ji hawaye sun taho na samu na lumshe idanuwana su kuwa suka ci gaba da gangarowa."

"Ban ji fitowarsa ba, saboda idanuwana a lumshe suke, kuma linzamin tunanina ya canja salo ya koma"

"tunanin abubuwan son da Yarima ya nuna min a fili, na tuna ranar da ya mallake ni a matsayin matarsa"

irin nuna so da ™aunar da ya yi mini a wannan daren ™waya Waya cal.

"Jin an sumbaci laSSan bakina shi yasa na dawo daga duniyar tunanin da na tafi, na buWe lumsassun"

"idanuwana sai na ga Yarima tsaye a kaina, na yi saurin ™wantar da kaina a cinyata na ce, ""Kai Yarima."""

"Cikin kunnena ya ce, ""Ke Yasmin me ye.?"""

"Na Waga Wanyatsa na nuna shi, ""Me ye,tawul, Yasmin sai in ™i Wauro tawul ni da matata ni ne fa kawai a"

"Wakin"""

"Da jin yanda sautin maganar ke fita ka san Yarima bai saba da yawan magana ba, saboda cikin nutsuwa"

yake yin ta.

"""Ki Wago Yasmin na zama naki fa."""

Na girgiza kaina.

"""Sai kasa riga."""

"Ina jin sa ya zauna dab da ni tabbas na ji sunkuyowarsa daidai da kunnena, saboda jin hucin numfashinsa,"

"madadin ya yi magana sai dai kawai na ji ya hura kunnena,tsigar naman jikina na ji ta yamutsa, na rasa ya"

zan yi sai dai kawai na koma gado na ™wanta a ™udundune.

"HaWani ya yi ya rungume a ™irjinsa, amma ta bayana, kalaman da suke fita daga bakinsa su suka sakani"

"na ji Wakin na juyawa da gadon da nake ™wance, jin ya ™ara hura mini saitin ™ofar kunnena yasa na mirgina Waya kusa da shi na samu na mi™e na gudu, na shiga banWaki, saboda na san nan kaWai ne in na shiga na tsira, shi ma idan na kulle saboda ™aton falo ne da Waki Waya kawai su ne Wakunan hotel Win."

"Na kulle ™ofar, amma sai na ji na jingina da ita tare da sulalewa ™asa na zauna, kai sai na ji ina jin kunya"

"ni kaWai a banWaki, na ™udundune kaina jikin cinyata, na dinga murmushin da zan iya kiranshi na daWi,wai don tsananin shirme irin nawa da na Waga fuskata sai in mayar wai kunya nake ji."

"Sai da na ™washi wajen mintuna sha uku a haka, sannan na yi sauri na mi™e tsaye saboda tunanin da na ji"

"ya faWo mini a take,shi ne sallah na san bai fi sauran mintuna a kira sallah ba,ko kuwa in ce lokacin sallah ya yi tun da garin arnaku muke balle mu samu kunnuwanmu da jin kiran Sallah."

Na saSule kayan dukkansu a gaban ™aton madubinsu na banWaki na kalli kaina tas na yi murmushi ganin

"ba ni da ko ™wantalan ™urji a dukkan jikina ballantana tabo, sannan ko'ina na jikina farinsu Waya,in an"

Wauke saman tsokar ™irjina.

Na shige ™wami na zauna dirshen sannan na saki famfunan dukkan biyun Waya na zubo da ruwan zafi

"Wayan kuwa na sanyi yake ™wararo min, cikin Wan gaggawa na gama wankana,gudun kada Yarima ya jira"

"ni da yawa, saboda na san shi mutum ne mai son jam'i. Ina fita sanye da rigar wanka,shi kuma yana sallame sallah."

"A zuciyata na ce har ya ™agara. Na Wauki kayana riga da wando,wandon ruwan ba™i ne rigar kuwa mai"

"dogon hannu ce ruwan madara, sannan rigar ba ta wuce ™ugu ba, na fito na zauna gaban madubi na yi"

"gaggawar shafa Wan Wetlips kawai nasa a laSSana, na taje gashin kaina na Waure shi na sakeshi a baya, sai kuwa turaran da na feshe jikina da shi."

"Alkyabbata na zura domin gabatar da sallah, ina isa wajen da na keSe mana domin sallah na ga Yarima"

"ya mi™e, sannan ya ce mini ""Bismillah."" Sai wannan lokacin tunani ya faWo mini cewa nafila ce Yarima ya yi irin waWannan halayyar ta son Addininsa yana ba ni mamaki, saboda ban taSa tunanin yana ma sallah ba, ballantana ya iya ri™e Addininsa da hannu bibbiyu, balle da na je gidan yari na ga irin yanda yake"

"baiwa jama'a wahala, ga mulki har na fitar hankali."

Bayan mun gama ne na ji ya Waga hannu sama yana jero sunayen Allah gaba Wayansu daga nan kuwa na

"ji ya faWa ga addu'ar Allahumma izzal Islama wal Muslimin har ™arshenta, sannan ya rufe da wata addu'a"

"wacce tun ina yarinya na ji ana yi mana ita, abin da ya bani mamaki kuma sai na ji ya rufe da Wayar ma wacce zan ce kowa tun yana yaro ma ya iya ta."

_Rabbana atina fidduniya hasanatan wafil alkhirati hasanatan wa™ina azaban nari._ _Rabbana latuzi™

™ulubana ba ada izhadaitana wahablana min ladin ka rahamatan innaka antal wahab._

"A take na tuna da malamin islamiyyarmu da yake ce mana ana son duk sallah a dinga karanta ta,falalarta"

"Allah kaWai ya san yawansa, sai dai yawan yin ta na kawo arzi™i duniya da lahira."

"Hankalina na ji ya ™ara nutsuwa a kan Yarima,ganinsa yanda yake kula da Addininsa. Muna kammalawa"

ya mi™e ya gabatar mana da sallar isha'i ni dai gaskiya na ji mamaki matu™a a kan yanda na ga Yarima na

"tafiyar da rayuwarsa,in na yi la'akari da yanda yake a baya, mutumin da ko motsi ma baya iya yi sai dai a yi masa."

Bayan kammala addu'armu ne na ga ya tashi ya buWe a™watinsa ni kuwa sai bin shi nake da kallon

"mamaki, wasu kaya na ga ya Wauko da alama dai na mata ne, ya zauna saman gado sannan na ji ya kira ni na tashi na je inda yake, nima na zauna a gefensa."

"""WaWannan kayan nake son ki saka mini su yanzu,zamu fita mu ci abinci a can."""

"Riga ce doguwa har ™asa take, amma sai Wan siririn hannunta, sai kuwa ´ar samanta mai dogon hannu"

"har izuwa wuyan hannunta, dole ta sa na tattare su na matse a tsakanin cinyata,gudun kada su ja ™asa,a cikin banWaki na isa gaban madubin banWakin na tare gashin kaina na Waure shi da Wan mayafin da na gani ma™ale a jikin kayan, na yi murmushi ganin na yi mugun ™yau, abin ka ga kalar jinin kare, sai kuwa"

"dogayen hannuwan rigar, amma ragowar jikinsu kuwa duk jinin kare ne (Maroon colour)."

"Na fito ina murmushi, sannan na yi saurin sakin rigar sai na ga take ta saman tsakanina da Wan leSunta"

"zai kai taku biyu ta cikin ce kawai ke ™wance a daidai ™afafuna. Na isa bakin madubi na zauna domin gyara fuskata, na gyare ta da wata irin hodar da take fitowa da ainihin kalar fatar jikinka,jan baki kuwa kalar kayana na saka, jinin kare kenan,dan in ™arasa zama su turawan har ma gashin ido na saka, gashin"

ya yi tsaye abin gwanin ban sha'awa.

"Girata kuwa sai na goga mata ™arin ba™in jagira, domin ta ™ara fitowa, na Wauki turare

Please Login or Register in order to submit comment