You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sande mu yan iskan yaran nan sun cinye.

Murmushi tayi tace laa kilan su luba najin yunwa yasa suka ci bara na daura mana wani.

Kawai binta nayi da kallo ina fadin Allah na gode ma ka bani Mata kyakkyawa ga hankali kuma

yar karama abinta.

Abincin ta kawo mukaci muka shiga hira anan ne

LADIDI'S POV

Lokacin da ya Kira aunty maryam zai bata rahoto dadi naji a raina Dan dama nice na rigashi da dabara nace masa ya fada Mata abinda luba tayi kar abar yarinya ta tashi ba gwaba kuma AI in ta Sami tarbiyya mu keda riba tunda mu zamu zauna da ita aiko ya dauka shine fa ya fada

Mata.

Wanka nayi na sheka ado kamin na dauko mana abinci tun a kitchen din nasan sun taba danko naji nauyin ya canja hakan yasa na bude na gani murmushi nayi Dan ko gyara kaina zanyi.

Budewa nayi kamr bansan me ya faru ba nace laa kila su luba ne kemin yunwa sukaci bari na daura mana wani abin. Irin kallon da yake bina dashi nasan na burgeshi ne. Wata kwarkwasa nasa har kitchen inajin haushi danko abincin ya biya raina guntun na sude dan yunwa nakeji

saboda kwakulata da mai gidana yayi.

Bread da kwai nayi mana sannan nakai masa na basa abaki daga nan muka shiga hira cikin so

da kauna.

LUBA'S POV

Kuka nasha abina na huce haushi sannan na kwanta bacci ya daukeni ina cikin bacci naji waya na ringing...nana ce dauka nayi tana kuka tana rokon sister Dan Allah kar kice bazaki dawo ba kar abinda akayi miki yasa kiyi zuciya na rikeni da Allah ki dawo kinji sis Dina? Nace naji zanyi tunani na kashe wayan batare da na saurare me zata sake cewa ba.

Message na gani daga uncle aliyu wai

"""yan Mata me yasa ake rangaba min Kira ko bata show din bai isa bane sai kuma an hada da kira? "" tsaki naja na rafka masa Kira aiko yana dauka na fashe da kuka nace abinda kayi ka kyauta dukda cewa ina da laifi Wanda ba da gangan nayi ba... bai dace ka fadawa aunty maryam har kasa tayi min birtsi birtsi da bulala ba, na dauka inada darajar da nafi karfin wulakanci a Wawrinka ashe abin ba haka bane... ok wani abin nayi ma kamata yayi ka kirani ka zaunar dani bawai kayi min cin mutunci ba toh bari kaji indan nace kai nakeso yasa kake min haka toh kaje gaka ga ladidi ni dama akwai wani mai gadi kuma yanaso kawai nice naki"

yarda amma bari kaji ni luba daya daya ka rubuta ka ajiye NA FASA AURENKA! in ga uban

da zai tursasa ni.

AFWAN AFWAN NAYI LATTI YAU AYI MANAGE DA WANNAN GOBE DA WURI ZAKU JINI

INSHA ALLAH.

KAI TSAYA ASHE FA AN BALLO WANI JAGWAL KO? TOH LUBA DE TACE TA FASA KO

SHIN ABIN ZAI YIWA ALIYU DADI? KOKO SABANIN HAKA NE?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

"23rd June,2020."

"[6/23, 3:19 PM] Miss Untichlobanty : [6/23, 3:10 PM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYIMIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

*CHAPTER 20*

AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....

*Not edited*

"AishaIsmail625 , aysherahmaddanlami, wannan shafin naku ne Allah yabar kauna"

ALIYU'S POV

Bayan na fito masallati ne nayi ma luba message saboda dazu naga kiranta ina tare da ladidi kamin na shige masallati ina fitowa kiranta ya shigo ina dagawa cikin murmushi zan tsokaneta Dan na dauka ma hakuri zata bani na kuskuren sa tayi sannan tamin godiya na gyaran da nasa

akayi Mata banci mutunci ta gaban ladidi ba kawai sai naji sabanin haka.

Ta inda take shiga ba tanan take fita ba Abu kamar wasa sai na bude baki zanyi magana sai naji ta daura magana. Jikina ne yayi sanyi Dan ban kyauta Mata ba amma ni ba da wata niya nayi ba banaso naci mutuncinta gaban ladidi yasa na gasata da aunty maryam tayi Mata

magana ta Mata toh menene kuma na duka.

Tunani na ya datse sanda tace ta fasa auren kuma zata bawa me gadi dama a raina nace masha Allah dama nasan yarinta ke damunta amma dakata! Ta fasa aure na saboda me gadi? Me take nufi wato ya fini ko me ? Toh dukda banason ta saina AURETA ba ita uwar taurin kai ba? Ko me akayi in bataso ta tada bori? Toh AI in tasan wata batasan wata ba zan AURETA

dan in kure taurin kan muga abinda zatayi.

Kiran wayar nayi taki ta daga daga baya ma naji switched off. Gida na shiga abina ina shirya

bomb din da zan Mata Dan jira zanyi ladidi ta Dan shekara sai nasa luba ma daga ciki.

Ya Allah ka jarabce ni da rasa Mata na nayi kuma karbi kaddarata ya Allah na rokeka saboda

tawakkalin da nayi kar ka kashemin wadannan kar ka rabani dasu. Shafawa nayi kamin nabar kofan masallatin.

LUBA'S POV

Ummi na samu nace Mata ummi nifa wallahi azo a sake zama na fasa auren uncle aliyu bige min baki tayi tace sannu shashasha kawai Dan yabaki haushi sai akace ki fasa aure? Haka zakiyi bayan auren da an bata miki rai kice sake ki? Zama nayi a kasa Wanda ummi tasan abinda zai biyo shine bori tace toh karma ki fara kinga yanzu SS3 kike ki rufe ido kiyi karatu kina

gamawa lokacin kin kusa shekaru 17 ayi miki aurenki.

Bori na fara nifa Allah in aliyu za a aurenin yasin ko karatun bazaiyi ba. Ummi tace subhanallah yau ko uncle din babu ? Kuma da kike batun bazakiyi karatu ba wa jahilci zai kashe ? Ki auri aliyun ki a gidansa sai kiyi university ko ya kikace. Mikewa nayi nace toh ai sai muga yadda zan aureshi ni dama can nasan ba sona ake a gidannan ba. A fito a fadamin ko tsintata akayi yasa

za'amin auren dole.

Bulala ummi ta dauko ta biyoni zonan yar banza in dauki cikinki wata 9 harda sati 2 awanni 13 nayi ina nakudar ki shine zakice tsintar ki akayi toh sai kin auri aliyun tukunna ma in baki aureshi ba wa zaki aura? Manna Mata nayi ta bankado labulen dakina ta shigo Luna wai

meke damunki ne? meyasa kikeson bamu ciwon kai? Me yasa kikeson maida daddynki karamin

mutum?

Maganarnan an gamata ke da kanki kikace a aura miki aliyu yanzu kice kin fasa? Ki bari idan kin huce ki sake tunani ... turo baki nayi nace nide acewa abba na na fasa. Toh ai shikenan. Abinda ta fada kenan kamin ta sauke ajiyar zuciya ta fice.

Da daddare ummi ta samu daddy ta fada masa kamin ta karashe ya daga Mata hannu yace kiramin yarinyar. Kwala min Kira tayi na shigo parlourn ina wani mika da hamma daddy yace in baki warware ba zan ware ki da Mari tsam na mutsu na zauna yace wani shiririta nakeji wai kin

fasa aure?

Nace nifa daddy ba aure na fasa ba uncle aliyun ne banaso! Ke dalla rufemin baki lokacin da mukayi justin duniya ki hakura burus kikayi mana kikace sai shi yanzu kuma kina wani magana da batada kan gado? Toh bari kiji gara ki sani aure ba fashi. Kuma in bakida hankali ki kawomin

kasa da credit shida gidannan saina ballaki.

"Mikewa nayi na koma daki ina fadin zakusha mamaki, sannan na fada kan gado na sai bacci."

Washe gari da asuba ummi ta tashi zata tasheni sallar asuba taga empty! Ban daki ko ina ta

duba babu ni babu alamata sai ta dauka ko zuciya nayi na tafi gidan aunty maryam toh amma da asuba kuma? Daddy na ta fadawa aka Kira su aunty maryam sukace banzo ba.

Uncle Aliyu aka kira shima yace bai ganni ba nan cikinsu ya duri ruwa aka fara cigiya ta a

unguwa amma babu alamata.

Abinda ya faru kuwa shine tun da magrib ina waya da nana nake fada Mata nifa idan aka ki yarda guduwa zanyi tace yayi mutuniyata toh amma in kin gudu ina zakije? Nace nima ban sani

ba. Maama tace toh me zai hana tazo nan ba tare da sanin kowa ba sai musa ta a BQ ko ya

kukace mu dinga bata su abinci daga nan.

Nace toh amma masu gadi zasu fada ai nana tace karki damu zan rufe musu baki aiko tunda daddyna bai yadda ba karfe uku nayi sneaking dama already nana ta sanar da masu gadi zuwa na Dan haka suka budemin kofa.

Inaji da safe anata cigiya na dan video call muke da su nana ina ganin komai.

Zama aka Kira da azahar na yadda za'a soma nemana Allah sarki har sun bani tausayi amma nasha alwashin idan ba auren aka fasa ba bazan fito ba. Gidajen radio da talabijin duk an watsa amma shiru babu labarina. Ladidi ko abin ya Mata dadi amma sai ta nuna tafi kowa damuwa.

Harkuka tayi anata bata hakuri ummi ma tasha kuka tace ma daddy na asanar cewa an fasa

auren kila na dawo.

Yace Sam ba'ayi haka ba idan naji ba haza San dawo gida shirme nake yunwa ma kadai ya

isheni ummi tace toh AI garin neman kudin abinci in na fada wani hali fa gashi dama ba hankali gareni ba? Yace a bari nan da sati sai ayi sanarwan.

Su nana kullum tsakar dare suke kawomin ziyara musha hira kuma Allah cikin ikonsa babu wadda ya taba tsammanin ina gidan kamar wasa har sati daya yayi Dan haka yau abbana suka

shirya suka tafi gidan yasa labarai... basusha wahala ba aka basu Dama domin yin magana.

Daddy na yace assalamu alaikum! Nine mahaifin yarinyar nan lubabatu da akayi sanarwa satin daya gaba ta cewa ta bata... luba diyar albarka idan kina jin mu yanzu haka ki dawo gida mun janye batunnan mun fasa. Aliyu ma ya bada nasa jawabin cewa ya fasa Niko tabe baki nayi

nace sai bayan kwana biyu zan fito.

Haka sukayi ta zuba ido suna neman ranta inda zan billo amm shiru. Washe gari ma haka abin ya fara daga musu hankali sosai toh kode na mutu ne? Da daddare ne su nana suka hadani da

Allah cewa na fito kullum sai ummi tayi kuka kawai sai na yanke shawarar zan fito gobe.

Washe gari ummi na rashi da safe ta leka daki na yadda ta Saba dukda bata tsammaci gani na ba ta ganni nayi wannan wawar kwanciyan nawa a da kullum make ni take amma yau cikin jin dadi ta rungume ni tana sumbatar goshina. Allah sarki diyata ta dawo lubabatu na uwata in kika

shiga umminki tayi kewarki.

Kureta nayi da ido Dan ta bani tausayi har ta rame nace ummi na kiyi hakuri na saki damuwa

amma babu yadda na iya ne sanda nace muku banason auren kuka dage sai anyi. Tace karki damu an fasa kiyi karatun ki kinji? Toh nace mika sha kuka.

Aka fada wa su aunty maryam an sameni aiko shikenan ban karajin anyi batun auren ba har lokacin WAEC dinmu yayi. A dakin jarabawa ne naji wasu dalibai na hira ta fari tace nifa wallahi ko da aunty kaltume ta rasu naso ni aka aura wa mijin ta gaskiya aliyun nan ya hadu. Ta biyu ne

tace nikam kullum sai kin mana zancen aliyunnan amma ko saninshi bamuyi ba ta fari tace aliyu

mukhtar fa! Ta uku tace wanne shi kenan? Ta biyu tace me me Ablimuk plaza ? Ta farin tace

shidai.

Ta biyun tace wow gaskiya nima naji ance gayen ya hadu ta ukun tace nikam ban sanshi ba. Ta biyun tace dama ance miki shugaban kasa ne da kowa sai ya sanshi? Mtsww ta ukun tace kanku akeji toh dukda ban sanshi ba toh yamin kuma zan Nemo bayani akansa. Ta farkon tace sannu Sara me bakar tak*shi Sato dan ubanki ya fi namu kudi shine zaki wani ce ya miki zaki kwata? Ta biyun tace ku da kuke hauka bakusan matansa 2 ba ? AI daddy naji yana cewa

matansa biyu amma dayan na sirri ne. Kinsan daddy na aminin yayansa ne.

Ta farkon tace ince wancan lubar ance ta sansa? Yayar mamanta ke auren yayansa? Ta biyun tace kwarai nima naji hakan toh mu tambayeta mana. Ta uku tace yarinyar dake da shegen fi'ili ga reni cab a dawo lafiya. Wajena suka zo suka ce sannunki luba take na musu nace sannunku. Sukace wai da gaske kinsan Aliyu mukhtar? Nace na sanshi amma munyi fada ban

kulashi Dan haka inma sako me daku bazan iya kaiwa ba.

Sukace haba yar uwa toh ko numbarshi kya bamu AI ko hannu na mika alamun abani littafi

suka miko min hannunsu Niko na rubuta na cire numbar karshe nace su nemi wannan da kansu. Daidai lokacin aka kawo papers Dan haka babu halin magana.

ALIYU'S POV

Ya ABBA ne ya tisa ni a gaba yace toh aliyu ga luba fa kaga yadda ta kafe yanzu ya kake tunanin za'ayi? Kaga de har gida ta bari akan kar ta aureka an tambayeta inda ta zauna ma tace bazata fada ba kar a kuma cewa za'ayi auren ta rasa wajen buya wadda ke nuna in aka

sake takura Mata zata gudu kuma dai kasan matsayinta.

Ajiyan zuciya na sauke nace AI ya ABBA kuma kunyi gaggawa bai dace sanda takai shekara goma tace ta yarda ayi auren kuka daura a lokacin ba da kun bari ko zuwa yanzu kunga ko ta fasa ba matsala. Uncle ABBA yace toh ka saketa mana tunda bata ma San da auren ba! Nace kai gaskiya bazan iya ba ni bansan yadda zanyi da ita in tazo gidan sai in sanar da ita. Ya

ABBA yace toh kadai yi a hankali kasan kamar me aljanu kar mu sake nemanta mu rasa!

TOH FA NAJI WANI LABARI KO KUNNE NA NE? TOH BARI NA TAKA RAWA ASHE

LUBAR MU MATAR ALIYUN CE MA TOH YANZU DE YA ZA AYI TA YARDA TAJE GIDAN?

"KU BIYONI A NEXT CHAPTER DANJIN YADDA ZA'A KAI LUBA A DABARA, SHI IN ANKAITA"

ZATA ZAUNA KO ZATA ARCE?

IN KUNYI COMMENTS DAYAWA IN BAKU UPDATE IN NAJI SHIRU KUWA TOH SHIKENAN

NIMA ZAKUJI SHIRU

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

"23rd June,2020."

"[6/23, 3:18 PM] Miss Untichlobanty : DAN ALLAH YAN UWA IDAN AKWAI WACCE TAYI COMMENT BAN MATA REPLY KUYI HAKURI BA SHAREKU NAYI BA WASU MESSAGES DIN WAITING SUKE SAKAMIN"

"[6/24, 6:31 PM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYI MIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

*CHAPTER 21*

AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....

*Not edited*

"*MaryamyakuraMuhammad,husnalhakeem, aisha_gidalle da Usumaima3315 wannan shafin"

naku ne Allah yabar kauna.*

LUBA'S POV

Har yau ba'a sake yi min zancen uncle aliyu kuma nima ban koma gidan aunty maryam ba Dan nayi zuciya da gaske gashi har mun gama su WAEC da NECO har JAMB mun yi kuma nayi Dan kokari dukda nana ta fini a JAMB tanada 218 ni kuma 210 Dan haka ummi tace zanje

gidan aunty maryam celebration.

Nace babu Inda zani ta buga ta raya nace bazan fa je ko ina ba tace toh AI shikenan kinyi wa

kanki dama wata gagarumar kyauta za'ayi miki wadda zai MATUKAR baki mamaki amma tunda

bakyaso shikenan da sauri nace bari na shirya ina mikewa rikeni tayi tace ai ba yau bane sai

ranan asabar yanzu dai gyara zamuyi. Nace gyara kuma sai kace me shirin yin aure ?

Tace banda abinki keda za'ayi taro ayi su hotuna ai kune idon kowa zai zama akai Dan Haka dole ayi gyara. Nace kuma haka ne. Aiko ummi kullum sai tayi min gyara ga bakin shayi da take

bani wai na kara kwarjini ne bansan tsimi take tace min ba!

Nide cikin jin dadi da kaguwa nake cewa ummi kidan fada min menene kyautar tace wannan

kyautar zai canja rayuwar ki baki daya. Tsalle na soma Dan ni na dauka burina na hada kayan gyaran jiki ne zai cika ashe de akwai lauje cikin nadi.

Ranar juma'a ne aka Nemo mai lalle da kitso suka baza min abina sai walwala nake ina tunanin yadda hankalin kowa zai dawo kaina Dan nasan zanfi nana hadewa. Dukda bawai kyashi make

Mata ko wani Abu ba.

Aiko washe gari gidan mu da gidan aunty maryam an cika anata San barka da sa alkhairi gefe

naja ummi nace wai ya naji ana Allah yasa alkhairi yasa a dore.

Tace Allah yasa ALKHAIRI wa sakamakonki mana sannan yasa iliminki da kwazo ya dore nace

aiho masu cewa Allah yasa gidan ta ne fa? Tace ah ah ke bakyaso alkhairi ya zama gidanki?Nace inaso mana yadda sukeyi ne kamar aure akayi min.

Dariya tayi tace sai kace yar tsana ki shirya maza daddynki zaiyi magana dake. Dakinsa na

wuce yayinda ummi ta sake jaddada wa matan kar a kuskura a kirani amarya Dan surprise akeso Amin suka amsa da ba matsala.

Daddy na yamin wa'azi sosai akan rayuwa har na danyi kuka nace daddy wai ya kake magana kamar zamu rabu ne yace ai zaki tafi jami'a ki hadu da mutane iri iri kuma kinga yanzu kin girma kinyi shekaru 16 sure ko wani lokaci Dan haka ki natsu kinji diyar albarka ? Toh nace na

rungumeshi daga nan muka wuce gidan aunty maryam.

Hotuna mukasha dukda matan basuda yawa duka da na gidan mu da gidan aunty maryam basufi su 100 ba ai kuwa ba'a damu da yi. Hoto da nana ba kamar itama ba graduation tayi ba

har naji ba dadi.

Har na gaji Dan inata tsimayin sanda za'a bani kyauta ta na aunty maryam da iya hajjo ne kawai suka riko hannuna sukace muje nace ba tare da ummi za'a nuna min kyautar ba? Aunty maryam tace ai ita tana can ta rigamu zuwa ashe duk sani ake a kwano ummi tana gida babu

inda taje.

Daure min ido akayi da muka shiga mota sukace so suke ayi min surprise da yake nasan aunty maryam wayaiyace shiyasa ban daura ayan tambaya ba ni duk na kagu naga menene ake ja

min rai.

Tsayawa akayi na washe baki Dan nasan an iso kofofi naji ana shiga dani har AC mai dadi ya dakeni. Zaunar dani akayi na bude idon nagan my a wani daki dai dai misali mai mugun kyau

komai na dakin blue ne yadda nakeso.

Dukda ban gane ba neme neme na fara da ido ina neman kyautar amma na tsaya sanda naga

katan leda a gefena. Budewa nayi naga katan ciye ciye ne. Aunty maryam tace maza kici abinki kinji yanzu zamuje mu dauko kyautar. Ina lashe hannu nace uhm Dan magana bazai samu ba.

Fita sukayi nikam naci gaba da ciye ciye da hannu bibbiyu ina jinjina kai kamar wata

kadangaruwa.

ALIYU'S POV

Tunda na fadi plan din kowa ya yarda amma toh yadda zan zaunar da luba bayan an kaita shine

matsalar. Sanda su aunty maryam suka fito daga side dinta kuma side Dina na da.

Sukace toh aliyu mu mun gama namu ga luba de an kawo ma ka rike amana kaji ko? Sannan ka bita a hankali don Allah. Aunty maryam tace kai hajjo kiji da wani zance yarinyar ko tsarki ma

batada shi. Hajjo tace AI zata samu... ratan dai kaji ni ko?

Sosa kai nayi a raina nace ni dama babu abinda zanyi Mata kawai so nake na nuna Mata batafi

karfinmu ba yayinda a zahiri nace insha Allah.

Suna fita na kafta Mata sakata na wuce dakin ladidi abina Dan nasan yanzu haka luban tayi bacci Dan kayan ciye ciyen nan ba haka kawai nabar su kazar ba. Kuma kan ta tashi sai an

jima.

A gida kuwa duk an watse su ABBA ana fatan zaman ya dore Dan sun tsorata da luba zuwa yanzu saide addu'a.

Washe gari da safe ba duba ta aiko ta bingire hannunta dama dama da abinci. Karba nayi na ajiye na cire alewar dake bakinta na gyara Mata kwanciya ina ja Mata kumatu kamin na fita

abina.

LUBA'S POV

Ina tashi naji kaina na ciwo sosai nayi mika har zan sauko ba tuna banyi addu'a ba nayi kamin na sauka sai lokacin na fara tunanin ina kyauta ta kuma me yasa na kwana anan ? Fita nayi nagan ni a parlour komai fari kalle kalle nayi kamin na bude wata kofa kitchen ne turo baki nayi

Dan kofar fita nake nema.

Sunan aunty maryam na fara Kira ina bude wata kofa ban daki ne sai wani daki daya kofar da

nake tunanin na fita ne toh shi a kulle Kira nayi amma kowa wayar sa a kashe. Na uncle aliyu

na Kira Dan zuwa yanzu na fara tunanin ko saida ni akayi.

Dagawa yayi yana fadin wow I am honored yau her royal highness luba da kanta ke kirana. Toh sarauniya me zan miki? Cikin Muryan kuka nace uncle aliyu an sace ni kazo ka taimake ni yace

yimin bayanin me ya faru...

Nace kawai ni da su aunty maryam munzo wani gida na fara ciye ciye su kuma suka tafi dauko

min kyauta ta daga nan basu dawo ba kuma nima ban sake sanin komai ba sai yanzu na tashi.

Kode bigesu akayi aka dauresu? Yace karki damu your savior is here kawai sai aka bude kofar.

ALIYU'S POV

Ina zaune muna cin abinci ni da ladidi wacce itama batasan luba tana gidannan ba nace yau abinci Dan kadan zata sakamin sauran zanci anjima tace toh. Wayata ne tayi haske dama tana silent Dan haka nace kawo sauran ki gani bari in adana a dakina. Ba karba sannan na nufi

bangare na Wanda ladidi bata shiga in ba Dan tayi shara ba saboda a bangaren ta nake zama.

Bata zargi komai ba ta bani na wuce ina fadin yanzu zan dawo yayinda ta soma cin abincin ta. Dauka nayi cikin tsokana nace wow ! I am honored yau her royal highness luba da kanta ke kirana. Toh sarauniya me zan miki? Cikin Muryan kuka tace uncle aliyu an sace ni kazo ka

taimake ni nace yimin bayanin me ya faru...

Cikin muryar tsoro da alamu kuka take yanzu kam tace kawai ni da su aunty maryam munzo

wani gida na fara ciye ciye su kuma suka tafi dauko min kyauta ta daga nan basu dawo ba kuma nima ban sake sanin komai ba sai yanzu na tashi.

Kode bigesu aka yi aka daure su? Dariya ke cina da alamu yarinyar nan ta kalli cartoon dayawa shiyasa bata da wayo cikin murmushi nace karki damu your savior is here ina mai bude kofar side din juyowa tayi da sauri ta saki wayar ta rungume ni kamar rayuwata na jiki na sai karkarwa

take ta hada gumi dukda ko akwai AC a kunne.

Abinda na soma ji tattare da ita a karo na farko tun rana yarinya naji saboda ban sake raba ta da jikina ba tun yarintar ta iyaka mu gaisa da hannu ko na shafa kanta ko kuma naja Mata kumatu. Tsimi tsimi nayi ina zare ido kamar mara gaskiya amma sai na shafa kanta nima muryata na rawa nace luba karki damu babu Wanda ya saceki a cikin gida na kike kuma ko

ladidi bata sani ba....

So ake a aura miki wannan me gadin shine ni da aunty maryam da hajjo muka hada baki cewa a Sato ki a boyeki a gidana kinga sai a dauka kin bata sai an fasa sai ki koma gida Dan haka banda aunty maryam ko ummi kar Kira sai kin fada min sannan ki dinga saka wayar ki a plane

mood sai zakiyi chatting ne kawai zaki cire sannan ki rufe su last seen dinki.

Banda posting status banda fita waje idan ba haka ba kuwa a gano inda kike karki bari ladidi ma ta ganki. Tace kutma. Sai kace Kurkuku gaskiya bazai sabu ba! Tureni zatayi ta wuce nace kin shirya auren me gadi kenan? Matansa uku fa kuma kinsan masu gadin nan suna shaye shaye

kuma duk Dan shaye shaye yana amalala.

Da sauri ta dawo tace zan zauna kuma zanbi doka nace yauwa kinga ni banason daukan risk ma zan sayo miki sabon waya nasa miki sim sai ki dinga social media dinki amma banda WhatsApp wancan wayar sai ki kashe ta in zakiyi waya da aunty maryam kiyi ta wayata Gyada

kai tayi tana zazzare ido Dan taji batun fitsarin kwance.

Abincin na mika Mata nace zan dinga kawo miki abinci na sati daya kamin na gyara kitchen din

Please Login or Register in order to submit comment