You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nifa Allah bana son komawa ni dakai nakeson zama... saboda

kafi min su Kaine ka nuna min gsky tun ina karama kuma ka soni su kuwa banda......

Da sauri ya toshe Mata baki yace kul luba wadannan fa iyayenki ne koda ni bai zama dole na musu biyaiya ba ke wajibi ne kuma kuskure kowa yana yinta nima nayi har sau biyu ban tsawatar miki da wuri ba na barki kina nema ki tsoma kaina a ruwa sannan na kuma yadda aka boye auren mu Wanda na tabbata kaunar da nake miki ne ya janyo min yin wannan sukacin

saide har yau abinda na kasa ganewa shine yadda akayi na fara son yarinya...

Ji yayi ta rungumesa tana kuka tace uncle maimata. Yace me? Tace abinda ka fada dazu da gaske kana kaunata? Murmushi yayi yace sosai kuwa luba ban gano hakan ba sai randa baki kwana a kirji na ba kika kwana a wani waje ranan da aka kashe mana jinin mu kuma ake ma

soyaiyar mu barazana. Kuskure na na uku shine da ban taba fada miki ina kaunarki ba.

Lubabatu...ni Aliyu bala bakabe ina matukar sonki kuma kaunar ki ya ratsa jinina saide inaso ki sani.... San kara aure.... da sauri ta zabura saboda yadda gabanta ya fadi... shi kuwa ko a jikinshi yace inde har Allah zai halittu min wata Wanda tayi daidai da ke zan aura amma in bani

watan ki ke daya ce a duniya toh dake zan zauna.

Ajiya zuciya ta sauke tana duka kirjinsa cikin wasa tace har ka bani tsoro wallahi kamar hanji na zai zazzago. Dariya yayi yace Allah uwar yayana harda hawaye ya fadi haka yana goge Mata

hawayen.

"Tafiya sukayi suna isa asibitin yakaita wajen likitanta bayan sun gaisa yace likita dama batun matata ne tace tunda wannan abin ya faru bata fane meke Mata dadi ba takanji ciwon mara, sannan bata iya zama a inda babu iska. Luba tace kuma ni daya sai inji inason nayi kuka"

sannan wani lokacin haka kawai ana cikin zama sai na fara bacci.

Dan murmusawa aliyu yayi saboda ya tuna yadda takeyi ne sanda taje da ciki bai sani ba kawai ita daya sai tahau bacci. Akwai ranan da ta shiga ban daki bayan sun raya sunna tace zatayi fitsari kamin nan shi ya cire bedsheet shiru shiru bata gama ba yace zan shigo ba shiru dama kullum yakan tsokaneta tare zasuyi wankan amma sai ta dage bazai shigo bayin ba.

Yana budewa yaga ta baje akan shadda tana baccinta harda yawun bacci.

Har ya gama tunanin sa luba tanata Jerowa likita abinda takeji ita dai dr murmushi kawai takeyi sanda taga abin ba karau bane tace toh naji daga nan AI ko baki min bayani ba nasan me ke

damunki.

Kallon aliyu tayi tace ka tuna lokacin da na sanar dakai matarka ta rasa cikinta? Yace sosai

kuwa likita har haushi kika bani saboda yadda kike wannan murmushin taki Dan dariya tayi tace toh fa baro baro haka zaka fada min? Toh shikenan yanzu ko zan birge ka.

Abinda baka sani ba matar ka tana dauke da cikin yan 4 ne zaro ido aliyu yayi yace ban gane ba Dana yara 4 na rasa ? wallahi ladidi kin shiga uku. Tace tsaya mana lokacin da kishiyar ta ta jefeta guda daya ne ya fita sauran yaransu uku suna nan kuma yanzu haka watan su uku harda

kwanaki idan kunaso zamu iya yi muku ultra sound da pregnancy scan domon kuga hotansu.

Abinda yasa na boye muku kuwa shine idan kun sani zakuyi ta ritita cikin Wanda zai janyo a

sake kai masa wani farmaki sai nayi shiru sai ya Dan kara kwari amma nayi mamaki da baka gane ba domin ko yanzu ka taba zakaji taurin su.

Yace tabbas sanda take da cikin jikina ya bani dukda ban tabbatar ba kuma wannan ne karo na

farko da aka dauki cikina. Bayan kin sanar damu cewa babu cikin na lura cikin ya Dan taso ma amma sai nayi tunanin ko kibar da tayi ne ya kawo Mata tumbi ashe de.

Rungume luba yayi yana zura hannu cikin riganta ya shafa cikin ita kam kuka ma take sharara masa don farin ciki ta kasa cewa komai har sanda tasa likitan yin kuka. Tace toh muje a dauka mana hotan likita waiyo dadi Allah na a tare sukace Alhamdulillah suna mikewa domin a nuna

musu jariran su.

ья

LUBA

ья

ALIYU

ья

A gida kuwa yan sanda sune gidan uncle abba sukayi musu tambaya dama yanzu ummi a

gidan suke yini sai dare suke komawa gida asuba tana yi su sake dawowa.

Bayan an gama musu ne aka nemi ganin luba domin ayi Mata tambaya akaji wayam an neme ta sama ko kasa babu ita babu labarin ta. Anan ne aunty maryam tace ba shakka fita tayi ta tafi

wajen yaron nan. Nace kaji aunty maryam da karfin hali shekara 3 fa kika basa.

Su luba ko tun a mota sukace tunda akwai ciki yanzu kam dole a barsu inma wabi auren ne a

sake daurawa babu me rabasu ko anki ko anso.

Aliyu ne yace ta zauna a mota ya bude Mata window yayi locking yace zai shiga ya fara magana dasu kar a kawo ma yaransa lahani komi rintsi kar ta fito. Da murmushin sa ya shiga hannunsa dauke da hoton yaran su. Yana shiga yaji shar aunty maryam ta kwasheshi da Mari....

ummi ta dada masa wani uncle ABBA ya bada biyu lafiyaiyu daddy ma ya sauke mai yan

sandan ne suka rikesu da sauri sukace ya haka? Ya zaku sashi a gaba da duka babu dalili.

Suna hada ido da Dan sandan yace nazifi ? Inspector yace malam Ali? Dama wai duk wannan zancen kai ake nufi? Musabaha sukayi su uncle abba sukayi sakoko ummi harda rike haba.

Zama sukayi uncle ABBA yace inspector ya naga kaji sanyi haka ? Kamashi fa zakuyi muma

nan zamu kai karar sa yayi zina da yar mu yana Mata karyan ya AURETA harda dirka Mata ciki.

Inspector yace tabbas nasan malam Ali shekaru biyar kenan da suka wuce shine ya ceci diyata da matata ba'a keta musu haddi ba domin lokacin an harbeni bana hayyaci na ma.

Daddy yace mutum na iya canjawa wancan alin da wannan da banbanci.

Aunty maryam tace ita wancan hamshakiya gwamma uwar matar Zamu samu ganinta ko sai mun yanki ticket mun cika form? Wayansa ya dauko ya Kira dayan layinsa Wanda ya bari a

mota Dan kar a gane ya bata waya yace ta shigo amma tayi a hankali don Allah yaransa.

Tana zuwa bakin kofar da sauri ya taro ta yana sannu sannu ko baby? Ina ke miki zafi? Tafiyar nan da kikayi bai miki wani illa ba ko? Ummi ta fashe da kuka tace kaji shi ko inspector ance

masa cikin ma ya zube amma bai yarda ba wallahi bashida kunya ko kadan.

Kallonta inspector nazifi yayi yace wannan yarinyar AI nasanta karde kuce min ita ce lubabatu? Tabbas randa kayi min taimako wannan yarinya kuma tare lokacin bazata wuce shekaru 14 ba ko? Aliyu yace girman jikina shekarunta 11 a lokacin. Yauwa inspector AI na fada ma nace lokacin shekarar mu daya aure washe garin Ranan sanda nazo Dubai a hospital ka tuna har ka

bani shawarwarin rayuwa amma Dana koma bayan kwana 5 ban same ku ba?

Shiru inspector yayi yace gaskiya kayi hakuri malam aliyu nasan de munyi maganganu amma gsky bazan iya tuna me mukace ba. Yace ka gani ko? Kowa zai tuna komai amma da anzo batun aurena da uwar 'ya'ya na toh lokacin ne aka manta ko ace min be faru ba ma. Me kuke nufi da ni ne? Duba kalli ku gani Allah ya albarkace mu da yara har uku ya fada yana nuna

musu hotan.

Dafe kirji aunty maryam tayi tace tace ke suwaiba(ummi) mun banu mun lalace ya kuma dirka Mata wani. Hayaiyakowa tayi zata cafko luba da ta makale a jikin aliyu. Ya aiko Mata wani kallo batasan sanda ta koma ta zauna ba tana huci. Dauke kai tayi tace inspector ko zan iya sanin

dalilin zuwanku?

Dagowa inspector yayi yace munzo ne muyi arresting dinka......

WAIYO KIRJINA HAR WANI FAFAT YAKE YI... YANZU KARDE TAFIYA ZA'AYI

DASHIABAR LUBA A HANNUN SU AUNTY MARYAM?!

GASKIYA DOLE NAYI WANI ABU BAZAN ZAUNA INA GANI A BARAR MANA DA TRIPLETS

DINMU BA DAYAN MA YAYI ALLAH YA TSARE NA GABA!

AYI COMMENT KO NA KUMA ZUBAR DA BIYU DAN NAGA KWANA BIYU BACCI KUKEYI

BAKWASON YIN COMMENT KUMA DE KUNSAN NA IYA YAJIN AIKI

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

"10 July,2020."

8 -

"[7/12, 5:17 AM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYI MIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

WHATSAPP: 08146448881

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

*CHAPTER 34*

*AFWAN FOR THE TYPING ERRORS ... *

*Not edited*

inspector yayi yace munzo ne muyi arresting dinka ne amma idan nayi haka ban ma hallacci ba zan haka zan cika maka takardan beli amma fa saide kayi hakuri an Riga an shigar dakai kotu Dan haka dole ne kaje saide zanyi kokari na nema maka lawyer murmushi aliyu yayi yace

karka damu hakan ma na gode.

Fita sukayi aliyu ya mara musu baya yana sake yi ma inspector godiya dafa kafadarsa yayi yace AI kayi min hallacci dukda cewa abinda nayi yanzu bai dace ba na hada aiki da personal life Dina toh amma kuma ka ceci citizens of Nigeria dan haka da wannan zan daga maka kafa

amma yanzu dole muje dakai ka bamu statement dinka.

Luba kuwa lungu ta samu ta takura ta rike hotan yayanta Sato ma babu Wanda zai tayata farin ciki Allah ya azurtata da samun da tunowa da cewa zasu iya kawo Mata wargi yasa ta sidade

jiki ta shige dakinta ta ranbatsa mukulli tayi kwanciyarta anan bacci ya dauketa bayan ta shanye

ice cream.

.......

Bokan ladidi ne zaune ya rantaba uban tagumi yana karanta wasikar jaki bayan ya saurari bayanin da aljanin da zai gyara uhm uhm din aliyu saboda ya samu sun shirya. Yace yanzu aljani matuidi babu yadda za'ayi ka gyara aikin? Matuidi yace na fada maka tunda ya shiga

matsala ya kama addu'a gam ya rike ni ko unguwar da yake naje sai gabana ya fadi.

Boka yace toh jeka zan tattauna da aljani zatsiwit ...boka yace zatsiwit nina mini halin da ake ciki

da batun yaron nan Ali dan ban taba yin aikin da nake nadama sai tasa. Nuna masa yayi boka yace zatsiwit........

Ni ban gane sauran me yace masa ba saboda wani yaren su da ya soma amma de kamin mu

wuce gaba ina da magana.

"Akwai wasu mutane, normally kawai zasuyi su sallah da sauransu amma da sun shiga matsala toh lokacin za'a tuna Allah sune azumi, zikirin nan kamar bakinsu zai fita. Sallar nafilan nan ma ayi ta yi har sai kai yayi ciwo daga sauki yazo kwana daya, biyu sai a watsar toh de ku sani"

manzon Allah yace:

"""Ku tuna da Allah a yayinda kuke cikin jin dadi shi kuma zai tuna daku a yayin da kuka shiga"

"tsanani"" tirmidhi be ya rawaito."

Allah ya sake cewa:

" Therefore remember Me (by praying, glorifying), I will remember you, and be grateful to Me (for My countless Favors on you) and never be ungrateful to Me. Quran (2:152)"

"""Ku tuna, ni zan tuna ku. Sannan ku kasance masu godiya a gareni kuma kar ku kasance masu"

"butulci "" Quran (2:152)"

Toh a gaskiyan lamari ba sai na tsawaita ba nasan dayawa daga cikin ku sai duniya ta dau zafi ta muku atishawar tsiya in akayi rashin sa'a ma ta muku bugun shinkafar year shafi'u tukun ake

koma ga Allah toh gaskiya mu gyara yan uwa wannan Sam bai dace ba.

Wasu haka bazaka taba sanin sun iya sa hijab ba sai da RAMADAN a dauki sallama za'a tafi masallati bararam ana tafe ana surutu wai zuwa masallatin ma kuma sai a mayar dashi gasa. Har ana duba hijab din wace yafi kyau da tsada... can you imagine wata fa bama sallah da jin wa'azi taje ba taje ne de kawai ta bawa idonta abinci ko ta hadu da samari toh kuwa asara ta

sameki kinji kunya.

Abin haushin matan auren ma ba'a tsira ba wata ana sallah tana duba kasar ganinki wai taga ko

holland ko wax? Me tauraro ok babu idan ma akwai na wace wata ce kaji min kayan takaici.

Haka kuma mazannan zakuyi ta bin yan Mata da mujiya ana duba yar lukuta da siririya toh gaskiya ya kamata mu Mike musan me muke yi musan ya kamata.. you didn't come to this

world to waste your time and return to you lord with nothing to show.

NAJI ANA JITA JITA WAI ANA SAYAR MA MUTANE DA LITTAFI WHATSOEVER NIDE NAWA

BA NA KUDI BANE IN WANI YAR KARBI KUDINKI TOH KI KARBI ABINKI YAR UWA SHIYASA NA BADA HANYOYIN DA ZAKI SAMENI A SAMA DOMIN MU GAISA DA DAI SAURANSU.

Ban garen ladidi kuwa sai washe gari ta farka inda ta koma yar tatata luku kawai take ita

batasan me tayi ba yanzu duk wannan wulakancin Dan ta zubar da cikin shege ne ake yi Mata shi? A dake ka a hanaka kuka.

Aliyu kama direct wajen Samir ya tafi bayan ya tashi a police station da sallamar sa ya shiga ya

samu shida mamansa suns parlour gaisawa sukayi kamin aliyu yaja shi suka fice.

Samir yace aliyu ya akayi ne? Ajiyar zuciya ya sauke yace mutumi na batun nan ce de ta aure na da luba nikam dama na sanar dakai na tabbata bazaka manta ba. Samir yace dude na yarda dakai yanzu ya ake ciki? Aliyu yace banda wannan batun kasan na fada ma shirmen da nayi akan matar nan ladidi toh shine fa yanzu zamu shiga kotu tunda kaga kai lafiya ne me zai hana

ka kare ni.

Samir yace aiko baka fada ba indai naji batun case din dole na nemeka yanzu de menene

charges din ? Aliyos yace toh da fari de wai domestic violence and rape ne yanzu kuma an kara

min da adultery.

Samir yace innalillah wa inna ilaihi raji'un gaskiya aboki na bazan maka karya ba kana cikin matsala dukda cewa kotun naga ba Shari'a court bane amma ko a haka fa dauri shekara 2 ne fa

laifin zina kawai. Toh kuma ga rape.

"Wanda in section 358 of the criminal code, it states that  any person who commits the offence of rape is liable to imprisonment for life, with or without canning "

Wato duk wani mutumi Wanda ya aikata FYADE toh hukuncinsa daurin rai da rai ne ko da tara

ko babu.

Aliyu yace AI inada gaskiya ta kuma cire Mata da hakori da nayi ni jinina ta kashe min nasan

Allah yana tare dani... innallaha ma'ana.

Zuwa yanzu kowa ya fice daga sabar su aliyu Dan gani suke bata lokaci suke kuma babu me

basu haushi kamar luba saide har yau sunki bari aliyu ya tafi da ita. Sati na kewayo wa aja nufi kotu.

Ana zaune har alkali ya shigo suka Mike bayan ya zauna suka zauna nana tana shafa bayan luba alamun rarrashi. Dan sanda ne ya rako aliyos har inda zai tsaya bayan anyi introducing

case.

Alkali yace ina lauyan me kara? Lauyan ladidi ne ta mike Wanda yan human right ne suka tsaya Mata tace sunana hindatu Bashir nice mai wakiltar wadda take kara. Alkali yace ina lauyan Wanda ake kara? Samir ya Mike cikin harshen turanci yace ya mai girma mai Shari'a sunana

Samir Abduljalal nine Wanda nake kare Wanda ake kara.

"Alkali yace zamu fara da fyaden da kayiwa matarka, fyade na cin mutunci."

Hindatu tace ya mai Shari'a zanso nayi wa malam aliyu tambaya.

Mai Shari'a yace go on. Tace malam aliyu ko zan iya sanin inda kake sati biyu kamin faduwar abun? yace ina asubiti ne lokacin. Tace shin ko mene dalilin da yasa aka kamaka a asibiti? Yace heart attack ne ya kamani tace ko me yasa heart attack ya kamaka? Samir ne yace objection my lord lauyen me kara tana kokarin tunowa client Dina abinda ya janyo ciwon zuciya

ta kama Wanda zai iya tashi masa.

Alkali yace korafi bai karbi ba gaban luba ne ya tsinke har a cikin cikinta taji ace an fara case da gwalesu innalillah. Lauya tace malam Ali kai Mike sauraro yace saboda a ranan ne aka rabani da matata uwar yaya na. Tace toh AI duniya bata sanka da wata Mata ba face ladidi kuma a iya

sanin duniya babu Wanda ya rabaku. Aliyu yace MATATA LUBABATU ADAM NAKE NUFI!

TOH A SUBURBUDO COMMENT IDAN BA HAKA BA BAZAKU JINI BA SAI JIBI.

TOH GASHINAN DAI AN SHIGA KOTU KO YA ZATA KAYA?

BOKA DE YA SAMU TALABIJIN YANA HANGO YADDA RAYUWAR SU ALIYU KE TAFIYA...

SHIN KUNA TUNANIN ME NAKE TUNANI?

BARI NAGA DA YAN WATTPAD DA FACEBOOK DA WHATSAPP KO SU WAYE SUKA FI SO

NA? BARI MU GANI

A BIYO NI DAN JIN YADDA ZA'A KAYA. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

"12th July,2020."

Yauwa kuma a mance da VOTE nayi fushi abi na.

"[7/13, 3:56 PM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYI MIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

WHATSAPP: 08146448881

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

"*Maryam Muhammad, fatemah bintu,Maman musa, maman areef, maman khairat,maman"

jannert da maman da maman dukanku wannan page din naku ne. Allah yabar kauna!d'*

*CHAPTER 35*

*AFWAN FOR THE TYPING ERRORS ... *

*Not edited*

Lauya ne tace malam Ali ko zaka iya sanar da kotu randa ka kara aure? Yace tun bayan ladidi ban sake aure ba. Lauya Hindatu tace amma kace mana matarka mu kuma ladidi kukasan ka aura yace eh sanda na auri lubabatu kamin na auri ladidi. Hindatu tace amma toh me yasa ka

fara zama da ladidi kamin lubabatu?

Yace saboda tana karama lokacin da na AURETA. Hindatu tace ko shin kanada sheda? Shiru yayi tace babu kenan ? Yace akwai ya dago yana kallon idon luba kamin ya dauke Wanda hada

idon da sukayi sako ya isar mata.

Lauya tace zan iya ganin su yace na farko Allah ne na biyu kuwa ita matar tawa na uku kuma aminina. A ransa ko fadi yake Allah ka gani matata ce amma shedun duk sun manta Dan haka

babu wani Abu dazanyi saide na bada shedun karya.

Tace ya mai Shari'a zanso ganin shedun daya ambata in an bani dama. Judge yace an baki

dama. Kiran luba aka fara tazo ta tsaya.

Hindatu tace baiwar Allah ko zamu iya saninki? Goge hawayenta tayi tace nice lubabatu Adam uwar gidan aliyu. Hindatu tace wato kin yarda ke matarsa ce ? Tace kwarai kuwa ya ya sanar

dani a boye tun bankai haka ba amma yace kar na fada ma kowa. Hindatu tace idan karya ce fa yayi miki Dan yaga ke yarinya ce bakida wayo saboda yayi yadda yakeso dake? Luba tace bazai taba yi min karya ba kuma ba jikina yakeso ba domin da jikina yakeso da sanda nakai

masa kaina ina karama bazai kyaleni ba.

Hindatu tace wato kin taba kai masa kanki tun a karama bazanyi mamaki ba idan yanzun ma kaikanki kikayi. Samir ne yace objection my lord lauya hindatu tana kokarin tura magana tare da

yin kazafi ma matar Wanda nake kara judge yace korafi ya karbu lauya hindatu a kiyaye.

Hindatu tace zanso naga aminin nasa my lord yace kotu ta baki dama. Samir ne ya Mike ya

zare hulansa na lauyoyi yaje ya tsaya tace wow I see no kake kare abokinka Akan tabar Gazans da yake aikatawa hularsa ya mayar yace objection my lord lauya hindatu tana kokarin tayi cuwa cuwa ta daure magana ne duk sanda na cire kulata ni ba lauyan sa bane ni aminin sa ne kuma duk sanda na mayar da hulata babu alaka tsakanin dashi illa ta lauya da Wanda yake

karewa.

Alkali yace korafi ta karbu lauya hindatu a kiyaye. Tace mr Samir shin Kaine aminin Wanda ake kara yace eh nine tace ko zaka iya fadamin tun yaushe ka sanshi? Yace tun muna yara muka San juna kuma har yau muna tare. Tace masha Allah abota me kyau! shin da gaske ne abokinka sanda ya fara auran lubabatu kamin ya auri ladidi? tace tabbas wannan babu shakka. Tace toh ko kana wajen sanda aka daura ? Tsarewa yayi kunsan lauya da iya kwantara karya yace tabbas nine ma na karba masa auren a wajen mahaifinta. Daddy ne ya Mike yace karya

kakeyi munafiki samiru ashe kaima ka lalace?

"Alkali yace order order a saura a saura nan ba kasuwa bace ko dandalin yan siyasa. Zama daddy yayi, hindatu tace toh malam Samir mahaifin yarinya yace karya kake ko kanada abin cewa ? Yace ya cadets ne a mazauninsa dan haka wannan bata cikin abinda za'ayi considering."

Sannan kuma inada sheda dazai tabbatar da an daura auren ranar haihuwar ta ne.

Hindatu tace oh really toh bismillah yace bazan iya aikata hakan ba har sai kin sallame ni na mayar da hulata lokacin na zama lauya kuma zan kare client Dina. Tace ya mai girma mai Shari'a da wannan tambayoyi da nayi da kuma yadda mahaifin yarinyar ba ya karyata su domin babu mahaifin da zaiso kashe auren yarda nake cewa kotu tayi gaggawa daure aliyu na laifin zina da yayi sannan kuma a dauresa na FYADE da yayi sanadiyyar ya kasa gabatar da wasu hujja kwarara kuma aci sa tara mai yawa na canja Ma client Dina ladidi halitta da yayi ta hanyar

cire Mata hakora.

Zama tayi bayan an sallami luba itama ta zauna Samir ya mayar da hularsa alkali yace lauyan Wanda ake kara ko kana da wata sheda da zai tabbatar mana da lubabatu matar aliyu ne ba zina yake ba kuma shin ko akwai wata sheda ta kariya da zaku bayar na aika aikar da yayiwa

matar sa?

Projector Samir ya kunna yace ya mai girma mai Shari'a zan haske muku hotunan da suka

dauka ne a ranan da ta cika shekara 10 kuma aka daura auren.

Haskowa ya fara yace ya mai girma mai Shari'a wannan hotan shi da ita minti biyar kamin a daura auren tana kwalliyar birthday dinta duk ta jagwalgwala fuska tayi musu selfie. Hindatu tace ya mai girma mai Shari'a wannan hotan zai iya zama an dauka ne kawai na birthday baiyi

proving komai ba.

Alkali yace ra'ayinki bai karbu ba tunda lauyan bai gama nuna hotunan ba. Samir ya tafi hoto na gaba ina suna zaune ga damin goro da kudi damin naira dari dari. Yace wannan hotan mahaifiyar yarinyar ce ta dauka ga can maryam yayar mahaifiyar a gefe su kuma maza lokacin

ana shirin karbar auren kenan.

Wani hoto na uku ya sake nuna wa yace ga kuma hotansu su dukansu harda cousins dinta nana da mama bayan an daura auren. Hindatu tace karfa ku manta ance ranan haihuwar ta ne Dan haka akwai yuwuwar ayi family picture Samir yace menene hadin ranan haihuwa da goro da kalin cingam tare da sisin gwal?

"Shiru tayi Samir yace ya mai girma mai Shari'a batun FYADE kuma bai aikata FYADE ba domin kuwa shi kansa ba a haiyacin sa yake ba ansa masa kwaya a bin sha Wanda bamusan waye yayi masa hakan ba Ga result nan na jininsa a ranan da abin ya faru ta nuna tabbas akwai kwaya a jininsa kuma a iya sanin duniya,police station har ma da asubiti ba'a taba kamashi da"

shaye shaye ba.

Da wannan nake rokan kotun nan mai albarka da ta wanke mr aliyu daga zargin da ake masa ta

kuma sa bangaren da suka bata masa suna su biyashi tara sannan abar masa matar sa. Alkali

ne yace lauyan me kara ko kinada abin cewa ? Tace zanso gabatar da shaida na mai gadin gidan tare da mai chemist da kuma mahaifin yarinyar.

Alkali yace kotu ta baki dama fitowa sukayi tace bawan Allah zanso sanin ko kai waye yace nine mai gadin gidan malam Ali tace ko zaka iya fada mana abinda ka sani game da shi da kuma matana dake zaune tare da shi? Abinda ya fada ma yan sanda haka ya maimata musu babu ragi babu Kari domin shine iya gaskiyar abinda ya sani kuma ya fahimta. Tace mun gode sannan ta kalli mai chemist tace ko zamu iya sanin ko kai waye? Yace nine malam ubaliyo mai chemist.

Please Login or Register in order to submit comment